Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 38

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 38

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 38: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 38. Dr. Laura na niyar juyowa don ta bata amsa, ba…

3,351 words

Dr. Laura na niyar juyowa don ta bata amsa, ba zato ba tsammani, Suka hango Dr. Mark tare da dr. brown sun nufo ƙofar ɗakin, Kusan a tare suka shigo.

Gaisawa suka Yi da dr laura, Cikin girmamawa su Angel suka gaishe da su, Bayan sun amsa masu, suka tayasu murnar farkawar ɗan uwansu

Kafin daga bisani Dr Mark Ya soma Yin magana"Dr. Ke muke nema, Sojojin nan sun Kira Awaya, idan ba damuwa zamu Iya zuwa office muyi magana"

Amsa mashi tayi da toh, ba tare da 6ata lokaci ba suka fuce daga ɗakin.

Hankalin Angel yaƙi kwanciya burinta taji me zasu tattauna, fatanta Allah yasa su amince da maganar maidasu Nigeria.

Bayan fitarsu ɗakin kaitsaye office din dr Laura suka nufa, kowan nan su ya samu wuri saman kujera Ya zauna suna fuskantar Juna da ita

"Ina sauraronku, me sojojin suke ce ne"? A ƙagare ta tambayesu Dr mark Ne ya soma kora mata jawabi"Commender dinsu ne Ya kirani awaya, Ya sanar dani cewa Chief na Isod Ya Amince zai kar6i case din Yaran...." tunkan Ya ƙarasa maganar, dr laura tasaki murmushin farin ciki

"Bayan haka, sun ƙulla Yarjejeniya tsakanin ita ummin american da su sojojin, zuwa Anjima zasu zo asibitin domin shirya yaran, zasu ɗauke su zuwa gidanta, sai dai zamuyi kewarsu saboda Commender din ya faɗamin next week chief na isod zai bar ƙasar tare da yaran" ya ƙarasa maganar idonshi Akan dr laura, mood din fuskarta ya canza zuwa damuwa, ba ta yi tsammanin zasu bar ƙasar da wuri ba, zaman da su ka yi da su na kwana huɗu ba ƙaramin sabo su ka yi da juna ba, sai dai ta wani 6angaren taji daɗi kodan saboda Angel da ta roƙe ta akan ta taimaka masu su koma ƙasarsu.

"Dr lafiya? Naga kamar yanayin fuskarki Ya canza? Ko baki ji daɗin maganar bane"? dr. Mark ne yayi maganar ganin ta haɗe fuska, Murmushin yaƙe tasakar mashi "No ba haka bane, Na saba da yaran ne, banaso su yi nesa dani, banyi tsammanin zasu bar ƙasar da wuri ba, inaso zan nemi alfarma abar mana su ko da one month ne su yi anan kafin su tafi"

Dr brown yace"ba zai yiwu ba dr, da ace case dinsu a hannun sojojin yake zamu Iya neman alfarmar abar mana yaran su zauna a wurinmu, sai dai kash sun riga da sun damƙa case din hannun chief na isod, kuma kinsan shi ba ɗan ƙasar nan bane, A ƙasar shi yake zaune Aiki ne mai muhimmanci ya kawoshi america, tun cikin weekend daya wuce yaso barin ƙasar, saboda case din Yaran Ya fasa tafiya, yanzu haka da nakeyi maki magana, yana shirye shiryen barin Washinton zai shigo garin mu saboda ya haɗa kan yaran ya tafi dasu, mutumin babu wasa a aikinsa, Baison 6ata lokaci.

Jikin dr. laura ba ƙaramin sanyi yai ba, tana son su Angel, ganin duk ta damune yasa Dr mark kwantar mata hankali"Tafiyarsu ba yana nufin mun rabu da su ba, Kada Ki manta Sojojin ƙasarmu ne suka tsince su, bayanan su da komai Yana a hannunsu, kuma zasu cigaba da bibiyar rayuwar yaran, wannan dalilinne ma yasa suka haɗasu da Ummin america.

Gyaɗa kai Dr Laura Tayi"Ni damuwata depression din dake damun yaran, da kuma Yaron dake fama da ciwon zuciya, Hankalina bai kwanta da Ummin america ba, Shin zata Iya bamu su kulawar da zata sanya su manta da damuwarsu? nafa santa bata da mutunci macace mai izza kuma ta shahara wurin Iya karuwanci....." Damuwace ƙarara kan fuskar dr laura, idanuwanta tuni sun ciko tab da kwalla.

"Yaran sunfi buƙatar kulawar mace wadda tasan ciwon haihuwa, bawai karuwa ba! Wadda ta saba ƙwacewa matan aure mazajensu tana fasiƙanci da su! Yakamata Kuyi tunani akan hakan, Ni zanyima Commender din nasu magana, akan su canza masu wadda zata raine su, Yara fa har goma sha ɗaya za'a damka ma karuwa, gaskiya basuyi tunani mai kyau ba, zata Iya 6ata su" ranta amuƙar 6ace take Yin maganar.

Cikin kwantar da murya Dr mark yace"ina baki shawara dr, kada kice zaki shiga maganar nan! Tun ranar da major ya kawo shawarar abata kulawar yaran, Kin nuna kuskuren yin hakan, amma sai basu damu ba, saboda sunsan halinta, kuma sunsan zata Iya ne, kamar yadda yace ta saba yi masu aiki, so bai kamata ki damu ba"

Dr brown ya ɗaura da cewa"sunfi mu sanin wacece Ita, Mu sanin da mukayi mata na karuwa ne, su kuma a matsayin ma'aikaciyarsu suke kallonta, ba zasu ta6a damƙa mata amanar yaran ba tare da sun aminta da ita ba"

Gyaɗa kai Dr Laura Tayi"Shikenan na haƙura, bazan yi masu magana ba, amma inaso zan ba Masoyiya Angel Kyautar waya, saboda inaso mudinga Yin magana da ita akai kai"

"Na fahimci kina son yaran sosai, Ni kaina na kamu da ƙaunarsu, Har na fara jin kewarsu" acewar dr. Mark

Dr brown yace"aini har ƙasarsu zan Iya zuwa ganinsu idan naso, don haka banda damuwa, muna atare da su"

Sun jima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani, Kowa ya koma bakin aikinsa.

*DAULAR ALHAJI MUSA*

*Dr Shureim❤*

Ƴan kwanakin da yayi a gidan Uncle ɗin nasa Rayuwarshi ta fara canzawa, a yanzu dr. Shureim baida matsalar komai, ta kowani 6angare yana samun kyakkyawar kulawa, kullum yana acikin gida, idan ya gaji da zaman ɗaki yakan fito ya zagaye gidan tare da zeenatu, yana matuƙar jin daɗin kulawar da take bashi, sun shaƙu da juna kamar sunyi shekara atare, hatta abincin atare suke cin shi, sai dai akwai wani abu da ya fara damun zeenatu, hoton da yake yawan kallo awayar shi, abun yabi mashi jiki kamar ibada, Idan ya fara kallon hoton baya so kowa yazo kusa da shi, kuma baya son kowa yasan hoton menene yake kallo, duk idan ta faɗo ɗakin shi yana cikin kallon hoton da sauri yake danna power button na wayar ya kashe ta, ta rasa gane wacece yake yawon kallo? Don ta fahimci ba ƙaramin so yake yi mata ba, gashi ita kuma Allah ya jarabceta da masifaffan kishi, ba ta son ganin yana kallon hoton, Har kuka take yi a 6oye ba tare sanin kowa ba.

A Kishingiɗe yake saman katafaren gadonshi, tun safe bai fita ko'ina ba, ko ƙofar bedroom dinsa bai leƙa ba, farin short ne ajikinsa, babu riga, gaba ɗaya hankalinsa na akan screen din apple laptop dinsa dake ajiye saitin kanshi daya ɗaura saman pillow,

Sam bai ji takun tafiyarta ba, saboda hankalinshi baya atare da shi, wankan swiss lace ne a jikinta, launin ash colour riga da skirt sunbi shape din jikinta, kamar a jikinta aka ɗinka kayan, duk da bata ƙiba kayan sunyi bala'en Yi mata Kyau, Tani da Lami ne sukayi mata Make up, hatta ɗaurin ɗan kwalin kanta sune suka ɗaura mata shi, ziririyar sarƙar wuyanta ta diamond ce, stone din jikinta sai ƙyalli Yake Yi, ta yafa gyale a saman kafadarta, hannunta ruƙe da handbag, fragrance din turaren jikinta mai daɗin shaƙa ahanci.

Hankalinta ba akwance yake ba, tun kafin ta shigo ɗakin tayi mashi sallama bai amsa bata ba, har ta gaji da yin sallamar shiyasa ta yanke shawarar shigowa don ta ga ko bacci yake yi ne Tun kafin ta ƙaraso gaban gadonshi blue eye balls dinta suka sauka akan screen din Laptop nasa

Ras taji gabanta yai mugun faɗuwa, zuciyarta tamkar zata faso ƙirjinta saboda zafin da take yi mata, zeenatu tana da saukin kai sai dai tana da zuciya idan ta hasala, ranta ya 6aci sosai ganin abunda yake kallo, hoton da ta tsana a duniyar nan duk da batasan hoton menene yake kallo ba, ranta ya bata cewar budurwarsa ce yake kallo.

Idanuwanta sun makance, bakomai suke hango mata ba face dr shureim ɗinta rungume da mace a kirjinsa.

Runtse ido tayi da karfi ta fasa wata irin gigitacciyar ƙara wadda tayi silar firgitar da shi, da sauri Ya miƙe tare da wurga idonshi Kanta, tuni ta saki jakar hannunta ƙasa, Zafafan hawayene suka wanke fuskarta.

Hankalinshi ba ƙaramin tashi yai ba, a hanzarce ya sauko daga saman gadon ya nufeta fuskarshi da alamun ruɗu ya furta"zeenatu! Lafiya? Meya faru?

Girgiza mashi kai tadinga yi tana faɗin"kada ka matso kusa dani yaya shureim, inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un" gaba ɗaya ta gama rikitar dashi"zeenatu ki natsu kiyi min bayani meya faru dake? Ko wani abu ne ya tsoratar da ke?

Cikin shessheƙar kuka tace"yaya shureim bazan Iya jurewaba, zuciyata zata Iya bugawa, tun ɗazu mukayi magana dakai akan zamu fita yawo atare, kace min inje in shirya kafin in dawo kaima za ka shiga wanka ka kimtsa, ashe baka yi komai ba, ko wankan ma bakayi ba, ka zauna kana kallon hotonta saboda tafi ni mahimmanci awurinka, ba tun yau ba kullum ne saina ganka kana kallonta, wai wacece wannan ne? Dame tafi ni? Numfashinta na fita da hucin zafi ta ƙarasa maganar, tare da juyawa da gudu ta fuce daga ɗakin nashi.

Hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba, idonshi akan bayanta harta 6ace ma ganin shi.

Dafe kanshi yai da hannu ɗaya, har cikin ranshi baiji daɗin kalamanta ba, baiso yai silar 6ata mata rai ba, duk da bai fahimci inda maganganunta su ka dosa ba, lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kafin ya ware su a hankali, yayin da zuciyarshi ke tariyo mashi furucin da tayi mashi, yasan bai kyauta mata ba, ta ƙwalla fa rai akan son su fita tun Jiya shi da kanshi yai mata alƙawarin yau zai ɗauke ta a sabuwar motarshi su fita yawo.

Cikin sanyin murya ya furta"am sorry my zeenat, " da sauri Ya nufi toilet don yai wanka.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_

~Middle step~

سجن القدر❤🤍❤

_THE PRISONERS E23🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

Confusion of the heart💫

Sir mubarak ne zaune Cikin Motarshi, da su ka yi parking dinta a harabar ajiye motoci na asibitin Obinna,Tanƙameman asibiti ne Ya haɗu tamkar ba wurin Jinyar marasa lafiya ba, An zuba dukiya wurin gininsa, suna da ƙwararrun ma'aikata na gida Nigeria dana ƙasar waje.

Su biyu ne acikin motar, Shi yana a back seat na motar Ya zauna a hakimce, A yayin da Driver-operator dake driving dinsa Yana zaune saman driver's seat kowan nan su na sanye ciki kakinsa na sojoji, sun yi shiru, Sanyin A.c din motar na ratsa fatar jikinsu, ga dukkan alamu wani muhimmin abu ne ya kawo su asibitin, akwai wanda suke Jira Ya ƙaraso, tsawon mintuna Biyar, wani kyakkyawan matashin likita Ya nufo motar da saurin shi kamar zai yi tuntu6e.

A gaban motar su ya dakata da yin tafiyar, ya kai hannu yai knocking glass din motar, turo ƙofar da a kayi ne Yasa shi yin saurin gyara natsuwar shi, Sam hankalin shi ba a kwance ya ke ba, tun da sir mubarak ya kira shi awaya ya sanar da shi game da zuwan shi asibitin gaba ɗaya ya rasa natsuwar shi, saboda sanin matsayin shi a ƙasar.

"Dr fawan, shigo ciki mana " muryar Sir mubarak ce ta fargar da shi, Jiki na rawa ya shiga motar, ya zauna yana faman zazzare idonshi yace"daddy, ina wuni Ya gida ya Iyali" sir mubarak yace"lafiya lou fawan, Ya aiki ya fama da marasa lafiya" tun da ya fara magana bai ɗago Ya daura idonshi akan fuskar fawan ba, Hankalin shi na akan Wayar hannun shi da yake daddanawa.

Still muryarshi na rawa ya furta"Lafiya lou daddy, sai ga kiranka, Na ɗanyi mamaki" sai da ya ambaci hakan sir mubarak Ya ɗago da ido ya kalli fuskar fawan, duk da sanyin A c na motar, abun mamaki zufa ce ke tsastsafo mashi, kallon tuhuma sir mubarak yake jefa mashi, saboda zufar daya gani a saman goshin shi.

"Ya akai naga kana zubar da gumi? Ko baka da lafiya ne"? Yawu fawan Ya haɗiya tare da cewa"babu komai, Lafiya ta ƙalau"

Ta6e baki Sir mubarak Yai"Okey, Inaso ka kaini gidan kajin da kuke kiwo kai da Jazz," da alamun ruɗu akan fuskar dr Fawan yace"Gidan kaji? Daddy ban fahimci abunda kake nufi ba, waye ya buɗe gidan kaji" yanayin yadda ya furta maganar, babu alamun yasan da zancen.

Fuskar sir mubarak a ɗaure tamau yace"You know who I am. I don't need to explain this to you, Don haka kada ka 6oye min gaskiya, wani gidan kaji ne kuka buɗe kai da jazz? Da kanshi ya faɗa mini cewa kun zuba jari don kuyi kiwon kaji, kusan kullum ne saina kama shi yana yin waya akan gidan kiwon kajin ku"

Hankalin dr fawan ba ƙaramin tashi yai fa, Muyarshi na rawa ya furta"`wallahi thumma tallahi daddy bansan da zancen gidan kaji ba, sai dai ko ƙarya dr jazz yayi maka, ka ji na rantse maka da Allah..." Lamarin ya ɗaurewa Sir mubarak kai, Sojan dake zaune a driver seat Ya natsu Yana sauraron su, ta cikin ear-view mirror din motar Yake kallonsu.

"Fawan, Ka faɗamin gaskiya, ni nasan Jazz ba zai ta6a yi mini ƙarya ba, na lura gaba ɗaya baka acikin hayyacin ka, idan ma saboda ni ne to ka kwantar da hankalin ka, babu abun da zan yi maka, ni dai buri na shine ka kai ni gidan Kajin ku, inaso in gansu, nayi maka alƙawarin idan ka rakani na gansu zan ƙara maku jari"

cikin ruɗu dr fawan ya girgiza kai yana fadin"bazan yi maka ƙarya ba daddy, ina ganin ka tamkar uba agareni saboda ƙaunar dake a tsakanina da Jazz, wlh Daddy ni bamu ta6a yin maganar buɗe gidan kaji da dr jazz ba"

Da kakkausar murya Sojan dake a gaban motar yace"Sir, this boy isn't telling us the truth. Why don't we take him to the headquarter? Maybe if we do, he'll tell us the truth."(yalla6ai Yaron nan bazai fada mana gaskiya ba, Me zai hana Mu shiga dashi headquarter Wata'ƙil idan mu ka je can Ya faɗa mana gaskiya)

Zaro ido waje dr fawan yai, jin ance za'aje dashi headquarter, sir mubarak yace"kada ka damu ai basai munje headquarter ba, akwai bindiga a ƙuguna, "yai maganar tare da sanya hannu ya zaro bindigar Ya ɗaurata saman laps dinshi, tsabar tashin hankali ne tsantsa akan fuskar fawan.

Sir mubarak yace"idan na kashe ka na kashe banza, sai dai idan munje lahira ayi mana hisabi, don haka ka faɗa min gasiya, idan ba haka ba zan tarwatsa kanka da bindigar hannuna" bawan Allah dr fawan duk sun tsoratar dashi da barazanar su, ƴan hanjin cikin shi sun kaɗa.

Hawaye tuni sun soma wanke fuskarshi, cikin sanyin murya yace"ko da zaka kashe ni daddy, bazan fasa faɗa maka gaskiyata ba, wlh rantsuwar ɗan musulmi bani da masaniya akan maganar gidan kaji, daddy banyi niyar fada maka ba, amma don in kare kaina zan sanar dakai wani abu da baka sani ba" Hankalinsu gaba ɗaya yana akan fuskarshi.

Numfasawa yayi kafin ya ɗaura da cewa "Daddy, jazz baya zuwa aiki, yau kusan wata ɗaya da sati, bansani ba ko kunsan da hakan, Ni kaina na damu da canzawarshi,". Zuciyar Sir mubarak a hautsine Ya furta"idan kuwa har hakane Dr fawan baka kyauta mini ba! Meyasa tuntuni baka kira awaya ka sanar dani cewa baya zuwa aiki ba? Kusan kullum sai na ganshi ya shirya zai je asibiti, hakan na nufin ba aiki yake zuwaba wani wurin daban ya ke tafiya? Ya jefa mashi tambayar yana mai jin ɗaci acikin zuciyarshi.

"Ka yi hakuri daddy, Bana son in shiga tsakaninka da shi, sannan ni bansan baku da masaniya akan hakan ba"

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Sir mubarak ne ya furta hakan, zuciyarshi tayi matuƙar karaya da jin cewa jazz baya zuwa aiki, Ya fara zargin shi akan ƙarairakin da ya ke yi mashi, bai ta6a tunanin Jazz zai yi mashi haka ba, duk da irin ƙaunar da yake nuna mashi.

Idanuwan shi tuni sun kaɗa jawur, zuciyarshi ta motsa.

"Bana so Jazz ya san cewa nazo asibitin nan! Ko nayi magana dakai! Kaja baki kayi shiru," dr fawan ya amsa mashi da toh daddy, in sha Allah bazan faɗa mashi ba.

"Ka share hawayen ka," da sauri dr fawan ya zaro hanky ya soma goge fuskarshi.

"Dr fawan, Na yarda da jazz sai dai a yanzu na fara zargin shi, wallahi If I find out that he's doing something wrong, sai ya ɗanɗani kuɗar shi," rai a6ace ya furta maganar, ya ƙara da cewa "dr fawan nagoda da bayanan da ka bani, zaka iya komawa bakin aikin ka" jiki na rawa dr fawan ya fito daga cikin motar, Bayan yayi masu sallama Ya nufi cikin asibitin yana faman sauke ajiyar zuciya.

Shiru su ka yi babu wanda ya ƙara magana acikin motar, Lamarin ya ɗaurewa Sir mubarak Kai, Mamakin shi ƙaryar da jazz yai mashi na cewa Sun buɗe gidan kaji, da kuma zuwa aikin da yake yi ashe duk ƙarya ne.

Driver-operator, Ya fahimci halin da sir mubarak ya shiga na damuwa, cikin kwantar da murya yace"Sir, pls kada hakan ya dame ka, nasan ba daɗi mutumin daka yarda dashi ya sa6aka, sai dai fa har yanzu bamu da tabbacin abun da dr jazz ya ke yi, mu kyautata mashi zato, sannan shawarar da na ke so in baka yalla6ai, me zai hana mu fidda rana ɗaya, Mubi bayan shi ba tare da sanin shi ba, a lokacin da ya shirya zai tafi aiki,"

Ta cikin mirror din motar Yake duban sir mubarak, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon drivern yace "Ka kawo shawara mai kyau, tabbas inason sanin me jazz yake aikatawa, nagode da shawararka, zamu Iya tafiya"

Cikin girmamawa Ya amsa mashi da toh, sannan ya tada motar Ya fito da ita daga cikin harabar ajiye motocin, atsanake ya ke yin driving har suka haura saman titi, sir mubarak bai dai na cizon yatsanshi ba, saboda Ya damu da jazz, Ƙaunar da ya ke yi ma mahaifiyar shi ce ta shafe shi, ko ƴa'ƴan shi da ya haifa bai jin su kamar yadda yake jin jazz, hankalin shi ba zai ta6a kwanciya ba idan har bai gano abun da ya ke aikatawa ba, ya jima yana danne zuciyarshi akan ƙin amincewa da zargin yaron da ta ke yi, abun da ya jawo shi ga bincikar shi a yanzu ya fahimci aduk lokacin daya kama jazz yanayin waya da zarar Yaganshi yake rasa natsuwarshi, Jikinshi ya hau kerma, shiyasa ya fara suspecting dinsa.

❤ANEELERH❤

Tun kafin ta sallame sallar azahar wayar ta dake ajiye saman drawer take ta buga ringing, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa, sai da ta kammala sallar ta ɗaga hannu tayi addu'a ta shafa a fuska, kafin ta miƙe da sauri ta nufi drawer ta ɗauki wayar, murmushi ta saki ganin sunan surukar arziƙi ya bayyana akan screen din wayar, aranta ta ayyana halan baby junaid ne ya matsa a kirani awaya.

Bayan ta ɗaga kiran ta manna wayar a kunnanta, kafin ta furta sallama muryar junaid ta katse mata hanzarin ta.

"Mommy, baby junaid ne, ni ne na kira ki awayar granny," har sai da ta ji gabanta Ya ɗan faɗi, da mamaki tace"junaid da gaske kai ka kirani? Ina mommy adama? Ko dai itace ta baka wayar don ka yi mini magana"

muryarshi da shagwa6a yace"mommy ai bata nan, suna a falo, Ni kaɗai ne a ɗakin..." tun kan ya ƙarasa maganar tace"Junaid bana hana ka ɗaukarwa mutane waya ba? Faɗamin ya akai ka iya buɗe mata waya"?

"Mommy wasa nake maki, itane ta bani wayar, ta fita falo, ni kaɗai ne a ɗakin"

A faɗa ce tace"ƙarya ka ke yi mini junaid, ba ita bace ta baka wayar, kaine ka ɗauka ka kira ni, maza ka aje mata wayarta tun kan na 6ata maka rai," ta yi maganar tamkar ranta ya 6aci sai dai azahiri ta yarda bashi wayar akayi, kawai tana son ta hayaƙa shi ne.

Sautin kukan shi ne ya cika mata kunnuwanta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull