Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 14
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 14: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 14. Ƙarasowa tayi daga gabanshi Ta ɗan russina ta…
3,371 words
Ƙarasowa tayi daga gabanshi Ta ɗan russina ta gaishe shi cikin girmamawa, shiru bai tanka mata ba, hakan da yai mata yasa ta fahimci babu lafiya, ba ta ta6a ganin damuwa akan fuskar dattijon ba sai yau, cikin sanyin murya tace"Yalla6ai na duba acikin gida baka nan shiyasa nazo duba ka a garden, fresh fruit ne na kawo maka" tai maganar tare da ɗukawa ta ajiye mashi kayan marmarin.
Da buɗar bakinsa sai cewa yai"Owais Ya dawo gidan nan"! murmushin gefen fuska Hajjaty tasaki"yalla6ai owais Ai baya a ƙasar Ko kamanta ne" yamutsa fuskarshi yai" Oh toh na manta, "har zata miƙe ta kuma cewa"Ko kana buƙatar wani abun ne"? Girgiza mata kai yai"bana son kowa yasan ina a garden"! amsa mashi tayi da toh kafin ta kama hanyar fucewa Kaitsaye ta nufi Entry hall na shiga gidan, Zuciyarta a cunkushe take da tunanin meke damun dattijon? Ta ya ya zata Iya sani? Duk ta damu kanta akanshi saboda Kyautatawar da yake yi masu bazata so ta gan shi a irin wannan yanayin ba.
Adai dai Ƙofar shiga Falon suka ci karo da matashin dake ƙoƙarin fitowa, Dogo siriri bai da ƙiba ko misƙala zarratin, Fari sol dashi daga ganin shi farar fata ne bai haɗa komai da jinsin baƙaƙe ba, Jikinshi na sanye da Kayan likitoci farin wando, Farar shirt daga sama ya ɗaura Lapcoat, Fararen idanuwashi na manne da farin glass, Masha Allah Kyakkyawan gaske, Sumar kanshi har saman wuyanshi,
"Jazz! " yanayin yadda ta ambaci sunanshi ne yasa shi cin burki, Yana kallonta, fuskar shi a ɗaure yace "Me kike buƙata? Allura ko tiyata"? Dariya ta ɗan saki har fararen haƙoranta suka bayyana.
"Kinga sauri nakeyi Yanzu aka kirani awaya, Ina da patient" yai maganar yana ƙokarin bi ta gefenta Zai je wuce, ruƙo Hannun shi da tayi ne yasa shi yamutsa fuska Hada bubbuga ƙafarshi atakure Yake kallonta
Cikin sanyin murya ta soma magana"Jazz kana araye obinna ya ke6ence kanshi a garden? Hankalina ya tashi ganin damuwa akan fuskarshi...." Tunkan ta ƙarasa maganar Jazz Ya zame glass ɗin idon shi, Yanayin fuskarshi Ya canza sosai, ba tare daya ce mata uffan Ba ya nufi garden ɗin gidan, bin bayanshi tai da kallo fuskarta ɗauke da murmushi don tasan muddin Jazz yaje garden, damuwar obinna ta ƙare, Saboda kaifin basirar dake gare shi Tsab zaiyi mashi solving matsalar shi. Kamar yadda Hajjaty Tabar Obinna haka Jazz ya same shi a kishingiɗe saman darduma, ya ɗan lumshe idanuwanshi, bai ta6a kayan marmarin da ta kawo mashi ba.
Sautin muryar Jazz ce ta daki kunnanshi"ina gwanin wani ga nawa!Kai ni fa bani da tamkar dattijon nan aduniya, Akanshi zan iya faɗa da kowa, duk mutumin da bai daraja gemunshi ba babu mutunci tsakanina dashi...." Cikin ɗaga murya ya ke yin maganar.
Hakan ba ƙaramin faranta zuciyar obinna yai ba, a tsanake yake kallon shi,
Kashe mashi ido ɗaya Jazza yai"ku fa tsaffin nan sai ana lallashinku ana tarairayarku, da zarar mutun ya haura shekara 70 a duniya sai kaga ya fara ɗabi'u irin na Yara, haba Uban mu maganin kukan mu, Idan Yunwa kake ji ba sai kai magana abaka abinci ba? Shine don rigima zaka ke6e kanka cikin garden salon ka jamana bala'e ace bamu baka kulawa yadda ya dace"? fuskarshi a ɗaure yai maganar, still murmushine akan fuskar obinna, A faɗace Jazz Ya nuna mashi hanya da yatsan hannun shi"maza tashi ka koma gida idan ba so ka ke Kaji ɗanyar geza a jikin ka ba, " Wannan maganar da yayi tayi matuƙar bashi dariya sosai Obinna ya tuntsire da dariya yana kallon shi, jinjina kai Jazz yai hada ruƙe qugu yace"Na fahimci rashin mabugi ne ke damun ka, " yai maganar tare da juyawa yana neman bulalar da zai buge shi, Dariya hada dafe ciki obie yake yi, Yayin da yake kallon shi,
"Mutun bai rasa ci da sha ba, Sutura Allah ya hore mashi, wadatar arziƙi da ta ƴa'ƴa mai yafi wannan aduniyar nan"? A faɗace yai maganar, kamar wanda aka 6ata ma rai, alhalin nan duk cikin zolayane, ganin yayi nasarar sanya shi farin ciki yasa shi matsawa kusa dashi.
Hannayenshi ya ruƙe acikin nashi"haba sanyin idaniyata, Dan Allah kafaɗin menene damuwarka? Ashirye nake dana sanyaka farin ciki," fuskarshi amarairaice yai mashi maganar,
Lumshe ido obie ya ɗanyi kafin a hankali ya waresu kan fuskar Jazz
"Shi ne damuwata, Kafi kowa sanin hakan, bansan ya zanyi ba, inason ganin shi, ban ta6a tunanin zai ɗauki tsawon lokacin nan batare da yazo kawo min ziyara ba," farin ruwane kwance acikin idanuwanshi, Hankalin Jazz ba ƙaramin tashi yai ba.
"Kamar yadda ka damu dashi, shima haka ya damu dakai! Ayyuka ne suka yi mashi yawa, pls ka yi mashi uziri...."
"Jazz Inaso Owais Ya halacci shagalin da za'ayi na murnar zagayowar ranar haihuwata, Amma nasan abune mai wuya ya iya zuwa" shiru Jazz ya ɗanyi yana kallon fuskarshi.
"Idan zaka Iya bani dama zan sa shi yazo, Nayi maka alƙawarin hakan," Yai maganar tare da kai hannu ya ɗauki 6arin kanka Cikin kayan marmarin da hajjaty ta kawo ma Obinna, Abaki Ya tura yana sha.
"Na bar maka komai a hannunka, Indai zaka Iya cikamin burina na ganin Owais Ya halacci taron nan,"
"Kada ka damu dattijo, ko babu mota ba abun hawa sai owais yazo kasar nan, " yai maganar tare dakai hannu zai ƙara ɗaukar Ayaba, Obie Ya ka6e mashi hannu
"Jazz ka raina girman gemuna, Kowa yana jin shakkar tunkarata amma kai Ko kaɗan ba ka Jin kunyar kallona ido cikin ido, " dariya yasaki tare da cewa'Suma don basu son ainihin wanene kakana ba, shiyasa suke jin shakkarka, "
"Ba aiki zaka je bane"? zaro ido waje yai sai lokacin ya tuna da mara lafiyan da zaije dubawa, da sauri ya mike yana faɗin"Rigimamman tsoho ni nayi nan Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana, ' har ya miƙi hanyar zai bar garden ɗin ya kuma dawowa ya zuƙunna a gaban farantin kayan marmarin ya ɗibi mai uban Yawa Kafin ya mike yana faɗin"Allah yaja da ran dattijon arziƙi tsoho mai ran ƙarfe, An buga dakai an barka, Namijin zaki uban dawa"
Murmushi ne ɗauke akan fuskar shi, idanuwanshi akan bayan Dr jazz har saida ya 6ace ma ganin shi tukunna ya ɗauke idon shi.
*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E9🔥💫_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
~Middle step~
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._
Wuraren ƙarfe biyar da rabi na marece, Aneelerh ta fito daga cikin toilet bayanta a goye da baby junaid tayi mashi wanka ta ɗaura mashi towel, A saman Gado ta kawantar da shi fuskar shi ɗauke da murmushi, ɗan zaro mashi ido tayi"Why are u smilling at me"? "Mommy daɗi nake ji, Angel zata dawo" aɗan ruɗe ta bi shi da kallo"Junaid! Waya faɗa maka Angel zata dawo"? Da yatsan hannun shi ya nuna mata saitin zuciyarshi, murmushi ta saki haɗi da ɗan girgiza kanta"my baby boy nima ina ji araina ƴar uwarka ta kusa bayyana in sha Allahu nan bada jimawa ba, in dai tana numfashi a doron duniyar nan...."tunkan ta rufe baki yace"Mommy Angel tana sona? ɗaga mashi kai ta yi alamar eh"Angel tana sonka junaid tun kafin zuwanka duniya ta ƙwalla fa rai akan son ganin ka,"
Ta yi maganar tare da juyawa ta nufi gaban mirror ta ɗauko Mayukan shafawarshi, a saman mattress ɗin ta ɗaura su, ta soma shafa mashi ajikinshi.
"Aunty Aneelerh,!" muryar zahra ce daga waje take kwaɗa mata kira, A hanzar ce Junaid ya buge hannun Aneelerh data ruƙe shi, ya damƙi towel ɗinshi dake yashe saman katifar, Lamarin yai matuƙar ɗaurewa Aneelerh kai, ganin yadda yake kiciniyar ɗaure qugunshi, duk don saboda zahra kada ta gan shi babu kaya, Kafin zahra ta faɗo ɗakin tuni ya kammala maida towel ɗinshi sai faman haki yake yi, ƙasa ƙasa da murya tace"junaid ban kammala shafa maka man ba", turo mata baki yai"Ni ae bana sho Aunty zahra ta gane min abuna, idan ta tafi sai ki ƙarasa shafa man...."kumshe dariya Aneelerh tayi abakinta.
"Aunty Aneelerh Abie da daddy suna son Yin magana dake, Na riga na faɗa masu komai game da tada zancen 6acewar su tajuddeen, sun amince da yin hakan" Farin Ciki ne ya bayyana akan fuskar Aneelerh"Zahra, zanje yanzu mu yi magana da su, Ga junaid nan ki cigaba da shafa mashi..." kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon toshe mata baki da Junaid yai da tafin hannun shi, Kallon fuskarshi tayi, 6acin rai ta gani akanta.
Ta6e baki zahra tayi idonta akan fuskar Baby junaid,"Kin ga Aunty Aneelerh Ki tashi ki je suna a palour, bana so damar nan ta wuce mu, Ki barni dashi zan ƙarasa gyara mashi jikin" amsa mata ta yi da toh, kafin ta sakko daga saman gadon ta nufi closet ta buɗe ta curo mayafinta bayan fitarta ɗakin, Junaid ya takure kanshi jikin headboard na gadon, lallashinshi ta soma yi"haba habibina meye na 6ata fuska nifa ma mommyn ka ce, zo nan in gyaran maka jikin ka, Maƙe mata kafa ɗa yai"so ki ke ki kalle mun abuna, ni banso, Zan jira mommy ta dawo"
ɗaure fuska tayi ganin zai 6ata mata lokaci yasa ta haye gadon ta cafko shi, ya dinga kuka yana shure shuren ƙafa, daƙyar ta samu ta shafe mashi jikin tana fadin"ɗan jakar uba, Jiki duk madara, da ace baka da kyau ko kallo baka ishe ni ba" tur6une mata fuska yai hada jifarta da harara, Miƙewa tai daga saman gadon ta sauko ta nufi closet din kayan su ta ɗauko mashi riga da wando, ta dawo ta zauna gefen shi, a tsanake ta zura mashi a jikinsa, tunkan ta kammala Wayar Aneelerh ta soma ringing "Wayar mommy tana ringing" junaid ne ya sanar da ita
"Ni bana ɗaga wayar mutun idan bashi ya bani izni ba" gatsina mata hanci yai"Angel ce ke kira aunty zahra dan Allah ki ɗaga, kada ta katse" kwantar da kanshi tai saman ƙirjinta, faɗi yake ni ki sake ni, inje in ɗaga kiran Angel" taƙi barin shi ya motsa, suman kanshi take shafawa da hannunta, shiyasa ya ke gudun zahra ta ɗauke shi, kamar ta samu lallausan bready haka take daƙuna shi.
Bayan fitar Aneelerh A palour ta taras da Uncle ɗan Iya tare da abie hada Mommy da Ummi zaune saman Sofa, cikin girmamawa ta ƙarasa tare da zuƙunnawa ta gaishe su, A mutunce suka amsa mata, daga ƙasan sofa ɗin da mami da ummi ke azaune ta jingina bayanta, tare da sunnar da kanta tana jiran jin me zasu ce.
Gyaran Murya uncle ɗan Iya ya yi, hakan yasa ta ɗago da ido ta kalle shi, ya ƙwama farin Glass a fuskarshi Ya ɗan sauko har saman karan hancinsa, a halitta baƙi ne wulik, kamar ba jinin Abie ba, yana da Manyan idanuwa hancin shi a wargaje yake, Haka bakin shi manyan la66a ne dashi, wandon shadda ne a jikin shi Daga sama Malun malun ce babi Ƴar Ciki, Ya ƙwama Hula Akanshi Ga uban sanƙo, a saman Kujera mai mazaunin mutun uku suke zaune su Biyu, gyaran murya yai kafin ya soma magana"Zahra ta faɗa min komai, a gaskiya kun kawo shawara mai kyau, Kunyi tunani na hankali" yana magana yana watsa hannayenshi Ɗabi'arsa ce Yin hakan. "bai kamata don abu ya haura shekaru da faruwa muja baki muyi shiru, tun da har yanzu bamu da tabbacin suna araye ko sun mutu! Idan ko suna araye ba ƙaramin ganganci mu kayi ba, Na watsar da zancen 6acewarsu, wata'ƙil Silar tada zancen Allah Ya bayyanar mana dasu....." tun da ya soma magana suka natsu suna sauraronshi, Aneelerh ta duƙar Da kanta ƙasa Farin Ciki duk ya cikata, gani take kamar ma har an riga an ganso su.
"In sha Allah zanyi magana da ziyad babban ɗan jarida ne muddin labarin nan ya je gare shi ina mai tabbatar baki da cewa cikin ƙanƙanin Lokaci Duniya zata ɗauka tamkar bai jima da faruwa ba, a manyan Kafafan sada zumunta za'a yaɗa labarinsu, irin su BBc, CNN, and ONt, muma kuma zamu bada gudummuwar mu, wurin Yaɗa hotunansu a social media"
Bayan Uncle ɗan Iya ya takaita da zancen nashi Abie ya ɗaura da cewa"kafin Gobe ki tabbatar kin tattara duk wasu hotunansu Tajudden kin tura mashi, Sannan Adage da addu'a duk danasan kina ƙoƙari wurin yi masu, Mamie ta fadamin kullum sai kin tashi yin nafilfili dare, naji daɗin jin hakan sosai, Allah yayi maki albarka" amsa mashi ta yi da ameen, Mamie tace"Ubangiji Allah ya bayyanar mana dasu, Allah yasa silar tada zancen 6acewarsu da za'ayi su bayyana, mungode sosai" godiya suka hau yiwa Uncle ɗan Iya, kafin daga Bisani Aneelerh ta miƙe tare da yi masu sallama ta Nufi bedroom ɗinta tsabar zumuɗi kamar zata tashi sama, lokacin da ta shiga ɗakin, A kwance ta samu zahra tana fuskantar ceilling hannunta a ruƙe da wayarta, ga dukkan alamu Chatting take Yi, Baby junaid tuni ya jima dayin bacci yana kwance saman ƙirjinta. Jin motsin shigowar Aneelerh Yasa ta ɗan kawar da kanta daga kallon wayar ta take Yi ta kalli Aneelerh tunkan ta ƙarasa shigowa ciki Ta lura da tsantsar farin Cikin dake akan fuskarta
"Yah aunty Aneelerh Ina fatan komai lafiya"tana murmushi tace"abie yace in tura ma Uncle hotunansu tajuddeen wlh bakiji daɗin da naji ba,"Zahra na murmushi tace"Allah yasa Adace sister, nima zan tayaku sharing a instagram page ɗin mu," Godiya Aneelerh ta yi mata, ringing ɗin wayarta ne Yaja hankalinta ga duban saman pillow, Da sauri ta nufi wayar takai hannu ta dauke ta
"Bansan wanene ke kiranki ba, Tun ɗazu bayan kin fita wayar ke ta ringing ban daga ba"
"Why ba ki ɗaga ba zahra, Surukata ce fa" ta6e baki zahra tayi"matar da ke son ƙwace mana baby junaid ɗinmu ai ƙwara daban ɗaga ba" picking call ɗin Aneelerh tai tare da kanga wayar a kunnanta.
Cikin girmamawa tayi mata sallama"Assalamu akaikum" on the other hand Hajiya adama ta amsa mata da"Wa'alaikum salam daughter In law, ina kika shiga inata kira ba aɗagawa"? aneelerh tamkar tana agabanta tace"Bana akusa da wayar ne bansan kun kira ba" gaisawa sukayi kafin hajiya adama tace"guest what"? ɗan zaro ido Aneelerh ta ɗanyi tana wurwurga eye balls ɗin ta can tace"kun dawo ƙasar"? Sautin dariyar hajiyar adama ne yasa ta saki murmushin farin ciki. "Mun dawo, in sha Allah end of this month zamu shigo Abuja, two days kin daina kiran layina Why? Ko dan saboda kada na ƙwace maki Yaro"? Cikin Jin kunyar maganarta Aneelerh tace"ba haka bane mommy, wlh ina ta zucci zuccin in kira ki Allah ne bai nufa ba" Tai maganar a yayin da take kokarin zama saman stool, Ta gaji da tsayuwar, Zahra ta kasa kunne tana sauraron Firarsu.
"Idan ma don saboda dashi ne to ki kwantar da hankalin ki, babu wanda zai raba ki da ɗanki, Munyi magana da abdallah Ya fahimtar dani game da cutuwar da zakiyi idan muka ce zamu raba ki da shi, Ni kaina bazanso Inyi silar sanya ki baƙin ciki ba...." buɗe ido Aneelerh Tayi Wani irin farin cikine tsantsa akan fuskarta, Zahra da ta tsareta da ido tana kallonta, sai faman yi mata mimi da baki takeyi donta fada mata me Hajiya adama ke fada mata wanda yasa ta farin ciki
"Zan kira mamin naki mu yi magana, Sannan akwai wata gagarumar kyauta dana shirya maki idan mun zo zaki gani" Hawayen farin Ciki ne su ka wanke fuskar Aneelerh, kasa jurewa tayi batasan lokacin da kuka ya kubce mata ba. Muryar Hajiya adama a ɗan ruɗe take fadin Aneelerh why? Kuka kuma? Meya faru? cikin shessheƙar kuka tace mata kukan farin Cikine, taji daɗin ƙaunar da take nuna mata, tana alfahari da su, samun surukai irinsu abune mai wuya, Hajiya adama taji daɗin daɗaɗan kalaman da Aneelerh take faɗa mata, tsawon lokaci suna waya Kafin daga bisani Tayi mata sallama, Idanuwanta acike tab da ƙwalla ta wurga su kan fuskar zahra tambayarta ta shiga me suka tattauna da Hajiya adama? Nan Aneelerh ta sanar da ita komai, Fasa ihu zahra Tayi tare da jefar da wayarta gefenta, ta sauke junaid daga saman jikinta a hankali ta kwantar dashi, kafin ta sauko daga saman gadon ta nufi Aneelerh ta rungumeta kamar zata maidata ciki, Farin Ciki duk Ya cikasu, Miƙewa Aneelerh tayi bayan ta ajiye wayar gaban mirrror, Rawa suka soma takawa ita da zahra, hada ɗebo shoki suna kifawa saman goshinsu, Yayin da suke sakin Dariyar murna.
*EVIL FOREST*
A ƙalla yau satin su ɗaya acikin kogon dutsen ba tare da sun motsa ba, saboda marasa lafiyan cikinsu, jikinsu yai tsauri, duk da haka suna ƙoƙarin basu kulawa ta musamman, Danish Ya haɗa masu garin maganin da su ke sha suna samun warakar raɗaɗin ciwonsu, A cikin gorar ruwansu ya ke jiƙa masu maganin, Bayan haka duk in za su yi tsarki da ruwan zafi su ke yin shi, danish ne yai masu dabarar yin hakan, Alhamdulillam Jikinsu Azeeza yayi kyau sauƙi ya samu, ba su rasa ci da sha ba, kullum ne sai sun ci abinci sau uku, Danish ne ke ƙoƙarin yi masu farautar abunda zasu ci wani sa'in zoman daji yake kaso masu ko tsuntsaye hada kayan marmari ya ke samo masu, saboda su ya ke hana idonshi bacci, A zaune yake kwana shi da Angel dinsa, tana ɗebe mashi kewa, shaƙuwace mai ƙarfi a tsakaninsu. Burinsu marasa lafiyar cikinsu su ƙarasa wartsakewa ko sun samu su cigaba da tafiya.
Yau tun da sanyin safiya ta soma Jin hayaniya acikin kunnuwanta, ƙasa ƙasa take iya jin maganganunsu, Tsantsar mamaki ne ya kamata Jin muryoyin su Batul, tamkar a mafarki, a harzarce ta buɗe idanuwanta tare da miƙewa zaune tana ƙarewa Kogon dutsen kallo, Haris ne kaɗai ya rage a kwance yana bacci, Ya ƙudundune kanshi cikin bargo, ƙoƙarin tariyo abunda ya faru jiya ta soma yi, da wata irin kasala ta miƙe tsaye tare da yin hamma, abu biyu ya ɗaure mata kai da farko tayi tsammanin zata ga su Azeeza sai dai bata kowa ba. Hankalinta A matuƙar tashe ta fito tana ƙarewa Dajin kallo, Kamar daga sama tajiyo muryar Jemimah tana ambaton Sunan da take kiranta dashi"Genie!' ras taji gabanta Ya faɗi, A ruɗe ta wurga ƙwayar idonta kansu, Gaba ɗayansu ne banda Haris, Yau wata rana sun fito daga kogon dutse jiki yayi kyau, Sai wasa suke Yi suna tsalle tsalle, Farin Ciki duk ya cikasu, Bakunansu awashe kamar gonar auduga, ba ta san lokacin da hawaye suka soma wanke fuskarta ba, Nan ta ke ta zube saman gwiwowinta tare da kifa kanta ƙasa ta yi sujjada tana godewa Allah da ya nuna mata wannan ranar, Haƙiƙa tayi farin ciki mara misaltuwa, kafin ta ɗago daga sujjadar Jemimah ta watso da gudu ta faɗo saman bayanta, sai tiƙar dariya ta ke yi tana fadin"Genie Daɗi kamar zai kashe mu, Wlh daɗi muke ji, wannan wurin mai kyau bamu ta6a ganin irin shi ba, Genie Yau zamuje gidan daddynki ko"? Kasa ɗagowa Angel tai, wani irin yanayi take jin kanta. Ƙarasowa Azeeza tayi Hannunta ruƙe cikin na Gabriel, Sauran Ƴan uwansu na abiye da bayansu, agaban inda tayi sujjadar suka tsaitsaya suna kallon ta "Angel muna son yin magana dake"muryar parveen ce ta ratsa kunnanta, daƙyar ta iya haɗiye kukan da ke shirin kubce mata ta ɗago da kanta, tare da zagayo da hanneyenta biyu ta ruƙe Jemimah gudun kada ta faɗo daga bayanta Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, tun daga kan fuskar Azeeza dake ta sakin murmushi, fatar jikinta tayi haske sosai dama ita can launin skin ɗinta na farar fata ne, da launin gashinta, ta rame sosai ta ƙara komawa ƙarama. ɗauke idon ta tayi daga fuskar Azeeza ta mayar dasu kan fuskar parveen, itama ta faɗa duk sunyi haske kamar fatalwu, Murmushi ta ɗan saki tare da kallon Batul dake a tsaye tana sakar mata murmushin ƙauna.