Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 56

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 56

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 56: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 56. Aneelerh da ƙarfin Hali tace"idan kinga na fita…

3,317 words

Aneelerh da ƙarfin Hali tace"idan kinga na fita gidan nan to nagama faɗin ta cikina ne, Kuma wallahi koda gigin wasa kika ce zaki ta6a lafiyar jikina saina naƙasa ki bakisan wacece Ni ba" ta faɗa tana jefa mata harara, lamarin Ya ɗaurewa Hajiya falmata kai, ganin karfin hali na Yarinyar nan data zo gidanta tana Yi mata rashin Kunya. Goya hannayenta tayi saman ƙirjinta"ina sauraronki, Me ya kawo ki gidana!" Gyaɗa Kai Aneelerh Tayi"zuwa nayi don Inyi maki nasiha, don na fahimci Wadda iyayenki suka yi maki tuni shaiɗan Ya hure maki kunne, dan Allah Jibarki cikin shiga ta mutunci kamar wata mutuniyar arziƙi, al'halin nan kuwa fuska biyuce ke, A fili musa a zuciya fir'auna, Haba baiwar Allah, Da hankalinki da tunaninki da shekarunki kika za6i ki sa6awa Allah don kawai ki ji daɗin duniya? Kin manta da Allah yana ganinki kuma zaki mutu ki koma gareshi, a ko'wani yanayi mutuwa tana iya riskarki, idan taƙamarki kuɗine ki tuna Allah ne Ya baki Arziƙin bake kikayi ma kanki ba, Idan yaso zai Iya ƙwace wa, kuɗi da kike gani wallahi masifane Idan baka tafiyar dasu ta hanyar da ta dace ba, Ita kuma rayuwar duniya jin daɗinta ƙalilan nan bata da tabbas, bakisan yaushe zaki mutu ba, kin sanya mugunta aranki saboda Allah Ya azurtaki, Kina cutar matasan Ƴan mata, waɗanda Iyayen su suka sha wahalar basu tarbiya ke kuma kina gur6ata masu rayuwarsu, Allah kaɗai yasan adadin Ƴan matan da kika 6ata, kin goga masu jarabar da bazasu Iya gogeta ba, Kin cutar da rayuwarsu mutane suna kuka da su saboda sun addabi rayuwar al'umma kuma ire-iren ku ne ku ka yi silar lalacewarsu, wallahi kiji tsoron Allah kamar yarda ba zaki so ayi da ƴar ki ba to kema kada Kiyi da ɗan wani, duk da naji irinku Harda ƴa'ƴan naku kuke Yi, saboda shafewar basira da neman duniya kun makance bakwaji bakwa gani ku ala dole saikun siyama kanku tikitin shiga wuta"? Tun da Aneelerh ta soma Yi mata magana da faɗa haɗi da tsiwa take ta faman zare ido tana binta da kallo, tun da take arayuwarta wani ɗan adam bai ta6a gigin tunkararta Ya faɗa mata magana game da abunda Take aikatawa ba sai Yau da Allah Ya haɗa ta da Auntyn Zahra mai dimple, Ayoyin kur'ani aneelerh ta soma karanto mata tana fassara mata, kamar an rufe mata baki takasa dakatar da ita duk irin masifar da take da ita yau an kashe mata bakinta "Allah Yana son bayinshi waɗanda suka aikata 6arna suka tu6a saboda tsoronshi suka koma gareshi, dan Haka ina baki shawarar tunkafin lokaci Ya qure maki Hajiya falmata ki Gyara Halayanki, Ni bance zan sanyaki ki shiryu ba don nasan irinku taurin kaine daku kamar kwakwa, ko malamai sunyi maku nasiha bakwaji bakwa gani sai ranar da Allah Ya damƙe ku tukunna zaku gane kurenku, Ni in banda ma shafewar basira, wai ku bakwa tuna mutuwa da kwanciyar ƙabari ne? Baku tuna duk abunda kuka mallaka zai ƙare, daga kai sai halinka za'a binne ka a ƙabarin ka fa? Ke yanzu kin za6i ki mutu kina aikata mummunan zunubi na bin Ƴan uwanki mata? Ga hakkin Iyayen da kika sanyasu zubar da hawayensu ta silar lalata masu rayuwar ƴa'ƴa da ki ka yi ga kuma Matasan ƴan matan da kika gur6ata ma rayuwa, wannan fa zunubine mai cigaba da yaɗuwa ko bayan kin mutu zaki cigaba da samun kamasho acikin shi, saboda kinbar tarin ƴan matan da kika gur6ata agari suna aikata fasadi, wallahi kiji tsoron Allah tunkafin lokaci Ya qure maki, Ina ƙara jan hankalinki ki tuba ki koma ga Allah tunkan mutuwa ta risƙe ki don ita bata kwankwasama mutun ƙofa balle Yace zai shirya mata"

Wata irin zuface ta soma wanke goshin Hajiya falmata, Haƙiƙa kalaman Aneelerh sun fara karya mata zuciya, sai faman zare ido take Yi, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin maganar Aneeleerh ba, Yarinyar tayi matuƙar burgeta kuma ta bata mamaki da har ta iya yi mata nasiha batare da jin shakkarta ba, saboda mutane dayawa basa Iya yin magana agabanta, amma Ita wannan ido cikin ido take furta mata magana .

"hajiya falmata, duk runtsi duk wuya kada ki Karya zuciyar wanda Ya aminta dake! Ina magana akan zahra da ta dauke ki tamkar mahaifiyarta saboda ƙaunar dake a tsakaninta da ƴarki fatima, Kin karya mata zuciya, naji daci lokacin da na sameta ta kulle kanta acikin toilet tana Yin kuka babu ci babu sha ita kaɗai batare da kowa ya sani ba, Kin hanata runtsawa saboda taƙi baki haɗin kai ku aikata sa6on Allah, haba baiwar Allah, idan kece akayima yarki haka zakiji daɗi! Don kawai mutun Na buƙatar agazawarka sai kayi anfani da dukiyarka donka cutar dashi? Babu wanda yafi ƙarfin ya nemi taimako a duniyar nan, koda ba a wurin mutun ɗan uwansa ba, zai nema awurin Allah Idan har baka agazama bawansa ba tayaya kake tunanin zai agaza maka?

Jinjina kai Aneelerh tayi, Tuni zafafan hawaye sun wanke fuskarta cikin muryar kuka taci gaba da cewa"Kin ƙona mata rai, zahra ta yarda dake fiye da tsammaninki, tana kuka tana fadamin yadda ta aminta dake amma kika karya mata zuciya, Zahra da kike gani tafi ki Hankali, Yarinyar tana da tawakkali, tana jin tsoron Allah, Na jarabata don inga ko tana da wayon jure ƙaddara idan ta sameta, Ni dakaina nabata shawarar ta baki haɗin kai, da buɗar bakinta sai ce mun tayi ita ko duniya za'a mallaka mata bazata ta6a amincewa ta sa6ama Allah ba, saboda tana jin tsoron shi kuma tana jin tsoron ranar da zata koma gare shi, Hajiya falmata kin ta6a tunanin hakan? A matsayinki na babbar mace wadda ta haura shekara arba'in da ɗuriya a duniya? Shekaru sunja amma baki tsoron mahaliccin ki? Kina amfani da dukiyarki wurin Gur6ata duniyarki da lahirarki, maimakon kiyi amfani da su wurin taimakon bayin Allah marasa ƙarfi wadanda zasuyi alfahari dake ko bayan ba ranki kuma ki samu lada awurin Allah, Yanzu ina amfanin irin wannan rayuwar da kika daukarwa kanki"!?

Ƙafafuwanta ne suka gaza ruƙeta, Jiri Ta soma gani a cikin idanuwanta, adaddafe ta nufi sofa ta zauna tana faman fitar da numfashi.

Hankaɗe Kafaɗa Aneeleerh Tayi"Alhamdulillah nagama faɗar ta cikina, duk wanda yayi da kyau don kanshi, akwai mutuwa akwai hisabi, maganar kuɗi Kuma nazo maki da su miliyan Uku Cuf, Idan ma kina son ƙari zan ƙara maki, saboda inaso kisan muba jinin faƙirai bane idan arziƙine muma mun gaje shi gaba da Baya"

Ɗaga murya Aneelerh Tayi da ƙarfi ta furta sunan Mahboob, shigowa ɗakin Yayi hannun shi ruƙe da jaka baƙa, tunkan ya ƙarasa yake bin ko'ina da kallo, ganin haɗuwar falon gidan aranshi Ya ayyana Lallai hajiyar nan ta tara shiyasa take tsula tsiyarta son ranta saboda tana da arziƙi.

"Zoka ajiye mata tsiyarta," Aneelerh ta faɗa tana nuna mashi gaban Hajiya falmata, Ta zabga uban tagumi da hannu biyu, da alamun nadama atattare da ita.

Koda mahboob Yayi arba da fuskarta saida yasha jinin jikin shi ganin yadda ta haɗe rai, ga gumi na fita a goshinta.

Kamar mai jin tsoronta Haka Ya ajiye mata jakar agabanta.

Aneelerh ta ruƙo hannun shi acikin nata, har sun ɗaga ƙafa zasu bar falon muryar Hajiya falmata ta dakatar da su "Dan Allah Ku tsaya"!! Kusan atare zuciyarsu ta buga, a sukwane suka waiwayo suna dubanta, Gabansu ba ƙaramin faɗuwa yayi ba ganin ta fashe da kuka, miƙewa tayi daga saman sofa din ta nufe su tana fadin"wallahi nayi nadama, dan Allah kuyi haƙuri da abun kunyar dana aikata, Nima ba halina bane ƙawayene suka tunzurani har na faɗa harkar" zubewa tayi saman gwiwowinta agaban aneelerh tana kuka tace"Tun da nake a rayuwata wani ɗan adam bai ta6a yi mini nasihar data ratsa zuciyata ba sai akanki, bansan wacece ke ba, amma nayi sha'awar In yi koyi da kyawawan halayanki, duk naji na tsani kaina, na zubda mutuncina da girmana a idon zahra, wallahi naji kunyar da ban ta6a jin taba, Naji ƙuncin Halin dana jefa zahra, saboda ni tagaza runtsawa Na hana baiwar Allah yin bacci na hanata cin abinci, na jefa rayuwarta cikin ƙunci batare da nayi tunanin raɗaɗin da zataji acikin Zuciyarta ba, wallahi nayi nadama koda ace bazaku yarda dani ba, Na tuba kuma in sha Allah bazan ƙara aikata zunubin nan ba, angama bi'iznilillahi, saboda inaso Inyi kyakkyawan ƙarshe kuma inaso in tsira ranar gobe ƙiyama, In sha Allah daga yanzu nagama yin amfani da dukiyata don in sa6awa Allah, da kuma gur6ata tarbiyar ya'yan mutane....."daƙyar ta ƙare maganar tana faman jan magina.

Ba Aneelerh ba hatta Mahboob Yayi mamakin wannan Ikon Allahn, sun yi sototo suna kallonta kamar sakarkaru duk ta zama abun tausayi tsoron Allah ya shigeta, wata'ƙil dama itace silar shiriyarta shiyasa Allah Ya haɗasu da ita.

Muryar Hajiya falmata na rawa tace"Ku taimaka mun dan Allah, inason in wanke kaina awurin zahra, saboda inason taci gaba da kallona kamar yarda tasanni ada, Nayi alƙawarin zan taimakamata, kuɗin da ku ka zo dasu na yafe mata ku ɗauka ku maida mata su, Sannan inaso taci gaba da yin aiki a company dina, Kayan da suke son ayi masu order A dubai gobe in sha Allah zasu iso Nigeria"

Kallon juna mahboob da Aneelerh suka ƙara Yi, Atare suka furta Alhamdulillah, Aneelerh tace"nagode ma Allah daya bani baiwar Iya tsara kalamin da har suka ja hankalinki, Naji daɗi dana zama silar shiriyarki, Ina fata zaki canza rayuwarki daga Yau ki koma ta gari, wadda kowa zaiyi alfahari da ita"

Jinjina kai Hajiya falmata tayi Cikin sanyin murya tace"in sha Allah," ruƙo hannayenta aneelerh tayi acikin nata, miƙewa tayi tsaye suna fuskantar juna "Ki godema Allah, saboda Yana son ki da shiriya shiyasa Ya baki damar gyara rayuwarki tun da sauran numfashinki,"

Jinina Kai Hajiya falmata tayi. Aneeleerh ta ƙara da cewa"sai dai kiyi haƙuri, ba zamu maida kuɗinba, nariga dana kawo maki dasu, Ki ruƙe su a hannunki, zahra kuma bazata ƙara Yin aiki a companynku ba, zan nema mata aiki awani wurin"!!

Magiya hajiya falmata tadinga yi mata akan tayi haƙuri su koma da kuɗin, ta yafe masu, amma Aneelerh taƙi yarda, mahboob ne yace ta jira zasu yanke shawara a tsakaninsu, ruƙo hannun Aneelerh yai acikin nashi yajata zuwa gefe ɗaya akwai tazara tsakaninsu da hajiya falmata, tayi kasake tana kallonsu "Aunty aneelerh tunda tace ta yafe kuɗin mu koma dasu kawai, ai ba roƙonta mukayi ba" Girgiza kai aneelerh tayi"nidai hankalina bai kwanta da matar ba, wallahi irinsu shaiɗanune Mahboob, inajin tsoron ace wani tuggun zata kitsa mana shiyasa tace ta yafe kuɗin, ƙwara mu maida mata aniyarta" Yamutsa fuska mahboob yai"aunty aneelerh just ki gane, ni dai na yarda da ita, sau dayawa zaki ga mutun yana aikata ba daidai ba idan Allah yaso shi da rahama saiki ga ya shiryu cikin sauƙi batare da ansha wahala ba, Yanzu ki duba matar can, hada fa kukanta kuma har zuƙunnawa tayi saman gwiwowinta tana roƙonmu, why bazamu yafe mata ba? Komai ya wuce, ita kanta zahran ba ƙaramin daɗi zataji ba saboda tana son fatima ƴarta aminnan junane tun tuni, sannan taci burin zuwa obie estate, bayan haka aikin nan da take Yi a companyn su ba ƙaramin ƙaruwa take Yi ba, ita kanta tana faɗi da bakinta irin alheran da take samu ta silar aikin da suke Yima mutane, idan ma da wata manufa tace hakan to mu barta da Allah, In sha Allah babu abunda zata Iya yi mata," gyaɗa kai Aneelerh tayi"shikenan na amince da buƙatarta, mu koma mu faɗa mata" komawa sukayi cikin falon, bayan sun sanar da ita shawarar da suka Yanke ta dinga yi masu godiya farin ciki duk Ya cikata, kafin tafiyarsu saida ta roƙe su alfarma akan su taimaka mata, tana so zahra taci gaba da ganinta a matsayin mahafiyarta, tasan ayanzu bata da sauran mutunci a idonta. Aneelerh ce tabata shawarar yadda zata tsara ma zahra, duk don ta amince da cewa ba halinta bane, sun jima agidan kafin daga bisani sukayi mata sallama, sunyi rabuwar mutunci da hajiya falmata, har musayar number sukayi da Aneelerh saboda acigaba da zumunci.

( kunji abun da Ya faru, kafin washe garin ranar da zahra taje kaima Hajiya falmata kuɗinta)

Wuraren ƙarfe takwas na dare, motar drivern da yaje dauko su Alhaji ubaid daga airport ta kunno kai gate din gidan, tunkafin ƙarasowarsu, Dr Shureim da zeenatu suna atsaye bakin Entry hall din falo, hannunsu ruke cikin na juna, daga ita har shi jallabiyace ajikinsu, ta yafa mayafi akanta, tsantsar farin cikine akan fuskokinsu, sunyi matuƙar ƙagara da son ganinsu. Zeenatu sai faman washe baki take Yi, tunda tayi tozali da motar dake shigowa tana tunkaro bakin entry hall din Da zamudi tace"ya shureim kana ganin aunty benazir zata Iya gane ni kuwa? Saboda mommy ta fadamin tun ina jaririya ta 6ace ba'a ganta ba" Fuskarshi dauke da murmushi yace"idan ma bata gane ki ba, da zarar anyi mata bayani zata shaidaki, zan faɗa mata cewa zeenatu ce ɗiyar uncle musa, and my wife to be" tuntsirewa tayi da dariya taji daɗin maganarshi, muryarta da shagwa6a tace"amma ya shureim ai ni banaso ka faɗa mata, wallahi kunya nake ji, ko mommy layla ma kada ka fada mata please da daddyn ku" ta faɗa tana duban face dinshi. "Ai ni nafiso suji My zeenatu, saboda a fara shirye shiryen shafa fatihar auranmu" zaro mashi blue eyes dinta tai kafin tai saurin sanya tafukan hannayenta biyu ta rufe fuskarta cikin jin kunyar maganarshi ta furta"dan Allah yaya shureim dina kada ka fada masu yanzu, nidai kunya nake ji"

"Kunya kamar bafullatana, kin manta mommynki baturiya ce, daddy musa kuma Hausa fulanine, kakarmu bafullatana ce kakan mu namiji kuma bahaushe ne, Ni bansan inda kika gado Kunyar nan taki ba, a haka zamuyi aure kina jin kunyata"?

Kafin ta bashi amsa, motarsu Alhaji ubaid ta ƙaraso gab dasu, bayan drivern yai parking, da sauri Dr shureim Yaja hannun zeenatu suka ƙarasa bakin motar, yakai hannu ya buɗe masu murfin back seat, a hankali ta zuro da ƙafarta dake sanye cikin takalma, ƙarasa fitowa tayi tun daga ƙasa dr shureim yake binta da kallo, wankan atamfa ne a jikinta riga da skirt, ta kashe daurin dankwalinta, yalwatacciyar sumar kanta ta sauka gadon bayanta, gyalen asaman kafaɗa ta yafa shi, idan kaganta ahaka bazaka ta6a ce wa ta ta6a yin aure ba, kamar budurwa saboda babu abunda ya canza a jikinta, dama bata ta6a shayarwa ba.

Wani irin kallon so da ƙaunar ƴan uwantaka suke jefa ma juna tsakanin ta da shureim, idanuwan kowannansu ya ciko tab da ƙwalla, La66anshi na kerma ya furta sunan ta"be.. Nazir! Yar uwata rabin raina, Jinin jikina Dagaske ke ce idanuwana suke nuna min? Fashewa tayi da matsanancin kuka, gaba ɗaya ta faɗa saman chest dinshi, ya zagayo da hannayenshi biyu ya rungumeta tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi, Zeenatu dake tsaye tana kallonsu hawaye tuni sun wanke fuskarta, tsananin tausayin benazir ne Ya kamata, Fitowa Alhaji ubaid yai daga cikin motar shida Hajiya layla, ya dauki wankan shadda, itama layla Atamfar ce ta sanya sunyi anko da benazir hatta daurin dan kwalinsu da mayafin da ta daura a kafaɗa iri dayane dana benazir, idanuwansu na akan dr shureim da benazir, sun ƙanƙame juna sai kuka sukeyi kamar waɗanda suka rasa mafaɗi a duniya, zagayawa zeeenatu tayi ta 6angaren da su hajiya layla suke koda sukayi arba da ita, Hajiya layla ta buɗe mata hannu da fara'a akan fuskarta take fadin"Zonan My daughter zeenatu" kamar jira take yi da sauri ta ƙarasa ta faɗa jikin Layla, rungumeta tayi sosai, tana dan bubbuga bayanta ta furta"kin ƙara girma daughter, tsawon lokaci bamu haɗu ba, Daddynki Ya hanaki zumunci da ƴan uwanki, baison kina taka wajen mu, gashi mu kuma muna ƙaunarki" ta faɗa tana raba jikinta da na zeenatu, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, kallon Alhaji ubaid tai"sannunku da zuwa daddy" miƙa mata hannu yai da sauri ta ƙarasa gare shi, Yai hugging dinta yana fadin"fatan mun same ku lafiya," ɗagowa tai da kanta tana fadin"Lafiya lou daddy mu shiga daga ciki" Drivern daya daukosu Yana daga tsaye ya jingina bayanshi jikin motar, Yace"yalla6ai ku ƙarasa shiga gidan, za'a shigo maku da kayan naku" amsa mashi sukayi da toh, layla tace da su shureim ayi haƙuri adaina kukan ya isa haka mu shiga cikin gidan inyaso kun ƙare kukan naku acan" Alhaji ubaid na murmushi yace"ke ko kibarsu mana, An daɗe ba'a haɗu ba, Jini ɗaya ba wasa ba, mundai godema Allah daya bayyana mana ita da ranta da lafiyarta ubangiji Allah Ya ƙara tsare mana ita, layla da zeenatu suka amsa mashi da ameen, Gaba suka fara Yi, Ya rage saura zeenatu data ƙura ma benazir da shureim ido.

Ta kwantar da kanta saman kafadarshi, yayin da hawaye masu ɗumi suke cigaba da wanke fuskarta, cikin muryar kuka take fadin"yaya shureim nayi danasanin duk wani abu daya faru arayuwata, wallahi nayi danasani mara amfani, bansan meke damunaba, hakanan na tafi nabar dangina nabar mijina, babban takaicina ƴar jinjirar dana bari cikin jini, na haura ƙafa na tafi nabarta saboda rashin hankali irin nawa, bansan meyasa na aikata hakan ba" cikin jin ƙunar rai ta ƙare maganar. Ɗaura hannunshi yai saman bayanta cikin rauni na murya ya soma magana"kiyi haƙuri benazir, wallahi ba laifinki bane, ni nasan duk rashin jin maganarki bazaki ta6a iya aikata hakan ba, Ina yi maki kyakkyawar zato, ki kwantar da hankalinki My sister" cikin kwantar da murya yake lallashinta Shessheƙar kukan zeenatu ne Ya janyo hankalinsu ga kallonta, idanuwanta sunyi luhu luhu, da mamaki akan fuskar benazir ta furta"yaya shureim a ina muka samu kyakkyawar matashiyar baturiya"? Fuskarshi dauke da murmushi yace"zeenatu ce, nasan ba lallai kisanta ba, saboda ba'ajima da haihuwarta ba ki ka tafi, ɗiyar uncle dinmu ce, ki kalli fuskarta dakyau"

Farin cikine Ya lullu6e benazir, Yarinyar ta burgeta, Gata ƴar kyakkyawa da ita, miƙa mata hannu tai zonan ƴar uwata, Ina fata an fada maki wacece ni, idan ma ba'a sanar dake ba toh nidai sunana benazir, Ƙanwar dr.shureim" fashewa Zeenatu tayi da dariyar farin ciki, Hawaye nabin fuskarta. "zonan In rungumeki ajikina, Nima yau inji ɗumin ƴar uwata" jiki Na rawa zeenatu ta nufi benazir suka rungume juna kamar zasu koma mutun ɗaya Cikin shessheƙar kuka Zeenatu take fadin"Aunty benazir munyi kewarki sosai, Mommyna tana bani labarinki, najima ina son ganinki arayuwata, duk da bamu ta6a haɗuwa ba amma kullum idan nayi sallah sai nayi maki addu'a Akan Allah Ya bayyanar mana dake idan kina araye, Idan bakya araye Allah Yajiƙanki yakai rahama agareki, ashe da rabon zamu haɗu...."dakyar ta ƙare maganar saboda kukan daya cimmata, daga ita har benazir din kukan sukeyi, Kalaman zeenatu sunyi matuƙar ta6a mata zuciyata, tayi mamakin irin ƙaunar da take Yi mata, ita da bata ta6a ganinta ba, labarinta kaɗai aka bata, haƙika taji dadi mara misaltuwa, kaunar zeenatu ta shigeta, tayi fatan Ace itama ƴarta data bari tana yi mata addu'a.

"Aunty benazir dan Allah kada ki ƙara tafiya kibarmu, wallahi muna kaunarki nida mommyna" sosai benazir ta fashe da kuka tana fadin"in sha Allah bazan ƙara tafiyaba, nadawo kenan zeenatu, naji dadin kalamanki agareni, ƴar uwata rabin raina" Dr.shureim Ya natsu yana kallonsu, idanuwanshi sun kaɗa jawur, hawayen dake gangarowa saman kuncinshi sai ƙara ninkuwa sukeyi. Cikin sanyin murya yace dasu'Mu shiga cikin gidan" amsa mashi sukayi da toh, hannun benazir acikin na zeenatu suka dunguma zuwa babban falon gidan. Lokacin da suka ƙarasa ciki, Alhaji ubaid da Hajiya layla suna a zaune saman sofa mai mazaunin mutun biyu, a yayin da Hajiya sarah ta zauna saman 3 sita, Alhaji musa yana daga zaune gefenta, kamar kullum fuskarshi babu annuri, kamar wanda akayiwa albishir da ranar mutuwarshi, shaddar jikinshi ta zauna mashi launin blue sky, daddadan kamshin turarenshi Ya karade hancin kowa, Hajiya sarah Lace ne ta sanya kalar shaddarshi, head dinta kalar takalman ƙafarta, sunyi kyau abunsu kamar sabbin ma'aurata

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull