Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 52
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 52: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 52. Gaba ɗayansu sun shiga yanayi mara misaltuwa, ba…
3,371 words
Gaba ɗayansu sun shiga yanayi mara misaltuwa, ba zato ba tsammani Boss Man yaji dirar wani abu saman bayanshi, da sauri ya ɗago da kanshi idanuwan shi sun canza launi sun kada jawur kamar mai fama da ciwon ido, yayi mamakin ganin pillow da aka jefo mashi ya fadi ƙasa, da sauri ya ɗaga ido sama don ganin wanene ya wurgo mashi pillow saman bayanshi, karaf idanuwan shi suka sauka akan Danish dake tsaye can second floor, hannun shi ruƙe da wani pillown Yana niyar ƙara jeho mashi, fitowar shi kenan daga ɗaki idanuwanshi suka hango mashi Angel ɗinsa rungume da wani ƙato, shine fa yaje ɗaki ya ɗauko fululluka har biyu Ya jeho mashi ɗaya.
Ya haɗe fuska babu annuri, kayan bacci ne ajikinshi riga da wando launin pink sunyi bala'en yi mashi kyau.
Harara ya watsa ma boss man, ganin Angel taki barin ƙirjin mutumin yasa shi ƙara daddagewa ya wurgo mata pillow, da sauri boss man Ya tarbe pillown a hannun shi, Lamarin ya ɗaure mashi kai, sai yanzu ya gane dalilin dayasa yaron yaƙi sakar mashi fuska tun jiya yake daure mashi fuska, ashe kishi ne ke damun shi.
"Unaisah"! Jin boss man ya ambaci sunanta yasa ta ɗago da kanta tana kallon shi, mamaki ne ya kamata ganin pillow a hannun shi, da ido yai mata nuna da bayanta, da sauri ta juya don ganin wanene, a tsaye ta hango shi ya ruƙe qugu yana aiko masu da harara.
Batasan sa'adda ta tuntsire da dariya hada dafe ciki, da zolaya boss man yace"kishine ya addabe shi shiyasa yake jifar mu da pillow, faɗa min meke a tsakaninki dashi.
Tana dariya tace"babu komai, shaƙuwace a tsakaninmu, baya son yaganni tare da wani idan ba ƴan uwanmu ba, haushi yake ji"
"Kice ƙwara in lalla6a in gudu, tunkan ya sauko don wannan har buguna zai Iyayi, " ya fada tare da damƙa mata pillow din hannun shi, Ya juya da sauri ya nufi ƙofar fita Yana faman sakin murmushi, bai ta6a ganin namiji mai kishi ba irin Danish.
Zukunnawa tayi ƙasa ta ɗauki ɗayan pillow, ta haɗa dana hannunta, ta nufi upstairs, Har tsoron tunkarar shi take Ji, saboda yadda ya kumbura fuska, soft red lips dinsa sunyi suntum da su" Koda ta haye up din, taga Ya dunƙule hannu kamar zai nausheta, wurga mashi pillows din tayi saman faffadan kirjinshi, da gudu ta sauko down tana tiƙar dariya, akan idonta ya tattara pillows din ya nufi dakinshi ya shige.
Yau da wuri suka yi breakfast dinsu, saboda gyaran jikin da ummi zatayi masu.
A Katafaren Home beauty station ɗin dake a cikin part dinsu, saboda su aka tadani komai na cikinsa, ɗakin Ya haɗu, bangon dakin beauty shelf ne An jera Kayan gyaran jiki kala kala, dana gyaran gashi acikin kowani shelf, hada foot care product and skin care product, Ga wani faskeken mirror a jikin bango, daga gabanshi wasu hadaddun kujerune kusan guda takwas, A saman kujerun kowa Ya samu wuri Ya zauna su shidda ne matan dake acikinsu, banda mazan tun bayan da suka kammala yin breakfast suka tafi ɗaukar karatu a inda suke Yin sallah. Suma matan acan za'a dinga yi masu karatu.
Kowaccensu tana sanye da bathrobe a jikinta, Ummi ce ta basu rigunan, saboda da taji daɗin gyara masu sumar kansu.
Kujerar farko Unaisah ce zaune asamanta, ta biyu batul ce akusa da ita, sai Parveen itama ta hakimce saman tata kujerar, daga gefenta Jemimah da Azeeza ne saman nasu kujerun bayan su sai Hannah.
sun natsu suna kallon faces dinsu ta cikin madubi sai faman sakar ma juna murmushi suke yi kamar wasu zautattu, daɗi suke ji za'a gyara masu sumar kansu, har sun fara imaginning din kyawun da zasuyi
babu mai magana acikin su, saboda ummi tana acikin dakin ta hanasu surutu
tana a sanye da dogon wando ƴar rigar data sanya daƙyar ta rufe cibinta, babu mayafi akanta.
"Dawa zamu fara" ta faɗa tana dubansu, har suna haɗa baki wurin furta Ni, "bari in za6a da kaina" ta fada tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, a ƙarshe ta tsayar da idonta Kan Unaisah da Batul, daku zan fara, saboda yawan sumar kanku" saukowa su ka yi daga saman kujerun, ta juya ta nufi Corner din da Sink Yake, gefen shi beauty cabinet ne mai ɗauke da jerin shampoo da conditioner da suran mayukan gyaran gashi.
Taci baƙar wahala wurin gyara masu gashi, musamman mutun biyun nan Unaisah da Batul, saboda yawan gashinsu ga tsawo, da ruwan zafi ta jika sumar bayan ta jiƙu ta shafa shampoo ta cuccuɗa ko'ina na gashin, bayan ta wanke shampoo din ta sanya conditioner na tsawon mintuna kafin ta wanketa, tayi masu amfani da Hair dryer ta busar masu da sumar kansu, ta fara shafa masu smoothing serum ta ɗauki comb taci gaba da sharce gashin, tunkafin ta kammala take santin kyawun sumar kansu, bayan ta gama sharce gashin ta kwarara masu hair oils kala daban daban saman sumar taci gaba da cuɗasu da hannuwanta, tuni gashin ya ciza launin shi dark brown sai ƙyalli yake yi da ɗaukar ido, ƙamshin hair oils din data shafa masu Ya cika hancinansu.
Lokacin da suka kalli sumar kansu ta cikin madubi, Ihun farin ciki suka saki suna faman yi mata godiya tace su koma zu zauna, bata gama gyara masu ba, su Azeeza sunyi zuru suna jiran suma ayi masu, sai faman santin su Unaisah da Batul suke Yi har suna fadin suma kalar nasu za'ayi masu.
Ummi tayi ƙoƙari wurin gyara su, Yara kamar ƴa'ƴan wani shege maiji da raina, saida tayi amfani da almakashi ta datse sumar kansu ta rage tsayinta ta dawo dai dai tsakiyar bayansu, hair style din da tayima Batul da Unaisah Triple twist half up ne, Bayan ta gama dasu ta bi sauran ɗaya bayan ɗaya ta wanke masu sumar kansu kamar yadda tayi masu Unaisah haka suma tayi masu banbancin wurin hair style ne, saida ta miƙar masu da gashinsu ta hanyar yin amfani da Straightener, kafin ta ɗaure ma Azeeza da Jemimah gashinsu da ribbom guda biyu gefe da gefe wutsiyar gashin ta sauko har saman kafaɗunsu.
Duk wannan gayun da akayi masu, Jemimah bata gode ba, ta sanya rigima akan sai an maida launin gashinta kalar nasu Batul, Ummi taci dariya, bata ta6a tsammanin zata ji ƙaunar yaran ba sai yau, su kansu sunyi mamakin yadda ta dage damtse wurin Yi masu hidima, Abu kamar wasa Jemimah ta fashe masu da kuka, ita damuwarta launin gashinsu Yafi nasu kyau, da ita da azeeza sumar kansu blonde ne kalar na turawa, ita Azeeza bata damu ba sai murna take yi an gyara mata gashi, jemimah daice ta matsa lamba, ummi harta fara tunanin ta canza mata launin gashin da yake suna da Hair dye cikin jerin Kayan gyaran gashin su, Unaisah ce tace abar mata launin gashin kanta, saboda yana dakyau ba lallaima idan aka maida mata kalar nasu yayi kyau ba," daƙyar suka lallashi Jamimah tadaina yi masu kuka.
Tsawon lokaci kafin Ummi ta kammala Gyara su, hatta skin dinsu da akaifunsu da tafukan ƙafafuwansu duk saida ta gyara masu, ko'ina ka kalla na jikinsu saiya burgeka, kamar basu ta6a shan wahalar rayuwa ba, tun bayan da aka gama kowannansu Ya koma bedroom dinshi, bacci mai nauyi ya dauke su, duk don saboda gyaran gashin da akayi masu kada Ya 6ace yasa suka kwanta ta rubda ciki.
*OBIE ESTATE*
Danƙara danƙara motocine masu numfashi suke ta kurɗaɗowa ta cikin babban gate din Obie Estate a ƙalla sunkai goma sha wani abu gaba da bayansu motocin fusatattun sojoji ne sun mimmiƙe tsaitsaye hannayensu ruƙe da manyan bindigu, jiniyar motocin jami'an ta karaɗe ko'ina na yankin, da matsakaicin gudu suka haura saman titin da zai sada da su da Airport, Motar farko zungureriya tana ɗauke da dattijon arziƙi tare da Dr.Jaz, mota ta biyu sanate president lateef ne zaune a mazaunin baya shi da Iyalansa Hajiya madina da ya'yan ta biyu Ziyad da zuhra, Mota ta uku Hajiya saratu ce a cikinta tare da twins zayn da zaid, da shi kanshi pravin din, Motar bayansu Sir mubarak ne tare da Hajiya Turai, daga motarsu sai ta sauran ƴan uwa da abokanan arziki da suka hallara domin zuwa tarban babban baƙonsu, kowan nan su yayi shiga ta alfarma, mazan cikinsu shaddojine ajikinsu, matan kuma wankan abaya suka ɗauka, har sun kusa isa Airport din ba zato ba tsammani suka soma hango wasu hamshaƙan motocin daban sun biyo ta titin da zai jagorance ka zuwa Aso Villa, Ƙarshen Haɗuwa ta glass din motocinsu suke hangen su, tunkafin suga su wanene acikin motocin ransu ya basu Mr.president ne tare da muƙarrabansa shima yazo tarban ɗan uwan nashi, abun yayi matuƙar ƙayatar dasu, basu yi tsammani zai halacci zuwa Airport din ba, zuwan bazata yai masu, Motocin shugaban ƙasa na ƙarasowa suka haɗe da nasu motocin Yawan adadin motocin suka ƙaru, hankalin kowannansu akwance yake sun ci burin haɗuwa da babban baƙon nasu, duk sun ƙagara su ƙarasa Airport din.
"Ziyad Ina fata baka faɗa ma Ƴan uwanka ƴan jarida ba ko"? Sanate lateef ne yai maganar a yayin da yake zaune gefen Hajiya madina a back seat na motarsu.
Ziyad na murmushi yace"ai daddy tuni na sanar dasu ku jura zuwansu kawai" Buɗe baki sanate yai"amma dai wasa kake min ko? Kadai san Kawun naka bai san taron ƴan jarida,"
Ziyad na sakin murmushin shaƙiyanci ya zuge mashi glass din motarsu, har sai da gaban Senate yadan buga ganin motocin ƴan jarida birjik sai faman sharara gudu suke yi har sunfi nasu motocin sauri duk dan su ƙarasa su dauki rahoto. Dafe kai Senate yai"ziyad kana da matsala, yanzu menene na gayyatar waɗannan mutanan ina amfanin yin hakan"?
Sai lokacin Hajiya madina ta sanya masu baki a maganarsu"ai indai ziyad ne dama ka daina damun kanka, ka riga da kasan halinshi, jikin shi har 6ari yake yi idan ya samu abun daukar rahoto"
Dariya ziyad yai jin abunda mommyn shi tace, shi dai senate lamarin ya ɗaure mashi kai.
Kusan atare motocin suka yi parking a wurin da aka tadana domin ajiye motoci, jami'an suka diddiro daga saman motocinsu suka soma bubbuɗe masu murfin motocin, ɗaya bayan ɗaya suke fitowa, Ƴan jaridan ma suka fito Hannayensu ruƙe da Cameras, wasu a wuya suka rataya cameran su, wasu kuma sun ruƙe welcome sign a hannun su duk da akwai tazara a tsakanin su saboda mugun tsaron dake wurin dan ma yan jarida ne masu naci da ba wanda ya isa ya tsaya a wurin.
Lokacin da Sharafudden Ya fito daga cikin Motarshi gaba ɗaya ido Ya dawo kanshi, mutumin babu wasa a fuskarshi, kamanninshi sak da mahaifinshi Obinna, launin fatarsu ne ba ɗayaba, Yana da hasken fata sai dai bai kai na Obie ba, nashi yadan yi duhu, fatarshi taji hutu, babban mutunne mai cikar kamala, ya iya dattako ga wadatar arziƙi, kusan duka halayan Owais shiya ɗauko babu abunda ya bari mashi, hatta kyawun fuskarshi na mahaifinshi ne, Yana da tsawo da fadin ƙirji, wankan suit ne a jikinshi, ya manna farin glass a idonshi, security detail din dake take mashi baya sunyi mashi rumfa, Cikin takun ƙasaita Ya nufi mahaifinshi dake ta faman aiko mashi da sakon murmushi, rungume juna sukayi, ƴan jarida kamar jira suke yi nan fa suka fara daukarsu hotuna, bubbuga bayanshi obie yai da hannun shi yana fadin"Nayi kewarka son, tsawon lokaci ka hanani ganinka sai yau, da yake ɗan uwanka zaizo yanzu zan dinga ganinka akai akai"dagowa yai da kanshi daƙyar yake murmushi kamar yana yi mashi wahala ya motsa baki ya furta"aymin afwa baba, kana araina koba dan shi ba, nayi niyar shigowa gidan yau saboda nayi kewarka" obie yaji dadin kalamanshi, da hannu ya nuna mashi sauran ƴan uwanshi, Jiki na rawa dr jazz da twins suka ƙaraso suna gaishe shi cikin girmamawa, ɗaya bayan ɗaya yake amsa masu, bayan sun kammala ƴan gaishe gaishen nasu, suka ɗunguma gaba ɗayansu suka shiga Arrival area din, duk Inda suka gifta ma'aikatan airport din sara masu suke yi, sau da ƙafa suke Yi masu biyayya, a katafaren waiting area kowannansu Ya samu wuri Ya zauna sun natsu suna jiran ƙarasowar jirgin baƙon nasu.
Jami'an suna a kewaye da su, Ƴan jaridan ma suna a tsaitsaye acen baya suna jiran Ya ƙaraso don su fara ɗaukar rahoto.
Vip Area din Ya cika maƙil da ɗaruruwan mutane wasu ma daga baya suka zo, Ko'ina ka kalla kawunan Bil'adama ne, kowanene wannan Babban baƙon daya tara dubban jama'a dake cike da ɗaukin ganinshi? lallai ba ƙaramin mai farin jini bane, shi ɗin na musamman ne.
Agogon bangon Nigeria Yana bugawa ƙarfe goma shabiyu adai dai wannan lokacin sautin katafaren jirgin shugaban ƙasar dake shawagi bisa sararin samaniya Ya karaɗe Kunnuwan mutane, gaba ɗaya ransu ya basu cewar jirginshi ne Hakan yasa su ka fara sakin murmushin farin ciki,
A katafaren Filin tashi da safkar jirage masu zaman kansu, Jet din ya sauka a hankali Yake bin runway har Ya ƙaraso dai dai Inda zai dakata, tsawon mintuna kafin ƙofar Jirgin ta buɗe matattakalar shi ta sauko ƙasa, hadadden red carpet, ma'aikatan airport din suka shimfiɗa mashi tun daga bakin stair din har izuwa entry din Vip area, mutanan dake aciki tuni sun mimmiƙe suna atsaitsaye curko curko suna jiran ƙarasowarshi.
Musamman Ƙungiyar masu daukar hoto da 'yan jarida sun Harzuƙa Jira suke kawai Ya duro da ƙafarshi waje don su fara haska shi da kyamarorinsu kowa burinshi ya kasance mutun na farko da zai fara ƙyalla mashi camera,
Jami'an sun kewaye Jirgin saboda su bashi tsaro, Maimakon mutumin da suke tsammani Ya fara saukowa sai suka ga Security detail dinshi Royal Canadian Mounted Polices suna fitowa daga cikin jirgin, zaratan Maza Ƙarfafa Masu Ƙira Irinta zakuna, Sanye Cikin kakinsu, Qugunansu a soke da bindigu Pistols, A bakin stairs ɗin Suka Tsaya sun haɗe da sojojin Nigeria dake a bakin jirgin.
Lokacin da Ya zuro ƙafarshi dake sanye cikin wasu hadaddun leather shoe Hankalin kowa ya dawo kanshi, tabarakallahu ahsanul khalikin, ƴan jarida har goga kafada suke Yi garin yin saurin haska shi da camera, A hankali Ya ƙarasa fitowa, Babban mutunne ya fito sanye Cikin tailored suit, sun zauna mashi, Sunbi shape ɗin Jikinshi, Fari ne Ba irin sosai ɗinnan ba, daga ganin fatarshi hutu ya zauna mashi, kanshi babu hula, Sai ka rantse da Allah matashin saurayi ne, saboda haɗuwarshi da iya ɗaukar wankanshi, sumar kanshi akwance take tasha gyara, tsakiyar gashin kan nashi akwai siraran hurhurar gado, da akayi gayu da ita, ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,Yana da tsayin fuska, Manyan idanuwa, ga dogon hanci, bakowa bane wannan face PRIME MINISTER HATEEM OBINNA! namijin zaki uban dawa, ɗaya tamkar da dubu, gwarzon Namiji mai ɗauke da suffofin jagwaranci, mutun mai daraja da ƙima a idon al'umma. yana da farin jini ba Iya kasarshi ba a ƙasashe da dama rububin shi suke Yi saboda kyawawan ɗabi'unshi da halayanshi, mutumin maƙurane a 6angaren Kyau, ilmin addini dana zamani, uwa uba Ya fito daga babban Gida, kallo ɗaya zakayi mashi ka shaida ruwa biyune, gashi Hamshaƙin Mai kuɗi Ya shahara Aduniya.
Cikin dattako Yake taka matakalar benan, All eyes on him mutanen dake can nesa suna hangenshi kamar zasu ƙetare Iyakarsu su faɗo gabanshi donsu Tarbe shi, Fitowarshi Keda Wuya Uwar Gidan shi Gimbiya Mujeedat ta sauko daga cikin jirgin, nan fa kallo Ya koma Kanta, Hankalin maza ya tashi, Ko mace ta kalleta saita girgiza balle Namiji, ahaka ma ta sanya Arab gown launin fara ajikinta, Ta rufe fuskarta da Niqab, dirin Jikinta Yafi komai jan hankali, da kuma kyawawan idanuwanta da suka bayyana sun sha uban ado farare ƙyal, price din takalman ƙafarta kaɗai sun ishi wani talakan jari, hatta hannayanta Safa ce ta sanya, Mijinta yana matuƙar jin kishinta shiyasa duk inda zasuje da niƙab a fuskarta, bayan ta fito, matasan ƴa'ƴansu biyu suka fito tare da Faryat ƴar gidan saratu, sunyi shiga kala ɗaya data mahaifiyarsu dukansu matane, dogaye masu kyan sura, atare dasu akwai advisors dinsa, manyan mutane masu bashi shawara, sun hada da chief of staff, national security advisor, Fararen turawa sun ɗauki wankan black suit, kowan nan su ya manna sunglases a idanuwanshi, ajere suke taka shimfiɗaɗɗan red carpet din da zai jagorance su zuwa Vip arrival area, lokacin da suka karasa jama'a kamar zasu haɗiyesu tsabar murnan ganinsu, Bawan Allah bai nufi kowa ba sai Mahaifinshi Obinna, Hannu bibbiyu ya rungume shi ajikinshi, tsawon shekara basu ganaba sai yau da Allah Ya nufa zai samu damar zuwa Nigeria, Wata irin runguma yayi ma Obinna, gaba daya mutane suka sanya ihu suna tafa masu, Ƴan jarida Sun dage sai daukarsu hoto suke Yi, sautin ƙarar kyamarorinsu ya cika airport din ji kake kyat kyat, Gimbiya Mujeedat, da fara'a akan fuskarta ta rungume Hajiya saratu, kamar ƴan uwan juna, Faryat kuwa da gudu ta faɗa jikin Zayn tana dariya, bayan ta rungume shi ta kuma rungume Zaid, sai daɗi take ji taga ƴan uwanta, Nazli da Yazrin kuwa kamar basu son ganin mutane, dama suna da wuyar sha'ani har ƙwara Yazrin tafi sakin fuska akan Ƴar uwarta nazli, daƙyar suke rungumar ƴan uwan mahaifinsu, izzace ta bala'e suke fama da ita, su ala dole ga jinin sarautar daular larabawa, Bayan prime minister Ya saki mahaifinshi, Ya rungume ya'yanshi sharafudden kamar zasu koma mutun ɗaya tsabar yadda suka hade jikinsu. Tuni ƙwalla ta cicciko tab a idanuwansu, daƙyar suke yima juna magana, ɗaya bayan daya saida yabi ƴan uwanshi ya rungumesu, kafin ya soma gaisawa da sauran manyan mutanan da suka zo tarbarshi, yaji dadin ganin daruruwan al'ummar da suka taru domin shi, wannan abun farin ciki ne, Obie ne yai mashi magana akan Yan jaridan da ke son yin magana da shi, A hankali yake bin welcome sign din dake a ruƙe a hannunsu.
Rubutun dake ajiki ya soma karantawa acikin zuciyarshi kamar haka
_The entire country of Nigeria, welcomes Prime Minister Obinna with open arms!_
_A very special welcome to Prime Minister Hateem Obinna, on behalf of the entire nation!_
_- Prime Minister Hateem Obinna, we are delighted to have you in our country!_
_We're happy to extend a sincere and heartfelt welcome to Prime Minister Hateem Obinna!_
Ƙayataccen murmushine ya bayyana akan fuskarshi, ƙwallar da yake 6oyewa baisan sa'adda ta soma gangarowa saman kuncinsa, farin cikine Ya cikashi, yaji dadin kyakkyawar tarbar daya samu, mintuna ƙalilan yayi jawabi ma ƴan jarida yayi masu godiya da irin tarbar da suka yi mashi
Daga bisani Jami'an dake bashi tsaro suka yi mashi ƙawanya da iyalinshi zuwa wurin da aka tanadar masu da jigunannun motocin da zasu yi jigila da su, bayan kowan nan su ya shiga cikin mota, kusan atare drivers din dake tukasu suka tada su, A hankali suke driving dinsu zuwa hanyar komawa Obie estate.
Duk inda suka gifta Jiniyar motocinsu ya karaɗe ko'ina, cikin ƙanƙanin lokaci suka ƙaraso Cikin estate din, a harabar ajiye motocinsu suka yi parking, gaba ɗaya kowa ya futo suka dunguma zuwa cikin katafaren falon gidan, Jami'an da yazo dasu tuni an ware masu part din da zasu zauna a babban masaukin baƙin gidan, haka zalika advisors dinshi suma An basu nasu Yankin da zasu zauna, bajimawa zasuyi a kasar ba, Ƴan kwanaki ne zasuyi kafin su koma Canada, masu aikin gidan sai safa da marwa suke Yi wurin kai masu kayan abincin da aka shirya masu, idan zasu gaisa da mutane harshen turanci suke Yi, har yaren french suna jin shi sosai, Gimbiya mujeedat kuma Tafi jin larabci da turanci, haka ƴa'ƴanta ma hausa wahala take yi masu, faryat dai ce ta ƙware wurin yin hausa sai turanci, Prime minster ma Yana jin harshen hausa amma yafi ƙwarewa wurin Iya yaren mahaifiyarshi turanci da faransanci, sai spanish.
Yinin Ranar gidan Ya cika maƙil da jami'ae, sojoji da ƴan sanda, sun kewaye ko'ina na sashen Estate din, tsaron gidan Ya ƙaru, Kafin mutun ya samu damar shiga estate din sai sun tantance shi da na'ura daga kasa har sama zasu bincike shi kafin ya samu damar ƙarasawa ciki, babu mahalukin daya isa Ya shiga gidan koya fita lami lafiya batare da jami'ae sun cacike shi ba, tun karfe ɗaya na rana Ƴan uwa da abokanan arziki suke ta taruwa domin Yima baki barka da zuwa.