Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 16

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 16

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 16: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 16. A Kwance ya ke saman shimfiɗeɗan gadonsa, Kamar…

3,204 words

A Kwance ya ke saman shimfiɗeɗan gadonsa, Kamar kullum cikin shigar larabawa, hannun shi a ruƙe da wayarshi, Ya ƙurawa Hoton wallpaper ɗin shi ido, ko ƙyaftawa bai yi sam baya gajiya da kallon hotonta, Yanayin fuskarshi Ya nuna tsantsar damuwa, a hankali ya ɗaura yatsun shi saman hoton kan wayar yana shafa fuskarta, lumshe idanuwanshi Ya ɗanyi kafin a hankali ya ware su kan hoton, waƙar larabci ya soma rairawa da daddaɗar muryarsa duk akan hoton wadda ya ke kallo, ya dage yana yi mata waƙa mai nuni da ƙaunarta da yake yi, Tunawa da bata a raye yasa shi dakatawa da raira waƙar, Ya jefar da wayarshi gefe ɗaya saman mattress ɗin, haɗi da kifa kanshi saman pillow, kamar ƙaramin yaro ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, abun ne yana damunshi ya hana rayuwarshi sakat.

"Shureim, Ka yi haƙuri Ka daina sanya damuwa aranka, I know it hurts you, but worrying won't make anything better, it'll only make things worse kuma ka tuna Allah yanasan bayinsa masu tuba, Kana fa da ilmin ka ba sai na tunasar da kai ba,"

bai tsammaci jin muryarta ba, A hankali Ya ɗago da idanuwanshi Waɗanda su ka kaɗa jawur da su, ya ɗaura su kan fuskar Zainab.

Tana a tsaye cikin shiga ta riga da skirt, kanta sanye da hula, ga dukkan alamu daga kitchen ta fito.

"Babu wanda yasan nashigo shureim, Satar hanya nayi don nasan idan hajiya layla ta sani ba za ta bar ni in zo wurin ka ba......." numfasawa ta ɗanyi kafin ta ɗaura da cewa"Tuntuni na so mu samu lokaci muyi magana sai dai ban samu damar yin hakan ba saboda baka nan, till today" har cikin zuciyarshi ba ƙaramin sanyi yaji ba, yunƙurawa yai tare da miƙewa ya zauna ya jingina bayansa jikin headboard din gadon Yana kallonta, Still hawaye basu daina wanke fuskarshi ba, Zainab ta damu dashi sosai, har mamaki ta ke yi yadda wasu iyayen Allah ya basu damar haihuwar ƴa'ƴa nagartattu amma suke watsi da su, basu damu da damuwar su ba, yayin da wasu neman ƴa'ƴan su ke yi ruwa Ajallo, tana matuƙar jin takaicin haka.

"Aunt Zainab, Kin tabbata ba wanda yasan kin shigo? Ina mommy da daddy ne" "Layla tana a palour, mahaifin ka kuma Yana a garden shi da kawunka Musa" Jin hakan Yasa shi saukowa daga saman gadon shi Ya nufe ta, tsayawa yai suna fuskantar Juna.

"Ka faɗa min wani taimako ka ke so In yi maka? in sha Allahu babu abunda zai gagara, a shirye nake da in share maka hawayen ka"

Hannayen ta biyu ya ruƙo a cikin nashi gabanta sai faɗuwa ya ke yi, tsoronta kada wani daga cikin Iyayenshi ya faɗo ɗakin, muddin hakan ya faru zata ɗanɗani kuɗarta ne.

"Aunt Zainab I feel in my heart that she's still alive! Tun bayan da abun ya faru I've never dreamed of her as dead, I've always seen her alive in my dreams." tun kafin ya ƙarasa maganar ta katse shi "How could that be possible, Shureim? Mutumin da ya mutu ai baya dawowa and the dreams you're having aren't real Don't believe what you see in your dreams."

Fuskarshi a yamutse ya ke dubanta

"Amma ni inaji araina bata mutu ba!" kafe mata yai akan zancen shi Ta fahimci ya fara zaucewa, Zaifi ta lalla6a shi don ta kwantar mashi da hankalin shi"shureim, idan ma tana araye da buƙatar mu shirya plan don mu tabbatar da abunda muke zargi,"

Jinjina mata kai yai alamar yana fahimtarta.

"Dole Ka bi duk a bun da zan faɗa maka," amsa mata yai da in sha Allah, mu zauna sai muyi magana" girgiza mashi kai tayi"a'a ina tsoron Mahaifiyarka ta faɗo dakin nan, Just A tsaitsaye zan faɗa maka matakin da zaka ɗauka domin mu ci nasara akan binciken da zamu yi" zame hannunta tayi daga cikin nashi da sauri ta nufi ƙofar ɗakin ta leƙa tana duban ko'ina don kada wani ya faɗo masu, ganin bakowa yasa ta gyara labulan ɗakin nashi, ta juyo da sauri ta nufe shi Yayin da take cigaba da yin maganarta"mataki na farko shine Dole ka tanƙwashi zuciyarka, ka danne raɗaɗin da ka ke ji ka daina sanya damuwa aranka"

"Mataki na Biyu Ka daina gudun Iyayen ka, Ina nufin Ka koma masu tamkar yadda ku ke da su Ada, Biyayya sau da ƙafa, ka nemi yafiyarsu akan 6ata masu rai da ka ke Yi....." tun kan ta kai ƙarshen maganar ta lura da canzawar da yai, a marairaice yace da ita"Aunty zainab taya zan iya yin hakan? Ni bana jin zan Iya sakar masu fuska mu koma kamar yadda muke ada" murmushi ta ɗan saki kafin tace"Shureim kenan, Nafi so ina magana kana fahimtata, ta wannan hanyarce kaɗai zamu Iya gano meke wakana a tsakanin Iyayenka" jinjina mata kai yai alamar ya fahimta.

Har ya buɗe baki zai yi Magana ya ji ta yi saurin katse shi da cewa

"Me ka ke buƙata in kawo maka? nasan kana jin Yunwa"

A ruɗe ya ke kallonta da mamaki Akan fuskarshi, Me ya kawo zancen yunwa acikin maganar su.

"Ko dai kana buƙatar chips in haɗo maka da shi"? Ta wutsiyar idon shi Ya hango Layla A tsaye bakin ƙofar, Ta kifa ɗaurin ɗan kwalin atampa akanta, Riga da skirt ne sun bi shape ɗin jikinta, duk da alamun manyantaka atattare da ita, hakan bai 6oye kyawun surarta ba.

Wahalallan Yawu ya haɗiya haɗi da sauke nauyayyar ajiyar zuciya, aranshi ya ayyana ko yaushe tazo bakin ƙofar! Sai yanzu ya fahinci dalilin canza maganar zainab, ita tun kafin layla ta shigo tajiyo takun takalmanta saboda bata sanya takalmi idan ba mai tsini ba, Ba don Allah yasa taji motsinta ba da ko ta yabawa aya zaƙin ta

"Aunty zainab wai meyasa ki ke son takurani akan dole sai naci abinci, nace maki bana jin yunwa ki tafi kawai, Ni bana buƙatar ganin kowa akusa da ni, ana dole ne" Ranshi a matuƙar 6ace yai maganar, tare da Juya mata baya, Ya ruƙe qugu da hannu ɗaya, Zainab dake kallon bayanshi tace"Shureim zama da yunwa zai Iya haifa maka wata matsalar, abunda bama fata, Ni bari naje na faɗawa mahaifiyar taka kaƙi cin abinci wataƙil idan ita tayi maka magana ka ci" Har zata Juyawa shureim Ya juyo a sukwane Ya daka mata tsawa"Karki Kuskura ki ce zaki haɗani da ita, Ko kin faɗa mata abanza, matar da bata damu da ci na ko sha na ba....." Sai da yai wannan maganar, Layla ta kai hannu ta ɗan kwankwashi Jikin Ƙofar ɗakin nashi Don hankalinsu ya dawo kanta, tamkar basu san da zamanta ba suka ɗago suna kallonta, Fuskarta tasha uban make up, gashinta baki wulik har mid back ɗinta, Cikin takun izza da nuna isa Ta nufo su tana magana"Zainab Nagode da kulawarki akan ɗana, ki ƙyale shi, shureim ya daina jin maganar kowa a yanzu bansan laifin me mu ka yi mashi ba da yake gudun mu,' tun da ta fara magana Zainab take sauke ajiyar zuciya, jin bata gano me suke tattaunawa ba, shureim ko sai ƙara ɗaure fuskarshi ya ke yi kamar zata fashe saboda tsabar nuna fusatarshi.

Idanuwan mahaifiyarshi akan fuskarshi, Cikin girmamawa zainab tace"Shureim har yanzu yaro ne, tun da yana a ƙarƙashin kulawarku, sai ana haƙuri dashi ana kuma lallashin shi da jan shi a jiki ta hakanne zamu iya sanin meke damun shi" jikinta na ɗan kerma tayi maganar, gyaɗa kai Layla tayi"is Okey, ba sai kin koyamin yadda zan Kula da ɗana ba, Ni da na haife shi ni nasan kayana, Zaki Iya tafiya ki bamu wuri" ta yi maganar tare da nuna mata ƙofa da hannu.

layla kenan Ita ba'a mata gwaninta, Jiki asanyaye zainab ta kama hanyar fita ɗakin tana tafiya tana waiwayon shureim da ido take Yi mashi alamar Ya sake mata, kada ya manta da shirinsu, Lumshe mata idon da yai ne yasa ta fahimci ya gane me take nufi, Bayan fitar zainab, Layla ta tsare shi da idanuwanta

"me zan yi maka wanda zaisa Ka daina guduna? Haba Shureim saboda na kore ka cikin fushi shine ka kama Hanya ka tafi egypt wurin Ammi, Kasa ta kirani awaya tana ta zazzaga min masifa, ' ranta a6ace take yin maganar, har ya harzuƙa zai mayar mata da martani kalaman zainab suka faɗo mashi arai da sauri ya danne fushinsa, abunda ta tsana dashi tana magana Yana shareta, Wuyan farar jallabiyar jikinshi ta damƙa da hannayenta waɗanda ke a sanye da awarwaro da zabba na zallar zinari, Jijjiga shi tai"Shureim so kake baƙin cikin ka ya kashe ni? Na rasa benazir kaima kuma kana neman ɗaura min hawan jini, so ka ke zuciyata ta buga in mutu shureim"? hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba, ganin hawaye sun ciko idonta.

Duk da yasan ta yi hakanne don ta samu kanshi, sassauta muryarta tayi tare da sakin Kwalar rigarshi"Kai kaɗai nake gani naji daɗi, Meyasa ba za ka manta da abunda yawuce ba, ina magana kana share ni, kasan bana son hakan, Yana ƙona min rai" baisan sa'adda hawaye suka cigaba da wanke fuskarshi ba, muryarshi na ɗan rawa ya furta"?mommy saboda ni za ki zubar da hawayen ki"? Muryarta a kausashe tace"Shureim, how many times have I cried for you? I understand that you're trying to drive me crazy," Shureim ka daina ƙaunata" Tai maganar tana watsa hannayenta' shiru Ya ɗanyi yana kallon fuskarta, tabbas ya ga 6acin rai acikinta.

"Astagfurillah" jin ya ambaci haka Yasa ta zaro idonta akan fuskarshi "Mommy, I didn't know you cared about me that much, I thought you'd stopped loving me, amma yanzu mommy akaina kike zubar da hawayenki"?

Mamakin kalaman shi ne yasa ta kafe shi da ido ba ƙyaftawa, Hadisi Ya soma janyo mata da ayoyin al'kur'ani mai girma waɗanda ke magana akan wanda Ya ƙuntatawa iyayen shi.

"Shureim ka sani kuma kake take sani? Shine Ka rufe ido Kana ƙuntata min? Meyasa"? Marairaice mata fuska yai"ya zanyi! Sharrin zuciyane da kuma sharrin shaiɗan, sune suke azalzalar zuciyata akan abunda Ya faru, sunƙi bari na manta komai," Dafa kafaɗar shi tai da hannunta ɗaya"Ka yafe min shureim, nayi maka alƙawarin zan tarairaye ka na baka kulawa kamar yadda muke ada, Sannan inaso kamanta da abunda ya wuce, Ba laifin mu bane, mu ne sila, amma kaine ka aikata komai ba tare da ka yi shawara damu ba, kai kasan ba yadda za'ai da hankalin mu da tunanin mu mu goyi bayanka akan aikata hakan, a lokacin da ace ka yi shawara damu wlh shureim ba zamu goyi bayan abunda ka aikata ba" har cikin zuciyarta ta ke magana, Shi kanshi Yaji jikinshi yai sanyi, zuciyar shi ta karaya, tabbas maganar da ta faɗi gaskiya ne.

" Mommy, ni ne ya kamata na nemi yafiyarki, akan gudun ku da nake Yi ke da Daddy, Dan Allah ku yafe min, na gane kuskurena"

yai maganar yana ƙoƙarin zubewa saman gwiwowinsa da sauri ta ɗago da shi ta rungume shi tana ɗan bubbuga bayanshi da yatsun hannayenta, Farin ciki duk Ya cikata, ta manta when last ta ji ɗumin shureim a jikinta, saboda rashin jituwar dake a tsakanin su.

Muryar shi da alamun karaya ya furta mata"Mommy, ana 'uhibuk kathiran" Hawayen da suka taru acikin idanuwanta ne suka soma gangarowa saman kuncin ta, still ba su raba jikinsu daga na juna ba, martanin maganarshi ta mayar mashi"i love u too My son, ba zan Iya misalta farin cikin da nake a ciki ba, Shureim ka faranta min rai," ta yi maganar tare da raba jikinsu daga na juna, fuskokin su ɗauke da murmushin ƙauna

"Idan har dagaske mun shirya inaso daga yau ka goge duk wasu hotunanta dake a cikin wayarka, kallonsu baida amfani shureim, saboda suke fama maka raunin dake a cikin zuciyar ka"

Shiru yai yana kallon fuskarta, har sai da ta kai ƙarshen maganar, Har ga Allah bai jin zai Iya goge hotonta a wayarshi, don ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya suke yi ba aduk lokacin da ya kalle su, Allah ya jarabce shi da ƙaunarta, Yafi sonta akan kowa na duniyar nan, duk da bata araye.

Gudun kada ta zarge shi, yasa shi yin saurin cewa"saboda farin Cikin ki mommy zan yi deleting ɗinsu, ni kaina bana son abunda zai ƙara shiga tsakanina da ke,"

Gyaɗa kai ta yi "Shureim ka ɗauko wayar ka goge su agabana In gani" tuni yasha jinin jikin shi, ba don yaso ba ya amsa mata da toh, slowly ya juya ya nufi gadon shi ya ɗauko wayar, Kafin Ya kai mata, wayar ta hau ruri, hakan ba ƙaramin daɗi yai mashi ba, Waiwayowa yai still tana a tsaye tana kallon shi"who's calling u"? Ta jefa mashi tambayar, Nuna mata screen ɗin wayar ya yi sunan Daddy ne Ya bayyana akai" Umarni Ta bashi ya ɗaga kiran Ya kara wayar a kunanshi, Muryar Alhaji Ubaid ce ta ratsa kunnuwanshi"Shureim Uncle ɗin ka na son ganin ka, gamu nan zamu shigo cikin gidan" muryarshi A sanyaye ya amshi mashi da toh, takaicin shi ɗaya layla taƙi tafiya, ta tsare shi da ido, adan dole sai ya goge hotunanta awayarshi.

A hankali ya zame wayar daga kunnan shi, matsawa yai kusa da ita, Bayan ya cire password Na wayar Ya miƙa mata adai dai kan Gallery ɗinshi, Ta kar6i wayar tana duba hotunan, Ta yi mamakin ganinsu kamar hauka, hada wanda ya ke a rungume da ita saman ƙirjinshi, ta6e baki layla tayi, hankalin shureim ba ƙaramin tashi yai ba ganin zata danna delete all, jikin shi har tsume ya ke yi.

"Assalamu alaikum"! Muryar zainab ce ta katse mata hanzarin ta, a sukwane ta juya tana binta da kallo, a bakin ƙofa ta tsaya"Alhaji ne ya shigo tare da kawun shureim, Shine yace nayi maki magana..." yatsina fuska layla tayi"Naji, ga ni nan zuwa" Miƙa wa shureim wayar tayi"ka tabbatar ga goge su, sannan ka fito ku gaisa da kawunka," Amsa mata yai da toh, Bayan ya kar6i wayar, fitar ta keda wuya Ya cire memory ɗin wayar, Ya 6oye shi a cikin rigar pillow, Ajiyar zuciya ya sauke Ba ƙaramin daɗi yaji ba, don ji ya ke kamar za'a raba shi da ranshi idan akace ya goge hotunanta.

Toilet ya shiga ya wanko fuskarshi, Ya futo Ya nufi dressing mirror, cikin jerin turarurrukansa ya ɗauki ɗaya ya feshe shi a jikin shi, bayan ya ajiye ya fito daga ɗakin Ya nufi babban palourn.

*GIDAN ƊAN IYA*

Tun da ta fito daga cikin toilet ta ke a tsaye bakin wardrobe, daga ita sai Towel ɗaure a ƙirjinta, Ya sauko har saitin gwiwarta, a ƙalla Tafi ƙarfin mintuna goma, ba tare da ta motsa ba, idanuwanta na akan Jerin suturarta da ke a ninke sun sha guga, ba komai ne ya tsaida ta ba fa ce neman kayan da zasu dace da tarban Manyan baƙin su da zasu Yau, Ruwan ido take yi, duk kayan da ta ɗauko sai taga kamar ba zasu dace da ita ba, Wayarta dake a jiye saman drawer ce ta soma ringing, nan ta ke taji gabanta ya faɗi fatanta Allah yasa basu bane suka ƙaraso, Da ɗan saurinta ta nufi wayar tare da kai hannu ta ɗauketa, ko da ta duba screen ɗin wayar, babu sunan wanda ya kira, Baƙuwar number ce, kokwanto ta shiga yi akan ta ɗaga ko karta ɗaga? Don ita a tsarinta bata ɗaga baƙuwar number in dai ba wadda ta yi saving akan wayarta ba ce, kusan sau uku kiran nashigowa Yana yin rejecting ba tare da ta ɗaga shi ba, tayi kasaƙe kamar an dasa mata Aya,

Shigowa Cikin ɗakin Zahra ta yi, bakinta ɗauke da sallama, turkish gown ce a jikinta launin pink ba ƙaramin kyau tayi mata ba, tayi rolling veil saman kanta. Ganin Aneelerh a tsaye yasa tace"lafiya? Ya akai naga baki shirya ba? Ko kin manta cewa suna a hanya? Sun fa kusa isowa, Na rasa meke damunki, Ko har yanzu kewar baby junaid ɗin ce bata sake ki ba"? Harara Aneelerh ta ɗan jefa mata, Ba tare da tace koma ba, ta ɗaura wayarta saman mattress, kafin ta juya ta nufi wardrobe din Kayan da ta bari a buɗe.

"Zahra zo Ki tayani zabar kayan da zan sanya, Ruwan ido Ya hana ni ɗauka tun ɗazu" murmushi zahra ta saki yayin da take tunkarar wardrobe ɗin"Aunty aneelerh, shiga za ki yi ta mutunci, ta kece raini, Lace ko shadda su zasu fi dacewa, " Ta yi maganar tare da Kai hannu cikin wardrobe ɗin kayan ta janyo mata wani haɗaɗɗan lace launin golden colour, ta miƙa ma Aneelerh, Fuskarta ɗauke da murmushi ta kar6i Kayan da zahra ta miƙa mata"na yadda ke ƙwararriyace a6angaren iya zabar kayan da zasu dace da mutun, nafi karfin 15 mins ina neman wanda zasu dace dani na kasa, sai da ki ka zo" Zahra tace"kada ki manta aikina ne, burina kiyi kyau auntyna, surukanki su ganki a mutuncenki, bari naje na ɗauko maki sarƙar da zata dace da kayan, ' amsa mata Aneelerh tayi da toh, Wuce wa zahra tayi agaban drawer chest Ta zuƙunna ta dauko mata jewelry box dinta, Ta buɗe ta lalubo mata necklace da earrings launin Lace ɗinta, maida box dinta tayi kafin ta miƙe ta daura mata su gaban mirror.

"Aunty aneelerh, Ga su nan saman mirror, Pls Ki shirya da wuri, Ni zan je na taya su mami shirya masu abincin"

Amsa mata ta yi da toh ta ƙara da yi mata godiya, Bayan fitar zahra, Aneelerh ta shirya tsaf cikin Lace ɗinta, riga da skirt, sun yi bala'in yi mata kyau, sun ɗan kama jikinta, shape ɗinta ya fito sosai, Kamar a jikinta aka ɗinka kayan, a gaban mirror ta zauna tana yin make up, lip gloss ta shafa ma la66anta, Ta ɗan shafa hoda, ta ɗauki brush tana gyara jagirarta, ' Sumar kanta Ta sauko har saman bayanta, ƙarar Shigowar text a wayarta ne yasa ta ɗan kalli 6angaren da wayar take ajiye saman gado, sai lokacin ta tuna da baƙuwar number da ake ta kiranta ɗazu, sai da ta fara Ɗaura dan kwalin leshin Kafin ta miƙe ta nufi wayar ta ɗauke ta, Da yatsan hannunta ta janyo sakon A hankali ya buɗe, Ta yi mamakin ganin Sunanta da aka rubuta da manyan haruffa, menene ma'anar sakon? Just Aneelerh? Wanene wannan? Kiran number ta soma ƙoƙarin Yi sai dai taƙi shiga, A ƙarshe ta hakura ta daurata saman pillow, Gaban Mirror ta koma ta ɗauki jerin turarurruka tana feshe jikin ta da su, tunawa da baby junaid ɗinta yasa ta ɗan saki murmushi, tayi missing ɗinshi sosai, yau tun da safe Mahboob Yaje kai shi school, Bayan ta haɗa da shi da kuɗin fetur, kusan sati biyu da fara zuwanshi makarantar, kullum da fara'a yake tafiya, yana zumuɗi, da zarar an kaishi Ya ke saka masu rigima sai sun dawo dashi gida, Har atashi daga school ɗin Yana yin kuka, Fuskarshi jawur ake dawo mata da shi. Malaman makarantar har sun canza mashi suna daga Junaid zuwa babyn mommy, saboda sunanta da yake yawan kira masu.

Daga waje tajiyo muryar Zahra tana kwaɗa mata kira"Aunty Aneelerh! " girgiza kai tayi aranta tace"Ko yaushe ne zahra zata daina Yi min irin wannan kiran talaucin kamar zata ƙararmin da sunana"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull