Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 36

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 36

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 36: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 36. Bayan tafiyarta obinna ya dubi aminin nasa"shegen…

3,353 words

Bayan tafiyarta obinna ya dubi aminin nasa"shegen bisa, faɗamin waya koya maka kallon mata? Ni dai ya iya sanina dakai mace bata agabanka, sai gashi yau kana neman zauce wa saboda kaga Mace" da zolaya ya yi mashi maganar.

Tuntsirewa Inyamurin yai da dariya yana faɗin"Don kawai na gani na yaba, matar ce ba ƙaramin burgeni take yi ba, inason mace mai tsafta da iya ado, sannan kasan Ni ma'aboci son ƙamshine, gaskiya ta tafi da imanina, ka taimaka min inaso na mallake ta, dagaske nake ba wasa ba"

Da mamaki akan fuskar obinna ya ɗan zaro idona yana kallon shi, yayi mamakin jin abun da ya furta, kuma ga dukkan alamu dagaske yake har cikin ranshi.

"Amma dai zolaya ce wannan ko"? Jan gemun shi yai tare da cewa"na ta6a yi maka zolaya akan irin wannan maganar"? Girgiza kai Obie yai" Bamu ta6a ba, sai dai nayi mamakin kalamanka, tun da muka taso baka ta6a nuna kana buƙatar mace ba, ka haramtawa kanka tara Iyali, gaba daya rayuwarka akan kasuwancinka ta ƙare"

Fuskar Inyamurin da fara'a ya yace"wannan karan dagaske nake, Inasonta da aure mutumina, ka yi min hanyar da zan samu shiga wurinta, don bana son abun ya ɗau lokaci" farin cikine tsantsa akan fuskar obinna abunda yajima yana yi mashi fata

"In sha Allah, zanyi maka ƙoƙarin yin hakan, nima nayi maka sha'awar auranta, Matar tana da hankali da natsuwa"

Cigaba da tattaunawa sukayi a tsakaninsu.

A 6angaren Hajjaty kuwa, Jikinta duk yai sanyi tun da ta baro garden din gabanta ke faɗuwa, tsigar jikinta na tashi, duk akan kallon da abokin obinna yayi mata.

Gaba ɗaya hankalin ta baya atare da ita, tafiya ta ke yi Zuciyarta nayi mata saƙe saƙe, har ta ƙaraso entry hall tana ƙoƙarin bi ta ƙofar palourn Cikin rashin sani suka bangaji juna ita da Hajiya saratu da ke ƙoƙarin fitowa daga falon, Ta kimtsa cikin shiga ta alfarma, da alama wurin aiki zataje.

Da sauri Hajjaty ta ɗago su ka yi tozali da Hajiya saratu, Rass taji gabanta Ya faɗi, Muryarta na kerma ta furta"kiyi haƙuri ban lura dake ba..." daƙyar ta ƙare maganar ganin irin ƙasƙantaccen kallon da Hajiya saratu ke watsa mata.

Tana huci ta furta"baki da hankaline? Ko makauniya ce ke? Wato tsabar nuna isa har kin kai matsayin da zaki iya haɗa kafaɗa ni ko"! Fuskarta a ɗaure tamau tayi maganar.

Hankalin Hajjaty ba ƙaramin tashi yai ba, sam bata lura da pravin dake abayan Hajiya saratu ba, Ya shirya cikin black suit, hannunshi ruƙe da wayarshi daya kara a kunnanshi, Waya yake yi amma hankinsa na akan Hajjaty da hajiya saratu

"Bada sanina na bangaje ki ba, hankalina baya atare dani"

Harara Hajiya Saratu ta watsa mata tamkar ƙwayar idonta zata faɗo ƙasa"Ƴar rainin wayau, wai bana hanaki shafa mahaukacin turaren nan a jikinki ba? Ke baki da hankaline? an gaya maki Zawarci haukane" Rai a6ace ta faɗi hakan tare da ruƙo Mayafin Sarin Hajjaty da hannunta.

Idanuwanta tuni sun ciko tab da ƙwalla.

"Wlh daga rana irin ta yau idan na kuskura na ƙara jin ƙamshin turaren ƴan borin nan naki saina sauke maki kwandon rashin mutunci akanki,"

Azafafe ta ƙare maganar, tare da ingiza hajjaty tayi taga taga zata faɗi, Pravin harya Yunƙura zai tarbeta, da sauri Ya fasa ganin matsiyacin kallon da Hajiya saratu ta watsa mashi

"Wuce muje" cike da isa ta ba shi umarni, da sauri Yabi bayanta suka nufi parking space.

Da ido hajjaty tabi su da kallo, hawaye tuni sun wanke fuskarta, jikinta na rawa ta nufi cikin gidan, masu aikine ke ta kai komo acikin babban palourn.

Ba tare data bari sunyi tozali da wani ba, tayi saurin nufar bedroom dinta, harta kusa shiga taci karo da twins sunyi shirin zuwa office.

Atare suka ɗago suna kallonta, muryarta na rawa ta furta"ina kwananku kun tashi lafiya" Harara Zayn ya watsa mata"ji wata tambayar rainin wayau nan, taya zaki tambayi mun tashi lafiya? Bayan gamu kin gan mu a tsaye kan ƙafafunmu"

Zaid yace"Zayn, please watch your tongue Hajjaty tamkar uwa take agare mu," a harzuƙe yace"what! ƴar aikin ce zata zama uwar mu? oh Ko dan saboda tana ƴar india? To ai mu ba indiyawa bane ubanmu ne ɗan can, Nifa baki burgeni saboda ban yadda dake ba, ina zargin hada ke ake cin amanar mahaifiyar mu"

Afirgice Hajjaty ta zazzare ido tana duban fuskar zayn da yayi mata, tuni zufa ta soma tsastsafo mata.

"Pls zayn ya isa haka, idan ba zaka girmamata ba, bai kamata kana gaya mata magana akan idonta ba" yai maganar tare da jan hannun Zayn suka nufi hanyar fita palourn.

Ba zata Iya jure wulaƙancinsu ba, da sauri ta nufi bedroom dinta, tana shiga ta faɗa saman gado ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita.

Hajiya saratu tuni ta shige cikin mota, pravin na atsaye ya ruƙe murfin motar"Lafiya? Ba zaka shigo bane"? Tayi maganar tana dubanshi ganin yaƙi motsawa Ya kafe ta da ido.

"Bana so na 6ata maki lokaci, Ki tafi kawai Ni zanje a motata" da mamaki akan fuskarta tace"saboda me"?

"Cikina ne Ya 6aci ina buƙatar shiga toilet, " yai maganar yana shafa flat stomach dinsa Ta6e baki tai sam bata kawo komai aranta ba tace"Okey, saina dawo" duƙowa ya yi saitin fuskarta ya manna mata peck a fore head dinta"Ki kulamin da kanki My wife, zanyi missing dinki, Ni kona minti ɗaya banaso kiyi nesa dani" kwa6e fuska tayi

"kalaman ka ba zasu hanani tafiya office ba, sai dai su 6ata min lokacina, pls ka kula min da kanka," murmushin yaƙe ya sakar mata, Aranshi bai ji daɗin maganarta ba, halinta ne bata Iya kalaman soyayyaba kuma ba ta cika son yana yi mata ba.

"please take care of ur self, ayi aiki lafiya"ya ƙare maganar tare da tura murfin motar ya rufe mata ita.

Security din dake zaune a driver seat na motar yaja ta suka nufi shantalelen titin da zai fiddasu daga estate din.

Shu'umin murmushine Ya bayyana akan fuskar Pravin, Jiki na rawa Ya juya ya nufi entry hall, adai dai lokacin twins sun fito hannunsu ruƙe cikin na juna suka ci karo da shi.

Gaba daya suka tsareshi da ido suna kallon shi Fuskarshi da fara'a ya furta"Kyawawan samarina har Kun kammala Shiryawa za'a tafi office," zaid ne yai ƙoƙarin faɗin"daddy, ina kwana ka tashi Lafiya" Ya amsa mashi da lafiyalou My son, kafin ya maida dubanshi ga Zayn da ya haɗe rai.

"Lafiya zayn ka tsare ni da ido? Ko ba ka da lafiya ne"? Basarwa yai"lafiyata qalou daddy, just nayi missing dinka ne, amma ya akai daddy naga ka dawo gida? Ba aiki zakaje ba"?

"Key ɗin mota ɗina na bari a ɗaki, shi zanje na ɗauko" zayn yace"bari na ɗauko maka key din" yai maganar yana ƙoƙarin juyawa a hanzarce pravin ya damƙi hannunsa"bana so ku makara yakamata ku wuce ku tafi office, zanje na ɗauko da kaina, Ku kulamin da kanku,' bai jira amsar su ba, yabi ta gefensu ya nufi cikin falon.

"Zaid sai da na faɗa maka matarcan baƙar munafuka ce, saboda ita daddy yayi mana ƙaryar zai je ya ɗauko car key a ɗaki" Yana huci yayi maganar Zaid yace"please bro, ka yi mashi kyakkyawan zato, bai kamata kana zarginsu ba"

Tsoki Zayn yaja"wlh duk ranar dana gano ainihin abunda suke aiwatarwa saina tona masu asiri awurin mommy, ita kuma matar can saina koreta daga gidanmu ta koma can ƙauyansu na Indiya," ya ƙare maganar tare da jan hannun zaid suka nufi motarsu.

Hajjaty na akwance cikin mawuyacin hali, idanuwanta sunyi luhu luhu sun rune zuwa Ja, sai faman shessheƙar kuka take yi, Har ya shigo ɗakin bata sani ba, Haye wa yai saman gadon ya zauna daga gefenta, Cikin sanyin murya Ya furta"My heart beat" har cikin kunnanta ta ji muryarshi, sai dai takasa ɗagowa ta kalle shi, hakan Ya tabbatar mashi da ranta Ya 6aci.

"kiyi hakuri, banji daɗin kalaman da saratu ta furta maki ba, ba yadda zanyi ne shiyasa ban dakatar da ita ba, nasan ranki ya 6aci but pls ki daure,"

Cikin shessheƙar Kuka tace"bazan iya jurewa ba, nagaji nagaji nagaji da irin wulaƙacin da suke Yi mini, sun tsaneni basu ƙaunar ganina, ita da zayn shima yaci mutuncina, zaid ne kaɗai ke ƙaunata"

Dafe kanshi yai da hannu ɗaya, Kafin Yace"pls Ki ɗago muyi magana" "Ai bana son kallonka, raina ƙara 6aci yake yi" lumshe idonshi yai haɗi da ware su saman Bayanta.

"Ban ji zafin kalamanki ba, saboda laifina ne, Ni ne silar komai, " sai da yai wannan furucin ta ɗago da kanta, tana fuskantar ceilling, taƙi Yarda su haɗa ido. Ba zato ba tsammani taji Ya kwanto da kanshi saitin fuskarta, ƙamshin turarensu ya addabi hancinansu.

"Ki faɗamin me kikeso nayi maki wanda zai kwantar maki da hankalinki" Harara ta watsa mashi muryarta da shagwa6e ta furta"pls ka tashi ka tafi office, ka zauna kana 6ata lokaci akaina" "Saboda kin cancanta ne, lokacina nakine, har aikin sai in fasa zuwa idan kinaso" Yai maganar Yana kashe mata ido.

Batasan ya akai ta tsinci kanta da sakar mashi murmushi. "Inaso na faranta maki, don haka ki shirya dama kin faɗamin kinason haihuwa" zare mashi ido tayi'acikin gidan nan? Salon aganni da ciki a tuhumeni" da zolaya yace"sai kice na Obinna ne, kinga shikenan kin kashe bakin magana' fashewa sukayi da dariya cike da nishadi.

"Idan hakan ta faru ko kowa zai ƙyaleni, Hajiya saratu saita kasheni" jan kumtunta yai da hannunshi"Ai ko dana kasheta nima," lumshe ido tayi"pravin ka tashi ka tafi office aiki na jiranka.

'Waya faɗa maki Ina yin aiki ni? Nifa salary kaɗai nake kwasa, bana yin Aikin komai ko naje office din, P.a dina ke taimaka min," ya ƙare maganar tare da ɗaura tafin hannunsa ɗaya saman chest dinta, a hankali yaci gaba da yin squeezing dinsu, numfashintane ya soma canzawa ta soma cizon la66anta.

"Faɗamin Ina kika je"? Cikin yanayi najin shauƙi ta amsa mashi da cewa"Garden naje kaima Obinna da amininsa Kayan marmari" ganin ya ɗaure fuskarshi yasa tace"lafiya' "Mutumin bai kwantamin araina ba! Bana son kina zuwa wurin obinna idan abokanansa suka zo, dattawan nan shegen son mata garesu, musamman irinki babu namijin da zai ganki ya kawar da idon shi"

Ta6e la66anta tayi yayin da suke kallon juna "Are you jealous of me?Meyasa shi obinna baka kishi da shi sai abokanan..." kasa ƙarasa maganar ta yi jin ya mannata da ƙirjinshi"saboda shi na yarda dashi, bazai ta6a nuna kwaɗayi akanki ba, dattijon yana da kamun kai, kuma baida burin ƙara aure tun da matanshi suka rasu, shi ko amininsa Jan kunne tsaf zai Iya cewa yana sonki"

"Idan hakan Ya faru mai za ka yi mashi" tayi maganar tana shafa Wuyanshi da yatsun hannunta. Kashe mata ido ɗaya yai kafin Ya bata amsa da cewa "Gemun shi zan tsige" dariya suka saki, da sauri Ya haɗe bakinshi da nata, Hannayenshi Biyu tallabe da kanta tamkar zasu cinye harsunan junasu.

*San Antonio Texas*

*Army headquarter*

Babbar headquater ce mallakin sojojin san antonio, Haɗaɗɗen gini mai girma da faɗi, launin fentin head quater din army green ne, Tun daga bakin entry way na shiga headquater din zaka fara cin karo da Giant soldiars Cikin ta da wajenta maƙil Yake da Gwarazan sojoji sadaukan Gaske masu ƙirar zakuna, kowan nan su Ya kimtsa cikin shiga ta Kakinsu, ƙafafuwansu sanye da army boots, sun ruƙe Jibga jibgan bindigu a hannuwansu, haka zaika ƙugunansu a soke suke da pistols, babu wasa akan fuskarsu cikin taku na majiya ƙarfi suke kewage ko'ina na Gate din shiga headquater din.

Danƙareriyar motace Haɗaɗɗiyar gaske mai numfashi ƴar ubansu ƙirar Mercedes-benz S-class launin black ta sharoro da matsakaicin gudu kaitsaye ta nufi Bakin Hq din, tunkafin ta ƙaraso sojojin suka ƙura ido suna jiran ganin wani isasshen ne wannan ɗan kasada mai shirin zuwa lahira yake yi masu tuƙin ganganci a saman titin su.

Sai da mai motar yakusa zuwa gabansu, Ya rage gudun motar, tamkar na cikin motar baisan da sojojin dake tsaron headquater dinba, Ya soma ƙoƙarin kutsawa zai ƙetare gate din, aiko kamar mayunwatan zakuna suka tunkari motar, Wasu fusatattu daga cikinsu tuni sun saita motar da bindigar hannusu, da kakkausar murya suke faɗin

"Hey! Stop the car! Otherwise we'll attack you"!

Gaba ɗaya sun kewaye motar, Da ƙarfi wani baturen Soja Ya daki gaban motar da tafin hannunsa tamkar zai 6alle ta, A harzuƙe ya furta

"Ka sauke glass ɗin motar, Idan ba haka ba zaka fuskanci horo mai tsanani daga gare mu"

duk wannan suratan da sukeyi na cikin motar yaƙi fitowa babu alamun zai buɗe murfinta, Hakan ba ƙaramin hayaƙa su yayi ba"

"You're running out of time. I want you to come out of the car now! If you don't, I won't hesitate to shoot! This isn't a game, I'm serious. you have five seconds!" baturen sojan da ya dafe motar da tafin hannunsa ne Ya furta hakan, Sai da suka gama harzuƙa Zuciyarsu a maƙogaro, a lokacin da basuyi tsammani ba, mamallakin motar Ya tura murfin Ya buɗe, Rai 6ace suka ƙura ido suna jiran ganin wani isasshen ne wannan uban Ji da kan.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_~*BossLadiesWriters*~_

_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_

~Middle step~

_The Prisoners E22🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

_UMMIN AMERICA🔥🔥🔥_

A hankali ta zuro ƙafarta ɗaya daga cikin motar wow, high hills ne launin army green sanye a ƙafarta, sunyi bala'en yi mata kyau, Launin fatar ƙafarta ka ɗai abun kallo ce, kai kace hasken rana bai ta6a shafarta ba, tsabar kyan fatar da salƙinta.

Tun kafin ta ƙarasa fitowa sojojin suka sassauta fushin fuskarsu, Jikin kowan nan su yai la'asar ƙamshin shu'umin turaren jikinta ya daki hancinansu har cikin maƙoshin su fragrance din ya ratsa, Tabarakallahu ahsanul khaliƙin, gaba ɗaya ta tafi da imanin su, basu san sa'adda Bindugun hannunsu suka faɗi ƙasa ba, Ta yi matuƙar tafiya da hankalinsu, wani irin mayataccen kallo suke bin surar jikinta da shi kamar zasu kai mata hari.

Black american ce, A zubin halitta tana da tsayi da jiki, Launin fatarta Chocolate colour ne, Bodycon ce a jikinta, long sleeved gown dai dai gwiwa rigar ta tsaya mata launin Army green, daga ganin ta kaga ƴar duniya hayaƙin taba, baƙar a shana ƙona gari, Irin Ruƙaƙƙun karuwan nan ne Waɗanda suka amsa sunansu A harkar Bariki,Wannan da kuke gani bakowa bace face UMMIN AMERICA, hamshaƙiyar macace mai zaman kanta, Idanuwanta A tsaitsaye suke, Bata da mutunci, kuma bata da kunya ko misƙala zarratin,Tun daga kan shigarta zaka shaida fitsararta, Gaba ɗaya rigar ta bayyana tsiraicinta, boobs ɗinta sun cika faffaɗan kirjinta, tamkar zasu fasa rigar su fito waje don atakure suke an matsesu.

Flat tommy ɗinta tamkar ba'a saka abincin acikinsa tsabar ɗamewarsa, ga Uban qugu dake gareta tamkar ɗaura mata shi akayi saboda faɗinsa, ko kofi aka ɗaura a tudun mazaunanta tsaf zai zauna batare da ya faɗo ba.

Wani irin daddaɗan ƙamshine ke fita saƙo da lungu na Jikinta.

Round face gare ta,Tasha Uban make up, tamkar an zanata don kyau, Ga eye lashes da akayi mata fixing masu tsayi, dogon hancinta Na manne da Nose ring mai kyan gaske, Haka yatsun hannunta na dama na sanye da knuckle ring, long nails din yatsun hannunta fixing dinsu akayi.

Sumar kanta tasha gyara, sai dai daga gani hair wing ne ta daura ba asalin sumar kanta ba, amma zai wuya mutun Ya iya ganewa.

Hankalin maza fa ya tashi haiƙam, gaba daya sun rasa natsuwar su, sai faman haɗiyar yawu suke yi kamar zash lashe ta.

Muryarta tamkar ana busa sarewa ta furta"Zan Iya shiga Ciki"? Har suna haɗa baki wurin bata amsa da cewa"You're welcome"

shu'umin murmushi ta sakar masu, har dimple din gefen fuskarta Ya lotsa, juyawar da za ta yi, mazaunanta suka girgiza gaba daya sojoji suka zabura tamkar zasu tallabe mata shi.

Komawa Cikin motar tayi, kafin ta rufe motar, wani daga cikin sojojin yai saurin datse mata murfin, A tsanake taci gaba da yin driving ta nufi cikin head quarter din.

Ta tafi tabar su da jarabar kallon surar jikinta da su ka yi, ba zasu iya jurewa ba ai ko da sauri suka nufi cikin head quarter din donsu samu damar ƙare mata kallo ko sun rage raɗaɗin da zuciyarsu ke yi masu.

Bayan tayi parking ɗin motar, ta fito hannunta ruƙe da i phone dinta, Hankulan sojojin dake Zarya a headquarter din gaba ɗaya ya dawo kanta, kamar sun samu talabijin, Matarce akwai Iya jan hankalin maza da surar jikinta, duk idan Tayi taku ɗaya jikinta sai ya girgiza hakan ba ƙaramin hayaƙa maza yake yi ba.

All eyes on her, Sojojin Tamkar zasu kai mata hari, sai dai ba damar Yin hakan,Wani irin ƙwarjini gareta, A fuska bata da wasa, Zazzafa ce, Me zaman Kanta.

Ta wutsiyar ido take kallon masu ɗago mata hannu da masu yi mata alamar suna son yin magana da ita.

Ko kallo basu ishe ta ba, jefi jefi takan ɗan wurga eye balls dinta akansu, da gangan take kashe masu ido ɗaya ko ta ciji lower lip dinta da harshe, ɗabi'arta ce Yin hakan, duk don ta ƙara hayaƙa su.

Kaitsaye ta nufi hanyar da zata sada ta da office din commender domin amsa kiran da yayi mata, tasan ko'ina na headquarter din, don ba baƙuwarta bace, Ba yau bane rana tafarko da ta fara shigarta.

Tun kafin ƙarasowar ta, tuni Anyi mata iso wurinshi, jiranta kawai Yake yi, yana daga zaune saman chair, acikin katafaren office dinsa, komai na cikinsa army green ne, hatta desk din gabanshi, dake dauke da computer dinsa, da wayar hannunsa tare da flag and map, daga jikin bangon office din akwai book shelf, da jerin hotunansa da awards dinsa, bashi kaɗai bane a office din hada Major.

Shigowarta office din, Tuni sanyin Iskar A.c ɗin cikinsa ta gauraya da ƙamshin shu'umin turarenta.

Har saida suka shaƙe shi sosai a hancinansu.

Da kwarkwarsa ta ƙarasa gaban desk dinsa, kamar yadda ta saba yi mashi duk in tazo office dinsa haka yau ma tayi mashi, Ta buga ƙafa tare da sara mashi, hakan ba ƙaramin ƙayatar da shi yai ba, har sai da suka saki murmushi, tun kafin Ya bata iznin zama, ta zauna saman chair din dake facing dinsa, ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, murmushi ta sakar mashi haɗi da ɗaga mashi gira ɗaya ta kashe mashi ido.

A wayance ta soma yin magana cikin harshen turanci"fatan na same ku lafiya" lumshe ido commender yai tare da kai hannu ya gyara zaman wuyan rigar kakinsa.

"Lafiyalou ummi, I'm glad to see u, Ina fata kiran da mukayi maki bai taƙura maki ba"?

Ɗaga mashi gira tayi alamar eh ba tare da ta furta ba, a mutunce suka gaisa da junansu. Bayan kowan nan su ya natsu, Major Ya miƙe ya bi ta ƙofa ya fuce waje jim kaɗan ya dawo hannayen shi ruƙe da mugs na coffee guda biyu ya ɗaura su saman desk, ya ɗago da ido Ya kalli Ummi"zaki Iya sha" ta furta okey, kafin takai hannu ta dauki mug din ta soma kur6an coffee din, da alama ya yi mata dadi kusan sau uku tasha kafin ta ajiye mug din, ta dawo da dubanta ga commender"am all eyes"

"Dalilin da yasa na kira ki ummi, Magana ce mai muhimmanci muke san yi da ke, Ina fata za ki bamu haɗin kai kamar yadda kika saba taimakon mu" cikin harshen turanci commender yayi maganar a tsanake.

Hankalin major na akan ƙirjinta har wani ƙara leƙensu yake yi kamar zai zura kanshi cikin rigarta.

Kallon da Commender ya watsa mashine yasa shi saurin kawar da idonshi ya kame mutuncin kansa

"Babu takura, ko da yaushe ina maraba da ku, zaka Iya faɗin komai ka ke so kai tsaye"

ta ƙare maganar tana shafa saman boobs dinta da yatsun hannunta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull