Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 48

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 48

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 48: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 48. Tun da zahra ta shiga gidan, takasa zama, tana a…

3,370 words

Tun da zahra ta shiga gidan, takasa zama, tana a tsaye tana jiran fitowar hajiya falmata don ta miƙa mata kuɗinta, mai aikin gidan ce ta fito daga part din dakin nata ta dubi zahra"ki zauna mana gatanan fitowa" galla mata harara zahra tayi'ba zama nazo yi ba" murmushi mai aikin tasaki kafin ta wuce ta nufi kitchen Jim kaɗan, Hajiya falmata ta sauko down stairs, sleeping dress ne a jikinta riga da wando ta yafa mayafi akanta. Fuskarta babu walwala ta dubi zahra"zauna mana" tayi maganar tana nuna mata sofa Harara zahra ta watsa mata"ba zama nazo yi ba, kuɗinki na kawo maki" tayi maganar a fadace ta ajiye mata jakar gaban kujerar da take a zaune Har ta juya zata fita muryar hajiya falmata ta katse mata hanzarinta "Zahra! Dan Allah ki zauna inaso muyi magana badan halina ba" Batayi mata gardama ba tace"dan kin haɗani da Allah, shiyasa zan zauna badan haka ba wallahi ko kallo baki ishe ni ba" murmushi hajiya falmata tasaki. Bayan zahra ta zauna tana faman haɗe rai tace"ina sauraronki sauri nake yi in tafi" "Nasan zakiyi mamaki zahra, kuma ba lallai ki yarda da abunda zan faɗa maki ba, abunda Ya faru a tsakanina dake badagaske bane, jarabaki nayi saboda wani dalili nawa...." da mamaki zahra take dubanta, jinjina kai hajiya falmata tayi"tabbas ba halina bane, nayi ƙoƙarin jan ra'ayinki ne don insan dawa ƴata take tarayya" Tunkan ta kare maganar zahra tasaki dariyar rainin wayau tana fadin"dallah malama dakata! Banason zancen banza, harni zaki raina ma wayau? Ki gama zubda mutuncinki agabana kuma ki dawo kina fadin jarabani kikayi akan me kenan? A tsiwace ta furta hakan Numfasawa hajiya falmata tayi"zahra dalilin dayasa nayi maki hakan, Mun samu sabani nida wata aminiyata hajiya naja'at akan ƴarta dake bin mata, ta laƙafa mun sharrin cewa ƴata fatima ce ta koya mata, saboda ita kaɗaice suke tarayya, sannan ita taba yarta tarbiya tasan bazata ta6a aikata hakan ba, faɗa sosai mukayi da ita, ta zageni taci mutuncina, damuwar duniya ta isheni, lokacin dana dawo gida narasa ya zanyi in tuhumi fatima saboda nima ina tsoron ace ƴata tana aikata kalar abunda Yarinyar aminiyartawa take yi, nasan zaiyi wuya fatima ta faɗa min gaskiya, kinji dalilin dayasa na yanke shawarar yi maki hakan saboda nasan ke kaɗaice aminiyar fatima, duk wani abu da zatayi saida shawararki, atare kuke yin komai, Ni a tunanina ta hanyar dana 6ullo maki zan samu abunda nake nema na gano abunda ƴata take aikawata ashe ba haka bane nayi babban kuskure zahra, dan Allah Ki yafe min" fashewa tayi da kuka hawaye nabin fuskarta, baiwar Allah zahra tuni zuciyarta ta karya, sam bata kawo komai aranta ba, ta yadda da kalaman hajiya falmata, cikin shessheƙar kuka tace"Amma meyasa zaki yi jarabawar dani? Kin hanani bacci kin hanani cin abinci, kin jefa rayuwata cikin matsanancin tashin hankali, babban abun takaicina shine karya min zuciya da kikayi saboda na ɗauke ki tamkar mahaifiyata ina ganin girmanki, ashe dama duk plan ne kika shirya min"? Hajiya falmata na matsar ƙwalla tace"kiyi hakuri zahra nasan ban kyauta maki ba, dan Allah ki rufe min asiri kada kowa Yaji maganar nan, saboda banaso ayi tsammanin nima ina aikatawa ne sannan, maganar kuɗin da nake binku ni tuntuni na yafe maku, wallahi na bar maku su babu abunda zanyi dasu, sannan maganar yin order na kaya daga dubai in sha Allah gobe zasu iso Nigeria, inaso kuci gaba da gudanar da aikinku a companyna ke da fatima, don bazanso in rasa mace mai nagarta da tawakkali irinki ba, komai kuke so zanyi maku zahra, ni dai fatana ki manta da duk wani abu daya faru a tsakanina dake, Ki cigaba da daukata tamkar mahaifiyarki" Rushewa zahra tayi da kuka, kamar ranta zai fita, bata ta6a tsammanin komai zai zo mata da sauƙi ba, harta fidda ran cigaba da aiki a companynsu da kuma damar zuwa obie estate ashe da rabon mafarkin ta ya zama gaskiya. Cikin shessheƙar kuka tace"In sha Allah mommy babu wanda zaiji maganar nan, komai Ya wuce amma dan Allah kada ki ƙara yi min wasan nan, ni kaɗai nasan raɗaɗin da naji acikin zuciyata" Jinjina kai hajiya falmata tayi da karyayyar murya tace"bazan ƙaraba zahra, nima nayi danasani, dan Allah ki tsaya mu yi breakfast atare kada kice zaki tafiya" Zahra tace"sauri nake yi wata rana zan dawo, Ina fatima take"? Hajiya falmata tace"bata nan, jiya ta tafi gidan uncle dinta amma yau zata dawo saboda aikin da zakuyi tare" murmushin farin cikine Ya bayyana akan fuskar Zahra, sai faman washe bake takeyi harta fara tunanin irin rashin mutuncin da zatayi ma Aneelerh idan ta koma gida, Godiya sosai hajiya falmata tayi mata, itama zahra tayi mata godiya da fara'a suka rabu. Ta ruƙo jakar kuɗinta a hannu, tana fitowa daga falon da gudu ta nufi motar mahboob tana dariya haɗi da yin rawa tana jujjuya, Mahboob tamkar baisan komai yace"zahra kin haukace ne? Lafiya kike dariya kamar wadda ta zauce ga hawaye akan fuskarki" da sauri ta share hawayen da gyalen jallabiyarta Tace dashi"bro ka tayani murna yau ina cikin farin ciki, amma fa kada ka tambayeni meyasani shiga yanayin nan" Mahboob na murmushi yace"shakuruminki aini ba ɗan jarida bane da zan tsareki da tambaya, Yanzu dai shiga mota muje gida muyi magana akan haƙƙina," Da farin ciki tace"ai mahboob kamar yadda Allah Ya rufa min asiri kaima zan rufa maka asiri, kai dai muje gidan" ta faɗa haɗi da shiga motar, ya tada suka nufi Hanyar komawa gida.

*EX-PRISONERS🥳*

*At abuja Nigeria🛬*

Alhamdulillah Matafiya sun samu damar sauka Lafiya basu wayi gari ba sai acikin Katafaren Luxury Villa Mallakin Chief Owais sharafuddeen Obinna! haɗaɗɗiyar Daular arzƙi ce wadda zamu Iya kiranta da Aljannar duniya saboda Kayan alatun dake acikin ta, Katafaren gini ne mai girman gaske ta 6angaren tsayi da faɗi Yana ɗauke da Sassa Uku acikinsa, a ɗaya daga cikin Part din gidan aka yima Prisoners masaukinsu, A hankali nake bin ginin da kallo domin in ƙarasa ga cikinsa, ta ko'ina na kalla ƙyalƙyalin gilassai ne suke kashe min idona da kyawunsu, wasu irin haɗaɗɗun floor-to-ceiling Glass windows ne masu mamaye bango, daga ƙasa har sama glass ne, Kana Iya hangen Katafaren Main falo din dake acikin sashen ta glass windows din, Ga wasu sliding doors ƙofofi masu zuge kansu da zarar sun gama tantance mutun saboda gidan Yana da mugun tsaro ba iya mutane ba hada na'urori ke sarrafa shi, ba za ka ta6a Iya ƙetare Gingirimeman entry way din gidan ba tare da An tantance ka ba, daga ƙasa har sama, bana tunanin ko aljani zai Iya shiga salin alin ba tare da na'ura ta haska shi ba, salon kuma ace nayi karya (😂)

Dafa ƙofar glass din Nayi da hannuna ɗaya, Na'ura ta tantance ni aka bani iznin shiga ciki, Slowly glass din Ya soma zugewa, Na baza ido ina kallon tsaruwar Falon da kallon shi kaɗai zai Iya faranta zuciya, launukan painting cikinsa black, gold and white, An ƙawata shi da manya manyan sectional Chersterfield sofas, saiti biyu ne a palourn, Ƴan ubansu masu numfashi masu tafshi da daɗin zama ga jerin Throw pillows launuka daban daban saman kowace sofa, daga tsakiyar Katafaren falon wani faffaɗan Glass table ne daga saman shi an ɗaura flowers Vase, Furannin har ƙyalli suke Yi masu launi daban daban, bayan haka a kowani sofa hand din akwai Round glass table, mai dauke da kayan ƙyale-ƙyale na ado, daga saman jigunan ceilling din falon wasu ƙayatattun Crystal chandeliers ne masu girman gaske, An ƙawatasu da ado, kusan guda Uku ne a saman silin din, Haskensu Ya mamaye ko'ina tamkar da rana, Idan ka kalle su sai ka yi tsammanin zasu rubzo maka saman kai, sobada girman su, ga wata faskekiyar flat screen tv wadda idan kana kallo da ita sai ka yi tsammanin mutanan ciki zasu fito waje saboda girmanta, Bayan sofas din falon akwai hamshaƙan armchairs har guda biyu, hatta saman floor din falon Kayan adone aka ɗaura samansu, sparkling floor lamps ne ajiye a kasa suna bada nasu hasken mai ƙyalƙyali, akwai Kayan jin sauti, Ga Dogayen labulaye dake kewaye da falon an zuge su, A ƙalla Part din Yana ɗauke da Faluka sun kai Uku, bayan wanda na zayyana ma ku, daga cikin falon farko kana Iya hangen furniture din da ke a cikin falo na biyu ta hanyar Glass window, komai zaka Iya gani, Gidan fa Ya haɗu Ga glass elevator gefen twins stairs din dake a falon, ta ko'ina sanyayyan sanyin A.c ne ke ratsa fatar jikin bil'adama mai ni'imar gaske, bayan haka ta cikin glass din falon zaka Iya hango Sashen da tanƙameman swimming pool din gidan Yake, ruwan dake acikinsa launin sky blue ne, da wasu kujerun shaƙatawa a gefenshi, da sauran ababen more rayuwa, Idan muka koma Dining room wato ɗakin cin abincin gidan abun ba'a magana, shima a kewaye yake da floor-to-ceilling glass windows, kana Iya hangen abubuwan dake wakana daga wajen ɗakin cin abincin, An ƙawata shi da haɗaɗɗun dining tables, na farko zungureren table ne mai mazaunin mutun goma sha biyu, da me mazaunin mutun shidda, da kuma tabur mai mazaunin mutun uku, kowan nan su saman shi an ƙerashi da zallar glass, ƙafafuwansu kuma wooden legs ne, wasu haɗaɗun gujerune kewaye da tables din, daga saman ceilling din ɗakin cin abincin ƙaton kwan fitila ne ke haskaka cikinsa, ga kuma Zungureriyar floor lamp, Itama nata hasken Daban Yake, agurguje zamu leƙa Cikin Bedrooms din dake a part din, A ƙalla ɗakunan kwanan dake a cikin part din sun kai goma sha biyar, Just for one part, ƙofar shigar kowani ɗaki ta glass ce sai dai baka Iya hangen abunda ke ciki idan har na cikin ɗakin ya zuge curtain dinsa ba, ƙofar da kanta take zugewa da zarar mutun Ya kusance ta take sliding a hankali, Idan ka shiga ɗakin idanuwanka zasu fara Yin Arba da wallpaper ta bango mai matuƙar jan hankali, kowani room Yana ɗauke da hamshaƙan king-side beds masu tausasan Katifu kalar wanda ko mutun bai jin bacci idan Ya hau su sai dai aji sautin minsharin shi, saman gadon shimfiɗe yake da tausasan bedsheet, da jibgegen bargon lullu6a kafi mage laushi, ga jerin matassan kai daga gaban gadon.

Gefe da gefen gadon nightstands ne, wadanda ke ɗauke da bedside lamps, daga bakin gadon faffaɗan wooden table ne mai ɗauke da drawer chest a jikin shi, ga wani haɗaɗɗen rag carpet shimfiɗe ƙasa mai dumbujejen gashi gashi ajikinshi tsaf mutun zai Iya kwanciya saman shi saboda laushinshi, ga wani ƙayataccen dressing mirror gabanshi haɗaɗɗiyar kujerace, daga can cikin ɗakin akwai dressing room, aljannar duniya kamar ka shiga company saboda haɗuwar Large walk in closet din daya mamaye kowani bango na dakin sanya suturar, suturun sanyawa ne an jera su, daga waje zaka Iya ganin kayan dake a cikin closet din, 6angaren Kayan bacci, dana Dogayen riguna, 6angaren english wears dana atamfofi ga laces, da jerin coat, ga 6angaren takalma kala kala, dana jakkuna, kai komai fa an zuba shi babu ce kaɗai ke babu, shima ɗakin Yana da nashi dressing table, mai ɗauke da oval-shaped mirror, Mai Kyan gaske.

Ataƙaice Idan fa nace zan tsaya zayyana daular Owais sharafudden tabbas zamu ƙare littafin akan bayyana kyawunsa, sai dai mun shiga cikin labarin sannu a hankali zan ƙarasa zayyana maku haɗuwar wasu 6angarorin na gidan.

*CHIEF OWAIS✊*

Gajiyar tafiya ta hana shi ta6uka komai, ga6o6in jikinsa sunyi mashi nauyi, tun da ya fito daga bathroom yake a kwance saman katafaren king bed dinsa, ya lullu6e surar jikinshi da Cashmere robe launin dark navy, Iya gwiwarsa rigar ta tsaya mashi, ya ɗaure igiyarta daga saiting flat waist dinsa, mutumin fa akwai ƙirar ƙarfi, Kyawawan idanuwanshi A lumshe suke tamkar maiyin bacci, Yalwatattun eye lashes dinsa sun kwanta luf, a hankali Yake motsa soft thin lips dinsa tausasa launin pink, dogon hancinsa Yayi tsaye babu lanƙwasa Yayin da yake fitar da numfashi cikin kwanciyar hankali, ya zagayo da hannun shi ɗaya ta saman yalwatacciyar sumar kanshi, ba za ka ta6a gane a wani yanayi yake aciki ba, ya tada kansa asaman tattausan pillow.

Alert ne ya shigo wayarshi, tamkar baisan motsawa A hankali ya miƙa ziraran yatsun hannunsa na dama ya janyo wayar dake ajiye saman nightstand, daƙyar yake iya buɗe eyes dinshi akan screen din wayar, Doorbell alert ya gani alamar wani yana son shigowa room dinsa, unclock button ya danna, a hankali ƙofar room ɗin ta zuge, mutun biyu ne sanye cikin kakinsu, baƙaƙen kaya, dogon wando tare da black shirt, daga sama sun ɗaura long coat, kowannansu ya 6oye fuskarshi da face mask, idanuwansu ne kaɗai zaka Iya gani, suna da faffaɗan ƙirji, agaban gadon shi suka dakata da yin tafiya, cikin girmamawa suka haɗa baki wurin furta

"Barka da safiya Yalla6ai, fatan ka tashi lafiya, Ya gajiyar tafiya" tun da suka fara magana basu ɗago da ido sun kalle shi ba, saboda a ƙa'ida shi ba'ayi mashi magana ana kallon cikin idon shi, hakan babban laifi ne.

Bai da niyar yi masu magana, bai kuma buɗe idanuwanshi ba tun da ya lumshe su, aran su su ka ayyana yau qasaitar tashi ce ta motsa, kamar gumaka Ya shanyasu a tsaye suna jiran amsar shi, sai da ya mula yasha iska kamar baison motsa la66ansa Ya furta"Lafiya" muryarshi tamkar ana busa sarewa.

Big Guy yace"Sir, is there anything you need?" ya tambaye shi ne don shi a ƙa'ida ba'ayi mashi abun da bai ce yana so ba, ko da kuwa abinci ne ka kawo mashi duk mun yunwar da yake ji in dai bashi yace yana so ba to zai ce maka ka koma dashi inda ka ɗauko shi sai in yaga dama ya ke kar6ar shi"

Jin yayi shiru yasa Big Guy kuma cewa"yalla6ai zamu Iya yin magana ta waya"? Sai lokacin Ya ɗaga mashi kai alamar eh, ajiyar zuciya Big Guy ya sauke tare da kallon mutumin dake a gefen shi wanda suke kira Boss Man, murmushi su ka sakar ma junan su, sun ƙwammace su yi magana dashi ta text message saboda wahala yake basu in dai a baki zai furta masu magana.

Slowly ya ware reddish brown eyes dinsa akan screen din iphone dinsa, a tsanake yake yin typing.

Jin ƙarar shigowar message ta wayar Big Guy ne yasa shi yin saurin curo wayar daga cikin aljihun coat dinsa Ya duba abun da Chief ya rubuta mashi

_I need My breakfast right now_

cikin girmamawa big guy yace "I'll bring it to you immediately,"

Ya faɗa tare da Juyawa ya fuce daga ɗakin, Boss Man daya ya rage a tsaye ya natsu yana jiran jin me zai ce.

A lokacin da bai yi tsammani ba, muryar Chief ta katse shi"Have a seat" wuri ya samu saman doguwar sofa din ɗakin Ya zauna "Check your phone, I sent you a message." Ya bashi umarni. Da sauri Boss Man Ya zaro wayarshi daga aljihu ya soma karanta saƙon chief din nasu.

"Ya kake fatan ka tashi lafiya" murmushi ya saki har saida ya ɗago dakai Ya kalli fuskarshi, Yana matuƙar yin mamakin girmama shi da yake yi duk cikin waɗanda ke aiki a ƙarƙashinsa shi kaɗai Owais Yake gatantawa, suna mutunci da juna.

"Lafiyalou Alhamdulillah, Ina fata kaima lafiya, don na lura kamar gajiyar tafiya bata sake ka ba" abaki Ya furta mashi maganar, shi kuma Ya bashi amsa ta text message.

"Nagaji sosai, amma alhamdulillah, lafiyata ƙalou, Ina fata ka leƙa wurin Ƴar taka, "

Still fuskar Boss man da murmushi yace"ban kaiga zuwa ba, Yanzu nake shirin shiga na duba ta"

Text ya rubuta mashi"Make sure you give her a big hug. I know you've missed her for a long time."

Idanuwan shi ne suka cicciko tab da ƙwalla, tuni jikinshi yai sanyi, cikin sanyin murya ya furta"in sha Allah, zanyi hakan, daren jiya ko runtsawa banyi ba saboda jiran ƙarasowarku Nigeria, duk don saboda Inyi tozali da ita, sai dai ban samu damar Yin hakan ba, saboda Bayan nayi sallar asubahi a masallaci bacci Ya dauke ni, saida na shigo gida nake jin labarin ƙarasowar ku......" dakatawa ya ɗanyin da yin maganar, ganin text din da owais Ya tura mashi.

"Don't let the tears fall from your eyes, Otherwise, I won't let you see your daughter." fashewa yayi da dariya jin abunda yace mishi, har saida ya ɗago ya dubi fuskar Owais, Hankali kwance sam idanuwanshi basa akan fuskar Boss Man ɗin.

"Kana da mutunci, shiyasa muke ƙaunarka, wallahi tunda nake arayuwata ban ta6a ganin matashin saurayi mai wadatar arziƙi, da kyau da asali, mara girman kai irinka ba, saboda kowa naka ne, babu ruwanka ka ji daɗin rayuwarka, bazan ta6a mantawa da alheran da kayi mun ba, nasan bazan Iya biyanka ba amma ina fata Allah Ya wadatani da abunda zan faranta maka da shi"

Tunda ya fara magana Chief owais Ya natsu yana sauraron shi, idanuwanshi akan screen din wayarshi.

Tambaya ya jefa mashi"What's her full name?"

cikin girmamawa Boss Man yace"UNAISAH ZAHEER TAJUDDEEN" lumshe idanuwanshi yayi, ƙamshin turaren jikinsa yana ƙara daɗaɗa hancinsa.

"She looks like you" dariya Boss Man ya saki yana duban fuskarshi Yace"tayaya akai ka sani? Kaida baka kallon mutane, Ni nasan baku haɗu da ita ba"

Kafin Owais Ya furta magana, alert Ya shigo wayar shi, unclock button ya danna, door room din ta zuge, Big Guy ne ya shigo da food trolley, Ya gunguro shi zuwa gaban wooden table din gadon Owais, a saman shi Ya jera mashi kayan Lafiyayyan breakfast dinsa, Bayan ya gama da zolaya Boss man yace"Big Guy, mutumin fa yau baya iya cin abinci da kanshi, ko zaka mashi abaki"? Big Guy na murmushi yace"If he gives me the opportunity to do that, I'll do it har wanka zan dinga yi mashi...."daƙyar Ya ƙare maganar ganin yadda Chief owais Ya ɗago da sexy eyes dinsa akan fuskarshi, cikin jin kunyar maganar daya furta ya sunnar dakai ƙasa Yana faɗin"afwan Sir, su6ul da baka nayi"

Fuskarshi a ɗaure Ya furta"If you ever repeat this mistake, you'll spend the rest of your life in prison." Dariya Boss Man yayi jin abunda chief yace, Big Guy na murmushi aranshi Yana fadin"Ai bazan ma ƙaraba, Yanzun ma albarkacin boss man naci"

Ajiye wayarshi yayi saman nightstand, Ya yunƙura Ya miƙe Yana faman Yamutsa fuskarshi, Big guy dake satar kallon damtsen hannun shi sai faman jinjina kanshi Yake Yi, dawowa yayi end bed din Ya zaune gaban glass table din dake shaƙe da abinci.

Serving dinshi big guy Ya fara Yi, Ya miƙa mashi mug na coffee, Kafin Ya fara sha sai da Ya fara fadin"Boss bismillah" Man na murmushi Yace"A'a yalla6ai, Ni ina na isa In haɗa Kafaɗa dakai wurin cin abinci, kaima ka sani bamai yiwuwa bane, sannan Ni a ƙoshe nake, Madam ta girka min abinci na cika ciki na"

Ta6e baki Chief Owais Yai, ba tare daya ƙara furta komai ba.

"Yaran fa har Yanzu bacci suke Yi yalla6ai, na lura ba ƙaramin gajiya suka yi ba, musamman Kyakkyawan matashin nan dake acikinsu, mai kama dakai,' yamutsa fuska owais Yai jin ance mai kama da shi.

Fresh fruit ya soma ɗauka Yan sha, duk wani motsin shi akan idon Boss Man, Yaron ba ƙaramin burgeshi Yake Yi ba, ƙaramin mutun da halin girma, Idan kaji shekarun chief owais zaka sha mamaki, girman jikine kawai dashi da kuma babban matsayi da Allah Ya bashi, uwa uba Ya iya dattako.

Boss man Yace"An kammala shirya masu breakfast dinsu, masu aiki suna can suna aikin jera masu, Yanzu su kaɗai muke jira su farka don su ci" ya faɗa yana duban fuskar chief, Jinjina kanshi ya ɗanyi batare daya ɗago da idona ba ya furta"hakan Yayi kyau"

Miƙewa Boss Man Yayi"Ni zan shiga Cikin gidan, Ka ci abinci Lafiya our chief" Ya ambaci hakan tare da Juyawa Ya fuce daga ɗakin, Ya rage saura Big guy dake saving dinshi.

*🤍EX-PRISONERS❤*

Kwance take saman katafaren gadon ɗakin Danish, tun daren Jiya da suka ƙaraso kowannansu aka ware mashi ɗakin shi, mutun biyu ɗaki ɗaya, Danish ne kaɗai Aka mallaka mashi bedroom ɗaya saboda shine babbansu, Angel da Batul ɗakinsu daban, Azeeza da jamima ɗaki ɗaya, Parveen da Hanna suma nasu daban, Gabriel da Naufal room ɗaya, Javed da haris a ɗaki ɗaya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull