Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 47

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 47

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 47: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 47. Manna wayar yai saman kunnanshi da alamun kiɗima…

3,106 words

Manna wayar yai saman kunnanshi da alamun kiɗima ya furta"Sihiri kuma!! Alhaji ubaid Yace"to haka dai mai gemu Ya faɗa mana, baka ga yadda jikinta ke fitar da gumi ba kamar wadda aka tsamo daga kogon ruwa, bari na kanga maka wayar kaji haukan da take Yi mana" on the other hand Alhaji Ubaid Ya matsa gaban benazir Ya saita wayar abakinta.

Muryarya ce ta ratsa kunnuwan dr shureim"Ni ku sake ni, Ku ƙyaleni ku daina ruƙe mun hannuna, wurin Mijina zanje nabar mashi ƴata a gida ita nake son gani, wallahi ku rabu dani dole in tafi" Jikin taƙaura yai la'asar, a sukwane Dr shureim ya miƙe tsaye da waya kare a kunnanshi.

Muryarshi na rawa Ya furta"daddy najima ina zargin hakan, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wallahi da ina da halin da zan Iya zuwa Jos acikin daren nan da babu abun da zai hana inzo don in cece rayuwar ƴar uwata, amma duk da haka daga nan ɗin ma zan Iya taimakawa, Daddy Idan Aunty zainab tana akusa ka miƙa mata wayar!"

Jikin Alhaji ubaid na 6ari ya miƙa ma zainab Wayar yace ta kar6a dr shureim ne ke son Yin magana da ita, da sauri ta sanya hannu ta kar6i wayar tana fadin"dr shureim kaga wani ikon Allah ko? Tsawon shekara goma sha shidda Yau benazir ta dawo gida, wlh tsabar farin ciki bansan inda zan tsoma kaina ba, sai dai na damu da yanayin da take aciki"

Numfasawa dr shureim Yai tare da cewa a tsanake"Aunty zainab, yanzu bani da natsuwa, zuwa gobe da sassafe zan shigo Jos din, amma kafin nan ki duba ɗakina a cikin drawer chest na bedside drawer gida na uku, akwai robobin ruwan zam zam da wani malamin mu na ƙasar egyp ya bamu su don mu dinga yin amfani da su muna taimakon mutanan da suke fama da matsalar sihiri, ki ɗauki ɗaya Kije ki buɗe bakin benazir Ki matsa mata shi ki tabbar ta shanye shi duka in sha Allah, sauran sihirin dake ajikinta zai barta ne kafin goben mu ƙaraso" amsa mashi tayi da toh, yace ta miƙa ma mahaifiyarshi wayar da sauri ta miƙa mata, yatsun hannun layla na kerma ta kar6i wayar.

Cikin shessheƙar kuka tace"shureim benazir ɗinmu ta dawo gida, sai dai kamar bata acikin hayyacinta, duk ta faffasa la66anta da haƙoranta.

Cikin kwantar da murya dr shureim Yace"Ki sanya handsfree Inason daddy yaji maganar da zanyi" da sauri layla ta mayar da wayar handsfree, zainab tuni ta shige ɗakin dr shureim neman ruwan zam zam.

"Mommy daddy, dan Allah ku kwantar da hankalinku, wallahi Allah ne ya taimaki rayuwar baiwar Allah nan Ya Karya sihirin dake a jikinta, kuma ya dawo mana da ita da ranta, wani mugun aka samu mara imani mai zuciya irin ta kafuran farko Yai silar rabata da danginta tsawon shekara goma sha shidda, wallahi tun lokacin dana ji yanayin da benazir ta gudu tabar gida raina ya bani cewar wani abunne Ya faru da ita, haƙiƙa munyi sakaci wurin kula da ita, gaba ɗaya mun ɗaura mata lafin guduwarta babu wanda ya ta6a yi mata kyakkyawan zato akan meyasa ta gudu tabar jinjira acikin kwamin wanka, Kuma bata nemi kowa ba ta kama hanya tayi tafiyarta, anyi amfani da halayanta na rashin jin magana da rashin Kunya da take dashi anyi mata abun da yasa tabar mu saboda ansan kowa zai yi tsammanin ita ta gudu dakanta tunda dama bata jin magana, da ya ke Allah ba azzulumin bawansa bane sai gashi ya dawo mana da ita a lokacin da bamuyi tsammanin ganin ta ba" gaba ɗaya sun natsu suna sauraron muryar dr.shureim, hatta security officers din gidan duk suna sauraron shi ga dukkan alamu suna gamsuwa da bayananshi duba da yadda suke gyaɗa kawunansu.

"Banaso wani daga cikinku Ya tambayeta meyasa ta tafi, ko kuce zakuyi mata faɗa dan Allah kada kuyi mata hakan, Kuma kada ku faɗa mata abun da ya faru da mijinta da ƴarta, naji tana ambaton sunansu, ku sanar da ita cewa suna nan kuma zaku haɗata da su idan ta kwantar da hankalinta, idan ba haka ba zata Iya zaucewa idan taji cewa babu su"

Kamar malami da ɗalibansa haka shureim keyi masu magana suna amsa mashi da toh.

"Zuwa da safe kafin mu ƙaraso, a kira likitan gidanmu Ya duba lafiyarta," suka amsa mashi da toh.

"Mommy idan zainab ta bata ruwan zam zam din, in dai bacci bai ɗauke ta ba, ki taimaka mata tayi wanka taci abinci, idan kuma tayi bacci ku ƙyale ta kada ku takura mata" layla ta amsa mashi da toh.

Shigowa falon Zainab tayi hannunta ruƙe da robar zam zam ta ƙara so gaban sofa din da benazir ke akwance tana sambatu, muryarta harta disashe fuskarta ta kumbura suntum.

Zuƙunnawa tayi agaban sofa din, ta cizge murfin robar, da sauri Alhaji ubaid ya rurruƙe mata hannuwan Benazir, daƙyar ta Iya buɗe bakinta ta kafa mata ruwan zam zam din ya dinga shiga cikin ƙaramin bakinta, gaba ɗaya ta shanye ruwan, ko mintuna biyar ba'ayi ba da bata ruwan bacci mai nauyi ya ɗauketa, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, zufar jikinta tuni ta soma daskarewa, addu'o'i zainab ta dinga karantowa cikin harshen larabci tana tottofa mata saman fuskarta da jikinta, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma iyayenta ba, tuni layla tayi sallama da dr shureim ta miƙa ma Alhaji ubaid wayarshi ya sanya hannu Ya kar6a ya tura a aljihun jallabiyarshi, security office din dake atsaye bakin ƙofar falon suka yi masu sallama da niyar gobe da safe zasu dawo duba jikin benazir, Alhaji ubaid yai masu godiya kafin suka fice daga falon.

Hajiya layla ta dubi zainab kije ki kwanta mun gode sosai, dan Allah gobe da a suba ki shirya mata lafiyayyan breakfast din da zata ci" amsa mata tayi da toh, ta mike ta nufi room dinta, ya rage saura Alhaji ubaid da Hajiya layla a falon, kallon juna sukayi lamarin Ya girgiza su, abun daya ɗaure masu kai wanene yayi masu wannan muguwar aika aikar!!! Atare suka ɗaura idanuwansu kan benazir tsantsar sonta da ƙaunarta ne Ya kamasu, Har cikin zuciyarsu basu ji daɗin ƙaddarar data afka mata ba, tayi matuƙar basu tausayi ganin irin mayuwacin halin da take aciki, fatansu Allah Ya toni asirin baƙin azzulim daya yi silar barinta gida!!! yadda suka ga Rana haka suka ga dare, babu wanda Ya runtsa acikin zukatan nan guda huɗu, Hajiya layla da Alhaji ubaid, Dr shureim da Zainab, akan kunnuwansu aka fara kiran sallar asubahi!!!!

Dr.shureim Tun bayan daya dawo daga sallar asuba Yake ta faman shirye shiryen tafiya jos, tuni Yayi wanka ya kimtsa cikin shigar shi ta larabawa Yabi ko'ina na jikin shi Ya feshe da turare, Hannun shi ɗaya ruke da wayar shi ɗayan hannun Yana ruƙe da car key dinsa, takalmasa Ya zura a ƙafa Jiki Na rawa ya nufi ƙofar fita daga ɗakin bayan ya fito bai nifo ko'ina ba sai part din Alhaji musa don Ya sanar mashi da zancen bayyanar benazir da kuma tafiyar da zaiyi zuwa jos, abakin ƙofar ɗakin ya dai daita natsuwarshi, ya ɗaga murya yayi mashi Sallama, kusan sau uku kafin muryar Alhaji musa ta amsa mashi "Wa'alaikum salam shureim shigo ciki mana" ajiyar zuciya ya sauke, tare da sanya hannu Ya ture ƙofar ta buɗe, baiyi tsammanin zai ganshi tare da wani ba, ashe bashi kaɗai bane, su biyune shi da Hajiya Sarah suna zaune saman Sofa ɗin ɗakinshi, An jera masu kayan breakfast a saman sofa table din gabansu, mutumin babu annuri akan fuskarshi, Jallabiyace a jikin shi hajiyar tashi kuwa ta ca6a uban adon lace a jikinta, ta kashe ɗaurin kallabinta, wutsiyar gashin kanta ya sauka har saman wuyanta Fuskarta da fara'a take kallon shureim"barka da safiya My son, fatan ka wayi gari lafiya" shureim na murmushi yace"yawwa mommy, ina kwananku' ta amsa mashi da Lafiya lou, tare da nuna mashi wuri saman armchair ta ɗakin tace"bismillah ka zauna mana" tun da ya shigo Alhaji musa bai ɗago Ya kalli fuskarshi ba, Hankalin shi na akan abincin da Yake ci, plate ne agabanshi shaƙe da farfesun nama Yaji ƙayan hadi sai ƙamshi Yake Yi, a tsanake Yake cin abun shi. Kasa zama shureim yayi idanuwanshi akan fuskar Alhaji musa Yace"uncle barka da safiya" kamar bazai amsa mashi ba ya furta"lafiya" da ido Hajiya sarah tayi alamar yayi haƙuri da halin uncle din nashi, murmushi shureim ya sakar mata yaɗan jinjina mata kai "Ko zaka Bari idan Ya gama cin abinci sai ku yi magana, don bai cika son yana cin abinci ana yi mashi magana ba" hajiya sarah ce ta fada, Kafin dr shureim ya bata amsa muryar Alhaji musa ta katse mashi hanzarinshi"Shureim ina jin ka, faɗi abunda ya kawo ka" Ba ƙaramin daɗi Yaji ba, da fara'arshi ya fara magana"uncle bansani ba, ko daddy ya kira ka awaya ya sanar dakai abun farin cikin daya faru a daren Jiya" sai da ya ambacin hakan tukunna alhaji musa Ya ɗago da ido yana dubanshi alamar yana son jin ƙarashen zancen "Ƴar uwata Benazir ta dawo gida a daren Jiya ƙarfe goma sha biyu na dare!!!" Tsantsar mamaki da al'ajabi ne Ya bayyana akan fuskar alhaji musa, sai dai babu alamun zai furta magana sai faman jinjina kanshi yake yi. Hajiya sarah kuwa Tsabar farin ciki mikewa tayi tsaye tare da ɗaga hannyenta sama tana ambaton"ALHAMDULILLAH!! wayyo Allah shureim Allah Yasa ba wasa kake Yi min, dagaske Benazir ta dawo gida da ƙafafuwanta ko kawota akayi"? Shureim na murmushi yace"da kanta ta dawo gida, kuma abun mamaki tana ta sambatu tana ambaton sunan daddy da mommy da mijinta da ƴarta, kuma muna hasashen kurciya ne akayi mata da har ta gudu tsawon shekaru bata dawo gida ba, shiyasa nake so inje jos din Yanzu......." Hawayene suka wanke fuskar Hajiya sarah, Muryarta na rawa ta furta"shureim nima zan bika muje jos din, nasan shima uncle din naka zai je sai mu tafi atare..." kafin ta ƙare maganar Alhaji musa ya dakatar da ita ta hanyar cewa"Ya isa haka? Kinsan bana son shouting" shiru suka yi gaba ɗayansu, duk suka sha jinin jikinsu. Kallon shureim yayi"ina zaka je da safen nan, naga ka shirya ga key din mota a hannu"? Cikin sanyin murya yace"jos zan tafi, Inason ganin benazir"

Ta6e baki Alhaji musa yayi, tsawon mintuna ɗakin yai tsita, saida ya mula yasha iska tukunna yace"zanyi waya da yaya ubaid din, basai kaje jos din ba, zansa su zo nan abuja..." har saida gaban shureim Ya faɗi jin abinda Yace, bashi ba hatta Hajiya sarah arude take duban fuskarshi, kallon mara hankali take binshi da shi don wanna Yafi ƙarfin a kira shi da izzah, Tayaya zai nuna ƙarfin iko akan Yayanshi? Waye ya dace yazo gidan wani? Almost 16years yarinya ta 6ace sai Jiya ta dawo ƙarfe sha biyu na dare ko kaɗan bai nuna danuwarshi ba, kuma babu alamun zai je ya taya yayanshi murnar ganin yarsu da suka yi? Muryarta na rawa ta furta"am..amma hakan bai dace ba, nayi mamaki daka furta wannan maganar, kodai baka ji abunda shureim Yake faɗi bane? Ƴar wurin Yayanka benazir ce data 6ace tsawon shekaru ta dawo gida a daren jiya ƙarfe goma sha biyu na dare Yakama ka tashi ka shirya mu tafi" da buɗar bakinshi sai cewa yai"Umarni kike bani"? Da ƙarfin hali Ta furta"A'a kawai ina ƙoƙarin faɗa maka abunda Ya dace ne" tamkar zaki Haka ya yunƙura ya miƙe Ya dubi fuskar shureim da mamaki Ya gama kamashi "Nace bazaka je jos ba, ka koma ɗaki ka zauna, zansa Iyayen naka su zo tare da ƴar uwar taka abuja" gyaɗa kai dr shureim yayi jiki amace yace"toh uncle, na hakura, zan jira su zo ɗin" ƙwalla ce ta ciko idanuwanshi da sauri Ya juya ya fuce daga dakin. Bayan fitarshi Alhaji musa Ya nuna Hajiya sarah da Yatsan hannunshi"koda gigin wasa kada ki kuskura ki ƙara shiga tsakanina da shureim idan muna magana, abune da ya shafeni da dangina banaki ba, don haka ki kiyaye" yana gama fadin hakan a fusace yakai hannu ya yago tissue ya goge bakinsa ya nufi cikin dakin. Jiki asanyaye hajiya sarah ta zauna saman sofa din, lamarin Ya ɗaure mata kai, wannan rashin adalcin har ina? Meyasa zai dinga iko da yayanshi? Ko dan Yana da dukiya ne? girgiza kai tayi ahankali ta furta"wannan ba adalci bane" ta faɗa haɗi da miƙewa ta nufi hanyar fita daga ɗakin. Bawan Allah dr shureim abun duniya ya isheshi, Uncle musa Ya bashi mamaki, bai ta6a jin haushinshi ba sai yau daya nuna ƙarfin iko akan iyayenshi, Ya fahimci ma bai damu da dawowar benazir ba saboda babu annuri akan fuskarshi duk da yasan halin shi ne hakan, amma yaji ɗaci aranshi, don me zai dinga juya mahaifinshi son ranshi bayan shine agaba dashi, ko a shekaru Alhaji ubaid Ya zarce Alhaji musa nesa ba kusa ba saboda shi ba wasu shekaru gare shi ba, shiyasa ko a jam'iyarsu ake kiranshi da ƙaraminsu babbansu. Abun ya ɗaurewa Dr. Shureim kai, har ya fara tunani kodan Yana da dukiyane shiyasa yake sarrafa kowa yadda yake so? In banda rashin ta ido har zai Iya buɗe baki yace zai kira iyayan nashi suzo abuja maimakon shi ya tattara iyalansa suje can jos din su tayasu murnar dawowar ƴar su, Anya kuwa Uncle musa bai fara shan ƙwaya ba"? Saƙe saƙe zuciyar shureim take Yi mashi hakanan ya samu kanshi da kokwanton uncle din nasa. "Shureim dan Allah ka yi hakuri da abunda uncle dinka Ya faɗa maka, wallahi banji daɗi ba, bai kyauta ba, wannan ai ba adalci bane, bansan meyasa yake yin haka ba" Muryar Hajiya sarah ce ta katse mashi zancen zucin nashi, har ya kusa shiga ɗakin shi Ya ci burki tare da Juyowa baya yana dubanta Damuwace ƙarara akan fuskarta, kamar yadda shima tashi fuskar damuwarce Murmushin yaƙe ya ƙaƙalo akan fuskarshi da karyayyar murya ya furta"kada hakan ya dame ki mommy, da ace bansan halin uncle din nawa bane, amma nasani, shiyasa nake yi mashi uziri, bakomai zan jira su zo din kamar yadda ya fada" Gyaɗa kai hajiya sarah tayi har cikin ranta bataji daɗin abin daya faru ba "Bari na kira maka zeenatu, nasan zata ɗebe maka kewa, kafin isowarsu" still da murmushi akan fuskarshi Yace toh, zan jirata Bayan tafiyarta, Ya shiga dakin shi, asaman gado ya jefar da key din hannun shi, Ya tu6e arab tur6an dinsa Ya jefar saman gado, Ya zauna daga gefe hannu bibbiyu ya zabga uban ta gumi takaici Ya ishe shi, mahaifinshi Yafi 6ata mashi rai saboda shine silar komai, da ace tun farko bai bari uncle musa ya raina shi ba da duk hakan bata faru ba. Yayi zurfi acikin tunanin shi muryar Zeenatu ta katse shi "Yaya shureim ɗina" a hanzarce ya ɗago da ido yana dubanta, ta zumbula dogon hajibi har ƙasa Yake ja, ta ruƙo round plate mai ɗauke da mug, sai faman sakar mashi murmushi take yi, kwata kwata babu natsuwa atattare da ita, kafin shigowarta ɗakin mommynta ta faɗa mata xancen ganin benazir shiyasa take ta yin farin ciki, ita fa tun da take bata ta6a ganin benazir ba a hoto kaɗai tasanta saboda kafin guduwar benazir tana ƴar jinjirarta. Ganin yadda take tafiya babu natsuwa yasa shin saurin motsa la66ansa da niyar ya dakata da ita, sai dai ina kafin yai yunƙurin yin hakan tuni tayi tuntu6e da takalmanshi daya cire a tsakar ɗakin, Mugs din data dauko yai tsalle sama Ya dira daman ƙafarta ruwan coffee mai zafi Ya ɗalli ƙafarta, zafin da tajine yasa ta jefar da plate din hannunta, ta duƙe saman floor tana kuka, da sauri Ya miƙe ya ƙarasa gabanta, ya zuƙunna tare da kai hannu ya damƙi ƙafafuwanta Ya soma tottofe su da addu'o'i, ta dage sai kuka take yi mashi, abunka ga farar fata wurin da ruwan coffeen Ya ta6a yayi jawur kamar zai fashe. Kukanta duk Ya cika mashi kunnuwanshi, a hankali ya ɗago Yana dubanta, hawaye sun wanke fuskarta, lokaci ɗaya ya soma tariyo sambatun benazir tuni yaji jikinshi yai sanyi, haƙiƙa Yana matuƙar tausayin rayuwar ƴa mace, fuskar benazir ce ta dinga yi mashi gizo akan fuskar zeenatu, har baisan sa'adda Ya rungume ta a kirjinshi Ya zagoya da hannanyeshi saman bayanta, Yana ɗan bubbuga shi cikin sigar lallashi, ƙanƙameshi zeenatu tayi kamar zata koma cikin cikinsa, daddaɗan ƙamshin turarenshi ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba, tuni ta haɗiye kukan da take yi, tayi kwance abunta sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, dr. Shureim sam ya manta dawa ya rungume a jikinshi, kewar benazir duk ta addabe shi, Ya jefa zeenatu cikin yanayi najin shauƙin shi, yayin da shi hankalinshi nacan wani wurin daban...............

Idan muka koma 6angaren zahra, tun wuraren ƙarfe shidda Mahboob Ya shigo mata da jakar kuɗin motarta da wayar da aka saida mata, shaf shaf ta shirya cikin jallabiya ta yafa mayafi akanta, tace da mahboob ya taimaka ya kaita gidan Hajiya falmata, yace zai kaita amma bisa sharadin zata bashi nashi kason, tunda ai yayi mata ƙokari, a lokacin taƙagara da taje tace mashi ta amince su tafi kawai, kafin su bar gidan saida ta fara cire miliyan ɗaya ta ajiye su cikin drawer, ya rage saura 3m dai dai kuɗin da zata bata. Tana zaune a back seat na motar mahboob, yayin da shi kuma yake zaune a mazaunin driver, a tsanake yake yin driving har Allah Ya kawo su gidan Hajiya falmata. A parking space mahboob yai parking din motar yace da ita ta shiga yana jiranta, ta amsa mashi da toh, ta buɗe motar ta fito ta nufi ƙofar shiga babban falon gidan" Murmushin gefen fuska Mahboob ya dan saki yayin da yake bin Bayan zahra da kallo, ya zuro ƙafarshi daga cikin motar daya bar murfinta abuɗe Wayarshi ce tayi ringing daga cikin aljihu da sauri Ya zura hannu ya duba mai kiranshi sunan Aunty Aneelerh ne Ya bayyana Picking call din yai ya kara wayar a kunne"Babbar yayanmu, mun karaso gidan fa, Yau zahra zata sha mamaki, wallahi bakiga yadda take ta zubda uban gumi ba, kamar wadda tayi ma sarki ƙarya fadawa suka kamo ta" tuntsirewa yayi da dariya, Muryar Aneelerh da sautin dariya tace"baiwar Allah, ina fata yau hankalinta zai kwanta, naji daɗi da nasarar da muka samu, ubangiji Allah Ya ƙara tsare mata ita" ya amsa mata da ameen

Ta kuma cewa"Idan kuka dawo gida, ka faɗa mata cewa motarta da wayarta jingina ka bada su, idan tanaso ta baka kuɗin za'a dawo mata da su, sannan please bana so tasan cewa jiya munje gidan hajiya falmata, ya amsa mata da toh, daga haka sukayi sallamar.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull