Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 31

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 31

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 31: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 31. Agaban Sofa table ɗin Ya dakata da yin tafiya, da…

3,313 words

Agaban Sofa table ɗin Ya dakata da yin tafiya, da kakkausar murya yace"Ke! Miƙe tsaye tun kafin ran ki ya 6aci" Jikinta na kerma ta ɗago da kanta hawaye sun wanke fuskarta sharkaf, abunka ga farar fata face ɗin ta yi jawur, Blue eye balls dinta sun ciza launin su idon nata ya rune, small pink lips ɗinta tsabar ƙarantarsu tamkar na jariri.

Cikin rashin natsuwa ta zube saman gwiwowinta, Idanuwanta na kallon tiles ɗin ɗakin "Dad...am sorry bazan ƙara ba, nasan bana jin magana bani da natsuwa amma ka yafe min, kada ka hukun......"

Gigitacciyar tsawar da ya daka mata ce tasa ta yin saurin toshe kunnuwanta da tafin hands dinta

A razane take faɗin "Na shiga uku daddy, nace maka bazan ƙara ba, Nagane kuskure na"

Muryarshi a kausashe Ya furta sunanta"Zeenatu? Sau nawa ina gargaɗin ki akan ki daina faɗo min ɗaki ba tare kin nemi izni na ba? Waya baki iznin shigowa ciki"?

Wahalallan yawu ta haɗiya, idanuwanta sunyi luhu luhu sai faman wurwurga eye balls ta ke Yi kamar ƙwayar zata faɗo ƙasa.

"Am sorry dad..." katse ta ya yi"Kin Iya tsallan kwaɗi?" tun da ya fara magana bata bari ta ɗago sun haɗa ido ba sai Yanzu da ta ji yace Tsallan kwaɗi

A hargitse ta zare mashi manyan idanuwanta A matukar ruɗe take girgiza mashi kai"daddy bazan Iya ba, Ni bansan yarda akeyi ba, ai nace ka yi haƙuri bazan ƙara ba"

Gyaɗa kai Yai"Tashi ki fuce ki bani wuri shashasha, daga yau karki kuskura ki ƙara faɗo min ɗaki"

Zuciyarta ba ƙaramin karaya tayi ba, duk sai ta ji ba daɗi, ba ƙaramin kewar daddyn nata tayi ba, maimakon Ya nuna farin Cikin ganinta saima korar ta da yayi.

Ganin yarda ta tsare shi da ido taƙi motsawa ne Yasa shi daka mata tsawa"nace ki tashi ki fuce min daga ɗaki tun kafin In yi ball dake" fuskarshi a haɗe Yai maganar ba annuri.

A gurguje Zeenatu ta miƙe ta juya tana tafiya Jikinta na kakarwa har Ta kai bakin ƙofar fita ɗakin, ta ji ba za ta iya jure fushin daddynta ba, tasan duk akan kuskuren da ta yi mashi ne.

Yana atsaye ya goya hannayenshi saman faffaɗan kirjinshi Ya natsu Yana kallon Bayanta, Har ta kusa fucewa daga ɗakin A lokacin Ya juya zai shige ciki ba zato ba tsammani ya ji an rungumeshi ta baya, ƙanƙameshi ta yi tana faɗin"wlh daddy ba in da zan je, ai na faɗa maka kuskure ne bada sani na na 6arar maka da coffee, yakamata ka yi haƙuri ka yafe min, Ni banason kana fushi dani saboda kai mahaifina ne, kuma inason ka sosai bazan Iya jurar fushin ka ba"

Har cikin zuciyar shi ba ƙaramin sanyi ya ji ba, kalaman zeenatu sunyi matuƙar kashe mashi jiki, Ba tun yau ba duk idan ta 6ata mashi rai ko ya kore ta daga ɗakinsa ba ta tafiya shiyasa yai mata hakan don ta ga ne kuskuren ta yasan dole ta dawo ta bashi haƙuri.

Da hannu ɗaya ya ruƙo hijabin jikinta Ya janyota zuwa gabanshi, Ya kwantar da kanta saman chest ɗinshi, A hankali ya ke ɗan bubbuga bayanta da hannayenshi cikin sigar lallashi, hakan da yai mata ba ƙaramin kwantar mata da hankali yai ba, harta fara samun natsuwa.

Tsawon mintuna kafin ya raba Jikinshi daga nata, fuskarta jawur idanuwanta har sun ɗan kumbura.

"Kin 6ata min riga da hawaye" tana faman zazzare ido ta furta"am sorry"

"Is okey, kinsan banason ganin hawayenki, meyasa kike min kuka"?

"Daddy ai kai ne ka sani yin kuka, Ina baka haƙuri kaƙi ka saurareni"

"Zeenatu ɗago ki kalli Cikin idona" daƙar ta Iya ɗagowa ta sanya idonta cikin nashi gabanta Ba ƙaramin faɗuwa yai ba saboda ƙwarjinin da yai mata.

"Bansan meyasa ki ke jin tsorona ba, Nifa daddynki ne, saboda kawai kin 6arar min da coffee shine duk kika ɗaga hankalin ki? Ni shine abunda Ya 6ata min" fuskarshi a ɗaure tamau yai mata maganar.

Muryarta na ɗan rawa ta furta"dad..dy ai kai ne baka dariya ko murmushi ba ka yi min kullum fuskarka a ɗaure, kuma baka son ina zuwa kusa da kai, nasan saboda rashin natsuwata ne amma in sha Allah daddy zan daina, ina yin addu'a ma har tsakar dare Akan Allah ya yaye min..." Yatsan Hannun shi ya daura saman lips ɗinta

"Ya isa haka, Karki kuskura na ƙara ji kin ce bana son kina zuwa kusa dani, kinji ko? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh

Mayar da ita Yai saman chest ɗinsa, Yaci gaba da shafa bayanta Yana ƙara lallashinta.

A haka Hajiya sarah ta riskesu, a bakin ƙofar shiga room ɗin nashi taci burki, farar mace alkebbar mata doguwar riga ce a jikinta fitted gown ta lace, Kusan rabin ƙirjinta awaje Yake, Tubarkallah na shanunta atsaitsaye su ke, tamkar bata ta6a haihuwa ba, light make up ne akan fuskarta, Ƙafafuwanta na sanye cikin High hills, sun ƙara mata tsayinta. Babu mayafi akanta zallar sumar kantace tasha ado tsabar haɗuwarta tamkar budurwa.

"May I come in"? Muryarta har cikin kunnuwansu, Alhaji musa ne ya bata Iznin shigowa ciki, ɗagowa zeenatu ta yi daga kan chest ɗinsa, Muryarta na ɗan rawa ta furta"daddy zan tafi"

"Da iznin wa"? Ya jefa mata tambaya, shiru ta yi tana ƴan kame kame, Sam ba ta son mommynta ta shigo ɗakin daddynta idan tana aciki.

Ƙarasowa Ciki Hajiya saratu tayi, kaitsaye ta nufi Alhaji musa, fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi take duban su shi da zeenatu.

"Masha Allah, Uba da ƴarsa kunyi kyau fatan ban takura maku ba"

Zeenatu ce tai saurin cewa"Mommy, na shigo gaida daddy ne dama, yanzu zan tafi" kallon da Alhaji musa Yai mata ne yasa ta yin saurin canza magana"A'a ba yanzu zan tafi ba, sai daddy ya bani iznin tafiya"

Ta yi maganar tare da samun wuri saman sofa ta zauna, Jikinta nata yin kerma acan cikin zuciyarta addu'o'i take karantowa.

Matsawa Hajiya sarah Ta yi dab da shi, duk da shakkarshi da ta ke ji hakan bai hanata nunawa mijin nata soyayya, tarairayarshi ta ke yi kamar sabon jinjiri ta haka ta ke iya samun damar Iya sarrafa shi.

Hannayenta ta ɗaura saman waist dinsa, Daddaɗan ƙamshin turarenta tuni ya fara Kashe mashi jiki.

"Baby, jiya ka hana kowa yazo kusa da kai, kuma ina buƙatar ka, Na kwana da son kasancewa atare da kai" cikin harshen turanci ta ke yi mashi magana, gogan naka babu fara'a akan face ɗinsa ya ƙame a tsaye kamar soja.

"Zeenatu, ta shi ki je ɗakin Yayanki shureim, Tani ta faɗa mini tun safe ba ki ci abinci ba, nayi mata magana ta shirya mashi abincin aɗakinsa, Za ki Iya zuwa can kuci atare da shi"

Kamar Jira ta ke yi mommyn ta yi mata magana, da sauri ta miƙe ta nufi hanyar fita daga ɗakin Har Allah Allah take aranta, saboda bata son ganin Iyayen ta suna yin romancing din junansu agabanta Kunya take ji kuma hakan Yana jefata wani hali.

Baya fitar Zeenatu ta dawo da dubanta akan fuskar shi.

Muryarshi a kausashe Ya furta "Baki da kunya? Baki ga me kika ruƙe min ba ne"

Kashe mashi ido ɗaya tayi muryarta da kwarkwasa ta furta"kaine ka koyamin rashin Kunyar," hakan da tayi mashi ba ƙaramin jefa shi yanayi tayi ba, dama Shi mutunne da baya wasa da duk wani abu da jikinshi ke buƙata.

"Yanzu ina da aikin da zanyi, Da anjima zan neme ki" marairaice mashi fuska tayi"A'a baby, yanzu nake buƙatarka ni, kusan 3 days baka atare dani, bazan iya jurewa ba."

Yamutsa fuskarshi Yai, Kafin Yai yunƙurin ƙara furta wata kalma, tayi saurin zame wuyan rigar jikinta, Ba ƙaramin shammatarshi tayi ba, gaba ɗaya ya rasa sukuni, Baisan ya akai ba ya tsinci kanshi asaman gado sun tsunduma suna Korar shaiɗanu, Suturar jikinsu A saman floor na tsince su bansan ina zan kaisu ba, Laundry ko toilet? (🤣 wato duk izzar namiji sai in bai haɗu da mace ba)

Tuni Dr shureim Ya kammala shiryawa, Ya canza suturar jikinshi, still Arab dress ne, kayanshi na gado, Yana daga zaune gefen gadon shi, Hannun shi ruƙe da Wayarshi Yana kallon hoton abar ƙaunarsa da ya buɗo a gallery.

Ba zato ba tsammani Yaji Muryar matashin saurayi Yana Kwaɗa sallama daga bakin ƙofar ɗakinsa, slowly ya ɗago da ido yaɗan Juya yana kallon Saurayin dake sanye cikin black suit, dogo kuma faffaɗa, Hannun shi ruƙe da Ƙatuwar shopping back mai ɗauke da sunan *Obinna tech*

A sukwane Dr shureim ya ɗaura wayarsa saman mattress Ya yunƙura ya miƙe Still idonshi akan mutumin.

"Dr shureim Barka da warhaka" Muryarshi babu natsuwa ya furta"yawwa barka dai" duk yasha jinin jikinshi saboda mutumin babu fara'a akan fuskarshi kamar wanda aka ɗaurawa aure da mutuwa.

"Saƙo ne daga Uncle ɗinka" nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tunawa da saƙon da uncle musa Yace za'a kawo mashi.

A hanzarce ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin, Ya miƙa hannu biyu ya kar6i kayan daga hannun mutumin haɗi da yi mashi godiya.

Fuskar shurem ɗauke da murmushi ya nufo cikin ɗakin, A saman gado Ya ɗaura shopping back ɗin, Bayan yayi bismilla, Ya buɗe ta tare da zura hannu Ya zaro kayan dake aciki, har saida gabanshi Ya ɗan faɗi.

Apple laptop ce, tare da Apple watch, abu na ƙarshe da ya gani Unexpected Danƙareran Key ɗin Mota, Zubewa yai saman gwiwowinsa agaban Kayan Yana duban su, A tsanake Ya ke ƙare masu kallo, haƙiƙa Yayi farin Cikin Kyautar nan da uncle musa yai mashi ya ji daɗi sosai, ɗaga Hannayenshi sama Yai, Ya soma jera addu'o'i Yana yiwa kawunsa bisa irin farin cikin daya Sanya shi ayau, Ya faranta mashi sosai.

Bai gama shan mamakin Kayan ba, Muryar mutumin da ya kawo Kayan ta katse mashi addu'o'in da ya ke yi.

"Dr shureim Zan iya shigowa Ci ki? Da sauri Ya miƙe tsaye Yana kallon shi.

Manyan Akwatuna ne guda Biyu a hannun shi ya ruƙe handle ɗinsu Yana Jansu irin masu tayoyin nan.

"Bismillah" yai mashi nuni daya shigo Ciki, Bayan ya shiga Cikin ɗakin agaban tafkekiyar Glass wardrobe ɗin ɗakin mai faɗi Ta mamaye bangon da take a jikinsa, Anan mutumin Ya dakata da yin tafiya ya buɗe akwatunan, Farin Ciki Ya hana dr. shureim Rufe bakinsa.

Arab dress ne kala kala Na maza, Kalar waɗanda Yafi so, A ƙalla sunkai kala Hamsin sababbi fitigil dasu shaƙe cikin akwatin, Hada Arab turban ɗin da Yake naɗawa akanshi.

Atare da mutumin suka soma jera kayan acikin wardrobe ɗinsa, Bayan sun kammala jera kayan, Man ɗin Ya buɗe ɗayan akwatin Wa'iya zubilla Uncle musa Ya gwangwaje ɗan nasa da Haɗaɗɗun leather shoes da tsadaddun turarurruka Na Larabawa, Da suran Kayayyakin amfani na gyaran Jiki, a gaban mirror suka jera Kayan, Bayan mutumin Ya kammala, Dr. shureim yai mashi godiya suka Yi sallama da shi.

Yana atsaye idonshi akan sabbin Kayanshi sai binsu ya ke yi da kallo, daɗi kamar wanda akayiwa albishir da gidan Aljanna.

Muryar Tani ce Ta janyo hankalin shi ga dubanta.

A yayin da ta ke shigowa ɗakin nashi

"Dr shureim barka da rana, Fatan Ka wuni Lafiya? Ya kwanan gidan uncle ɗin naka"

Hannunta biyu ruƙe da Faffaɗan wooden tray, daga saman shi jerin lunch ɗinsa ne.

Da fara'a akan face dinsa Ya soma Amsa mata gaisuwar"Alhamdulillah, Fatan kema Kina Lafiya ya aiki"?

"Lafiyalou, ai Munji daɗin zuwanka gidan nan, Ko ba komai zaka ɗebe ma Zeenatu kewa, Baiwar Allah jiya tayi murnar zuwanka, Tana matuƙar son yayanta" Fuskarta awashe Ta yi maganar, adai dai takai gaban table ta ɗaura mashi tray ɗin.

Murmushin gefen fuska Yasaki tare da faɗin"Allah sarki, Tun Jiya bata ƙara dawowa ɗakina ba, Idan ba damuwa ki kira min ita idan kin fita, nasan saboda Kunyar abunda Ya faru Jiya ne Yasa ta kasa zuwa gaishe ni da safe"

"Wlh kamar ka sani, abunda ya hanata zuwa kenan, ai zeenatu akwai kunya, Yarinyar kuma tana da mutunci ga kamun kai, Ga ilmi, ita dai taji daɗin rayuwarta, Gaskiya ba ƙaramin mai sa'a bane zai mallaki Zeenatu" tun da Tani ta fara Yi mashi sambatun Kyawawan halayar zeenatu Ya natsu Yana sauraranta haɗi da kallonta, Ya fahimci so ta ke Yi, Ta yi mata gyaran hanya awurin shi. Dama tun Jiya da yazo matar take ta yi mashi sambatu akan zeenatu.

"Idan badamuwa, inason Ganinta" washe baki Tani ta yi"Toh, yanzun nan zaka ganta," Da sauri Ta juya ta fuce daga ɗakin.

Tattara Kayan saman gadonshi yai, acikin Shopping bag ɗin Ya tura su.

Ajiyar zuciya ya sauke Ya koma gefen gadon shi ya zauna yana jiran ƙarasowar Zeenatu.

Akan Hanya Tani taci karo da zeenatu tana tafiya kamar munafuka, sam babu natsuwa atattare da ita, sai ƴan waige waige take Yi, har sai da suka bangaji juna da Tani tukunna ta zabura ta kalleta suka haɗa ido

"Ina kika shiga ne?"

"Ɗakin daddy" ta bata amsa "Hawayen menene akan fuskarki! Waya ta6amin ke" zumbura mata Baki Ta yi ba tare da ta bata amsa ba.

Ruƙo hannunta Tani tayi"Muje ɗaki ki gyara fuskarki, dr shureim ne yace in kira mashi ke" waro ido waje tayi jin ance Yaya shureim ke kiranta.

Jiki na rawa Tabi Tani suka nufi falo abakin stairs suka hau elevator takai su Second floor, Bayan sun fito da sauri suka nufi ɗakin zeenatu, sai da Tani ta jira tayo wanka tukunna ta taimaka mata wurin canza Kayan jikinta, Pakistan ta sanya riga launin blush pink har gwiwa, Tare da burgujejan wando Fari anyi mashi adon stones, Tani ta ɗaura mata Mayafi akanta, Babu makeup Iya kyawun fuskarta ne.

Flat shoes Ta zura a ƙafarta, Atare da Tani suka baro ɗakin Bayan sun sauko down, sai da Tani taja mata kunne akan ta natsu kada Tayi mashi hauka, ta amsa mata da toh.

A hankali take Yin tafiya tana nufar sashen room ɗinsa, a bakin ƙofar ɗakinshi ta la6e tana leƙensa Yana zaune idonshi akan screen ɗin wayarshi, Ya natsu Yana kallo ko motsi bai yi, Kunyace ta kama ta, muryarta Ƙasa ƙasa take ambaton sunanshi"yayana rabin raina" shiru dr a Shureim bai amsa mata ba

"Hubbyna" still shiru, da alama bai ji sautin muryarta ba.

Tunani ta soma yi ko menene ya ke kallon acikin wayarshi wanda yai silar ɗauke hankalinshi! Ras taji gabanta Ya faɗi sakamakon amsar da zuciyarta ta bata na cewa wata'ƙil hoton girl friend dinshi yake kallo.

Cikin sanɗa ta ke yin tafiya cikin ɗakin nashi duk don ta gano abunda Yake kallo, daga 6angare hannun dama na gadonshi ta zagaya tana yi mashi dogon wuya, ƙamshin turarenta ne Ya tona mata asiri, lumshe idonshi yai yana tunanin a ina aka samu fragrance me daɗin shaƙa a ɗakinsa, ɗagowar da zai yi keda wuya idonshi ya sauka akan zeenatu dake leƙan wayarshi, da sauri ya danna power button hasken phone ɗin ya ɗauke screen yai duhu.

Duƙar da kanta ƙasa ta yi, yanayin fuskarta ya canza"yaya shureim ɗina, ka wuni lafiya? Am sorry Jiya ban dawo mun gaisa ba" A hankali Ya miƙe ya zagayo ta Inda take atsaye dab da ita ya tsaya yana ƙare mata kallo.

Baisan ya akai ya tsinci kanshi da kallon wankan pakistan ɗin da ta ɗauka ajikin ta, ta yi bala'en yi mashi kyau, Yarinyar kamar Fure haka take da ɗaukar ido.

Tabbas Idan yaci gaba da kallonta zai shagala ne

Acikin zuciyarsa Ya ambaci

"A'uzubillahi minasshaiɗanirrajim"

A fili kuma Yace"Zeenatu, kada ki damu bakomai, ay nayi maki uziri kece kika takura kanki"

Muryarta da shagwa6a tace "Mommy ne tace inzo muci abinci atare, tun Jiya dana bar ɗakinka banci komai ba" Ya rasa gane wani irin yanayi yake ji atare dashi, tana yin magana blue eye balls ɗinta na jujjuyawa, Yatsun hannunta sai kerma sukeyi saboda rashi natsuwarta.

Abu mafi jan hankali a jikinta ƙirjinta kamar zasu tsonewa mutun ido "Ki jirani awaje"! Abunda Ya furta mata kenan "Yaya shureim ba abinci zamuci atare ba"? "Eh, amma ba'a cikin ɗakina ba, kinsan babu kyau mace da namiji su ke6e a ɗaki ko"? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh

"Bari na ɗauko mana kayan abincin sai mu koma dining room" tuna abunda ya faru Jiyane yasa shi yin saurin cewa"No! Ni zan ɗauka," amsa mashi tayi toh" Ya zagaya other side ya ɗauko tray din Kayan abincin da hannu biyu ya ruƙo shi, yana agaba tana bayanshi, a Haka suka ƙarasa cikin Haɗaɗɗen ɗakin Cin abincin gidan, Dining tables har kala Uku, Kowanne a kewaye da chairs, a saman table Ya ɗaura masu tray ɗin, suka zaune suna fuskantar juna, Hankalin shi ba ƙaramin kwanciya yai ba, A inda suke Masu aiki Na iya hangensu daga main palour.

Sai faman sakar mashi murmushi take Yi

"Yaya shureim, zamu dinga fita yawo atare ko? Kaga kullum ina agida daddy baya barina zuwa yawo, tun da na kammala secondry school kullum Ina agida" ta ƙarasa maganar tare dakai hannu ta ɗauki serving spoon ta buɗe warmer ta Fried rice ta zuba masu a plate Biyu, ta sanya masu spoons aciki.

Suna ci suna Yin fira ga lemunsu me sanyi a glass.

"Kada Ki damu, Munyi magana da daddynki, Yace yanason ina taimaka maki da wasu abubuwan"

Washe baki Tayi"yaya shureim zamu fara fita shan ice cream da zuwa cinema? And shopping ko"? Ɗaga mata gira yai alamar eh, cizon pink lips dinta tayi"Yaya shureim Amma ka ta6a yin soyayya"? Ƙiris ya rage ya shake saboda surutun zeenatu, girgiza mata kai yai"ban ta6a ba ke fa"? "Maza dayawa suna haukan sona, Ni kuma nafison auran miskilin namiji, mai ilmin addini dana zamani kuma Yana amfani da su, sannan me Koyi da sunnar Annabi Muhammad SAW"

Tunda ta fara lissafa kalar namijin da takeso, dr shureim ya dakata da cin abincinsa, Ya natsu yana kallon pink lips ɗinta, taƙi tsayar da idonta wuri ɗaya Sai faman ƙeƙƙeftasu takeyi kamar babie.

"Yaya shureim kai fa watakalar mata ka ke son Aure" baisan sa'adda Ya furta"ra'yinmu ɗaya" zare mashi ido tayi

"What"? Girgiza mashi kai tayi"amma yaya shurem idan ra'ayinmu ɗaya kenan bakason mace me surutu? Mara natsuwa mai rawar kai haka"? Murmushi ya sakar mata har dimples dinsa suka lotsa. "Nidai nace Ra'ayinmu ɗaya" ya sake nanata mata maganarsa, murmushin gefen fuska tasakar masa"indai dagaske Ra'ayinmu ɗaya da kai, Toni inason Namiji mai surutu mara natsuwa mai rawar kai, kaga kenan Kaima kana son mace irin haka"

dariya ce ta kubce mashi, Harya shaƙe da abinci Da sauri ta miƙa mashi lemu Ya kar6a Yana kur6a, Gwanin ban sha'awa haka suka cigaba da cin abinci tana Janshi da surutu.

*DAULAR OBIE ESTATE*

A ɗakin Hajjaty, Kwance suke asaman gadon sun mannewa juna, Babu sutura a jikinsu zufa duk ta wanke jikinsu tamkar A.cn ɗakin Bata aiki, tsawon awanni da suka gama sharholiyarsu baccine Ya ɗauke su, Faɗaɗan tafukan hannayenshi ya cikasu da boobs ɗinta, ƙafarshi ɗaya tana a tsakankanin cinyoyinta sosai Ya shigeta, Ahaka bacci yai awon gaban dasu.

Sautin ringing ɗin wayarshi ne Yai silar farkawarshi, Idanuwanshi sunyi jawur dasu, kasala duk Ta baibaye shi, daƙyar Ya Iya zame jikinsa daga nata, wani irin mayataccen kallo yake binta dashi, ji yake kamar ya ƙara second round don Baya gajiya da ita, matsawa yai saitin face dinta, ya kama lips dinta yai sucking dinsu, kafin A hankali Ya zame tongue ɗin ya mayar saman nipples dinta sosai yai sucking dinsu kamar zai karar dasu.

wayarshi sai ringing ta ke Yi yaƙi mayar da hankali kanta.

Jin Zafin abun da Yake yi mata ne Yai silar farkawarta, idanuwanta sunYi mata nauyi muryarta a disashe ta furta sunansa"Pravin pls ya isa haka, Yakamata Ka tafi, marece har Yayi, Nasan Hajiya saratu zata neme ka,"

ɗagowa yai da idonshi Ya kalli face dinta "Kin gaji dani ne"? Girgiza mashi kai tayi"kaima ka sani bani gajiya da kai pravin, da ace zan gaji da kai da tuni na rabu da kai" daƙyar take yin magana idanuwanta na lumshewa har yanzu mayen shi ta ke Yi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull