Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 54
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 54: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 54. Shigowar dr.jazz ke da Wuya, Manyan ƴa'ƴan shi…
2,944 words
Shigowar dr.jazz ke da Wuya, Manyan ƴa'ƴan shi suke shigo ajere kowannansu sanye da hadaddun jallabiyoyi, Mutun Na farko Sir mubarak ne daga bayanshi Senate lafeef ne, wanda ke abiye dashi His excellency Abdul Razak ne Gomnan Jihar lagos, baisan Yaushe Suka shigo garin abuja ba, Yayi mamakin ganinsu, zuwan bazata suka yi mashi, ga kuma His excellency Deen Obinna Na jihar kaduna state, Daga bayanshi mai girma sharafudden Obinna ne, Hannun shi ruƙe dana ɗan uwanshi Prime minister hateem obinna, abun gwanin ban sha'awa, bayansu sai Saratu data shigo itama jallabiyarce a jikinta ta yafa mayafi akanta, Fuskar kowannansu ɗauke da annurin farin ciki, maimakon Ya taso Ya karaso garesu, sai kawai su ka ga ya fashe da kuka, haɗi da sanya tafukan hannayenshi biyu Ya rufe fuskarshi.
Jikinsu duk Yai sanyi, duk da ransu yana basu cewar kukan farin Cikine Ya ke yi, gefe da gefen gadon kowan nan su ya zauna kamar masu neman gafara, Senate lateef Ne Ya fara magana "Baba meyasa ka yin kuka? Dan Allah kada ka karya mana zuciyoyin mu, munci burin mu faranta maka a wannan ranar mai albarka rana mafi daraja agaremu, ranar da abun alfaharinmu Yazo duniya" ta tsakankanin yatsun hannunshi Yake satar kallonsu, Muryar saratu da shagwa6a tace"baba please kadaina wallahi bamu jin daɗin ganin hawayenka masu tsada suna zuba ƙasa" "Baba idan baka daina kukan nan ba, muma zamu fara" acewar Sir mubarak Mr.president sharafudden Yace"Daddy ka bamu dama mu share maka hawayenka da hannayenmu please" His excellency Deen Ya kar6e da cewa"daddy saboda kai, muka kamo hanya tunda duku duku muka shigo abuja, saboda muhimmancinka agare mu, dan Allah ka buɗe fuskarka ko mun samu damar ganinka, munyi kewar mahaifinmu" kalamansu ba ƙaramin karya mashi zuciya suke Yi ba, sai dai yakasa cire takufan hannayenshi daga saman fuskarshi, Allahu akhbar, wato Iyaye dabanne, duk mun muƙamin mutun shi bakomai bane agaban Iyayenshi, gaba ɗayansu nan manyan mutanene masu ruƙe da manyan muƙaman ƙasa, masu ƙima da daraja a idon duniya, Yau gasu zazzaune gefen gadon mahaifinsu, sun tasa shi agaba suna lallashinshi, abun da yake ƙara haddasa mashi jin ƙaunarsu Biyayyar da suke yi mashi, tun suna ƙanana har zuwa girmansu bai ta6a danasanin kasancewarsu a matsayin ƴa'ƴanshi ba, basu ta6a sanyashi ciwon kai ba, samun ƴa'ƴa nagartattu irinsu abune mai wuya a zamanin nan, damuwarshi tasu ce, suna matuƙar ji dashi suna gatanta shi suna kyautata mashi shiyasa suke damun cigaba arayuwarsu saboda albarkar dayake sanya masu. Muryar His excellency deen Ce Ta katse mashi tunaninshi "Baba munji kayi shuru baka ce komai ba, Idan akwai abunda ke damunka please Ka faɗa mana, baka da tamkar mu a duniyar nan, ashirye muke da mu share maka hawayenka" da zolaya Sir mubarak Ya dubi jazz"faɗamin gaskiya kodai kaine ka 6ata mashi rai"? Jazz na murmushi yace"wallahi bani bane..." daƙyar ya ƙare maganar ganin irin kallon tsiyar da hajiya saratu take watsa mashi, Muryarta a kausashe tace"tunda ka kawo cake din miƙo min shi ka fuce kabamu wuri," Jiki asanyaye Jazz Ya nufeta Ya miƙa mata tray din, Tasa hannu ta ƙarba tana faman jifarshi da harara, sam bayason barin Ɗakin, idan Yana atare da su ji yake kamar Yana acikin danginshi mantawa yake yi da shi bakowa bane a family dinsu. Har Ya juya zai fuce Muryar Hateem ta dakatar dashi"Zonan jazz" dakatawa yai dayin tafiyar da sauri Ya koma gaban gadon, Hateem Ya sanya hannu ya kar6i cake din hannun saratu Ya miƙa mashi"kamar yadda ka kawo shi kai nake so ka fara bashi" ɗaure fuska hajiya saratu tayi badan tana jin shakkar Yaya hateem ba da kuwa babu abunda zaisa ta bashi cake din, bawan Allah Jazz sai faman sakin murmushi yake yi, ya kar6a Yana fadin"nagode daddy hateem," jinjina mashi kai Yai batare daya ƙara furta komai ba. Baba, zamu tafi bamusan ko mune ke bakason gani ba, His excellency abdul razak ne Ya furta hakan, Sai lokacin Dattijon arziƙi Ya zame tafukan hannayenshi daga saman fuskarshi, tsufanshi Ya ƙara bayyana sosai, tamoji tamoji duk Ya kame fatarshi, Zaro hanky Sir mubarak Yai daga cikin aljihun shi, Ya soma share mashi hawayenshi, Bayan Ya kammala yasoma dubansu ɗaya bayan ɗaya, bi da bi, gaba ɗaya kamannin fuskarshi suka ɗauko, Musamman sharuffudeen da hateem tamkar yai kakinsu, hatta hasken fatarsu kalar nashi ne, launin idanuwansu ne dai kalar na mahaifiyarsu reddish brown.
Ganin yadda duk suka damu ya sanya shi sakar masu fuska, cikin sanyin murya yace"kai nifa ba wani abu ke damuna ba, Farin Cikin ganinku ne ya sanya ni kuka, don haka ku kwantar da hankulanku, Jazz miƙo min cake din nan" Ya faɗa Yana ƙoƙarin saukowa daga saman gadonshi, mimmiƙewa sukayi tsaitsaye suka kewaye shi, Tuni damuwar fuskarsu ta washe Miƙa mashi cake din Jazz Yai, sai da suka fara kirga mashi one two three kafin Ya hura Iska Candles din jiki suka mutu, tafa mashi hannu sukai, sai faman sakin murmushi yake Yi, "Wazai fara bani cake din" ya fada yana dubansu, Matsa ma jazz hanya sukayi Ya matso kusa dashi, Hajiya saratu ji take kamar ta ingiza ƙeyarshi taji haushin kasancewarshi acikinsu, aganinta bashi ya dace Ya shigo cikinsu ba, Ina laifin su twins suda su ke jikokinshi.
Shikuwa Hannunshi Har kerma yake yi wurin daukar wuƙa, Ya gutsiro cake din Ya miƙa mashi abaki, Ya soma ci atsanake Yana duban Jazz hada ɗaga mashi gira Ya furta"Waye ya haɗa min wannan? Yai min daɗi" Jazz yace"mommyna ce ta haɗa maka shi" jinjina kai yai"amma ta iya na jinjina mata" daɗi jazz yaji An yabi cake din mahaifiyarshi, saratu kuwa takaicin duniya ya isheta. Daya bayan ɗaya suka soma bashi cake din Yana ci, Kafin shima Ya kar6a Ya bi kowannansu Ya bashi abaki, Bayan sun kammala ci, Ya daura cake din saman table, Rungumarsu Ya fara yi ɗaya bayan ɗaya yana bubbuga bayansu da hannayenshi kamar yadda ya saba yi masu tun suna Yara. Saman gadonshi Ya koma ya zauna yace masu duk su zazzauna yana son yaita kallonsu, hakan ba ƙaramin daɗi yai masu ba, kamar yadda ya basu umarni haka suka samu wuri saman mattress din suka kewaye shi.
Banda jazz wanda tuni Yajima da komawa ƙofar ɗakin, ganin irin kallon barazanar da hajiya saratu take Yi mashi kamar zata shaƙe shi.
Tun wuraren ƙarfe goma sha biyu na safe, Hamshakan motoci keta kurɗaɗowa cikin gidan tunkafin lokacin da za'a fara gudanar da shagalin Ya gabato, sun Cika gidan, kasancewar Baba Obie mutunne mai tarin jama'a, wasu ma ba a ƙasar suke zaune ba, amma aranar sai gasu sun shigo Nigeria duk don saboda su halacci taron taya murnar ranar haihuwarshi, Masu aikin gidan sai zarya suke Yi wurin Kaima baƙi abinci dana sha, kitchen ya zama Dandalin magulmata, Bakunansu ko gajiya ba su yi da surutu.
"Yau zamu ba idanuwanmu abinci har su ƙoshi" Safa ce tai maganar, Sophia tace"Hmm, aini yin aiki agidan nan gaba ta kai ni gobarar titi ajos, waiku kunga haɗuwar Prime minister Hateem da matarshi! Wow masha Allah, Allah Yayi halitta" Marwa tace"shi kaɗai kika gani kenan, baki ga Mai girma sharafudden ba, ai hadashi jiya cikin waɗanda sukaje airport tarbo prime minister, wallahi mutumin ba ƙaramin burgeni yake Yi ba, dashi da ɗan uwanshi hateem, mutanan badai aji ba, komai nasu da dattako suke Yin shi.
Abla tace"yau zamuci uwar sabada, zamu tashe mu watse, Mu raƙarƙashe don nasan dole agayyaci mawaƙa da makaɗa, Ni nama rasa wani kaya zan sanya wallahi"
da zolaya safa tace"kalar dangi, Uban wa kike tunanin zai barki ki shiga hall din taron? Ke kin isama? Sannu isassa mai walkin sa, ai kawai ki tsaya a iya matsayinki, Ta ina zaki nemi haɗa kafaɗa da Manya manyan hamshaƙan attajiran masu kuɗi, ai idan kin ganki a hall din can to amatsayin mai raba abinci zaki je" dariya suka saki.
Abla tace"Nima fa da wasa nake wallahi, Ai ni tsoronma shiga zan ji, jiya izuwa yau bani da kwanciyar hankali saboda jami'an sojojin da suka kewaye estate din ciki da waje, nasan duk zuwan hateem ne yasa aka ƙara tsaro har haka"
Marwa tace"niko inaso na tambaya, abun yaɗan tsaya min araina," har suna haɗa baki wurin tambayarta menena, Numfasawa tayi kafin ta soma magana"kunsan ni ban jima da fara aiki acikin gidan nan ba, abun da yaɗan ɗaure mun kaina, taya akai hateem da yake ɗan kasar Nageria Yake mulkar ƙasar turawa mai girma kamar canada, dama hakan yana iya yiwuwa? Ta tambaya tana duban fuskokinsu, Safa ce tafara Kora mata jawabi"bazai yiwu ba sai dai idan ya kasance, shima ɗan kasarne, Misali kamar idan acan canada aka haife shi, kinga yana da ƴancin da zai Iyayin duk wani abu da ɗan kasar zai yi, ko kuma idan mutun ya zauna a wata ƙasa wadda ba tushen shi ba, har na tsawon adadin shekarun da zai iya cika duk wasu sharudda daya cancanta ya zama ɗan kasar shima yana da right da zai Iya aiwatar da duk wani abu da ɗan ƙasar zaiyi, shi kuma Hateem da kika gani asaline dasu a kasar canada, tushen mahaifiyarsu ne, Allah yajiƙanta, ta fito daga babban family daya shahara a ƙasar canada, bakomai nasani dangane da tarihinsu ba nima hajjaty ce tafara bani, kinsan mahaifinsu yayi yawon duniya sosai, kuma yana da farin jinin al'umma, duk inda ya shiga saiya samu kyakkyawar tarba, Ya zauna a kasashe daban daban tunkafin Ya auri matarshi ta farko, mariganya Hajiya kudirat, Allah yakai rahama ƙabarinta, itace ta haifa mashi Yan ukun shi, Senate lateef, sir mubarak da abdul razak na lagos, bayanshi sai Deen obinna, da kuma saratu autarta, Hajiya kudirat jinin sarauta ce, ta fito daga tsatson sarkin yarbawan jihar lagos, marwa tace"Ikon Allah shiyasa hajiya saratu take da jinkai, Ashe suma Izzar sarautace a jininsu" murmushi kowannansu ya saki, Safa ta numfasa kafin ta ɗaura da cewa"sharafuddeen kuma da Hateem uwa ɗaya uba ɗaya suke, Idan kika lura sunfi kamanceceniya da juna, duk da gaba ɗaya ya'yan obie dashi suke kama, babu wanda ya ɗauko mahaifiyarshi, har ƙwara Saratu ta ɗauko kama da Hajiya kudirat, bari in baki amsar tambayarki, Hateem dai a hannun dangin mahaifiyarshi can ƙasar canada Ya taso acan aka haife shi, kuma acan aka raineshi, mahaifiyarsu bata ta6a zama a kasar nigeria ba, Idan kinga tazo to zamane na ɗan lokaci, sai dai shi obie din ya taka yaje inda take tare da ahlinsa, shiyasama har family house garesu a ƙasar canada, shi kuma sharafudden da kika ga Ya taka matsayin shugaban ƙasa a nigeria bayan mahaifiyarsu ta haifeshi a canada, to shi ba a kasar aka raine shi ba, Ya zauna a hannun dangin mahaifinshine anan nigeria tun Yarintarshi har zuwa girmanshi, Idan kina neman ƙarin bayani game da hateem, Ki binciki tarihin Barack obama tsohon shugaban ƙasar america Kusan tafiyarsu ɗaya kinsan shima mahaifinshi ba ɗan kasar america bane, tushen mahaifinshi daga africa ne" murmushi kowannansu Yasaki, Marwa tace"ai basaima na bincika ba, Na gamsu da bayaninki sosai, Kin wayar min dakaina, Da ina kokwanton taya haka zata yiwu ɗan nigeria ya mulki wata ƙasa, amma yanzu kin goge min kokwantona, gaskiya abun Ya ƙayatar dani, balle shi hateem ma da ba Iya haihuwarshi acan akayi ba, Tushen mahaifiyarshi ne"
firar da sukeyi bata dauke masu hankali Ga yin aikinsu ba, kasancewar sunada yawa, akwai wadanda ke zaryar kai abinci, ba iya su kadai bane. "Ni dai fatana Allah yasa uban Ƴan ji da izzar nan yazo yau" sophia ce tai maganar, Abla tace"Ai ga ƴar uwarshi nan uwar ji da Izza, Itama ta duro gidan, zanso inga haduwarsu" Safa tace"Kina nufin Nazli"? Jinjina kai Able tai"ita nake nufi, Yarinyar badai Ji da kai ba, ta Iya haɗe fuska bata da fara'a, Har ƙwara Yazrin tafi sakewa da mutane duk da itama bakowa take hulda dashi ba" Marwa tace"ke kuwa ai dole suyi izza, jinin sarautar dubai, Jikokin sarkin sarakai, Ga uba shugaban ƙasa sukutun da guda, uwa uba ga kyau kamar su suka tsara halittarsu, Ni wallahi burgeni suke Yi, takun tafiyarsu kadai abun kallone" Safa tace"ga kuma Hindu, nasan itama yau zata shigo gidan, itada mahaifiyarta Hajiya sarauta, mace mai ji da izza" Ta6e baki Sophia tayi"Um, nifa mutun ɗayace bana son ganinta, Hajiya laurat saboda bata da mutunci matar, ƙyamar talaka gareta" Dariya Abla tasaki tana fadin"kin kuwa san dole ta halacci taron nan, zata haɗu da ƴar uwarta Aunty masifatu, mu kuma mun shiga uku" dariya suka sanya gaba ɗayansu kafin suka maida hankalinsu akan aikin dake gabansu.
*HAJJATY❤*
A kwance suke saman gado, manne da juna, yahanata sakat tun ɗazu take son leƙawa kitchen pravin Ya hanata motsawa, ga tarin ayyuka dake jiranta, tun asuba ya shigo ɗakin.
Muryarta da kasala take ambaton sunanshi"Pravin pls ka tashi ka tafi ɗakin matarka, baccin Ya isa haka, Ina da ayyukan da zanyi kada aji ni shiru a matsayina na babba acikin masu aikin gidan nan"
A hankali Ya buɗe idanuwanshi da suka kaɗa jawur yana dubanta dasu.
Sai faman lumshe su yake yi, don ba ƙaramin nauyi suka yi mashi ba, Short ne ajikinshi babu riga jallabiyar shi tana a saman mattress din, Ita kuma Iya undy ne tayi daurin gaba dashi, shara shara kana Iya ganin tsiraicinta. Kamar baisan furta maganar yace"dan Allah ki ƙyaleni, bana jin daɗin jikina ne, ki kwantar da hankalin ki babu wanda zai damu don baki aiki" Ya faɗa haɗi da ɗaura hannunshi saman sumar kanta dake akwance saman bayanta, a hankali yake shafa gashin Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Na roƙe ka, ka tashi ka tafi dan Allah, Matarka zata Iya nemanka" "Meye damuwarki aciki, duk kin wani ɗaga hankalinki"
Murguɗa mashi baki tai"Pls my baby boy, kasan yau babbar ranace agaremu, yakamata mu shiga cikin dangi ai hidima tare damu" Jinjina mata kai yayi'okey, naji zan tafi but before that, Inaso zan gargadeki, kinga yau akwai manyan mutanan da zasu halacci taron nan, banason inga gifcinki awurinsu, don na lura ba ƙaramin jan hankalinsu kike yi ba"
Farfari tayi mashi da ido"idan kaga banje wurinsu ba to bana numfashine, hakanan kawai kake min baƙin ciki, don kada in samu mijin aure, kai kayi aure ni kuma ka hanani sakat" da zolaya tayi mashi maganar.
Lumshe mata ido yai, ya tsare kirjinta da kallo kamar ba yanzu ya gama tsotsarsu ba.
"Nidai na faɗa miki kuma na ƙare maganata, idan kika ƙara yi min irin wannan maganar zanyi maganinki ne" "Ashirye nake dana kar6i kowani irin hukunci da zakayi min, nasan dai bazaka Iya cutar dani ba" ta faɗa tana tura mashi kirjinta, aiko da karfi Yakai masu cafka, ta fasa ihu tana dariya, kutsa kanshi yai cikin undy dinta Ya cigaba da wasa da jikinta, tsawon mintuna kafin ya fito da kanshi ya haɗa uban gumi, sai faman sakin nishi take Yi tana haki kamar wadda tasha gudu "Ki rakani toilet muyi wanka, jikina ya 6aci sosai" harara ta jefa mashi"ni bazan bika ba, kaje wurin hajiya saratu tayi maka wanka" zaro ido yayi"ahaka ɗin" ɗaga mashi gira tai alamar eh. 'Idan ta tambaye ni waye yai silar jefa ni yanayin Nan me kikaso in fada mata" Da shagwa6a tace"saika fada mata nice" da karfin hali ta furta hakan Dariya pravin yai"aiko da wa'adin aikin ki agidannan Ya ƙare, har kashe ki zata Iyayi, don ba ƙaramin kishine da ita ba, daga ni harke zata yi mana korar kare"
"Kaga sai mu koma ƙauyanmu na indiya mucigaba da yin bautar shanu" dariya suka sanya gaba dayansu Bayan sun lafa ya sanya hannu biyu ya cuccu6eta Ya nufi bathroom da ita, Jim kadan Ya fito da ita ya ɗaurota saman kafadarshi, asaman gado ya kwantar da ita Yasanya mata bargo ya lullu6eta yana fadin"ki kwanta ki huta pls, bana son kina aikin wahala, inyaso da anjima saiki shiga cikin gidan" amsa mashi tayi da toh badan taji maganarshi ba. Shaf shaf Ya zura jallabiyarshi Yai mata sallama kafin ya fuce daga Cikin ɗakin, Fitarshi keda wuya wayar shi daya manta saman bedside drawer ta soma yin ringing, Ba tare data futo daga cikin bargon ba, Ta mika hannu tana laluban wayar har tayi nasarar Cafkota, ta fiddo da kanta tana duban screen din A tsanake ta furta sunan daya bayyana da manyan haruffa.
*Jan le6e* ta6e baki ta ɗanyi aranta ta ayyana kowane ne wannan mai suna jan le6en? Sunan ma dariya yaso ya bata wai jan le6e, bazata Iya picking call dinba saboda Ya hanata ɗaga mashi phone idan aka kira, ko wayar bai bari ta ta6a ba, Sau ɗaya kiran ya shigo tai rejecting ba'a ƙara kira ba.
Ajiye mashi wayar tayi saman drawer, ta dan lumshe idanuwanta yayin da zuciyarta ke tariyo mata fuskar kyakkyawan ɗansu da suka rasa, taji baƙin cikin mutuwarshi har yau idan ta tuna shi sai hawaye sun cika idanuwanta, tana matuƙar ƙaunar yaron, tsawon mintuna kafin ta yunƙura ta sauko daga saman gadon, donta kimtsa ta nufi kitchen.
Idan muka koma 6angaren Unaisah, tun bayan kammala sallar asuba, ta nufi ɗakin danish ba tare da sanin kowaba, tana shiga ta same shi kwance saman lallausar carpet din dakinshi amaimakon saman gadonshi, dogon hijabi ne a jikinta launin maroon, zuciyarta duk ba daɗi, daga gefenshi ta zauna tana duban kyakkyawar fuskarshi, lokaci ɗaya taji gabanta na faɗuwa, sakamakon ganin yadda yake firgita acikin baccin shi, da sauri ta ɗaura Hannayenta saman ƙirjinshi Nan fa hankalinta Ya ƙara tashi Jin temperature dinshi, kamar na daren jiya, lamarin Ya ɗaure mata kai, Ga sanyin A.c har yayi yawa amma shi zafi ne a jikinshi, babu sassauci, Muryarta na rawa ta soma ambaton sunanshi"Danish! my Man? Wake up! Meke damunka? Why nake jin jikinka da zafi" can cikin baccinshi yake jin miryarta.