Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 46
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 46: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 46. Gyaɗa kai yai"okey, Allah ya sawaƙe sister yanzu…
3,364 words
Gyaɗa kai yai"okey, Allah ya sawaƙe sister yanzu dai faɗamin me kike buƙata ne Kin dai san ban da ko sisi"
Murmushin takaici tasa kar mashi jin abinda yace
"Mahboob ba kuɗi zan roƙe ka ba, taimako nakeso kayi min dan Allah, bana son ka tambayeni dalili kawai ka yi abun da nace maka, kuma bana son kowa Ya sani daga ni sai kai"
"Kada ki damu, Ina jin ki" a ƙagare Ya furta mata hakan "Inason zan siyar da motata ne da wayata, saboda ina buƙatar kuɗi ko akwai wanda ka sani da zai Iya siya a yau din nan'? Ta jefa mashi tambayar tana duban fuskarshi.
Mamakine ƙarara akan fuskarshi, Har saida Yaɗan saki baki da ido Yana dubanta Kafin yace"ke kuwa me zai ja ki siyar da motarki da wayarki? Runtse ido ta dan yi hawaye na ƙoƙarin cin ƙarfinta tace dashi"Mahboob banason tambaya! Kawai ka taimaka mun in zaka Iya in kuma ba za ka yi ba to ka tashi ka tafi kaban wuri"
"Shikenan Naji, nayi shirun, amma dai kinsan kowa zai saye su sai kin faɗi ko? Ba lallai asamu wanda zai siya da mutunci ba"
Ɗaga mashi kai tayi"Ni wannan ba damuwata bace, indai kuɗin zasu kai 4m Ya wadatar"
"Okey, amma ni shawarar da zan baki mai zai hana ki bada motar da wayar taki jingina? Idan kika samu halin biyan kuɗin sai ki Kar6o Kayan ki, zahra kinsan babu mai siya maki su idan kika rasa na hannunki kuma ni bazan juri ara maki motata ba" Ya faɗa Yana yamutsa fuskarsa, Harara ta watsa mashi da rinannun idanuwanta"kai fa banza ne wlh, Ni ina ruwana da motarka? Koda zan rasa abun hawa mahboob bazan ta6a aron kayanka ba"
Murmushi ya ɗan saki tare da miƙewa yace"to Aunty zahra, Ni zan tafi, in sha Allah zan samu wanda zai siya, amma ki sani zamu kasa kuɗin gida uku, Ki kwashi kaso biyu ni kuma ɗaya...."
Tunkan ya ƙare maganar zahra ta rarumi pillow aguje tabi shi da gudu ya fuce daga ɗakin Yana tiƙar dariya muryarta ashaƙe take fadin"wallahi mahboob ka fita idona, Ni ba tsarar wasanka bace, kuɗin nan da gumina na tarasu bada gumin wani ba' rai a6ace take yin maganar, bayan ta gama zazzaga mashi masifar ta juya ta koma cikin ɗakinta tana faman tallabe cikinta dake yi mata kukan yunwa.
Safa da marwa ta soma Yi A tsakar dakin duk ta ƙagara da jiran kiran mahboob, Fatanta Allah yasa asamu wanda zai sayi motar.
Wuraren ƙarfe 8 na dare, Kiran mahboob Ya shigo wayarta jiki na rawa ta ɗaga ta kara a kunnanta, Anan yake sanar da ita cewa abokinsa Ya ce yana so harma sunyi cinikin motar akan miliyan uku da rabi zai siyeta, ita kuma wayar zai siyeta dubu ɗari biyar idan ta bari ahakan zuwa gobe da safe zai kai mashi Motar da wayar, daga nan zai tura mashi kuɗin, tsabar farin Ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha, duk da tayi asara ba kaɗan, saboda an karya kuɗin motar da wayar, amma hakan bai dameta, burinta ta sauke nauyin dake akanta, Bayan sun gama wayar, ta zuƙunna takai goshi ƙasa tana godiya da Allah, daga bisani ta mike tana tiƙar rawa, da gudu ta fito daga ɗaki ta nufi kitchen, ta ciko plate da abinci, ta buɗe frigde ta dauko lemu mai sanyi kafin ta dawo ɗakinta, ita kadai ta zauna tsakiyar gado tana ci tana sakin murmushi, baƙin cikinta ɗaya ta rasa damar da take da ita na zuwa Obie estate, tunawa da wannan yasata rushewa da kuka ga abinci cike abakinta.
*JOS CITY*
Dare ya tsala sosai, Gari yayi duhu, a lokacin da kowani mahaluƙi yake a makwancinsa domin runtsawa, baka jin sautin komai saina kukan tsuntsaye dana karnukan Layi dake Hargowa.
A hankali take tafiya Hannunta ruƙe da trolley, doguwa ce a halitta, siririya bata da ƙiba sai dai tana da hips, doguwar jallabiyace a jikinta, ta sanya niƙab ta rufe fuskarta, abun da zai baka mamaki ita kaɗai take Bin santar babu alamun tsoro atattare da ita, da taimakon street light ta ke samun damar ganin ko'ina, Har Allah Ya nuna mata gidan da take nema, Katafaren Villa ne Mai gingirimeman gate.
da sassarfa ta nufi gate din, tana zuwa gabanshi, Takai hannu ta soma ƙwanƙwasa ƙofar, tun tana yi a hankali har takai ga tsunto dutse ta cigaba da bugun ƙofar da shi kamar zata 6alle gate din'
Security officers din dake tsaron gidan guda Biyu ne cikin kakinsu suka fito daga ɗakunansu jiki na rawa suka ƙara so gaban gate din, da alamun mamaki akan fuskokinsu suka haɗa bakin wurin furta Wanene ke buga mana ƙofa a dai dai irin wannan lokacin"! Da fargaba suka furta maganar.
Cikin shessheƙar kuka da muryarta mai tsiwa ta furta"BENAZIR CE"
kallon Juna Officers din suka Yi, ɗaya yace"Wanene kuma haka? Mutun ko aljan? Wa ki ka zo nema agidan ko dai kin yi 6atan Hanya ne"
Tamkar zata fashe da kuka tace"dan Allah ku buɗe mun gate in shigo, ni ce benazir ɗiyar Alhaji ubaid"!
Ba ƙaramin ɗaure masu kai lamarin yayi ba, kasancewar su tsoffin masu gadin gidan, sunsan wacece benazir Yarinyar uban gidansu data 6ace tsawon shekara goma sha shidda, kokwanto suka soma Yi anya kuwa itace?
Officer mai gemu yace"kai, Da wuya ya zama gaskiya yarinyar da babu tabbacin tana araye kota mutu"!
Ɗayan kuma yace"Ai ni banma yarda ba gaskiya, Kusan shekara goma sha shidda da 6atanta sai Yau ƙarfe sha biyu na dare zata dawo! anya kuwa ba tarko bane aka ɗana mana"?
Mai gemu yace"amma kuma muryarta sak kalarta hajiya layla, Har tsiwar iri ɗaya da tayi maganar"
Jin sunƙi buɗe mata kofa yasa ta rushe masu da kuka mai sautin gaske a faɗa ce ta ke fadin"wai baza ku buɗe mun gate ba, na gaji da tsayuwa wallahi idan baku buɗe ba na shigo cikin gidan saina Sa an kore ku"
Yawu suka haɗiya atare mai gemu yace"Ke baiwar Allah, ba yadda za'ai mu buɗe maki gate ba tare da mun sanar da masu gidan ba, dan haka ki ƙara haƙuri mu faɗa masu"
Kafin suyi yunƙurin zuwa cikin gidan su sanar masu, ba zato ba tsammani suka ji ta bangaje ƙofar jikin gate din dake a kulle, nan take ƙofar ta buɗe, hankalin su ba ƙaramin tashi Yai ba, A firgice suke dubanta yayin da take shigowa ciki da akwatinta, Ko kallo basu isheta ba, da sauri ta nufi cikin gidan.
Kasa motsi suka yi Kamar an dasa masu Aya, tuni zufa ta wanke fuskokinsu, Mamakin su Taya akai ta Iya bugun ƙofa da ƙarfi Har jamlock mai ƙarko Ya zame kanshi! Tabbas suna hasashen ba mutun bace aljana ce, tuni suka sha jinin jikinsu.
Tana tafiya tana bin ko'ina na gidan da kallo, abubuwa da dama sun canza mata ba kamar yadda ta tafi tabarshi ba.
Adai dai lokacin Zainab mai aikin gidan tana a palour hannunta ruƙe da floor wiper tana goge tiles, ta saba ba tun Yau idan bata son aiki Yayi mata yawa takan fito har tsakar dare Tana aikace aikacen ta don ta rage wasu ayyukan na safe duk idan taji ƙarfi a jikinta.
Tamkar da rana saboda hasken Ƙaton kwan dake a falon Ya gauraye ko'ina, Hankalinta kwance ta duƙufa tana gudanar da aikinta ba zato ba tsammani taji an banko ƙofar falon.
A firgice Zainab ta ɗago tana kallon matar da ta fado cikin falon afujajen, tsabar firgitar da ta yi har batasan sa'adda ta jefar da wiper din hannun ta ba, tun daga ƙasa har sama take kallonta, Hankalin ta ba ƙaramin tashi yai ba, tsananin tsoro Ya kamata, Jikinta ya hau yin kerma, Muryarta na rawa ta furta"baiwar Allah wacece ke? taya ya akai kika shigo gidan nan? Ƙarfe sha biyu na dare"? Aruɗe take jefa mata tambayar.
Shessheƙar Kukan matar ne Ya ƙara firgitar da ita, ta soma Ja da baya tana ƙoƙarin guduwa cikin gidan don ta faɗo ma Hajiya layla abun da ke faruwa sai dai kafin Ta juya muryar Matar ya ratsa kunnanta cikin harshen larabcin take faɗin.
"AUNTY ZAINAB NI CE BENAZIR!! INA ABBANA! INA UMMI NA! INA MIJINA DA ƳA TA!!! A jere ta jefa mata tambayoyin.
Har abada ba zata ta6a mantawa da muryar nan ba, koda kuwa amafarkine Ta jita tabbas zata shaida mamallakiyarta.
A hargitse Ta juya Tana dubanta, A hankali benazir ta ɗaura ziraran yatsun hannun ta farare tas ta ruƙo ƙasan niƙab ɗin fuskarta ta ɗage shi sama" tsabar kiɗima da ganin fuskar da tayi kimanin shekaru sha shidda ba ta yi tozali da ita bane yasa Jikinta ya hau yin kerma, tsantsar mamaki da al'ajabi ne akan fuskarta, ta zazzare idonta akan kyakkyawar fuskar benazir, sam takasa yarda da abun da idanuwanta ke nuna mana gani take yi tamkar mafarki ne take Yi!!
Tayi wani irin haske Kamar ka ta6a jini ya ɗigo, Fuskarta sharkaf take da hawaye ta ko'ina, ga zufa dake tsastsafo mata sam babu kwanciyar hankali atattare da ita.
Tsantsar tashi hankaline Akan fuskar zainab, Muryarta adabarbarce ta furta"be..be..nazir! Dagaske ke ce ko dai idanuwana ne suke nuna min ba dai dai ba"?
Da ƙarfi ta furta"Ni ce Aunty zainab! Ki amsa min tambayoyin da nayi maki"!
Tana faɗin hakan Nan take Ta yanke jiki Ta faɗi ƙasa a sume, akwatin hannunta ya kife saman floor.
Juyawa Zainab tayi da gudun gaske ta nufi ɗakin hajiya layla, Hada yin tuntu6e tsabar sauri, tunkafin ta ƙarasa ta soma ƙwala mata kira na fitar hayyaci tamkar maƙoshin ta zai 6allo waje.
"Hajiya layla! hajiya layla"
Kaitsaye kiran ya daki dodon kunnuwan su daga ita har Alhaji ubaid dake kwance saman katafaren gadonsu, A firgice suka farka a lokaci ɗaya suka miƙe zaune suna ambaton Sunan zainab.
Doguwar jallabiya ce a jikin alhaji ubaid wuyan rigar ya karkace, Hajiya layla kuwa Rigar Bacci ce a jikinta, da sauri Alhaji ubaid ya kunna bedside lamp din ɗakin.
Sam babu kwanciyar hankali atattare da su, duk sun ƙura ido suna jiran ganin ta inda zainab zata 6ullo.
Kamar daga sama suka ji ta banko ƙofar ɗakin tana faman Yin haki. Da mamaki Akan fuskar Layla tace"Zainab baki da hankali ne? Ko kin makance ne? Taya zaki faɗo mana ɗaki a irin wannan lokacin ba tare da kin nemi iznin shigowa ciki ba"!
Kafin zainab ta bata amsa Alhaji ubaid Ya katse mata hanzarinta da cewa"Zainab Lafiya kike ƙwala mana kifa? Kowani abun ne Ya faru"?
Cikin rawar murya ta furta"dan Allah kuyi haƙuri ku yafe ni, bana acikin kwanciyar hankalina ne shiyasa na faɗo maku ɗaki ba sallama nasan bai dace ba" dogon tsoki Layla Taja"Ba dogon bayani na tambaye ki ba, Ki faɗi min uban mi Ya kawo ki ɗakin mu?
Bata kai ga ƙarasa maganar ba, Alhaji ubaid Yai saurin katse ta da cewa"Ya isa haka, Haba kin cikata da faɗa, Kin ƙi bari tayi mana bayani dangane da abunda ke faruwa" tsuke fuska Layla Tayi.
Cikin sanyin murya zainab tace"dama BENAZIR ce ta dawo!"
Kallon juna Alhaji ubaid da layla suka Yi lokaci ɗaya, kafin suka dawo da dubansu ga zainab, Har suna haɗa baki wurin tambayar wacece Benazir!! Tsabar ruɗanin da suka shiga Zainab tace"benazir ƙanwar dr shureim Ƴar wurinku itace ta dawo, Yanzu haka tana acikin palour ta yanke jiki ta faɗi a sume.
Girgiza kai layla tayi haɗi da cewa"baki da hankali zainab, dama na fara zargin kin fara shan ƙwaya, In ba haka ba, ta ya ya benazir da ta gudu da ƙafafuwanta zata dawo gida! bazai yiwu ba.
Alhaji ubaid Yace"ko dai mafarki ki ka yi ne zainab? Girgiza mashi kai tayi hada hawaye akan fuskarta tace"wallahi dagaske nake yi zaku Iya zuwa palourn ku duba benazir ce da kanta ta dawo"
Kusan atare suka sauko daga saman gadon, da sauri zainab ta basu hanya suka fuce har suna bange juna tsabar sauri.
Tunkafin su ƙarasa falon suka soma hango mutun kwance saman floor da baƙaƙen Kaya ga trolley dinta a gefe ɗaya, kasancewar ta yaye niqab din fuskarta hakan ya basu damar ganin fuskarta, wani irin mahaukacin bugu zuciyarsu tayi A matuƙar gigice suka furta sunanta"BENAZIR" adai dai lokacin gate security officers din gidan suka shigo falon da sallama sam babu kwanciyar hankali akan fuskokinsu ganin Yanayin mutanan gidan yasa suma suka ƙame suna faman zare ido.
Muryar Hajiya layla Na rawa ta furta"wallahi itace Benazir ɗina ce, Yarinya tace data 6ata, itace ta dawo da kanta" ta ƙare maganar jiki na 6ari ta nufi gaban Benazir dake kwance ta zube saman gwiwowinta tare da kai hannu ta ruƙo niƙab din fuskarta ta ƙarasa cire mata shi, Kowa dake a falon saida yai matuƙar Al'ajabin ganin Benazir, yalwataccen gashin kanta har gadon bayanta Ya nannaɗe kamar taliyar indomie, babu alamun wahala atare da ita, sai ma hutun dake kwance saman farar fatarta, wani iko na Allah, gaba ɗaya Jikinta Ya jiƙe da ruwan zufar dake tsastsafo mata, hatta baƙar jallabiyar jikinta ta manne ma fatarta saboda zufar data wanketa, ga wata zufar dake kurɗaɗowa ta cikin sumar kanta ta jiƙe sharkaf duk da sanyin A.c din falon.
Rushewa da kuka Hajiya layla tayi haɗi da ɗaura Hannayenta biyu saman kanta tana fadin"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Dan Allah kuyi wani abu akai mana kun tsaya kuna kallonta, sai kace baku gane ta ba, ɗiyata ce benazir Allah Ya dawo mun da ita da ranta" Sautin kukan ta ya cika ɗakin, Zainab ma tuni ta fashe da kukan farin ciki, security officers dake tsaye Jikinsu ya yi mugun yin sanyi, da farko sunyi tsammanin ba mutun bace amma daga bisani Bayan ta shigo cikin gidan suka dudduba ƙofar donsu tabbatar mutun ce ba aljana ba, ashe Jamlock ɗin ƙofar gate dinne basu kulle shi ba sun manta, shiyasa har ta samu damar sanya ƙarfi ta bangaje ƙofar ta shigo ciki.
Mamaki da al'jabi sun Hana Alhaji ubaid motsawa Ya kafe fuskar Ƴar tashi da ido Yana kallonta, ruwan hawaye ne kwance acikin idanuwanshi haƙiƙa ya yi farin ciki mara misaltuwa kusan shekara goma sha shidda Yau rana ɗaya Allah Ya kaɗo masu da hankalinta ta dawo wurinsu, Allah ne kaɗai Yasan uwa duniyar data shiga.
Cikin shessheƙar kuka zainab tace"yakamata muyi wani abu akai, Benazir tana buƙatar taimakon gaggawa, ga dukkan alamu wani abunne Ya faru da ita wanda Ya haifar mata da fitar da gumi a jikinta"
Da sauri Alhaji Ubaid Ya sanya Hannayenshi biyu, Ya cuccu6eta Ya juya ya nufi sofa mai mazaunin mutun uku Ya kwantar da ita, kallon zainab yai"je ki ɗauko min wayata a ɗaki" ta amsa mashi da toh, da ɗan gudunta ta nufi bedroom dinsu.
Jiki amace layla ta miƙe ta koma saman sofa hand din da benazir ke akwance ta zauna tana duban fuskar ƴartata Kamar Ta haɗiyeta haka take ji.
"Alhaji kun tabbata benazir ɗinmu ce ta dawo"! Mai gemu ne Yai mashi Maganar, Jinjina masu kai Yai"babu shakka itace Allah ya dawo mana da ita" Ajiyar zuciya kowan nan su Ya sauke tsantsar farin ciki Ne Ya kamasu.
"Muna tayaku murna, ita kuma muna yi mata fatan Allah Ya bata lafiya, Ubangiji Allah yasa ƙarshen wahalarta kenan, sannan Alhaji Muna baku shawarar a kira malamin da zai dubata don yanayinta dana gani a matsayina na wanda yake da sani a 6angaren sihiri, Yarinyar ka ba likita take buƙata ba, Malami take buƙata saboda duk wasu alamomi na jikinta sun nuna kamar sihirine daya daɗe a jikinta ya kwance !!! A firgice Alhaji Ubaid Da Hajiya layla suka ɗago suna duban mai gemu da yayi maganar, jinjina masu kai yayi"ba yau na fara ganin irin hakan ba, ina da tabbacin Yarinyar nan kurciya aka yi mata, amma idan kunaso ku gasgata zance na ku kira babban malamin da zai dubata" sam sun kasa magana sai bin shi da kallo da su ke Yi.
Daƙyar Hajiya layla Ta iya buɗe bakinta la66anta na kerma tace"amma benazir da ƙafafuwanta ta gudu tabar gidan tajudden Bayan ta haihu tabar mashi jinjira a cikin kwamin wanka, tayaya hakan zai yiwu? Wanene zai yi mana hakan?
Girgiza kai mai gemu yai"haka zakuyi tunani saboda bakusan dalilin tafiyarta ba, amma abun duba anan tayaya Uwa zata gudu tabar jinjirin ɗan da ta haifa ta hanyar raya sunna!! Duk irin soyayyar dake tsakanin uwa da ɗanta? Sannan idan har dagaske benazir ta gudu don son ranta tsawon shekara goma sha ɗaya meyasa zata dawo da ƙafafuwanta ba'a cikin Hayyacin ta? Ga zufa duk ta wanke suturar jikinta, Nidai shawarar da zan baku shine a tuntu6i malamin da zai dubata"
Jinjina kai Alhaji ubaid ya yi shi kanshi jikin shi ya yi sanyi da zancen Mai gemu, saboda akwai ƙamshin gaskiya a kalamanshi.
Shigowa falon Zainab tayi hannunta ruke da wayar Alhaji ubaid Ta miƙa mashi, Yasa hannu Ya kar6a.
"Dare Yayi yanzu, kada mu katse ma wani baccin shi, shawarar da zan bada shine a ɗebo ruwa a yayyafa mata in sha Allah zata farka, zuwa asuba sai a kira malamin da zai dubata" mai gemu ne Yayi maganar, muryar Alhaji ubaid a sanyaye yace"Inaso zan kira Dr shureim ne, saboda a irin wannan lokacin baya runtsawa Idonshi biyu Yana tashi domin Yin nafilfilin dare" ya ambaci hakan tare da Danna wayar hannunshi ya buga ma dr shureim Kira ta soma ringing.
Kallon zainab Hajiya layla tayi idanuwanta sun kaɗa jawur tace"ɗauko mun ruwa a fridge " amsa mata zainab tayi da toh, da sauri ta nufi hanyar kitchen.
Dafe kai Hajiya layla tayi da hannu ɗaya, Sumar kanta duk ta tarwatse saman bayanta, ta manta da yanayin jikinta, don ma babu wanda ke acikin natsuwar shi, hankalinsu na akan Benazir.
Bayan zainab ta dawo, hannunta ruƙe da bottle water me sanyi ta buɗe murfin ta miƙa ma Hajiya layla, Yayyafa mata tayi saman fuskarta, nan take ta sauke nannauyar ajiyar zuciyata muryarta da tsiwa take fadin"ina mahaifiyata Ina mahaifina! Ina mijina da ƴata Ina yayana shureim, suna ina ! Na shiga uku na bani na lalace Na rasa kowa nawa, wayyo Allahna na shiga Uku wallahi gida zan koma Nabar Yarinyata cikin Jini, tajuddeen kai na bama amanar ɗiyata nasan bazaka bari rayuwarta ta wulaƙanta ba. Dan Allah ka bani Ƴata ita nake son gani'
tunda ta fara sambatun nan zainab da hajiya layla suka fashe da kuka suna kallonta, ta runtse idanuwanta sai faman ciccije le6enta take Yi da haƙoranta tuni suka soma faffashewa, jini Ya soma tsastsafowa, dunƙule hannu tayi tana buge buge, da sauri zainab da hajiya layla suke rurruƙeta sosai suna ambaton sunanta
*DR.SHUREIM❤*
Lokacin da Kiran Alhaji Ubaid ya shigo wayarshi, Yana a zaune saman darduma cikin shiga ta larabawa, Yayi nisa acikin karatun qur'nin dayake yi Kiran Ya daki dodon kunnanshi, Hakanan yaji gabanshi Na faduwa, aranshi ya ayyana kowa ne ne ke kiranshi a tsakar daren na! ya salam, Sai da yakai ƙarshen Aya tukunna Ya zabura Ya miƙe Ya nufi wayar dake ajiye saman side drawer ya ɗauke ta yana duban Screen din, Hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba ganin sunan Abie dinsa Ya bayyana, kafin Ya ɗaga kiran saida Ya fara kallon agogon bango ƙarfe ɗaya da rabi na dare, picking call ɗin ya yi muryarshi na rawa ya furta"Assalamu alaikum Daddy!!!" muryar Alhaji ubaid Babu natsuwa Ya furta mashi"shureim Ƴar uwarka ta dawo gida daren nan cikin mawuyacin hali"! Da alamun ruɗu akan fuskar dr shureim Yace"bangane wa kake nufi ba daddy" muryar shi da sauti mai ƙarfi Yace"BENAZIR!! nake nufi ta dawo gida cikin daren Nan, Gatanan kwance tana buge buge zufa duk ta wanke jikinta, mun rasa ya zamuyi da ita"
Zafafan Hawaye ne suka wanke fuskar dr. shureim, tsabar farin ciki baisan sa'adda Ya zube saman gwiwowinsa Yayi sujjada, sosai ya fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya, Alhaji Ubaid Yana jiyo sautin kukan dr shureim Kamar ƙaramin Yaro.
"Shureim ba kuka yakamata kayi ba, dan Allah ka natsu muyi magana, hankalin mu ba'a kwance Yake ba, Ƴar uwarka bata acikin Hayyacinta, Mai gemu ya tabbatar min da cewa Kurciya ne akayi mata, saboda alamomin dake a jikinta na fitar sihirine"
Jin wannan maganar ta Mahaifin nasa ne yasa shi saurin ɗagowa daga sujjadar, arab turban dinsa tuni ya warware Yabar saman kanshi.