Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 55
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 55: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 55. "Dan Allah ka tashi kayi min magana meke damunka?…
2,935 words
"Dan Allah ka tashi kayi min magana meke damunka? Baka da lafiyane"? Daƙyar ya samu damar ware idanuwanshi Akan fuskarta, A daddafe ya samu Ya miƙe zauna yana dubanta, Short din Jiyane a jikinshi da singlet. Yaji dadin ganinta a room dinshi, Jiya yai zaman jiranta yai tunanin zata zo gare shi har bacci yai awon gaba da shi bata leƙo ba, till now. "Kayi shiru baka ce min komai ba, danish zafin jikin ka yai yawa, kodai inje in faɗa ma Boss Man Yazo Ya duba ka"? Girgiza mata kai yai, kafin ya motsa la66ansa Ya furta"babu abunda ke damuna, Lafiyata qalou, kece kika 6ata min rai" Hankalinta bai kwanta da kalamanshi ba, aɗan ruɗe ta furta"ba haka bane danish, dole akwai abunda ke damunka ba Iya 6ata maka rai da nayi bane, cos babu yadda za'ai Jikinka yadau zafi rau batare da dalili ba, Please ka faɗamin idan ba haka ba hankalina bazai kwanta ba, sannan kayi hakuri dan Allah, abunda ya faru Jiya wanda ya 6ata maka rai, In sha Allah bazan ƙara bari Hakan Ya faru ba" Cikin kulawa take Yi mashi magana, Jinjina mata kai yai"kiyi min alƙawarin ba zaki ƙara rungumar wani ƙato a jikinki ba, idan bani ba koda su Naufal ne" kiris ya rage ta saki dariya jin abunda yace Jinjina mashi kai tayi"in sha Allah My man kai kaɗai kawai," ajiyar zuciya ya sauke Ya samu sassaucin radadin da zuciyar shi ke yi mashi "Tunda naga yanzu hankalin ka ya kwanta fada min meke damunka? Menene ya haddasa maka zafin jikinka"? Ta faɗa tana duban ƙwayar idonshi, la66ansa duk sun bushe ƙamas. "Dagaske nake Yi maki babu abunda ke damuna, Nima bansan ya akai jikina ya ɗauki zafi ba" "Nidai hankalina bai kwanta ba, ka ba ni dama inje in faɗa ma boss man halin da kake aciki," haɗe mata fuska yai jin ta ambaci sunan boss man, sam bayason ji. "Bana buƙatar kowa ya dubani, ki kwantar da hankalin ki, zafin jikina baiyi min illa ba, don haka kija baki kiyi shiru" Jinjina mashi kai tay"maganar abinci fa? Jiya kace min ba ka ci dinner dinka ba, ni sam Na shafa'a" Yamutsa mata fuska Yai, hada jifarta da harara, murmushi tasakar mashi "Bari naje na duba dining, idan an shirya mana abincin breakfast dinmu, zan shigo maka da naka a ɗaki tunda baka son fita" ɗaga mata gira yai alamar okey. Miƙewa tayi da sauri ta fice daga dakin ta sauko down stairs, koda ta duba ɗakin cin abincin ba a jera masu komai ba, saboda time din da suke zama Yin breakfast bai cika ba" yanke shawarar neman ɗakin Ummi tayi don ta fada mata game da ɗan uwansu dake jin yunwa, wata'ƙil ta sama mashi abunda zaici kafin a shirya masu abincinsu. Batasan ina zata nemo room din ummi ba, tadaisan acan upstairs Yake, cos ta ta6a ganin tana saukowa saman bene, da sauri ta nufi stairs din tana tafiya Hijabin Jikinta naja da ƙasa, babu kowa a palourn duk suna adaki. A hankali take taka stair cases din Har ta samu ta haura can sama, Ta rasa wace hanya zata bi wadda zata sada ta da bedroom din Ummin america, Tafiya taci daga dayi tana bin ko'ina da kallo, aranta tana ƙara jinjina haɗuwar ginin, tana ta ƴan kalle kalle kamar baƙauya harta zagayo ta 6angaren Hagu batare data gano hanyar da zatabi ba, Ƙofar wani katafaren room Ta dakata da yin tafiyar, aranta ta tace"idan kuwa wannan ne ɗakin aunty ummi duk Yafi namu kyau" Ta cikin glass din ƙofar take hangen zallar haɗuwar kayan alatun cikinsa, kifa kanta tayi jikin ƙofar har ta danna madannin Jikinta batare data an kare ba, da alama mamallakin ɗakin Yayi recieving alert na neman iznin shigowa shiyasa ƙofar tafara ƙoƙarin zugewa slowly take sliding, da sauri Unaisa Ta saki glass din Jin yana motsi, abunka game karanbani, ganin ƙofar ta wage, sai kawai ta haura ƙafarta ciki, yau ta ga maƙurar aljannar duniya a ɗakin data faɗo, wuyanta kamar zai 6alle, tana tafiya tana ƴan waige waige kamar zatayi tuntube, tayi mamakin dukiyar da aka narka wurin tsara Kayan furniture din dakin, Yana da fadi da tsayi, ga wannan floor to ceilling window din a left hand din bangon ɗakin, Ta jikin glass din zaka Iya hangen wajen ginin Harma da manya manyan gine ginen dake acikin burnin abuja, bayan haka daga cikin bedroom ɗin zaka Iya hangen komai na cikin bathroom ta glass din ƙofar, sai dai da alama ba haka akeyin wanka acikinshi ba, da akwai hanyar da ake rufe glass din yai duhu idan mutun zaiyi using dashi.
Sai faman jinjina kai Unaisah take Yi, tajima tana mamakin wanene mamallakin daular nan da suke acikinta, bata ta6a yin tozali da shi ba, tadai ta6a jin sunan Chief of isod abakin Dr Laura. Tabbas Da ace tasan ɗakin wanene da batayi gigin shigarshi ba, ta zaƙe sai kurɗaɗawa take Yi can ciki ta shige kamar ɗakin baba tajo, shi kanshi bedroom din Yana da katafaren falonshi Har yaci uban na down stair haɗuwa, tana ƙoƙarin giftawa ta wata ƙofa dake a ɗakin, kwatsam kunnuwanta suka soma Jiyo mata sautin daddaɗan kiɗa Yana tashi, na taken waƙar satisfya
Wani irin daddaɗan ƙamshi Ya ratsa hancinta sosai ta shaƙeshi, a hanzarce ta ɗaura idonta saman kofar ɗakin rubutun sama ta karanta kamar haka *Gym room" nan take ta fahinci dakin menene, wato wurin motsa jiki ne" aranta ta ayyana bari ta dan leƙa taga wanene Ya kunna sautin kiɗa. Kasancewar ƙofar abuɗe take, Unaisah ta zura kai kamar 6arauniya tana bin ko'ina da kallo, an ƙawata room din da injinan motsa jiki, kala kala, ga kayan jin sauti, sam bata lura da shi ba, kamar yadda shima bai lura da mutun ba, Yadaisan akwai wanda ya shigo dakinshi saboda alert din da yai recieving awayarshi, saida Ya bada iznin shigo ciki tukunna ƙofar ta buɗe.
Sai faman wurwurga eye balls dinta take tana bin ko'ina da kallo, lokacin da tayi arba dashi wani irin mugun bugu ƙirjinta Yai, har saida ta dafe shi da hannu, tayi matuƙar firgita da ganin shi, Ya tattara hankalinshi gaba ɗaya akan Punching bag din da yake kaima naushi da hannayensa waɗanda ke sanye cikin boxing gloves, Cikin zafin nama yake motsa jikinshi, Ya haɗa uban gumi, zufa ta ko'ina take tsattsafo mashi, ƙirar ƙarfinshi Ta bayyana ga wannan sick pack din ƙirjinshi ruɗu ruɗu, Damtsen hannayenshi sun murmurɗe, Yana naushin jakar motsa jikin Breast muscles dinshi na shaking, babu riga ajikinshi, black short ne kaɗai Ya sanya wanda Ya tsaya mashi dai dai gwiwarshi, bata samun damar ganin fuskarshi dakyau ba, saboda ba ita Yake fuskanta ba. Ta natsu tana kallonshi, Ko idonta bata ƙyaftawa, ba zato ba tsammani taji an damƙi wuyanta ta baya, harta buɗe baki zata fasa Ƙara taji anyi saurin toshe mata baki, tsoro Ya kamata jikinta ya hauyin kerma, ɗungurugum taji an dagata sama Anjata zuwa cikin bedroom din, sai faman wuntsila ƙafafuwanta take Yi a ƙoƙarinta nata kwace kanta daga hannun mutumin daya dauketa, har ƙofar ɗakin Ya fito da ita Ya direta ƙasa, A firgice take dubanshi, bakomai bane face Big guy, kayan kakinsu ne a jikinshi, ya sanya face mask a saman fuskarshi, idanuwanshi na akan fuskarta, La66anta na kerma ta furta"wa..wa.. Wanene kai? Meyasa ka daukoni? Idanma saboda nashiga ɗakinne aini bansan ya akai na shiga ba, rashin sanine, ɗakin aunty ummi nake nema, danish ne Yake jin yunwa jiya baici dinner din shi ba kuma na duba dining ba'a shirya mana abinci ba" tsabar ruɗune yasa take yi mashi zuba har abunda bai tambayeta ba, taƙi barima Yai mata magana Sai da ta dasa aya tukunna Ya soma yi mata magana cikin muryar raɗa"kinsan ɗakin wanene kika shiga"? Girgiza mashi kai tayi alamar a"a gyaɗa kai yai"kada ki kuskura ki ƙara yunƙuri shiga ciki, Idan ba haka ba jikin kine zai gaya maki, Ni nayi mamakin ma taya akai kika samu damar shiga bayan ita kanta ƙofar sarrafata akeyi, Kodai ba mutun bace ke"? Ya fada haɗi da ɗage mata gira alamar yana jiran amsarta. Duk tabi tasha jinin jikinta, sai faman zare mashi gray eyes dinta take Yi, daƙyar Ta iya fadin"nifa bansan komai ba, ai na fada maka dakin aunty ummi nake nema" ta ƙare maganar tana murguɗa mashi baki. Har murmushi yasakar mata batare data gani ba saboda mask din fuskarshi, dama Yaji labarin rashin jin maganarta, gashi yanzu ya tabbatar dahakan" "Okey, ki koma ɗaki, yanzu zanzo in kawo maki abunda shi ɗan uwan naki zaici, kafin Ashirya maku naku abincin" amsa mashi tayi da toh, jikinta har rawa yake Yi wurin yin saurin haura ƙafa ta kama hanyar komawa ɗakin danish, tana tafiya haɗi da waiwayan big guy, Yana atsaye yana kallonta har saida ta 6ace ma ganin shi, tukunna ya kawar da idonshi daga gareta. Tun da ta koma ɗakin danish bata daina tariyo suffar mutumin da tayi tozali dashi a gym room ba, Ya tsaya mata aranta, taso ace sunyi ido biyu da shi, don ta samu damar ƙare ma fuskarshi kallo, shin wanene shi? Tabbas tanaso ta sani! Bada jimawa ba, Big guy yai sallama dakin danish, hannunshi ruƙe da tray din Kayan abinci ashake, bayan ta kar6a tayi mashi godiya, asaman carpet suka zauna ita da danish, ta dinga bashi abaki Yana ci, suna kallon juna yayin da acan ƙasan zuciyarta tunanin ɗan ta halikin nan take Yi, shi kanshi danish Ya lura da canzawarta, saboda tsabar tunani har a hanci tai ƙoƙarin cusa mashi abinci, saida ya damƙo hannunta tukunna ta ankara, yace mata me take tunanine tace mashi bakomai, badan ya yarda ba ya ƙyaleta, A ɗakinshi ta zauna duk don ta faranta mashi, sai da tasanyashi yai wanka ya canza kayan jikinshi tukunna hankalinta ya kwanta, damuwarta ɗaya yanzu zafin jikinshi sai ƙara ninkuwa yake Yi.
*Obie Estate*
Wuraren ƙarfe huɗu da rabi Estate din Ya cika maƙil da mutane babu masaka tsinke, manya mutane masu faɗa aji duk sun hallara, kama daga Ƴa'ƴan jam'iyarsu ta Action progressive party ministoci, sanatoci, gomnoni, da sauransu, Kowannansu Ya ɗauki wankan expensive shadda ta kece raini na shiga tsara, jikokin Obinna Na ƙasa nigeria da wadanda ma basa ƙasar saboda shagalin nan sun dawo Nigeria A yau din nan, daga cikinsu akwai ya'yan sir mubarak mazauna kasar canada, zaratan samari Zaki shine babban ɗanshi mai bi mashi Ibad, bayansu sai ƴa'ƴan His excellency abdul razak, babban danshi Yasir, tare da ƙanwarshi Yusra, sunzo ne tare da mahaifiyarsu Her excellency hajiya muhibbat, bayan su sai Ya'yan his excellency Deen, babban ɗanshi Justice Nadeem mai bi mashi Dr. nawaz tare da mahaifiyarsu suka zo Her excellency hajiya Jamila, bayansu kuma sai ƴar gidan mai girma sharafudden Hindu ƙanwar Chief Owais, tare da matayanshi suka zo Hajiya Malikat sarauta uwar gidanshi da kishiyarta Hajiya laurat, da kuma ƴar wurin Lateef zulaihat kanwar ziyad, gaba ɗayansu dai kowa Ya hallara ga yan matan hateem Nazli and Yazrin, gaba ɗaya matan sun ɗauki wankan Swiss cord lace yayi bala'en Yi masu kyau, A babban hall din dake acikin gidan aka gudanar da shagalin, An ƙawata cikinsa da kayan alatu, ko'ina ka kalla furannine da ƙyalƙyalin sparkling chandeliers, ga Banquet chairs da aka tanada domin baki su zauna, kowani table saman shi an ɗaura bouquet of flowers, tare da Crystal glasses and silverware, da sauransu, floor din hall din kuwa an shimfiɗe shi da ƙayataccen red carpet, daga can gaban hall din Gingirimeman Cake stand ne an ƙawata shi sosai, Mawaƙa da makaɗa hada maroƙa sun hallara, domin suma su kwashi rabonsu, an shirya kayan abinci saman zungureran table kala daban daban, sai mutun Ya za6a ya darje, duk haɗuwar taron nan mutun ɗayane bai hallaraba, Hakan ba ƙaramin ta6a zuciyar obie yai na, Yaci buri akan zuwanshi amma shiru babu shi babu alamarshi, mutane sai tambayar shi suke Yi, ya akai basu ganshi ba? Iyayenshi sun rasa amsar dazasu basu, sai dai suka dinga cewa bai kaiga zuwa ƙasar ba, farin jini gare shi shiyasa duk wanda yazo sai ya tambayi ina owais Yake, Taro Yayi albarka, Anci ansha anyi kullu wash rabu hani'an, Anyi harka ta arziƙi ta kece raini, daruruwan mutanan dasuka kawo mashi kyauta taban mamaki basu ƙirgiwa, baba obie Ya mori lokacin shi, Yayi farin cikin dabazai Iya misalta shi ba, Ƴan uwa da abokanan arziƙi sun faranta mashi rai, sun gwangwajeshi da Kyaututtuka na ban mamaki, Sun taka rawar girma, sai dai muce Alhamdulillah taro Ya tashi Lafiya, gab da magrib baƙi suka ragu waɗanda suka rage ƴan uwane na jini, da kuma mutanan Hateem.
*WAIWAYE ADON TAFIYA💫*
(Abunda ya faru bayan zahra ta faɗa ma Aneelerh halin da take aciki, Na kuɗi da hajiya falmata take binta bashi, bayan ta koma ɗaki damuwa ta isheta, tayi ƙarfin haline kawai wurin bata shawara akan ta amince da buƙatar hajiya falmata saboda tana son ta jaraba zahra ne don taga idan tana da hankali, tunani ta soma yi ta wace hanya zata Iya taimakonta? Nan take zuciyarta ta bata shawarar tayi amfani da sauran kuɗin nan da jami'an sirri suka bata, har yau bata ƙarar dasu ba, tamkar tana jin tsoron ta6a su, tun dai data siya ma baby junaid kayan wasa bata ƙara cirar ko naira biyar ba.
Ba tare da sanin kowa ba Aneelerh ta tuntu6i mahboob, a ɗakin shi ta same shi, ta tambaye shi koya san gidan hajiya falmata mahaifiyar ƙawar zahra? Yace mata eh yasan gidan, sun ta6a zuwa tare da zahran ma, tace toh so nake ka rakani gidan, da mamaki akan fuskarshi yace amma me zakiyi acan din kinsan ta ne? girgiza mashi kai tay alamar a'a, kawai inaso ka rakani muje, idan mun fita zan faɗa maka komai, amma kafin muje gidan zaka fara rakani banki, akwai wasu kuɗi da nakeson in cira, Jin ta ambaci kuɗi yasa mahboob saurin amincewa zai kaita gidan, a cikin motarshi ya dauki aneeleeh saida suka fara biyawa banki ta ciri kuɗin kafin suka nufi gidan hajiya falmata.
Lokacin da suka karasa gidan, A parking space mahboob Ya tsayar da motar, Aneelerh tace dashi ya jirata anan, ya amsa mata da toh, da sallama abakinta ta shiga palourn gidan, adai dai lokacin mai aikin gidan ta fito daga kitchen ta yi arba da aneelerh, fuskarta da fara'a suka gaisa tace mata wurin hajiya falmata tazo, Allah yasa tana nan, Mai aikin tace bata jima da dawowa daga office ba, ki zauna bari naje in sanar da ita, da sauri mai aikin taje ta fado mata, jim kadan ta dawo ta sanar da aneelerh sakon hajiya tace ta jirata gata nan zuwa, aneelerh ta amsa mata da toh, kusan mintuna biyar Aneelerh tana a tsaye ta ruƙe qugu tana jiran fitowarta, cikin jin fargabar ganin matar, sai faman bin palourn take yi da kallo.
Sautin takun tafiyarta ne Yaja hankalin Aneeleerh ga kallonta, A hankali take saukowa down stair, ta ɗauki wankan tsadaddan leshi, kanta yasha ɗaurin ɗan kwali, ta manna farin glass a idonta, Babbar macace tana da jiki, tana tafiya tsokokin jikinta na motsawa, Fatar jikinta tasha hutu har ta gaji, daga ganin fuskarta masifaffiyace, idanuwanta mitsi mitsi da su kamar na mutanan Yankin china, hancinta kuwa abaje yake, ga big mouth dinta yasha man baki.
Ta6e baki Aneeleerh tayi aranta ta furta jibarta dan Allah, ƙatuwar banza da ita kamar buhun masara, a haka take lalata rayuwar matasan ƴan mata, Allah dai ya shirya, wasu mutanan sunyi asarar rayuwarsu.
Lokacin da hajiya falmata ta ƙarasa saukowa daga saman benan, idanuwanta suka Yi mata tozali da kyakkyawar fuskar Aneelerh nan take taji ta burgeta, tayi mamakin ganin baƙuwar fuska agidanta, bakomai yafi tafiya da imaninta ba face Kyawun surar Aneelerh.
Ganin Yadda Ta tsareta da idone Yasa Aneelerh tayi saurin gyara mayafinta ta rurrufe jikinta, Aranta ta furta A'uzubillahi minasshaidanirrajin, Aniyarki ta biki baƙar mayya" Saman sofa din dake fuskantar Aneelerh Hajiya ta zauna, tana dubanta da wani irin mayataccen kallo.
Yamutsa fuska Aneelerh tayi fuskarta ba wasa tace"barka da Yamma" Hajiya falmata ta amsa mata da"barka dai, bismillah ki zauna mana"
Ɗaure fuska Aneela tayi"bana zama agidan da ake aikata sa6on Allah, saboda ni tsarkakakkiya ce, bai kamata in goga ma jikina najasa ba"!! Mamakine Ya kama hajiya falmata, a hankali ta sauke glass din dake saman fuskarta don ta samu damar ƙarewa Aneelerh kallo.
"Bansan wacece ke ba, sai dai na fahimci haukan talauci ne ke damunki shiyasa kika kwaso ƙafa kika zo gidana don in taimaka maki"
Dariyar rainin wayau Aneelarh Tayi kafin tace"ki kalleni daga ƙasa har sama, kema kinsan nafi ƙarfin ki kira ni da talauci, Ni banzo don nayi cece kuce dake ba saboda bani da lokacinki, Maganar kudin zahra da kike bin ta bashi ne" Shu'umin murmushi ne Ya bayyana akan fuskar Hajiya falmata da shaƙiyanci ta furta"oh, kinzo ne ki fanshe ta, shiyasa kika kawo min kanki? Donni banga alamun zaki Iya biyan kuɗin ba" Girgiza kai Aneelerh tayi ranta a6ace tace"wato shi dai jaki duk yadda akai dashi sai yaci kara, idan kina tunanin na kawo maki kaina ne don in fanshi zarah to ki daina, domin kuwa nafi ƙarfin ƙasƙantacciyar mace ballagaza jahila kuma daƙiƙiya irinki, Mace mara tsoron Allah, me yin amfani da dukiyarta don lalata rayuwar matasan ƴan mata masu neman nakansu, Wlh kinji haushin rayuwar......" gigitacciyar tsawa Hajiya falmata ta daka ma Aneelerh, tamkar damusa ta yunƙura ta miƙe tsaye tana duban Aneelerh da mummunar fuskarta babu annuri ko misƙala zarratin ta nuna mata Hanyar fita da yatsan hannunta"Ke Fuce kibar min gidana, tunkafin ranki Ya 6aci, matsiyaciyar banza masu ƙashin tsiya"