Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 58

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 58

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 58: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 58. tunda suka zauna Unaisah ta kasa samun sukuni,…

3,332 words

tunda suka zauna Unaisah ta kasa samun sukuni, yanayinta tamkar na mara lafiya, sai faman jujjuya spoon take Yi acikin plate din gabanta, da ke shaƙe da abinci, damuwar duniya ta isheta, sam babu sukuni akan fuskarta, A hankali ta ɗago da ido tana duban fuskokin Ƴan uwanta, tun daga kan Sajeed dake fuskantar Azeeza, suna cin abinci suna kallon juna, har zuwa kan Haris dake fuskantar Hannah, kafin ta kawar da idonta daga kansu ta maida su kan fuskar Naufal da javed, sun natsu suna cin abincinsu, hasken musulunci ya fara shigarsu, komai nasu cikin natsuwa suke yin shi, mayar da idanuwanta tayi akan face din jamimah, bakinta duk ya 6aci da maiƙo, ta samu cinyar kaza saici take Yi kamar tsohuwar mayya, ta cinye tsokar naman, Ƙashin take gwaigwaya kamar babu sauran naman alhalin gashinan saman tray guda aka jera masu chicken legs, girgiza kai tayi kafin ta mayar da dubanta kan Batul dake gefenta, ita dai duniya babu abunda ke burgeta irin taliyar indomie, tun ranar farko data fara cinta, kullum ne in zasu ci abinci saita ci ta, sam bata gajiya, da hannu take nannaɗota kafin ta tura abaki, rantane ya raya mata ana kallonta, dai dai time dinda ta tura taliyar abaki ta ɗago da ido suka kalli juna ita da Angel, da sauri ta haɗiya taliyar, cikin muryar raɗa ta tambayeta lafiya take kallonta? Ko tayi ƙauyancine"? Girgiza kai Angel tayi babu komai kawai burgeni kikeyi idan kina cin noodles da hannu" Gyaran murya ummi tayi masu atare suka ɗago suna kallonta. "Unaisa tun ɗazu na lura kamar bakya jin daɗi, meke damunki ne"? Murmushin yaƙe ta sakar mata"babu komai aunty ummi, ko kinga wani abu ne" ɗaga mata gira tai"ƙwarai kuwa, tun da gashinan kin kasa cin abincinki" Kafin unaisa ta ƙara furta wani abu, Muryar Haris ta katse su "Kodai Danish bashi da lafiyane? Tun jiya da rana ban ƙara ganin ya leƙo waje ba, naso naje na duba shi sai dai karatu Ya mantar da nayi yin hakan" Cikin nuna damuwa Sajeed yace"wallahi yana araina, tun ɗazu da muna awurin kar6ar karatu nake ta tunaninshi, bansan dalilin dayasa baya son zuwa cikin mu cin abinci ba, naga dazu da rana ke kika kai mashi lunch dinshi a dakin shi" ya faɗa yana nuna Unaisah da spoon din hannunshi. Naufal Yace"to me zai hana mu tashi muje ɗakin nashi mu duba su? Ni abunda ke damuna da danish baya son sakewa cikin mutane" Yai maganar fuskarshi dauke da damuwa. Javed yace"ai halinshine tun fil azal, kaima kasan Danish bai cika son zama cikin mutane ba, baison surutu kuma baison ana kallon shi" Gyaran murya Ummi tai masu, Hankalinsu Ya dawo kanta sun natsu suna jiran jin me zatace "Koda ace halinshi ne hakan bai kamata ku ƙyale shi ba, cos barinshi acikin ɗaki zai Iya haifar mashi da wata damuwar, duk da naga Unaisah tana ƙoƙarin dubashi, amma a ƙalla yakamata kuma kuna zuwa wurinshi kodan ku dinga ɗebe mashi kewa, kafin zuwa lokacin da zai saki jikinshi, nasan rashin sabone ke damun shi" Jinjina kai sukayi alamar gamsuwa da bayaninta, Sajeed yace"ku tashi muje dakinshi Inyaso sai mu tafi da kayan abincin mu ƙarasa ci acan" Yai maganar tare da miƙewa, da sauri Unaisa tace"a'a basai mun tafi mu duka ba, Ku zauna ni zanje in taho da shi" amsa mata sukayi da toh, da sauri ta miƙe ta nufi ƙofar fita daga dining room din Miƙewa Batul tayi Ummi tace Ina zuwa? Cikin sanyin murya tace ina so zanbi Unaisah ne" "Ki koma ki zauna, ai tace zasu dawo atare dashi ko"? Amsa mata tai da toh jiki asanyaye ta koma ta zauna. Shiru suka ɗanyi, abincinma sun dakata da cin shi, hakanan suke jin zuciyoyinsu na bugawa, Jemimah kadaice ke cin abinci ta cika masu kunnuwa da sautin taunar abincinta, da gangan take yi duk don ayi mata magana. Harara Azeeza ta watsa mata"dan Allah ya isa haka, ba zaki Iya ci a hankali bane"? Hanna tace"ki daina wahalar da bakinki, dagangan take yi duk don ayi mata magana" tuntsirewa tayi da dariya tana fadin"Eh din kuma gashi kunyi min maganar ba" girgiza kai ummi tayi fuskarta dauke da murmushi take dubanta, hankalinta kwance take yin magana. Kallon da naufal ya jefa matane yasa tai shiru tana ƴan ƙunƙuni. "Kuna burgeni, gaba ɗayanku" ta fada tana nuna su da spoon din hannunta. Batul tace"aunty ummi, kina nufin kina sonmu"? Jinjina mata kai tayi"haka nake nufi," murmushi su naufal suka saki jin abunda tace, Parveen na faman siɗar hannu tace"Aunty ummi ke baki haifi ƴa'ƴa bane, kamar yadda daddyn unaisah ya haife ta? Ko kuwa ita mace bata haihuwane sai maza"? Da mamaki Ummi ta dan zaro ido tana kallon parveen da tayi maganar, sam babu wasa akan fuskarta ita bilhakki take Yin maganarta. "Amma baki da hankali parveen, Kin manta labarin da unaisa ta ta6a faɗa mana ne? Macace take haihuwa ba namiji ba, itama Mommyntane ta haifeta ta jefar da ita cikin wannan abun kalar na toilet din gidan nan, namanta sunanshi" Batul ce tai maganar, Azeeza tace"eh kuwa hakane, Macace ta haifi unaisa ba namiji ba, to aunty ummi ke kin ta6a haihuwa"? tayi tambayar tana kallon ummin america wadda mamaki da al'ajabi suka cikata, sai kallonsu take Yi ɗaya bayan ɗaya, sajeed Ya duƙar da kanshi ƙasa sai faman sakin murmushi yake Yi jin wautar parveen. "Aunty ummi kinyi shiru baki ce komai ba, kina ta kallonmu" Hanna ce ta jefa mata tambayar, ta ƙura masu ido tana binsu da kallon mamaki, "wai kuna nufin bakusan komai ba, game da zamantakewar aure? Atare suka haɗa baki wurin furta"Aure kuma"? Gudun kada suyi wata 6aran 6aramar yasa Sajeed yin saurin cewa"aunty Ummi, Yakamata mu maida hankali akan abunda muke Yi yanzu," Ta6e baki taɗanyi kafin ta furta"okey, " ta fahimci baison maganar dama ta lura yafi su hankali shida Unaisah, bata ta6a ƙagara da sonjin labarinsu ba sai yau, tabbas tana son tasan tarihin rayuwarsu! Ya akai har suka kai wannan shekarun basusan komai dangane da zamantakewar aure ba? batun Yauba ta lura da ƙarancin wayewarsu, kamar babu ƙwalwa akansu, basu iya komai ba, In banda cin abinci da kwanciya bacci sunfi ƙwarewa a 6angaren nan.

_(Ummin america batasan su wanene prisoners ba, Mutanan da suka juri rayuwar kulle tun suna jarirai, basu ta6a ganin hasken rana ba, dare da rana basu da abunyi daya wuce idan ankawo masu abinci sau ɗaya suci sai kuma idan lokacin baccin su Yayi su kwanta, badan Allah Ya ƙaddara zuwan unaisah kurkukun ƙaddara ba, da kuwa abunda zasu aikata sai yafi hakan saboda su din tamkar baƙine a duniyar mutane, basusan komai ba, unaisah itace ta wayar masu da kansu dangane da mutanan duniya da wasu abubuwan da suka shafi rayuwar ɗan adam shiyasa ma har suke Iya sakin jiki suyi rayuwa acikinsu)_

Shin meya faru bayan Unaisah ta fita daga Dining room?

Cikin sauri ta nufi upstair, tunkafin ta ƙarasa ƙofar ɗakin danish ta dinga jin faɗuwar gaba, tamkar zuciyarta zata faso ƙirjinta, jiki na rawa ta nufi ƙofar room dinshi, zura ƙafarta keda wuya cikin ɗakin, taga babu kowa wayam har saman gadonshi babu mutun, sai faman baza ido take Yi tana faman ambaton sunanshi tamkar makoshinta zai 6allo"Danish! danish! my Man! Kana ina"? Shiru babu alamun zai amsa mata, ƙofar toilet dinshi ta tunkara lokaci ɗaya taji sautin gurnaninshi mai matuƙar firgitarwa ya cika ɗakin, cikin jin faɗuwar gaba ta sanya hannayenta biyu da ƙarfi ta ingiza ƙofar ta buɗe, tun daga bakin ƙofar toilet din ta ci karo da singlet dinshi, A hankali take bin ko'ina da kallo har tayi nasarar cin karo dashi kwance acikin kwamin wanka, wanda ke akewaye da glass, ya ƙunshe kanshi cikin kwamin, jikinshi sai kerma yake yi, faɗawa cikin toilet din tayi, Cikin sanyin murya take fadin"My man meke damunka? Meyasa kake yin gurnani? Baka da lafiyane" idanuwanshi dake a lumshe ya buɗesu sun kaɗa jawur dasu tamkar an wanke ƙwayar a cikin jini, Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, sam bata damu da yanayin da zata riske shi ba, Jiki amace ta shiga inda kwamin yake ta zuƙunna agabanshi tana dubanshi, fatarshi tayi wani irin haske naban mamaki, Ya cika kwamin da ruwa mai sanyi, amma saboda tsabar zafin jikinshi yasa ruwan ya koma na zafi.

Idanuwanta tuni sun cicciko da ƙwalla muryarta na rawa ta furta"My man dan Allah kayi min magana meke damunka? Meyasa ka shigo toilet ka kwanta cikin bathtub"? Ta faɗi hakan ne donta fahimci ba wani uziri bane ya shigo dashi toilet dinba, saboda bai cire short dinshi ba, Ahaka ya shiga cikin ruwan duk don ya sassauta zafin da jikinshi yai mashi. Da wata irin kakkausar murya ya furta"Kiyi nesa dani, zan iya cutar dake, bani bane, Ki tafi ki ƙyaleni, bana so in ta6a lafiyar jikinki" zazzare idanuwanta tayi waje tamkar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, muryarta adabarbarce ta furta"me..meyasa kace haka danish? Idan bakai bane to wanene? Nashiga ukuna! dan Allah kadaina furta waɗannan kalaman, Ni nasan bazaka Iya cutar....." kasa ƙarasa maganar tayi sakamakon ganin sa6ar macijin dake tsastsafo mashi saman fatar wuyan shi, Kafin ƙyaftawar ido danish ya rikiɗa ya zama Giant snake fari sol, Jikinsa yana da tsayi da kauri, mai santsi, Ya nannaɗe kanshi cikin kwamin wankan, Wani irin narkeken maciji danƙareran gaske yana da doguwar jela da siraran harshe, tsabar firgici da ruɗanin ganin abunda bata ta6a ganiba Ya hanata motsawa, jikinta ya hauyin kerma zufa ta wanke fuskarta, ko amafarki bata ta6a ganin mutun ya rikiɗa ba sai yau da Allah Ya nuna mata Danish ɗinta Ya canza halittarshi zuwa maciji, girgiza jikinshi yai nan take kwamin wankan da yake acikin shi Ya tsastsage Ya tarwatse, Ya faɗo ƙasa, aikuwa da gudun gaske Unaisah ta fito daga dakin, ta fasa razananniyar ƙara, tana gudu haɗi da yin tuntu6e, a matuƙar gigice ta fado saman bene, Mayafin kanta tuni yajima da barin jikinta, Sumar kanta duk ta rufe fuskarta, cikin tashin hankali take tattaka matakalar benan, tana kuka haɗi da ambaton sunan ƴan uwanta Adai dai lokacin Chief Owais Yana saukowa down ta cikin glass elevator, ya kimtsa cikin Dark jeans, daga sama ya sanya button-down shirt, yayin da ƙafafuwanshi ke asanye cikin patent leather shoe, gefenshi Big guy ne hannunshi ruƙe da car key, karaf idanuwan big guy suka sauka akan unaisah dake Faman zumbula gudu tana tunkaro down, ta cikin glass elevator din yake kallonta, kafin yai yunƙurin buɗe baki Yai magana, unexpected danƙareran macijin Ya kunno kai daga ɗakin ya daka tsalle Ya haura ta saman handrail din benan Ya rigata saukowa ƙasa, da buɗar bakinshi sai cewa yai"yalla6ai anya ban fara samun matsalar gani ba kuwa? Kodai tsufane Ya fara kamani"?

THE GIANT SNAKE😳🔥

Tamkar Chief Owais bai ji me big guy yace ba, Hankalinshi baya akanshi, har saida Ya furta"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! yalla6ai maciji nake gani, gashi can Yana tafiya"a matuƙar ruɗe big guy yai maganar, sai lokacin Chief owais Ya ɗaura idanuwanshi kan narkeken macijin dake ta faman jan jiki yana bin floor, Lamarin yai matuƙar ɗaga mashi hankali, tsantsar mamaki da al'jabi ne suka kama shi, Fitowa sukayi daga cikin elevator din tamkar a mafarki suke kallonshi sun gaza motsawa, tsabar ruɗi Yasa Unaisah ta rasa inda zata tsoma kanta, Hannayenta bibbiyu ta ɗaura saman kanta ta ƙware murya da ƙarfi ta furta"wayyo Allah na, nashiga ukuna! danish dina ya koma maciji, dan Allah ku taimaka min" sautin muryarta ya karaɗe ko'ina, hatta su Ummi dake a dining saida suka Jiyota, aiko Da gudun gaske suka soma fitowa daga dining room din, Hankalinsu a matuƙar tashe suka ɗaura idanuwansu akan fuskarta kafin wani yai yunkurin tambayarta lafiya meya faru, Giant snake din Ya daka uban Tsalle Ya haura ta ƙarafunan jikin bene Ya kurɗaɗa hawa Na uku Yabi jikin bango yaci gaba da tafiya ga dukkan alamu hanya yake nema.

Tsabar firgici da tsorone Ya kama su Batul, Azeeza tuni tajima da silalewa ƙasa ta sume, Ummin america jikinta sai kerma yake Yi, tamkar wadda sanyi ya kama, batul kuwa zufa ce ta soma tsastsafo mata, Parveen tuni ta saki fitsari a cikin wando, Jikin jemimah na kakarwa ta ƙanƙame naufal ta fashe da kuka tana fadin"mun shiga uku, wannan katon abun menene, Hankalin kowa ya tashi, da rarrafe Hannah ta lalla6a ta 6oye ƙarkashin dining table.

Unaisah dake atsaye Jiki ba ƙwari sai kuka take Yi tamkar ranta zai fita, Cikin zafin rai take Fadin"Danish ne ya zama maciji dan Allah ku taimaka min banaso wani abu ya same shi, za'a iya cutar dashi nasan bakowa bane zai yarda cewa mutum ne Ya rikiɗa"

Girgiza kai Gabriel Yai, Iduwanshi akan macijin La66ansa na kerma ya furta"taya haka zai yiwu? Danish ya zama maciji? Ko a tarihi ban ta6a ji ba"! Fashe masu tayi da matsanancin kuka"wallahi shine akan idona Ya canza halittarshi, ina maku magana kunƙi ku fahimceni, yakamata muyi wani abu akai danish zai Iya komawa prison" tana magana Hawaye nabin fuskarta, shatun Jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu saman fatarta,gana saman goshinta.

Chief Owais yayi tsaye a yayin da yake bin macijin da kallo, babu alamun tsorata ko firgita atare dashi, sai dai tsantsar mamaki da al'ajabi da ruɗanin da suka kamashi, big guy Har ya yunƙura zai zaro bindigar daya soke a waist dinshi Chief Yai saurin dakatar dashi ta hanyar ɗaga mashi hannu, A hankali Ya furta"Don't shoot him! Can't you hear what she's saying?

Zufa nabin fuskarshi yace"yalla6ai zai iya cutar damu, Maciji ne fa kodai baka ganshi bane"? Batare daya dube shi ba yace"naganshi"

Gaban sune yai mugun faɗuwar ganin yadda macijin Ya haura saman taga ya faffasata Gaba ɗaya glass din Jikinta Ya zazzago ƙasa, Jami'in dake kula da cctv footage din gidan ne suka watso da gudun gaske Cikin shiga ta kakinsu, hannunsu ruƙe da manyan bindigu, kafin owais yai yunƙuri dakatar dasu tuni sun Haura upstairs, sai dai kafin suyi yunƙurin kai mashi hari, Ya daka uban tsalle Ya fado saman floor na down stairs Yabarsu atsaye can saman third floor kamar sakarkaru, Hankalin Unaisa Idan yai dubu toh Ya tashi, Agigice ta fasa ƙara tana fadin"kada ku harbeshi! Ba maciji bane mutunne! Ɗan uwanmu ne danish, dan Allah na roƙe ku kada ku kashe mana ɗan uwanmu, wayyo Allah na Ya Allah ka kawo mana dauki"

Chief Ya kasa buɗe baki Ya dakatar dasu daga yunƙurin harbin shi da suke Niyar yi, Tuni sun saita shi, Kusa atare suka fara Sakar mashi alburishi, tamkar baisan sunayi ba, saima nannaɗe kanshi da yai a tsakiyar falon, Jikin ummi na rawa ta dinga ingaza su batul cikin dining room, da gudu sajeed dasu naufal dukansu suka koma dining din, har zata rufe ƙofa Sajeed Yai saurin furta Azeeza tana awaje, fitowa yai jiki na 6ari ya cuccu6i azeeza ya shigar da ita dining room din, Ummi taja kofa ta datse, duk da haka hankalinta bai kwanta ba, zufa duk ta wanke fuskokinsu, parveen kusan sau uku tana sakin fitsari awando, ta jiƙe sharkaf, bakinta cike da donut data tura takasa ƙarasa haɗiyeshi, kowa fa yasha jinin jikinshi.

Da kakkausar murya ɗaya daga cikin jami'an isod dake acan third floor Ya daka ma Unaisah tsawa haɗi da furta"ki matsa daga nan, Ki koma cikin ƴan uwanki" Fashewa unaisa tayi da kuka tana fadin"wallahi babu inda zanje, saidai ku haɗa dani ku kashe, Nace maku ɗan uwan mu ne ya rikiɗa ba yin kan shi ba ne"

Muryarta adisashe ta ƙarasa maganar, sam bata lura da chief Owais ba saboda bata acikin hayyacinta, tayi tsaye tana faman yin shessheƙar kuka, Umarni Chief Yaba big guy"ka kawar da ita daga gabanshi" cikin jin faɗuwar gaba Big guy ya nufi wurin Unaisah, kafin ya ƙarasa macijin Ya warware jikinshi daga nannaɗewar da yai, da wani irin sauri yake jan jiki Yana nufar ƙarshen falon inda glass door din nan take, fasa ƙara unaisa tayi har ta yunƙura zata bishi big guy yai saurin cafkota, aiko ta daddage ta gartsa mashi cizo a hannunshi azabar zafin da yaji ce tasa shi sakinta, a lokacin jami'an isod Sun watso da gudu sun sauko down Sai faman harba mashi bullets suke Yi, tsabar mamakine Yasa suka koma kokwanton macijin, da zarar harsashin ya daki fatarshi Yake faɗuwa ƙasa batare daya huɗa fatarshi ba, hakan ba ƙaramin tayar masu da hankali yai ba.

Wani irin bahagon tsalle ya daka saman glass din Ƙofar, Ya faffasa shi Yabi ta ƙatuwar huɗar daya 6ula Ya dira tacan Bayan gini, da gudun gaske unaisah tabi bayanshi, tamkar zata tashi sama, sam bata acikin hayyacinta, ba ta ji bata gani ta makance, gani take kamar hanyar komawa kurkukun ƙaddara yake nema.

Gaba ɗaya jami'an sunbi bayanshi aguje, Sai dai sun kasa cimmashi, unaisa tana gudu haɗi dayin tuntu6e har tafi jami'an sauri, duk inda ya nufa tana abiye dashi, sai faman ƙwala mashi kira take Yi tamkar ranta zaifita.........

Moving quickly Chief Owais Ya fito daga part din, Big guy yana abiye dashi, hankulan kowannansu Ya tashi, kaitsaye suka nufi Harabar ajiye motoci na gidan, wata dankareriyar mota suka nufa, Big guy ya buɗe mashi kofar ya shiga ya zauna shima Ya zauna, yai ma motar key, sai da yakusan ƙure speed din motar tamkar zasu tashi sama tsabar yadda take yin gudu direction din da macijin yabi suka nufa.............

*OBIE ESTATE🏙*

*HAJIYA SARATU❤*

A tsaye take gaban Dressing mirror, bata kaiga cire Swiss cord lace din Jikinta ba, babu mayafi akanta, hakan ya bayyana kitson zanan da akayi mata, fitowa pravin yai daga toilet jikinshi sanye da bathrobe fara ƙyal, da alama wanka Yai, sam bata lura dashi ba ta dai ji motsin mutun abayanta, amma dayake hankalinta ba akanshi yake ba shiyasa bata samu damar waigowa ta kalle shi ba, A hankali Yake ƙarema bayanta kallo, Kayan sun ɗanyi tighting dinta sun bayyana dirin jikinta, musamman faska faskan hips dinta.

Ba zato ba tsammani taji ya kwanto da kanshi saman wuyanta, ta baya ya rungumota, ya zagayo da hannayenshi saman flat stomach dinta. muryarta tamkar tame jin bacci ta murya"pravin meye haka"? Manna mata kiss Yai saman wuyanta, "Ba tambayata yakamata kiyi ba, ɗazu ina kallonki cikin taro, Kin saki jiki sai tiƙar rawa kikeyi Alhazawan nan masu dogon gemu sun tsareki da mazuran idanuwansu sunata kallon jikinki"

Ɗaure fuskarta tayi tamau, tare da sanya hannayenta biyu ta damƙi hannunshi dayake ƙoƙarin ɗaurawa saman ƙirjinta.

"Kaga Bana son surutu, Yanzu na dawo cikin gidan nagaji ina buƙatar in huta," yaƙi bari ta ƙwace kanta daga ruƙon da yai mata.

"Bansan meyasa kike Yi min haka ba! Sam baki darajani a matsayina na mijinki, bakya jin shakkar fadamin kin fita ba tare da iznina ba" a faɗace ta fusge kanta daga jikinshi ta juya tana dubanshi.

"Oh gidan Yaya hateem din ne saina nemi izinin ka zan shiga? Sai kace na tafi wata uwa duniya, ko kamanta ne? Acikin estate din nan gidanshi yake, na shiga wurin matarshi ne don mu ƙara gaisawa, shi kenan komai zanyi dole saina faɗa maka"? Ta faɗa tana jifarshi da harara, bawan Allah Ya tsare ta da ido yana kallonta, Idan tana yi mashi magana tamkar zata rufe shi da bugu

Guntun tsoki taja"ka daina kallona, ka wani tsareni da ido kamar zaka lasheni, ni bansan meyasa kake son zama ɗaki ba kamar wani munafuki, gasu baba can a falo ka shiga wurinsu ka zauna ayi fira dakai"

Shiru yai bai tanka mata ba, babu alamun zai daina kallon nata. Ta6e baki tayi"Idan baka da abunyi ni inada shi, don haka bani wuri In wuce"

ta faɗa tana ƙoƙarin bi ta gefenshi da niyar ta tafi, ba zato ba tsammani taji ya damƙi damtsen hannunta, ruƙo bana wasa ba, har saida ta ɗago idanuwanta azare take dubanshi.

"Kidaina yi min faɗa, bafa tsoronki nake ji ba, Ina raga miki ne saboda ƙaunar da ke atsakanina dake" har saida taɗanji gabanta ya faɗi rass, ganin yadda ya haɗe fuskarshi, kwata kwata babu annuri tamkar bai ta6a dariya ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull