Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 17

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 17

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 17: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 17. Zahra na shigowa ɗakin ta Waro ido waje tana…

3,330 words

Zahra na shigowa ɗakin ta Waro ido waje tana fadin"Wow!!! Tabarakallahu Ahsanul khaliqin Aunty aneelern kinga yadda ki kai kyau? Kamar wadda zata shiga gasar miss world," harara Aneelerh ta jefa mata fuskarta asake tace"Naji na gode Da yabo, ni dai yanzu faɗa min Kiran menene kike yi min"? Watsa hannu Zahra Tayi"dama ummi ne ta aiko ni zaki ci abinci yanzu ko sai anjima idan sunzo"? "Yunwa nake Ji zahra, ba zan Iya jira sai sun zo ba, ki samu plate ki zuba min dambun shinkafa, Ki haɗo min da lemu mai sanyi, " "Toh, Amma kafin nan mu ɗanyi selfy mana" ta yi maganar tare da Kunna camera din iphone nata, ta ɗaga Wayar Tare da ɗaura kanta saman kafaɗar Aneelerh, gaba ɗaya suka saki murmushi, ' kusan hotuna Biyar tayi masu atsaye kafin Ta nufi hanyar fita ɗakin tana faɗin"Idan surukan naki sunzo zamu ƙara yin wasu hotunan tare, Hakan Yana ƙara danƙon zumunci," fuskar Aneelerh ɗauke da murmushi ta ke bin Bayan Zahra da kallo, gefen gadon ta zauna tana Jiran dawowarta.

*EVIL FOREST*

Tun da garin Allah Ya waye Masu a cikin ƙurmin dajin, Kowan nan su Ya farka, Da wata irin matsiyaciyar yunwa, suna zazzaune abakin bishiya sun jingina bayan su, Sai hamma suke Yi, Jiya basu ci abinci da yawa ba kafin Kwanta, sauran Kayan marmarin da suka rage ne su ka sha, dan ma suna da jumurin yunwa, Hankalin su ba akwance Yake ba, Danish Yaƙi farkawa daga bacci, tsawon awanni tun daren Jiya da Angel ta sanya shi yin bacci yake ta yi, Ko motsi Ba ya yi numfashinsa ne kaɗai ke fita, tun suna sa ran zai farka har sun fara tunanin Anya kuwa Lafiya? Baccin ya wuce na hankali, domin kuwa tuni safiya ta jima da wuce wa sun shiga tsakar rana. Sun tsare shi da ido suna kallon shi, A saman shimfiɗar da Angel ta yi mashi, ya ke a kwance sun ƙudundune shi da bargo, tuntuni su ka so su tada shi daga bacci amma Angel ta hana su, ita aganinta bai kamata su takura mashi ba, tsawon wata ɗaya baya runtsawa kullum shine yin gadinsu, Na yau kawai Ya samu ya runtsa ai bai kamata su katse mashi hutun shi ba.

"Angel Yunwa mu ke Ji" Parveen ce Ta yi maganar, Fuskarta A kumbure ga miyan bacci a gefe da gefen bakinta, sumar kanta A haukace take babu gyara kamar Ƴar mahaukaciya, Angel da ke Fuskantar su tana zaune daga gefen shimfiɗar Danish, fuskarta sam babu walwala, abun ya fara damunta ganin yaƙi farkawa fatanta Allah yasa baccin lafiya ne ya ke yi. "Genie we are feeling hungry, pls cikina kukan Yunwa yake mini" Jemimah ce tayi maganar, tamkar zata fashe da kuka, idon Angel akan fuskokinsu, Batul sai hamma take Yi, tana faman yamutsa fuskarta.

"Ki jaraba Tada shi mana, wata'ƙil Ya farka, Tun da kinga mu bamu san kan dajin nan ba, balle mu ce zamu shiga ciki mu nemo abinci" Naufal ne yai maganar muryarshi da kasala.

"Ni zan Iya zuwa na nemo mana abincin sai mu ci" Gabriel Ne yai maganar, hannunshi ɗaya asaman sumar kan Azeeza da ke kwance saman ƙirjin shi.

Girgiza kai Angel ta yi"A'a Gabriel, ba sai ka je ba, Danish ne kaɗai zai Iya shiga dajin nan Ya dawo ba tare da wani abu ya same shi ba," bubbuga ƙafa jemimah tayi cikin shessheƙar kuka tace"wai genie Ya ki ke so Mu yi ne mu fa yunwa muke ji, Ki tada shi ki tada shi Kin ƙiya so kike mu mutu ko"?

Gaba ɗaya hankalinsu Ya koma akan jemimah dake Yiwa angel faɗa, ita kanta Angel kallon nata take yi, ganin yadda ta 6ata fuska, Kumatuntu sun yi jawur da su tsabar fusata. "Angel ku tada shi mana" Da sauri suka kalli Haris Da yai magana, Tun da su ka baro kurkuku, baya magana daga Eh sai a'a, su kaɗai ne abunda Yake iya furtawa, amma yau sai gashi yayi masu magana, sun ɗanyi mamaki kuma sunji daɗi ga dukkan alamu sauƙi ya samu Saboda maganar Haris yasa ta kai hannu ta bubbugi kafadar Danish, Muryar ta ƙasa ƙasa take furta sunanshi"Danish wake up! Ka tashi suna jin yunwa," shiru bai motsa ba, Kusan sau biyar tana yi mashi magana har acikin kunnanshi takai bakinta

Nan fa gabanta ya fara faɗuwa, Parveen tace"ki buge shi mana wata'ƙil ya farka" Ba tare da ta kalli parveen ba tace"bazan Iya ba" ta ambaci hakan tare da cigaba da kwala mashi kira.

"Angel nauyin bacci ne da shi, Ba haka yakamata Ki tayar dashi ba, let me help u, " Gabriel ne ya ambaci Hakan, Sai da ya fara janye azeeza daga jikinshi, tukunna Ya matsa gaban shimfiɗar Danish, bubbuga kafadarshi ya yi Da ƙarfi haɗi da ambaton Sunanshi"Danish! Danish!" yadda yake kware murya hatta su kansu sautin Ya cikasu, amma wani iko na Allah Danish ko girgiza Bai yi ba, Zuciyar Angel a jagule ta ɗaura Kunnanta saitin ƙirjinshi Bayan ta yaye mashi bargon, jin heart beat ɗinsa yasa ta ɗan sauke ajiyar zuciya sai dai ta yi mamakin dalilin rashin farkawarshi, Hankalin sauran ƴan uwan Yaƙi kwanciya, Gaba ɗaya suka dawo kewaye da shimfidarshi Kowa Ya zuƙunna Su Azeeza har sun fara shessheƙar kuka suna faɗin Wayyo Allah Danish ɗinmu meke damunka, dan Allah ka farka ka yi mana magana ko hankalin mu ya kwanta, Mu mun haƙura ma da abinci kai kawai muke so ka tashi.

"Ko dai suma ya yi ne? Ku duba cikin gorar ruwan mu idan akwai sauran ruwa ku ɗauko Mu yayyafa mashi" Gabriel ne yai maganar cikin rashin kwanciyar hankali, Angel tace"a'a kada ku watsa mashi ruwa, Zuciyarshi fa tana bugawa, bacci ya ke yi, kunsan Danish da nauyin bacci, Balle kuma da ya ɗauki tsawon kwanaki bai runtsa ba,' ɗaya bayan ɗaya suke jogana kunnansu saman kirjinshi don su ji idan zuciyarshi na bugawa, Hankalinsu Ya ɗan kwanta da jin sautin heart beat din nashi. "Nasan nan bada jimawa ba zai farka, Mu ɗan ƙara haƙuri" Miƙewa Jemimah tayi tare da bubbuga ƙafarta, abunka ga yaro ba haƙuri, Yunwa ce ta addabeta, Juyawa tayi gaba ɗaya suka bi bayanta da kallo, agaban korayen ciyayen dake shimfiɗe a wurin ta tsugunna, ta soma tsigowa tana turawa abaki tana ci, hakan da tayi ne ya tuna masu da Ganyen da ake basu a prison, aiko da sauri batul da Parveen da azeeza suka mimmiƙe agaban jamimah su ka zuƙunna kamar akuyoyi haka suke cizgar ciyawa suna ci, tsawa Angel da daka masu"Meye haka dan Allah? Kunsan wani irin ganye ne ku ke ci? Ku daina" a tsawace ta ƙarasa maganar, ta mike ta bi su ɗaya bayan ɗaya tana kwace ciyawar da suka damƙa a hannun su, Fashe mata da kuka Parveen da jemimah su ka yi Nan take taji zuciyarta ta karya, cikin shessheƙar kuka suke faɗin ba za su iya jurewa ba, yunwa ce ta addabe su, ta taimaka tabar su su ci ganyen, suna jin daɗin shi ahaka. Idanuwanta acike tab da ƙwalla tace"Is ok, Bari na shiga cikin dajin in nemo mana abincin da zamu ci," miƙewa Gabriel yai"Zan bi ki Angel" girgiza mashi kai tai"A'a gabriel, Ka zauna ka kula da su Azeeza, Yanzu zan dawo" ba don yaso ba ya amsa mata da toh, Kallon sauran Ƴan uwan nasu tayi"Javed Naufal, Ku kula da su Azeeza, Yanzu zanje na dawo," Naufal yace"meyasa zaki tafi ke kaɗai, bayan kin faɗa mana mu yi takatsantsan da dajin nan akwai mugayen halittun da zasu Iya cutar damu, why angel? Gaskiya ni ban goyi bayan ki tafi ke kaɗai ba, sai dai mu tafi mu duka," Yai maganar tare da miƙewa, Javed ma Ya miƙe, haris ne kaɗai Ya rage a zaune yana sauraronsu. Ita kanta gabanta faɗuwa yake yi gani ta ke yi kamar wani mugun abun zai iya faruwa da ita Murmushi ta ƙaƙalo akan fuskarta duk don ta kwantar masu da hankulan su yasa tace"Bawani abu fa, da zarar nayi addu'a Allah zai tsare ni har inje in dawo lafiya, ku kwantar da hankalinku" girgiza kai Gabriel yai"bazai yiwu ba Angel, bana so wani abu ya same ki ta silar mu, idan har ba zaki bari mu bi ki ba, To ki bari Danish Ya farka Ya je da kanshi ya samo mana abincin...." tunkan ya ƙarasa maganar Angel tai saurin katse shi da cewa"su Azeeza yunwa su ke Ji, Na yadda Gabriel Ka raka ni mu tafi, ku kuma ku zauna yanzu zamu dawo" Hankalinsu ya ɗan kwanta, Atare da Gabriel Suka nufi Cikin dajin, Hannunta ruƙe da ƙaramin kwandon su, komawa su azeeza su ka yi abakin bishiya suna zaman jiran dawowarsu.

Cikin dajin suka kutsa suna tafiya suna dan tattauna fira a tsakaninsu, ta ko'ina bishiyoyine masu tsayi Da faɗi, Rassansu sun lullu6e wurin da inuwar su.

"Hankalinka ya kwanta ka biyo ni, ni ban san ma ina zamu dosa ba, Ka ta6a shiga daji"? Ta jefa mashi tambaya, girgiza mata kai yai alamar a'a"bazan Iya tunawa ba Angel, na manta da komai na rayuwata, amma inaji araina koda ace ban ta6a shigowa daji ba, zai iya yiwuwa na ta6a kallon shi a waya, Ni yanzu burina mu fita daga Cikin Dajin nan, Ko mun samu mu tona asirin zaluncin da ake yi a cikin kurkukun ƙaddara, Angel na damu da rashin ƴar uwata, ina tsoron kafin mu yi nasara su kashe min ita" yayin da yake yin maganar yanayin fuskarshi ne Ya canza, abun ba ƙaramin ta6a zuciyarshi yake yi ba duk in ya tuna da ƴar uwarshi Gabriellah. Cikin nuna jin tausayin shi angel tace"ka kwantar da hankalin ka, Idan Allah yasa mai tsawaicin kwanace zamu ganta, in kuma ta riga mu gidan gaskiya, Allah Ya jiƙanta, yana daga cikin ƙaddarar bawa, ba dole ya rayu da abunda ya ke so ba, wata rana ma kowa zai mutu ba wanda za'a bari gadin duniyar......." fira ta yi daɗi sai nutsawa suke Yi, cikin Dajin ba tare da sunsan inda zasu dosa ba, Ga wata iska mai daɗi da ta ke kaɗawa, wasa wasa Ƙarfin iskar sai ƙaruwa ya ke Yi, ta cika masu idanuwansu daƙyar suke buɗe su.

Yayin da su Angel suka tafi nemo masu abinci, Sun yi zazzaune zaman jiran tsammani, Har sun fara lumshe idanuwan su saboda iskar dake kaɗa masu ba ƙaramin kasala take haifar masu ba, kwatsam! Ba zato ba tsammani kunnuwansu suka soma Jiyo masu wani irin sautin gurnani mai matuƙar rikitarwa da razanarwa, A firgice suka ware idanuwansu, Yayin da zuciyarsu ke buguwa da ƙarfi da ƙarfi tamkar zata 6allo ƙirjin su, tsananin tsorone Ya kamasu sai faman wurwurga ƙwayar idanuwansu suke Yi, a ƙoƙarinsu na su gano ta inda sautin gurnani ke fitowa, sai dai sun kasa sani kuma sun kasa ta6uka komai, Azeeza tuni ta shige ma Batul kamar zata koma Cikinta, Jikin su sai faman yin kakarwa yake yi saboda gurnanin ya cika kunnuwansu, Haris dake azaune gaban shimfiɗar Danish muryar shi adabarbarce ya ke ambaton sunanshi"da..da..nish ka tashi, pls ka tashi danish, Wani abu yana tunkaro mu' Da rarrafe su batul suka ƙarasa gaban shimfiɗar Danish, Cikin fitar hayyaci suke bugun Jikinshi don ya farka ya ceci rayuwarsu, duk sun bi sun ruɗe tsigar Jikinsu ta tashi haiƙam, Har suna haɗa baki wurin ambaton sunanshi"Danish mun shiga uku, dan Allah ka farka, Wannan wani irin sauti ne haka babu daɗin ji, ga Angel bata nan sun tafi tare da Gabriel, Ni dama nasan zai yi wuya mu bar dajin nan da ran mu' cikin shessheƙar ku ka suke magana hawaye na bin fuskokinsu, Jemimah da azeeza tuni sun rushe da kuka mai sautin gaske, tunkafin ma suga menene ke tunkarosu, sautin kukansu Jemimah shiya ƙara Janyo hankalin Abunda ke nufo su, basu san sune suke Janyo shi ba, babu wanda yai hankalin Ya tsawatar da su akan su daina Yin kukan suyi shiru, ba su yi tunanin yin hakan ba, lokacin da sautin gurnani ya ƙarfafa hatta ganyayyakin dake a wurin Girgixa suke yi, nan take idanuwansu suka tsaya cak akan wurin da suke zargin zai 6ullo, Kamar An Jeho suka faɗo ƙasan wurin, wasu irin Mugayen Halittun namun dawa, masu gashi gashi a jikinsu babu kyan gani gwanin ban ƙyama, Suffarsu tamkar ta majici sai dai sun gurmi maciji a halitta tsaf zasu Iya haɗiye mutun su nannade shi a cikin bakunansu, Tashin hankalin da ba'a sama shi Date, Wata irin gigitacciyar ƙara suka fasa, Ganin Yadda halittun suke Kurɗaɗowa saƙo da lungu masu Yawan gaske gasu manya manya, Gadan gadan suke tunkarosu Harwani nannaɗe Jikinsu suke yi suna harɗewa, tsabar firgi da tsoro ne yasa suka Watsa da gudun gaske kamar zasu Tashi sama, Gudu su ke yi na fitar hayyaci, gudun ceton rai, su kan su basu son Inda zasu dosa ba, wani ƙarin tashin hankalin Halittun da gudu suke binsu, Ga sauri da Allah yai masu, sun fuskanci matsanancin tashin hankali mara misaltuwa, musamman ƙananun cikinsu Azeeza da jemimah duk sun tarwatse kowa Da inda nufa, dan bala'i, Halittun suna lura da kowace kusurwa suka faɗa, Yadda suka raba kawunansu haka suma halittun su ka karkasa kawunansu wurin binsu, Haris da ba ƙoshin lafiya gare shi ba, tuni Numfashin shi ya soma sarƙewa, bakinshi ya soma fitar da jini, Gashi kowa Ya watse sun barshi, Yana ji yana gani halittar nan Ta ta taɗiye ƙafarshi gaba ɗaya ya kife ƙasa, tana gurnani ta wage bakinta masu haƙora a jere babu kyan gani, ta Zurma ƙafafuwanshi.....Innalillah

A 6angaren Azeeza da ke ruƙe da jemimah suna tiƙar gudu, hada tuntu6e sun rasa ina zasu dosa, Jemimah sai kuka take yi tana ambaton sunan Genie, Cikin rashin sanya Wasu muggan ƙayoyi suka Sargaho ƙafafuwansu kusan atare suka rubza ƙasa kansu ya daku.

A 6angaren Batul da parveen da Hannah da suka nufi Hanya ɗaya, Halittun nan sai binsu suke yi, sun rasa ina zasu dosa, suna gudu Sumar kansu Na rufe Masu idanuwansu, ba zato ba tsammani ƙafafuwansu suka zurma a cikin wani rami da ca6ali ya cika shi, gaba ɗaya su ka nutse cikin shi, Ko numfashi basu Iya fitarwa.

Idan muka Koma 6angaren Angel da Gabriel, lokacin da suka ƙaraso bakin wata bishiyar Mangaro sun tsaya suna tunanin hawa saman bishiyar don su tsigo su, atare suka haye suna aikin tsinkar magaro, sai da suka gama ɗibarshi a cikin kwando, Gabriel na yunƙurin zura ƙafarshi Ya sauko ƙasa kwatsam idanuwanshi suka sauka akan kurar dake ƙasan bishiyar tana cin wani namun dawa data kamo, wahalallan yawu ya haɗiya tare da kallon Angel, ita sam bata lura da abunda ya hango ba, "Gabriel mu sauko mana, Suna jiran mu" Muryarshi Na kakarwa yace"Angel mun shiga uku, wlh kura ce a ƙasa take cin nama," Sai lokacin ta wurga Idanuwanta ƙasan bishiyar, Gabanta yai mugun bugu, muryarta da tashin hankali ta furta Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Kafin Gabriel ya furta wani abu daga can cikin Dajin ihun muryar Naufal Ta karaɗe kunnuwan su, Kallon Juna su ka yi nan ta ke su ka fahimci babu lafiya a wurin Ƴan uwan su, zufa tuni ta wanke fuskarsu, ganin tana yunƙurin sauka yasa gabriel damƙo hannunta, muryarshi a hargitse yace"Kada ki sauka angel kashe ki za ta yi" Girgiza mashi kai tayi idanuwanta sun rikiɗa jawur dasu tace"ƙwara ta cinye ni, wlh sai naje wurin ƴan uwana, Baka ji ihun naufal ba, Allah kaɗai yasan meke faruwa dasu" kokawa suka soma yi da Gabriel a saman bishiyar, ya hana ta saukowa sai kiciniyar kwace kanta ta ke yi, aiko Suna cikin Yin kokawar nan Gaba ɗayansu suka ƙundumo ƙasa agaban kurar nan, Bakin ta ca6a ca6a da jini, Kafin ta ɗago da ido ta kallesu, Da iya ƙarfinsu na ƙarshe suka yunƙura suka miƙe a guje suka watsa, da gudu itama kurar tabisu tana gurnani, babu wanda bai fita hayyacin shi ba, lokacin da suka faɗo wurin da suka bar su azeeza hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, gabin babu kowa ga kuma Danish a kwance yana ta sharar baccin shi. Kafin Angel tayi yunƙurin zuwa wuri shi kurar nan ta dako uban tsalle ta faɗo masu, Da ƙarfi gabriel Ya fusgi hannunta tana kuka tana ambaton sunan danish Tana miƙa hannu yaja ta da gudu, wani iko na Allah kurar ta tsalle Danish tabisu da gudu, su kawai ta ke hari, kurɗaɗawa suka yi cikin dajin suna gudun famfalaki Kura ta zamar masu masifa ta hanasu sakat........."

*Boss Bature✍️*

Tun bayan da dr shureim ya fito daga bedroom ɗinshi ya nufi Palour, A zazzaune ya samu Alhaji ubaid tare da Uncle musa zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Layla tana a zaune saman sofa mai mazaunin mutun biyu, Idon shi na akan Uncle ɗin nashi, Ya ɗauki wankan tsadaddiyar shadda mai ɗaukar ido, ƙamshin turaren shi Ya cika palourn, idanuwanshi suna a lumshe, hannun shi na dama haɗaɗɗiyar agogon diamond ce wadda a ƙalla price ɗinta ya kai 300m, mutunne mai ji da naira, hutu ya zauna mashi ko Alhaji ubaid ba zai nuna mashi tarin dukiya ba, ko a muƙami bai kai shi matsayi ba, Alhaji musa ƙanine ga Alhaji ubaid uwa ɗaya uba ɗaya, kuma shine former president, akwai tazarar shekaru a tsakaninsu, A kyawun halitta Musa ya zarce Alhaji ubaid, Yana da hasken fata yayin da Alhaji ubaid yake da duhun fata, Sannan yana da Yalwatacciyar sumar kai tasha gyara ga sajen gefe da gefen fuskarshi baƙi wulik, Kamar matashin saurayi. Ya iya ɗaukar wanka ga aji ga kuma ji da kai. Daga ƙasan carpet dr Shureim ya zauna cikin girmamawa ya gaishe dasu, Alhaji ubaid ne kaɗai ya amsa mashi, kawun nashi kuwa ko arziƙin kallo bai samu ba, har sai da hajiya layla tace mashi"baka ji shureim yana gashe ka ba"? Ba tare daya buɗe idon shi ba yace"Naji," sanin halin shi yasa Shureim bai damu ba, Layla dai ce ranta ya 6aci dama ita bata iya 6oye fushin ta, Alhaji ubaid ko murmushi ne akan fuskarshi, Har yau mamakin Halin Ƙanin nashi Yake yi.

"Shureim, kasan shi fa mutumin turaine ba haka yake son ka gaishe shi ba, Ka matsa kusa dashi yaji ɗumin ɗanshi a jikin shi" acewar Alhaji ubaid,

Yatsina fuska layla tayi, aranta kuma ji take kamar ta shaƙe wuyan Alhaji musa, jin kanshi na matuƙar ƙona mata rai, miƙewa shureim yai tare da nufar sofa ɗin da musa ya ke a hakimce, ya zauna daga ƙasa, "Uncle sannu da zuwa, Ya gajiyar tafiya" sai lokacin ya ɗan ware idanuwanshi tare da kallon shureim na tsawon mintuna, sai da ya mula ya sha iska tukunna ya soma magana "Babu gajiya atare da ni, kai zanyiwa sannu, ni banzo da niyar in ganka ba, banma yi tunanin kana a ƙasar ba, sai da Ya ya ya ke faɗamin, shureim kafi ƙarfin ka tako kazo gidana ne? Laifin hada ni ya shafa kenan"? Tun da ya soma magana, hajiya layla take jifar shi da harara a fakaice batare da ta bari Alhaji ubaid ya gani ba, ita sam baya burgeta, haushin nuna isar da yake yi take ji, "Ay min afwa Uncle, bani da kwanciyar hankali ne shiyasa bana samun damar zuwa, amma kuna araina," Ta6e baki Alhaji musa yai ba tare da ya furta kalma ba

Hajiya layla tace"To ai kaima ɗin baka damu dashi ba, Ba ka neman shi taya zai yi tunanin kana buƙatar ganin shi a gidan ka......" bata ƙarasa maganar ba, da sauri ta dakata ganin irin kallon da Alhaji ubaid ya ke jefa mata, sam baya son tana shiga tsakanin shureim da ƙanin shi, saboda mugun son shi ya ke yi baya son 6acin ranshi.

"Kare shi za ki yi"? Alhaji musa ne yai maganar sautin muryar shi a kausashe, Shiru tayi bata tanka mashi ba, "Kada ki shiga tsakanin Uba da ɗansa, Kija baki kiyi shiru" Alhaji ubaid ne yai maganar, Ta6e baki tayi tana faman hura hanci. "Ae da kabarta yaya ta ƙarasa maganarta," yai maganar fuskarshi ɗauke da murmushi. Kafin ya kawar da idonshi daga kallonta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull