Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 28

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 28

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 28: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 28. Dr Mark jackson ne ya fara yi mata magana"mun…

3,368 words

Dr Mark jackson ne ya fara yi mata magana"mun nemi jin bayani daga bakin ɗan uwanki Gabriel sai dai bai bamu haɗin kai ba, Yace duk abunda muke son sani ke ce zaki amsa mana.

Jin wannan maganar yasa hankalinta ƙara ɗugunzuma.

Fahimtar yanayin ta ne yasa dr mark cewa" Ki kwantar da hankalin ki, Bamu zo da niyar mu takura maki ba, Ƴan tambayoyi ne zamuyi maki da zarar kin amsa mana zamu tafi, munfiso ki natsu kiyi nazari kafin ki amsa mana"

"Kin shirya"? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh, duk tabi tasha jinin jikinta. "Da farko zamu so ki fada mana Ya akai kuka tsinci kanku A daji? Waye ya kai ku can? Sojojin kasar mu suna hasashen ɗan Ta'addan daya gudu zuwa canne Yai garkuwa daku don ya kare kanshi daga farmaki da suka kai mashi, shin dagaske ne ko kuwa? Ƙura masu ido ta yi ɗaya bayan ɗaya take kallon fuskokinsu, tsabar fargaba ƴan hanjin cikinta sai kaɗawa suke Yi, Tarasa Tayaya zata fara basu amsar tambayarsu? sam ba ta jin zata Iya faɗa masu ainihin Abunda Ya faru da rayuwarsu, ita aganinta kamar idan suka ji zasu guje su ne, musamman idan Danish Ya farka a matsayin giant ba ƙaramar masifa zaija masu ba, Zaiyi wuya su yarda da abunda zata faɗa masu, saboda Labarin baƙar izayar da suka sha a prison ba kowane zai gasgata kalamanta ba, zama su Iya tunanin ƙarya take yi masu, bayan haka tana tsoron ta fada masu, su kuma su tara Ƴan jarida su sanar dasu a ɗauki hotunansu ayi share da labarin prison tabbas yin hakan zai jaza masu babbar matsalar da zata Iya ja su rasa rayukansu don tasan dole Shuwagabannin kurkukun ƙaddara su bibiyi rayuwarsu ko dan saboda abu biyun nan na farko Garkuwar kurkukun da su ka gudu da shi, Na biyu don kada su tona masu asiri.

duk da sanyin A.c dake ratsa fatar jikinta hakan bai hanata zubar da zufa ba, ta ko'ina take tsastsafo mata, Hakan ba ƙaramin ɗaure masu kai yai ba, farat ɗaya suka fahimci akwai wani gagarumin al'amari atattare da yarinyar sai dai zaiyi wuya ta iya sanar da su gaskitar zance.

Gyaran murya Commender yai mata, A hargitse ta wurga eye balls ɗinta akan fuskarshi

"Kin yi shiru baki ce komai ba meyasa"?

Dafa kafaɗarta dr laura tayi da hannu ɗaya"Ki kwantar da hankalin ki my daughter, Ki natsu ki bamu amsa, a shirye mu ke da mu taimaki yaruwarku, haɗin kanki kaɗai muke buƙata, kuma muna tabbacin zaki Amsa mana tambayoyin mu"

gaba ɗaya ta ruɗe saboda saƙe saƙen da zuciyarta ke yi mata, wani sashe Yana jan kunnanta akan karta kuskura koda gigin wasa tace zata faɗa masu abunda ya faru a rayuwarsu, Yayin da wani sashe na zuciyarta ke Jan hankalinta akan ta faɗa masu wata'ƙil su taimaka masu wurin kawo ƙarshen Azzaluman kurkukun ƙaddara, Yanzu idan ta 6oye masu taƙi faɗa masu gaskiya kwatsam wani abin da ba'a fata ya zo ya same su har su rasa rayukansu shikenan tarihin kurkukun ƙaddara zai cigaba da wanzuwa ne.

Sun tasata gaba kamar sun sami tv, duk sun ƙagara da su ji amsarta, gashi taƙi buɗe baki tayi magana.

"Idan har baki bamu amsar tambayoyinmu ba, zamu maida ku Dajin da muka ɗauko ku"! Acewar Major

Ras Taji gabanta ya faɗi, Lokaci ɗaya ta fashe masu da matsanancin kuka mai ratsa zuciya Cikin shessheƙar kuka take faɗin"Ni bansan komai ba, Bazan Iya tunawa ba, Namanta komai, ɗan uwana danish shi ya sani"

Ta ƙara rikita masu lissafi, Captain yace"kun haɗa baki ne? Mun tambayi ɗan uwanki Gabriel ya faɗa mana cewa ke kaɗaice kika san komai, Yanzu kuma mun tambayeki kince kema bakisan komai ba A tambayi Danish! Why kuke son Yi mana yawo da hankali....? Da alama Ya Hasala ne dan muryarshi a kausashe yake mata magana.

Da sauri dr laura ta katse shi"Sir, bata da ƙoshin Lafiya, Ni a ganina bai kamata mu tsareta da tambayoyi ba a yanzu, ƙaramar yarinya ce sai ana lalla6ata"

Sassauta fushin fuskarshi Yai, Cikin kwantar da murya yaci gaba da cewa"Okey, Share hawayenki, ki daina yi mana kuka bama so" Muryarta Na rawa ta amsa mashi da toh.

Miƙewa Dr laura ta yi ta nufi fridge ta buɗe ta ɗauko mata fanta me sanyi, ta haɗo mata da tissue, Ta dawo gefen gadon ta zauna tare da miƙe mata tissue ɗin, Hannayenta na kerma ta kar6a ta soma goge ƙwallarta da hancinta, Bayan ta gama share hawayen dr laura ta miƙa mata lemun kar6a tayi tare da yi mata godiya.

kamar tasan Mayyar fanta ce, Buɗe wa tayi agaban su ta kur6i ruwan lemun kusan sau uku tana sha, Sun tsareta da ido suna kallonta, hakan ba ƙaramin rikitar da ita yake yi ba.

"Pls Masoyiya Angel, Ki taimake mu ki taimaki rayuwarki da ta sauran ƴan uwanki, Ki faɗa mana gaskiyar abunda Ya faru a rayuwarku wanda yai silar haifar maku da ciwon damuwa, Idan har baso kikeyi mu maida ku daji ba" acewar Captain.

"Abunda mukeson sani shine Ya akai kuka tsinci kanku a ƙurmin dajin Evil forest? saboda ɗan ta'addan ƙasarmu da muke hasashen shine Ya kai ku can mun titsaye shi akan ya faɗa mana menene alaƙar shi da ku, Ya faɗa mana cewa Baisan komai dangane da ku ba, Ya taimaki wasu daga Cikin ƴan uwanku ne, Munyi dogon nazari akanku, da farko munyi tunani ƴan ƙasarmu ne ku, sai kuma muka ji kuna magana da wani harshe wanda bana nahiyarmu ba! Mun rasa gane daga wani Jinsi ku ke? sannan menene maƙasudin haddasa maku ciwon damuwa da baƙin ciki? lamarin ya ɗaure mana kai da ƙananun shekarunku? hada me fama da ciwon zuciya! Wani abun al'ajabin ɗaya daga cikin Ƴan uwanku yaƙi farkawa daga bacci mun rasa gane meke damun shi......" tun da major ya soma yi mata magana a tsanake ta tsare shi da ido tana kallon la66ansa har ya ƙare maganarsa, tukunna ta fara magana "Gaskiya ne abunda ɗan ta'addan ya faɗi, bashi ne yakaimu daji ba, Mun jima Acan kusan zance tun kafin mu mallaki Hankalin mu, bazan Iya tuna abunda Ya faru arayuwar mu ba, kome yakai mu Dajin, abunda na sani shine Munci baƙar wahalar rayuwa dani da ƴan uwana, wanda silar hakan yajaza mana depression...." Kallon Juna su ka yi, still sun fahimci bazata faɗa masu abunda suke son ji ba, sam bata son su sani babu alamun zata yarda da su.

Murmushin gefen fuska Major ya sakar mata"Ni dama tunda naga idanuwanki da ƙaramin bakin nan Naki raina ya bani kina da wayau sosai," duƙar da idonta ƙasa Ta yi zuciyarta na bugun uku uku.

Dr. Laura sam ba ta so suka matsa mata da tambayoyi ba, tuntuni ta basu shawarar su bari Yaran su saba da su tukunna amma da yake Sojoji ne Yana ɗaya daga cikin Halayansu, Idan suna son jin bayani daga bakin mutun ba wani uziri da suke Yi mashi dolenshi ya amsa masu.

"Yaren da ku ke yin magana da shi na wace ƙasa ne"? Captain ne Ya jefa mata tambayar.

Muryarta na ɗan rawa ta furta"Ni.. geria" Tsabar mamaki ne yasa su kallon Juna.

"Kina nufin daga Nigeria ku ke? Tayaya hakan zai yiwu? Dama Nigeria suna da farar fata ne acikin su? a iya sanina baƙar fatane mutanan Nigeria, Sannan matansu kuma basu da dogon gashi, kuma Launin idonki Kalar na mutanan ƙasarmu ne" Dr. Mark jockson ne Yai maganar da alamun mamaki akan face ɗinsa Dr. Laura na murmushi ta dube sa"kada ka bani kunya mana, ko mu a ƙasarmu ai akwai black americans, zai Iya yiwuwa suma suna da alaƙa da fararen fata ne ina nufin half cast"

"Dagaske Ku ɗin Ƴan Nigeria ne? Jinjina masa kai tayi"Eh, ai yaren da muke yin magana dashi hausa ne na nigeria, zaku Iya bincikawa" Ba ƙaramin mamaki suka yi ba, Hatta turancin da yaran suke magana da shi sak Na america ne bana Nigeria ba.

"Yanzu dai bazaki faɗa mana gaskiyar abunda ya faru da ku ba ko! To Shi ɗan uwan naki da kika ce yasan komai tayaya zamu Iya farkar da shi daga bacci"! Anzo dai dai wurin da tafi so, marairaice masu fuska ta yi"maganinshi Yana a nigeria, dan Allah ku taimaka ku maida mu ƙasarmu, idan ba haka ba ɗan uwanmu zai Iya mutuwa" hada ƙwallarta "Meke damun shi ne" Dr Brown ne yai mata tambayar, batare da ta yanke shawara da zuciyarta ba tace"nima bansani ba, Idan yafara bacci yana ɗaukar tsawon lokaci bai farka ba, to akwai maganin shi kuma yana acan ƙasar" Murmushi kowannansu ya saki, hakan yasa tasha jinin jikinta, Commender yace"Kin Iya acting, da farko kince bazaki Iya tuna komai daya faru a rayuwarku ba, amma ayanzu kin faɗi inda za'a samu maganin ɗan uwanki hakan na nufin tunaninki yana nan baki manta komai ba ko"? ɗaure mata fuska yai "Zaki faɗa mana gaskiya ne? Ko kuwa kunfi so mu je dake can headquater Ki amsa mana tambayoyinmu ta tsiya" tashin hankalin da ba'a sanya mashi date Maganar commender tayi matuƙar tsoratar da ita Jikinta Ya hau yin kakarwa duk tabi ta rikice, A ƙarshe data ga dagaske zasu titsayeta saita amsa masu tambayoyi ko su tafi da ita headquater, aiko da ƙarfi tasa wata irin gigitacciyar ƙara data firgitar dasu, Hannayenta Biyu ta sanya ta daddafe kanta tana faɗin"Nace maku ni bansan komai ba! Dan Allah ku maidamu ƙasarmu Nigeria, ɗan uwana zai Iya rasa ranshi, Na roƙe ku idan har dagaske zaku taimaki rayuwarmu to ku maidamu Nigeria wurin danginmu," kamar mahaukaciya haka tadinga nanata masu akan su maidasu Nigeria.

Hankalinsu Ba ƙaramin tashi yai ba, ganin yadda Ƙwayar idanuwanta suka burkice Launin Ciki Ya 6ace sai zallar farin idon, Jijiyoyin wuyanta dana Gaban goshinta shatunsu ya fito ruɗu ruɗu, Jefar da robar fanta hannunta ƙasa ta yi, a zafafe Ta miƙe saman gadon kamar ƴar daba, ta dunƙule hannayenta, taci gaba da ambaton Ku rabu dani ku ƙyaleni, Ku maida mu ƙasar mu Nigeria nace ku kaimu ƙasar mu, can muke son zuwa"

Har suna haɗa baki wurin lallashinta"sorry ki kwantar da hankalin ki, zamu tafi yanzu, Ki daina kuka ki kwantar da hankali, Ki koma ki kwanta, babu wanda zai Ƙara tambayarki wani abu" sun firgita da ganin haukan Angel.

Dr laura duk tabi ta ruɗe Sun rasa gane kanta.

Kallon Sojojin ta yi"Pls, Ku ƙyale yarinyar nan, Muje office muyi magana, idan ba haka ba za'a Iya samun matsala" gyɗa kai sukayi ba don sunso ba suka Juya tare da fucewa daga ɗakin tare da Likitocin, Ya rage da ita sai Dr laura.

"Pls My daughter kukan Ya isa haka, Ki koma ki zauna muyi magana kinji"? Lallashinta tashiga yi, Daƙyar Angel ke iya kallonta sumar kanta duk ta rufe mata fuska, dagangan ta ƙirƙirarma kanta Ciwon hauka.

Marairaice mata fuska Angel tayi"dan Allah ki taimaka mana, su maida mu ƙasarmu, banaso mu rasa ɗan uwanmu zai Iya mutuwa, maganinsa yana can, Nayi maki alƙawarin idan ya farfaɗo zan fada maku duk wani abu da ku ke son ji dangane da mu"

saukowa Angel tayi daga saman gadon, A sukwane ta zube saman gwiwowinta agaban Dr laura, Idanuwanta sun cicciko tab da hawaye take faɗin"Na roƙe ki Ki taimaka mana, kamar yarda Allah Ya taimake ki, Kice ma sojojin can sumaida mu Nigeria, Idan ba haka ba Ɗan uwana danish zai mutune, ba zaku Iya sarrafa shi ba, maganinsa yana acan, Ni na yarda ku sanya jami'an ku, su bimu can kasar don su shaida abunda na faɗa masu su sanya mana ido' Muryarta ashaƙe ta ƙarasa maganar. Tsananin tausayintane Ya kama dr. Laura har cikin ranta ta aminta da yarinyar, Miƙa mata hannu tayi"miƙe tsaye" da sauri Angel ta ɗaura hannayenta asaman na dr laura, ta yunƙura ta miƙe, ba zato ba tsammani taji ta rungumeta a kirjinta, ƙamshin turarenta Ya daki hancin Angel sosai ta ƙankameta tana faman sauke ajiyar zuciya.

Shafa sumar kanta dr laura tayi a hankali take yi mata magana "Ni tun farko banso suka tsareki da tambayoyinsu ba, sunyi gaggawar yin hakan, But Inaso ki kwantar da hankalin ki, Zanyi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin sun maida ku ƙasar ku, idan har kikayi min alƙawarin zaku faɗa mana abunda ya faru da ku bayan ɗan uwan naki ya farfaɗo kamar yadda kika ce" Cikin sanyin murya Angel tace"Nayi maki alƙawari shiyasa ma nace su sanya jami'an da zasu bibiyi rayuwarmu" ta ƙare maganar tare da raba Jikinta daga na Dr laura Shafa fuskarta tayi"is ok, Zanje muyi magana da su yanzu ki koma ki kwanta ki huta"

Amsa mata Angel tayi da toh, Bayan fitar dr laura, Daɗi kamar zai kasheta, don tana ji aranta zasu amince masu su koma Nigeria, juyawa tayi tana neman robar fantar data jefar a ƙasan tiles can ta hangota gefen nightstand zuwa tai ta ɗauko lemun ta koma gefen gadon Hankali kwance taci gaba da shan lemun fatanta Allah yasa su amince masu.

Gaba ɗayansu sun Hallara a katafaren ofishin dr laura, Kowan nan su Ya samu wuri ya zauna saman haɗaɗɗun kujeru, table ne Ya ratsa tsakaninta da su,.

"Shawarar da zan bada shine bai kamata mu takura masu da tambayoyi ba, duba da Yanayin yaran akwai ciwon damuwa atattare da su, tursasa masu zai Iya haddasa masu wata matsalar da bama fata" Dr laura ce ta kora jawabin idonta akan faces din sojojin Commender yace"Ya zamuyi kenan? Menene Mafita don muna buƙatar son Jin ainihin abunda ya faru da su a dajin nan" Numfasawa dr laura tayi"Munyi magana da yarinyar, tabbas bata manta komai ba, tasan abunda ya faru da rayuwarsu sai dai rashin yarda da tsoron fargabar abunda zai biyu baya idan ta faɗa mana sun Hana ta sanar damu, abun duba anan shine Babu yarda za'ae su saki jiki damu don ta yanzu, saboda basu sanmu ba bugu da ƙari kuma ba ƴan kasar mu bane, donni na yarda da maganarta, Idan har munaso muci nasara akansu dole sai mun yi masu abunda su ke so, ta hakanne zasu saki jiki damu har su faɗa mana gaskiyar abunda mu ke son ji daga gare su, sannan suna buƙatar wadda zata Kula da rayuwarsu tamkar mahaifiyarsu, Ta hakanne zasu saki jiki da ita har su Iya faɗa mata damuwarsu, abu na biyu shine Muyi masu abunda suke so! Musamman ita Angel din ta roke ni akan mu maida su ƙasarsu, Akan idonku kunga haukan da tayi mana tabbas akwai ƙamshin gaskiya a maganarta, tace maganin ɗan uwansu yana acan, kuma tace zamu Iya sanya jami'ae su bi su har can kasar sannan tayi alƙawarin idan harya farfaɗo zata faɗa mana duk abunda muke son ji.

Shiru suka ɗanyi na wani lokaci kowan nan su Yana nazarin maganar dr laura.

Numfasawa Major yai kafin ya soma magana"Me zai hana mu damƙa Case ɗinsu ya koma hannun Hukumar Isod? (Intelligence Special Operations Division) Tun da shugabansu Ɗan ƙasar Nigeria, su kaɗaine zasu Iya bincikar Ainihin abunda Ke faruwa da yaran, saboda suna da ƙwarewa a 6angaren.

Jinjina kai Commender yai da alama ya gamsu da jawabin Major

"Hakane ka kawo shawara mai kyau, case ɗin yafi dacewa dasu, Tunda Aikinsu ne Yin binciken sirri Harma da fafatawa idan ta kama kuma duk muna atare dasu banbancin kaɗan ne mu ba jami'an sirri bane su kuma duka sun Haɗa sunayin aiki a matsayin sojoji sannan kuma jami'an sirri"

Captain Yace"Nima na goyi bayan hakan, amma fa zaiyi wuya mu iya samun chief ɗin nasu a waya, So the best way to contact him is through email, We need to start making our request for the case through their email, If they show interest in the case, we will turn everything over to them."

Commender yace"shugaban nasu ai Yana a Washington (babban birnin america) kuma naji raɗe raɗen kamar cikin weekend da zamu shiga zai bar ƙasar ya koma Nigeria, duk da bani da tabbaci kunsan aikin nasu na sirri ne babu mai sanin shiga da fucen su, Idan har muka samu ya nuna interest akan case ɗinsu komai zai zo mana da sauƙi, In yaso sai mu damƙa mashi Yaran ya tafi da su can, mu kuma zamu dinga bibiyarsu don jin ya ake ciki"

Murmushi Dr laura tasaki, Har cikin ranta ba ƙaramin daɗi taji ba, Fatanta Allah yasa Chief ɗin Isod Ya amince da case ɗin Yaran, ko dan saboda Yarinyar da ta roƙe ta akan amaida su ƙasarsu"

"Doctor, how long do you think it will take for the children to be discharged"? captain ne yai mata tambayar,

Dr. Laura ta bashi amsa da cewa "After the three-day injection course is completed, we will be able to discharge them, Shima Ɗayan Yaron mai fama da ciwon zuciya Zamu Iya sallamar shi idan har aka Kiyaye sharuɗɗan da zamu rubuta na bashi kulawa ta musamman, " ta ƙara da cewa"zasu Iya zama a asibitin namu har zuwa lokacin da shi chief ɗin zai Amsa mana buƙatar mu"

Commender yace"dole ne mu sama masu wadda zata Iya kula da su tamkar ƴa'ƴanta kamar yarda kika bada shawara, wadda zata Iya tarairayarsu ta basu kulawar da zasu Saki Jiki sosai," Yai maganar yana kallon fuskar dr laura Major yace"why not bazamu damƙa amanar kula da yaran a hannun UMMIN AMERICA ba? Tun da itama Ƴar Asalin ƙasar Nigeria ce, hatta yaren da naji Yaran suna magana da shi itama tana jin shi sosai" Jin Major Ya ambaci sunan Ummin america yasa Dr Mark da dr brown Kallon Juna ga dukkan alamu sun girgiza da jin an ambaci sunanta, Dr laura ta zaro ido tana faɗin" The Baddest mistress? There's no way we can leave the children in her care, She's a dangerous woman. How could she possibly know how to take care of them?" hankalinta bai kwanta da zancen miƙa yaran ga Ummin america ba saboda sanin wacece Ita.

Bayan ta ƙare magana Major yace"Ai ba yau tafara Yi mana aiki ba, tana taimaka mana sosai akan irin case ɗin nan, Ina da tabbacin zata Iya! Fiye da yadda baki tsammani"Kwa6e fuska Dr laura Tayi don ita har aranta Fargabar Ummin americe take ji, Kowa yasanta sananna ce a 6angare Iya karuwanci tantiriyar ƴar bariki ce, tayi ƙaurin suna america shiyasa su ke yi mata laƙabi da Ummin america, tsabar Iya shaiɗancinta har award ake bata akan Iya Karuwanci.

"Mu zatayi ma aiki, bai shafi sana'arta ba, Kawai munaso Yaran su kace a hannunta amatsayin guardian ɗinsu, Kafin Mu damƙa mata su zamu yi yarjejeniya da ita idan har ta amince to lafiyalou ba zamu samu matsala da ita ba" ta6e baki dr Laura tayi"amma dai ba'a asibitin mu za'a gayyato mana ita ba, Don ina jin fargabar ta rikitar mana da ma'aikatan mu da surar jikinta"

Gaba ɗaya suka sanya dariya jin abunda tace, ta faɗi hakanne don tasan Ummin America kamar maganaɗisu take awurin Iya jan hankalin mutun da surar Jikinta, Dirine da ita na bala'e' Sunjima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani Commender yace

"Dr mun gode sosai da shawarar ki, Zamu koma bakin aiki Yanzu, Idan har Chief din isod Ya amince da buƙatar mu zamu tuntube ku"

Daga haka Sojojin sukayi Ma Dr laura sallama, Har bakin parking space na asibitin ta rakosu, Bayan tafiyar sojojin suka dawo Cikin asibitin.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

~Middle step~

_The Prisoners E18🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

*DAULAR OBIE ESTATE*

A katafaren ɗakin Hajjaty head maids ta gidan obinna, tsabar haɗuwarsa tamakar bana ƴar aiki ba.

fitowar kenan daga bathroom, ga dukkan alamu wanka tayi, ta ɗaure ƙirjinta da towel fari, iya gwiwar ƙafafuwanta ya tsaya mata, fatarta da lemar ruwan wankan da ta yo, a gaban mirror ta tsaya tana kallon kyakkyawan fuskarta har yanzu akwai sauran make-up ɗin jiya da ta yi jan bakin bai goge ba, don ita bata rabo da kwalliya a fuskarta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull