Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 65
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 65: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 65. A zaune take kan darduma, bata jima da kammala…
3,323 words
A zaune take kan darduma, bata jima da kammala sallar asubahi ba, hijab din data sanya launin milk, gaba ɗaya ta tattara natsuwarta akan addu'ar da take Yi, ta ɗaga hannayenta sama cikin harshen larabci take karanto addu'o'i, yayin da hawaye suka cika idanuwanta, bakomai take roƙo ba face Allah ya dawo mata da mijinta lafiya da ƴarta, bata da burin daya wuce tayi tozali da su, tayi matuƙar ƙagara da son ganinsu.
Ƙamshin turaren dr.shureim ne Ya dakatar da ita daga yin addu'ar da take yi, da sauri ta shafa saman fuskarta, A hankali ta fuskance shi, yana daga zaune gefen gadonta, bai jima da shigowa ɗakin ba, fuskarshi dauke da annurin farin ciki, Daren jiya da tunanin ƴar uwarshi ya kwana, ya damu da ita.
"Yayana nakaina, Ina kwana ka tashi lafiya"?
"Lafiyalou rabin raina, ina fata kin yi kwanan farin ciki agidan Uncle" shiru tadanyi tunawa da abunda ya faru duk da ta dauki hakan amatsayin mafarki, jinjina mashi kai tayi"Alhamdulillah, jiya naji dadin bacci, hada munshari, balle ni da nake atare da Zeenatu, yarinyar akwai shiga rai"
Murmushin gefen fuska dr shureim yasakar mata"hala tacika ki da surutu"? Girgiza kai benazir tayi"a'a, ai yarinyar kunya gareta, tana jin nauyin yi min magana yadda kasan bafullatana"
Dariya dr. Shureim yai kafin ya tsagaita yace"hakane tana da kunya, amma fa ta iya zuba kamar aku, sai kun saba da ita zata saki jiki dake"
Dr shureim yasaki baki yana maganar zeenatu, baisan cewa tana la6e cikin toilet tana sauraronsu, hannunta ɗaya ruƙe da qugunta, kalmar akun daya furta ta ta6a zuciyarta.
Murmushi benazir tasaki, abunda baisani ba tun jiya tasan da surutun zeenatu, kafin su kwanta bacci, sunyi firar dare, ta saki jiki da ita tamkar abokiyarta.
"Yaya shureim, Ni yanzu damuwata Mijina da ƴata, mami ta fadamin cewa basa ƙasar, amma sun kusa dawowa, ni namanta ma ban tambayeta sunan ƙasar da suka tafi ba" ta fada tana dubanshi"yaya shureim ko kana da number wayar taj"? Ras yaji gabanshi ya fadi, saboda shi baisan komai dangane da mijin benazir ba.
Shiru yai mata batare da ya iya furta mata kalma ba, don baisan amsar da zai bata ba
"Au namanta, kaima bakasan mijina ba ko? Lokacin dana aure shi......" bata ƙarasa maganarba cak ta ɗago suna kallon juna.
Cikin sanyin murya yace"ai ba laifi kikayi ba, lokaci bana acikin hayyacina, ban kaiga farfaɗowa daga radadin abunda ya same ni ba, Benazir bansan mijinki ba, bana zumunci dashi, saboda ni kaina bana cikin natsuwata, kuma hada ƙarin ni ba azaune nake ba, idan baki manta ba, da abun duniya ya isheni, tattarawa nayi na koma egypt wurin ammim mu da zama" daƙyar yake furta maganar, launin idonshi harya fara canzawa Numfasawa yai kafin ya ɗaura da cewa"nasan ban kyauta maki ba, amma kiyi hakuri, daga ni har ke ƙaddarar rayuwace ta afka mana,"Wallahi bazan Iya misalta maki ƙunci da radadin da naji ba, lokacin da labarin tafiyarki ya same ni, idan bazan manta ba, aunty zainab ce ta sanar dani komai dangane da guduwarki da jinjirar da kika bari, bayan haka bansan komai game da rayuwarsu ba nima ban jima da dawowa gida ba......."
Bai ƙare maganar ba ta tari numfashinshi da cewa"kana nufin baka ta6a haduwa da ƴata Angel ba? Amma ni ayadda mommy ta fadamin taj yana kawota gidan mu, suna daukar dawainiyar kula da ita kuma suna nuna mata hotona harma tana tambayarsu Yaushe zan dawo"
Zaro ido dr.shureim yai alamar mamaki da jin ƙaryar da mommynsu ta shirgawa benazir, duk da ba a ƙasar yake zaune ba, yasan komai dake faruwa a gidansu, ta hanyar aunty zainab dake fada mashi akai akai, shi dai a iya saninshi Hajiya layla bata zumunci da tajuddeen, hatta auran benazir da Alhaji ubaid ya bashi bada son rantaba, saboda ita ta tsani bare, balle shi da yakasance mai rufin asiri ba attajirin mai kuɗi ba, har fada saida sukayi da Alhaji ubaid saboda yabama ɗan jarida auran ƴarsu.
Ganin yanayin fuskarshi ya canzane yasa jikin benazir yin sanyi,
"Yayana kayi shiru baka ce min komai ba! Mommy ba gaskiya ta fadamin ba ko"? Adabarbarce ya girgiza mata kai yana kokarin tattara natsuwarshi yace"bahaka bane, ai ni bana a ƙasarne, bani da masaniya akan komai, lokacin dana dawo Nigeria shi taj din da yarinyar sun riga sun bar ƙasar, nima awurin Aunty zainab naji labarin"
Ajiyar zuciya benazir ta sauke, fatanshi Allah yasa kada ta kuma tambayarshi wani abun da zai kasa amsa mata.
"Mommy ta fadamin cewa yarinyar kamanninta sak dana tajuddeen amma hasken fatarta nawane ta dauko, yarinyar kyakkyawace idan zan iya tunawa, kafin na gudu nabarta dana haifeta saida na kalleta har naga launin idanuwanta ruwan tokane kalar na amminmu, kuma tana da curly hair kalar nawa, ni dai fatana Allah yasa bata dauko halina ba, banason ace bata jin magana.
Dariyace ta kubce ma dr shureim, sambatun benazir ba ƙaramin kayatar dashi suke Yi ba.
Zeenatu dake a la6e tana sauraronsu, takasa fitowa daga toilet din, zuciyarta ta kwaɗaitu da son jin wacece yarinyar auntynta benazir? Ya akai bata ta6a ganinta ba? Kamar dai ta ta6a jin labarin jinjirar da benazir ta bari awajen mommynta sarah.
Lokaci ɗaya dr shurem yadaina yin dariyar, hawayen dake taruwa cikin idanuwanshi suka soma gangarowa saman kuncinsa.
Da sauri ya kifa kanshi on his laps, Hankalin benazir ba ƙaramin tashi yai ba, Jiki na rawa ta mike daga kan dardumar ta koma gefenshi ta zauna haɗi da daura hannunta ɗaya saman bayanshi"yaya shureim meke faruwa? Meyasa ka zubar hawaye? Yanzu fa kake yin dariya? Kona fadi wani abune daya 6ata maka rai? Shiru bai ɗago ba, duk tabi ta ruɗe, zeenatu dake yi masu la6e jikinta yai sanyi jin dr shureim dinta yana zubar da hawaye, muryar benazir taci gaba da jiyowa tana fadin"dan Allah kayi min magana yayana nakaina, kasan bana son ganinka acikin damuwa" bazata iya jurar halin da dr shureim dinta ya shigaba, Har ta miƙa hannu zata buɗe kofar toilet din, sai kuma tafasa ta dan buɗe kadan ta yadda zata iya leƙen su
Ɗagowa yai da kanshi, hawaye sun wanke fuskarshi, benazir dake kallon shi itama hawayen ke fita a idonta Zura hannunshi yai cikin aljihun jallabiyar jikinshi ya zaro wayarshi, batare dayace komai ba, Ya miƙa mata wayar, karaf idanuwanta suka sauka akan fuskarta Yarinyar dake akan wallpaper dinshi.
Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, da sauri ya sanya tafin hannunshi ɗaya ya toshe mata bakinta, haɗi da girgiza mata kai, alamar tayi shiru, daƙyar ta haɗiye kukanta, yayin da suke kallon juna, sai yanzu tagane dalilin zubar hawayenshi.
A hankali ya zame tafin hannunshi daga saman bakinta, hakan ya bata damar yin magana Cikin rauni na murya ta furta"munyi babban rashi yaya shureim, babu rabon suyi rayuwa tare da ƴata Angel, yarinyar tana kama damu, kamar ni na haifeta, mutuwa tayi mana yankan ƙauna, Allah ya jiƙanta" daƙyar ta ƙare maganar a hankali ta mayar da rinannun idanuwanta kan hoton jinjirar yarinyar dake a nannanɗe cikin towel fari ƙal, an sanya mata kayan sanyi, farace sol kamar ka ta6a jini ya ɗigo, dara daran idanuwanta sun buɗe sosai.
"Bani da abun kallo daya wuce hotonta, da ita nake kwana da ita nake tashi, na mutu akan ƙaunarta, bazan ta6a daina sonta ba, kuma bana tunanin koda ace nayi aure zan samu madadinta a duniyar nan........ ⁉️❗
"Nayi danasanin abunda na akaita mata, har yau idan na tuna cewa da hannuna nayi hakan sai inji gaba ɗaya na tsani kaina...." cikin jin ƙunar yai ya ƙare maganar.
Tsananin tausayinshi ne ya kama Benazir, idanuwansu sun kada jawur Harta bude baki zatayi magana, Motsin buɗe kofar toilet Ya dakatar da ita, sam ta manta da zeenatu a toilet, da sauri ta goge hawayenta, dr shureim ma ya share hawayen shi muryarshi adisashe yace"wanene a toilet"? Kafin ta bashi amsa, zeenatu ta fito, fuskarta da alamun lemar ruwa, tamkar batasan me suke tattaunawa ba, Har kuka tayi masu saboda sun bata tausayi duk da bata fahimci kan zancen nasu ba, ita a tunaninta Yaya shureim dinta ya ta6a son wata, sannan hoton daya ta6a nuna mata awayarshi amatsayin nata yake kallo yanzu ta gane ba ita bace, ya 6oye matane, har cikin ranta ba ta ji dadin hakan ba, jikinta yai sanyi tamkar wadda ka zarewa laka.
Sun ƙura mata ido suna kallonta, fatansu Allah yasa bata ji me suke tattaunawa ba"
"Zeeentu dama kina acikin toilet tsawon lokacin dana shigo ɗakin"?
Jinjina mashi kai tayi"eh yaya shureim bansan ka shigo dakin ba, Uziri ne Ya ruƙe ni a toilet"
Ajiyar zuciya ya sauke jin tace batasan ya shigo ba.
"Ina kwana, ka tashi lafiya" muryarshi araunace ya amsa mata"lafiyalou" duban benazir tayi wadda tayi shiru tana kallonta, daga ita har dr. shureim din fuskokinsu sunyi jawur saboda kukan da suka sha, a hake suke ƙoƙarin 6oye mata damuwarsu bayan ga alama nan ta gani.
"Aunty Benazir, bari naje daki in yi sallar acan, namanta jiya ban ɗauko hijabina ba" ta fadi hakanne don ta basu damar cigaba da tattaunawarsu
Benazir tace"A'a basai kinje daki ba, Ga hijab dina kiyi da ita" ta fada tare da cire hijabin ta miƙa mata, da sauri zeenatu tace"a'a, Kibarshi, nafison naje daki nayi acan, naga kamar kuna yin magana ne keda ya shureim"
Murmushin yaƙe Benazir tasakar mata"kada ki damu ƙanwata, bawani abu muke tattaunawaba, kema zamu Iya yin firar dake"
"Assalamu alaikum!" Mom layla ce ta doko sallama, gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta, doguwar rigace a jikinta milk colour, ta yafa mayafi akanta, fuskarta dauke da fara'a take dubansu Har suna haɗa baki wurin gaishe da ita"ina kwana mommy? Kin tashi lafiya"?
Cikin kulawa ta amsa masu da cewa"lafiyalou Alhamdulillah, fatan na same ku lafiya, zeenatu ya akai naganki atsaye"?
Washe baki zeenatu tayi tana fadin"yanzu na fito daga toilet, nayi alwala ne zanyi sallah" Mom layla tace"okey, yakamata kiyi kada ki makara" amsa mata tayi da toh, da sauri ta nufi kofar fita dakin ta fuce cike da fargaban kada Aunty Benazir ta dakatar da ita, bayan ta fita daga dakin ajiyar zuciya ta shiga saukewa, haƙiƙa taji takaicin halin da taga dr shureim dinta da aunty benazir, ta shiga damuwa tabbas tana ji aranta wani mummunan abunne ya ta6a faruwa da su, a ƙagare ta ke da son jin wacece Yarinyar benazir dinta? Sannan kuma wacece matar da taji yaya shureim dinta yana magana akai har yake fadin bazai samu madadinta ba koda ace yayi aure, burinta ayanzu shine taga hoton matar da ya shureim yake nunawa benazir a wayarsa.
Da wannan tunanin ta nufi dakinta dake acan upstairs.
Bayan fitar zeenatu, dr shureim da Benazir suka miƙe tsaye suna fuskantar mahaifiyarsu dake binsu da kallon mai tattare da alamar tambaya.
"Meke damunkune? Ya akai naga fuskokinsu sun yi ja kamar wadanda suka yi kuka"! Tambayar data fara jefa masu kenan
Benazir ce tayi kokarin cewa"Ni da ya shureim ne muke yin firar yaushe rabo, mun tuna da rayuwar mu ta bayane kafin mu rabu"
"Hmm, yakamata ku manta da abunda ya wuce, tuna bayan nan baida amfani, tun da ba abun arziƙi bane ya faru"
Dr shureim yace"hakane mommy, zamuyi kokarin yin hakan" Shiru tadanyi na wani lokaci tana kallonsu.
Har dai Benazir ta fahimci kamar akwai wani abu dake akasan zuciyar mahaifiyar tasu "Mommy, kina son yin magana damu ne"? Girgiza kai tadanyi kafin tace"tausayin rayuwarku nake ji, ina jin fargaban ranar da zan mutu in barku a duniyar nan mai cike da ruɗani, saboda mahaifinku bazai iya tsaya maku ba, shi kanshi juya shi akeyi....." jikinsu ne yai sanyi jin abunda tace, tamkar tana basu wasiyya ne, matsawa tayi kusada su tare da ruƙo hannayensu acikin nata.
"Bazan 6oye maku ba, ji nake kamar wani abu zai faru"
"Mommy ki daina fadin hakan, Ki kwantar da hankalinki, Allah yana atare damu, ni bana so naji kina zancen mutuwa" dr shureim ne yai maganar.
"Addu'arki kadai muke buƙata mama, kidaina sanya damuwa aranki" benazir ce ta fadi hakan.
Gyaɗa kai Mom layla tayi"shikenan nadaina, Benazir yaushe zaki je gidansu Aneelerh? Murmurshi benazir tasaki kafin ta bata amsar tambayarta dr shureim ya riga ta fadi "zuwa jibi in sha Allah, zan kaita gidan dakaina"
Mom layla tace"naji dadin jin hakan, zanyi magana da mahaifinku shi yake da layin mahaifin Aneelerh, in yaso saiya fada mashi game da zuwanku, tun da babu wanda yasan gidan nasu, sai sun tura mana da adress dinsu.
Benazir tace"hakan yayi mun gode mommy, ki kwantar da hankalinki, don na lura kamar bakya jin dadi"
Murmushi mom layla tasakar masu, lokaci ɗaya kuma yanayin fuskarta ya canza ganin wani abu ajikin benazir, harta buɗe baki za ta yi magana sai kuma ta fasa tana kokwanto acikin zuciyarta.
"Mommy lafiya"? Benazir ce ta fargar da ita, ganin ta ƙura ido tana kallon wuyanta" Girgiza kai tayi'bakomai, bari na koma daki, namanta banyi azhkar ba, Ina fata kuma kunyi naku, koda yake nasan ma shureim yayi ke fa"? Ta fada tana kallon benazir hankalinta yafi karkata akan jan ta6on da tagani gefen wuyan benazir kamar Yakushinta akayi fatar wurin duk ta karkarce.
"Nayi mommy, bayan na kammala sallar asuba" Jim ta danyi kafin tace"okey, ku cigaba da firar ku, amma dan Allah adaina tuna bayan nan" Murmushi kowan nan su yasaki, insha Allah mommy"
Juyawa tayi ta nufi kofar fita dakin, zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, ta rude da abunda tagani, tambayoyi ta shiga jefa ma kanta me yakawo jan tabo da sahun yakushi saman wuyan benazir? Da wannan tunanin ta nufi dakinta.
(Abunda ya faru bayan Big guy ya fita neman hannah)
Cikin takun sauri Big guy ya nufi bedroom dinsu dake a down stairs, wata'ƙil aci sa'a ya ganta, hankalin shi ba akwance yake ba, saboda ya bincika ko'ina na part dinsu saƙo da lungu babu cikon yarinyar da yake nema, ba ƙaramin ruɗewa yai ba, fargabanshi kada ace wani wajen taje ta faɗa takasa fita, ɗaya bayan ɗaya ya ke shiga dakunan matan babu kowa, yabi hanyar da zata kaishi bedrooms din mazan, A bakin ƙofar dakin su Naufal Yaci burki, Ya dafe jikin glass door din, slowly kofar ta zuge, leƙawa ciki yai, a kwakkwance ya same su saman shimfiɗeɗan gadonsu, sun cunkushe kamar kinfin gwangwani, gaba ɗaya sun lullu6e jikinsu da bargo, buga ƙofar yai ranshi a jagule Ya juya zai fuce daga ɗakin ganin mazane zalla kuma gaba ɗayansu suke aɗakinsu naufal, Cak Ya tsaya da tafiya kwakwalwarsa ta soma tariyo masa abunda ya gani, da sauri Ya koma dakin ya tsaya daga bakin gadon yana kallon ƙafafuwansu da suka leƙo daga cikin bargon, a hankali ya ɗaura eye balls dinsa kan kafar da yake hasashen ta macace bata namiji ba, shape dinta ya banbanta data mazan kuma tafi kafafuwansu ƙaranta, hannu ya miƙa ya damƙi kasar bargon ya yaye shi, lokaci ɗaya big guy yasauke nannauyar ajiyar zuciya, hankalin shi ya kwanta ya samu natsuwa, Hanna ce a tsakiyar mazan ta ƙanƙame gabriel kamar zata koma cikinsa, Yayi mamakin ganinta tsumu tsumu acikinsu, gefenta na dama naufal ne da haris, daga 6angaren hagun katifar gabriel ne da javed, sunyi nisa acikin baccinsu. Acikin zuciyarshi ya furta"Kin tayarmin da hankalina" ya ambaci hakan tare da sakin bargon Ya juya ya fuce daga ɗakin nasu.
*Unaisah Angel💋❤*
Fitowa tayi daga cikin toilet, fuskarta da alamun lemar ruwa, Salsabeel yana daga zaune saman gadon Ya jingina bayanshi jikin headboard yayin da Giant snake din yake a kwance gefenshi ya daura kanshi saman laps dinsa.
Jin motsin fitowarta ne ya janyo hankalin salsabeel ga kallonta, baiwar Allah ba ƙaramin tausayi take bashi ba, ƴar ƙarama da ita ta ɗaurama kanta damuwar da ko wani babban bazai Iya jurarta ba, ganin yana kallontane yasa ta dan sakin fuskarta data kumbura suntum.
"Fuskarki kika wanko"?
Girgiza mashi kai tai"a'a alwala nayi" "Amma ba'a fara kiran sallar asuba ba" "Nafila nake so nafara Yi, kafin a kira sallar asuba, Inaso zanyi ma danish ɗina addu'a ne" Murmushi salsabeel yasakar mata, dama saida ya ayyana hakan aranshi "Kina kaunar ɗan uwan nan naki" "Fiye da yadda nake ƙaunar kaina" ta furta hakan tare da juyawa ta nufi kofar fita dakin don taje nasu ɗakin ta ɗauko Hijabin da zatayi sallah, har ta kusa fita daga dakin kamar ance ta waiwayo ta kalli gadon
Ba zato ba tsammani macijin Ya girgiza Yana kokarin tashi Da sauri ta furta"yanzu zan dawo my Man, kada ka biyoni, Nima bazan Iya yin nesa dakai ba, Hijabin sallah zan ɗauko a ɗaki" komawa macijin yai tare da daura kansa saman laps din salsabeel.
Ajiyar zuciya ta sauke haɗi da yin ƙayataccen murmushi, salsabeel dake kallonta shima murmushin yake yi, lamarin Danish na matuƙar bashi mamaki.
Juyawa tayi da sauri ta fuce daga dakin.
Moving quickly take tattaka matakalar benan, kasancewar ko'ina na part din da haske tamkar da rana baka ta6a gane lokaci saika kalli agogo, a tsanake take bin ginin da kallo Yayin da take saukowa down, zuciyarta tayi mata nauyi, zazza6in jikinta sai ƙara nunkuwa yake yi, Ita kadai tasan halin da take aciki, da ace zata Iya dauke ma danish abunda ke damunshi da kuwa tayi hakan, zaifi mata sauƙi akan taganshi a wuyanci hali.
Tana gab da zata dira ƙafarta kan floor din falo, ranta ya bata cewar akwai mutun awurin, wurga eye balls dinta tayi akan first floor bataga kowa ba, A hankali ta mayar da eyes din nata kan Second floor, rass taji gabanta Ya faɗi ganin mutumin nan da ta ta6a gani a gym room yana motsa jiki, Ya juya mata baya, bata Iya ganin fuskarshi da kyau, batasan ya akai ta tsinci kanta da yi mashi kallon kurulla ba, bakomai take son gani ba face fuskarshi, sai dai kash takasa ganinta, faffaɗan bayanshi kadai take kallo, Ba ƙaramin jikine da shi ba, murdadden damtsen hannayensa take kallo, da alama Ya ruƙe wani abu yana sha a cup, duba da yadda hannun shi na dama ke motsi, yayin da ɗayan hannun nashi ya zura shi a shorts pocket dinsa.
Aranta ta ayyana ko wanene wannan mutumin? daga gani yana da ƙarfi da tarin dukiya, komai nashi cikin ƙasaita yake yin shi, dai dai da yanayin tsayuwarshi abun kallo ce, yaɗan jingina bayanshi jikin benan.
Hankalinta ya karkata akanshi, ta manta da hijabin da zata je daukowa, ta tafi wani tunanin daban, ita so take taga wanene shi? Ranta yafi bata cewar Chief din da taji ana fadi ne,
"Unaisah" firgigit ta ɗauke idonta daga kallon chief da take Yi, Jin muryar Boss, da sauri yake tunkarota shigowarshi kenan part din, jallabiya ce a jikin shi, Ya sanya face mask a fuskarshi, tayi mamakin ganinshi a irin wannan lokacin, abunda bata sani lokacin da boss Ya ambaci sunanta, Chief owais Ya juya don ganin wanene ke magana, dai dai sa'adda ita kuma ta kawar da kanta, Natsuwa yai yana dubansu daga can saman second floor.
"Ba ki yi bacci ba"? Tambayar da boss ya jefa mata kenan a yayin daya ƙaraso gabanta yaci burki ya tsaya yana kallon fuskarta.
"Banjima da farkawa ba, amma meya hana ka bacci" ta tambaya tana kallon rinannun idanuwanshi masu dauke da tsantsar damuwa "Taya zan Iya yin bacci? Bayan kema bakiyi ba" Matashin murmushin ta ɗan saki, har cikin ranta taji dadin maganarsa, shi kuwa ji yake kamar ya rungumeta ko dan yaji sanyi aranshi, ya damu da halin da suke aciki ita da ɗan uwanta, tausayinsu ya hanashi sukuni har ya gaza runtsawa shiyasa ya fito don yazo ganin su.
"Yakamata ka kwanta ka huta boss, na fahimci ka damu dani, meyasa"? "Taya bazan damu dake ba? Kefa jinina ce, jinin dake yawo ajikina shi yake yawo ajikin ki....." da sauri Ya katse maganar, Jin su6ul da bakan da yai, murmushin gefen fuska tayi mashi, ga dukkan alamu taji dadin maganarshi
"Boss kayi shiri baka ƙarasa zancen ba? Ni wallahi idan kana Yi min magana sai inji kamar mahaifina"
"Meyasa kikace haka"?