Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 60
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 60: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 60. Tsananin tausayine ya kamashi ganin yadda ta…
3,338 words
Tsananin tausayine ya kamashi ganin yadda ta canza saboda damuwa. Cikin kwantar da murya yace"Yana ina "? Matsawa tayi daga bakin ƙofar, karaf idanuwanshi suka sauka akan giant snake din dake nannaɗe saman gadon kamar bacci yake yi. "Unaisa bai cutar dake ba"? Tambayar daya jefa mata kenan, Girgiza mashi kai tayi"a'a baiyi min komai ba, dan Allah ka taimaka mashi, nasan kai kaɗaine zaka Iya fahimtana,"
Jinjina kanshi yaɗanyi"okey, Ki kwantar da hankalin ki, kidaina kuka bana son ganinki cikin damuwa" Fuska amarairaice tace"dole in damu boss man, rayuwar ɗan uwana abun tausayice, bazasu ta6a ƙyale shi ba, tun yana jariri suke cutar dashi har izuwa girmanshi sunƙi su ƙyale bawan Allahn nan, mugaye in sha Allah bazasu ta6a yin nasara akanshi ba" Idanuwanshi tuni sun cicciko tab da ƙwalla "Dan Allah ka taimaka mashi, akwai ruwan zamzam da ake bashi na addu'a ina da tabbacin idan yasha zai dawo dai dai" Cikin sanyin murya yace"A ina za'a same shi"? "Ɗan uwanmune Ya bani address din gidan da zamu ɗauko, namanta takardar acikin aljihun uniform dina, ai kace min kayan suna a hannunku, idan ka duba zaka ga wandona launin baƙi, mu uku keda kalar kayan dani da batul saina danish, pls ka bincika ka dauko ta, Allah yasa bata faɗi ba, nasan ma zaiyi wuya asamu zam zam din koda an samu takardar adreshin" "In sha Allah za'a nemo zam zam din, ki koma ki zauna amma pls kada ki bari ya cutar min dake" amsa mashi tayi da toh" ajiyar zuciya ya sauke, tamkar karya tafi yabarta haka yake ji, duk da Ya yarda Yaron bazai Iya cutar da ita ba, tunda gashi ya same su asaman gado ɗaya batare daya sare ta ba, shi tausayin yaron ma yake Ji.
Juyawa yai da sauri Ya nufi down stair. Komawa tayi saman gadon ta haye, ta kwanta daga gefenshi taci gaba da yi mashi karatun qur'ani.
Da matsakaicin gudu motar chief ta ƙaraso bakin entry hall na shiga babban falon gidan baba Obie, dasauri jami'en Ya fito daga motar Ya zagaya other side Ya buɗe mashi murfin car din, Ya zuro kafarshi Ya nufi Cikin gidan da sauri, Kamar yadda yabarsu haka ya same su a tsaitsaye cirko cirko , damuwace ƙarara akan fuskokinsu, hankalinsu bazai ta6a kwanciya ba idan har ba gawar macijin suka gani ba.
"Owais"! Obie ne ya ambaci sunan shi da mamaki akan fuskarshi. Dagowa yai da kyawawan idanuwanshi ya daurasu akan faces dinsu, kamar yadda yake kallonsu haka suma suke binshi da kallo, Kamar yaune rana ta farko da suka fara ganin juna" "Owais Ina macijin"? hateem ne ya jefa mashi tambayar. Calmly ya furta"mun fitar dashi daga gidan" ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, Senate lateef Yace"Wacece yarinyar dake atare dashi? Munji tana kuka tana fadin ɗan uwanta ba maciji bane shin dagaske ne"! Jinjina kanshi yai alamar eh, ya ƙara da cewa"Ƴar uwarshi ce, ba maciji bane mutunne kamar kowa, ƙaddara ce ta afka mashi" "Wai kana nufin ɗan mutunne ya rikiɗa ya koma maciji"? His excellency deen ne Ya jefa mashi tambayar, gaba dayansu sun ruɗe da jin maganar, Abdul razak Yace"bazai yiwu ba, owais kodai ka fara shaye shaye ne? In bahaka ba ta ina mutun zai Iya komawa dabba kamar maciji? Ai sai dai idan ya kasance ba mutun bane shi" Obie duk Yafi su firgita jikinshi yaƙi daina yin kerma "Owais bana son ganin macijin nan, ku tabbatar kun fitar dashi daga gidan nan, Idan ba haka ba zai Iya cutar da rayuwar ahalina" "Baba ka kwantar da hankalinka, zuwa gobe in sha Allah zan shigo muyi magana, nasan yanzu ko nayi maku bayani ba lallaibane ku fahimceni ba, ni kaina hankalina ba a kwance yake ba" Girgiza kai obie yai"owais idan kaga na kwantar da hankalina to macijin nan baya acikin gidan nan, Ni ban ta6a ganin tashin hankali irin na yau ba, wai yaushema ka dawo kasar? Ita yarinyar dake tare da macijin ƴar wacece? A ina take zaune"? Shiru yai yana duban face dinshi, sam bayason yawan surutu, abu kadan ke hasala shi, baisan amsar da zai basu ba, don ya fahimci hankulansu ba akwance suke ba. Gyaran murya mai girma sharafudden Yai, hankalin owais ya dawo kan mahaifinshi"kada ka damu, ka koma bakin aikin ka My son, Ni na fahimce ka, kaje kawai zuwa gobe zamu nemaka donka zo ka warware mana rudanin da muke aciki" lumshe ido owais yai haƙika yaji dadin maganar mahaifinshi, dama yasan shi kadaine zai Iya fahimtar halin da yake aciki Kafin Ya juya saida ya fara kallon Obie, wanda tuni idanuwanshi sun kaɗa jawur, tausayin tsohon ne Ya kama shi, yayi matuƙar yin kewar kakanshi. Matsawa yai kusa dashi Ya rungume shi saman faffadan ƙirjinshi, baba Obie Ya kankame owais tamkar zasu koma mutun ɗaya. Cikin sigar lallashi yake yi mashi magana"nayi kewarka baba, kana araina, nasan ban kyauta maka ba, amma in sha Allah idan komai Ya lafa zuwa gobe zan shigo gidan" cikin sanyin murya obie Ya amsa mashi da toh, ji yake tamkar karya tafi yabarshi, yana matuƙar ƙaunar jikannan nashi. Iyayenshi dake kallonsu, murmushi ne saman fuskokinsu. Raba jikinshi yai daga na baba obie, yakai hannu Ya shafi dogon gemun shi, da zolaya ya furta"kakana nakaina, nifa da jarumta nasanka, kai ɗin Namijin duniya ne, dan Allah kada ka bani kunya, kada ganin macijin nan ya hanaka rintsawa adaren yau, kayi bacci ka huta gobe jikanka zaizo gareka, sabon cake zamu yanka atare" Farin ciki Ya cika obinna, yayin da yake duban owais, yana dariya yace"ka wahalar dani, bakasan irin kewarka da nayi ba, Na ƙwallafa raina akan son ganinka, ka manta dani owais, gobe idan kazo har tsallan kwaɗi zan sanyaka" dariya Iyayenshi suka sanya, Owais yace"kowani horo zakayi min bazan musa ba, Na cancanci fiye da hakan, Ni zan tafi, ku kulamin da kakana, Make sure he sleeps peacefully tonight." ya faɗa yana duban iyayenshi, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, owais ba ƙaramin burgesu yake Yi ba, saboda yana son mahaifinsu. Juyawa yai da sauri ya nufi ƙofar fita daga falon, idanuwan kowan nansu akan bayanshi, Harya ɗaga kafa zai fuce, muryar prime minister ta dakatar dashi "Owais! ina son yin magana dakai" a hankali Ya juya yana dubanshi, da sauri Hateem Ya nife shi, babu mai Iya jin abunda suke cewa saboda sunyi nesa da sauran mutanan. Dafa kafadarshi yai da hannu ɗaya, tunkafin hateem yai magana owais ya riga shi furta"uncle sai kunyi hakuri dani, ka zo kasar bansamu lokaci nazo gaishe ka ba" murmushin gefen fuska yasakar mashi"ni wannan ba damuwata bace, nayi maka uziri saboda nasan yanayin aikin ku,' ya faɗa yana dubanshi kafin yaci gaba da magana. "Inaso ka faɗamin dagaskene macijin nan mutunne"?
Jinjina kai owais yai"dagaske ne mutunne ya rikida, matashin saurayi" Shiru hateem yaɗanyi kafin ya kuma cewa"Ya sunanshi"?
"Danish" ataƙaice ya bashi amsa.
"Duk da bansan abunda ke damunshi ba, amma idan har mutunne ya rikida hakan na nufin aljanune atare dashi ko"? Ɗaga mashi kai owais Yai"haka muke tsammani" Hateem Ya numfasa kafin Yace"Inason ganinshi idan yadawo suffarshi ta ainahi, sannan Yakamata a kira sheikh imam ya duba shi, ina da tabbacin zai Iya taimaka mashi" Amsa mashi yai da toh, daga haka sukayi sallama owais ya fuce daga falon. Bayan tafiyar owais, su Hateem suka raka baba obie bedroom dinshi, babu yadda basuyi dashi ba akan ya kwanta ya runtsa amma Yaƙiya gani yake tamkar macijin zai faɗo ɗakinshi, duk yabi ya firgice, adole mutun biyu suka tayashi kwana, Sharafudden da senate lateef, sauran kowa Ya nufi masaukin shi. Hankalin Hateem Yaƙi kwanciya, Macijin Ya tsaya mashi aranshi, ya ƙwalla fa rai akan son ganin yaron, ko bayan daya koma Gidanshi dake a estate din, a ɗaki ya tarar da gimbiya mujeedat, tana faman yin zarya, ta kasa kwanciya saboda rashin dawowarshi, babu wanda yasan abunda ya faru a gidan baba obie sai wadanda ke zaune agidan. Bai sanar da ita komai ba, Saman gadonsu Ya haye ya kwanta yayin da idanuwanshi ke fuskantar ceilling, tayi mamakin ganin damuwa atattare da mijin nata, har tambayarshi tayi meke damunshi amma sai yace mata babu komai, bacci yake ji, ƙoƙarin faranta mashi tayi har saida ta tabbatar ya fara yin bacci tukunna hankalinta ya kwanta.
*SIR MUBARAK✊*
Babu wanda ya motsa acikinsu, tun da suka ji muryar mutumin daya kira layin jazz, Jikin kowannansu yai sanyi laƙwas tamkar an zare masu laka, har sun fara danasanin jahilin bugun da sir mubarak yaiwa jazz domin kuwa sun tabbatar sune sukayi kuskuren yanke hukunci batare da sun fara bincikarshi ba. Yarinyar dake a zaune dirshan idanuwanta sun kaɗa jawur yayin da hannuwanta ke asaman fuskar jazz.
kafin Sir mubarak Yai ƙwaƙƙwaran motsi, Muryoyin yaran dake tunkaro ɗakin Ya karaɗe kunnuwan sojojin Kusan atare suka ɗago suna kallon baƙin ƙofar shigowa ɗakin.
Matasan ƴan mata ne kowaccensu sanye cikin rigunan bacci, babu huluna akansu sai zallar sumar kansu mai tsayi har gadon bayansu, namiji ɗayane acikinsu shima kayan baccin ne ajikinshi, fuskokinsu a yamutse sai hamma suke Yi, ga dukkan alamu kukan ƴar uwarsu ne Ya farkar dasu daga bacci.
"Meya faru da yaya jazz dinmu? Su wanene ku"? Har suna haɗa baki wurin tambayar sojojin.
Cikin shessheƙar kuka Yarinyar dake ruƙe da dr. Jazz ta kware murya tana kallon ƴan uwan nata tace"Sun kashe mana shi, bansan su wanene su ba, kawai sun shigo mana gida sun kama bugunshi" Fashewa sukayi da kuka kamar gidan mutuwa, da gudu suka nufi inda yarinyar take a zaune, a kewaye da dr jazz suka zuƙunna Suna ambaton sunanshi tamkar ransu zai fita. Ba zato ba tsammani, sojojin suka jiyo muryar babban mutun Yana fadin"meke faruwane? Su wanene suka shigo gidan"? Fadowa cikin ɗakin Yayi, daga shi sai short a jikinshi babu riga, yana da faffaɗan kirji ga ƙirar ƙarfi kamar ɗan dambe, kallon ɗaya zaka yi mashi ka shaida farar fatane, fatarshi jawur take daga gani bature ne. Lokacin da yai arba da su sir mubarak a ɗakin Ras yaji gabanshi yai mugun faɗuwa, adabarbace ya furta"su wanene ku? Meya kawo ku cikin gidan nan"? Kafin wani ya furta kalma, Mutumin ya wurga idanuwanshi akan yaran dake kuka. Zaro idonshi waje yai ganin yadda suka raunata jazz, da ƙarfi yace"don ubanku ku faɗamin su wanene ku? Uban me yayi maku da kukayi mashi wannan bugun? Waye ya turo ku? Babu alamun tsoro akan idanuwanshi, sai ma dunƙule hannayenshi da yai da niyar yakai masu hari, An rasa me magana tsakanin Sir mubarak da su tiger. Gigitacciyar tsawa ya daka masu Yana fadin"bakuji ina magana ba? Idan har baku faɗamin ba, daya bayan ɗaya zan salwantar da rayuwarku" A harzuƙe tiger da Major suka zaro bindigunsu tare da saita shi, maimakon yaji tsoron bindigar hannunsu sai gani sukayi Ya sanya hannu ya daki ƙirjinshi da ƙarfi Yana fadin"Kunyi kuskuren shigowa gidan nan, abun hannunku bai isa yasa inji tsoronku ba, tunda kuka ta6a jazz sai kunyi danasanin haihuwarku da uwarku tayi acikin duniyarnan, kawai saboda zalunci saiku faɗo gidan mutane kukama bugun mutun baiyi maku laifin komai ba"? Tamkar mayunwacin zaki haka yake yi masu magana yana fitar da huci mai ɗumi Daƙyar sir mubarak Ya iya sarrafa kanshi, muryarshi a haushine ya furta"dan Allah ka faɗamin wanene kai, Ni da kake gani mahaifin jazz ne, mun shigo gidan nan batare da sanin shi ba, saboda mu atunaninmu wani mugun abun yake aikatawa....." a tsanake sir mubarak Ya kwashe duk abunda Ya faru dangane da zargin da yake yima jazz ya sanar da matashin saurayi Lokaci ɗaya sukaga ya sassauta fushin fuskarshi, ga dukkan alamu ya fahimce su. "Amma baku kyauta mashi ba, shiyasa akace zato zunubi koda ya kasance gaskiya, jazz dai ba mugu bane, mutumin kirkine fiye da tunaninka, waɗanda yaran kuma dakuka gani marayune basu da gata aduniyar nan daya wuce Allah sai kuma waɗannan bayin Allahn da suka taimaki rayuwarsu" yai maganar yana nuna jazz da hannunshi, Yaran dake sauraron su idanuwansu sunyi luhu luhu sunsha kuka kamar ransu zai fita don ba ƙaramin ƙaunar jazz suke Yi ba Cikin karyayyar murya sir mubarak yace"kana nufin Chief owais shine ke kula daku? ya tambayeshi saboda yaji muryar owais a wayar jazz yana da tabbacin shine Ya kira layinshi
Jinjina kai mutumin yai"ƙwarai kuwa, a ƙarƙashin kulawarshi muke gaba ɗayanmu, shi kuma jazz shine likatan daya dauki nauyinshi don kula da marasa lafiyan cikinsu, Yarinyar nan kuma daka ganshi atare da ita saman gado, bata da koshin lafiya, tana da ta6in hankali, ga magungunanta can saman drawer da alluran da yake yi mata, abunda yasa kuka same shi asaman kanta, ni nasan saboda babu mai iya rike mashi itane, idan dare yayi bayason tashina daga bacci, ni ne nake taimaka mashi wurin ruƙeta ayi mata allura saboda buge bugen da take Yi, idan har ba a ruƙeta ba baza a iya yi mata allura ba, tana da ƙarfine, kunyi zargin jazz yana aikata fasiƙanci da ita bahaka bane abunda na faɗa maku shine gaskiyar zance' Dafe kai Sir mubarak yai da hannu ɗaya, Wani irin matsanancin ciwon kaine ya farmashi, su tiger sunyi danasanin zargin jazz da sukayi jikin taƙaura yayi la'asar "Dan Allah ku taimaka mashi kada ya mutu, har yanzu baidaina bleeding ba" ɗaya daga cikin matasan yaran ce tayi maganar, fashewa sir mubarak yai da kuka tamkar ƙaramin yaro, cikin rauni na murya yake fadin"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'u! Jazz baka kyautamin ba, meyasa baka sanar dani ba, kabar ni inata zarginka gashi har nayi maka illah! Yanzu ya zanyi? Me zan faɗama mahaifiyarshi? Matar da ko bacci bata iyayi idan har bai dawo gidaba saboda ƙaunar da take yi mashi! Juyawa yai da sauri ya nufi inda yaran suke, bai bi takansu ba, ya sanya hannayenshi biyu ya cuccu6i Jazz Ya ɗaura shi saman kafadarshi, ya dubi su Tiger da rinanun idanuwanshi yace"major muje mu kaishi asibiti, kai kuma Tiger ka tsaya atare da army ku lallashi yaran dan Allah" ya ƙare maganar da sauri ya nufi ƙofar fita, Major yabi bayanshi bayan ya kar6i key din motar a hannun tiger.
Har sun kusa futa daga dakin, matashiyar nan mai fama da ta6in hankali ta fasa ƙara hadi da yunkurawa ta mike aguje tabisu tana fadin"mugaye ku dawo mana da ɗan uwanmu kada ku kashe shi, wayyo Allahna Yaya kana gani zasu gudu dashi " har takusa fucewa daga ɗakin, Mutumin Ya damƙo damtsen hannunta, Ya rungumeta a chest dinshi yaci gaba da lallashinta. Tiger ne ya soma lallashin ƴan uwanta dake kuka "Kuyi haƙuri, kuskure mukayi wurin bugunshi, mu ba mugaye bane kamar yadda kukayi tsammani, mutumin daya dauki jazz mahaifinshine ba wani ba, kuma asibiti zasu kaishi inda za'a duba lafiyarshi, da zarar yaji sauƙi za'a dawo maku dashi" cikin shessheƙar kuka suka amsa mashi da toh, banda mahaukaciyar yarinyar daketa ɗura masu ashar, kamar zata bugesu, mutumin ya ƙankameta ya hana ta kubce mashi.
Kusan rabin awa da tafiyar Sir mubarak, motar Big guy ta shararo da gudu cikin unguwar, tunkafin ya ƙarasa bakin gate din gabanshi ya fara faɗuwa ganin ƙofar gate din abude kusan ƙarfe goma sha ɗaya na dare, nan take ranshi ya bashi cewar wani mummunan abunne ya faru watakil shiyasa lokacin da chief Ya kira wayar jazz yace mashi ya ɗaga baiyi mashi magana ba!!!!😳😳😳
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✊✍️💋🤍*
A tsiyace yai parking din motar, tsabar sauri a buɗe yabarta, da gudun gaske ya nufi cikin gidan batare da jin shakkar komai ba, Shigar shi keda wuya cikin falon ya soma jiyo sautin kukan yarinyar nan mai fama da ta6in hankali, ta dage sai zazzaga masifa take yi tana fadin"wallahi saina tona maku asiri ranar lahira, dukanku sai kun shiga wuta tun da ku ka ta6a min yaya jazz ɗina". Zuciyarshi ce ta soma dukan uku uku, zaro bindigarshi dake soke a ƙugunshi yai, cikin sanɗa yake tafiya yana tunkarar Upstairs, Ya haura second floor, daga ƙofar ɗakin Ya la6e Yana sauraronsu.
"Ki daina magana mana, bakiji suna bada hakuri ba? Kuskure suka yi wurin bugunshi, bada son ransu ba"
Jin muryar mutuminsu yasa shi yin wuff Ya afka cikin ɗakin, Jin takun tafiyarshi ne Ya janyo hankulansu ga dubanshi, kusan atare suka ɗago suna kallon shi.
Nauyayyar ajiyar zuciya big guy ya sauke haɗi da furta"Ya Allah" kafin Ya daura eyes dinshi akan face din mutumin yace"meke faruwa ne ? Waya ta6a khadeeja take kuka? ya akai naga yaran duk sun farka daga bacci"?
A ruɗe yake jefa mashi tambayoyin, sam bai lura da Sojojin ba, waɗanda tun da ya shigo suke dubanshi da mamaki.
da ido mutumin Yai mashi nuni da sojojin"gasu nan, mahaifin Jazz ne yazo tare dasu, wani abune ya faru na rashin fahimta da yajawo har suka bugi jazz shine take ta kuka"
A hanzarce ya mayar da dubanshi ga Sojojin, Kusan atare suka buga ƙafa tare da Sara mashi.
Jinjina kanshi yaɗanyi da mamaki ya furta"Tiger ! Army Boy! Ya akai kukazo gidan nan?
"Tsautsayi da ƙaddara" acewar Tiger, Army ya kwashe duk abunda ya faru ya sanar da Big guy, sai lokacin ya lura da jinin dr jazz daya daskare saman floor, ga kuma Dressing mirror da daya fashe ta silar buga kan jazz jikinshi, cikin matsanancin tashin hankali ya furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji!"
Cikin sanyin murya Army Boy yace"sai haƙuri yalla6ai, rashin sanine, tabbas munyi kuskure, amma shima jazz din hada laifinshi, Yakamata ace komai zai yi ya sanar da Sir mubarak a matsayin shi na mahaifinshi bawai yayi gamon kanshi ba, kuma a yanayin yadda Sir mubarak yake riskarshi Yana yin waya ta sirri, kalaman da yake furtawa sun yi kamanceceniya dana masu safarar mutane"
Tiger ya ɗaura da cewa"yanzu haka sun tafi asibiti dashi, Muna jira muji daga gare su, In sha Allah zaiji sauƙi" Numfasawa big guy yai, jikinshi duk yai sanyi kamar wanda aka zarewa laka, babban tashin hankalin shi halin da suka jefa jazz basu ta6a tsammanin abun zai jaza mashi matsala ba.
Tuni idanuwan big guy sun kaɗa jawur tamkar zai fashe da kuka Ya soma yin magana"ba laifin shi bane, laifinmu ne da muka hanashi yasanar ma kowa dangane da aikin da muka sanya shi, saboda bama son kowa ya sani"
komawa yai daga gefen gadon dakin Ya zauna, Yana duban Yaran dake raku6e jikin bango, idanuwansu sunyi luhu luhu.
Mai ta6in hankalin tuni tayi shiru, sai faman zazzare idanuwanta take Yi tana dubansu.
Tiger yace"shi kanshi Chief Owais bazai ji dadi ba, ranshi zai Iya 6aci amma nasan zai fahince mu" Ganin yadda yaran suketa Yin hammar bacci, yasa Big guy yi masu magana"Kuje ku kwanta, Zuwa gobe idan Jazz Yaji sauƙi zamu dawo maku dashi"
Miƙewa su ka yi a jere suka nufi hanyar fita daga ɗakin jikinsu babu ƙwari, hankalinsu ba kwance yake ba saboda Jazz dinsu da babu lafiya.
Har sun kusa fita daga ɗakin, Big guy ya kwaɗawa ɗaya daga cikinsu Kira "Hawwa! zonan, matashiyar daya kira da hawwa ta juyo tana dubanshi, Ki ruƙe hannun khadeeja ku tafi da ita daki ta kwanta" ya fadi hakanne don yasan su kadaine zasu Iya control dinta har asamu tayi bacci.
Muryarta ashaƙe take fadin"ni bazan bisu ba, kuma bazan Yi baccin ba, wallahi sai kun dawo mun da jazz dina"
Lallashinta mutumin dake ruƙe da ita ya somayi"kinsan dai bazanyi maki ƙarya ba khadeejata, da kaina zan dawo maki dashi, Yanzu dai kije ki kwanta gobe zaki ganshi, amma idan har bakiyi bacci ba, toh bazan dawo maki dashi ba" Kwa6e mashi fuska tayi"kayi alƙawari"? Jinjina mata kai yai"in sha Allah" ta amsa mashi da toh, sakarni inje in kwanta" sakinta yai, tafiyarta sam babu natsuwa da sauri ta nufi su hawwa ta ruƙe hannunta acikin nata suka fuce daga ɗakin.
Bayan fitarsu, Big guy ya miƙe ya dubi mutumin"Muna buƙatarka da gaggawa, ka koma ɗaki ka sanya sutura a jikinka, idan kuma zamu Iya tafiya haka toh," ya fada yana nuna gajeran wandon jikin shi da hannu.
Mutumin yace"bari naje na sanya jallabiya, ƙwara aganni da mutuncina" da zolaya ya faɗa, murmushi sojojin suka saki, fice wa yai daga dakin.