Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 53
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 53: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 53. Wuraren ƙarfe huɗu Na marece, Lokacin mutane sun…
3,367 words
Wuraren ƙarfe huɗu Na marece, Lokacin mutane sun ɗan ragu, motocin ma'aikan Companyn su Zahra suka ƙaraso Estete din, basu ta6a ganin tashin hankali irin na yau ba, sun girgiza da ganin jami'ae a kewaye da estate din, Zahra Sarkin tsoro duk tasha jinin Jikinta, Kafin abasu damar shiga estate ɗin saida jami'ae suka basu umarnin su fito daga cikin motocinsu, ɗaya bayan ɗaya suka firfito matasan ƴan mata Ansha gayu, daga ƙasa har sama jami'an suka bincikesu hatta kayan decoration din da suka zo da su a mota. Saida suka duddubasu suka tabbatar babu makami ko wani abun cutarwa tukunna suka basu iznin shiga cikin gidan.
Da taimakon Hajiya saratu suka ƙarasa 6angaren da zasu fara aikin nasu, saida aka fara tarbarsu da lafiyayyan abinci suka cika cikunansu tukunna suka fara aikin tsara decoration din, acikin wani katafaren ɗakin taro dake acikin gidan suka hallara gaba ɗayansu interior designers din, Zahra da fatima sune gwanaye basu aiki sai dai su nuna ma sauran matasan ƴan matan yadda zasu tsara kayan adon suyi kyau, kasancewarsu ƙwararru a fagen Iya decoration tuni wurin Ya fara ɗaukar ido Ko'ina ka kalla kayan adone ke kyalkyali da walƙiya kamar zasu kashe idon bil'adama.
*CHIEF OWAIS✊❤*
Wuraren ƙarfe takwas na dare, Ya fito daga bedroom dinsa, har yayi shirin kwanciya bacci, sleeping dress ne a jikinshi launin sky blue, rigar tabi shape din broad chest dinsa, ta bayyana strong arms dinsa, walking gently ya nufi bakin handrail, Ya ɗaura faffaɗan tafin hannunsa asaman shi, A hankali yake buɗe kyawawan idanuwanshi Yana ƙare ma ko'ina na downstairs da kallo, tun da ya diro nigeria har Yau bai leƙa cikin estate dinsu ba, kuma babu wanda yasan da zuwanshi, ni'imtacciyar iskar wurin Ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya take yi ba, abubuwa da dama sunayi mashi yawo acikin kanshi.
"Barka da fitowa yalla6ai" muryar Big guy ce ta katse mashi tunanin shi, Yana daga tsaye gefen shi, Ba tare daya juya ya kalle shi ba, Ya amsa mashi da yawwa. Cikin girmamawa yace"yalla6ai ina fata kana lafiya" ya tambaya ne don ganin yanayin daya fito daga daki cikin shiga ta kayan bacci.
"I need coffee" abunda ya furta mashi kenan maimakon amsar tambayar da yai mashi.
Da sauri big guy ya juya domin ya kawo mashi abunda yake buƙata.
Badajimawa ba sai gashi ya dawo hannunshi ruke da Mug sai tiriri coffeee din Yake yi, Ya miƙa mashi bayan ya kar6a, sai da ya ɗauki lokacin kafin Ya fara kur6ar shi.
"Yalla6ai yaushe zamu shiga cikin gida ne"? Tamkar bazai amsa mashi ba Ya furta"tomorrow"Jinjina kai Big guy yai kafin ya kuma cewa"Yau kawunka na ƙasar kanada ya shigo ƙasar bansani ba ko ka gani a labarai" Yamutsa fuska yai da alama surutun big guy ya fara takura shi, daƙyar ya furta"Nasani"
Gyaɗa kai big guy yai"bari nabarka ka huta yalla6ai, mu kwana lafiya" ya amsa mashi da okey. Juyawa yai da sauri Ya nufi down stairs. Yana cikin shan coffee dinshi, yayin da yake bin ko'ina da kallo, Karaf idanuwanshi suka sauka Akan Danish dake ƙoƙarin fitowa daga ɗakin shi, Ya zuba hannayenshi cikin short pockets dinsa, damuwar duniya ta isheshi, Ya kasa runtsawa, saboda rashin ganin unaisah, tun ɗazu yake jiran zuwanta bata leƙo ɗakinsa ba, shi kuma bai Iya takawa yaje ɗakinsu, Kamar anyi mashi Iyaka da shiga, ko falo bai Iya zuwa idan ba Angel ta janyo shi ba, rashin sabone ke damunshi, kasancewar suna fuskantar juna hakan ya bashi damar ganin shi da kyau, duk da akwai tazara a tsakaninsu, dukansu suna a second floor na bene.
Kamar yadda Owais Ya jingina da handrail haka shima Danish ya ɗaura gwiwowin hannunsa saman handrail, da farko bai lura da shi ba, sai da ya wurga eye balls dinsa saitin inda yake fuskanta tukunna suka yi tozali da juna, ɗaure fuska danish yai, tunkafin ma yasan wanene shi yaji baiyi mashi ba saboda shi baya ƙaunar yaga Namiji idan har ba cikin ƴan uwansu maza ba, duk don saboda Babe Unaisah dinshi, yaji haushi ɗazu da asuba dayaga wani ƙato Ya rungumeta, har zazza6i saida ya lullu6e shi, ko abincin dinner dinshi baici ba, yaso ace Ya damƙeta da babu abun da zai hana ta yabama aya zaƙinta.
Chief Ya natsu yana kallon shi, abun da ya ɗan bashi mamaki Da yaron girman jikinshi, saboda yasan shekarunshi da sojoji suka faɗa mashi a bayanin da Gabriel Ya basu, bai wuci 20 years ba.
Tsawon mintuna suna kallon kallo a tsakaninsu, kafin daga bisani chief Ya juya mashi baya ya nufi bedroom dinsa ya shige, saukowa down Yai cikin sanɗa yake yin tafiya yana neman room dinsu Unaisah, ya rasa ta wace hanya zaibi ya gano ɗakinsu.
Firgita yai sakamakon Jin hannun mutun saman Bayanshi, abunka ga mai ji da ƙarfi, yayi tunanin wani ne zai cutar dashi, aiko ya damƙo hannun mutumin da niyar ya wurgo shi ƙasa sai kuma Ya fasa, Ya juya a hankali don ganin wanene, Boss man ne atsaye hannunshi ruƙe da Backpack din unaisa, Da mamaki akan fuskarshi yace"Sannu Iliya ɗan mai karfi, au da buguna zakayi daga kawai na dafa kafaɗarka? Haka ɗazu da safe ka dinga jifana da pillow saboda na rungume ƴar uwarka ko"? Cikin jin kunyar maganarshi Danish ya sadda kanshi ƙasa, ba tare daya furta komai na.
Murmushi boss man ya saki tare da miƙa mashi backpack din hannun shi"kar6i nan, ka kaima Masoyiyar taka Unaisah kace inji boss man, ta duba cikin aljihun jakar zata ga sabon sim dana sanya mata"
Hannu yasa ya kar6i backpack din, daƙyar ya iya furta mashi thank, kafin ya juya yanufi inda yake tunanin zai samu ɗakinsu.
Boss Man yana atsaye yana bin bayanshi da kallo, Har ya 6ace ma ganin shi kafin Ya juya ya nufi ƙofar fita.
Yayin da Danish keta faman neman ɗakinsu Angel, tana acan cikin toilet gaban madubi, daga zuwa Yin uziri taci karo da abun arziƙi a kirjinta, Duk tabi ta ruɗe ta rasa ina zata tsoma ranta don farin ciki, batasan yaushe breast suka fara fito mata ba, bata ta6a lura ba sai yau data tsaya gaban madubi tana bin jikinta da kallon ƙurulla, guntuwar rigar bacci ce a jikinta, Daƙyar ta rufe gwiwarta, sai faman ɗaɗɗage rigar take Yi tana ƙara leƙensu, sunyi ƙananu dasu basu fara nuna ba, kamar wadda akayi ma albishiri da gidan Aljanna sai faman sakin murmushi take Yi, itama yau irin abin ƴar gidan daddy sun fara fito mata, taci alwashin bazata bari Danish yagansu ba, sai sun ƙara girma sunkai kamar na unaiza tukunna, da gudu ta fito daga toilet ta nufi closet dinsu ta buɗe ta dauko ƙaramin mayafi ta koma cikin toilet, ta tu6e wuyan rigar, ta ɗaure kirjinta tamau da mayafin kafin ta maida wuyan rigar tana faɗin"Allah na gode maka, nan bada jimawa ba nima zan zama budurwa"
Duk wannan haukan da takeyi, batul tana akwance saman gadonsu, tayi nisa acikin baccinta, Adai dai lokacin zata fito daga toilet din tana zuro ƙafarta, tayi arba da danish tsaye bakin ƙofar dakin, Hannun shi ruƙe da backpack, Sai faman baza ido Yake yi don ya ganota, daƙyar ya samu ya gane dakin nasu, Jin motsin mutun yasa shi yin saurin ɗaura idonshi akan fuskarta, ido cikin ido suke kallon juna, wani abu daya ɗaure mashi kai, shu'umin murmushin daya gani kwance saman la66anta, hada ruƙe qugu da hannu ɗaya.
❤EX-PRISONERS❤
Sam ya kasa ƙarasawa gare ta, slowly yake bin jikinta da kallo, tun daga kan fararen ƙafafuwanta har izuwa saman gwiwowinta da suka kasance jawur da su kamar bata ta6a yin rarrafe ba, ɗagowa yai da eye balls dinsa zuwa saman Waist dinta da ya faɗaɗa, ganin irin mayataccen kallon da yake binta dashi ne yasa ta juya da gudu ta nufi can cikin dakin wurin closet dinsu, har sai da yaji gabanshi yaɗan faɗi lokacin data watsa da gudun mazannanta suka girgiza rigar ta bayyana shape dinsu, yawu ya haɗiya adam's apple dinsa Ya motsa sama da ƙasa.
Yaɗan ji shock ganin baƙon al'amari ajikin Babe unaisah dinshi, bai ta6a ganin girmanta ba sai yau da yai tozali da ita cikin short gown, Kayan arzuƙa sun fara ha66aka.
Cikin sanɗa take tafiya tana tunkaroshi, idanuwanshi akan fuskarta, still shu'umin murmushin nan take sakar mashi, hatta Yanayin tafiyarta ya canza, dogon wandon bacci ta zura a jikinta duk don Ya daina kallon mata jikinta. Dab dashi ta tsaya tana duban backpack din hannunshi, har cikin ranta taji dadin ganin jakar, daɗi kamar zai kasheta, haɗa ido sukayi da shi, mutumin duk ya susuce kamar wanda aka zare ma laka, sam babu kuzari a jikinshi tunda yai arba da hips dinta.
Harara ta jefa mashi haɗi da murguɗa mashi soft pink lips dinta, muryarta da shagwa6a tace"kallon ya isa haka, bani jakar nagode" ta faɗa tana ƙoƙarin ruƙo hannun backpack din, da sauri ya ƙanƙameta a wide chest dinshi, alamar bazai bata ba, ɗaure mashi fuska tai"wai meye haka? Baka ga dare yayi ba, yakamata kaje ka kwanta, ni bansan ma ya akai boss man ya baka back pack din ba, ai daya sani shiya kawo min da kanshi" bada wata manufa ta furta maganar ba, amma da yake jarabar kishi ce dashi, sai yaji kamar tana nufin tafi son ganin boss man akanshi shiyasa tace haka, aikuwa nan take Ya haɗe rai, babu annuri ko misƙala zarratin, ganin ya fusata yasa tace"meye faru my man"? Wurgar mata da jakar Yai ƙasa, da sauri Ya juya Ya nufi ƙofar fita kamar zaiyi tuntu6e, Jiki na rawa tabi bayanshi tana ambaton sunanshi"My man! Dan Allah ka tsaya muyi magana, Ni ce na bata maka rai ko? Pls am sorry bazan ƙara ba, Ka yafe ni pls, bazan Iya bacci kana fushi dani ba"
Har ya kusa fucewa daga ɗakin, Can kuma sai ya dakata kamar mai tunanin wani abu, Ba zato ba tsammani taga ya juyo a sukwane, ƙiris Ya rage ta hade kirjinta da nashi, gadan gadan Ya tunkarota hakan da yai ba ƙaramin tsoro yaso ya bata ba, Juya tayi da niyar ta faɗa toilet, ta 6oye sai dai kafin ta kai ga shiga taji Ya damƙi waist dinta da ƙarfi Ya ɗaga ta sama kamar ɗiyar roba, tadinga ihu tana fadin Am sorry my man dan Allah kada ka 6alla ni"
Batul dake a kwance tana sharar bacci, koke koken Angel ya fara takura mata sai faman mutsu mutsu take Yi alamar zata farka.
ya tsareta da reddish eyes dinsa da launinsu Ya ciza tamar zallar red, da kakkausar murya ya furta"meyasa kike son 6ata min rai"? Ya fada batare daya sauke ta ƙasa ba, Jikinta na kerma tana faman wutsil Wutsil da ƴan ƙafafuwanta tace"danish dan Allah ka ƙyaleni, kaga Batul dake bacci tafara takura da surutunmu, kuma ni bansan laifin me nayi maka ba, amma ina baka haƙuri ka tafi ɗaki ka kwanta"
Ta6e la66ansa Yai alamar bai damu ba, kafin ya sassauto da Voice dinsa"Kin hana zuciyata sakat, tunda safe da kika rungume ƙaton nan Hankalina ba akwance yake ba, nakasa samun sukuni, ni kaɗai nasan irin raɗaɗin da nake ji, ke ko ajikinki, baki leƙo dakina kin duba halin da nake aciki ba,saboda ke banci dinner dina ba, baki damu dani ba, ko nema na bakiyi ba, saboda kin samu wanda yafi ni ko"
Runtse idanuwanta taɗanyi, hadi da dafe kai da hannu ɗaya, dama saida ranta ya bata bazai ƙyaleta ba, saboda jarabar kishinshi, shiyasa yau ta hana shi ganinta, duk dan ta tsira daga fushin shi.
Shirun da tayi mashine Ya ƙara 6ata mashi rai, Baisan sa'adda Yai zazzafan taku Ya nufi Saman shimfidedan gadonsu, Ya jefar da ita Ta faɗa saman lallusar mattress din, da sauri ta juyar da jikinta tai kwanciyar rubda ciki, gudun kada Gyaran gashin da akayi mata ya tarwatse, Cikin shessheƙar kukan ƙarya Take Fadin"Nifa bada son raina ya rungume ni ba, Hijab din jikina ce ta taɗiyoni na tafi zan kife ƙasa shine Ya tarbeni na faɗa chest dinsa, kaima ka sani bani marmarin kasancewa da wani ɗa namiji idan bakai ba, dan Allah kadaina tayar da hankalinka akaina, saboda Ni taka ce kai kaɗai, shi mutumin ma da kake Yin kishi akanshi babbane ba matashi ba, Ya isa ya haifemu nida kai"
Tun da ta fara yin magana, Ya rasa sukunin shi, Gyaran gashinta Yai matuƙar jan hankalin shi, kamar princess, twisting din da akayi mata guda biyu saman gashin ya ƙara mata kyau, sam bata ji motsinshi ba, ta dage sai haƙuri Take bashi, jin hucin numfashinsa a jikinta Yasa tai wuff Ta juyo Tana fuskantar shi, har saida gabanta Yaɗan fadi ganin Yadda yai mata rumfa, tuni tasha jinin jikinta, muryarta na rawa ta furta"meye haka" Lumshe mata ido yai tare da waresu saman fuskarta, abun ya ɗaure mata kai, Yana neman ya rikitar da ita. Ganin dagaske kamar wani abu yake so yai matane yasa ta fara canza mashi fuska, zuwa ainihin true colour dinta, runtse ido tai da masifa tace"danish ka tashi ka tafi ɗaki, wallahi kada ka bari na buɗe ido na ganka ranka zai Iya 6aci" saida ta gama zazzaga mashi faɗan ta buɗe ido a hankali don taga idan ya tafi, ko gizau baiyi ba yana nan yadda yake, Cikin zafin nama ta daddage ta ɗaura hannayenta saman ƙirjinshi da niyar ta ingije shi, sai dai takasa yin hakan sakamakon wani abu daya tayar mata hankali, a ruɗe take kallon shi ayayin da take kokarin mikewa zaune ta jingina bayanta jikin headboard na gadon, Cikin sanyin murya ta furta sunanshi"My man"
Idanuwanshi tuni sun fara canza launi, numfashinshi na fita da huci hucin zafi.
"Faɗamin meke damunka? Baka da lafiyane? Meyasa naji zafi ajikinka"? Da wata irin kasala Ya kwantar da kanshi saman mattress dinsu, kasancewar Gadon Yana da fadi Batul tana daga can 6angare guda. "Kayi shiru baka bani amsa ba, kasan bana so Ina magana kana shareni," Daƙyar Ya iya buɗe baki Ya furta"am sorry idan na 6ata maki rai, yanzu zan tafi na kwanta" ya ambaci hakan tare da miƙewa ya sauko daga saman gadon, da sauri ta biyo bayanshi tana ƙwala mashi kira, sai dai kafin ta isa gare shi, tuni Ya fuce daga ɗakin, ƙofar tayi locking, kwantar da kanta tayi saman glass door Din, Jikinta yai mugun yin sanyi, hankalinta Ya tashi ssai, ta girgiza da jin zafin jikinshi tamkar hucin garwashin huta, taya zata iya runtsawa bayan bata da masaniya akan halin da yake aciki? Gashi ya faɗa mata baici dinner ba duk don saboda da ita! Ruwan hawaye ne suka taru acikin idonta, da sauri ta juya tana duban hadaddiyar wall clock din dakin ƙarfe 10 na dare, badan taso ba ta haƙura da bin bayanshi amma taci alwashin da asuba zata je ta dubashi, kamar yadda taga rana haka taga dare, bacci ya ƙaurace ma idanuwanta, sai faman juyi take Yi saman gadonsu, duk ta takura kanta ta hana zuciyarta sakat.
*FRIDAY MORNING🥳💃💃💃*
Bayan tasowa daga sallar asuba, dattijon arziƙi Ya nufi Sashen da bedroom dinsa Yake hannun shi ruƙe da sanda, Farar Jallabiyace a jikinshi, lokacin daya ƙarasa bedroom dinshi, da sandar hannun shi Ya tura ƙofar shigar shi keda Wuya kafin ƙyaftawar ido Hasken ɗakin Ya ɗauke, duhu Ya mamaye idanuwanshi, Abunka ga tsoho duk Yabi ya ruɗe, muryarshi Adabarbace yake fadin"subhanallah, Waye ya kashe min hasken ɗaki? jazz bana son shaƙiyanci nasan kai kaɗaine zaka Iya min haka? Wai jazz baka ji Ina magana" ya fada Yana cigaba da yin tafiya cikin duhu, Ya daura hannu ɗaya jikin bango Yana laluban Switch don Ya kunna hasken dakin, Cikin 6acin rai Yake Fadin"Jazz wallahi kada ka bari in kunna hasken ɗakin nan, ranka zai 6acine, wato raini Ya fara shiga tsakanina dakai shiyasa har kake Yi min shegantaka ko"?
Daƙyar Ya samu Ya shafo switch din, a harzuƙe Ya danna button din, A hankali Hasken ɗakin Ya soma gauraye ko'ina, tamkar da rana, Juyawar da zaiyi unexpected Yaga abunda Ya bashi mamaki da al'ajabi, wato gaba ɗaya furannine launin ja da yellow tun daga saman head boad har izuwa saman zanin gadonshi, An ƙawatasu masu kyan gaske har ƙyalli suke Yi, tamkar a mafarki Yake kallon ikon Allah, A hankali yake dogara sandarshi Yana tunkarar gadon tamkar maijin tsoronshi, saida Ya matso kusa Ya ƙura ido Yana so ya gane rubutun me akayi da furannin, karantawa yai
*"HAPPY 80TH BIRTHDAY TO OUR BACKBONE"*
Lokaci daya ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya, Farin ciki mara misaltuwa ya lullu6e shi, Sai faman sakin murmushi yake yi kamar wani zautacce, daga end bed din Ya zauna, Yana ƙarewa furannin kallo, ranshi yana bashi cewar ƴa'ƴanshine suka shirya mashi furannin, tabbas sune, Yayi mamaki babu wanda ya sanar dashi zasuyi mashi hakan, Kuma atare dasu ya dawo daga masallaci, tun a babban falon gidan suka rabu da juna kowa ya kama hanyar part dinsa.
Yayin da yake bin adon furannin da kallo, cikin sa'a idanuwanshi suka yi mashi tozali da birthday cards birjik aka ajiye mashi don Ya karanta, kusan guda bakwai daga saman kowani card an ɗaura fure, hayewa yai saman gadon har zuwa gaban cards din Ya ɗago dasu a hannunshi kowanne yana da tittle dinsa da kuma sunan mamallakinsa, Card din farko Sunan senate lateef ne, buɗewa yai ya soma karantawa kamar haka.
_"To my dear father, thank you for always being there for me, guiding me, and making me the person I am today. Your support, love, and encouragement have made me who I am, and I'm so grateful for that"_
tuni idanuwanshi sun cicciko da ƙwallar farin ciki, Ajiye card din lateef yai, ya buɗe card na biyu mallakin Sir mubarak Yana duban sakon cikin shi
_"From the bottom of my heart, I want to wish you a very happy birthday, Dad! Your wisdom, kindness, and sense of humor have always brightened my days" annurin fuskarshi sai ƙara nunkuwa yake Yi, haƙiƙa sunyi matuƙar faranta mashi da daɗaɗan kalamansu, Yana matuƙar ƙaunar ƴa'ƴanshi.
Ajiye card din sir mubarak Yai, ya buɗe Na Sharafuddeen calmly ya ke reading dinsa "Happy birthday, Dad! You are the best father in the world and we are so lucky to have you. May your day be filled with happiness and love." hawayen da suka taru acikin idanuwanshi tuni sun jiƙa fuskarshi, sumbatar card din Yai, kafin Ya daura shi saman wadanda ya karanta, Ya duba sakon Prime minister
_"I'm so glad to have a father like you, who has been a rock of support through the ups and downs of life. You've always encouraged me to be the best I can be, and that means the world to me. On this special day, I just want to say thank you for everything you've done for me. Happy birthday Baba tsoho much love"_
Dariya ya saki har fararen haƙoranshi suka Bayyana, Kalmar ƙarshe ta saƙon Hateem ne Ya bashi dariya daya ce baba tsoho. Lumshe idanuwanshi yaɗanyi yayin hawaye ke cigaba da wanke fuskarshi, abu ɗaya ne yake fargaba a duniyar nan ranar da zai barta saboda ƴa'ƴanshi, bai sani ba tsakanin shi da su wanene gawar fari, bai fata ma Wani daga cikinsu Ya riga shi tafiya, bazai Iya jurar rashinsu ba, Ya ƙwammace mutuwa tafara Yin awon gaba dashi.
Sumbatar card din Hateem Yai, kafin Ya buɗe na saratu
- On this special day, I want to let you know how much I appreciate everything you've done for me, Dad. You've always been my biggest fan and supporter, and I can't thank you enough for that. Wishing you a very happy birthday, with lots of love My Baba, Allah yabarmun kai, madubin dubawata" manna ma card din kiss Yai kafin Ya duba na sauran ƴa'ƴan nashi, waɗanda basu kaiga ƙarasowa Gidan ba, suma sun bada saƙon da aka rubuta masu a cards dinsu.
Farin cikin duniya ya cika Obie, kwanciya yai saman furannin idanuwanshi na fuskantar ceilling. Ba zato ba tsammani Yajiyo sautin muryoyinsu acikin kunnuwanshi, Suna faɗin"Happy Birthday To You, Happy birthday to You, Happy birthday to our Baba" zumbur Obinna Ya yunƙura ya miƙe daga saman gadon Yana duban ƙofar room dinshi. Dr. jazz ne Ya fara shigowa hannunshi ruƙe da madaidaicin Cake mai hawa huɗu daga saman shi an jera candle, ga cake knife gefe ɗaya.