Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 59
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 59: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 59. "Ke komai baki Iya ba dangane da zamantakewar…
3,332 words
"Ke komai baki Iya ba dangane da zamantakewar aure? Sai kace ba mace ba? Baki Iya soyayya ba sannan baki da lokacina sai idan kinga dama zaki bani hakki na? Abu kaɗan saiki rufeni da faɗa kamar ɗan cikinki? Ko kin manta matsayina awajenki? Idan kin manta bari na tuna maki, Ni mijinki ne a ƙarƙashin ikona kike, Nafi kowa Iko dake hatta mahaifinki, Aljannarki tana a ƙarƙashin ƙafata idan har bakiyi min biyayya ba tayaya kike tunanin zaki sameta"? cikin jin ƙunar rai Ya furta hakan, maimaikon yaga nadama akan fuskarta sai gani yai ta tuntsire da dariya har fararen hakoranta suka bayyana, fisge hannunta tayi daga ruƙon da yai mata.
Ta ruƙe qugu ta matsa dab dashi kafin ta soma magana"Naji abunda kace babyn baby, sai dai akwai gyara a kalamanka, bani ce nake a ƙarƙashin ikonka ba, Kaine kake a ƙarƙashin ikona, ko kamantane, agidanmu kake zaune, cin ka shan ka suturarka dama komai nice nake kula dasu, baka da wata power pravin, babu yadda za'ai nayi maka biyayya sai dai kai kayi min saboda nina cancanci hakan, Nice hula kaine ɗan kwalin, aljanna kuma ta mai rabo ce" da wulaƙanci take furta maganar, lamarin ya ɗaure mashi kai, a iya saninshi saratu tana da ilimin addini amma idan tayi wasu kalaman ba ƙaramin mamaki take bashi ba, Ƙululun bakin ciki Ya hana ya furta mata magana, idanuwanshi sun kaɗa jawur dasu, Ranshi Ya 6aci sosai a fusace Ya juya ya fuce daga ɗakin, ta6e baki tayi aranta ta ayyana"matsalarka ce koda yake laifina ne dana auri dangin kirishna, masu bautawa soyayya" ta faɗa tana dariya.
❤🤍❤
A Zazzaune suke saman tattausan carpet, ɗan ubansu zubin kafi mage Laushi dake A cikin katafaren falon gidan baba obie, daga tsakiyar Royal sofa set din falon carpet din Yake a shimfiɗe hadadden gaske, tamkar shimfiɗar sarakuna, an kewaye bakin carpet din da tuntun, asaman su dattijon arziƙi Ya ɗaura kanshi, Prime minister Hateem Yana a kishingiɗe shima ya ɗaura kan nashi saman tuntun, Basu kaɗai bane saman carpet din akwai senate lateef tare da his excellency deen da kuma His excellency abdul Razak duk sun kishingiɗa kansu saman tuntun, kowan nan su jabbiyace a jikinshi, ta obie data hateem launi ɗayane ruwan toka, hateem ya manna farin glass a idanuwanshi hannunshi na dama hadaddiyar Agogon azurface mai kyan gaske, zobenta ne a yatsun hannun shi. Jallabiyar sharafuddeen data his excellency deen launin brown ce, yayin data Senate lateef ta kasance milk colour, hankalinsu kwance suke shan firarsu, sun baro iyalansu a makwancinsu, yayin da su kuma suka haɗa majalissarsu afalo.
Babban tray ne aka ajiye masu kan carpet din, Saman shi Tea pot ce mai ɗauke da green tea, ga jerin kofuna, suna fira suna shan abunsu "Baba mun cika ka da surutu ko"? Senate lateef ne Yai maganar yana duban fuskarshi.
Ɗaura hannu yai saman gemunshi tamkar yana kitsa shi Yace"Ni ai banƙi kuyita surutu ba daga yau har gobe, wallahi bana gajiya da sauraronku, Ina jin daɗin ganin ku atare dani, nayi kewarku sosai"
Murmushi kowan nan su Ya saki, In ka cire hateem daya lumshe idanuwanshi ga dukkan alamu bacci yake ji. "Kamar yadda baka gajiya da sauraronmu muma haka bama gajiya da faranta maka," acewar his excellency deen lumshe idanuwanshi yadanyi hadi da jinjina kanshi His excellency abdul razak Yace"baba, akwai wata magana mai mahimmanci da nakeson Yi dakai, tunda yanzu duk mun haɗu agaban ka, Inaga Yakamata muyi anan idan ka bani dama"!
Mayar da hankali obie Yai akan abdul razak"ina sauraronka"
"Dangane da matasan family dinmu, bai kamata mu zuba masu ido muna kallonsu ba, yakamata kowan nan su ya fidda matar da zai aura"
His excellency Deen Yace"Ni kaina abun yana damuna, wani abin ɗaure kanma Yaran tamkar basu da ra'ayin ajiye Iyali, kaga Justice namu da dr nawaz sam basu son Inyi masu zancen aure"
Murmushi obie Yasaki yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.
Senate yace"har ƙwara Ziyad, idan nayi mashi maganar aure sai kaji yace inada wannan burin baba in sha Allah nan bada jimawa ba zan fidda matar da zan aura ka tayani da addu'a Allah ya bani mace ta gari"
Mai girma sharafuddeen dake sauraron yayyan nashi, hannun shi ruƙe da mug na tea da yake kur6a, da alama yana jin dadin tattaunawarsu.
Deen yace"su kuwa waɗannan ba'a maganar ƴa'ƴansu, dama ance magaji mafiyi, akansu na fara shaidar hakan" yai maganar Yana nuna Sharafuddeen da Hateem. Gyaran murya sharafudden yai kafin ya soma magana atsanake"lamarin Owais namu sai addu'a, Ni bana gane kanshi, mace bata agabanshi, na ta6a yi mashi zancen aure sau ɗaya sai ce min yai baya son ya ɗaurawa kanshi nauyin da bazai Iya sauke shi ba"
Murmushi kowan nan su ya saki, Obie yace"kada ku takura kanku akansu, lokacin yin auran nasu ne baiyi ba, da zarar time yayi babu wanda zan saurara acikinsu sai dai kawai suji sanarwar ɗaurin auransu a masallaci"
Jinjina kai sanate Yai"baba ka kawo shawara mai kyau, mu haɗa kowan nan su da abokiyar rayuwarshi, tunda muna da ƴan mata a family namu" His Excellency abdul razak Yace"wai Ina ɗan uwa mubarak Yaje ne"? Senate lateef Ya bashi amsa da cewa"ɗazu dai muna zaune naji wayar shi na ruri har nace mashi ya dubata ana kiranshi, tun da ya fita har yanzu shiru bai dawo ba, wataƙil ya wuce gidanshi" "Mu ma yakamata muje mu kwanta, mu huta" acewar deen. Daura ido obie yai akan fuskar Hateem babu alamun Yana sauraronsu. Gyaran murya yai mashi haɗi da zungurin kafaɗarshi da hannu, firgigit Ya ware idanuwanshi Yana faman yamutsa fuska"Idan bacci kake Ji yakamata kaje ka kwanta" girgiza kai yai"a'a ba bacci nake ji ba, Ina sauraronku"
da zolaya senate lateef yace"Oh, mu ka maida shashashu mun saki baki munata surutu ka kasa kunne kana sauraronmu, Wato kafi ƙarfin ka tanka mana"
Mai girma sharafudeen Yace"bacci yake ji fa, ba sauraronmu yake yi ba, tun ɗazu na lura dashi, baba ne Ya farkar da shi," ya faɗa yana duban hateem"malam ka tashi kaje wurin Iyalinka ka kwanta ka huta" Yamutsa fuska Hateem yai"Na faɗa maka ba bacci nake ji ba, idona biyu" ya faɗa yana zare mashi manyan idanuwanshi, dariya suka saki gaba ɗayansu.
Kafin wani Ya kuma furta kalma, kwatsam ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka Jiyo masu sautin fashewar glass, Baba obie Yace"kuna jin abunda nake ji kuwa? Ko dai kunnuwana ne suka jiyo mun badai dai ba"
Senate yace"kamar fashewar glass, bari in duba" ya faɗa yana mikewa tsaye, karaf idanuwanshi suka sauka akan Giant snake din dake ƙoƙarin faɗowa ta ƙofar glass din wani ɗaki dake acan upstair hawa na Uku, ras yaji gabanshi Yai mugun faɗuwa, Muryarshi na rawa ya furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'in!" Jin ya zabga salati yasa Sauran ƴan uwan nashi sukayi saurin miƙewa, tare da daura idanuwansu saitin inda senate Yake kallo, tashin hankalin da ba'a sanya mashi date, sunyi matuƙar firgita da ganin danƙareran macijin dake bin jikin bene Yana ƙoƙarin saukowa down, jikin baba obie Ya hau yin kerma abunka ga tsoho, Ido Ya raina fata, lamarin ya ɗaure masu kai, Deen yace"maciji kuma? Tayaya akai ya shigo gidan nan? ina jami'an dake tsaronshi? Wannan wani irin ganganci ne"?
Kafin wani ya bashi amsa, kwatsam suka jiyo takun tafiyar jami'an isod, da gudun gaske suke shigowa cikin falon, hannayensu ruƙe da bindigu, atare suka hada baki wurin furta"yalla6ai ku kwantar da hankalinku, zamu kawar maku dashi," A matuƙar ruɗe baba obie yace"baku da hankali, taya akai kuka bari maciji Ya shigo gidana? A haka kuke fadin mu kwantar da hankalinmu? Kun makance ne baku ganin girman shi? tayaya zaku Iya kamashi"! Da sauri Senate ya tari nunfashinshi"baba kayi haƙuri, zasu fitar dashi, mubarsu suyi aikinsu"
Daya daga cikin jami'an yace"kayi hakuri yalla6ai ba laifinmu bane, mu kanmu bamusan tayaya akai Ya faɗo cikin estate din nan ba, babu wanda yasan daga ina Yake"
da hannu deen Ya nuna masu hanya"ku shiga kuyi aikinku" da sauri suka nufi benan.
Adaidai lokacin Unaisah dake ta faman gudu ta shigo cikin falon tana haki, duk ta fita hayyacinta, kusan atare suka ɗaura idanuwansu akanta, da mamaki akan fuskokinsu suke dubanta, kafin wani yai yunkurin yi mata magana, Chief owais Ya faɗo falon tare da big guy, sunyi mamakin ganinshi babu wanda yasan yana a ƙasar, tsabar firgici da tsoro Ya hana Obie furta sunanshi sai faman binshi Yake Yi da kallo.
Umarni yaba big guy akan ya dauki Unaisah ya maidata gida, jin ya furta hakan yasa ta watsa da gudu cikin falon bata nufi ko'ina ba sai saman benan da zai sadata da macijin, da gudu big guy yabi bayanta, cikin shessheƙar kuka take fadin"dan Allah kada ku kashe shi, wallahi ba maciji bane, ɗan uwanane danish"
damƙo hannunta big guy yai, tadinga kiciniyar ƙwace kanta ranta amtuƙar 6ace ta soma zazzaga masu masifa tana fadin"wallahi babu inda zanje, nace maku dan uwanane, ku ƙyale shi ku daina harbinshi tunda bai cutar da kowaba, wayyo Allah na danish ɗina"
Sautin koke kokenta Ya cika gidan, hatta sauran mazauna gidan baba obie saida suka jiyota, ɗaya bayan ɗaya masu aikin gidan suke fitowa daga makwancinsu, Pravin bai jima da shiga ɗakin hajjaty ba ya jiyo sautin Kukan mutun agidan, sai gashi ya fito hajjaty na abiye dashi, Hajiya saratu kuwa jin sautin kukan Yasa ta fito daga ɗaki ta shigo falon, koda tayi arba da unaisa ga jami'ae da kuma shirgegen macijin dake bin bango, hannayenta biyu ta ɗaura akai tana ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Maciji acikin gidan nan? Wacece wancan Yarinyar? Ya akai ya shigo? Aruɗe ta furta hakan Kowa Ya shiga ruɗani, Jami'an sun dage sai antaya mashi Harsashi suke Yi, Ganin suna ƙoƙarin yi mashi illa yasa Unaisa tayi wani irin kukan kura, ta bangaje big guy da iya ƙarfinta na ƙarshe, ta haura sama da gudun gaske, duk yadda suka so su kawar da ita sun gaza yin hakan har saida tayi nasarar ƙarasawa inda yake, tsawa suka dinga dakata mata suna korarta daga gabanshi amma taƙi matsawa, macijin yabi ya nannaɗe kanshi Ya dunƙule waje guda saman floor, lullu6e shi tayi da bazar rigarta, tana kuka tana fadin"danish dan Allah ka saurareni, ka taimaki rayuwata, bana so na rasa ka, ka canza halittarka ka tabbatar masu da cewa kai mutunne ba maciji ba, idan ba haka ba zasu Iya kashe mun kai" cikin jin ƙunar rai take Furta maganar, ta ƙanƙameshi kamar zata maida shi jikinta, jami'an sun natsu suna kallon ikon Allah, Hajiya saratu sarkin tsoro sai faman baza idanuwanta take Yi, baba obie Yana la6e bayan Mai girma sharafuddeen, Senate Ya ruƙo hannunshi dake tayin kerma, A hankali Hateem Ya zare farin glass din dake asaman fuskarshi Ya ruƙe ahannunshi, komai ke faruwa akan idanuwanshi, tamkar amafarki suke kallon lamarin, an rasa wanda zai janyeta daga jikinshi. Abunda ya ɗaure masu kai babu alamun macijin zai cutar da ita.
Duk da baya iya furta mata magana, ranta yana bata cewar yana son ya rikiɗa ya koma mutun sai dai ya kasa yin hakan, jikinshi ya ɗau zafi sosai, cikin sanyin murya ta soma yin magana, hawaye naci gaba da wanke fuskarta "Ɗan uwana rabin raina, dan Allah ka canza halittarka, idan ba haka ba babu wanda zai yarda cewa kai mutunne zasu ci gaba da cutar min dakai" ta faɗa tana ƙara kankameshi a Jikinta. umarni Owais Ya ba jami'an akan su daina yunƙurin harbinshi, amsa mashi sukayi datoh, ya fadi hakanne saboda ya fara kokwanton mutunne kamar yarda ta faɗi, a faɗace hajiya saratu tace"akan me zaka basu umarnin su daina harbinshi? idan ya cutar da wani fa"? Ko kallo bata ishe shi ba, muryar baba obie Na rawa ya furta"Ku kashe macijin nan, bana son ganinshi, ku kawar mana da shi"
"Baba ka kwantar da hankalinka, Ni na yarda da maganar yarinyar ba maciji bane mutunne" mai girma sharafudden ne yai maganar.
A harzuƙe Obie Yace"tayaya mutun zai zama maciji? hakan bazai ta6a yiwuwa ba, Ni bazan ta6a yarda ba, ku kawar mana dashi kawai, idan baso kuke zuciyata ta buga ba, Ita kuma waccan Yarintar mai kasada ƴar wacece? Ku ɗauke ta mana daga Jikinshi kada ya sare ta"yai maganar yana nuna Unaisah da sandar hannunshi.
Duk yabi ya furgice masu, big guy ne ya kutsa ta cikin jami'an Ya nufeta, muryarshi ƙasa ƙasa tamkar tame Yin raɗa ya furta"Unaisah, ki tashi mu tafi gida, za'a dawo maki dashi" maƙe mashi kafaɗa tayi, la66anta duk sun bushe sun faffashe.
"Babu inda zanje, Ina atare dashi, Idan nayi nesa dashi, ba zaku Iya sarrafashi ba, zai Iya guduwa ya nufi wani wajen" magiya ya dinga yi mata akan ta miƙe amma taƙi tashi, hakan Yasa Chief owais motsawa ya haura saman benan Ya nufe su, Darewa jami'an suka dinga yi suna bashi hanya har ya kaiga ƙarasawa inda suke, faffaɗan tafukan hannaye shi ya ɗaura saman unaisa ya ɗaɗɗagota tare da ɗaurata saman broad shoulder dinshi, juyawar da zaiyi da niyar ya tafi da ita, giant snake din Yai wata irin girgiza da gudun gaske yabi bayan owais daya ɗauketa.
Jami'an suka saita shi da bindiga owais Ya hana su harbeshi yace masu su barshi akwai dalilin dayasa yayi hakan, Yana tafiya macijin Yana bin bayanshi, kasancewar ya ɗaurata saman kafadarshi tana Iya kallon giant snake din daketa ta faman jan ciki Yana nufosu, hawayenta tamkar zasu ƙare muryarta shaƙe take ambaton sunan Danish.
Ganin macijin zai sauko down yasa Hajiya saratu ta watsa da gudu zaninta har yana kwancewa ta ruƙo shi ta nufi hanyar part dinsu aguje ta shiga ɗaki ta datse kofa, tabi tagogi duk ta rufesu, a karshe cikin toilet ta shige tayi locking kanta.
Hankalin baba obie yai matuƙar tashi sai ƙara ƙankame jallabiyar mai girma sharafuddeen yake yi, Hateem kuwa ko kadan baiji tsoron macijin ba, tsabar mamakine Ya hana su furta magana, kowa ya baza ido yana kallon ikon Allah, duk inda owais yai da ita sai macijin yabisu, fucewa yai daga falon Ya nufi motarsu da su ka yi parking dinta abakin entry hall, Ya buɗeta Ya shigar da unaisah aback seat na motar, ya buɗe front seat a mazaunin driver Ya zauna yai mata key, da gudun gaske Ya fusgi motar, ta cikin glass din motar take kallon macijin daketa binsu da ƙarfi Ya daka uban tsalle Ya haura saman motar Yai kwanciyarshi.
Ajiyar zuciya ta sauke ganin yana atare dasu, bai nufi ko'ina ba sai sashen da gidansu yake, ta gate din Baya ya shigar dasu a bakin entry hall chief Yai parking din motar, Ya fito Ya buɗe back seat din Ya cuccu6i unaisah Ya ɗaurata saman kafaɗarshi Ya nufi Babban falo da ita, hankalin shi kwance tamkar baisan da zaman macijin ba, saukowa yai daga saman motar yabi bayansu da gudun gaske yake jan jiki.
Cikin takun sauri Owais Ya haura upstairs da ita, kafin Ya ƙarasa second floor, macijin Ya riga shi isa, wani wawan tsalle ya daka Yabi ta jikin bene Ya faɗo tagabansu, ƙoƙari yake ya nannaɗe ƙafafuwan owais sai dai yakasa yin hakan saboda owais bai bashi damar ruƙe mashi ƙafa ba, sai kakkauce mashi yake Yi, a haka ya ƙarasa bedroom din Danish Ya shiga daga ciki, Ya kwantar da ita saman gado, Shigowa ɗakin macijin Yai yana faman huci kamar zai kai mashi hari, saman gadon Ya haye Yana faman bin mattress din. Owais dake a tsaye ya goya hannayenshi saman wide chest dinsa, Ya natsu yana kallonsu.
Giant snake din Ya nannaɗe jikinshi agaban unaisah ya ɗago da kanshi Yana kallon owais, duk a tunaninshi wani abu zaiyima unaisah shiyasa Yabiyosu, shi kuma owais daya fahinci Baya iya cutar da ita shiyasa yai dabarar daukota sai gashi yaci nasara akanshi"
Fitowa yai daga ɗakin Yaja ƙofar Yai locking dinta, Yabarsu su biyu adakin Ya nufi down.
Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, zuciyarta sai dukan uku uku takeyi, tsananin tsorone Ya kamata, amma saboda ƙaunar da take yi mashi takasa motsawa, duk tasha jinin jikinta, muryarta na rawa ta furta sunan shi"danish ɗina" juyowa macijin yai da kanshi Yana dubanta, jikinta na kerma saboda ƙarfin hali ahaka ta miƙa mashi hannunta, jan jiki ya somayi yana nufarta, saman kirjinta ya nannaɗe kanshi, wani irin sanyi taji ya ratsata, lokaci ɗaya tadaina jin bugun da ƙirjinta keyi mata, asaman fatar shi ta ɗaura hannunta, a hankali take shafashi duk don ta kwantar mashi da hankalinshi, ita kaɗaice zata Iya fahimtarshi a halin da yake ciki.
Walking quickly chief Ya nufi Ƙofar fita daga part din, Kafin Ya ƙarasa Muryar Boss man ta katse mashi hanzarinshi"yalla6ai" cak Ya tsaya da tafiya ya waiwayo yana dubansu, su biyune suka fara shigowa shida big guy, daga bayansu sauran jami'an isod ne da suka Biyosu, hankalinsu duk ba a kwance yake ba, musamman Boss man da yaji labarin abakin big guy shigowar shi kenan gidan duk wannan budurin da akeyi baida masaniya yana a part dinsa.
Fuskar chief owais ta canza zuwa yanayi na damuwa. "Yalla6ai Ina macijin yake"? Big guy ne ya jefa mashi tambayar. Daƙyar Ya iya buɗe baki Ya furta"yana adakin shi, tare da yarinyar na kullesu" waro ido waje sukayi suna kallon shi Muryar boss man na rawa ya furta"kana nufin tare da Angel ka rufe su aɗaki? Idan ya cutar da ita fa"? Gaba ɗaya yabi ya ruɗe.
Big guy yace"ka kwantar da hankalinka, Ni na fahimci hikimar yin hakan, da ace bai daukota ba macijin bazai dawo gidan ba, bamusan inda zai shiga ba, amma yanzu kaga mun kulleshi aɗaki ta dalilinta"
Cikin rashin fahimtar kalaman big guy Boss man yace"bazai yiwu ba, Ƴata fa aka kulle aɗaki ɗaya da maciji, Idan ya kashe min itafa" dafa kafaɗarshi Owais Yai da hannu ɗaya"kadaina kiranshi maciji, mutunne, bazan iya yin abunda zai cutar maka da ƴarka ba, Kamar yarda kake jinta nima haka nake jinta, fatan ka fahimce ni" gyada kai Yai still hankalinshi bai kwanta ba. "A wani daki ka kulle su"? Atakaice owais Ya furta"A dakin shi" jiki na rawa boss man Ya watsa da gudu ya nufi upstair. Chief owais Ya maida dubanshi ga Big guy, "Things are starting to get out of control, and I don't know what to do now. But I want to see his brother, maybe he can control him. kaje ka zo dashi" ya faɗa in a cool voice, amsa mashi yai da toh, da sauri Ya juya ya fuce daga ɗakin, Kallon sauran jami'an yai"ku koma bakin aikin ku, ku tabbatar kun kula sosai" Cikin girmamawa suka amsa mashi da toh, juyawa sukayi da sauri kowa Ya nufi hanyar komawa bakin aikinsa. Shafa sumar kanshi yai da tafin hannun shi nadama, yanke shawarar komawa gidan obie yayi, yasan suna can hankali duk Ya tashi, ba lallai su iya runtsawa ba. Cikin takun sauri Ya fita daga part din, Ya nufi ɗaya daga cikin motocinsu, wani jami'i ne Ya nufeshi da sauri Ya buɗe mashi motar ya shiga a mazaunin baya, shi kuma ya zauna a driver's seat, yai ma motar key ya tashe ta, suka nufi cikin Obie estate......
Unaisa tana akwance idanuwanta sun kumbura suntum, kumatuntu sunyi jawur saboda kukan da tasha, busassun hawayene saman fuskarta, ta lumshe idanuwanta akan giant snake din daya ɗaura kanshi saman kirjinta, karatun qur'ani take raira mashi cikin disasshiyar muryarta daƙyar sautin ke fita, macijin Yayi lamo sai ƙara narke mata yake Yi, ga dukkan alamu yana sauraronta. Da karfi tajiyo muryar boss man Yana kwaɗa mata kira daga waje Unaisah, Unaisah!!. A hankali tasoma ƙokarin raba jikinta daga na macijin, ta lalla6a ta sauko daga saman gadon tana cigaba da yin ƙira'ar al'qur'anin, agogon bangon ɗakin ta kalla almost 10 na dare. A jikin glass door din Boss man Ya jingina yana leƙensu. Ƙarasowa tayi gaban ƙofa suna fuskantar juna, batasan sa'adda ta fashe mashi da kuka ba, Cikin shessheƙar murya take fadin"kaga irin ƙaddarar da ta sami ɗan uwana ko? Nayi ƙoƙarin na fahintar dasu cewa mutunne amma sunƙi su gane, sai harbinshi suke Yi da bindiga"