Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 19

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 19

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 19: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 19. Tun kafin sojojin su ƙarasa Gabansu yai wani irin…

3,339 words

Tun kafin sojojin su ƙarasa Gabansu yai wani irin faɗuwa saboda razanar da su ka yi da ganin shi, Wani abu ya ɗaure masu kai, har saida su ka kalli junansu da alamun ruɗu akan fuskokin su, Ba Iya kyawun Fuskar Danish bane Ya girgiza su, Zazzafar surar Jikinshi Ta yi matuƙar rikitar dasu, Kaf a cikinsu babu mai kalar ƙirar ƙarfin shi, Hakan ba ƙaramin kokwanto Ya saka masu ba acikin zuciyoyin su, har sun fara kokwanton Anya kuwa ɗan ta'addan da suka Biyo ne yai garkuwa da yaran? Ta ya ya za'ai ɗan ta'addan Ya iya sato wannan jibgegen ƙaton mai ƙirar sadaukan Yaƙi, a ganin su ko shi ɗan ta'addan bai kama ƙafar Matashin yaron ba wurin zubin halittarshi.

Muryar Gabriel da sassarfa yake Ambaton sunan danish Hannayenshi duka biyu akan jikinsa sai jijjigashi yake yi yana faɗin"Danish ka tashi, mun samu taimako za'a fidda mu daga cikin daji, Har ma an tafi dasu Angel, pls ka tashi, Bana so mu tafi mu bar ka"

Ko motsi Danish bai yi ba, ganin haka yasa shi juyawa yana kallon Sojojin, Sun ƙame a tsaye suna kallon Abun al'ajabi kusan suman tsaye sukayi yayin da suke kallon Danish "Dan Allah ku taimake ni, ɗan uwanmu ne, haka Allah ya halicce idan Yana yin bacci yakan ɗauki tsawon awanni bai farka ba," a ruɗe yake kora masu bayani, duk don ya samu su tafi da Danish kada suce zasu barshi anan, don ya fahinci tashin shi ba yanzu ba

Daƙyar ɗaya daga cikin sojojin ya iya shanye mamakin shi ya sarrafa kanshi wurin furta" bai da lafiya ne? Ko ya suma ne"?

"A'a, bacci ya ke yi, kuma ba zai Iya farkawa yanzu ba, ...."tun kan ya ƙarasa maganar ɗaya daga cikin soldiers ɗin Ya zaro penlight ya zuƙunna agaban shimfidarsa, da yatsun hannayensa yai amfani wurin gwale idanuwan Danish ya haskasu ya tabbatar da yana araye ga numfahi na fita a tsanake, Kallon sauran sojoji yai"he's alive" jin haka yasa suka gasgata maganar Gabriel, mutun Biyu suka ranƙwafa tare da ɗaura hannayensu da nufin su cuccu6i Danish sai dai wani abun ɗaure kai ko motsi baiyi ba, saboda tsabar nauyin sa duk irin ƙarfin da Allah ya yi ma sojojin na halitta da kuma na horon aikin da suka samu baisa sun Iya cuccu6ar Danish ba, A ƙarshe suka Yanke shawarar zuwa ɗauko stretcher domin ɗaukar shi, zaifi Yi masu sauƙi, abun ɗaukar Majinyatane da ake amfani dashi, Yana da maruƙi a jikin sa, saman shi faɗine dashi kamar allo, bayan sun ɗauko stretcher ɗin Saida suka haɗa ƙarfi su huɗu tukunna su ka iya cuccu6ar Danish tare da ɗaura shi saman abun ɗaukar, su ka ɗaga shi har zuwa Bakin helicopter din kafin suka samu damar shigar dashi ciki, Bayan sun tafi da danish Ɗaya daga Cikin Sojoji biyu da suka rage Ya ɗauki Back pack ɗinsu da ya gani a jikin bishiya, don suna buƙatar duk wasu shaidu da za su zamar masu hujja.

da hannu ɗaya ya ruƙo jakar ɗayan hannun kuma ya ruƙe hannun akwatin kayansu Yaja shi zuwa Bakin jirgin.

A can Cikin Dajin Gabriel ne Ya rage tare da Sojan nan, Suka kuma kutsawa cikin dajin Don ya sanar mashi akwai sauran Ƴan uwanshi, Abun dai ya ɗaurewa Sojan kai, Su fa duk a tsammaninsu ɗan ta'addanne ya yi garkuwa da su daga ƙasar su america Ya shigo da su Dajin, Saboda Yaran sunyi kama da mutanan ƙasarsu, Hasken fatarsu da Doguwar sumar kawunansu, a hasashensu kenan, sai dai duk da haka sun ɗanyi mamakin wasu abubuwa da suka sanyasu yin al'ajabi, tayaya har ɗan ta'addan ya iya guduwa dasu bayan ƙasarsu tana da mugun tsaron da babu wani shege da ya isa Ya ƙetare ta cikin Salama, Abu na biyu Ta ya ya Ɗan ta'addan Ya iya ɗaukar mutun mai mugun Nauyi irin matashin saurayin da suka gaza ɗagawa? Abu na uku da ya ɗaure masu kai Uniform ɗin Jikin yaran masu ɗauke da numbobi sunyi mamakin hakan.

Suna Cikin yin tafiya, Zuciyar Gabriel na dakan uku uku tamkar zata faso kirjinshi ga kishirwa da ya ke ji, babban tashin hankalin shi Ina Su Batul suka kutsane a cikin Dajin? Ga dare yana shirin yi masu adajin, fargabansa kada sojojin su ce zasu tafi.

"Kana tunanin ƴan uwanka zamu same su? Lokaci Yana ƙure mana" Sojan ne yai mashi maganar, gabriel bai samu damar amsa mashi ba saboda tashin hankalin da ya ke aciki, Sai faman wurwurga ƙwayar idanuwansa ya ke yi akan bishiyoyin dake a kewaye dasu, Suna Cikin yin tafiya suka ƙaraso gaban wannan ramin mai ɗauke da ta6o, har zasu gifta shi Kwatsam Sojan Yaji ya taka wani abu, Da sauri Ya ɗage ƙafarshi yana kallon Warin Slipper ɗin dake asaman ciyayin, Gabriel na ganin takalmin Ya zuƙunna tare da kai hannu ya ɗauke shi, Gabansa ne ya faɗi A gigice ya kalli sojan tare da furta"Takalman Ƴar uwata ne!" Ya gane slippers ɗinsu ne Da tsohuwa Tamira tai masu kyautarsu, dama tunda suka shigo Dajin da takalmansu suke yawo a ƙafafuwansu, shiyasa ko ƙaya ba ta ta6a shigarsu ba. "Dan Allah ka taimaka mun, wlh takalmansu Batul ne ƴan uwana" Muryarshi na rawa yake maganar, cikin ƙagara. Waige-waige Sojan ya ke yi yana bin ko'ina Na dajin da kallo, Kafin ya sauke idonshi akan Ramin ta6on, kasancewar Sojoji suna da ƙwarewa wurin sanin takan Daji, Nan take ranshi ya bashi cewar Ta6on da ke a wurin Ramine, mutun zai Iya rubzawa cikinsa, musamman wanda ke gudu cikin fitar hayyaci.

Matsawa yai gaban ramin, Bayan ya soke bingidar hannun shi a ƙugun shi, Ya ɗan zuƙunna saman ƙafarshi, a tsanake Ya tura hannun shi Cikin ramin ta6o, Cikin sa'a Ya damƙo gashin ɗaya daga Cikin su, matsar da hannun shi yai ya ruƙo Hannunta, Ya ɗago da ita gaba ɗaya jikinta ya 6aci kaca kaca da ta6on baka Iya ganin komai na fuskarta, hatta Gabriel bai gane wacece a cikin su ba, A ƙasa sojan ya kwantar da ita tare da ƙara zura hannun shi Ya ƙara cafko hannun wata ya curo ta, bayan ya kammala zaraso duka ukun Gabriel Yace mashi suke nan babu saura, Jin haka yasa Sojan Zaro wayarshi Ya sanar ma sojojin dake a bakin helicopter din cewa sun ƙara samu Yara Uku azo da stretcher a ɗauke su, Cikin ƙanƙanin Lokaci sai ga sojoji sunzo da abun ɗaukar, duka ukun suka ɗaurasu saman shi kamar tsummokarai haka suka nannaɗe.

Sojoji biyu ne suka tafi dasu zuwa Inda jirgin ya ke, Hankalin Gabriel Ya ɗan kwanta sam ya manta da Haris saida suka kamo Hanya zasu Nufi jirgin ba zato ba tsammani su ka ci karo da haris a sume, Ba tare da 6ata lokaci ba, Sojan da suke atare Ya sa6e shi saman kafaɗa, suka nufi Jirgin Bayan sun Shiga su dukansu. Matuƙar jirgin suka Tada shi, Da wata irin jijjiga tayoyin jirgin su ka soma motsawa suna yin tafiya sannu a hankali, Gabriel da ya kasance shi kaɗai idon shi biyu, farin Ciki duk ya cika shi, sam baiyi tunanin wace ƙasa za'a kaisu ba, hankalin shi bai kai nan ba, fatan shi su bar dajin Cikin ƙoshin lafiya.

Bayan tashin jirgin sama Ɗaya daga Cikin sojojin dake a tsaye bakin ƙofar helicopter ɗin ne Ya kanga Tactical phone ɗin hannunsa jikin kunnansa Yana magana Cikin Harshen turancin muryarshi na fita da amon murya saboda ƙarfin iskar Dajin

"We successfully apprehended the criminal. We are now on our way back to the U.S. with the eleven children we found in the forest." (Munyi nasarar cafke mai laifin, yanzu muna akan hanyar mu ta dawowa U.s, tare da yara goma sha ɗaya da mu ka samu a dajin)

Da wani irin speed jirgin ya karya kwana ya miƙi hanyar komawa ƙasar da ya fito.

*Alhamdulillah Finally Ex-prisoners sun Bar Evil forest Fatan Nasara*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E12🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._

*GIDAN ƊAN IYA*

Gaba ɗayan su sun Hallara a bakin Entry hall na shiga palourn gidan, Mommy da Mami sun yi matuƙar yin kyau cikin shigar Lace, Zahra da Aneelerh sai Abie da Uncle ɗan Iya sun yi shiga ta alfarma, Bakomai ne yasa su fitowa ba fa ce tarbar Su Hajiya adama, A ƙagare su ke da ganin baƙin nasu, badajimawa ba su ka kira Aneelerh awaya su ka sanar da ita cewa sun shigo garin abuja, har ta tura masu da addrress ɗin gidan.

Ƙarar Horn ɗin motarsu ne Yasa kowan nan su Sakin fuskarshi, da sauri mai gadi Ya fito daga ɗan ɗakin sa, Ya je ya buɗe masu gate.

A hankali Danƙareriyar Motar uncle abdallah ƙirar Kia optima ta kunna kai cikin gidan kai tsaye ya nufi wurin Ajiye motocin su, bayan yai parking ɗin motar, Ya fito daga ciki fuskar nan ɗauke da annuri, ya ɗauki wankan shadda gezna, ƙafafuwanshi na asanye da patent leather shoes launin Shaddar shi, ƙamshi ta ko'ina.

Zagayawa yai ta other side ɗin motar ya buɗe ma Hajiya adama ƙofa, ƙafar ta ta fara zurowa nan take Zahra ta ɗan zaro ido tare da kallon Aneelerh, murmushi gefen fuska Aneelerh ta sakar mata don ta fahimci abunda ya sa zahra mamaki, wato tsadar High hills ɗin dake ƙafar Hajiya adama.

Zahra ta ƙware wurin sanin farashin Kaya, A kunne ta yi ma Aneelerh whispering

"Surukar ki Ta ji naira yasin, Takalman ƙafarta kalar na saratu obinna ne" girgiza kai Aneelerh ta yi ba tare data tanka mata ba.

Lokacin da Hajiya Adama ta ƙara sa fitowa daga Cikin Motar ba ƙaramin tafiya ta yi da imaninsu ba, saboda tsabar wankan kece rainin da ta ɗauka na tsadadaddan Swiss cord lace launin brown mixed wit yellow, Riga da zani ne ta daura, kanta yasha ɗaurin ɗan kwali, sarƙar wuyanta da awarwaron hannun ta, da zabbanta duk na zinari ne, ta yarfa mayafin kayan saman kafaɗarta, babu make up a saman fuskarta zallar kyan da Allah ya yi mata ne, Hajiya adama akwai kyau ga diri.

Kallon abdallah ta yi fuskarta ɗauke da murmushi, da hannu yai mata nuni da surukansu da ke a tsaye suna fuskantar su

"mu je ko?" Sai lokacin ta lura da su, tafiya suka soma Yi a jere tunkan su ƙaraso Zahra take ta faman ingiza kafaɗar aneelerh

"ki je ki tarbo su,"

kunya ta hana Aneelerh zuwa, har saida suka ƙaraso, Abie Yana dariya Ya ruƙe hannun Abdalla suka fara yin gaisuwarsu ta manya"Marhaban marhaban lale surukai na gari, Sassannun ku, kun sha hanya, ku ƙaraso ciki" Ya ja hannun abdallah, Mamie da hajiya adama suka rungume juna fuskar kowan nan su ɗauke da murmushi, bayan sun raba jikinsu, Ummi ta miƙe mata hannu suka gaisa a mutunce"Sannu da zuwa Hajiya, mu shiga daga Ciki" ta yi maganar, tare da jan hannun hajiya adama wadda idonta ke akan Aneelerh, sai faman noƙe kai ta ke yi, "Kunya kamar bafullatana, Ni kaina da nake bafullatana Bani da kalar kunyarki," da zolaya hajiya adama ta yi maganar, Yayin da su ke shiga cikin babban falourn gidan, daddaɗan ƙamshin turarensu ya gauraya da sanyin A.c. A saman soma mai mazaunin mutum uku Mami da ummi da hajiya adama su ka zauna, Abie da Uncle ɗan iya su ka zazzauna saman 2 sita, Aneelerh tana zaune saman one sita, Yayin da zahra ta ɗan zauna saman hannun sofa ɗin da Aneelerh ke zaune, sai faman sakarwa juna murmushi suke Yi, Gaisuwa ta musamman suka ƙara yiwa junan su cikin girmama juna da mutuntaka.

Uncle ɗan Iya Yana faman washe baki Yace"Abdallah Kai ne ka koma haka?gaskiya mun daɗe bamu haɗu ba, tun lokacin da ka fito daga cikin mota, idanuwana su ka yi tozali da kai sai da gabana ya faɗi araina nace ina muka samu baƙin Bature, Abdallah hutu ya zauna maka daga kai har Hajiyar taka kun yada zumunci ko in ce mun yada zumunci Allah dai ya shiryemu" dariya suka saki gaba ɗayan su.

Ummi tace"Ya gajiyar tafiya? Nasan Kun jigata sosai, tafiya daga jos zuwa abuja ba abune mai sauƙi ba, kun ma yi ƙoƙari dana ganku da kuzarin ku"

mami ta ɗaura da cewa"Alhamdulillah mun gode ma Allah da ya kare mana ku ya tsare mana ku har ku ka ƙaraso Lafiya, wannan abun farin ciki ne agare mu, gamu ga surukanmu, mutane masu ƙima da daraja, muna ƙara yi maku barka da zuwa" Maganar Mami ta yi matuƙar faranta zuciyoyinsu.

Musamman Hajiya adama har saida ta ɗan saki murmushin da ya bayyana jerarrun fararen haƙoranta.

A tsanake tace "A gaskiya ba zamu Iya misalta farin Cikin da muke aciki ba, ni dama tun da muka fito daga cikin mota raina Ya bani munzo gidan mutunci da karamci musamman da naji gidan Uncle ɗan Iya ne Masha Allah, Fatan mun same ku lafiya" atare suka haɗa baki"Lafiya lou Alhamdulillah"

Uncle abdallah ne ya soma yin magana cikin dattako da halin girma "Mun jin daɗin samun ku cikin ƙoshin Lafiya, Abun farin cikine wannan kuma muna godiya da irin tarbar da muka samu, Ina yi mana fatan kamar yadda muka haɗu anan, Ubangiji Allah Ya haɗamu A gidan aljanna alfarmar Annabi muhammad SAW, kusan atare suka haɗu wurin furta kalmar SAW

"Yakamata mu fara yiwa annabi Salati" Abie ne yai maganar, tare suka ɗaga hannuwansu bayan sunyi salati ya ci gaba da jero masu addu'o'i Suna amsawa da ameen ameen Bayan ya kammala, Uncle ɗan Iya ya wurga idon shi kan Aneelerh da ke ta faman sakin murmushi tana noƙe kai Jin Muryarshi tasa ta ɗago da ido tana kallon shi Daƙuwa ya sakar mata"Ungo nan, jira ki ke sai mun ce ki je ki gaishe da surukan naki? yarinya sai ka ce jinin fulani" Tsuntsirewa su ka yi da dariya gaba ɗayansu, Yadda yai magana yai matuƙar basu dariya hada Aneelerh, Da sauri ta miƙe daga saman sofa ta nufi Hajiya adama daga ƙasa saman carpet ta zauna gefen ƙafar Hajiya adama, muryarta ƙasa ƙasa ta furta"Sannunku da zuwa, Ya gajiyar tafiya, ya kuma aka baro mutanan can" ɗaura hannu hajiya adama tayi saman kafaɗar Aneelerh

"Lafiyalou daughter in-law Fatan na same ki Lafiya" Aneelerh ta amsa da lafiyalou, kafin ta matsa gefen uncle abdallah Ta gaishe da shi, da fara'a ya amsa mata

Bayan sun gama gaisawa da aneelerh, Zahra ta gaishe dasu, suka amsa mata Kafin daga bisani, Mami tace"bismilla mu shiga ciki, Ku huta kada mu Cika ku da surutu, " ta faɗi hakan ne don tasan yanayi na matafiya yafi buƙatar hutu, Miƙewa su ka yi Mami da Abie na agaba Hajiya adama da uncle abdallah suna abiye dasu, wuce abie yai da uncle abdallah zuwa ɗakinsa, Itama mami ta wuce nata ɗakin tare da hajiya adama bayan tafiyar su.

Fira ta 6arke tsakanin Zahra da Ummi, a lokacin Uncle ɗan Iya ya fita waje domin amsa kiran da akayi mashi a waya

"Wlh ummi takalman ƙafarta kalar na saratu obinna ne, kinsan ko kuɗinsu yakai dubu talatin" Ɗan zaro ido Ummi ta yi" Tab Aneelerh ashe surukan ki Attajiran masu kuɗi ne, ai naga sarƙar wuyanta da awarwaron hannunta duk na zanari ne, gaskiya kin taki sa'a, Yarinya mai ƙashin arziƙi,"

kwa6a fuska Zahra ta yi"ni kuma mai ƙashin tsiya ko"? ummi na dariya tace"Ni dai bance ba, kema ina maki fatan miji na gari da surukai na gari" yatsina fuska ta yi ƙasa ƙasa da murya ta furta"Suruki na gari kamar Owais, surukai na gari hamshaƙan masu kuɗi irin hajiya sarauta" Aneelerh dake zaune saman carpet ta miƙe ta koma saman sofa ta zauna Ummi ta kalleta"nasan zasu buƙaci ganin jikansu, gashi ya tafi school till 6 na marece za'a tado su saboda lesson na Islamiya da ake Yi masu, " zahra tace"Zan kira mahboob A waya ya je ya ɗauko shi, Ni fa dama can banso aka sanya shi hada islamiyyar ba, ace kullum sai ƙarfe shidda zai dawo gida, in banda weekend,"

Harara ummi ta ɗan watsa mata"Sannu Uwarsa, islamiyarce ke ba ki so ya yi kenan sai dai na bokon" Girgiza kai zahra tayi"Ba haka nake nufi ba ummi, Yaron ya yi ƙaranta brain ɗinsa ma ƙarama ce ta ya ya ki ke tunanin zai Iya ɗauke duk abunda aka koya masa"

Tun da suka fara magana aneelerh ta yi shiru tana kallonsu, acan ƙasan zuciyarta kewar baby junaid ce ta addabeta, maganar zahra tasa duk ta ji ba daɗi ita kanta ba ta son Yana kaiwa har ƙarfe shidda sai dai ba yadda za ta yi ita kanta tana so yaronta ya saba da karatun boko dana addini.

Tsawon lokaci suna fira a tsakanin su jefi jefi har aka fara kiran sallah, Abie da Uncle abdallah suka fito da haramar zuwa masallaci, a harabar gidan suka yi arba da uncle ɗan Iya zaune saman Kujera Yana danna waya, Abie ya ce da shi Ya tashi su je masallaci, A nan suka jira shi ya shiga gidan ya ɗauro alwala kafin ya dawo suka ɗunguma zuwa masallacin dake a kusa da gidansu

Acan Cikin Gidan kowa ya koma ɗaki domin yin sallar magrib, hankalin Aneelerh Yaƙi kwanciya, Jin shiru mahboob bai dawo mata da yaronta ba, Gashi har an kira sallah. A zaune ta ke saman darduma hannayenta Biyu sama tana jera addu'o'i tasha dogon hijabinta.

Ba zato ba tsammani ta ji saukar mutun saman Bayanta, Ya ƙanƙameta Yana tiƙar dariya"babyn mommy is back" Gabanta harya faɗi sai da taji muryarshi tukunna ta sauke ajiyar zuciya, haɗi da ɗan sakin murmushi jin ya kirata da sunan da malamansu suke kiranshi wato babyn mommy, bayan ta shafa addu'ar, ta zagayo da hannunta ta ruƙo damtsen shi ta zagayo da shi tare da zaunar da shi saman laps ɗinta, Kamar kullum fuskarshi duk jirwayen hawaye, uniform ɗin jikin shi riga ce fara sai wando red colour, daga saman rigar akwai ƴar coat launin Ja, kafin ya ta fi school saida ta gyara mashi sumar kanshi amma yanzu da ta kalli sumar kan nashi A hargitse ta ke. Idanuwanshi luhu luhu ya furta"Mommy, kin ga banyi kuka ba yau ko? Ai kince in daina" smiling softly tace"jirwayen menene akan fuskarka" tai maganar tana nuna hawayen da indext finger dinta, kwa6e mata fuska yai"mommy ai ni bake nayi ma kuka ba, uncle mahboob ne da safe da zamu school, Ya cinye min chocolate ɗina da kika saka min a basket"

idanuwanshi cike tab da ƙwalla yai mata maganar, ranshi ya 6aci.

Ɗaure fuska aneelerh tayi"Na rasa gane me ke damun mahboob, shi bai siya maka ba sai dai ya cinye maka? Tir wlh andai ji kunya"

"Mommy don't worry, Ni ma ai na rama" "Dame ka rama" da mamaki ta yi mashi tambayar, hannu taga ya zura cikin aljihun wandonsa, ya zaro ɗan ƙaramin box mai kyan gaske Ya nuna mata "Menene wannan"? Shu'umin murmushi babyn mommy ya saki"pls mommy kada ki yi min faɗa, inaso yadda ya sani zubar da hawayena shima ya yi kuka, A motar shi na samu wannan, buɗe ki gani abun da ke a ciki" yai maganar yana miƙa mata box din, bayan ta kar6a ta buɗe akwatin, haɗaɗɗen zoben azurfa ne, na mata mai kyan gaske stone ɗin jikin shi har ƙyalƙyali Ya ke yi, Jinjina kai aneelerh tayi"Lallai Mahboob Ya iya kashe na ƴan mata kuɗi amma bai Iya kashe ma ƴan uwan shi ba, dama irinsu babu mai cin moriyarsu sai mata, kowace mai sa'ar ce wannan Ya siyama zobe kuma daga gani mai tsada ne" "Mommy daga ni sai ke, kada ki faɗa mashi ni na ɗauka, Mubar shi yai ta wahalar nema shima Ya ji idan akwai daɗi" Cikin 6acin rai ya ke yin maganar. "Babyn mommy, ai ni farin cikinka shine nawa, don haka kar6i box ɗin nan ka 6oye mana shi cikin rigar pillow," kar6ar zoben junaid yai da gudu ya nufi gado ya haye tare da ruƙo pillow ya zuge zip ɗinshi Ya tura box ɗin, abun mugunta ya samu sai faman sakin murmushi yake yi kamar gonar auduga

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull