Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 6

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 6

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 6: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 6. Faɗane ya kaure a tsakanin Salsabeel tsohon ƙashi…

2,952 words

Faɗane ya kaure a tsakanin Salsabeel tsohon ƙashi da Danish garkuwar kurkuku, Yadda Danish Ya ɗaga salsabeel Ya buga shi da kasa ba ƙaramin gigita Angel yai ba, lamarin ya tsoratar da ita babban abunda take jima tsoro kada Ya kashe shi da bugu, da ko ta shiga uku, ƙarfi ba ɗaya ba Danish ya zarce salsabeel Nesa ba kusa ba saboda shi matsayin babban giant ke gare shi masu haɗarin gaske, Salsabeel Kuwa Ko star ɗaya bai da ita a muƙamin Giant, ta inda Allah ya taimake shi ƙwarewar da ya samu A fannin sarrafa tsafi, ba don haka ba da tuni Danish ya jima da karkarya ƙasusuwan jikin shi, Bugun da ya ke yi mashi da ace Lafiyayyan mutun ya yi mashi wanda baida sihiri a jikin shi da tun a bugun farkon, ga6o6in jikin shi zasu daina aiki.

Ta rasa ina zata tsoma ranta ta ji daɗi faɗansu ya yi matuƙar ta6a ƙwaƙwalwarta, Ku ka ta dinga yi hannayenta daddafe da kanta, wani irin matsanancin ciwon kai ne ya farmata, muryar Salsabeel taji a raunace ya ke faɗa mata ta ɗauko zam zam ɗin, da sauri ta rarrafa ta nufi table ɗin har ta kusa ƙarasawa Taji an Janyo ƙafarta da ƙarfi Yai wurgi da ita gefe ɗaya har saida kanta ya bugu da bango tsabar raɗadi Yasa nan ta ke ta sume. Sai faman huci ya ke yi yana gurnani, gaba ɗaya ya gama naƙasa ƙwarin gwiwarsu , shi kanshi Salsabeel Yana durƙushe ƙasa kanshi Ya bugu sosai ga6o6in jikinsa sun rauna, akan idon shi Danish Ya jefar da table ɗin da ƙafarshi, Kayan marmarin da ke asaman shi duk su ka tarwatse ƙasa, Ashe yana sane da robar Zam Zam ɗin hannunta, Kafarshi Ya ɗaga da niyar ya ta ke ta don ta fashe, A kiɗime Salsabeel Ya fasa ƙara tare da Miƙewa Yana jan kafarshi Ya nufi Danish.

Shu'umin murmushi ne Ya bayyana akan fuskar shi hada juyowa ya kalli Fuskar Salsabeel Ya ɗaga mashi gira muryarshi tamkar ta mashayin giya ya furta"What?"

"Kada ka fasa ta na roƙe ka ko dan saboda ƙaunar da ke a tsakanina da kai danish, Nifa ne Ya yan ka, Yau da hannun ka ka ke buguna kamar zaka kashe ni? Sai ka ce baka sanni ba? Laifin me muka aikata maka? Kalli kaga yadda ka Bugi ƴar uwarki Angel kamanta irin ƙaunar da ke atsakaninka da ita"? Ta6e la66ansa yai"who is she"? Tambayar daya jefa mashi kenan

Muryar Salsabeel tamkar zai fashe da ku ka Ya ce "Ka kalle ta da kyau yar uwarka ce Angel, Ba ka yi kewarta ba? Idan bazan manta ba lokacin da ka ke rashin lafiya saboda matsalar da idon ka ya samu sunanta ka ke faɗi acikin sambatun ka ko ka manta ne"? Kwa6e fuskarshi yai Alamar bai tuna komai ba.

Salsabeel sai Jan hankalin shi ya ke yi da surutu A yayin da ya ke tunkararshi duk don ya samu damar ɗauke robar zamzam ɗin da ya ke Yunƙurin fasawa.

"you're trying to deceive me" Danish Na ambaton hakan Ya dire ƙafarshi saman robar, kukan Kura Salsabeel Yai tare da cakumar Wuyan shi Da iya ƙarfin shi na ƙarshe Ya daddage Ya janye Danish gefe ɗaya, A gaban robar Sabsabeel Ya zuƙunna Yana Kallon Yadda ruwan Cikin ta ya tsiyaye ƙasa, Tsabar takai Ci yasa shi Fashewa da kuka kamar ƙaramin Yaro, ƙululun baƙin ciki ne ya addabi zuciyar shi, Damar da su ke da Ita ta ƙare, zaiyi wuya su tsira.

Jikin Salsabeel na tsuma Ya yunƙura tare da miƙewa Ya ɗaura idanuwanshi akan Bayan Danish wanda ke ƙoƙarin Tunkarar Angel don Ya ƙarasa kasheta, A hankali ya ɗaura yatsun hannun shi saman rigar jikin shi ta kakin Giant, For the fast time da yai nufin bayyana ainihin suffar shi, Cire Rigar jikin shi yai tare da jefar da ita ƙasa, Faffaɗan ƙirjine dashi Irin na sadaukan Ya ƙi, 6an6are mask ɗin da ke akan fuskarshi Yai tare da jefar dashi saman rigarshi.

Namijin Duniya Kyakkyawan gaske, fatar jikin shi Jawur ta ke, Ya fito a baturen shi, Idan ka kalli fuskar shi ba za ka ta6a yarda cewa shi jinin tsohuwa Tamira ne, saboda ita mummunace tsufa Ya 6oye kyanta.

"Na bika ta lalama ka ƙi banin haɗin kai yan zu zan yi maka ta tsiya, Danish ko ni ko kai A yau ɗin nan" Jin miryarshi yasa Danish dakatawa da yin tafiyar, cikin Takun Qasaita Ya waiwayo yana kallon shi, ganin ya tu6e rigarshi yasa ya fahimci shirin faɗa Ya yi, jijjiga jikin shi yai nan ta ke ya rikiɗa ya koma Jibgegen zaki ƙosasshen gaske sai gurnani ya ke yi yana wage bakin shi.

Hankalin Salsabeel Yai matuƙar tashi ganin ya rikiɗa, saboda shi sihirin shi bai kai ƙarfin da zai Iya rikiɗa ya canza halitta ba, ganin yadda ya ke tunkaro shi a fusace Yasa shi ja da baya ya soma tunanin me yakamata yayi don Ya dakatar dashi, idan ba haka ba A kashe zai kashe shi har lahira.

Waige waige ya dinga yi yana bin ɗakin da kallo har idon shi ya sauka akan Wuƙar yanka kayan marmarin da ke yashe saman floor, Ba zai iya ɗaukarta ba don bai son Ya cutar dashi, Lallashinshi ya soma yi yana faɗin"Am sorry Danish ni ba faɗa zanyi da kai ba, Pls ka saurare ni Danish dan Allah ka canza halittarka zuwa ta mutane ina son yin magana da kai....." Magiya ya dinga yi mashi amma ɗan tahalikin nan yaƙi sauraron shi, Juyawa yai da gudu ya nufi saman gadon ɗakin Ya daka Uban tsalle Ya haye saman shi tare da sanya hannu ya rarumo bargon dake nannaɗe saman shi, dai dai lokacin da Danish Yai kukan kura Ya daka tsalle da suffar Zaki Zai kai mashi hari Yai saurin Rufe shi Da bargon Ya nannaɗe shi a ciki, Allah ne ya taimake shi Ya bashi ƙarfin da shi kanshi yasan bana shi bane, a saman floor suka faɗo, Sosai Ya matse Danish Acikin bargon, ruƙo bana wasa ba kamar zai kashe shi, tun yana jin sautin gurnanin shi har ta kai ga yai shiru babu motsi alamar ya suma.

Tsabar farin Ciki yasa shi sakin dariya yayin da hawaye ke bin fuskarshi, tunawa da lokacin su da ke shirin ƙarewa saura Mintuna 30 ya rage masu kacal, A hanzarce Ya zame bargon da ya lullu6e shi a ciki, har ya koma suffar shi ta mutane a ƙasa ya kwantar dashi, Miƙewa Salsabeel yai da sauri ya nufi robar zam zam ɗin da ya tsiyaye, Ya ɗauko ta a tsakiyar tafin hannun shi ya dawo ya zuƙunna agaban Danish, a hankali ya buɗe mashi ƙaramin bakin shi ya dinga matsar robar ta ƙarfi kamar zaiyi hauka daƙyar ya samu ɗigon Ruwan Ya faɗa bakin shi, Ɗigo ɗaya kacal, Gani ya ke kamar ba zai isa ya dawo hayyacin shi ba, hakan yasa shi cigaba da matsa robar duk don ya samu ruwan ya ƙara ɗigowa a ƙarshe da ya gaji ya jefar da robar ƙasa, ya dafe kanshi da hannu biyu zuciyar shi na harbawa da matsanancin sauri.

faɗuwar da gaban shi ke yi ya tabbatar mashi da cewa wani mummunan abu na faru da wani nashi ko dai mahaifiyar shi, ko kuwa yaran da ya ke ƙoƙarin taimakon rayuwar su, Miƙewa yai a zabure Jiki ba ƙwari ya nufi Angel da ke yashe ƙasa tun ɗazu da Danish ya jefar da ita ta sume bata ƙara motsi ba, hannu biyu ya sanya tare da ɗaukar ta, Ya dawo ita gefen Danish Ya kwantar da ita, kafin ya ƙara miƙewa Ya nufi Kayan saman table da Danish Ya watsar dasu ƙasa, A cikinsu ya samu robar ruwa, ya ɗaukota tare da dawo wa gaban su Ya zuƙunna yana faman fitar da huci Shi kanshi a raunace ya ke daurewa kawai ya ke yi duk don ya samu ya ƙarasa taimakon su.

A Saman fuskar Angel Ya watsa ruwan a Firgice ta farka haɗi da miƙewa tsaye tana Faman zazzare idanuwanta fuskarnan jawur ta kumbura suntum.

"Unaisah" Cikin sanyin murya Salsabeel ya ambaci sunanta ko da ta kalle shi a tsoroce Ta furta"wanene kai"! Ras Ya ji gaban shi ya faɗi, Can kuma sai ya tuna da fuskarshi daya cire, shiyasa bata gane shi ba.

"Salsabeel ne" kallon shi ta dinga yi kamar yau ta fara ganin shi, ita kanta ba haka ta yi tsammanin zata ga fuskarshi ba.

"Ga ɗan uwan ki nan, Na yi ƙoƙarin ɗiga mashi ruwan zamzam ɗin sau ɗaya abakin shi bansani ba ko zai farka acikin hayyacin shi ko kuwa akasin hakan, Ba zan Iya jiran farfaɗowarshi ba, hankalina ba akwance yake ba, Ina tsoron wani abu ya sami mahaifiyata Don haka zan tafi wurin ƴan uwanki nasan tana atare dasu" Angel na ƙoƙarin buɗe ba ki tace mashi ya tafi da ita kada yabarta anan gudun kada Danish ya farka a matsayin Giant ya kasheta sai dai kash kafin tayi maganar Salsabeel tuni ya 6ace ma ganin ta...

A 6angaren Su tsohuwa zafreen kuwa Dambe su ka yi bana wasa ba, Saboda tsabar zalunci sai da ta cire mata kunnuwanta duka biyun ta cinye su, Jini duk ya wanke jikin tsohuwa tamira, duk yadda taso ta ƙwaci kanta ta kasa saboda rashin ƙwarin Jikinta, har sai da zafreen ta kwantar da ita ƙasa ta dinga buga kanta Ga ƙasa tuntuna motsi har ta kai sumewa.

Mahaukaciyar dariya zafreen ta saki ganin ta yi nasara akanta, Faɗa da aljani ba riba maganar da zafreen ta furta a yayin da take miƙewa ta nufi wuƙar da batul ta yi amfani wurin yi mata Illah, Jinin da ke a jikin wuƙar ta lashe kafin ta juyo ta dawo kan tsohuwa Tamira, Ta zuƙunna tana Shafa Jikinta da tsinin wuƙar"Na jiye maki baƙin Ciki, domin kuwa ayanzu ɗin nan zar farke Cikin ki, In kwashe ƴan hanjin dake a cikin ki In cinye su, idan kin isa Ki kwaci Kanki, ƙazamar banza har ni za ki kalli idona Ki gaya mini magana kamar bakisan wacece ni ba....." ta ambaci hakan tana mai sakin murmushi

Yunƙurin caka mata wuƙar ta yi ba zato ba tsammani taji an buge kanta da wani abu mai nauyin gaske tamkar dutse kafin ta yi yunƙurin juyawa don taga wanene taji an ƙara buga mata shi akanta, nan ta ke kanta ya juye Ta kife ƙasa,.

Batul ce a tsaye Tana haki, Hannunta ruƙe da sandar Zafreen da ta jefar ƙasa, ƙarfin sihirin da ke a jikin sandar ne yasa har ta yi nasarar kwaɗeta da ita, daddagewa tayi da ƙarfi taci gaba da buga mata sandar, Jijiyoyin wuyan ta duk sun furfuto waje saboda tsabar 6acin rai, babu sassauci atattare da ita tun tsohuwa zafreen na motsi har ta kai ga idanuwanta sun Juye, Jefar da sandar Batul ta yi ƙasa tare da ɗaukar wuƙar da zafreen ɗin ta jefar, Saman ruwan cikinta ta haye ta daddage ta dinga luma mata wuƙar Jini yadin ga ambaliya kamar an kunna fanfo harta saman fuskarta, Kacaca tayi mata sai da ta farketa, A ƙarshe dai Baful ta yi nasarar kashe tsohuwa Zafreen ko shura wa ba ta yi ba nan ta ke rai yai halin shi, harta mutu batul bata daina farke jikinta da wuƙar ba, saboda bata acikin hayyacinta, kuka ta ke yi tamkar ana zare ranta.

Farfaɗowa tsohuwa Tamira ta yi a hankali ta buɗe idanuwanta da suka ruƙida su ka yi jawur dasu, ta wurga su kan Batul da ke a zaune saman Zafreen tana aikin fiɗa.

Muryarta na rawa ta ambaci sunanta"Ba..tul.." Sai lokacin ta jefar da wuƙar hannunta, jiki na rawa ta sauko daga saman jikin zafreen ta rarrafo Zuwa gaban tsohuwa Tamira.

Fuskarta jaga jaga da hawaye hada majina, taci gaba da yin kuka tana faɗin"Ta zalunce mu ba mu yi mata laifin komai ba, ta kashe mana ƴan uwan mu ta gama da rayuwar mu....."

Hannun tsohuwa na kerma ta ɗaura shi saman sumar kan Batul da ke a tarwatse daƙyar take iya yi mata magana"Batul babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani dasu wurin baku haƙuri akan irin jarabtar rayuwar da kuka fuskanta, Ku yi haƙuri kuyi haƙuri Allah yana atare da ku......." Da numfashinta na ƙarshe ta ƙarasa maganar nan ta ke rai yai halin shi, A matuƙar kiɗime Batul ke Fuskarta.........

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E4🔥💫_

*Daga alƙalamin Hafsat Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._

wani sabon kukan ne ta kuma fashewa dashi ga matsanancin ciwon kai da ya takura mata, saboda tsabar kuka shatun jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu kamar zasu fasa fatarta, hatta saman fore head ɗinta jijiyoyin ne....

A 6angaren su Haris kuwa da ke a cikin ɗaki, tun suna kuka har sun fidda rai da ƴan uwan su zasu rayu, Tun suna iya jiyo sautin shessheƙar kukansu har ta kai ga yanzu basu Iya jin komai, A bakin ƙofar ɗakin tsohuwa Tamira suka zuzzuƙuna, Zuciyoyin na tafarfasa Gabriel yasha kuka Idanuwanshi har sun ƙafe, Haka zalika Naufal da javed babu sauran mai walwala akan fuskokin su, Mubeen kuwa Dama ba ƙoshin lafiya ce da shi ba tun lokacin da aka dawo dashi kamar mutun mutumi ko magana bai Iya yi, Daƙyar ne yai tsawaicin kwana.

A firgice su ka ɗago Da idanuwan su Jin Dirar mutun a Cikin ɗakin su, jiki na kerma suka miƙe suna kallon shi ba su san wanene shi ba, ganin su da Salsabeel ya yi ba ƙaramin karya mashi zuciya su ka yi ba, tausayin su ne ya kama shi, Cikin sanyin murya ya soma yi masu magana.

"Ku kwantar da hankalin ku, Ba cutar da ku nazo yi ba, Nima ɗan uwan ku ne nasan ba ku ta6a gani na ba, Sunana Salsabeel Ni ɗa ne ga tsohuwa Tamira"! Duk da basa acikin hayyacin su sai da suka zazzaro idonsu akan fuskarshi.

Cikin shessheƙar kuka Haris yace"ƴan..uwan mu suna a cikin ɗakin tsohuwa Tamira, Zafreen Ta kashe mana su, Muna jin sautin kukan su sai dai mun gaza ceton su saboda ta datse ƙofar....." tun kan ya kai ƙarshen maganar, Salsabeel Ya wuce da wani irin sauri Ya sanya hannu Ya daki Jikin ƙofar Nan ta ke ƙofar Ta buɗe.

A fujajen Ya faɗa Cikin Ɗakin Hankalin shi a matuƙar tashe Ya ke binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, tun daga kan su azeeza dake kwance cikin Jini saman gadon Tamira har izuwa kan su Parveen da ke a sume ƙasa Babu kaya a jikinsu, Ga Uniform ɗin su yashe a kasa da ta Cire masu, Da ƙarfi Ya ambaci kalmar Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un runtse idon shi yai sosai tare da bugun iska da hannun shi daya dunƙule, Tsabar ƙunar da zuciyar shi ke yi mashi zafinta tamkar zai fasa ƙirjin shi, Zafafan hawaye ne su ka soma wanke fuskarshi Kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu haka ya ke Ji.

"Ya Allah ka ɗauki raina In huta Idan ba haka ba zan kashe kaina ne" Muryar Batul ce ta janyo hankalin shi ga Kallonta, wa'iya zubillah Wani mugun bugu Zuciyar shi ta yi ganin mahaifiyar shi kwance cikin Jini, Kunnuwanta Biyu babu su Ga kuma gawar tsohuwa Zafreen A can gefe ɗaya, tangal tangal yai kamar zai kife ƙasa Da sauri ya tsayar da kan shi Yana faman fitar da huci mai ɗumin gaske, Ba dan Zuciyar Imani ba wlh da ɗaya daga cikinsu baƙin ciki ba zai bari Ya rayu ba. Daga Salsabeel ɗin har su Haris Allah ne bai nufa zuciyar su zata buga ba, Amma tashin hankalin da su ka fuskanta a wannan baƙar ranar baya misaltuwa. Batul sam bata lura da shi ba, Ta zama mahaukaciyar ƙarfi da ya ji kamar ma ta zauce, Agaban gawar mahaifiyarshi ya zuƙunna cikin rauni na murya ya furta"ya za ki yi mini haka mommy na? Meyasa za ki mutu ba tare da mun cimma burin mu ba, why ki ka tafi ki ka barni ni kaɗai a cikin wannan Duniyar mai cike da ruɗani"? Daƙyar ya ke iya furta maganar, cikin rauni na murya yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri saman kuncin sa, tun da ya soma magana Batul ta ɗago da runannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa jawur dasu ta ƙura su akan fuskarshi ba ta Iya gane wanene ba saboda batasan shi ba, A halin da ta ke a ciki bata Iya Fahimtar Kalaman shi.

"Hada kai Aka kashe min Ƴan uwana ko! Kai ne ka kashe su wlh kaine"! ɗago wa yai tare da kallonta, Kafin yai yunƙurin furta magana, Batul ta daddage ta Haye saman jikinshi tare da dunƙule hannunta tadinga kai mashi bugu ta ko'ina tana faɗin Mugaye azzalumai wlh ba zamu ta6a yafe ma ku ba, Kun cutar da rayuwar mu, kun kashe mana ƴan uwa, wai laifin me muka aikata ma ku ne....? bata ƙarasa maganar ba kuka Yaci ƙarfinta, Rashin sani yafi dare duhu, sam bai ji komai da abunda ta yi mashi saboda hankalin shi ba akanta Ya ke ba, Yana akan gawar mahaifiyar shi, Bawan Allah Ya ji mutuwarta Fiye da tunanin mai tunani, Ya yi danasanin irin rayuwar da su ka ɗaukarwa kansu yanzu gashi ta mutu tana aikata sa6on Allah, Sai dai shi Allah gafurirrahim ne mai rahama mai Jin ƙai, Maganar su ta ƙarshe ya soma tariyo acikin kanshi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull