Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 45
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 45: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 45. "Hakane, amma kada ki damu, dama dalilin dayasa…
3,372 words
"Hakane, amma kada ki damu, dama dalilin dayasa na kira ki, game da zuwanmu gidane, Naga saƙon ankon da kika tura mini nagode, so abunda nikeson kiyi mini, Inaso ki fada min me baba yafi so"? murmushi saratu tasaki, Har cikin ranta taji dadin tambayar da tayi mata.
"Gift ne zaki shirya mashi na birthday dinshi"?
"Eh, na tambayi yayanki akan ya faɗa min me yafi so, kinsan halin shi, cewa yai shi baisani ba, Duk abunda yayi mini in siya mashi, Ni kuma nafi son abun zai burge shi sosai"
Dariya hajiya saratu tayi tana fadin" Gaskiya baba ni kaina bazan Iya cewa ga abunda yafi so ba, amma kwanakin baya naji yana magana da abokinshi akan yana son suturar su na al'adar inyamurai, tun lokacin dai banji sun ƙara magana ba, kuma ba akawo kayan ba, idan har kika shirya mashi su a matsayin gift dinsa, Nasan zai yi farin ciki sosai kuma zaiyi mamaki"
"Okey, Send me his measurements through WhatsApp, and please don't let anyone know. I want to surprise him." ta amsa mata da toh nima agaida mun da yayan nawa, ko na kira shi sai yaga dama yake ɗagawa, Ina nan ina jiran shi zamu haɗu ne" sautin dariyar hajiyarne ya cika kunnanta da ba'a tace"Ai kin fi kowa sanin yayan naki, sai dai ki ba wani labari" Sun jima suna waya kafin daga bisani sukayi sallama, Ajiyar zuciya ta sauke, tana ƙoƙarin zama gefen gadonta, Muryar Hajjaty ta katse mata hanzarinta, tayi mamakin jin sallamarta, don koda gigin wasa bata ta6a tako ƙafarta zuwa ɗakinta ba, Jim ta ɗanyi kafin ta furta"Wacece" ta fada tamkar bata gane me magana ba"
"Hajjaty ce" jinjina kai Hajiya saratu tayi tuni mood din fuskarta Ya canza, jim ta ɗanyi kafin tace"zaki Iya shigowa"
A hankali ta turo ƙofa ta shigo ɗakin, tun daga ƙasa hajiya saratu ta soma binta da wani matsiyacin kallo, pakistan ne ajikinta farare, ta ca6a uban ado, sai dai babu ƙamshin turaren nan, sai ka matsa kusa tukunna zaka Iya jin shi, hannunta biyu ruƙe da wooden tray, kayan abincine shaƙe asaman shi.
Lamarin ya ɗaurewa Hajiya saratu kai, tayi sototo tana kallon ta Muryarta na ɗan rawa ta furta"Ina wuni" yamutsa fuska tai"da ban wani ba kin ganni, shin wai ma me ya akawo ki room dina? Makuwa ki kayi ne"? Fuska adaure ta mata maganar. Duk tasha jinin jikinta, adabarbarce ta furfa"am..umm...dama abincine na kawo maki, Ni na girka shi da kaina abincin ƙasar mu ne..." daƙyar ta ƙare maganar a tsananin tsoroce.
Murmushin yaƙe hajiya saratu ta sakar mata"dama ke ce kike kawo min abinci? Ina masu aikin gidan ne? Ko sunyi yaji ne"
"Suna a kitchen suna aiki, kawai nayi ra'ayin in kawo maki ne da kaina, nasan zaki ji daɗin girkin tun da baki saba cin kalar shi ba" hankalin ba akwance ba take yin maganar, Ruƙe ha6a hajiya saratu tayi tana faman jinjina kai tace"To fa, sabon salo, tanan kika biyo? An gaya maki bani da hankali ne da zanci abincin da kika girka da hannun ki? Wato bokan ki ya haɗo ki da maganin barbaɗe kin zuba min aciki shine ki kawo mun don inci in mutu saboda kinsan abinci ne lago na ko"?
Hankalin Hajjaty ba ƙaramin tashi yai ba, cikin sanyin murya tace"Allah shine shaidata, tun da nake arayuwata ban ta6a takawa naje wurin boka ba, kuma ni banzo da niyar in cutar dake ba, abincine kawai na kawo maki, dan Allah ki kar6a ki ci......" Kafin ta ƙarasa maganar, Hajiya saratu ta dakata mata tsawar data firgitar da ita, jikinta ya kama kakarwa, nuna mata hanyar fita tayi daga ɗakin"Fuce min daga ɗaki tunkafin Inyi ƙwallo da tray din hannun ki, Ƴar rainin wayau, wallahi na fi ƙarfinki ba za ki ta6a cin galaba akaina ba, tunda can baki ta6a girka abinci kin kawo min don inci ba sai yau da kika shirya kashe Ni"?
Tuni idanuwan Hajjaty sun cicciko tab da ƙwalla, cikin shessheƙar kuka tace"meyasa kika tsaneni? Laifin me nayi maki? Duk cikin masu aikin gidan nan ni kaɗaice ke bakiso, idan laifi nayi maki ki faɗa min sai in gyara"
A tsawace Hajiya saratu tace"wai ke baki da hankali Ne? Kin manta wacece ni acikin gidan nan? Ko kin fara shaye shaye ne? Ni narasa gane wani tsautsayin ne ya kawo ki cikin ɗakina, I don't know where you get the nerve to talk to me face to face, ke ga ta6ararra dallah fuce ki ban wuri"
Juyawa Hajjaty tayi da sauri ta fuce daga ɗakin, Kamar zatayi tuntu6e, gutun tsoki Hajiya saratu taja tare da samun wuri ta zauna gefen gado, tana mai mamakin ƙarfin hali irin na Hajjaty.
_~*✊💋BossLadiesWriters💋✊*~_
~The return of Benazir~
سجن القدر❤🤍❤
Bayan fitar Hajjaty daga ɗakin Hajiya saratu, zafafan hawaye ne su ka wanke fuskarta, taji ɗacin maganganun da saratu ta faɗa mata, ita har ga Allah bada nufin komai taje kai mata abincin ba, dama Pravin ne ya bata shawarar ta rinƙa kyautata mata, wata'ƙil ta fara ƙaunarta, saboda ta faɗa mashi tana son su dinga shiri da matarshi.
Kafin tabar ƙofar ɗakin sai da ta ajiye tray din ƙasa, ta share ƙwallar fuskarta, tukunna ta ɗauka ta nufi ɗakin twins da niyar ta kai masu abincin wata'kil su ci.
A lokacin Zayn yana zaune saman gado Ya tasa laptop dinsa agaba Yana operating dinta, zaid kuma Yana a kwance gefenshi hannun shi ruƙe da Wayar shi Yana daddanna ta.
Sallamar hajjaty ce ta janyo hankulan su ga duban ƙofar ɗakin.
Zayn tamkar bai ji ba yai shiru yaƙi amsawa sai zaid Ne ya amsa mata tare da bata Iznin shigowa ciki, A hankali ta shigo da tray muryarta asanyaya tace"barkan ku da hutawa, fatan kun wuni lafiya" da fara'a akan fuskar zaid ya ce"lafiya lou auntyn mu, yau ke ce da kan ki ki ka zo kawo mana abinci"? Ya yi maganar tare da ajiye wayar shi ya sauko daga saman gadon Ya nufe ta, zayn ko kallo bata ishe shi ba, baiwar Allah taji daɗin sakar fuska da zaid ya yi har cikin ranta taji ta ƙara ƙaunar shi.
"Abincin ƙasar mu ne, ni na girka shi da kaina, na kawo maku ne don ku ɗanɗana" hannu biyu zaid yasa ya kar6i tray din Daga hannunta yana fadin"gaskiya kina ji da ƴa'ƴan nan naki, wallahi munji daɗi, kamar kinsan kuwa yunwa muke ji, Yanzu nake shirin kira akawo mana abinci mu ci"
Asaman table ya ɗaura tray din, sai faman sakin murmushi take Yi yayin da take kallon fuskar zaid, buɗe warmer ya fara yi, ƙamshin Abincin ya daki hancinsa, Jinjina kai yai tare da ɗago da ido Ya kalle ta"Aunty, Ya sunan wannan haɗin"?
"Chicken tikka masala" ta faɗa still da murmushi kan face dinta.
"Daga jin ƙamshin abincin zai yi daɗi, balle ma daya kasance hannu mai albarkane Ya girka sa" ya fada yana nade hannun rigarsa.
"Zaid! Kada ka kuskura ka ci abincin nan! Kai baka da hankaline"? Ras taji gabanta ya fadi jin abun da zayn yace.
Fuskar zaid a ɗaure ya dube shi"kaga bana son zancen banza, babu ruwanka dani, Kaja baki kayi shiru idan bazaka ci ba"
Ya ƙare maganar tare da maida dubansa ga hajjaty "mun gode Aunty, Idan nagama cin abincin zaki ji feed back dina" jiki asanyaye ta amsa mashi da toh, da sauri ta fuce daga ɗakin tana faman sauke ajiyar zuciya.
Ƙamshin Abincin da Zaid ke ci duk Ya cika mashi hanci da maƙoshi, dauriya ce kawai Yake yi, Yana danna laptop Haɗi da satar kallon Zaid, da gangan yake cuko spoon da abincin Yana turawa abaki, hada sambatun shi"wannan abinci kamar a aljanna aka dafa shi? Kai ka ji wani ɗanɗano mai daɗi, gaskiya duk wanda baici abincin nan ba an barshi a baya" Harara Zayn ya watsa mashi sam bai lura ba, saboda Ya bashi Baya.
Ajiye spoon din ya yi cikin abincin, ya tsiyaya lemu mai sanyi acikin glass, Ya ɗauka Yasha rabi, Ya ajiye.
"bari na ɗan shiga toilet" ya faɗa hadi da miƙewa da sauri Ya nufi toilet door ya shige, shigar shi ke da wuya Zayn ya janye laptop dinsa, cikin sanɗa Ya rarrafa saman mattress din zuwa gaban table din, Yana faman yamutsa fuska Ya ɗauki spoon Ya zura a plate din abincin aranshi yana fadin ba lallai ma abincin yai daɗi ba, mutuminka tun da yayi one spoon abaki, Tsabar daɗi kunnanshi har motsi suke yi, Yana ci yana satar kallon ƙofar toilet gudun kada Zaid Ya riske shi Yana cin abincin Hajjaty, a ƙarshe Ya ajiye spoon din Ya duma hannu ya ɗauko cinyar kaza Yadinga cizga Yana ci, Kusan Rabin abincin plate din ya cinye, ya ɗauki lemu Ya kur6a, Jin motsin za'a buɗe ƙofar toilet Yasa shi yin saurin sauke glass din lemun saman table, ko hannun shi bai goge ba, Da sauri Ya koma can saman gadon Ya jingina bayanshi jikin headboard ya ɗauki laptop dinsa Ya cigaba da operating dinta.
Fitowa zaid Yai daga toilet, Yana faman yarfa hannun shi, Satar kallon fuskar zayn yayi, mutumin Ya haɗe rai babu annuri, Sai dai Ya manta bai goge bakinshi ba, yayi dama dama da maiƙon abincin da ya ci.
Ƙayataccen murmushi zaid ya saki aranshi ya ayyana"babyn mommy ai nasan zaka aika, shiyasa na shiga toilet don na baka damar ka ci, ɗan rainin wayau anaso ana kaiwa kasuwa" Ya faɗa Yana zama bakin gadon, da zolaya yace"Zayn ya akai naga abincin dana rage an ci shi"?
Muryar zayn ba wasa yace"ka tambayi wanda kaba ajiya, Ni meye ruwana aciki"? Gumtse dariya Zaid yai"amma dai da kunya wallahi, Ni dai nasan babu 6era agidan nan" rai a6ace zayn yace"ban san iya shege zaid, Uban waye 6eran"?
"Ai ni ban kama suna ba, kawai nayi maganata ne" dogon tsoki Zayn yaja yana faman hura hanci, Aranshi ya ayyana Ina ma zaid Ya rage abincin da kuwa ya cinye shi duka, don ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba.
*SIR MUBARAK🤍*
A Hankali Yake tafiya Yana tunkarar ɗakin Dr. Jazz, Daga shi sai short A jikin shi da singlet, Tura ƙofar Yayi baiga kowa a ɗakin Ba, shiga Ciki Yai Yana bin ko'ina da Kallo zanin gadonshi a hargitse Takalman shi Yashe saman floor, tunani ya shiga yi aranshi ko ina ya shiga? Ko dai yana a toilet ne Ko ya shiga Garden, Yanke shawarar zuwa garden ɗin ya yi don Ya dubo shi, Ahanzar ce Ya juya da niyar ya fuce kwatsam Muryar Jazz ta katse mashi hanzarin shi.
"Oh tsayawa za ka yi Kana kallonta? Babu abun da zaka Iya yi mata? Sai kace ba ka san Hanyar da zaka kashe ta ba idan haukanta Ya motsa"! wani irin bugu zuciyar Sir Mubarak Tayi Jin Kalmar Kisa, A firgice ya juya baya Yana bin toilet door ɗin ɗakin da kallo, don Ya fahimci acikin toilet yake Yin wayar, Cikin tafiyar sanɗa Sir Mubarak Ya nufi ƙofar toilet Ɗin Ya kanga kunnan shi Yana sauraron shi.
"Ai ba dole Saina zo ba, Kaima zaka Iya sarrafata, Idan taƙiya Kawai ka bi Hanyar da nace maka, ka kashe ta kowa Ya huta," shiru Ya ɗanyi can kuma yaji yaci gaba da cewa"ba yadda za'ai inzo, Ina tsoron asirina Ya toni, hmm bakasan halin da nake aciki ba, ko jiya saida na kamo Hanya zanzo gidan, ganin ana bin motata yasa na karya kwana na nufi asibiti, saboda raina ya bani akwai wanda ke bin diddigina dole Inyi takatsantsan"
Hankalin Sir Mubarak Ba ƙaramin tashi yai ba, sai faman jinjina kanshi yake Yi, Bai ta6a tsammanin Jazz Yana da wayau ba sai Yau, Har yasan Ana bibiyarshi wato shine Ya canza Hanya, Hakan ya ƙara tabbatar mashi da zargin shi akanshi.
"What are you doing here, baby?"
Muryar Turai ce ta ratsa kunnanshi, Hatta dr Jazz dake a toilet, Sai da Ya ji sautin muryar mutun a ɗakin shi, a yayin da yake atsaye gaban sink, wandon crazy jeans ne da shirt a jikin shi, da sauri Yai rejecting call din Ya tura wayar cikin aljihun wandon shi, Jikinshi Ya hau Yin kerma, Tsananin fargabane Ya kama shi, A hankali Yake tafiya yana nufar ƙofar fita, Kafin fitowarshi da sauri Sir Mubarak Yai wuff Ya nufi Turai dake kallonshi da mamaki akan face dinta ganin Yadda ya ke yima Jazz la6e a ɗaki, Harta buɗe baki zata ƙara yin magana ya yi saurin sanya faffaɗan tafin hannunsa Ya toshe mata bakinta, tare da janta zuwa wajen ɗakin.
Lokacin da Jazz ya fito daga toilet din zufa na bin fuskarshi, ya dubi ko'ina baiga mutun ba, Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, har wajen ɗakin Ya leƙa bai ga kowa ba, Hakan yasa shi kokwanton wata'ƙil Kunnuwanshi ne suka jiyo mashi ba dai dai ba, hankalinshi ya kwanta, komawa ya yi cikin ɗakin Ya kwanta saman gadonshi, yayin da idanuwanshi ke fuskantar ceilling, ga dukkan alamu wani abu yake tunanowa wanda yasa shi fitar da ƙwalla a idon shi.
A bedroom Sir mubarak Ya shigar da turai suna tsaye suna kallon juna, kallon tuhuma take bin shi da shi.
"Nayi mamakin ganinka a ɗakin Jazz kana yi mashi la6e, meyasa"?
Fuskarshi a murtuke babu annuri yace"laifi ne don uba ya shiga ɗakin ɗanshi"? Aruɗe tace"ba laifi bane, amma meyasa kake yi mashi la6e"? Shiru ya yi yana duban fuskarta, A yadda suke atsaye suna fuskantar juna, Ko kafaɗarshi bata kai ba, saboda ƙarantarta, doguwar rigace a jikinta ta shan iska, ta tufke blonde hair dinta da ribbom.
"Ka tsare ni da ido kana kallona, Baka bani amsar Tambayata ba"! a ƙagare ta faɗa, Ya rasa ya zaiyi ya kawar da hankalinta daga tambayar da take yi masa.
Dubara ce ta faɗo masa, da sauri Ya sanya Hannu biyu ya ruƙe waist dinta, sama ya ɗaga ta kamar ɗiyar roba Ya kwantar da ita saman gadon shi Rumfa ya yi mata da faffaɗan kirjin shi, tuni tasha jinin jikinta.
"Kin tsareni da tambaya ke ga mai ɗa ko? Ni da ke waye yafi wani iko da shi? Yawu ta haɗiya muryarta na ɗan rawa ta furta"kai"
"Kinsan da hakan shine kike yi min tambayoyi kamar ƴar jarida"? Shiru tayi mashi tana faman zazzare green eyes dinta. "Jibarki ƴar mitsila dake kamar in matseki nake ji" dariya ce ta kubce mata, natsuwa yai yana kallon fararen haƙoranta.
"Yanzu dai faɗamin me kike shiryawa a birthday din Baba? Ba za kiyi kitso da ƙunshi ba"?
"Idan zaka kai ni inda za'ai min kitson da ƙunshin inaso, sai dai anko din da zasu sanya nasan hajiya saratu bazata barni in shiga cikinsu ba ko da na siya" a marairaice ta ƙare mashi maganar.
Jan hancin ta ya yi da hannun shi"Ina ruwanki da ita? Ai ba dole sai kin shiga cikinsu ba, babban tarone fa za'ayi akwai manyan baƙi da zasu zo, kema zaki samu ƙawaye acikin su"
Da shagwa6e ta furta"baby ba zaka gane ba, hajiya saratu bata son ganina, ita fa haryan zu kallon ƴar aiki take Yi mini, hada faɗa min wai ba ata6a canzawa tuwo suna, ni dai inajin fargabar ta disgani acikin su, ƙwara Inyi zamana acikin gida zai fiye min kwanciyar hankali" daƙyar ta ƙare maganar ganin yadda ya tsare ta da ido, kallon so da ƙauna ya ke yi mata.
"Meyasa kike kira na baby? Ko kunya bakya ji? Nayi maki kama da ƙaramin Yaro ne?" fuskar shi a ɗaure yai mata maganar. Kashe mashi ido ɗaya tayi"I call you baby because you're like a baby to me, and I still take care of you kuma ina feeding dinka" ɗan zaro mata ido ya yi da sauri ta rufe baki tana faman zazzare mashi ido.
Da zolaya ya furta"raini ya fara shiga tsakanina dake, saboda ina tu6e kaya agabanki ko"? Runtse mashi ido tayi tana faman tiƙar dariya.
Jinjina kanshi yai"ki saurare dakyau, daga yanzu idan saratu ta faɗa maki magana ki dinga mayar mata da martani, ki daina nuna kina jin tsoronta shiyasa ta rainaki, Kina jina ko"? Tana faman zumbura mashi pink lips dinta tace"ni bazan Iyaba, saboda ta girmeni ko a shekaru kuma ƙanwarka ce,"
"Umarni nake baki ba shawara ba, kada na kuskura na ƙara ganin kin dawo gidan nan kinayi min jan ido akan saratu tayi maki wani abu, idan ba haka ba zaki kar6i horo mai tsanani daga gareni," muryar shi a kausace yake yi mata maganar Kama kunnanta ya yi da yatsan hannun shi"Idan kunne Ya tsira"? Da sauri ta ƙarasa mashi karin maganar"Jiki Ya tsira My baby" murmushi yasaki tare da manna mata kiss saman soft lips dinta.
*GIDAN ƊAN IYA*
Zahra ce zaune saman prayer mat, ta zumbula dogon Hijabi, fuskarta sharkaf da hawaye, tun da ta kammala sallar Magrib bata motsa ba, hannunta ruƙe da cazba sai faman janta take Yi, damuwar duniya ta isheta, tun ɗazu data farka daga bacci ta kasa Yin wanka ko abinci bata ci ba, babu kuma wanda yai tunanin ya leƙo ta, tayi trying kiran layin mahboob yaƙi picking call din, har yanzu bai leƙo cikin gidan ba, ga lokaci yana ta tafiya gani take yi kamar ana ƙara gudun agogon ɗakinta, hannayenta biyu ta ɗaga sama tana jera addu'o'i akan Allah Ya kawo mata mafita.
Muryar Aneelerh ce ta ratsa kunnanta"Yar uwata rabin raina, tun safe baki ci komai ba, Ga abinci na kawo maki" Shafa tafin hannunta tayi saman fuskarta, Rai amatuƙar 6ace ta yunƙura ta mike haɗi da fuskantar Aneelerh, dake tunkarota, hannunta ruƙe da madaidaicin tray, mai ɗauke da plate din shinkara da ƙaramar warmer ta miya, tare da lemu mai sanyi.
Kafin ta ƙaraso zahra ta dakatar da ita ta hanyar yi mata magana"Aunty Aneeleeh idan kin kawo abincin nan domin in ci ne to ki maida shi kitchen! Bana buƙata" a faɗace ta furta.
"Haba zahra, kashe kanki ki ke so Ki yi ne? Tun safe baki ci komai ba, Ni kaɗai na damu dake, dan Allah ki kar6a ki ci"
Harara zahra ta wurga mata cikin 6acin rai tace"Ai ni kingama zubda girmanki a idona, tun da har kika iya bani shawarar In amince wurin aikata sa6on Allah, Kin ban mamaki aunty aneelerh, bansan haka kike ba" tana magana tana jan majina.
Jinjina kai Aneelerh tayi"Laifina ne zahra, Ni da na damu dake shiyasa kike gaya min magana son ranki, daga taimako? Daga yau ka da ki kuma tsammanin zan ƙara baki shawara idan har baki kar6i abincin nan ba" wani ɗan iskan kallo Zahra ta watsa mata, har saida ta dasa aya amaganarta tukunna zahra ta ruƙe qugu kamar ana tunzurata tace"Idan har kin damu dani, meyasa ba zaki taimaka mu nemi mafita atare? Saima ƙoƙarin da ki ka yi don ganin kin sanya ni a gur6atacciyar hanyar da zan lalata duniyata da lahirata, ke ba mai ƙaunata bace aunty Aneeleeh, bana sonki kuma bana son ganin ki!, Yakamata ki nisanta kan ki dani, Idan ba haka ba zan yi maki rashin mutuncin da baki ta6a tsammani ba!!"
A kausashe Ta furta maganar tana nuna Aneelerh da cazbahar hannunta kamar zata rufe ta da bugu.
Gyaɗa kai Aneelerh tayi tama rasa bakin magana, kalaman zahra sun bata mamaki, bata ta6a tunanin zahra zata Ya furta mata su ba.
Juyawa ta yi da sauri ta nufi ƙofar fita, adai dai lokacin Mahboob yana ƙoƙarin shigowa ɗakin suka ci karo da Aneelerh, har gaishe ta ya yi amma ko kallon shi ba ta yi ba, hakan yasa shi tsammanin ko wani abu Ya faru ne.
Zahra na jin sallamar shi da sauri ta sanya hannu biyu ta share hawayen dake akan fuskarta, komawa tayi daga gefen gadonta ta zauna tana dubanshi.
Riga da wandon shadda ne ajikinshi, hannun shi ruƙe da key din motar shi.
"Zahra Lafiya ki ke yi mini kiran talauci? Ina akan hanyar dawowa gida naga miss calls dinki, Allah dai yasa lafiya"
Cikin sanyin murya tace da shi"ka zauna mahboob mu yi magana" zama yai da ɗan mamaki akan face dinsa yace"meyasa ki kuka? Naga idanuwanki sun kumbura wanene Ya ta6a ki? Ko ke da aunty Aneelerh ne"?
A hanzarce ta girgiza mashi kai tana faɗin"bakomai, banajin daɗi ne kaina ke ciwo"
"Kin sha magani" cikin kulawa yake yi mata magana, ɗaga mashi kai tayi alamar eh ta ƙara da cewa"Aunty Aneelerh ce ta bani maganin"