Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 57
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 57: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 57. Jin takun tafiyarsu yasa hajiya sarah ta ɗago…
3,216 words
Jin takun tafiyarsu yasa hajiya sarah ta ɗago tana dubansu, wani irin farin cikine ya lullu6eta ganin benazir, Jiki na rawa ta miƙe tana faman sakin fara'a fararen hakoranta tarr dasu ta nufi benazir tana fadin"ashe rai kanga rai? Benazir dagaske kece idanuwana suke nuna min? Wayyo Allahna, Idan ma mafarki nake Yi toh kada atadani abarni in tayi dan Allah" Rungume juna sukayi, Benazir ta fashe da wani sabon kukan bata ta6a tsammanin zata samu kyakkyawar tarba a wurin ahalinta ba, Tabbas sun bata mamaki tayi tunanin kamar yadda ta gudu babu wanda zai saurareta donta dawo gare su. Hajiya layla sai faman sakin murmushi take Yi ita da Alhaji ubaid hankalinsu na akan Hajiya sarah data rungume benazir, Shi kuwa Alhaji musa ko kallo bata ishe shi ba, tamkar baisan sun shigo falon ba.
"Allah sarki benazir, Ashe da rabon zamu sake ganawa a duniyar nan! Tsawon shekaru sai yau Allah Ya nufa zan ƙara Yin tozali dake" ta fada tana duban benazir da hawaye suka gama wanke fuskarta Cikin shessheƙar kuka tace"Aunty Sarah nayi danasani, naji haushin kaina, naji na tsani kaina saboda komai ya faru arayuwana laifina ne, tunda nida kaina na gudu na tafi batare da nayi shawara da kowa ba, Dan Allah ku yafe min, nasan na 6ata maku rai" Idanuwan hajiya sarah tuni sun cicciko tab da ƙwalla, kasancewarta mace mai tausayi. Cikin karyayyar murya ta furta"dan Allah ki daina fadin hakan, Komai ya riga daya faru kuma ya wuce"
Kafin benazir ta kuma yin magana muryar Alhaji musa ta katse masu hanzarinsu "Idan kun gama jimamin, ku ƙaraso ku zauna" cikin isa Ya furta hakan, sai lokacin Benazir ta ɗago da ido tana dubanshi, Ya haɗe rai babu annuri sam a fuskarshi, gani take kamar baiyi farin ciki da dawowarta ba. Ruƙo hannunta Hajiya sara tayi acikin nata, suka ƙarasa tare da samun wuri kowannansu ya zauna, zeenatu da dr shureim suna zaune saman lallausan carpet, Benazir kuma tana agefen hajiya sarah, ta ƙankame hannunta. A tsanake Alhaji musa Yasoma yin magana batare daya ɗago da ido ba "Da farko, Inayi maku barka da zuwa, yayana da kuma hajiya layla,' kwa6e fuska layla tayi aranta tace"dallah jibarshi ɗan rainin wayau" Numfasawa yai tamkar bayason buɗe baki Ya furta"benazir," amsa mashi tayi da na'am. Dawo nan ki zauna" yai maganar yana Nuna saman carpet daga gefen hannun sofa din da yake zaune, jiki asanyaye ta miƙe ta dawo inda ya bata umarni ta zauna. Kowa ya natsu yana jiran jin me Alhaji musa zaice da ita. "Meyasa kika gudu daga gidan auranki har na tsawon shekaru baki nemi kowa ba"? Kafin benazir ta bashi amsa hajiya layla tayi saurin cewa"Bai kamata kayi mata wannan tambayar ba, kodai mu da muke Iyayenta bamu tambayeta komai ba, duba da halin da tadawo gidan" Ranshi a matuƙar 6ace ya dago da ido Yana binta da matsiyacin kallo batare daya furta komai ba Sai Alhaji ubaid ne yace"wannan maganar bata shafeki ba, tsakaninshi da ɗiyarshine don haka ki daina sanya masu baki" harara ta wurga ma Alhaji ubaid"kaima ka sani bazan ta6a rufe baki na ba, akan me zai tambayeta meyasa ta tafi? Lokacin da ta gudun ya nuna damuwane akanta? Ko kuwa ya bada gudummuwar da za'a nemota ne eye? Daga zuwanmu gidanshi zai tsareta da tambaya? Dama ya kira mune don Ya tuhumi ƴar mu badan Ya tayamu murnar ganinta ba" tunda tafara zazzaga masifa hankalin hajiya sarah dana zeenatu ya tashi haiƙam, shi kanshi shureim jikinshi yai sanyi laƙwas, benazir dai ta saddar da kanta ƙasa hawaye na cigaba da wanke fuskarta.
Lallashinta Alhaji ubaid Ya soma Yi, Alhaji musa kuwa sai faman jinjina kanshi yake Yi, Yama rasa bakin magana
Hajiya sarah na faman yarfa hannu tace"dan Allah kiyi haƙuri aunty, idan ranki ya 6aci, nasan ba'a kyauta ba, Ni tun farko banso yace kuzo nan ba, har magana nayi mashi akan mu yakamata mu taka muje tayaku murna amma ya hanamu zuwa...." daƙyar ta ƙare maganar ganin irin kallon da Alhaji musa ke binta dashi, ba arziƙi taja baki tayi shiru
Jinjina kai yaɗanyi kafin ya ɗaura da cewa"Allah Ya huci zuciyarki Hajiya layla, Naji bazan ƙara tambayarta ba," tayi mamakin jin abunda yace, har saida ta kalli cikin idonshi, murmushin gefen fuska yasakar mata afakaice, kafin Ya maida dubanshi ga benazir"ina yi maki barka da zuwa My daughter, naji daɗi da kika yi tunanin dawowa gida, ki kwantar da hankalinki, kuma ki share hawayenki, abunda ya faru ya riga daya wuce" Ajiyar zuciya benazir tadan sauke, cikin sanyin murya ta soma magana"nagode uncle, sannan idan na 6ata maka rai, kayi hakuri, nasan komai ya faru laifinane, dana kama hanya na tafi" Lumshe idanuwanshi yadanyi kafin ya waresu akan fuskarta"kada ki damu ni ban ruƙe ki araina ba, kawai dai banji dadin guduwar da kikayi bane na tsawon shekaru batare da kin tuntu6emu ba, amma yanzu tunda kin dawo da ranki da lafiyarki falillahil hamdu, sai dai fatan Allah ya kyauta gaba, In sha Allah zanyi ƙoƙari dan ganin na inganta maki rayuwarki, duk wani abu da kike buƙata ki sanar dani zanyi maki shi, kada ki ƙara yunƙurin guduwa saboda muna buƙatarki, zaifi ki sanar damu idan ma wani abune ya 6ata maki rai a tsakaninmu zamu Iya sama maki solution, Ina fata kina jina" Ɗaga mashi kai tayi alamar eh, lamarin Alhaji musa ya ɗaurewa hajiya layla kai, bata ta6a tsammanin ya iya tsara kalami irin haka ba, hatta Alhaji ubaid yai mamakin yadda ya sakar ma benazir fuska yana yi mata magana cikin lallami, aranshi ya ayyana wata'ƙil tsananin tausayinta ne Ya kamashi, yaji dadin hakan, hankalin hajiya sarah ya kwanta dana zeenatu, sai faman sakin murmushi suke Yi, haka zalika dr.shureim shima murmushi ne akan fuskarshi. "In sha Allah uncle bazan ƙara yunkurin guduwa ba, duk runtsi duk wuya zan zauna atare daku, nima nayi danasanin abunda na aikata, Gyaɗa kanshi yai, Hajiya sara tace"tun ɗazu fa na sanya masu aiki sun shirya maku lafiyayyan abinci, yakamata muje muci kada ya huce" da fara"a akan face dinta ta furta hakan, Miƙewa sukayi atare suka dunguma zuwa dining room, benazir ta girgiza da ganin daular uncle musa, Gidan Ya tafi da imaninta. Saman dining chairs suka zazzauna, ga kayan abinci an jera masu saman table," Tani da lami ne suka zo domin yin serving dinsu, Bayan sun gaishe da alhaji ubaid da hajiya layla, suka soma zuzzuba ma kowannansu abunda yake ra'ayin ci, hankalinsu kwance suke ci baka jin sautin komai saina ƙarar cokulansu. Jefi jefi zeenatu take satar kallon benazir da zarar sun haɗa ido sai ta sakar mata murmushi, Ta fahimci yarinyar ba ƙaramin so take Yi mata ba, Dr shureim na kallonsu, shima murmushine akan fuskarshi, Hajiya layla dai taƙi sakewa, itafa har yau har gobe bazata ta6a yadda da alhaji musa ba, gani take yi kamar akwai wata manufa atare dashi, abincin ma daƙyar take cin shi"
Bayan sun kammala cin abinci, Hajiya sarah ta rakasu zuwa masaukinsu da zasu zauna, Hadaddun bedrooms aka ware masu, Zeenatu ta hana benazir sakat, tsabar Iyayi hada ɗauko bargonta da pillow ta dawo down stair dakin benazir donsu dinga kwana atare, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,
*SIR MUBARAK✊*
Yana acikin dangi suna ta yin firar yaushe rabo tare da Ƴan uwanshi, Wayarshi dake acikin aljihunshi ta soma Yin ruri, kusan sau uku kiran na shigowa yana yin rejecting batare daya ankare ba, saboda hayaniyar ƴan uwan shi da suke Yin fira a tsakaninsu, a babban katafaren falon gidan, a kira na huɗune, Senate lateef dake zaune gefenshi ya ankarar dashi ta hanyar yi mashi magana ka duba wayarka tun dazu nake jin sautin ringing ɗinta, amsa mashi yai da toh, sai da ya fara curo wayar ya duba sunan mai kiran nashi tukunna ya mike yai masu sallama Ya nufi ƙofar fita daga babban falon, bayan ya fitone Ya dakata da yin tafiya, Yabi kiran da aka yi mashi, bugu ɗaya aka ɗaga kiran "Major, ince dai lafiya? Naga miss call dinkane" On the other hand major yace"yalla6ai yaron nan na wurinka jazz Ya fita daga gida Yanzu haka da nakeyi maka magana munbiyo bayanshine muna asaman titi," Cikin saurin murya sir mubarak yace"gani nan zuwa, kubi a hankali kada ku bari yaganku yaron wayau ne dashi, yanzu zamu biyo diddiginku" tunkafin maijor ya amsa mashi yai saurin yin rejecting call din, Ya dannawa driver dinshi Kira bugu ɗaya ya daga"Ina jiranka abakin entry hall na gidan baba, kazo da mota ka daukeni" Ya ƙare maganar tare da kashe kiran, Jikin shi har tsuma yake yi fatan shi Allah ya basu nasarar kama jazz don ganin menene yake aikatawa, Badajimawa ba baƙar mota ƙirar Range rover ta shararo da matsakaicin gudu bata nufi ko'ina ba sai bakin entry hall adai dai nan Tiger Yai parking dinta, Jiki na rawa sir mubarak Ya buɗe front seat na motar ya shige tare da bashi umarnin su tafi, reverse yai kafin ya karya kwana Ya nufi tanƙameman gate din fita daga estate din dake a kewaye da jami'ai, tunda suka hango sir mubarak ta tagar motar basu yi gigin dakatar dasu ba, kaitsaye motarsu ta haura saman titi, da gudun gaske tiger yake driving dinsu tamkar zasu tashi sama, sir mubarak yai amfani da phone dinsa wurin bin diddigin su major, cikin sa'a suka samo location din da suke, dare ne tamkar da rana saboda hasken street light daya gauraye ko'ina, hanyar da suka biyo kwata kwata babu mutane, sababbin gine gine ne a unguwar, wani ginin ma ba'a kammala shi.
Rage gudun motar tiger yai ta hanyar glass din motarsu suka hango motar major tana tafiya a hankali ga dukkan alamu sun ƙaraso inda dr jazz Yake shiyasa suka rage speed din motar, bayan major yai parking din motarsu, kusan atare suka fito shida wani matashin saurayi dukansu suna asanye cikin kakinsu na sojoji, daga bayan motarsu Tiger yai parking din tasu motar, fitowa sukayi atare shida Sir mubarak, koda su Major sukayi arba dashi a hanzarce suka buga ƙafa tare da sara mashi, Jinjina masu kai Yai yayin da yake bin gine ginen da kallo Ya ce"ina ku ka ga jazz din Ya shiga"? Ya jefa masu tambayar cikin ƙagara da sonjin amsarsu.
Major yace"Wancan gidan mai jan gate Ciki Ya shiga" yai maganar yana nuna wani katafaren gida, Da sauri Sir mubarak Ya nufi gate din, Major da Army din da suke atare kowannansu Ya zaro bindigarshi, shima Tiger Ya curo tashi pistol din, gefe da gefen sir mubarak Suka Jera sun saita bindugunsu saboda tsaro gudun kada akawo masu hari tunda basusan adadin miyagun da yake mu'amala da su ba, Cikin sanɗa suke tafiya suna bin ko'ina da kallo, ta ƙofar jikin gate din da aka bari abuɗe suka shiga, babu kowa abakin gate din tamkar anyi shara, Sir mubarak yace"Anya major akwai mutane acikin ginin nan? Naji shiru babu motsin komai, kodai kunyi kuskurene"? Girgiza kai major yai"Yalla6ai tabbas cikin ginin nan ya shigo, ba mu yi kuskure ba, akan idonmu ya fito daga cikin motarshi Ya buɗe gate kafin Ya koma ciki Yajata zuwa cikin gida" Gyaɗa kai sir mubarak Yai"okey mu ƙarasa ciki" kaitsaye suka nufi katafaren ginin da suke tsammanin zasu samu hanyar shiga cikin gidan, adai dai bakin wata ƙofa, suka dakata A hankali Major Ya turo ƙofar cikin sa'a suka sameta abuɗe, ɗaya bayan ɗaya suke shiga, Hadadden palour ne An ƙawata shi da furniture, ga sanyin A.c ta ko'ina mai ratsa fatar jikin mutun. Sunyi mamakin ganin babu kowa a palourn, ko motsin mutun babu, daga cikin falon akwai bene da zai kai mutun up stair, yanke shawarar haurawa saman benan sukayi, Cikin sanɗa suke tafiya kowa ya saita bindigarshi saboda tsaro, a second floor suka dakata da yin tafiyar suna bin ko'ina da kallo, ƙofofin ɗakunane ta ko'ina, Sam sun kasa motsawa saboda sunfara kokwanton anya akwai mutane agidan Tiger yace"shirun yayi yawa, kada fa ace tarkone aka ɗana mana don mu afka" Major yace"ai shi soja da kasada akasanshi, Idanma tarkon ne suka shirya mana to bamu bane zamu rufza aciki ba, sune zasu afka, wata'kil watan tonuwar asirin su ne Ya kama"
Sir mubarak Ya natsu Yana sauraronsu, ya rasa madafa sam bayason suyi kuskuren shiga gidan mutane, don ya fara kokwanto. Army yace"yakamata mu fara dudduba ɗakunan nan wata'ƙil mu same shi aciki" Ya furta hakan tare dakai hannu Ya buɗe ƙofar ɗaki Ɗaya, karaf idanuwanshi suka sauka akan matasan Ƴan matan dake akwance saman bedmattress, cikin shiga ta kayan bacci"a matuƙar ruɗe ya juya yana kallon Sir mubarak Ya furta"yalla6ai ƴan matane kwance saman gado, Anya kuwa bamuyi kuskure ba"! Matsawa sukayi zuwa bakin ƙofar da Army yake a tsaye, kowan nan su Ya leƙa Sun yi mamakin ganin kyawawan ƴan mata kwance suna sharar baccinsu farare tass dasu kamar jinsin larabawa. Rai amatuƙar 6ace sir mubarak ya dubi Major"kace min nan jazz ya shigo to yana ina? Waɗannan ƴan matan alamace dake nuna cewa Gidan wani ne muka faɗo" Tuni major yasha jinin jikinshi, Muryarshi adabarbarce ya furta"yalla6ai wallahi da idona naganshi Ya shigo gidan nan, Ga army nan ka tambaye shi, ai tare dashi muka shigo, kuma shima yaga jazz din" Yai maganar yana nuna army da hannun shi Kallon Army sir Mubarak Yai, da kakkausar murya ya furta"idan har kukasa naji kunya wallahi zakuji ajikin ku ne" hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, Jin abunda yace masu, Guntun tsoki Yaja tare da juyawa da niyar Ya fuce daga gidan, kwatsam ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka soma Jiyo masu shessheƙar Kukan mace cikin murya mai ƙaraji take fasa ƙara tana fadin"Bana so! Ka ƙyaleni Nace maka banaso, Ni ka ƙyaleni, ka sake ni ka rabu dani...." sautin gigitacciyar ƙarar data fasa gaba ɗaya Ya cika ginin, Kallon juna sojojin sukayi kafin da gudun gaske suka nufi Hanyar da suke jiyo sautin kukan Yarinyar, Sir mubarak kamar zai yi tuntube, cikin zafin nama suka haɗa ƙarfi wurin bangaje ƙofar ɗakin, A tsiyace ƙofar ta bude, Hankalin sir mubarak Idan yai dubu to ya tashi, A matuƙar gigice sojojin suke kallon abun da ke faruwa, Lamarin yai matuƙar ɗaga hankulansu, musamman Sir mubarak Ya gaza yadda da abunda idanuwanshi suke nuna mashi, Tuni zufa ta soma wanke fuskarshi, Sam baiji motsin shigowar mutane ɗakin Ba, Ya duƙufa akan abunda Yake aikatawa, Rigar shaddar shi da wandonshi gaba daya suna asaman floor, Singlet ce kaɗai a jikinshi sai gajeran wando Fari, Ya haɗa uban gumi, matashiyar yarinyar daya danne saman gado sai kuka take Yi, tana bugun bayanshi da hannayenta, A wahalce take harba ƙafafuwanta cikin fitar hayyaci kamar ranta zai fita, ta gama galabaita, tuntana kukan neman agaji har muryarta tafara disashewa, wani irin kukan kura sir mubarak Yai cikin zazzafan taku Ya kutsa kai Cikin ɗaki, da hannayenshi biyu ya damƙo wuyar singlet din Jazz da ƙarfin gaske Ya wurgar dashi kasa gaba ɗaya ya kife kanshi ya daki tiles, Jiki na kerma ya ɗago yana dubansu ɗaya bayan ɗaya kafin ya tsayar da idanuwanshi akan fuskar Sir mubarak dake tsaye kanshi tamkar mayunwacin zaki, hankalinshi yai matuƙar tashi da ganinsu duk yabi ya ruɗe ya susuce, jikinshi ya hauyin kerma, sai faman zazzare idanuwanshi yake Yi, Muryarshi na kakarwa ya furta"daddy...." bai ƙarasa maganar da zaiyi ba, Sir mubarak Ya damƙo wuyanshi ya ɗago dashi tsaye cikin rauni na murya ta wanda ya karaya yake fadin"Jazz ka kasheni, Ka cuceni, dama abunda kake aikawata kenan? Ƴan mata kuke tarawa acikin gida, donku lalata rayuwarsu sannan ku kashe su? Nasha kama ka kanayin waya kana fadin kaji ashe mutanene kajin, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un" cikin jin ƙunar rai yace"Wallahi baka isa ka ɗaura min hawan jini baa, Kafin ka kasheni ni zan fara kasheka don ubanka, Mugu azzalumi fasiƙi, Jazz ka bani mamaki, ka cuce ni kuma ka cuci mahaifiyarka,' Cikin shessheƙar kuka Sir mubarak Yake furta maganar, Ya shaƙe wuyan Jazz sai faman mutsu mutsu yake Yi, don ya ƙwaci kansa.
Yayin da sojojin suke a kewaye da gadon da yarinyar take, duk tabi ta tsorata jikinta sai kerma yake Yi, short gown ce a jikinta, yalwatacciyar baƙar sumar kanta duk ta rufe gefe da gefen fuskarta, tamkar wadda tasha gudu sai faman yin haki take Yi. Sautin ƙarar da jazz Ya fasane Ya janyo hankulansu ga duban shi, wani irin radadin azabane Ya ziyarce shi sakamakon buga kanshi da sir mubarak Yai jikin Mirror din dakin, gaba ɗaya madubin Ya zube, Jini Ya wanke fuskar Jazz hatta gaban farar shirt din jikinshi Yayi ca6a ca6a da jinin shi, daddafe kanshi yai da hannu bibbiyu cikin mawuyacin hali Yake sambatu "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Daddy ka kashe ni, Na shiga uku na bani na lalace, daddy ka rabani da rayuwata" Yarinyar dake zaune saman gadon, ganin yadda suka raunata shi yasa ta fasa ƙara da ƙarfi ta furta"yaya Jazz, Wayyo Allah na kun kashe min shi, mugaye azzumai baiyi maku laifin komai ba amma kuna cutar min dashi" Da gudun gaske ta duro daga saman gadon ta kife ƙasa, sam babu natsuwa atare da ita, da rarrafe ta ƙarasa gabanshi, Ta sanya hannu biyu ta ɗago dakanshi ta daura saman laps dinta, Cikin shessheƙar kuka take fadin"Wallahi Allah bazai barku ba, Ku baku da burin daya wuce ku cutar da rayuwar waɗanda basu ji ba basu gani ba, Sai Allah ya saka mashi, ku dukanku sai kun shiga wuta" ta fada tana nuna su da yatsan hannunta, kallon juna sojojin sukayi, sunyi matuƙar girgiza da jin kalaman Yarinyar, sun fara kokwanton Anya kuwa Zargin da sukeyi mashi gaskiya ne? Tayaya yarinyar da ake cutar da rayuwarta, kuma take fada don an ta6a mutumin dake ƙoƙarin rabata da mutuncinta!! Fashewa tayi da kuka Hannayenta tuni sun 6aci da jinin dr jazz tana kuka tana ambaton sunanshi"yaya jaz dan Allah kada ka mutu kabarmu, wallahi idan ka mutu nima saina kashe kaina" Zuciyar sir mubarak ce ta soma harbawa da ƙarfin gaske, Jiri ya soma ƙoƙarin kwasarshi, Gaba ɗaya ya gama rikicewa, Hankalinshi atashe Yake kallon Kwalaben alluran dake ajiye saman bedside drawer tare da sirinji, hada magunguna, Adaddafe Ya nufi drawer din da niyar Ya duba kwalaban don ganin na menene, sautin ringin wayar Jazz ne Ya dakatar da shi, da sauri ya daura rinannun idanuwanshi inda yake jiyo sautin daga cikin aljihun wandon shaddarshine, Major ne yai saurin daukar wandon Ya binciko wayar cikin aljihun, Ya miƙa ma sir mubarak, yatsun hannun shi na kerma ya ruƙe wayar, batare daya duba sunan mai kira ba Yai picking call din Ya sanya kiran handsfree.
Sautin muryar mutumin dayaji tayi matuƙar gigitar dashi, har baisan sa'adda Ya saki wayar jazz ta fadi saman floor, sojojin dake atare dashi duk sun sha jinin jikinsu, kallon kallo suka soma Yi a tsakaninsu, cikin matsanancin tashin hankali, sautin shessheƙar kukan matashiyar ya cika dakin, dr jazz tuni Ya jima da sumewa.
*EX-PRISONERS💔*
Gaba ɗayansu sun hallara a dining room, domin cin abincin Dinner dinsu, mutun ɗaya ne ke babu acikinsu, Yana can dakin shi, mazan suna fuskantar matan, sunyi shiga kala ɗaya wandon jeans da farar shirt,matan kuma dogayen rigunane a jikinsu, Aunty ummi ce kaɗai ta banbanta dasu, riga da skirt ne ajikinta sun matseta, shape din jikinta Ya bayyana muraran, babu mayafi akanta, sa6anin su Batul da sukayi rolling veils.