Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 5
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 5: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 5. Mutun ɗaya ce ta rage A tsaye Fuskarta jaga jaga da…
3,263 words
Mutun ɗaya ce ta rage A tsaye Fuskarta jaga jaga da hawaye ta rasa ya za ta yi don tasan itama zata dawo kanta ne idon ta gama dasu Deeja gani ta ke kamar ƴan uwan su sun mutu saboda wasu daga Cikinsu babu numfashi atattare dasu Musamman jemimah da Azeza zaiyi wuya su rayu. zafreen ta gama kashe masu rayuwarsu ta wulakanta su kamar dabbobi.
A haukace Batul ta nufi table ɗin da ke ɗauke da Tunkunyar shayin nan ta ɗaɗɗago shi da hannu biyu, tana haki ta nufi tsohuwa zafreen da ta duƙufa asaman su Rubina, ta daddage ta buga mata shi, Ko gizau batayi ba, Komawa ta yi tare da ɗauko kujerar table ɗin ta dawo ta kuma buga mata ita saman kanta, still bata ɗago ba.
A fujajan ta koma cikin ɗakin tana neman abunda zata ƙwala mata, Duk ta bi ta haukace sai waige waige ta ke yi fuskarta sharkaf da hawaye, har zata juya ta wutsiyar idonta ta hango Rigar wuƙa da ke a so ke a tsakanin littattafan cikin Book shelves ɗin ɗakin.
Tsohuwar ajiye ce wuƙar da tsohuwa Tamira ta ba Danish Kyautarta a lokacin da ya buƙaci yana son datse sumar kan shi, ashe ya maida mata ita shiyasa ko lokacin da Angel ta yi mashi magiya akan ya bata wuƙar Yaƙi bata saboda bata atare da shi, da gudu Batul ta nufi book shelves din ta zura hannu ta ɗauko rigar wukar ta zaro ta Jikinta har salƙi ya ke yi saboda tsabar kaifinta, wuƙar sihiri ce mai haɗarin gaske, Cikin zafin nama ta watsa aguje bata nufi ko'ina ba sai kan Tsohuwa Zafreen a lokacin ta gama da su Rubina juyowar da za ta yi ke da wuya Batul ta daddage ta Luma mata wuƙar Cikin idonta, kafin ta yi wani yunƙurin yin amfani da sihirinta Batul ta ja wuƙar Tun daga kan idonta har zuwa saman wuyanta ta tsartsarga mata Jikinta, Wani irin ƙarfine yazo mata, Dama jinin ta akan akaifa ya ke, Zuciyar ta bushe, Gaba ɗaya tsohuwa zafreen ta gigice saboda azabar zafin da taji na shigar wuƙar, Ta yi ƙoƙarin Buge Batul sai dai Allah bai bata Ikon Yin hakan ba, ba ƙaramin Illah Batul ta yi mata ba, Sai dai duk da haka wani abun mamaki babu ɗigon Jini da ya fito daga idonta, duk inda Batul ta fasa mata da wuƙar kamar ana ɗinke fatar wurin haka ta dinga haɗewa tamkar ba'a ta6a tsaga ta ba.
So ta ke ta lalubo sandar hannunta saboda ƙarfin sihirinta yana a jikin sandar, Idan har babu ita Sauran sihirin da ke a jikinta ba lallai Ya iya yi mata tasiri ba, Daƙyar ta samu ta yi wurgi da Batul gefe ɗaya gaba ɗaya ta kife ƙasa kanta ya daku, wuƙar hannunta ta kufce mata, yunƙurawa zafreen ta yi tare da miƙewa tsaye Jikinta na kakarwa ta soma tafiya tana tunkararta, so ta ke kawai ta kashe ta har Lahira, Cikin fitar hayyaci Batul ta miƙe zaune daga kwancen da ta ke a ƙasa, Ja da baya ta dinga Yi har sai da ta ƙurewa bango.
Tuni tsohuwa zafreen ta cimmata, tafin ƙafarta ta ɗaura saman Yatsun hannun Batul ta murjesu, tsabar raɗaɗin da Batul ta ji ne yasa ta fashe da matsanancin ku ka na fitar hayyaci, wata irin zufa ta soma tsasstafo mata
"Kafin ki kashe Ni, Ni zan fara kashe ki, Dabba kawai, Kin yi kuskure da ki ka soka mini wuƙa A cikin idona, Angaya maki cewa Ni Mutunce da zan mutu farat ɗaya? Tana huci ta yi tambayar, janye tafin ƙafarta tayi daga kan yatsun hannun Batul ta ɗaura ƙafar saman jikinta da ƙarfi ta danna shi tare da murza ƙafar, Jini ne ya soma gangarowa ta cikin bakin batul Nan ta ke Numfashinta ya soma kokawar ɗaukewa.....
Ba zato ba tsammani tsohuwa Zafreen Taji an buge mata kanta da ƙarfi gaba ɗaya ta kife ƙasa, ta baya aka shammace ta, A hanzar ce ta ɗago don ta ga wanene, a matuƙar ruɗe ta ke kallon fuskarta, Ba kowa bace face TSOHUWA TAMIRA.
"Ban yi mamakin ganin ki ba Dama na jima da zargin cewa ba ki atare damu Tamira!" zafreen ce tayi maganar muryarta akausashe, saboda tsabar 6acin rai facial musles din tsohuwa tamira har kerma su ke yi, Hankalinta yai matuƙar tashi ganin yadda zafreen ta lalata rayuwar Yaran da ta raina gaba ɗaya ta gama da rayuwarsu, ta yi danasanin zuwan da ta yi amakare da duk hakan bata faru ba, idanuwanta sun yi jawur dasu tamkar garwashin wuta, wani irin hu ci ta ke futarwa
Yunƙurawa tsohuwa zafreen ta yi tare da miƙewa tsaye, Ido cikin ido su ke kallon juna babu sassauci akan fuskokin kowannan su.
"Ni dama ba ki ta6a burgeni ba, Muguwa azzaluma baƙar kafura, Ban ta6a ganin dabba Jahila daƙiƙiya irin ki ba, Wai ke baki da hankali ne? Ke fa mutunce waɗannan yaran da kika lalata rayuwar su mutanene fa ba dabbo bi ba, Laifin me su ka yi maki da har su ka cancanci wannan hukuncin daga gare ki"? Rai amutuƙar 6ace ta jefa mata tambayar.
Ɗaure fuska tsohuwa zafreen Ta yi, idanuwanta sun kaɗa jawur dasu, Babu ko alamun imani akan fuskarta
Tana magana tana huci kamar mayun waciyar zakanya" Ni kike gayawa magana? Ka da ki manta ke bakowa bace a gidan kurkukun nan face ƙasƙantacciya mai rainon Yara, dole Ki yi mini biyayya saboda ni ke agaba da ke, Nafi ƙarfin ki Tamira nesa ba kusa ba, Idan har kina son ki tsira da ranki to ki gaggauta barin wajen nan tunkafin In yi maki mummunar Ill......"Bata kai ga ƙarasa maganar ba, tsohuwa Tamira ta daka mata tsawa har saida ta furgita, karo na farko kenan da taga Rashin tsoro acikin idon Tamira.
Nuna ta ta yi da yatsan hannunta"ko da can baya da na ke girmamaki ba dan ina jin tsoron ki bane sai don Ƙudirin da na ke dashi na son Rushe Baƙin tarihin da kuka kafa, Ajali ne ke kiran ki shiyasa har ki ka yi gigin shigowa cikin ɗakina, A yau inaso in nuna maki ƙarfin ikon da na ke shi wanda na samu awurin rainon yaran da nake yi, Zafreen Yau zaki yaba ma aya zaƙinta, Ko da zan rasa raina ne saina fara ganin bayanki wulaƙantacciya kawai"a fusace ta ambaci hakan idonta akan fuskar zafreen ga dukkan alamu mamaki da al'jabi ne ya hana ta mayarwa Tamira martanin maganarta. bata ta6a tsammanin tsohuwa Tamira zata Iya yada mata magana ba tare da jin shakkarta ba.
"Tsautsayi da ƙaddara ne suka jefo waɗannan Watsastsun ƙafafuwan naki cikin ɗaki na, Kin ga babu mai kallon mu bare aji sautin mu, Yau zan huce haushina akan ki...." Tunkan ta ƙarasa maganarta, tsohuwa Zafreen ta 6ace ma ganinta, Hankalin tsohuwa Tamira Ba ƙaramin tashi yai ba, babban abunda ta ke ji ma tsoro kada ace ta bar ɗakin, In kuwa haka ta faru zasu fuskanci azabtarwa domin kuwa za ta je ne ta fallasa su.
Jin motsin mutun abayanta yasa ta yi saurin Juyawa, Har saida gabanta Ya ɗan faɗi ganin tsohuwa Zafreen ta bayyana cikin shigar jajayen kayanta hannunta ruƙe da sandarta, ashe 6acewar da ta yi don ta ɗauko sandar hannunta ne ta kuma mayar da suturarta.
"Na yi tsammanin kin ji tsoro kin gudu ne"; acewar tsohuwa Tamira
Mahaukaciyar dariya zafreen Ta saki tare da cewa"Babu tsoro a cikin zuciyar tsohuwa Zafreen! Tamira kin shiga Uku! Kin tsokanowa kanki Bala'e da masifar da ba za ki Iya jurarsu ba, Zan kashe ki har lahira bayan na gama da ke zan ƙarasa kashe waɗanda basu mutu ba a cikin Yaran can naki, Zan sha Jinin su In ci tsokar naman su"
Tana kai ƙarshen maganar ta, ta yi kukan kura tare da Afkawa tsohuwa Tamira, gaba da gabanta Aljani Ya taka wuta, Domin kuwa Zafreen tafi Tamira ƙarfin sihiri, Faɗane ya kaure a tsakanin su kamar dawakai, ba ka iya jin komai sai sautin buge bugen su da gurnaninsu uwa namun dawa, Ƙura ta karaɗe cikin ɗa ki, Kusan atare su ka canza suffofin su, Tsohuwa Zafreen ta rikiɗa ta koma Damusa, Tamira ta koma kura, Ko a namun dawa Damusa ba abokiyar karawar Kura bace, Faɗan nasu Ya canza salo, kamar a filin daga su ka cigaba da kaima junan su Hari duk suka raunata kawunan su.
*ANGEL*
Tsawon lokaci tana a sume saman Gadon da aka kwantar da ita, fatar jikinta jawur da Jinin da su ka yi mata wanka dashi duk ya daskare mata, zai yi wuya yabar Jikinta, saukar ruwan sanyin da ta ji ajikinta ne ya farkar da ita a firguce ta farka, sai dai ta kasa buɗe idanuwanta saboda nauyin dasu ka yi mata, hatta bakinta Yaƙi buɗuwa la66anta sun kumbura suntum wani irin zogin azaba su ke yi mata.
Ba zato ba tsammani kunnuwanta su ka jiyo mata muryar SALSABEEL.
"Meyasa ki ka yi gaggawa? Kin manta me na faɗa ma ki? Sai da nace ku yi takatsantsan idan ba haka ba za ku ja ma kan ku ne damu kan mu...." Sam ta ƙasa motsa bakinta, Idanuwanta kaɗai ta iya samun damar buɗe su akan jikin shi, Yana atsaye Cikin shigar Giant ko'ina na jikin shi arufe kamar yarda ta ganshi a shekaran Jiya. Ta yi mamaki sosai saboda a tattaunar da su ka yi da ita ya faɗa mata cewa ba zata sa ke ganin shi ba, sai ga shi Ya dawo yau, hakan ya tabbatar mata da cewa suna acikin haɗari gaba ɗayan su, taja masu bala'e. Rushewa ta yi da matsancin kuka raunin da ke abakinta yaci gaba da fitar da jini
Tsananin tausayin ta ne Ya kama shi, ganin yadda suka raunata Jikinta sun gur6ata mata tsaftatacciyar fatarta, tsabar takaici da danasanin gaggawar da ta yi ne yasa ta yin kukan, tana so ta yi ma shi magana sai dai ta kasa saboda sautin muryar ta yaƙi fita ko da tana yin kukan babu sauti.
"Ban faɗi hakan don na fama maki ciwon da ke acikin zuciyarki ba, Nasan kina yi ne duk don ki cece rayuwan ƴan uwan ki, don kuma ki cika mana alƙawarin da ki ka ɗaukar mana, sai dai kash gaggawar da ki ka yi ta yi silar jefa rayukan mu cikin haɗari, Zai yi wuya mu tsira sai dai bazan bari Ki rasa ran ki ba, Zan yi maku ƙoƙari Ayau ɗin nan ku fuce daga cikin kurkukun nan kafin Hankalin Matsafan ya dawo kanku, Mun ci sa'a shuwagabannin kurkukun basu aciki, Sauran da suka rage Giant ne masu haɗarin gaske, Ni kaina da na ke da sihiri a jikina bazan Iya ja dasu ba, A yanzu haka da nake Yin magana da ke nayi ƙoƙarin Sarrafa ɗakin Da ke ɗauke da madubin tsafin su shiyasa ba zasu Iya ganin mu ba, Nan da Awa ɗaya Zamu Aiwatar da komai Idan har lokacin nan ya cika kuna acikin kurkukun nan mu dukan mu zamu Mutu bayan azabtarwa da zasu Mana."
Baiwar Allah duk da raɗaɗin da bakinta ke yi mata ahaka ta daure ta cije ta soma Yi mashi magana muryarta araunace daƙyar sautin ma yake fita
"Sun cire min uniform ɗina, Ruwan zamzam din Yana a cikin aljihun wandona bansan Ya zanyi ba" cikin ƙunar rai ta ambaci hakan
"Zanje na ɗauko maki Uniform ɗin ki, cikin minti ɗaya" Yana ambaton hakan ya 6ace ma ganinta.
Yunƙurawa ta yi daƙyar ta miƙe zaune, Ƙarnin Jinin jikinta ya addabi hancinta, bargon da ke shimfiɗe saman gadon ta janyo ta yafa ma jikinta, Zuciyarta acunkushe take da damuwar halin da ƴan uwanta su ke a ciki, Ita ba ta damu da kanta ba, sune damuwarta. Fatanta Allah yasa tsohuwa zafreen bata cutar dasu ba kamar yarda ta faɗa mata.
Durowa Cikin ɗakin salsabeel Yayi hannu shi ruƙe da uniform ɗinta, Jar vest ɗinta da wandon ta Ya miƙa mata su, yatsun hannayen ta na kerma ta kar6e su, Agaban shi ta zura kayan bayan ta kammala sanya su ta zaro ƴar ƙaramar robar zamzam daga cikin aljihun wandonta, Idanuwanta acike tab da ƙwala ta kalle shi tare da cewa"Ta ya ya zan Iya ganin Danish har in bashi ruwan zam zam ɗin"?
"Bamu da isasshen lokaci, A saman bayana zan goya ki in kai ki inda Ya ke kuma zan taimaka maki mu bashi ruwan, ya kai ƙarshen maganar tare da Juya mata baya ya zuƙunna daga bakin gadon, matsowa ta yi tare da kama bayan shi ta haye, Ya yunƙura Ya miƙe, Daga inda ya ke goye da ita Ya 6ace 6att....
Ba su dura a ko'ina ba sai A wani katafaren Ɗaki mai tsawo da faɗi komai na cikin shi launin Ja ne, hatta dogayen labulayen da ke a kewaye dashi red colour ne. wani irin sanyi ne ke ratsa sassan Jiki acikin ɗaki kamar sanyin A.c, daga gani special room ne na kurkukun ƙaddara, Tsadaddun furniture ɗin da ke a cikin ɗakin kaɗai abun kallo ne.
Jin shiru bata motsa daga saman bayan shi ba yasa shi yi mata magana muryarshi cikin raɗa ya furta" Mun ƙaraso, Ki tashi ki ga ɗan uwanki" yanayin yadda ya yi mata maganar ne yasa taji gabanta Faɗuwa shi kanshi Salsabeel ɗin A tsorace Ya ke da abunda zai Biyo baya balle ita kuma da ta ke Ƴar ƙwaruwa wadda bata taka kara ta karya ba. Tsoro ya hana ta ɗago ta kalli inda Danish ɗin Ya ke duk irin kewar shi da ta yi, Sosai ta runtse idanuwanta Hannayenta ƙanƙame da Salsabeel.
"Na faɗa maki bamu da isasshen lokaci ki sauka mana" yai maganar tare da zuƙunnawa don ta sauka, Kamar wadda ƙwai ya fashe mawa akai jiki na kerma ta sauko daga saman bayanshi, sai lokacin ta samu damar Ware idanuwanta sosai Tana ƙarewa ɗakin kallo tun daga kan labulayen dake a cikin shi har zuwa kan shimfiɗaɗen Carpet ɗin dake a ƙasa Ga wani ƙayataccen table mai ɗauke da Dinner set, plate ta gani na tangaran mai ɗauke da kayan marmari, ga wani apple da aka datsi saman shi, hada sawun haƙoran mutun, Ga wani glass cup mai ɗauke da wani abu acikinsa ruwane amma launin shi yayi bright red kamar an surkashi da wani abu. Duk fa wannan kalle kalle da ta ke yi ba ta yi tozali da shi ba, saboda ta hana idonta kaiwa gare shi, Har sai da Sabsabeel yai mata gyaran murya tukunna ta soma Juyar da ƙwayar idanuwanta a hankali ta ɗaura su kan katafaren king sized bed ɗin da ke kafe a cikin ɗakin, Gado ne irin na sarakuna launin shi Golden Colour an shimfiɗe shi da lallausan Bedsheet launin Ja, slowly ta sauke idonta akan dogayen ƙafafuwanshi wa'iya zubilla tsabar ruɗu yasa ta dabarbarce saboda ta kasa yadda cewa shine, Halittar Jikin shi gaba ɗaya ta canza, Ya zama jibgegen ƙato, Samun Namiji mai irin ƙirar ƙarfin shi zaiyi wuya, ƙira ce mai matuƙar tsoratarwa, rikitarwa da kuma jan hankali, Ga dukkan alamu bacci ya ke yi a giant ɗin ma bai bar halin shi na yin bacci ba, Dogon wandone Baƙi A jikin shi, Sai Jar t shirt ta matse jikin shi, ta bayyana ainihin surar shi, musamman damtsen hannayen shi tamkar zasu fasa rigar saboda tsabar ƙarfi.
Sun canza shi sosai Farar fatar wuyan shi hada zanen tattoo launin baƙi da Ja wanda ya kasance Tambarin kurkukun ƙaddara ne duk wani Giant yana da Zanan a wuyan shi, sun rage mashi tsayin sumar kanshi, Anyi mashi kitson zane guda shida, wutsiyar kitson ta sauka har saman Broad-shoulders ɗin shi, Ya koma kamar ƴan iskan turawan nan, waɗanda tun daga suffarsu zaka shaida cewa, ba bu Ɗigon Imani A zuciyar su.
Zafafan hawaye ne su ka wanke fuskarta a yayin da ta ke ƙare mashi kallo, Ta gaza yarda da abunda idanuwanta su ke Nuna mata, Wai Danish ɗinta ne Ya koma haka? Hankalin shi kwance ya ke sharar bacci babu alamun damuwa atattare da shi, duk irin kewar shi da ta yi shi baisan ma da zaman ta ba balle sauran ƴan uwan shi, saboda zalunci na mutanan nan sun rabasu da ɗan uwansu.
Cikin shessheƙar Kuka Ta furta Sunan shi"Da..Nish.." walking nervously ta nufi bakin gadon ta zauna daga gefe tana ƙare mashi kallo, Ya yi wani irin haske mai kyan gaske, tsabar kyan fuskarshi tamkar zai kashe mata ido, la66ansa sun yi jawur dasu kamar na Jinjiri, Dogon hancin shi ya tafi tsaye ba lanƙwasa, kwarin idon shi ta zuba ma ido, dogayen eye lashes dinshi masu kyau da tsari.
"Don't waste Our time! Mintuna kaɗan suka rage mana," Muryar Salsabeel ce ta fargar da ita, Ji ta ke kamar ta faɗa mashi ta rungume shi a jikinta ko ta samu sassauci a cikin zuciyarta.
Matsawa kusa da ita sabsabeel yai "Ki buɗe murfin robar, Ni zan hau saman gadon In ruƙe shi gudun kada ya farka ya ham6are ki, naushin giant yana da haɗari sosai Bugu ɗaya su ke Yiwa mutun ya mutu In ba wani iko na Allah ba' Wannan maganar da ya yi ta ɗaga mata hankali, ta ƙara jin tsoron shi.
Yatsun hannunta na kerma ta soma ƙoƙarin buɗe murfin, tana dab da zata Ƙarasa cire shi, Kamar An ce ta kalli fuskarshi taga ƙwayar idon shi na motsi ta saman kwarin idon shi, da ƙarfi ta furta"Ya farka"
Sautin miryarta ne ya daki dodon kunnanshi, Aiko kamar an zungure shi Ya ware manyan idanuwanshi launin russet brown akan fuskarta, wani irin ƙwar jini yai mata a furguce Ta miƙe daga gefen gadon Tana ja da baya, idanuwanta azazzare, Salsabeel da ke yunƙurin ruƙe kafaɗun shi don Ya hana shi miƙewa A zafafe Yai wurgi dashi tun daga saman gadon Ya ƙundumo ƙasa Ji ka ke tummm, Hankalin Angel fa ya ƙara tashi ganin yarda ya jefar da babban mutun kamar Salsabeel yadda kasan kallon tamola haka ya jefar dashi wanda a haife salsabeel zai Iya haifarshi, Durowa yai daga saman gadon Yana huci Kamar mayunwacin zaki, breast ɗin shi har motsi su Ke yi, Wani matsiyacin kallo da taga yana binta dashi yasa ta haɗiyi yawu mai zafin gaske, kallon da Danish ke yi mata kamar ma baisan wace ce ita ba, Tunkararta Ya soma yi Yana gurnani har wani jijjiga jikin shi ya ke yi, babban abunda ta ke ji ma tsoro kada Ya rikiɗa Ya canza halitta don ta fahimci abinda ya ke shirin Yi kenan, Juyawa ta yi da gudu tana neman inda zata 6oye kanta don kada ya cimmata, saida ta gama shan wahalar kewaye ɗakin Kwatsam taga Ya bayyana agabanta. Ɗagowa ta yi a tsananin tsorace ta ke kallon shi tana girgiza mashi kai haɗi da marairaice mashi fuska don Yaji tausayin ta amma ina ai ko kallo arziƙi bata ishe shi ba, Muryar Salsabeel ce ta karaɗe kunnuwanta a kausasace ya ke bata Umarnin ta gudu daga gabanshi kada ta bari ya Damƙe ta.
kafin ta yi yunƙurin Canza hanya Cikin rashin sa'a ta ji Ya damƙi qugunta Kamar ɗiyar roba Ya ɗaga ta sama Muddin kuwa Ya bugata da kasa sai qugunta Ya 6alle saboda ƙarfin dake gare shi bana Mutun bane na baƙin shaiɗanin aljani ne, Yana ƙoƙari makata Da ƙasa Salsabeel ya cimma shi Gaba ɗaya yai wurgi da ita ƙasa ta kife robar zamzam ɗin da ke a hannunta tuni ta gangara ƙarƙashin table ɗin da ke a ɗakin gashi murfinta ya fara zamewa zai cire saboda buɗeshin da ta fara Yi, ruwan da bai wuce Kur6a ɗaya ba Ya kare idan ya zube shikenan sun rasa damar da su ke da ita.