Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 49

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 49

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 49: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 49. Saboda Rashin lafiyar danish yasa ta gudo daga…

3,370 words

Saboda Rashin lafiyar danish yasa ta gudo daga ɗakinsu ta dawo nashi tana matuƙar jin tausayinshi batasan wani abu ya same shi, gani take kamar idan tayi nesa dashi wani abu zai faru da shi, gown din Jiyace a jikinta red colour, tayi uban squeezing, hatta sumar kanta a haukece take babu gyara sunsha bacci kamar ba za su farka ba, daɗin lumbutsetsiyar katifar gadonne Ya sanya suka shagala, daga ita har shi garkuwan, ya cire suit jacket din jikinshi Iya farar shirt dince Ya bari, da gajeran wando fararen laps dinshi kamar ka ta6a jini ya ɗago tsabar hasken fatar, ya ɗaura kanshi saman wuyanta, yayin da hannayenshi biyu ke a ruƙe da waist dinta, zafin jikinshi ya daidaita bakamar da suna acikin jirgi ba zazza6i ya lullu6e shi, Yanzu ya samu sauƙi numfashinshi na fita cikin kwanciyar hankali, Sanyin A.c din dakin ya ƙara masu ƙaimi wurin Yin baccin nasu kamar matattu.

Mutsu mutsu ya soma yi alamar zai farka, wata irin matsiyaciyar yunwace ta addabe shi, tun Jiya baici ko mai ba, ko ruwa bai gifta maƙoshin shi ba, Dogon numfashi yaja idanuwanshi sunyi mashi nauyi Ya gaza buɗe su, da wata irin kasalalliyar murya ya soma ambaton sunanta"My Angel! My Angel" badan la66ansa na akusa da wuyanta ba da kuwa zaiyi wuya ta iya jin muryarshi.

Kamar an zungureta, a firgice ta farka tana faman zare gray eyes dinta haɗi da ambaton sunanshi"Danish are u okey? Ko jikin ne"?

Daƙyar Ya iya janye head dinsa daga saman wuyanta Ya daura shi saman tattausan pillow, a hanzarce ta yunƙura Ta miƙe zaune tana faman mutsistsike idanuwanta da hannunta donta samu damar ƙare mashi kallo.

"My man, yunwa ko"? Tun kafin ma ya faɗa mata abunda Yake Ji ta riga shi faɗi. Ɗaga mata gira yai alamar eh, murmushi ta ɗan sakar mashi har dimple dinta Ya lotsa"Danish banga ka yaba kyan ɗakinka ba, ko da yake baka acikin hayyacinka, saboda kana Jin Yunwa, bari naje naga ko zan samo maka abunda zaka ci, kafin in dawo ka shiga toilet kayi wanka, sai ka canza kayan jikinka" kamar ƙaramin yaro haka takeyi mashi magana.

Wurga eye balls dinshi yayi akan katafaren ɗakin nashi, kamar na ɗan shugaban ƙasa tsabar haɗuwarshi.

Saukowa Angel tayi daga saman gadon, tana tafiya tana waiwayon shi, daɗi kamar ya kashe ta, haƙika taji daɗin canjin rayuwar da suka samu, har ta fara tsara masu irin rayuwar jin daɗin da zasuyi, sai dai ta ɗan shafa'a da zancen kurkukun ƙaddara.

Tun da ta fito daga ɗakin take faman ƙwala ido tana kallon haɗuwar katafaren falon, Cikin sanɗa take Yin tafiya kamar 6arauniya, fararen ƙafafuwanta babu takalma, bata nufi ko'ina ba sai ɗakin su Azeeza a hankali ta zuge ƙofar ta faɗa cikinsa, tayi mamakin ganinsu a tsaitsaye saman bed mattress kowacce ta ruƙe pillow a hannunta, sai tsalle suke Yi suna fadin"gamu agidan daddyn Genie" dariyace ta kusa kubce mata da sauri ta toshe bakinta da tafin hannunta, wato su duk a tunaninsu gidan daddyn Genie ne aka kawo. yara sun zama ƴan hutu. Fitowa tayi daga ɗakinsu ta nufi ɗakin Parveen tana shiga ta sameta a zaune tsakiyar gado, bacci yaƙi sakinta ga yunwa tana ji sai faman yin hamma take Yi, sumar kanta kamar ta mahaukaciya duk ta yamutsata, ta gimtse eyes dinta, hannah na akwance gefenta sai sharar baccinta take Yi.

Ƙumshe dariya Angel tayi da sauri ta fito ta nufi ɗakin su Haris don ta duba su, lokacin data shiga ɗakin gaba ɗayansu bacci suke yi daga shi har javed duk sun cire suit jacket dinsu sunbar shirt da gajeran wando.

Fitowa tayi dakinsu ta nufi, ɗakinsu Naufal, adai dai lokacin Gabriel Ya fito daga wanka, daga shi sai short, Ya ruƙe short toilet Yana tsane sumar kanshi, Naufal kuma yana zaune saman mirror chair Ya ƙura ma madubin ido da alama gabriel din Yake jira ya fito daga wankan shima Ya shiga.

Gaba ɗaya basu lura da Angel ba, da zolaya gabriel Yace"mutumin kyau kake kallo a madubi naga tun ɗazu ka tasa shi agaba ko ƙyafta ido baka Yi"

Ba tare daya juyo ya dube shi ba yace"Kai nake jira ka fito daga toilet din nima wankan nake son Yi"

Gabriel Yace"amma dai kasan toilet din nan ba kalar na prison bane, akwai ruwan zafi dana sanyi kada kaje ka ƙona fatarka, kazo in nuna maka Yadda zakayi amfani da shi"

Harara Naufal Ya watsa mashi"bana buƙata, nima zan Iya dakai na" gabriel na dariya yace"bana so ka yi danasani" miƙewa naufal yai ya nufi toilet din Ya shige, shigar shi ko minti ɗaya ba ai ba sai gashi ya fito Yana haɗe rai Ya kalli gabriel"nifa bangane komai ba" dariya ce ta kufce ma Angel gaba ɗaya suka juya suna kallonta, har ta juya zata gudu Gabriel Yai saurin zuwa ya ruƙo hannunta"Sister yaushe kika shigo? Ba sallama? "6atan Hanya nayi, ni banma san na faɗo ɗakinku ba"

Naufal Yace"kindai shigone yi mana leƙen asiri, kuma kinga abunda kikeson gani, gashi har kina dariya" girgiza kai tayi"wallahi ni ba abunda nashigo gani, ba ri ma in tafi" ta faɗa tare da Juyawa da sauri ta fuce daga ɗakin,

Kallon Naufal Yai"muje ko" sai da ya fara murguɗa mashi baki, kafin Ya Juya suka nufi toilet din, Ya nuna mashi yadda zaiyi amfani da komai, kafin Ya baro shi a cikin toilet din.

Tana cikin tafiya Muryar Batul ta katse mata hanzarinta"Angel"a firgice ta Juya tana kallonta, buɗe baki tayi haɗi da zare idonta, ganin Batul ta fito tana faman Yin hamma haɗi da Yin miƙa duk a lokaci ɗaya "Yaushe kika tashi"? "Yanzu, na duba ɗakin banganki ba ashe kina anan" tunda ta fara magana idonta ba akan Angel Yake ba, Katafaram Falon take ƙarema kallo, kamar maijin tsoron shi, sai faman ƙyafƙyafta idanuwanta take Yi, bakinta hada Miyan bacci, kwata kwata babu natsuwa atare da ita, musamman sumar kanta tafi komai haukacewa.

Miƙa mata hannu Angel tayi"idan zaki bini taho mu tafi, Nima kitchen nake nema, danish ne Yake jin yunwa" da sauri batul ta ƙarasa ta nufeta ruƙo hannunta tayi acikin nata, Har sun ɗaga ƙafa zasu motsa kwatsam muryar Ummin america ta katse masu hanzarin su"Where are you all going? Wa ya Baku iznin fitowa daga ɗaki"? Har saida gabansu Ya faɗi, duk suka sha jinin jikinsu, A hankali take saukowa down stairs, kimono robe ce a jikinta har ƙasa rigar takai mata, Tabi shape din jikinta, takalman ƙafarta high hills ne, hair wing din dake akanta launin black ne.

Tana tafiya Hips dinta na jujjuyawa kamar ana kaɗasu, agabansu ta tsaya haɗi da Goya hannayenta saman tudun kirjinta tana kallonsu, idan ta kalli Angel sai ta kalli Batul, kamar wasu munafukai sunyi wuƙi wuƙi da ido, musamman Batul duk tasha jinin jikinta, saboda mugun jin shakkarta take ji, har ƙwara Angel ashirye take da tayi mata rashin kunya idan har ta ƙetare iyakarta.

"Ke! Meye sunanki"! Ta jefa ma batul tambayar, muryarta na rawa ta furta"BATUL"! ta6e baki ummi tayi tare da daura idonta kan Angel"ke fa"? Ɗaure mata fuska Angel tayi kamar bazata tanka mata ba tace"UNAISAH" "Me kuke nema ne"?

Angel ce tayi ƙarfin halin bata amsa da cewa"ɗan uwana ke jin yunwa, shine na fito don in sama mashi abun da zai ci" Ta6e la66a ummi tayi"An shirya maku breakfast din ku a dining, dama ku nake jira ku farka" ta faɗa tana nuna masu dining room da hannunta, atare su ka kai idonsu ita da batul suka kalli ɗakin.

"Ku koma ku tada sauran ƴan uwan naku, su fito mu yi breakfast, idan mun kammala inaso zanyi magana da ku"

Amsa mata su ka yi da toh, da sauri suka juya suka nufi bedrooms din ƴan uwansu, tana a tsaye tana bin bayansu da kallo, bakomai yafi bata mamaki da yaran ba face doguwar sumar kansu data lullu6e bayansu kamar hijabi, aranta ta ayyana ɗawainiya da yaran nan ba abune mai sauƙi ba, gyaran gashin kansu kaɗai wata wahalar ce mai zaman kanta, gashi an faɗa mata babu shige babu fuce balle tace zata kai su saloon, kuma babu damar a gayyato masu yi din suyi masu, dole sai dai ita ce za ta gyara su.

Daya bayan ɗaya suka bi ɗakunan yan uwansu suka shiga domin tada wadanda basu farka daga bacci ba, saida suka taimaka ma Azeeza da jamimah suka wanke fuskokinsu da bakunansu, tukunna suka fito daga ɗakin, Kayan jiya ne a jikinsu sai mayafin da suka yafa akansu, Hankalin su ba ƙaramin tashi yai ba, musamman azeeza tun da tayi tozali da ƙwan fitilun falo jikinta Ya hau yin kerma, duk ta firgice, Parveen kuwa baki yaƙi rufuwa kamar lefen sakarai sai faman zazzare idanuwa suke Yi, saboda yanzu ne suka samu damar ganin ko'ina na cikin gidan dakyau, Hanna kuwa daƙyar take taka tiles din floor, da takalmi ta fito amma saboda tsabar ruɗu a hannu ta ruƙe takalman ta rungumesu a ƙirjinta, gani take kamar in ta taka ƙasan da takalman zai fashe, Naufal da Javed har tuntu6e suke yi garin yin kalle kalle gidan yayi matuƙar ruɗar dasu, shi ko Haris jiki sai kerma yake yi basa ban ban, shima crystal Chandelier din ceilling ne Ya ruɗar da shi ga sanyin A.c da yayi mashi yawa, hatta gabriel dake da wayewa yau dai an ƙure shi, sai faman jinjina kai Yake yi yayin da yake bin katafaren falon da kallo, abunda zai baka mamaki jamimah hankalinta kwance babu abunda ya ruɗe ta koya tsoratar da ita, sai faman washe baki take Yi komai ta kalla saita nuna shi da yatsa tace"menene wancan" ta ishe su da tambaya kamar rainon ɗan jarida, Ummin america dake a tsaye bakin ƙofar shiga dining room din, lamarin ya ɗaure mata kai, tayi matuƙar yin mamakin ƙauyancin su, gasu dai a halitta kamar ƴa'ƴan masu kuɗi, tafiya suke yi tamkar suna jin tsoron taka floor, sunƙi maida hankali su shigo su ci abinci, sai faman ƴan kalle kalle suke Yi kamar wuyansu zai cire.

Mutum ɗaya ce babu acikinsu, Angel da ta tafi bedroom ɗin Danish, Batul dai tana atare da su Haris.

Gyaran muryar da ummi tayi masu ne ya janyo hankalinsu ga kallonta. Da hannu ta nuna masu ƙofar shiga"ku zo ku shiga" ba tare da sun tanka mata ba, suka nufi ɗakin cin abincin, koda suka shiga sai suka koma suna bin ko'ina da kallo, Parveen ce ta furta"La'ha'ilah! Wannan duk namune"? Ta jefa tambayar tana nuna kayan breakfast din dake a jere saman zungureran table.

Ummi ce ta bata amsa da cewa"naku ne, kowa ya samu wuri ya zauna" su parveen anga banza, tuni taja kujera ta zauna, ɗaya bayan ɗaya kowannansu Ya samu wuri ya zauna, sai faman baza ido suke Yi suna bin komai da kallo, jamimah tana jinjina kai tace"Yau zamu ci daɗi, wallahi munji daɗi muma mun zama ƴan gayu, gidan daddyn genie akwai abinci da kayan wasa"

Azeeza taƙi ɗagowa dakai, ta ƙanƙame jikinta saman kujera, ita kwan fitila ne damuwarta, na ɗakinsu bai kai na falo dana dining room girma ba, sun hanata sakat, Gabriel dake kallonta cikin muryar raɗa ya ambaci sunanta"My azeeza" ɗagowa tayi da ido tana kallon shi sai faman yamutsa fuska take Yi "Meke damun ki"? Da index finger ta nuna mashi saman ceilling ba tare da ta kalla ba, muryarta ƙasa ƙasa tace"zai Iya faɗowa saman kanmu"

Murmushi ya sakar mata"ki kwantar da hankalin ki, ba zai ta6a faɗowa ba, idan ma zai faɗo sai na tare maki shi, hakan yayi maki"? Sai lokacin ta ɗan saki murmushi jin abun da yace ta jinjina mashi kai alamar eh.

Parveen sai faman haɗiyar yawu take yi ta ƙosa su fara ci, sai dai sun gaza sanya hannu ganin yadda Ummin america ta tsare su da ido ko kyaftawa ba tayi, tana daga tsaye bakin glass door din dakin, ta lura basu cika ba shiyasa ta tsaya tana jiran sauran su ƙaraso don su fara ci.

"Menene wannan abun" jamimah ce tayi tambaya tana nuna wata roba Kallon robar Gabriel yai a jikinta an rubuta Honey.

"Zuma ce a ciki, kin ta6a sha"? Girgiza mashi kai tayi alamar a'a, ta kuma nuna dafaffan ƙwai tace"wannan luluyayyan abun fa"? Harara ya dan jefa mata"Ƙwai ne, pls ki daina yi min tambaya baki ga ana kallon mu ba"? Ta6e mashi baki tayi"to aini inason in sani ne ko," har tayi shiru can kuma kamar an cikare ta tace"Gabriel kace ƙwai ne, to shima kamar ƙwan fitila mai bada haske Yake"shiru yayi yana kallonta ba tare daya furta komai ba,

(abun da yasa take tambayarshi saboda bakomai ne suka sani dangane da nau'ikan abinci, ko a kurkuku snacks da nama suke ci da kayan marmari, haka zalika a asibiti da suka zauna bakomai ne suka sani ba yawanci duk kalar abunda suke ci a prison ne, yau sunci karo da wasu nau'ikan abincin dana sha wanda basu ta6a yin tozali da su, shiyasa jemimah ta tsare shi da tambayoyi kamar ƴar jarida)

Batul dai sai satar kallon ummi take yi ita kanta ummin ta lura da kallon ƙurullan da Batul take Yi mata, shiyasa ta tsaida idonta akanta, tunda tayi hakan batul ta saddar da kanta ƙasa cikin jin kunyarta.

Abun da Ya faru, Lokacin da suka kammala tada ƴan uwansu Angel ta nufi ɗakin Danish, shigarta keda wuya ta taras dashi atsaye gaban mirror Yana faman yin haki Ya dunƙule tafukan hannayensa kamar wanda zai yi dambe, Kafin ta buɗe baki ta tambaye shi lafiya, idanuwanta suka sauka akan madubin daya fasa, ƙwaƙƙwaran naushi ya kai mashi gaba ɗaya ya zube ƙasa ya tarwatse.

Rass taji gabanta Ya faɗi, a tsananin tsoroce ta furta"Na shiga uku! danish meyasa zaka fasa masu madubi? Kasan kuwa tsadar dake gare shi? Wai meke damunka ne? So kake kaja mana bala'i daga zuwa gidan mutane har ka fara yi masu 6arna" hankalinta atashe tayi maganar tana duban bayanshi.

A hankali Ya jiyo yana kallon cikin sanyin murya ya furta"mutun na gani aciki Yana kallona, shiyasa na naushe shi" Zaro ido waje tayi can kuma ta tuntsire da dariya hada dafe ciki, ɗaure mata fuska yai ganin tana yi mashi dariya.

Nuna shi tayi da yatsa tana fadin"mutumin da ka gani acikin madubin kaine ba wani ba, ai saida naso in nuna maka kanka a mirror amma kaƙiya, ka nuna baka son kallon shi gashi nan Yanzu ka fasa masu madubi mai tsada, Ni dai ba ruwana" ta faɗa fuskarta da murmushi.

Kallon rashin fahimta yake binta da shi, ya rasa gane me take nufi, kamar bata fahimci abunda ya faɗa mata ba.

Gudun kada wani ya shigo ya taras da 6arnar da Danish yayi yasa tayi saurin juyawa tana yan dube dube cen idonta ya sauka kan wani abu yayi mata yanayi da tsintsiya da sauri ta ɗauko ta tattara broken glass din ta turasu kasan gadon shi dan bataga dust bin a dakin ba ajiyar zuciya ta sauke

Kafin ta ɗago tana dubanshi"kai kaɗai muke jira, zamu yi break fast, ka shiga toilet ka wanke face dinka da bakinka, idan mun gama cin abincin sai kayi wankan" toilet door Ya nufa, har ya kusa kaiwa ƙofar ta tuna da madubin toilet, da karfi ta furta"dakata danish" cak ya tsaya da tafiya, da sauri ta nufi ƙofar toilet din ta buɗe ta shige ciki, towel ta ɗauko ta rufe madubi, saboda tsaro tasan zai Iya Fasa shi kamar yadda ya fasa na room dinsa.

Fitowa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya ta dubi fuskarshi"nasan idan ka shiga ciki zakaga towel na lullu6e wani abu dashi, kada ka buɗe shi, madubi ne bana so ka fasa shi kamar yadda ka fasa na ɗakin ka, Idan ba haka ba zasu ce saika biya su ne kuma kaga bamu da kuɗi, kai ba kama san menene kuɗi ba, Ni zaka bari da aikin biyansu" ta faɗa tana yamutsa mashi fuska, bawan Allah yayi tsaye yana kallonta.

"Ina jiran ka, kada ka daɗe ka yi sauri ka fito suna jiran mu"

Amsa mata yai da toh, kafin ya bude kofar ya shiga, Ƴan mintuna ya fito daga ciki, har yayi brushing teeth dinsa, daga kasa har sama take bin shi da kallo, a ganinta basai ya tsaya sanya kaya ba tun da ba wanka yayi ba, Ruƙo hannun shi tayi acikin nata kamar wani ƙaninta"muje ko"? Ta faɗa tana ƙoƙarin janshi.

Adai dai lokacin da suka sauko falon, ƙofar shigowa cikinsa ta zuge a hankali, atare Angel da Danish suka juya baya jin takun tafiyar mutun.

Basu san wanene ba, amma saida taji gabanta Ya faɗi, ganin kakin dake a jikinshi na baƙaƙen Kaya, kuma ya rufe fuskarshi da face mask, 6oyewa tayi bayan Danish ta ƙanƙame shi tana leƙen mutumin da ke tunkaro su.

Bugun zuciyarta na ƙaruwa kamar zai fasa ƙirjinta.

Miƙa ma Danish hannu yai da niyar su gaisa, Danish Yaƙi bashi hannu saboda rashin yardar da shi, gyaran murya ya ɗanyi kafin ya soma magana a tsanake"zaku Iya kira na da Boss man, ina ɗaya daga cikin masu kula da ku," ya faɗi hakan ne don su saki jiki da shi.

Ajiyar zuciya Angel ta sauke, jin muryarshi ta kamilallun mutane.

Dawowa tayi daga gaban shi ta tsaya tana dubanshi, ido cikin ido suke kallon juna ba tare da ƙyaftawa ba.

Tsawon mintuna kafin ta furta"Ina kwana," ya amsa mata"lafiyalou Angel, kin tashi lafiya? Ya kuma gajiyar tafiya" Tace"lafiyalou, gajiya tabi jiki, mun gode da kulawa" da alamun jin daɗin maganarta ya furta"Naji daɗin ganinki da ranki da lafiyarki, ina fata baki da wata damuwa" maganarshi taɗan so ta ruɗar da ita, amma sai ta basar tace"nima haka" da ƙyar ta furta ganin irin kallon da yake binta dashi, duk saita sha jinin jikinta, ta rasa gane kallon menene yake yi mata, dauriyace kawai yake yi, yaso ace zai iya bayyana mata kanshi a yanzu sai dai bazai yiwu ba.

"Ciki zamu shiga Ni da Danish, suna jiranmu a dining" ta fada don ta samu damar guduwa daga kallon da mutumin yake binta da shi.

Ɗagowa yai da ido ya dubi fuskar danish, har saida yaɗan ji gabanshi ya faɗi ganin yadda ya ɗaureta tamau babu annuri, dama tunda ya shigo falon yake mamakin kyawunshi da body structure dinshi don shi sai yanzu ya samu damar ganin shi, abakin abokan aikinsa yaji suna zuzuta kyan yaran da kamanninsu da Chief dinsu.

"Ɗan uwan naki bai magana ne? Yaƙi bani hannu mu gaisa" murmushin yaƙe tasakar mashi"rashin sabone, Yana da wuyar sha'ani amma idan kuka saba zai saki jiki da kai"

Jinjina kai boss man yai"okey, mu shiga ciki, Nima can zanje" a fakaice ta yamutsa fuska, aranta ta ayyana wannan mutumin zai takura mata ga shi da kallon tsiya kamar zai lashe mutun" a fili kuma taja hannun dashi suka nufi dining room din, Boss man na abiye da bayansu, kwata kwata babu alamun ƙauyanci atattare da Danish, sai dai jefi jefi yake satar kallon kayan alatun dake acikin katafaren falon.

Lokacin da suka shiga dining room din da sallama abakunansu, gaba ɗaya hankulansu Baful Ya dawo kansu, Ummin america tuni ta samu wuri ta zauna, ganin Angel da suka yi da danish nan fa suka fara sakin murmushi kamar wasu zautattu, kujera taja ma danish ya zauna Yana fuskantar ummi, ita kuma Angel ta zauna daga gefen shi, Sai daga bisani su Gabriel suka lura da Boss man daya shigo, kallon juna suka yi da alama sun ɗan tsorata da ganinshi saboda dressing din jikin shi yayi shige dana Giants din kurkukun ƙaddara.

Sai da Angel tace"ku gaishe shi, sunan shi Boss man, Yana ɗaya daga cikin waɗanda zasu dinga kula da mu" har suna haɗa baki wurin furta mashi gaisuwa, a mutunce ya amsa masu yaji daɗi yadda Angel tayi masu bayanin wanene shi.

Ummi ta dube shi awayance tace"barka" ya amsa mata da"yawwa ya kike fatan kin wayi gari lafiya" a yayin da yake ƙokarin zama gefen kujerar dake a kusa da ita, wadda ke fuskantar Angel, don yaji daɗin kallonta.

Ummi tace "Lafiyalou," daga haka ta miƙe ta soma yin serving dinsu, a plates ta zuzzuba ma kowannansu abinci, ta dauki cups ta tsirara masu tea dake acikin flask, Bayan ta gama ta koma ta zauna"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull