Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 27

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 27

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 27: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 27. A Kwance take saman Prayer mat, Tasha Dogon…

3,346 words

A Kwance take saman Prayer mat, Tasha Dogon Hijabi a jikinta duk ta ƙudundune kanta acikinsa, daga gaban dardumar Qur'anic Stand ne, ga dukkan alamu Bacci ne Yai awon gaba da ita a yayin da take Yin karatun al'ƙur ani mai girma.

"Zeenat! Kiran Sunanta da akayi ne Yasa ta firgita a Hazarce Ta farka daga baccin ta ɗago da kanta tana faman zazzare dara daran Kyawawan idanuwanta farare ƙal launin Ocean Blue, Masha Allah Kyakkyawar matashiyar budurwa Kamanninta sak Alhaji musa tamkar yayi kakinta, sai dai Daga gani Farar fatace Haskenta ya ɗare na mahaifinta, Fara ce sol Jawur da ita, tana da yalwatacciyar sumar kai Launin blonde har saman fore head ɗinta kwantaccen gashi ne, ga doguwar fuska, dogon hanci da ƙaramin baki launin pink, Ba ta da ƙiba ko misƙala zarratin siririya ce, abu ɗayane ke da girma a jikinta, dukiyar fulaninta acike suke kamar an jera balon balon.

"Zeenat! Bacci ki ke Yi"? Muryar Mahaifiyartace ta rasa kunnuwanta, da sauri ta zabura ta miƙe tare da wurga ƙwayar idanuwanta kan Mai shigowa ɗakin, babbar macace mai cikar kamala, Ta ɗauki wankan Shadda ajikinta launin Ja, Tasha uban ado akan fuskarta, baturiyace Siririya bata da ƙiba, daga ganin surarta a wurinta matashiyar budurwar ta gado hasken fata da launin ido, da kuma doguwar sumar kai, Hajiya Sarah Uwar gida kuma amarya awurin Alhaji musa, ta ɗaure kanta da kallabi, hakan bai 6oye doguwar sumar kanta da ta sauko har gadon bayanta, Necklace ɗin wuyanta da earrings ɗinta na zallar diamond ne sai ƙyalƙyali suke Yi da ɗaukar ido.

Muryarta Adisashe ta amsa mata"mommy karatun ƙur'ani nike Yi bacci ya ɗauke ni bansani ba" ta yi maganar tana Yin miƙa haɗi da yin hamma

"Ba ki ji dirar motoci ba ne"? Ras Taji gabanta Ya faɗi, Muryarta na rawa ta furta"dad... daddy is he back "?

Ta6e baki Hajiya Sarah tayi"ya dawo tun ɗazu, yanzu haka yana a ɗakinsa, yace baya son takura, kinsan halinsa"

Hankalin Zeenat Ba ƙaramin tashi yai ba, ta rasa gane farin Ciki za ta yi ko baƙin Ciki, Tana son mahaifinta sosai, sai dai tana mugun jin shakkarshi saboda rashin sakar masu fuska da baya yi, duk da wani lokacin idan yaso yana nuna masu so da ƙauna.

Jin ta yi shiru zugudum tana faman zazzare ido Yasa Hajiya Sarah cewa"ya naga kamar baki farin Ciki da dawowarshi"? A hanzare ta girgiza kai" "I'm so happy he's back, na yi murna ai shi ɗinne baya son takura"

Murmushi tasakar mata"Albishirinki"! Da mamaki ta tsayar da eye balls ɗinta kan face din momyn nata "Goro"! "Fari ko ja" "Fari" Matsawa Mommyn ta yi kusa da ita Cikin raɗa ta furta mata"Ba shi kaɗai ya dawo ba, Hada Yayanki Dr shureim yanzu haka Yana kwance a bedroom ɗin da aka ware masa" Tun kafin Hajiya sarah ta ƙarasa Maganar, Zeenat ta zube saman gwiwowinta tare da ɗaura goshinta saman tiles ta yi Sujjada tsabar farin cikin jin anzo mata da sahibinta

"Ah lallai ashe Har yanzu Kina son Yayan naki, Hada Yin sujjada" ɗagowa Zeenat Tayi, tare da miƙewa tsaye Hijab ɗin jikinta sai Ja da ƙasa Yake yi.

"Mommy bazan Iya jurewa ba, Zanje wurin Yayana inyi mashi barka da zuwa" tsantsar farin cikine akan fuskarta

"No kada ki je Yanzu ki bari masu aiki su kammala Girka mashi abinci, In yaso sai ki je ki kai mashi a ɗakinsa, Daddynki ne Ya bada Umarnin A girka mashi abinci hausawa"

Zeenat da takasa rufe bakinta don Murna duk tabi ta ƙagara don a kwaɗaice take da son ganinsa "Na faɗa maki zuwanshi ne Don ki kimtsa, Ki gyara kanki, Nasan Halinki da sanya dogon Hijabi salon kije mashi ahaka, Ki samu Ko ɗan gyalene ki yafa a kafaɗa," turo baki zeenat tayi da ƴar shagwa6a tace"Mommy ae shima Yaya shureim ɗin yafi son mace mai sanya dogon hijabi"

"To ai bance bayaso ba, tun da acikin gidane ki samu gyale ki yafa" ta ƙare maganar da zolaya ta furta"Muslimatun matar limam" Dariya Zeenat ta sanya tana kallon mommyn nata.

"Zan koma kitchen, Ki tabbatar kin shirya da wuri"

Amasa mata tayi da toh

Bayan fitarta, da sauri Zeenat ta cire hijab ɗin jikinta, ta nufi toilet ta shige, cikin Ƴan mintuna ta fito Sanye da bathrobe (rigar wanka) fara Ƙyal a jikinta, hannunta ruƙe da short towel tana tsane sumar kanta, Bayan ta kammala tsane gashin, a gaban tafkeken dressing mirror ta zauna saman chair tana Gyara Jikinta, Hair dryer ta kunna Ta busar da sumar kanta, Bayan ta gama ta soma shafa tsadaddun Mayukan shafawarta dake a jere gaban madubin.

Zeenatu muguwar sangartacciyace ta saba tun tana ƴar ƙarama duk In za ta yi make up ko zata sanya sutura masu aikin gidansu ne ke taimaka mata, saboda ba ta Iya komai na aikin wahala ba, hatta sanya ɗan kunne bata Iyaba wahala take sha, Yau saboda zumuɗin zuwan ya ya shureim bata bari wani ya taimaka mata wurin sanya sutura ba, tun tana agaban mirror mai aiki ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta ta nemi zinin shigowa, ta tambayeta Ko tana Buƙatar wani abu, tace mata a'a taje kawai za ta yi komai da kanta, ashe da rabon tasha wahala.

Gaba ɗaya saida ta faffasa kayan kwalliyar gaban mirror, bata da natsuwa ko misƙila zarratin tana da rawar kai da zumuɗi, tun daga kan Hoda da ta ɗauko zata shafa, Ta sil6e daga hannunta gaba ɗaya ta tarwatse a saman tiles, garin hodar ya zube, Ta kuma janyo janbaki a tsiyace take murza ma la66anta nan take ya gutsire guntulan Ya faɗi ƙasa ta jefar da shi, duk kwalbar turaren data ɗauka sai ya sil6e ƙasa Ya daki tiles kwalbar ta fashe ruwan Ciki Ya tsiyaye, hakan bai dame ta ba, don ta yi asararsu.

Bayan Ta kammala ƴan shafe shafenta, bata bi takan kayan da ta faffasa ba, tsallake su ta yi ta nufi tafkekiyar glass wardrobe ɗinta, daga wajen glass ɗin kana Iya ganin jerin suturar sanyawarta ashaƙe tamkar a company, Abayas, shadda atampa leshi, material, english wears, Pakistans, ga jerin Kayan baccinta, komai fa anzuba mata su, shalelen daddy musa

Da hannu ta zuge glass wardrobe ɗin, Ta ƙura ido tana tunanin suturar da zata sanya don ta burge Yayanta shureim, idanuwanta ne su ka sauka akan haɗaɗɗiyar atampa, yatsun hannunta na kerma ta cafko ta, tana kiciniyar ciro atamfar ai ko gaba ɗayan jerin Kayan da ke a gidan tsakiya suka zazzago saman tiles, ko ajikinta, saida ta 6arar da kayan wardrobe ɗin wurin neman sutura ɗaya kacal da zata sanya a jikinta, Ga abu a fili ta ɗauka tasa shine bazata Iya ba, tafi so saita haukata komai na ɗakin tukunna a ƙarshe tabar masu aiki da wahalar gyara mata su.

Tamkar zata fashe da kuka, ruwan ido Ya hanata ɗaukar Kayan da zata sanya don ta burge Yayanta.

"Assalamu alaikum" Muryar ɗaya daga Cikin masu aikin gidan ce babbar mace wadda suke Kira da Tani.

Da sauri Zeenat ta juyo tana kallonta, "Yawwa Tani, shigo ciki ki taimaka min narasa wasu Kaya zasu dace dani, Inaso ne na burge yaya shureim"

Baki asake Tani take bin ɗakin da kallo, Sam ba ta yi mamakin ganin yadda Zeenatu ta faffasa Kayan Kwalliyarta da turarurrukanta ba, Halinta ne yin 6arna kamar 6era.

"Haba zeenat, Dubi yadda kika zazzago da ninkakkun Kayan Cikin wardrobe ɗinki ƙasa, sannan kinbi kayan kwalliyarki da kwalaban turare duk kin faffasa su why pls? Harfa larai na turo donta taimaka maki ki shirya a tsanake amma sai ki ka ce mata ta tafi za ki yi da kanki, yanzu kin kyauta abun da ki ka yi"? Cikin kwantar da murya take Yi mata magana.

Zumbura mata Baki Zeenat tayi"Nifa bana son faɗa, Idan ma na faffasa su ai daddy zai canza min wasu, kuma ai bada gangan nayi ba ko"

Girgiza kai Lami tayi haɗi da sakin murmushin takaici "Oh, Saboda kinsan daddynki zai siya maki wasu shiyasa kika faffasa su? Ke Baki damu da asarar dukiyar da za'ayi ba kenan"?

Bubbuga ƙafafuwa Zeenatu tayi fuskarta a tur6une tace"Ni ki daina Yi min faɗa, Nace maki ba laifina bane kuma in sha Allah zan gyara, pls ki taimaka min In gyara komai kada mommy tazo taga ban shirya ba"

Gyaɗa kai Tani tayi"ai dole kam in tayaki gyarawa, idan ba haka ba hada ni zata shafa"

Ƙarasa shiga ɗakin Tani tayi, cikin ƙanƙanin Lokaci ta ɗauko Parker ta tattara Kayan kwalliyar da zeenatu ta faffasa ta zubar a trash can na ɗakin, Ta koma bakin wadrobe din ta soma ninke mata kayan da ta zubar a kasa ta jera mata su a cikin wardrobe, duk tana a tsaye ta ruƙe qugu tana kallon tani.

Wani haɗaɗɗan Cord lace ta ɗauko mata Red colour anyi mashi adon flower yellow.

"Zeenat wannan zaiyi maki kyau sosai, Red and yellow, kalar farare ce sannan kuma kyawawa irinki"

Washe fararen Haƙoranta tayi Jiki na rawa ta sanya hannu ta kar6i kayan da Tani ta miƙo mata, Sai da Tani ta taimaka mata wurin ɗaura zani da ɗaura ɗan kwali don ba ta iya ba, masha Allah Lace ɗin Yayi bala'en Yi mata kyau.

"Bari na ɗauko maki Takalman da zaki sanya" Tani ta yi maganar tare da nufar Shoe rack din ɗakin, Inda jerin takalman Zeenatu suke na gayu masu tsini da flat, ta ɗauko mata yellow kalar head ɗinta.

Ta dawo ta ajiye mata su agabanta, ta koma ta ɗauko Jewelry box dinta, ta ɗauko mata sarƙar diamond da earrings, Bayan ta kammala sanya mata su, sai da ta gyara mata make up ɗin fuskarta.

Ita kanta Tani Kyawun Zeenatu ya tafi da imaninta, Inaga wanda Akayi adon domin shi.

"Kinyi kyau sosai shalelen daddy musa, Muje kitchen ɗin in shirya maki dinner dinsa ki kai mashi"

Ta amsa mata da "Toh"

Daƙyar take yin tafiya da high hills din ƙafarta, Bawai don bata saba sanya takalmi mai tsini ba, sai don rashin natsuwarta.

Bedroom ɗinta a second floor Yake, Ƙa'ida ne idan zata sauko down stairs sai dai Ta hau elevator saboda a wurinta wahala ne taka bene. Atare da Tani suka Hau elevator ɗin ta sauko dasu down, da kwarkwasa take yin tafiya tana taka tiles sautin na bada kwas kwas kwakwas.

Kaitsaye kitchen suka nufa, tun daga Cikin Katafaren palourn gidan kana Iya hangen Masu aikin dake safa da marwa acikin kitchen, a tsakiyar falon ta dakata da yin tafiya.

Tani tace "Bari na ɗauko maki Kayan abincin" ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta nufi kitchen, badajimawa ta fito hannun ta ruƙe da wooden tray faffaɗan gaske, daga saman shi wasu haɗaɗɗun Warmers ne da flatware da sauran kayan abinci"

"Anya kuwa zeenatu zaki Iya ruƙe tray din nan? Naji da nauyi, ko dai In raka ƙi ɗakin nashi"?

Girgiza mata Kai tayi"a'a Zan Iya ki bani kawai" miƙa mata tray din tani tayi, Ta rurruƙe shi da hannu Biyu, tana tafiya tana rangwaɗa, Tani dake a tsaye ta ƙurawa bayanta ido, ita tasan daƙyar zata Iya kai shi ɗakin ba tare da ta 6arar dashi ba.

Ɗakin da aka warema Dr shureim a gidan baida banbanci dana sarki saboda luxury furniture dake a cikinsa, sam ta manta ba ta tambayi Tani a wani room ya sauka ba, sai faman wurwurga eye balls ɗinta take yi a ƙoƙarinta nata gano masaukinsa, Cikin sa'a ta hango ɗaya daga cikin ɗakunan dake a rufe ƙofar shi ta buɗe hakan na nufin anan aka saukar da shi.

A lokacin Yana a kwance saman katafaren gadon ɗakin, Ya cire Jallabiyar jikinsa, Iya short ne fari, ya zame arab turban din kansa, Kwantacciyar sumar kanshi baƙa wulik, ya sanya singlet tabi shape ɗin ƙirjinsa.

Bacci ne ya ɗauke shi gefen shi wayarshi ce ajiye yana cikin kallon hotunan abar ƙaunarsa bacci yai awon gaba da shi.

"Yaya shureim ɗina" Muryar Zeenatu ce ke ƙwala mashi kira, tun kafin ta ƙarasa bedroom ɗin.

"Ya ya shureim am coming" kasancewar tana da zaƙin murya mai tsiwa har cikin kunnanshi yake jin muryarta.

"Yaya shureim" firgigit! ya farka daga baccin haɗi da miƙewa zaune la66ansa na ambaton sunan Allah, idanuwanshi har sun canza launi saboda bacci.

ɗakin Yabi da kallo a ƙoƙarin shi na ya gano ta inda zata 6ullo, sautin takun tafiyarta ne Yaja hankalin shi ga kallon ƙofar ɗakin.

Daƙyar ta ke tafiya, sai faman zabga murmushi take yi akan fuskarta, tun da ta shigo ɗaki ta tsayar da blue eyes ɗinta akan fuskarshi, da ƙarfi ta furta hubby na" kamar a mafarki shureim ke kallon zeenatu, kamar yau ya fara ganinta sam ya kasa motsawa daga zaunan da yake saman gadon.

Ganin yadda take yin tafiya babu natsuwa yasa shi yin saurin furta"bari nazo na taimaka maki" maimakon ta dakata da yin tafiyar tun da yace zai taimaka mata, sai ma ta ƙara saurin tafiyar da take yi, a hanzarce dr shureim ya haura ƙafafuwanshi ya sauko daga saman gadon sai dai kafin yai saurin zuwa gareta, Cikin rashin sa'a takalmin ƙafarta ya karkace ai ko Gaba ɗaya Ta saki tray ɗin hannunta Ya kife saman tiles kayan abincin ciki duk suka tarwatse, Nan take zanin da aka ɗaura mata Ya warware Ya zame ƙasa, Daga Ita sai ɗan pant ɗinta.

Runtse ido dr shureim yai, ba arziƙi ya dakata da yin tafiyar.

Jikinta sai kerma yake yi, Kunya duk ta isheta muryarta na rawa ta soma magana"wayyo Allah na, Am sorry yaya shureim wlh duk zumuɗin ganinka ne bansan ya akai zanin ya warware ba, gashi na zubda maka kayan abincin" ta yi maganar tana faman yarfa hannayenta, Kunyar duniya ta ishe shi

"Yaya shureim bari na koma Tani ta gyara min ɗaurin zanin, yanzu zan dawo maka da wani abincin tun da wannan Ya 6are" saboda tsabar ruɗu Anan tabar mashi zanin da kallabinta da ya warware, da takalmanta, da gudu ta juya ta fuce daga ɗakin

A hankali dr shurem ya buɗe idanuwanshi Yana kallon 6arnar da Zeenatu tayi mashi, rashin natsuwar yarinyar ba ƙaramin burge shi yake yi ba, Saboda yana samun nishaɗi sosai, tsabar shiririta ita da tace za taje a gyara mata zani ta tafi tabar zanan a ƙasa.

Yaushe rabon da ya yi dariya irinta yau harya manta, Hada dafe cikinsa tun da zeenatu tabar ɗakin bata ƙara dawowa ba saboda Kunya gare ta, kamar ba jinsin turai ba, Tani ce tazo ɗakin ta bashi hakuri game da 6arnar da zeenatu tayi mashi yace mata bakomai ai yarinyace yana yi mata uziri, Bayan tani ta kwashe kayan da ta 6arar mashi, Ta koma kitchen ta canzo mashi wani abincin ta dawo ta kawo mashi, kafin Tani tabar ɗakin sai da ta tattara kayan zeenatu da ta bar masa zaninta da ɗan kwalinta da takalman duka ta kwashe ta fuce da su, dr shureim yaso ta dawo suyi fira sai dai yasan abune mai wuya ta bari su ƙara haɗuwa yau sai dai zuwa gobe idan kunyar ta sake ta.

*PRISONERS MIDDLE STEP💋❤*

Ƙarfe 7 na safe agogan San antonio ta buga, adai dai lokacin Sojojin sun zo duba marasa lafiyansu daga headquater, mutun uku ne Commender, Major, tare da Captain sun zo cikin shigarsu ta kaki, A office ɗin dr. Laura davis suka fara zama domin tattaunawa.

A6angare Angel tana ƙudundune cikin bargo tasha baccinta, sai mutsu mutsu take yi duk ta yamutsa bedsheet ɗin ga dukkan alamu mafarki take Yi, A firgice tafarka Haɗi da yakice bargon ta wurgar da shi gefe ɗaya, hannayenta biyu saman fuskarta, cikin shaƙaƙƙar murya take ambaton sunan Danish, Mummuna mafarki tayi akanshi Ya farka Ya rikiɗa ya zama dodo Yana shan Jinin mutane, Hankalinta duk yabi ya tashi haiƙam gani take kamar mafarkinta zai iya zama gaskiya.

Ta yi zurfi acikin tunaninta muryar Nurse ta Fargar da ita "Barka da safiya Masoyiya Angel, fatan kin wuni Lafiya" da sauri ta ɗaura idonta kan fuskar nurse ɗin

In a cool voice ta amsa mata Lafiyalou

"How are you feeling today? Are you experiencing any pain?" girgiza kai Angel tayi"A'a" "Okey, nasan zaki buƙaci shiga toilet, ki gyara fuskarki, akwai sojoji da suka zo suna son ganawa dake, Amma kafin nan Zan kawo maki breakfast ɗinki ko kina da za6i na abunda kike son ci"?

Girgiza kai Angel tayi"a'a" Okey daga haka Nurse ɗin ta juya ta fuce, Saukowa tayi daga saman gadon abakin ƙofar shiga toilet ta zura slippers dake ajiye saman carpet, kafin ta tura door din ta shige ciki.

A hankali take tafiya tana bin ko'ina na toilet ɗin da kallo A tsaftace yake fari ƙyal Kamar ba'a ta6a amfani da kayan Cikinsa ba.

Agaban mirror Ta tsaya tana kallon Kyakkyawar fuskarta, batasan lokacin da murmushi Ya kubce mata ba, nan take dimples ɗinta biyu suka lotsa, yatsun Hannayenta, ta tura cikin sumar kanta, a hankali ta soma barbaza gashin, aranta ta ayyana inama akai su saloon Agyara masu gashin kansu ba ƙaramin kyau za su yi ba, fanfo ta kunna Ruwa Ya soma kwararowa cikin sink, ta shigo da niyar ta wanke fuskarta sai kuma ta tsinci kanta da sha'awar son Yin alwala, nan take ta canza ra'ayinta, Tsarki ta fara yi kafin ta soma Yin ta a tsanake, bata manta komai na daga yadda akeyin alwala ba, bayan ta kammala Yi, ta fito daga Cikin toilet ɗin tana Tunanin tayaya zata Iya yin sallah bayan babu Hijabi? Buɗe ƙofar da akayine yasa ta ɗago tana kallon mai shigowa nurse ce ta shigo hannunta ruƙe da tray na kayan breakfast ɗin Angel asaman table ta ɗaura mata shi.

Ɗagowa tayi suka hada ido da juna"Is there anything you need?"

Da sauri tace"Hijabi da abun sallah inaso zanyi" Da murmushi akan fuskar nurse ɗin tace"are u muslim"? Ɗaga mata kai Angel ta yi alamar eh, nurse ɗin tace"Okey, ki jira ni yanzu zan dawo"

Fuce wa tayi daga ɗakin, Angel ta sauke ajiyar zuciya, tana ƙare ma ɗakin kallo, shigowa nurse ɗin tayi hannunta ruƙe da hijab da Prayer mat ta miƙa mata, Farin Ciki a wurin Allah bakinta yaƙi rufuwa. "Thank u so much" nurse ɗin na murmushi tace da ita"never mind" ita kanta batasan Ina ne alƙibla ba, sai da ta tambayi nurse ɗin tayi amfani da wayar hannunta wurin yi mata bincike ta gano mata Alƙiblar da zata fuskanta tukunna ta shimfiɗa carpet ɗin, a tsanake ta kabbara sallah, saman chair nurse din ta zauna tana jiranta, Raka'a Biyu Angel tayi kafin ta sallame sallar, wani irin daɗi take ji yau tayi sallah, bakinta yaƙi rufuwa, tafin hannayenta biyu ta ɗaga sama tana karanto addu'o' kirari tafara yi ma Allah kafin tayi ma ƴan uwanta da suka rasu addu'a, da su kansu a ƙarshe ta roƙi Allah akan Ya haɗa ta da ƴan uwanta ba tare da ta sha wahala ba, Allah yasa daddynta Yana araye, da auntynta Aneelerh. bayan ta kammala Yin addu'ar, Ta shafa a fuska, ta yunƙura ta mike, ta nannaɗe prayer mat ɗin da hijabin ta dubi nurse ɗin

"Kin gama" ɗaga mata kai Angel tayi alamar eh, Miƙewa tayi tare da zuwa gaban angel ta kar6i carpet din da hijabin juyawa tayi ta nufi closet ɗin ɗakin ta buɗe ta sanyasu aciki.

"Aduk lokacin da kika buƙaci yin ibadarki zaki iya ɗauka ki yi" godiya Angel tayi mata, daga bisani ta zauna zaman Cin breakfast, lafiyayyan kalaci aka haɗa mata, tana ci tana tunane tunane sam tamanta da sojojin dake jiranta.

Sai da ta kamalla cin abincin ta ƙoshi, Nurse ɗin ta tattara komai ta fuce dashi, Zama tayi gefen gadon idonta akan ceilling ta ƙurawa haɗaɗɗen kwan ɗakin ido, Yayin da zuciyarta ke tariyo mata abubuwan da suka faru.

Ba zato ba tsammani ta tsinkayi muryoyinsu a yayin da suke shigowa ɗakin, A hanzarce ta miƙe tana faman zazzare gray eyes ɗinta akansu, sojojinne tare da likitocin, saman doguwar sofa ɗin ɗakin suka zauna a jere suna fuskarta, Dr Laura davis ta zauna gefenta, Kamar wata mara gaskiya duk ta kama kanta, Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba.

"Masoyiya Allah fatan Kin wayi gari lafiya? Ya jikin naki" muryarta adabarbarce tace"da sauƙi sosai" cikin kulawa suke Yi mata magana da harshen turanci

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull