Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 67
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 67: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 67. Ziririyar sarƙar wuyanta ta zallar diamond ce,…
3,286 words
Ziririyar sarƙar wuyanta ta zallar diamond ce, haka zalika Ziraran yatsun hannunta na dama suna sanye da Ring set na Gold komai nata me tsadane ita kanta lu'u lu'un ce.
Yanayin yadda ta kwanta da alamun kasala atattare da ita, ta ɗan lumshe idanuwanta, fuskarta sam babu walwala, kamar akwai wani abu dake damunta.
A lokacin da bata yi tsammani ba, muryar prime minister Hateem ta karaɗe kunnuwanta, sallama ce yai mata yayin da yake shigowa dakin, Cikin shiga ta jallabiya launin maroon, daddaɗan ƙamshin turarenta dana ƙamshin turaren wuta ne Ya daki hancinsa Har saida Ya lumshe idanuwanshi, mutunne shi ma'aboci son ƙamshi, sai kuma Allah Ya haɗa shi da mace ma'abociya son kamshi da son ado, shiyasa a kullum take ƙara shiga ranshi, soyayyarsu bata tsufa, Idan suna atare da juna daukar kansu suke Yi tamkar sabbin ma'aurata.
Bata samu damar amsa mashi sallamar shi ba, daƙyar ta iya buɗe idanuwanta da sukayi mata nauyi, launinsu ya rikiɗa zuwa ja, saboda rashin baccin da batayi ba adaren jiya kuma shine sila, Ya hanata sukuni, bai ta6a burkice mata ba irin Na jiya, Ƙiri ƙiri Ya takura kanshi, Ya hana kanshi runtsawa, kuma yaki fada mata abun da ke damun shi, daga ita har shi jiya babu wanda ya runtsa, saboda ta maida damuwarshi tata.
Koda ya shigo dakin, a hankali ya daura idanuwanshi kan fuskarta, sai yaji ba daɗi har cikin zuciyarshi yasan bai kyauta mata ba, tunda ya riga da yasan halinta na damuwa da damuwarshi.
Daga gaban gadon Ya dakata dayin tafiyar, ya goya hannayenshi on his broad chest yana fuskantarta.
Ba zato ba tsammani, yaga ta galla mashi harara haɗi da murguɗa mashi ƙaramin bakinta.
Nan take ya fahimci fushi take yi da shi, ranta ya 6aci. Cikin harshen turanci tace"Sannu da dawowa"
Ta inda gimbiya mujeedat take burge shi, duk mun fushin da zatayi dashi hakan bai hanata kula da shi
"Yawwa, fatan na same ki lafiya"
Yamutsa fuska tayi fuskarta babu annuri ta soma magana tamkar bata son furtata.
"Mijina baka kyauta min ba, ka hana kanka runtsawa nima kuma ka hanani runtsawa, nayi koƙarin faranta maka duk don na kawar maka da damuwarka amma babu abunda ya canza, Ka jefa ni cikin wani hali daga daren Jiya zuwa yau, meyasa ba zaka fadamin meke damunka ba? Ko ban isa nayi maka magani bane? Nasan ka yarda dani, sannan baka 6oye min komai, sirrinka nawa ne amma meyasa jiya kaƙi fadamin damuwarka" sautin muryarta tamkar ana busa sarewa tsabar daɗinta.
Idanuwanta aruntse take yi mashi magana, don ta fahimci idan tana kallon cikin idanuwanshi bazata samu ƙwarin gwiwar yi mashi magana ba"
Sauke hannayenshi yai daga saman kirjinshi, ya zagayo ta gefen da take a kwance Ya zauna, yana duban fuskarta Ƙayataccen murnushine kwance kan la66ansa, yasan ta kan mace, idan ranta ya 6aci cikin sauƙi yake faranta mata
"Uwar gida sarautar mata, Gimbiyata, Ina neman afwarki ranki shi daɗe, bai kamata gimbiya tana fushi da bawanta ba, Ni fa a karkashin inuwarki nake, da taimakonki nake samun natsuwa da kwanciyar hankali, taya zanso na 6ata maki rai? Bayan kece linzamin dake sarrafa ni...." Tun da yafara gaya mata daɗaɗan kalamansa, ta fara sassauta fushin fuskarta, A hankali ta buɗe idanuwanta kan fuskarshi, da sauri ya kama kunnuwansa Yana fadin"Am sorry My wife, na gane kuskurena" Ta6e mashi baki tayi"Ni so nake ka fadamin meke damunka? Da har yai silar hanaka runtsawa, kalli fuskarka duk ta yamutse, idanuwanka sun ƙanƙance saboda rashin baccin da baka yi ba" ta faɗa tana faman 6ata fuska, yayi shiru yana kallonta batare daya furta mata komai ba.
"Kai nake sauraro! Meke damunka? Sannan naji kana waya ɗazu, akan za'a tura da jet zuwa sudan, wa za'a ɗauko"? Ta jefa mashi tambayar cike da son jin amsar shi.
Ya rasa amsar da zai bata, Ta kafe shi da ido. Gyara muryarsa yadanyi kafin yafara magana a tsanake.
"Sheikh imam nake son gani, baya a ƙasarne ya tafi sudan, Ina buƙatar ganinsa da gaggawa akwai taimakon da zaiyi mani"
Fuskarta da alamun mamaki ta furta"meyasa kake son ganin shi? Wani kalar taimako zaiyi maka"
"Wani matashin yarone yake fama da aljanu sun hana rayuwarshi sakat, jiya ina zaune tare da baba muna yin firar yaushe rabo, a lokacin da bamuyi tsammani ba, yaron ya faɗo falon gwanin ban tausayi, duk mai imani idan yaji irin jarabtar da yaron yake fuskanta sai ya tausaya mashi....." tun da ya fara magana gimbiya mujeedat ta yunƙura ta miƙe daga zaune tana dubanshi, Ya fayyace mata komai sai dai bai faɗa mata da suffar da ya ga yaron ba.
"Na yanke shawarar yin magana da sheikh Imam akan halin da yaron yake aciki, Ina da tabbacin zai taimaka mashi In sha allah, yanzu haka da nake yi maki magana, sheikh imam Yana akan hanya, Ina tsammanin nan da ƙarfe goma jirgin daya ɗauko shi zai yi sauka a nigeria.
Yanayin fuskartane Ya canza, yayin da take kallonshi, Ya rasa gane kallon menene take yi mashi, har dai yagaza jurewa jin shirun yayi yawa yace"baki fahimci abunda nake fadi bane? Ko bakiji dadi bane"? Girgiza mashi kai tayi"ko ɗaya mijina, wani abune yadan bani mamaki, nasan halinka ne yin taimako, indai abune daya shafi aikin Allah kana akan gaba, amma tunda nake arayuwata ban ta6a ganin tausayi da ya kai wannan ba atare dakai, saboda yaron jiya ba ka yi bacci ba, aduk lokacin da ka dawo gida a yanayi na damu nasan yadda zan shawo kanka in kwantar maka da hankalinta harma kayi bacci, amma adaren jiya saboda damuwar halin da yaron yake, waɗannan dabarun nawa basuyi maka aiki ba, bayan haka ka tura da jirgin da zai dauko malamin da zai duba shi daga Sudan zuwa Nigeria, saboda kana buƙatarshi da gaggawa don ya duba yaron...." ta faɗa fuskarta da alamun ruɗani, yayin da Hateem ya natsu yana sauraronta abunda bata sani ba ayanzun ma da take yi mashi magana hankalin shi yafi karkata kan agogon dake sanye a wrist din hannun shi, burinshi goma ta buga.
"Abunda yafi ɗaure min kai mijina, wanene yaron? Menene alaƙarka da shi? Yanayin yadda ka nuna damuwa akanshi ko ɗan cikin ka sai haka"
Jim ya ɗanyi kafin ya furta"bani da alaƙa da shi, bansan shi ba! Kuma ban ta6a ganin shi ba, kamar yadda na faɗa maki adaren Jiya idanuwana suka fara yin tozali da shi, tun daganan sai naji ƙaunarsa ta kama ni, har naji ina son na taimaka mashi, sai nake jima kamar nike da alhakin ciwon shi, idan har ban taimaka mashi yaji sauƙi ba Allah zai iya kamani da laifin ƙin tallafa masa da banyi ba"
Murmushin gefen fuska Gimbiya mujeedat ta sakar mashi har fararen hakoranta suka bayyana.
"Kai din na dabanne mijina" ta faɗa tana matsawa kusa dashi, ta ɗaura hannunta na dama saman sumar kanshi.
"Samun miji kamarka a duniyar nan abune mai wuya, kana da tausayi da jinƙan na ƙasa dakaina, sannan kowa naka ne, burinka ka faranta ma wanda yake acikin kunci koda ta silar hakan kai zaka rasa naka farin cikin, ni kaina ina ilmantuwa da kyawawan ɗabi'unka da halayanka, shiyasa nake alfaharin mallakarka da nayi a matsayin mijina" lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kalamanta ba ƙaramin faranta mashi suke Yi ba, tamkar tana ƙarfafa mashi gwiwane.
Zame hannunta tayi daga kan sumar shi zuwa gefen fuskarshi idanuwansu cikin na juna "Kamar yadda ka sani, duk abunda kakeso nima inason shi, koda bana son shi saina yi kokarin koya ma kaina yadda zanso shi saboda mijina yana son shi, don haka nima ina goyan bayanka akan Yaron, Allah ya baka sa'a mijina ya cika maka burinka na ganin yaron ya samu lafiya, A shirye nake dana bada gudummuwata wurin ganin mun inganta rayuwarshi" Murmushine ya bayyana akan fuskar prime minister, kallonta kadai da yake yi natsuwa yake samu, musamman idan tana ƙarfafa mashi gwiwa da daɗaɗan kalamanta. "In sha Allah zamuyi nasara, yaushe zaka bani iznin zuwa ganin yaron"?
"Na yanke shawara idan yaji sauƙi, zan gayyace shi zuwa gidan mu, zamu shirya mashi dinner."
Tsantsar farin cikine akan fuskarta"naji dadin jin hakan mijina, wallahi har na ƙosa naganshi, duk na kagu gashi bazamu daɗe a ƙasar ba, kwanaki kadan suka rage mana" ta fada tana 6ata fuska alamar bataso hakan ba. Damƙo hannunta yai da take kokarin shafa wuyanshi, fari sol dashi, ga wani shu'umin kamshi dake fita sako da lungu na jikinta, sumbatar tafin hannu yai, ba tare da ya sake shi ba ya dago da reddish eyes dinshi akan fuskarta"yaron marayane bashi da kowa, Owais ne ke kula da su, zan nemi alfarmar yabar min shi mu tafi canada atare, inaso ya maye min gurbin abunda narasa" sai yanzu ta fahimci damuwarshi.
Tausayinshi ne ya kamata, tuntuni tasan yana da burin samun ɗa Namiji, yaso ta ƙara haifa mashi ƴa'ƴa sai dai shiru babu alamun zasu sake samun ƙaruwa, kuma lafiyarta ƙalau saboda shi yasa bata yin tsarin Iyali, Allah ne bai nufa zata ƙara haihuwar ba.
Kafin ta buɗe baki tayi mashi magana, wayarsa dake ajiye cikin aljihun shi ta soma yin ringing, ya riga da yasan wanene Ya kirashi. Da sauri Ya saki hannun Gimbiyarsa, Ya zura hannu ya zaro wayar picking call din yai tare da karata a kunnanshi, gimbiya mujeedat ta kura mashi ido tana kallon shi "Alhamdulillah, Allah ya kawo ku lafiya," iya abun da taji ya furta kenan, zame wayar yai daga kunnanshi yana dubanta yace"sun sauka lafiya" Gimbiya mujeedat tace'shiyasa naga farin ciki akan fuskarka, sheik imam yaƙaraso kenan, bari nayi magana da masu aiki su shirya maku breakfast dinku" Ta fada tana kokarin daukar phone dake ajiye on nightstand da sauri ya ruƙo hannunta, ta dago da ido suka kalli juna "An shirya mashi breakfast dinshi, tun acikin jirgi, ina da tabbacin babu yunwa ko gajiya atare da shi, nafi buƙatar idan ya ƙaraso mu tafi gidan Owais din" "Amma kaifa? Baka ci komai ba, Yakamata kayi breakfast dinka, zaka fi samun kuzari" Girgiza mata kai yai"Bana buƙata, saboda bani da natsuwar cin abinci, Idan har yaron nan bai dawo dai dai ba, nafi son idan Ya samu sauƙi, muci abincin atare da shi" Tsantsar mamakin kalamansa ne ya daure mata kai, bata ta6a ganin ƙauna kalar wannan ba, Ko a shirin film.
"Amma kasan bana iya yin breakfast ba atare dakai ba, idan har baka ci ba, nima bazan ci komai ba, har sai ka dawo gidan" cikin tausasa harshe tayi maganar.
"Yau kawai, Kiyi hakuri kiyi breakfast tare da su Yazrin, bazan jima ba, in sha Allah atare zamu yi lunch dinmu"
Kwa6e mashi fuska tayi hadi da marairaice mashi tamkar zatayi mashi shagwa6a ta furta"bazan takura maka ba, Na kar6i uzurinka"
"Ki tashi ki shirya inaso ku gaisa da shekh imam kafin mu wuce gidan owais" amsa mashi tayi da toh, kafin ta sauko daga saman gadon, shima ya miƙe yana bin bayanta da kallo, har ta 6ace ma ganinsa, jim kadan ta fito sanye da Abaya launin Maroon tayi rolling mayafi akanta, ruƙo hannunta yai acikin nashi, suka nufi kofar fita daga dakin. Lokacin da suka shigo babban katafaren palourn gidan, masu yi masu hidimane suke ta gudanar da aikace aikacen su, kowan nan su sanye da uniform baƙin wando da farar shirt, matasan ƴan mata, duk inda Suka gifta jiki na 6ari suke gaishe dasu cikin girmamawa, yayin da su kuma suke amsa masu da fara'a.
Yanke shawarar zuwa bedrooms din Ƴa'ƴan su suka Yi, kafin ƙarasowar Ya sheikh, Yana da buƙatar suma su kasance cikin shiri donsu yi mashi kyakkyawar tarba.
elevator suka hau ta daukesu zuwa upstairs, bayan ta sauke su suka fito batare da sun saki hannayensu da suka ruƙe acikin na juna ba, kaitsaye suka nufi bedroom din ƴan matan su.
Gaba ɗaya ta tattara hankalinta akan Apple laptop din dake agabanta, yayin da take zaune a tsakiyar katafaren gadonta dake acikin hamshaƙin ɗakin kwananta daya gaji da haɗuwa, ko dakin sarauniya Albarka, farace sol kamanninta sak dana Mahaifinta Hateem, yadda kasan ta macen aljanna saboda kyanta da dirinta, kamanninta sun 6aci dana Hateem, tamkar yayi kakinta, Hasken fatarta ne kadai ta dauko na mom mujeedat da doguwar sumar kanta, mace ce mai aji, mai ji da ƙasaita da izza, bakowa bace wannan face NAZLI, itace first born dinsu, a ƙalla zata kai shekara ashirin da takwas a duniya, tana asanye da lace Camisole daga sama ta ɗaura silk robe launin hot pink, a tsanake take operating laptop dinta cikin ƙwarewa, yayin da kyawawan idanuwanta dake a manne da farin glass suke akan screen din laptop nata, daga gefen gadon ƙayataccen round table ne daga saman shi china tea set ne, jefi jefi takan kai hannu ta dauki cup ta kur6i coffee din dake aciki, Nazli agogo sarkin aiki bata gajiya tana da hazaƙa da ƙwarewa a 6angaren Iya kasuwanci, Company guda take juyawa na mahaifinsu dake a ƙasar Canada, ƙamshin turaren jikinta ya buɗe ko'ina na room dinta, hatta sumar kanta kamshin turaren data turara ma gashinta ne ke fita, kullum ne sai ta turara jikinta da gashin kanta, Nazli badai tsafta ba.
"Assalamu alaikum" Muryoyinsu ne suka janyo hankalinta ga duban ƙofar shigowa room dinta dake a kulle, daga inda take tana Iya hangen su ta cikin kofar, saukowa tayi daga saman gadon, sumar kanta ta rufe bayanta tamkar hijabi tayi mata, daura idonta tayi akan cashmere slippers dinta dake ajiye saman lallausan carpet, ta zura su cikin kafarta, kafin ta nufi kofar cikin takun izza, ta sanya hannu biyu ta ruko handle din kofar ta buɗe ta. Fuskokinsu dauke da murmushi suke kallonta, sai dai ita babu alamun murmushi akan fuskarta, haka take bata da fara'a, taji dadin ganinsu amma bazaka Iya gane hakan ta yanayinta ba saboda tsabar ji da izzarta, Cikin harshen turanci tace
"Good morning, Mom and Dad! I'm so glad to see you, yau kun riga ni zuwa room dina, yanzu nake koƙarin kammala aikin da nakeyi a laptop...."
Ta ƙare maganar tare da matsawa ta rungume daddynta, hannu biyu ya daura saman bayanta"barka da safiya daughter, Ina fata kin tashi cikin koshin lafiya"
Muryarta ƙasa ƙasa ta amsa mashi da cewa"
"I'm doing well, Dad. I've been thinking about you since yesterday. I've missed you."
Gimbiya mujeedat tace"oh shi kaɗai ki ka gani shiyasa kika rungume shi ko? Da zolaya tayi maganar.
Ɗagowa Nazli tayi tare da miƙa hannu zata rungume mujeedat, da sauri gimbiya mujeedat taja da baya tana fadin"nayi fushi, ba tun yauba na lura kinfi ji da daddynki, shiyasa nima nafi ji da Yazrin daboda tafi nuna damuwa akaina"
Marairaice mata fuska Nazli tayi haɗi da kama kunnanta"agafarce ni sanyin idaniyata, mahaifiyata abun alfaharina" Sakin fuska mujeedat tayi"nayi hakuri amma kada ki ƙara yi min hakan, Daga yau ni zaki fara hugging kafin daddynki" ta faɗa tana kallon Hateem dake kallonsu, fuskarshi dauke da murmushi yace"na fahimci kishi kike yi dani akan Nazli, Yarinya tafi son ubanta, da ni da ita ƙaunace mai ƙarfi, baki ga kamannin fuskarmu ba? Shiyasa take ji dani, ke kuma kije da Yazrin itace take kama dake"
Farfari tayi mashi da ido batare datace komai ba, ta rungumo nazli ajikinta tana ɗan bubbuga bayanta da hannu tace"sannu agogo sarkin aiki, tun da sassafe ko breakfast bakiyi ba kin fara danna laptop, Ina fata na same ki lafiya"? Ɗagowa tayi da kanta tana fadin"Ina lafiya mommy, bana so aiki yai min yawa shiyasa nake ragewa" ta fada tana dubansu.
"Naji dadin ganinku, duk da ni yakama naje na sameku, ban samu damar yin hakan ba,"
Prime minister yace"bakomai daughter, muma munji dadin ganinki, Inaso ki shirya Zanyi baƙo Ƴan mintuna suka rage su ƙaraso, daga sudan zaizo, gaisawa zakuyi da shi," Batare da ta tambaye shi wanene zaizo ba tace"in sha Allah daddy, yanzu zan sauko down"
Amsa mata yai da toh, kafin ya dubi mujeedat, muje ko" ya runƙo hannunta suka juyawa zuwa dakin Yazrin,
A lokacin Yazrin tana daga kwance cikin bathtub dake a bathroom dinta, ta jiƙe jikinta da ruwan kumfa mai ɗumi, ta lumshe idanuwanta yayin da take shaƙar ƙamshin bath soft dinta daya karaɗe toilet din tamkar an fesa turare, A kalla zata kai shekaru ashirin da biyar, Yazrin ƙarshe ce afagen haduwa bata baro komai na mahaifiyarta mujeedat ba, launin fatartane kadai kalar na hateem, haskenta bai kai na mujeedat ba, daga ita har Yazrin babu wanda yafi wani kyau, ta inda suka banbanta Yazrin tafi Nazli sauƙin Kai da iya mu'amala da mutane, Ita Nazli bata son bare, ƙiwuya gareta kamar ƙaramar yarinya ga ji da izza, magana ma wuyar furtata take ji.
Sautin ƙarar door belt ne ya katse mata jin daɗinta, A hanzarce ta ɗaure jikinta da ruwan dumi, kafin ta fito ta ruƙo towel dake sagale jikin hanger ta ɗaure qugunta da shi, Shigowa Bedroom din tayi da sauri ta nufi wardrobe dinta, shaf shaf ta zura jallabiya a jikinta, ko tsane jikinta bata samu damar yi ba, sumar kanta duk ta nannaɗe saman kafadunta.
Buɗe kofar ɗakin tayi fuskarta dauke da kayataccen murmushi, dimples dinta biyu sun lotsa
Su kansu da sukayi tozali da ita saida suka saki fara'a, Yarinyar akwai shiga rai, da wuya kaga fuskarta adaure, kafin su bude baki suyi mata magana ta ware hannayenta biyu ta hadasu ta rungume tana fadin"Mom dad, tunkafin nazo gaishe ku kun riga ni zuwa, kunsa naji nauyin hada ido daku"
Ta faɗa tare da ɗagowa da kanta tana faman kare fuskarta da tafin hannunta Dariya kowan nan su yasaki, Prime minister yace"barka da safiya daughter, fatan mun same ki lafiya"? Jinjina mashi kai tayi"lafiyalou daddy, amma ni baku kyauta min ba, maimakon ku bari ni in fara zuwa gaishe daku" ta fada tana bubbuga ƙafafuwanta da shagwa6a.
"Ladar da nake kwaɗayin samu, Kun rigani kwashe ta" dariya mujeedat tasaki tana fadin"Wato ke har yanzu baki girma da shagwa6a ba"
Hateem yace"barta tayi abunta, don bata da ƙanine shiyasa take yi mana shagwa6a"
Nuna kanta tayi da yatsanta"saboda nice auta mommy, dagani babu ƙari, kunga kuwa dole nayi shagwa6a" ta fada tana ruƙe masu qugu, Ba ƙaramin nishaɗi take basu ba, Hateem yace"baki fada mana ya kika wayi gari ba,"
"Na tashi lafiya daddy, tun safe nasha coffe, yanzu haka wanka nakeyi a toilet naji ƙarar knocking dinku shiyasa na fito"
"Kina nufin baki ƙarasa wankan ba"? Acewar mujeeda. Yazrin tace"tun ɗazu fa na kammala, kawai inajin daɗin kwanciya acikin ruwane"
"Okey, Ki koma ciki ki shirya muna jiranku a downstairs, daddynku ne zai yi bako daga kasar sudan, yanaso ku gaisa dashine"
Yazrin tace"okey mom, bari na shiga ciki in shirya"
Ta fada tare da kallon Daddynta, harta buɗe baki zatayi mashi magana, sautin ƙarar dirar motocin dake shigowa gidan nasu ya katse mata hanzarinta, muryarta tamkar tame yin raɗa ta furta"bakon ya karaso kenan, bari nayi sauri naje na sanya kayan mutunci" ta juya da sauri ta shige cikin dakin Murmushi kowan nan su yasaki, mujeedat tace"yazrin kenan, tana bani nishaɗi, sai dai narasa gane halin wa ta dauko atsakanin nida kai" Nuna ta yai da yatsa"ke mana, har sai an fadi, ni dai kin san ba haka nake ba, idan kika dubi ɗabi'un Nazli sak kalar nawane" Hararar zolaya ta yi mashi"nazli fa hada izza ta sarauta ke ɗawainiya da ita, kai ina kaga sarauta? Nice na gajeta, sai dai ta 6angaren siyasa nan kafi karfi, kuma shi ɗan siyasa da fara'a aka sanshi, hakan na nufin halinkane yazrin ta dauko bani ba"
"Gorin sarauta zaki yi min"? Ya faɗa yana kanne mata ido.
Tana dariya tace"ni dai bance ba, ai kafi ƙarfin ayi maka gori, dani dakai babban gorone magogin ƙarfe"
Ta fada tare da ruƙo hannun shi"muje kada su jimu shiru, ina tunanin sune suka ƙaraso" atare suka nufi down stair.