Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 18
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 18: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 18. "Shureim, Idan na tashi tafiya abuja atare da kai…
3,310 words
"Shureim, Idan na tashi tafiya abuja atare da kai zamu tafi, bazan barka a gidan nan ba, don Na fahimci akwai masu takura maka, Shiyasa duk ka rame kayi duhu," Cikin kulawa yake yi mashi maganar, hannun shi ɗaya asaman kafaɗar dr shureim ɗin, Layla ta yi mamakin jin abunda yace, mutumin da ko ƴa'ƴan shi bai sakar masu fuska shine ya ke zancen zai tafi da shureim, kwa6e fuska ta yi don ta fahimci so ya ke ya ƙuntata mata.
Alhaji ubaid yana murmushi yace"naji dadin jin hakan, wata'ƙil idan kuka je can yafi sakewa, don na fahimci shureim baya son zama gida..." kafin ya ƙarasa maganar, layla ta katse shi da cewa ''ae sai ku tsaya kuji ra'ayin shi ko? Idan ya ce yana son zuwa can ɗin," Tana rufe baki Alhaji musa yace"ai ba shawara nake nema dashi ba, Umarni ne" Cikin isa Ya furta hakan, Kafin ya kalli dr shureim, ka shirya komai naka idan muka tashi tafiya atare zamu tafi"
Lamarin ya ɗaure mata kai, shi dai Dr shureim yai shiru bai tanka masu ba, Girgiza kai Hajiya layla tayi'bazai yiwuwa ba, haba dan Allah duka yaushe muka samu shureim ɗin ya dawo wurin mu, Sannan kuma yanzu kace zaka tafi dashi? Aɗan bari ya huta mana, Shi kaɗai fa nake gani inji daɗi," rai a6ace take magana, Sun natsu suna sauraronta, sai da takai ƙarshen Aya tukunna Alhaji ubaid yace da ita"meye na tada jijiyoyin wuya? Guduwa zai yi dashi ne? Bafa raba ki zaiyi dashi ba, Yana so ya zauna gidan shi na ɗan wani lokaci," fuskar Alhaji musa aɗaure yace"idan na ga dama zaici gaba da zama awurina ne kuma ke baki isa ki hana shi ba" murmushin fuskar Alhaji ubaid bai washe ba yace"ba girmanku bane ku tsaya kuna sa'insa akan Shureim sai kace wani ƙaramin yaro, ko da ya ke laifin ka ne shureim tuntuni nake baka shawarar kayi aure ka ƙi yi, da ace kana da Iyali babu wanda ya isa yai iko da kai" da zolaya yayi maganar, Shureim dai ya natsu yana jinsu, Ya jima yana jin takaici yadda rayuwa ta canza mashi, Ya koma tamkar ƙaramin yaro a idon kowa, saboda raunin zuciyarshi.
daƙyar Alhaji ubaid ya samu Ya maida sa'in sar tasu Wasa, dama can basu jituwa tsakanin Layla da ƙanin shi tunfil azal. "Yakamata mu tashi muje muci abinci, zainab ta shirya mana a dining" layla ce tayi maganar, Ɗaya bayan ɗaya suka miƙe tare da nufar Dining room.
*Kaɗan daga Cikin Na sati mai zuwa idan Allah ya kaimu da rai da lafiya*
*Evil forest*
Sautin Ƙarar Danƙararen Helicopter mai saukar angulu Ƙirar UH-60 Black Hawk mallakin Sojin Ƙasar america ne Ya karaɗe ko'ina Na Cikin Dajin Evil forest Hatta rassan bishiyoyin da ke a cikin dajin girgiza suke yi saboda ƙarfin iskar fankar Jirgin, Shawagi jirgin yake yi a saman Iska Yana kewaye ko'ina na tsawon mintuna talatin, Yayin da Hot soldiers din dake a tsaye saman jirgin cikin shigarsu Ta ka ki sun ɗaura ɗamarar Yaki, Sai dai ga dukkan alamu Sun kammala gudanar da abunda Ya kawo su Cikin Dajin, Ɗaya daga Cikin sojojin dake a tsaye bakin ƙofar helicopter ɗin Hannun shi ruƙe da tactic phone Wayar da sojoji suke yin amfani da ita wurin yin sadarwa ga Manyansu dake acan Headquater, Cikin Harshen turancin Yake Yin magana muryarshi na fita da amon murya saboda ƙarfin iskar Dajin
"We successfully apprehended the criminal. We are now on our way back to the U.S. with the eleven children we found in the forest."
Da wani irin speed jirgin ya karya kwana ya miƙi hanyar komawa ƙasar da ya fito......, Nima kuma na ajiye alƙalamina.
*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E11🔥💫_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
~Middle step~
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._
Gaba ɗaya Haris ya fidda rai da rayuwa, tun da halittar nan ta zura ƙafafuwansa cikin wawakeken bakinta, tsabar tsoro da firgici sun hana shi motsawa jini duk ya wanke bakinsa har saman rigar sa, jikinsa yai wani irin mahaukacin zafi na fitar hayyaci, Bawan Allah sai sambatu ya ke yi yana ambaton Sunan Danish dana sauran ƴan uwan su don su kawo mashi agaji.
Ba zato ba tsammani ya ji Sautin dirar wani abu daram! tamkar zai fasa kunnansa, tsabar firgitar da yai ne yasa nan take ya sume saman koraren ciyayin.
Wani Gabjejen Bature ne A tsaye cika shigar Kaya na tatattun Ƴan ta'adda babu ɗigon Imani akan fuskarsa, Hannunsa ɗaya ya ruƙe da Bindigar da yai amfani da ita wurin harbin Halittar da ta nannaɗe Jikin Haris, yayin da ɗayan hannun ya ke ruƙe da cigarette.
Hankalin shi a kwance ya ke zuƙar Tabar Cikin ƙwarewa Har ta hanci Hayaƙin Ya ke fita, kwarkwararrun idanuwanshi na akan Haris dake kwance Ya sume, Tuntsirewa Baturen Ya yi da dariya hada ɗan girgiza kanshi, da ƙarƙarfan muryar sa ta Mashaya giya cikin harshen turanci ya ke faɗin
"wani irin ganganci ne ya kawo ka ƙurmin daji da ƙananun shekarun ka, ba ka da hankali ne? Matashi da kai kake son ƙare rayuwarka abanza? Ina iyayen ka su ke"?
kamar zautacce Shi kaɗai ya ke yin maganar shi, sam bai fahimci Yaron Ya sume ba, Sai da Ya gama Magana kafin ya matsa inda Haris yake a kwance, Ya zuƙunna Bayan Ya soke pistol ɗin a qugunsa, Ya sanya hannayensa Biyu Da ƙarfi Yake jan jikin halittar, Har sai da yai nasarar zaro ƙafafuwan Haris daga bakinta, Allah yaso ba ta kai ga Gatsa haƙoranta akan legs ɗinsa ba, da ko ta yi mashi babbar illa, Bayan Ya zame jikin Halittar da karfi Ya jefar da ita gefe ɗaya, yunƙurawa yai ya miƙe tsaye yana kakka6e tafin Hannayensa, Zuƙar Tabar sa Ya ƙara Yi"Bani da zuciyar Imanin da zan Iya taimakon ka, ka gode wa Allah da na raba ka da dabbar nan, da ko yau Ka rasa ƙafar zuwa gidan Iyayen ka" Yana magana yana sakin dariya idanuwansa akan fuskar Haris.
Sautin kururuwar neman a gajin da ya Ji ce Tasa shi Kan ga kunnansa ga iska Don Ya ji da kyau, Muryar Naufal ce Ya ke faman Fasa Ihu, Da gudu Baturen Ya kutsa Cikin Dajin Yana Tunkarar inda sautin Ƙarar ke fitowa, ta wutsiyar idon shi ya hango gifcin mutune sanye da Jajayen kaya, Ta tsakantsakin jibga jibgan Bishiyoyin dake a kewaye da wurin da yake, Cikin Zafin Nama Ya daka uban tsalle ta tsakiyar wasu bishiyoyi, Kamar an jeho shi Ya faɗo Tsakar wurin da Su Naufal su ke, Gaba ɗaya sun fita hayyacin su, Halittun sun kewaye su sai gurnani su ke yi, Naufal da javed sun ƙanƙame Juna, Kuka hada majina fuskokin su jaga jaga da hawaye, wandunansu a jiƙe sharkaf da ruwan fitsarin da suka saki, Ɗan iskan murmushi dangerous terrorist Ya saki kafin Ya zaro bingidar da ke soke a qugunshi, Ya saita Jikin Halittun ɗaya bayan ɗaya yake sakar masu alburushi, duk wadda ya harba nan take Tsakiyar Cikinta yake tarwatsewa Ƴan hanji su fito waje, Sautin harbin bindigar da basu ta6a ji bane Yasa su rikicewa Kusan atare suke yanke jiki saman koraren Ciyayin suka faɗa a sume, Tuntsirewa Baturen yai da dariyar shaƙiyanci Yana faɗin
"Yaran nan kuna da ban dariya, Sai ka ce ba maza ba? Kun iya shiga daji amma ba ku Iya faɗa ba? Zaman gida da sanya buje zaifi da cewa da ku, In yaso kun cigaba da taya iyayen ku shiga kitchen yin girki" acikin harshen turanci ya ke yin maganar.
Gabanshi Ne yai mugun faɗuwa Jin ƙarar Jirgi A cikin kunnuwansa, Da sauri Ya kai idanuwansa saitin rassan bishiyoyin da suka lullu6e sararin samaniya, nan ta ke yanayin fuskar shi Ya canza daga annuri zuwa tsantsar baƙin ciki, fargaba da tashin hankali, Juyawa yai da gudun gaske tamkar zai tashi sama Haka ya dinga buga uban tsalle Yana gudun Ceton, ga dukkan alamu bai da gaskiya shiyasa ya ƙe ƙoƙarin gujewa waɗanda suka kawo mashi Hari, tuni Ya jima da jefar da tabar hannun sa, kwata kwata Baya a cikin Hayyacinsa, shi kansa baisan in da ya ke wurga ƙafafuwanshi ba, saboda tabar firgicin da ya shiga, ko ma su wanene su ka biyo shi sun shammace shi bai yi tsammanin za'a gano inda ya 6uya ba.
Sautin Ƙarar danƙareran Helicopter mai saukar angulu Ƙirar UH-60 Black Hawk mallakin Sojin Ƙasar amurka ne Ya karaɗe ko'ina Na Cikin Dajin Evil forest Hatta rassan bishiyoyin da ke a cikin dajin girgiza su ke yi saboda ƙarfin iskar fankar Jirgin, har wani jijjiga ya ke yi tamkar zai fasa dodon kunnan mutun, Shawagi ya ke yi a saman Iska Yana kewaye ko'ina.
Hot soldiers din da ke a tsaye baƙin ƙofar jirgin zafafan gaske fusatattun sojoji masu ji da ƙarfi, cikin shigarsu Ta ka ki sun ɗaura ɗamarar Ya ki, Ɗaya daga cikin su Hannayen sa biyu Na ruƙe da Telescope abun hangen nesa, Ya kanga shi saitin idanuwansa, Sojan da ke a gefen shi Yana Ruƙe da Tactical phone wayar da sojoji ke Yin amfani da ita wurin yin sadarwa da Manyansu dake acan headquater, Cikin Harshen turanci Ya ke Sanar da su cewa Sun ƙaraso Dajin ayanzu hake suna kewaye shi domin gano Location ɗin da ɗan Ta'addan Ya 6uya a dajin.
Me ruƙe da abun Hangen nesan ne Ya soma magana Yana ɗaga murya ya ke faɗin A samu wuri a sauke Jirgin Yana zargin me laifin Yana a yankin da su ke, Jin maganar Shi Yasa sojojin dake sarrafa Jirgin su ka Soma ƙoƙarin Samun wurin Da zasu Sauka, A hankali helicopter ɗin Ya ke yin ƙasa tunkafin ya ƙarasa direwa, Sojojin suka soma diddirowa ƙasa Sautin Army boots ɗin dake a kafarsu Yana bugun ƙasa kamar zasu dare ta, Hannayensu ruƙe da Jibga jibgan bindigu, Haka zalika qugunansu na soke da pistols ƙananun bindugu, Sun rufe kawunansu da helmet (hular kwano) Hatta faces ɗin su ba ka Iya gani, Iya idanuwansu ne kaɗai a bayyane, Kusan su shidda ne su ka sauko daga jirgin, Da hannu Commender ɗin su ya rarraba su zuwa gida Uku, kafin ya basu Umarnin shiga Dajin, Da gudun gaske Su ka faɗa cikin zafin nama su ke kurɗaɗawa Cikin ƙurmin Dajin, Babu tsoro ko fargaba suna da ƙwarin gwiwa akan aikin su da ƙwarewar su, kuma suna da tabbacin za su yi nasarar Yin aikin da aka turo su, saboda duhun dajin Da fitilu masu haske su ke yin amfani wurin haska gabansu.
Gaba ɗaya sun Yi matuƙar galabaita, tun suna tiƙar gudu Hancin Angel Ya soma bleeding zufa duk ta wanke fuskokinsu da jikinsu, Maƙoshinsu ya bushe ƙamas sai azabar raɗaɗi da ƙaiƙayin da ya ke yi masu
ƙafafuwan su Zogin azaba su ke yi masu, Sun rasa ina zasu tsoma ransu su ji daɗi, Suna a tsaka mai wuya tsakanin mutuwa da rayuwa, Kurar dake a biye dasu Tana gab da zata cimmasu, Wani irin uban tsalla ta daka tana Gurnani Ta takaiwa Ƙafar Angel Cafka da haƙoranta, wata irin gigitacciyar ƙara ta fasa ita da Gabriel a matuƙar razane.
Kurar na ƙoƙarin Gutsire ƙafar Ba zato ba tsammani, Sautin dirar bullet Ya ratsa kunnuwan su, Basu san daga Ina aka harbo bullet ɗin ba, Gaba ɗaya ya tarwatse Kan kurar, Nan take ta saki ƙafar Angel Ta faɗi ƙasa tana birgima, wata irin nauyayyar ajiyar zuciya Gabriel Ya sauke Yayin da zufa ke cigaba da wanke fuskarshi, angel kuwa Tsabar firgice ne Yasa ta yanke Jiki Ta faɗi ƙasa a sume tamkar matatta.
Hankalin Gabriel Ba ƙaramin tashi yai ba, Ganin yadda Angel ta zube, Cikin shessheƙar kuka ta wanda ya gama galabaita muryarsa na kakarwa ya furta sunan ta da ƙarfin"Angel! no!No! Don't die Angel, Na shiga Uku, Pls Angel ki tashi Ina zansa rai na!"
Fuskarsa sharkaf da hawaye yake yin maganar, Zuciyar shi a karye Ya zube saman gwiwowinsa agaban Angel, Ya dinga kuka yana jijjiga jikinta Da hannayenshi, Sam baya acikin hayyacin sa, shiyasa ma bai yi tunanin Su wanene suka kashe Kurar ba, duk a tunanin shi Angel ta mutu ne, duk yabi ya zauce ya rasa madafa.
Jin Takun Tafiyar Mutanan da ke tunkaro shi ne yasa shi saurin wurga eye balls ɗinsa da suka kaɗa jawur Yana duban su, Sojoji ne Su biyu Hannayen su Ruƙe da Bindugu, duk da baya acikin hayyacinsa saida Ya zabura yana neman guduwa a zaton shi Gianta ne na gidan kurkukun ƙaddara.
Kakkausar Muryar Sojan ce ta ratsa kunnuwanshi"Don't Move or else i will shoot ur head wit My gun"
Wannan maganar da ya yi ce tasa Gabriel dakatawa da yin tafiyar ba tare da ya juyo ya kalle su ba, ya soma magana cikin rawar murya
"Just kill me so that I can finally rest, Na rasa ƴan uwana, bani da burin cigaba da yin rayuwa a duniyar nan, ku kashe ni kawai idan ba haka ba ni zan kashe kai na" Yana magana zufa na tsastsafowa ta jikin fatar shi.
Muryar Sojan ce ta kara ratsa kunnanshi cikin harshen turanci yace
"ba zamu kashe ka ba, rayuwarka tana da mahimmanci a wurin mu, Aikin mu shi ne mu shiga tsakanin ku da mugun da ya yi garkuwa da ku Ya kawo ku cikin Dajin nan, Idan ka bamu haɗin kai zamu mai da ku ƙasar ku" tun da Sojan Ya soma Yi mashi magana Cikin kwantar da murya, sai ya ji natsuwarshi ta fara daidaita, kuma ya fahimci ba jami'an kurkukun ƙaddara ba ne.
Da sauri Gabriel Ya waiwayo baya yana dubansu, a jere suke tsaye su biyu, Yawu ya haɗiya Muryarshi still adabarbarce ya furta"idan har dagaske kuna son taimakona, akwai ƴan uwana da suke a cikin dajin, muna acikin mayuwacin hali, wasu mugayen halittune suka biyo mu, ina tsoron su kashe min su" Jin wannan Maganar Yasa ɗaya daga cikin sojojin ya tasa ƙeyar gabriel Gaba, Zuwa Cikin dajin.
Yayin da ɗayan Sojan da su ka bari a tsaye gaban Angel ya soma magana ta hanyar yin amfani da tactical phone ɗin hannun shi, Ya sanar da commender game da yaran da suka tsinta a dajin, suna zargin ɗan ta'addan ƙasarsu ne ya gudo dasu cikin dajin yai garkuwa da su don ya kare kanshi daga farmakin da zasu kawo mashi.
Commender ɗin ya ba da Umarnin A tattaro yaran dukansu, a lokacin har sunyi nasarar Cafke ɗan ta' addan da su ka zo kamawa, Mugun ɗauri suka yi mashi duka jikinshi suka nannaɗe da igiya suka ɗaure shi tamau bayan sun yi mashi allurar kashe ƙwarin Jiki gudun kada ya kubce masu saboda sanin shi da su ka yi, mugun ɗan ta'adda ne mai hatsarin gaske, A cikin jirgin suka wurga shi.
A saman Kafaɗa Sojan Ya ɗaura Angel Ya nufi wurin da suka sauke helicopter ɗinsu, A ciki ya shigar da ita ya kwantar, Bada jimawa ba, sai ga wasu sojojin su biyu ɗauke da Nufal da Javed saman kafaɗin su. bayan sun shigar dasu Cikin jirgin sai ga kira daga Ɗayan Sojan daya tafi da Gabriel gaba ɗaya suna jin muryarshi ta cikin wayarsu, sanar da su yai akwai sauran yaran da zasu nemo acikin Dajin, Yana buƙatar a turo Wasu sojojin da zasu ɗauke su, Umarni commender yaba sauran sojojin da suka dawo akan su je su zaƙulo sauran yaran, Da gudu suka kutsa cikin Dajin.
Gabriel da sojan da ya taso ƙeyar sa suna cikin Tafiya sai faman wurwuga ido gabriel yake yi a ƙoƙarin shi na ya gano inda su Batul su ke, Gabanshi sai faɗuwa ya ke yi tsoron sa kada ace halittar nan ta hanɗame su, Har zasu gifta kwatsam ta wutsiyar ido Soja Ya hango launin jajayen kaya ƙuɗundune cikin koraren ciyayi da sauri ya furta"wait" hakan yasa Gabriel dakatawa da yin tafiyar, Reverse sojan yai tare da juyar da kanshi Ya wurga ƙwayar idanuwanshi saitin wurin da ya hango jan uniform ɗin, Gabriel na yin tozali da su da ƙarfi ya furta sunan Azeeza, da gudu ya nufi wurin da suke maƙale da juna babu numfashi, Sojan na ganin Ya tunkari wurin shima yabi bayanshi, agabansu Gabriel ya zube saman gwiwonsa Yana Ambaton sunayen su cikin karyayyiyar murya ta wanda ya Sare, kafin sojan Ya motsa Sai ga sauran Sojojin da commender ya turo sun kutsa ta wurin da suke. suna ƙarasowa ba tare da 6ata lokaci ba suka ciccire ƙayoyin da suka sargafe ƙafafuwan Azeeza da jemimah, Kafin su ka ɗauke su saman kafaɗunsu, da hanzari suka juya dasu zuwa cikin jirgin. Bayan tafiyar su Sojan Ya ce da Gabriel Za su Iya tafiya yanzu? Da sauri ya girzgiza kai, cikin disasshiyar murya ya faɗa mashi"Akwai sauran mutun uku da babu acikin su" Sojan Yace ya tashi su shiga neman su, Ba su buƙatar 6ata lokaci, Akwai Iya adadin da aka basu, Idan har ya cika zasu tafi ne" jin haka yasa Gabriel Miƙewa shi kansa ba ƙoshin lafiya ne dashi ba, ƙarfin haline kawai. A ƙalla sun shafe tsawin mintuna goma shabiyar suna neman Su Batul, Sai kurɗaɗawa suke Yi cikin dajin babu su babu alamarsu, ganin zasu 6ata lokaci yasa sojan ce mashi"Su tafi kawai, Zai iya yiwuwa sun rasa rayukansu ne" kamar ƙaramin yaro haka Gabriel ya fashe mashi da kuka tare da zubewa saman gwiwowinsa Ya ruƙe ƙafafuwan Sojan Ya dinga kuka Yana roƙonshi akan kada su tafi su bar ƴan uwan shi a dajin, Shi yana ji aranshi suna araye wata'ƙil sun faɗa wani wurin ne sakamakon muggan halittun da suka tsoratar dasu,' Tsawa Sojan Ya daka mashi a harzuƙe Ya hambare Gabriel da ya ruƙe mashi ƙafa.
Muryarshi a kausashe yace "Get up and let's go. Otherwise, we'll leave you here in the forest." Hawaye na bin kuncin Gabriel, Ya girgiza mashi kai yana faɗin"bazan Iya tafiya nabar su ba, Atare muka sha wahala, bai kamata mu tsira mu ƙyale su ba, ni banga gawarwakinsu ba, Tayaya zan yadda sun mutu," numfashi yaja kafin ya ɗaura da cewa"Zaku iya tafiya da waɗanda kuka ɗauka, Ni ku barni anan zanje na nemo ƴan uwana ko da ace zan rasa raina ne" Juyawa Sojan Yai a fusace Ya soma tafiya, Sai da yai nisa zuciyarshi ta soma tariyo masa kalaman Gabriel, Dakatawa ya ɗanyi yana wani tunani, ga dukkan alamu kalaman sun ta6a zuciyarshi, A hankali ya ɗan waigo Baya yana dubanshi, Bawan Allah Ya kifa kansa saman ciyayi, Sai kuka yake yi kamar ranshi zai fita, takaicine ya ishe shi ga samu ga rashi, Yasan muddin sojojin suka tafi shida barin dajin har bada, a ƙarshe ma ya rasa ranshi, sai dai baya jin zai Iya binsu alhalin sauran ƴan uwanshi da suka sha wahala suna acikin dajin! ya zasuji idan suka dawo hayyacinsu suka taras babu su? Me zai biyo baya?
A lokacin da Gabriel baiyi tsammani ba, muryar Sojan Ta ratsa kunnanshi
"Yaro ka ci albarkacin sarƙar cross ɗin da ke a wuyan ka, A karo na biyu zan Taimake ka, mu gano sauran Ƴan uwan naka" wani irin farin Cikine ya lullu6e Gabriel Jiki na rawa ya yunƙura Ya miƙe, kafin su fara tafiya sai ga sauran Sojojin da su ka je kai su Azeeza hada ƙarin wasu kusan su shidda suka nufi Dajin neman sauran Yaran, Marece ya nutsa abun da sojojin suke gudu dare ya yi masu a dajin saboda Sanin hatsarin dake gare shi, Daƙyar Gabriel Ya samu Ya gano masu hanyar wurin da suka yi shimfiɗarsu, da gudu Ya nufi Danish da ke a kwance yana sharar baccin shi.