Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 66
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 66: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 66. "Saboda Yana ƙaunata fiye da yadda yake kaunar…
3,347 words
"Saboda Yana ƙaunata fiye da yadda yake kaunar kansa, ya sadaukar da farin cikinshi saboda ni, nayi rashin ji aƙuruciyata, na azabtar da daddyna amma duk idan na tuna ayanzu sai inji haushin kaina......" sambatu take yi mashi sam batasan me take furtawa ba, abune ya haɗe mata ga radadin da zuciyar ta keyi mata shiyasa take yi mashi zuba, tana magana hawaye na taruwa acikin idanuwanta.
"Amma meyasa kike jin haushin kanki ayanzu"? Muryarshi araunace ya furta mata maganar.
Shesshekar kuka ta soma yi mashi tana fadin"saboda nagane cewa bani da masoyi a duniyar nan daya wuce shi, bani da tamkar shi har abada, Har yau idan na tuna cewa shine silar duk wani abu dana koya aduniyarnan ba ƙaramin dadi nake ji ba....." kasa ƙarasa maganar tayi, sakamakon janyota da yai zuwa jikinshi ya rungumeta sosai, haɗi da daura hannayenshi saman bayanta yana lallashinta, bata kawo komai aranta ba, sai dai bugun zuciyarta da taji ya ƙaru, tajima tana mamakin yanayin da take tsintar kanta idan Boss yana akusa da ita, sakankancewa takeyi taji kamar daddyn ta ne ya dawo.
"Ya isa haka, ki daina kuka Unaisah, In sha Allah, daddynki zai bayyana, bama ke kadai ba da sauran ƴan uwanki duk zamu binciko maku danginku"
Ajiyar zuciya ta shiga saukewa, takasa raba jikinta daga nashi, tamkar zata koma cikinshi.
Duk wannan abun dake faru atsakanin Boss Man da Unaisah, akan idon chief owais, yayin da yake kur6ar coffee dinsa.
Tunawa da Hijabin da zata daukone yasa tayi saurin furta"boss namanta, alwala nayi zanje daki na dauko hijabi da prayer mat, yakamata na tafi idan danish yaji na dade zai Iya biyoni, yanzuma da ƙyar ya bari na fito" ta fada tana raba jikinta daga nashi. "Nagode da kulawarka agaremu," "Kada ki damu, muje na rakaki ɗakin," "Banaso na takura maka, naga idanuwanka sun kaɗa jawur, baccine a idonka yakamata kaje ka kwanta" ta fada tana kokarin kakaro murmushi Ruƙo hannunta yai acikin nashi da zolaya yace"saifa na biki Allah, ai tunda baki runtsa ba nima bazan yi bacciba, zan zauna atare daku har sainaga abunda ya turema buzu naɗi" Dariya tadan saki jin maganarshi ta ƙarshe, atare suka jera zuwa bedroom din nasu. Koda suka ƙarasa dakin, arude ta furta"Boss babu batool fa"! Ta fadi tana faman zare ido akan gadonsu.
"Calm down ur mind, nasan inda suke, ba sace su akayi ba, abunda ya farune dazu ya tayar masu da hankulansu, shine na rakasu dakin Ummi, nasan yanzu haka sunyi nisa acikin baccinsu" ajiyar zuciya ta sauke, har taji sanyi aranta.
"bayin Allah, nasan daƙyar suka Iya runtsawa, musamman Azeeza tafi kowa tsoro a cikinsu" ta furta hakan tare da kama hanyar closet dinsu, bin bayanta yai da kallo harta 6ace ma ganin shi.
Maganar amininshi ce ta fado mashi aranshi, a ranar daya kira shi video call yana daga kwance saman gado shida Angel dinsa.
Tuni idanuwanshi suka cicciko tab da ƙwalla, haƙiƙa yayi babban rashin da bazai ta6a samun mai maye mashi gurbinshi ba" A hankali Ya furta"Allah Yajiƙanka aminina" "Boss mu tafi" muryar unaisa ce fargar da shi ga kallonta, Harta zura hijabin ajikinta launin milk, Iya gwiwa ta tsaya mata, hannunta a ruƙe da prayer mat. Lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke, dama ranta babu daɗi, dauriya kawai take Yi, "Meyasa kika 6ata fuska"? Zumbura mashi baki tai kafin tace"kaine mana, kaƙi jin maganata ni nasan baccine ke addabarka, amma kaƙi zuwa ka kwanta, kalli idanuwanta har sun canza launi sun yi jawur da su..." cikin kulawa tayi maganar In a cool voice ya furta"karki damu dani, babu bacci atare dani, idona ne keyi min ciwo, kafin na fito daga gida saida na ɗiga magani" Unaisa sarkin tausayi, duk sai taji ba dadi, jin baida lafiya. "Allah yabaka lafiya boss, amma dan Allah kaje ka kwanta kayi bacci" Bakomai ya tuna ba face maganarta lokacin da tana yarintarta, Idan baida lafiya ya kwanta don yai bacci, saman jikinshi take hayewa tana fadin ai wallahi bazan bari kayi bacci ba, ka jira sai lokacin da nima zanyi sai muyi atare, idan ta fadi hakan to bai isa yai bacci ba, dole yajira har zuwa time da zata gama wahalar dashi tukunna suyi bacci, yayi zurfi acikin tunanin shi muryarta ta dawo dashi "Ka ƙura min ido kana kallona, ko nayi maka kama da wanine"? mamaki take bashi idan tana magana. Adabarbarce ya furta"um...bakomai mu tafi kawai" Ya ruƙo hannunta acikin nashi, Suka nufi ƙofar fita daga dakin.
Kafin dawowarsu dakin danish, Tuni Big guy ya kawo mashi fresh fruit, a faffadan tray ya ajiye mashi saman mattress, abunka ga maciji, ɗai ɗai yake ɗauka da baki Yana lunkuma shi, Cikin ƙanƙanin lokaci Ya shanye kayan marmarin, bayan Ya kammala ci, Big guy ya tambayi Salsabeel Ina Unaisah take? Yaga babu ita adakin salsabeel Yace ta fita dauko hijabin sallah ne, amsa mashi yai da okey, kafin Ya dauki tray din Ya juya yabar dakin.
Adai dai lokacin daya sauko down hannunshi ruƙe da tray, Unaisah da Boss man suna kokarin nufar benan, Da mamaki big guy ya furta"wa nake gani kamar Boss namu? Me ye hana ka runtsawa"? Fuska asake Boss Ya nufe shi yana fadin"abunda ya hanaka runtsawa nima shi yahana in runtsa"
Dariya big ya saki"kai dai fadi gaskiya mutumina, nasan me ya hanaka yin bacci, damuwace ta isheka da fargabar kada maciji ya sari ƴarka, koba haka ba"? Ya faɗa yana ɗage mashi gira da zolaya. "Baka da dama Big guy, ai dole na damu, ita kaɗaice fa ƙwallin ƙwal, bugun zuciyar,"ya fada idanuwanshi akan unaisah wadda tuni Ta haura saman bene don ta isa ga dakin danish "Na fahimci ba ƙaramin so ka ke yi ma yarinyarnan taka ba, nima kuma inasonta, me zai hana ka bani auranta?da zolaya yai maganar Harara Boss Ya watsa mashi shima da zolayar yace"ka dai bi a hankali, kada mamallakinta Yaji ka, kaima kasan me zai biyo baya," Da sauri Big guy ya toshe baki yana fadin"au namanta, ashefa ka bayar da ita, balle ma nasan koda baka bada ita ba da wuya ka bani ita, don na fahimci kafison inda zata huta" dariya boss yasaki yana fadin"kamar ka sani, kaima din ai ba daga baya ba, sai dai kayi mata tsufa, ina laifin ka nemi ummi mana zata dace dakai....." tunkan ya ƙare maganar, Big guy ya galla mashi harara"Allah Ya kiyaye, in rasa wazan nema sai karuwa" Boss yace"abar dai kaza cikin gashinta, kaima din ai tubabbe ne, nima labari naji" "Ina ganin girmanka man, mu bar maganar, bana son tuna baya, Ni bansan ma wani munafukinne yabaka labari ba, wallahi da zan sani saina takaita jin dadinsa" Dariya Boss yai ganin yadda ya 6ata fuska.
"Sorry mutumina, zolayatace kawai, ni bansan komai ba, kaine ka kama kanka,"
"Next time idan ka ƙara min wannan wasan, A jikin ƴarka zaka gani" Ya fada tare da bi ta gefen Boss Ya wuce yana dariya, shima Boss din dariyar yakeyi "Ai kai ƙaramin ɗan iskane, sai dai ka cika baki indai akan Angel dinane, don kuwa kasan ko kallon banza kayi mata a jikinka zaka gani," Big guy bai juyo ya dube shi ba, Yai tafiyarshi.
Bayan komawar Unaisah dakin, a kishingiɗe ta samu salsabeel harya gaji da zama, macijin yana nannaɗe gefenshi.
Tayi tunanin bacci yake yi hakan yasa ta soma yin sanɗa tana tafiya duk don kada ta farkar dashi, shimfida dardumar hannunta tayi, kafin ta daidaita natsuwarta, ta kabbara sallah.
Boss na kokarin shigowa dakin aka fara kiraye kirayen sallar asuba, daga bakin kofar ya tsaya yai gyaran murya, salsabeel daya lumshe idanuwanshi jin gyaran muryar da Boss yai mashine yasashi bude idanuwanshi "Sannu da kokari, Mun hana ka bacci," yamutsa fuska salsabeel Yai, bacci yana neman yaci ƙarfin shi "Baku kuka hanani bacci ba, ni na hana kaina saboda ɗan uwana" ya fada yana duban macijin. Kallon shi Boss Yai, gwanin ban tausayi ya langwa6e kansa, bawan Allah takaicin duniya ya ishe shi. Shiga cikin ɗakin Boss Yai, a bakin gadon ya dakata da yin tafiyar yana kallon Giant snake din "Bacci yake yi"? Ya jefa ma salsabeel tambayar "Bazai Iya runtsawaba, idan har ba Ƴar uwarshi tana atare da shi ba, sai kuma idan ya dawo ainihin halittarsa" Cikin tausayawa boss yace"kayi hakuri, wata rana sai labari, In sha Allah ƙarshen wahalarka ne Yazo, wadanda suka yi silar ƙuntata rayuwarka, bi'iznillahi ajalin su ne yazo, zasu ɗanɗani kuɗarsu har sai sunji dama ba a halitto su a duniyar nan ba, sai sunyi danasanin rayuwarsu....." kalamai masu dadi da kwantar da hankali Boss yake fada ma giant snake din, yayi lamo yana sauraronshi.
"Naji an fara kiran sallar asuba, Bari nashiga toilet inyi alwala, idan na fito kaima saika shiga ka yi mu tafi masallaci," yai magabar yana duban salsabeel. Batare da 6ara lokaci ba, Boss ya shiga toilet ya dauro alwala, bayan ya futo salsabeel Ya shiga shima yai alwalar,, sallama sukayi ma Unaisah dake zaune saman darduma, kafin suka tafi.
Kamar jira take Yi, subar ɗakin, jiki na 6ari ta miƙe ta nufi gadon ta haye gefen shi tana kallonshi, ta fahimci bacci yake ji, hakan yasa ta janyo bargo ta lullu6asu don ta taimaka mashi yai bacci.
*EX-PRISONERS❤*
Lokacin da Batul ta farka daga bacci, jikinta duk ba daɗi, tamkar mai fama da zazza6i, mura tayi mata mugun kamu, muryarta daƙyar take fita, fitowa tayi daga cikin bargon idanuwanta sunyi luhu luhu, ƙoƙari take tabar dakin duk don kada ta ƙara haɗa ido da ummi, tayi tsammanin zata ganta asaman gadon sai ganinta tay kwance saman carpet, ta lullu6e half body dinta da bargo, tafi ƙarfin ta haɗa shimfiɗa da su shine ta dawo kan carpet ta kwanta. Muryar batul kasa kasa ta ke ambaton sunan parveen, Daƙyar ta samu parveen ta farka daga bacci, tana faman yin miƙa haɗi da yin hamma, juyawa tayi 6angaren su Jemimah ta soma tada su daga bacci ɗaya bayan ɗaya suka farka suna faman mutsustsuke idonsu.
Cikin muryar rada take yi masu magana"ku tashi mu tafi ɗaki, lokacin sallar asuba yayi," ruƙo hannun jemimah tayi ta sauko da ita daga saman gadon, Parveen ta ruƙo hannun Azeeza suka sauko.
"Bana so ta farka ta ganmu, kada ku yi surutu mu lalla6a mu bar mata ɗakinta" ta faɗa tana dubansu, Jinjina mata kai su ka yi alamar toh.
Cikin takun sanɗa suka nufi ƙofar fita dakin, sai da suka fita Batul ta tuna da kayan ummi dake a jikinta, dafe kai tayi da hannu ɗaya"nashiga uku ashe ban cire mata kayanta ba, Parveen ki ruƙe hannun Aziza dana jemimah ku tafi ɗakin mu zan biyo ku daga baya"
Maƙe kafada jemimah tayi"ni tsoro nake ji, idan abun nan ya ganmu fa"? "Kada ki damu, babu shi ai, waɗannan mutanan sun kashe shi" daƙyar batul take Yi masu magana "Batul baki lafiya? Idanuwanki sun kumbura jawur, muryar ki kamar ba'aji sosai" Azeeza ce tayi magnar.
Kafin batul ta bata amsa parveen tace"sanyine ya kamata, sai da na hana ta kar6i rigata amma ta kar6a tasaka"
"Amma ai aunty ummi ta bani kaya na saka, Kawai bana jin daɗine bawani abu ke damuna ba, Ku tafi ɗaki zan biyoki" Ta faɗa tare da juyawa ta nufi ɗakin.
A tsananin tsoroce suke tafiya suna tunkarar benan, parveen tana aruƙe da hannun azeeza dana jemimah, har yanzu basu daina jin fargabar macijin ba.
Bayan batul ta koma dakin Ummi cikin sanda take tafiya, harta ƙarasa gaban gadonta, ta cire mata kayanta, ta ɗauki doguwar rigar parveen data jefar ƙasa, ta zura a jikinta, Juyawar da zatai keda wuya, taji sautin datse kofar ɗaki, rass taji gabanta ya fadi ganin ummi atsaye bakin kofar ta goya hannayenta kan ƙirjinta, fuskarta a murtuke babu annuri, idanuwanta sun ƙanƙance.
Hankalin batul ya tashi matuƙa, agigice ta furta"aunty ummi ina kwana" Harara ta galla mata"daban kwana ba kin ganni atsaye? Kilbabba uwar iyayi"
Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Ai na cire maki kayanki, gasunan kan gado, Ni dakinmu zan tafi, wajen unaisah"
"Idan kinga na ƙyale ki kin fita daga dakin nan, to kuwa kin gyara sautin muryarki ne, wallahi baki isa kija min bala'e ba, Har kayan sanyi na baki, na kuma kashe sanyin a.c, saboda baƙin hali irin naki saida kika bari mura tayi maki mugun kamu duk don kija min masifa ko"?
Hawayene suka soma wanke fuskar batul, muryarta na rawa tace"ba haka bane aunty ummi, nima bayin kaina bane, bansan mura ta kamani har haka ba, dan Allah kibarni in koma cikin ƴan uwana"
Shu'umin murmushi ummi tayi mata, "Zan barki ki tafi, amma kafin nan saina fara kawar maki da murar nan, don haka mu shiga toilet inyi maki wanka da ruwan zafi"
Zazzare ido batul tayi hadi da girgiza kanta"dan Allah aunty ummi ki ƙyaleni, ai ni ba yarinya bace, da zaki min wanka, ni kawai ki rabu dani nayi maki alƙawarin babu wanda zaisan ina yin mura"
Ɗaure mata fuska ummi tayi zaki wuce mu shiga toilet ko saina 6ata maki rai"?
Cikin jin ƙunar rai, batul ta maƙe mata kafaɗa"ni bazan shiga ba, Na fada maki banaso, ki ƙyaleni," atakure take Yi mata magana, makoshinta radadi yake yi mata. Ganin ummi na tunkarota ne yasa ta soma ja da baya tana kuka, kokarin kubce mata tayi da sauri ummi ta damƙo sumar kanta, tajata ta ƙarfi ta shigar da ita toilet tana fadin"Ke har kin isa ki kufce min, ƙaramar ƴar shila dake, me zan gani a jikinki? da har kike fadamin ke ba yarinya bace" sautin kukan batul ya cika dakin ummi, gigitacciyar tsawar data kwatsa matane yasa tayi saurin jan baki tayi shiru, hawaye na cigaba da bin fuskarta.
Ummi tafi ƙarfinta, da girmanta da komai, Tayi mata wanka da ruwan zafi, tamkar zata sale mata fatarta, fitowa ummi tayi daga cikin toilet din, ta nufi closet din kayanta, tana faman sakin murmushin mugunta, riga da wando ta dauko masu kyan gaske, na saƙa launin pink, waɗannan kayan tsohuwar ajiyace tuntana ƴar shekara sha bakwai a duniya take 6oyansu, tana matukar son kayan, rigar tana da hula hannunta dogone.
Komawa toilet din tayi kamar yadda tabar batul haka ta sameta, ta ƙanƙame kanta jikin bango, dan pant ne ajikinta, hannunta biyu tallabe da kirjinta ta kakkare boobs dinta.
Jefa mata kayan ummi tayi da sauri ta kar6esu.
"Ina jiranki aɗaki, salon kuma ki daɗe, idan kika ƙara mintuna wani wankan zan sake yi maki" cike da isa ta furta maganar, kafin ta juya ta fuce daga toilet din, abakin ƙofar ta dakata tana jiran fitowar batul.
Jin motsin buɗe toilet door dinne yasa ummi kai idonta ga dubanta, har saida taji gabanta ya fadi, ganin kyan da kayan sukayi ma batul, rigar tayi mata daidai, wandonma haka, kamar don ita aka saƙa kayan, bata sanya hular ba, yalwatacciyar sumar kanta ta sauko har gadon bayanta dark brown.
Sai faman ƙanƙame jikinta take yi, ganin yadda ummi ke kallontane yasa ta duƙar da idanuwanta ƙasa, duk tasha jinin jikinta.
Batasan ya akai ta tsinci kanta dayi ma fuskar batul kallon sani, sai dai tarasa tuna dawa take yi mata kama. Matsawa tayi kusa da ita, takai hannu ta ruƙo hular rigar ta sanya mata ita, sai taga ta ƙara yi mata kyau.
"Ki daina ganin ina kallonki, ba kyau kikayi min ba, Munin fuskarki nake kallo" shiru Batul batace mata komai ba, bayan ta kammala gyara mata hular rigar, ta nuna mata gado"ki koma ki kwanta, har zuwa time da muryarki zata dawo dai dai kinji ko"? Maƙe mata kafaɗa batul tayi"ni bazan kwanta ba, dan Allah kibarni in tafi daki wajen ƴan uwana, Inason ganin Unaisah" muryarta shaƙe ta furta maganar. "Wato saboda kinga makwancina shiyasa kika fara rainani ko? Har kina da bakin fadin Bazaki yi abu ba idan nasaka ki, Dalla ni wuce ciki ko inyi ball dake"
Ƙin matsawa Batul tayi, gani take kamar ummi zata iya kasheta, furucin da tayi mata jiya sun firgitar da ita, sun kuma tsaya mata aranta.
Zabura tayi da niyar ta nufi kofa don ta gudu, ai kuwa azafafe ummi ta damƙota kamar ɗiyar roba haka ta ɗaga ta sama, ta nufi gado ta jefar da ita, ta kuma janyo bargo ta lullu6eta tana fadin"idan kika kuskura kika leƙo koda kankine saina murƙusheƙi" Muryar batul da shessheƙar kuka take fadin"aunty ummi dan Allah kibarni in tafi, banason kwanciyar, ni wajen ƴan uwana zanje" ummi dake tsaye tana kallon bargon tace"idan kina son fita daga dakin nan to ki fara gyara muryarki"
"Ai ni bansan yadda zan gyarata ba, ki bani magani in sha"
Ta cikin bargo batul take Yi mata magana.
Tunani ta somayi aranta, ina zata samo mata maganin mura? Tasan ba'a rasa dakin ajiye magani a gidan tun da na jami'ae ne kuma yaran an tanadar masu komai da zasu buƙata saboda rayuwar kullece aka shirya masu.
Boss man kadai take da contact dinsa, awayarta, daukar wayar tayi dake ajiye on bedside drawer ta danna ma Boss kira, cikin sa'a ya ɗaga kiran.
Cikin girmamawa ta gaishe da shi"barka da asuba yalla6ai" On the other hand muryar boss ta amsa mata da cewa"wa'alaikum salam, ummi barka da safiya" "Yawwa barka, Allah yasa dai ban katse maka baccinka ba"
"Kada ki damu, idona biyu yanzu nake shirin zuwa cikin gidan, ko akwai wani abu da kike buƙata"?
"Taimako nakeso kayi min in ba takura, maganin mura nake buƙata"
"Wanene ke baida lafiya"? Da sauri tace"nice zan sha, Yaran dake atare dani lafiyarsu ƙalau' amsa mata yai da okey, idan zan shigo gidan zan taho maki da shi"
"Nagode" katse kiran tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, Batul dake a ƙumshe cikin bargo, abun duniya ya isheta.
Muryarta shake tace"aunty ummi banyi sallar asubaba, kuma ina jin yunwa" Guntun tsoki ummi taja"kiyi min shiru malama, ni ma ai banyi sallar ba, kuma ina jin yunwar bawai bana ji ba"
Ta fada Tare da samun wuri daga gefen gadon ta zauna tana gadin Batul, hannunta ruƙe da wayarta, chatting ta kama yi, batul tayi shiru cikin bargo tana faman matse ƙwalla.
A katafaren Villa Mallakin Hateem Obinna, haddadiyar daula kuma aljannar duniya wadda idan ka zura ƙafarka acikinsa sai ka yi tsammanin ƙasar dubai ka shiga, Hamshaƙin Gidanshi a kewaye yake da Jami'ae sojoji da ƴan sanda, mugun tsaro ake yi mashi, babu wanda ya isa ya ƙetare gidan hateem cikin sauƙi idan ba Mahaifinsa ba da yayyansa, amma bayan wadanda kafin mutun ya samu iznin shiga ciki sai ya ci baƙar wahala don kuwa daga ƙasa har sama zasu bincike ka da na'ura, har ƙwara mutun ya shiga masarauta yafi mashi sauki, akan Gidan prime minister, tsaruwar ginin gidan kuwa da haduwarshi ba'a magana, gaba ɗaya Obie estate babu gidan da yakai Na prime minister In ka cire Villah din Owais.
*Gimbiya Mujeedat👑*
A kishingiɗe take saman Katafaran gadonta na alfarma, kalar na sarakuna waɗanda suka gaji Arziƙi, gadon a kewaye yake da labulaye launin royal blue, an ƙawata shi da lallausan zanen gado fari ƙyal, haɗi da matassan kai launin blue and white, gefe da gefen gadon bedside drawers ne suma launin royal blue, daga saman su Fitilune masu bada haske launi daban daban, an zuba mata tsadaddun furniture a ɗakinta, ya ƙawatasu sosai da kayan alatu.
ta ɗaura kanta saman pillow, Rigar dake a jikinta Silk robe ce launin ice blue, tabi shape dinta ta bayyana dirarran dirin jikinta, A halitta Gimbiya Mujeedat doguwace, fara sol tana da dogon wuya, hutu ya zauna mata ta ko'ina Allah Ya hore mata, Kyau kamar ita ta zana kanta, fararen idanuwanta tamkar an ɗiga masu zaiba, launinsu dark black ne, ga tarin ziraran eye lashes dinta da suka ƙawata kewayen idanuwanta sun yi mashi rumfa, dogon hacinta a tsaye yake babu lanƙwasa, siraran la66anta launin ja tamkar na jarirai tsabar ƙarantarsu da laushin fatarsu, tana da yalwatacciyar sumar kai baƙa wulik mai santsi da silbi, har gadon bayanta, Tabarakallahu ahsanul khalilin Gimbiya mujeedat maƙurace afagen kyau, uwa uba ta fito daga tsatson masarautar daular larabawa, bugu da ƙari First Lady ta ƙasar Canada, ajin farko ce ita, zan iya cewa baba Hateem Ya more mata 😉