Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 68
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 68: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 68. Adai dai lokacin zungureriyar motar da ta ɗauko…
3,354 words
Adai dai lokacin zungureriyar motar da ta ɗauko Sheikh imam daga airport, ta karaso bakin entry hall nagidan Prime minister a hankali tayi parking, gaba da bayanta motocin sojoji ne da suka dauko shi domin bashi tsaro, fitowa sukayi daga cikin motocinsu, wani ƙato daga cikinsu ya buɗe mashi murfin mota, A hankali sheikh Imam malik Ya zuro kafarsa ta dama dake asanye cikin takalma na alfarma, kafin Ya ƙarasa fitowa, masha Allah, magadan annabawa, kallon ɗaya zakayi mashi ka shaida maluntakarsa, yayi shiga ta alfarma shiga ta larabawan saudi arebiya, farar throbe ce, daga sama ya daura wata shara sharar riga, kanshi yana asanye da kufi ƴar karamar hula ta malamai, an nannaɗeta da black turban, Yana da godon gemu, babban mutunne ya manyata don harya fara tsufa gashin gemunshi hada furfura ta manyantaka, duhun fatarsa mai kyau ne, kai daga ganin shi baida wasa irin malaman nan ne masu zafi akan addini, babu tsoro a idanuwanshi, mutunne mai cikar kamala, ya shahara a 6angaren wa'anzartawa da yin da'awa ta addinin musulunci, yayi gwagwarmaya a kasashe daban daban babu inda bai shiga, kuma yana cin nasara akan da'awarsa, shaidanun aljanu kansu tsoronshi suke Ji, Suna jin shakkar zama a inda shekh imam malik yake, mutunne shi mai koyi da sunna ta manzon Allah SAW, Ya ruƙe Allah ɗaya azuciyarshi, kainuwane shi dashen Allah, badai mutun ba sai Allah, ta ko'ina jikinshi ƙamshin turarensa ne mai dadin shaƙa a hanci, hannun shi na dama ruƙe da cazbaha.
A hankali Yake bin ko'ina da kallo, Yayin da yake shaƙar kamshin iskar data gauraya da ƙamshin turarensa.
"Ya mu'allim, mu ƙarasa shiga ciki," ɗaya daga cikin Sojojin ne yai mashi magana haɗi da nuna mashi kofar shiga babban falon, ɗaga kafarshi yai atsanake yake yin tafiya, suna gab da zasu shiga falon, Prime minister ya fito tare da gimbiya majeedat, Murmushin dake kan fuskokinsu ne ya ƙara faɗaɗa, da sauri hateem Ya mika mashi hannu suka gaisa cikin girmamawa"Marhaban bika babana, barka da sauka, ya gajiyar tafiya" ya fada tare da rungumeshi, bayan sun raba jikinsu daga na juna Sheikh imam yace"ai ni babu gajiya atare dani, ni da aka gatantani kamar wani basarake haka aka daukoni a privet jet, hankali akwance naci na koshi na cika tumbina" Ya fada yana nuna tumbinshi da cazbahar hannunshi, gaba daya suka sanya dariya gwanin ban sha'awa, sheikh imam mutunne mai son barkwanci amma fa sai idan yaso.
Prime minister yace"Akara makallah ai kafi karfin basarake awurinmu, ku fa magadan annabawane, kunfi duk wani mai muƙami a karkashin tafin kafarku Yake"
Murmushi Shekh imam Yasaki, Tare da daura idanuwanshi kan fuskar Gimbiya mujeedat, kafin yayi magana tayi saurin gaishe shi cikin harshen larabci.
Da zolaya yace"Hateem dama ana ganin fuskar matarka? Ya akai yau baka rufe lu'u lu'un ka ba"? Koba ita bace matar nan da ake yi mana 6oyanta ba? Kodai Ƴarce"? Kunyace ta rufe gimbiya mujeedat, Ta sanya hannu ɗaya ta kare fuskarta Hatta jami'an dake a kewaye da Ya shekh Imam saida suka saki murmushi .
Dariya prime minister yasaki a fakaice ya harari Jami'an dake atsaitsaye suna kallonsu, jiki na 6ari suka juya kowa yakama gabanshi, don sun fahimci me yake nufi, wato suna kalle mashi matarshi.
"Ya sheikh Mu ƙarasa cikin falon, mun barka atsaye gashi ka kwaso gajiya" prime minister ya fada tare da ruƙo hannun shi, Suka nufi babban falon Gidan, Gimbiya mujeedat tana abiye da su.
"Hateem Irin wannan daula haka? Anya kuwa kuna tunawa da mutuwa? Ka ajiye lu'u lu'u agidanka ga kuma kayan alatu ta ko'ina, maimakon ku bari sai mun shiga Aljana muji daɗi" Ya faɗa yana Jijjiga cazbahar hannunshi, Dariya suka sanya gaba dayansu, A saman Royal sofa kowan nan su Ya zauna, suna fuskantar juna da sheikh imam, sai faman jinjina kai yake yi yana bin gidan da kallo, duk maganar da sheikh imam zaiyi yanayin amfani da harshen turanci saboda mujeedat yasan bata jin hausa sai dai turanci da larabci.
"Yanzu kai hateem, Har kake iya kwana acikin daular nan? Wannan haɗuwa haka ai sai mutun ya manta da tur6aya aka halicce shi" Murmushi suka saki suna dubanshi Sautin takun takalman Yazrin da Nazli ne Ya janyo hankulansu ga dubansu, Hannunsu ruƙe cikin na juna suke yin tafiya suna tunkarosu, kowaccensu ta yafa mayafi akanta, Bayan sun ƙaraso, Cikin girmamawa suka gaishe da shekh Imam, Abunda Ya burgeshi da yaran tarbiyarsu, A saman lallausan carpet din dake a atsakankanin Royal sofa din suka zauna kowaccensu ta nade kafafuwanta "Masha Allah, Matan hurul aini har a duniya, Hateem, wacce zaka bani acikinsu in cike sunnah"? Ya faɗa yana duban faces din Yazrin da Nazli, Yazrin sai famam sakar mashi murmushi take Yi, Nazli kuwa tunda ta gaishe dashi ta sunnar da kanta ƙasa. "Duk wadda ka za6a malam, zamu baka Ita" acewar mujeedat, Shekh imam yace"Uwargida maganarnan taki bata kai zuci ba, ni nasan kin faɗine kawai, taya zaku ba yarinya auran dattijo? Mai jan cazba, balle ƴan matan zamani basu son auran malamai" Murmushi kowannansu yasaki, banda Nazli. Biyu daga cikin masu aikin gidanne suka nufo falon, hannunsu ruƙe da faɗaɗan farantai daga sama an jera drinks masu sanyi da snacks. Tunkafin su karaso sheikh imam yace"waɗannan fa? Badai ni zasu kawo mawa ba? Bayan abincin da naci acikin jirgi har wani ƙari za'ayi min? A'a gaskiya Ni a koshe nake, Ko ruwa bana jin zai Iya wucewa ta makoshi na" Prime minister yace"babana adai daure ko ruwan ne kasha," Gyaɗa kai yai toh, naji iya ruwan zansha, Asaman carpet suka daura farantan, mai aikince ta zuba mashi Apple juice mai sanyi a cup ta miƙa mashi, Yasa hannu ya kar6a, Kur6a uku yai ya dawo da dubanshi gasu Nazli"ƴan matan hateem ina fata na same ku lafiya? Ya karatu? Ko da yake nasan kun kammala, to Ya aiki" Atare suka amsa mashi da cewa"lafiyalou Alhamdulillah," jinjina kanshi yai"Masha Allah," bayan ya ajiye cup din alamar ya kammala sha, Prime minister hateem Yace"nasan yanzu ka kwaso gajiya, ko zamu bari zuwa anjima idan ka huta sai mu fara shiga gida ku gaisa da baba kafin mu wuce can gidan Owais din inda Yaron yake"? Girgiza kai sheikh imam yai"A'a, tun da mahaifin naku baisan da zuwana ba, to ba yanzu zanje gaishe shi ba, nafi buƙatar ganin yaron, don agaskiya ni babu gajiya atare dani, ka tashi mu tafi kawai," Kallon mujeedat Hateem yai"zamu tafi, in sha Allah bazamu daɗe ba, a taya mu da addu'a" murmushi tasakar mashi"ubangiji Allah yasa ayi asa'a, Ina yi maku fatan alkhairi" amsa mata yai da ameen, kafin ya maida dubanshi gasu Nazli da Yazrin"daughters ku tayamu da addu'a, ga mommynku nan zatayi maku bayanin komai dangane da zuwa sheikh imam" amsa mashi sukayi datoh, kafin ya ɗago Ya kalli Ya sheik wanda tuni Ya miƙe tsaye, miƙewa hateem yai atare suka nufi kofar fita falon, tunkafin su ƙarasa Jami'en dake atsaye bakin motar data dauko sheikh daga Airport Yai saurin bude masu motar, Bayan sun shiga daga ciki, jami'en Ya zauna a driver's seat Ya tashi motar, atsanake Yake yin driving dinsu........
*Chief Owais✊❤*
Tun bayan daya dawo daga masallaci, Yin sallar asuba bacci ya addabi idanuwanshi, adaddafe ya shiga bathroom yai wanka, within minutes ya fito waist dinshi ɗaure da white towel, kan mirror chair ya zauna da niyar ya kimtsa kanshi, sai dai yakasa tabuka komai saboda kasalar data kame sassan jikin shi, idan har ba baccin nan yai ba to kuwa bazai ta6a samun sukuni ba, kyawawan idanuwanshi sunyi mashi nauyi daƙyar yake iya buɗe su, miƙewa yai bai nufi ko'ina ba sai saman katafaren gadonshi, Ya haye ya kwanta tare da jan bargo ya lullu6e rabin jikinsa, In a short time bacci yai awon gaba da shi.
Tsawon awanni yanata sharar baccinsa, tun karfe shida har goma da rabi ta buga, Yayin da numfashinshi ke fita cikin natsuwa da kwanciyar hankali, phone dinsa dake ajiye gaban dressing mirror ta soma yin ringing, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa, ringin din ya fara takura mashi, mutsu mutsun farkawa daga bacci ya somayi, A hankali Ya ware fararen idanuwanshi dake fuskantar ceillin din dakin nashi Tsawon minutes, kafin Ya laluba hannunshi Cikin kasala Ya ruƙo wayar ya duba sunan me kiranshi, sunan Uncle Hateem ne Ya bayyana akan screen din wayar, Kiran harya kusa katsewa yai saurin yin picking, tare da manna wayar akan kunnansa "My son, Ina fata ban takura maka ba" Yamutsa fuskarshi yadan kafin ya furta"Barka da safiya uncle, fatan ka tashi lafiya"? "Lafiyalou, naji muryarka da alamun bacci bai isheka ba" "Kiran wayarka ne Ya tashi ni daga bacci, Ina fata lafiya" "Banji dadiba amma kayi hakuri da takura makan da nayi, ni kaina bansan dililin dayasa na damu da yaron ba" "Ba damuwa uncle" "Yanzu haka da nakeyi maka magana Muna akan hanyar zuwa Gidan naka tare da sheikh imam" Lumshe ido owais yai har cikin ranshi yaji dadin jin zuwan Sheikh imam "Ina yi mashi barka da zuwa, Allah ya kawo ku lafiya" Hateem Ya amsa mashi da amen mun gode son," daga haka sukayi sallama da juna. Daura wayar yai saman side drawer ya sauko daga saman gadon Ya nufi dressing room din dakin shi, badajimawa ba ya fito sanye da jallabiya launin sky blue, tayi bala'en yi mashi kyau, Gaban dressing mirror din dakin ya tsaya tare dakai hannu cikin jerin turarurrukansa ɗaya bayan ɗaya yake dauka yana feshe jikinshi, tuni ƙamshinshi ya karaɗe dakin. Diamond wrist watch din shi dake ajiye gaban mirror ya dauko Ya zura a hannunsa, Kafin Ya miƙa hannu Ya dauki Phone dinsa, A tsanake Yake pressing dinta, Layin Boss Ya danna ma Kira, Bugu Uku Yai picking, gaisawa suka farayi kafin Ya furta"Sheikh Imam Ya ƙaraso, Ina buƙatar ganin kowannanku a main falo, domin mu tarbesa"
Boss Ya amsa mashi da Toh, In sha Allah, Yanzu zan sanar da su" daga haka Yai rejecting kiran.
A dai dai lokacin, Unaisah ta kuma farkawa daga baccin da yayi awon gaba dasu ita da giant snake din, Cikin sanɗa ta sauko daga saman gadon, tana tafiya tana waiwayon gadon, ta kudundune shi da bargo, ta ƙagu da son ganin ƴan uwanta shiyasa zata fita taje gare su, batasan a wani hali suka kwana ba. Bayan ta fito daga dakin down ta sauko, Moving quickly ta nufi Hanyar da zata hau bene taje dakin ummi, Har ta kusa haurawa saman staircases miryar boss man ta katse ta"Unaisah"! Cak ta tsaya haɗi da waiwayowa tana dubanshi, "Ina zakije ne"? Muryarta adisashe ta furta"dakin aunty ummi, Inason ganinsu batul ne, ai ka fadamin acan suka kwana" "Hakane, Nima dakinta zani je, amma tunda gaki bari in baki sako ki kai mata" ya fada tare da zura hannu cikin aljihu ya curo maganin mura ya miƙa mata.
"Wanene bai da lafiya"? Hankalinta atashe ta fada tana bin maganin da kallo.
"Ummi ce ke bata jin dadi, mura ce ta kamata" Ajiyar zuciya Angel ta sauke tayi tunanin ko cikin ƴan uwanta wani ke bai da lafiya.
Kar6ar maganin tayi, har zata juya muryarshi ta dakatar da ita"Sheikh imam yana akan hanyar zuwa gidan nan, malamin da zai duba ɗan uwanku danish" Waro ido waje tayi lokaci ɗaya ta fashe da dariyar farin ciki, Murmushi yasaki Dama ya fada matane don ya faranta mata rai. Idanuwanta cike tab da ƙwalla take fadin"Alhamdulillah, wayyo Allah wallahi naji dadi, fatana Allah yasa ayi asa'a danish ɗina yaji sauƙi ya dawo kamar kowa"
Boss yace"in sha Allah zamuyi nasara, yanzu kije ki kai mata maganin, idan kin fito ki same mu a falo, Amsa mashi tayi da toh, jiki na rawa ta nufi benan ta haye sama, burinta takai mata maganin sannan ta kwantar masu azeeza hankalinsu kafin ta dawo falon don taga sheikh imam"
Abakin ƙofar dakin Ummi ta dakata tare dakai hannu ta dafi glass door din A hankali kofar ta buɗe, Zura kafarta keda wuya sukayi kicibus da batul, sam hankalinta ba akwance yake ba, ganin ummi ta shiga toilet tsawon lokaci bata fitowa ba shiyasa ta yi dabarar guduwa daga dakin don ba ƙaramin takura tayi ba, baiwar Allah suna haɗa ido da Unaisah, ta faɗa jikinta, Hannu biyu ta ƙanƙameta dasu kamar zata koma cikinta, tun daga kan yadda ta rungumeta ranta ya bata cewar babu lafiya, A hankali itama ta zagayo da hannayenta saman bayan Batul.
"Meke damunki sister? Baki da lafiyane"? Ta fada batare data raba jikinsu daga na juna ba Muryar batul ashaƙe da mura ta furta"babu komai, Mu tafi dakinmu, Ni kadaice na rage su azeeza sun tafi tun ɗazu, Ni ko sallar asuba banyi ba" Hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yai ba, Jin muryar Batul ashaƙe kamar an ɗaure mata makoshi, A hanzarce ta raba jikinsu, ido cikon ido suke kallon juna, ta ɗanyi mamakin ganin kayan dake ajikinta masu kyan gaske. Aruɗe ta furta"batul! Dama kece baki da lafiya ba aunty ummi ba? Garin yaya mura tayi maki mugun kamu"? Shiru batul tayi mata batare data furta komai ba, saboda tana jin tsoron ummi taji ta fada ma wani. Da sauri ta canza akalar maganar tasu"Meke damunki? Naga fuskarki ta kumbura idanuwanki sun yi ja, ko kema baki lafiya"? "Ni lafiyata qalou, damuce ta hana ni yin bacci..." bata ƙare maganar ba batul ta kuma cewa "Ina danish dinmu"? "Inaso zanyi maku bayanin komai amma sai mun koma ɗaki, Yanzu ki fada min ya akai mura ta kama ki? Ina kuma aunty ummi"? Murya ƙasa ƙasa Batul tace"nima bansan ya akai ta kamani ba, aunty ummi kuma tana a toilet, itace ma ta kira awaya don akawo min magani, kuma kinga ta bani kaya na sanya" tayi maganar tana nuna mata kayan sanyin jikinta. Ajiyar zuciya Unaisah ta sauke" mun haɗu da boss man shine ya bani maganin mura in kawo, ni nama yi tsammanin aunty ummice ba lafiya kamar yadda ya fadamin ashe kece" Jinjina mata kai batul tayi"Allah ya baki lafiya sisterna, kayan jikinki sunyi maki kyau, a ina aunty ummi ta samu kayan nan dai dai size dinki kamar donke aka dinka su"?
"Nima bansani ba, Mu tafi daki" atakure tayi maganar, tare da ruko hannun Angel, tajata suka nufi down stairs.
*Daga Alƙalamin Boss Bature💋✊✍️*
Adai dai lokacin Su parveen suna a zazzaune tsakiyar gadonsu Batul, sun kewaye juna, sai faman zazzare idanuwansu suke yi don har yanzu basu daina jin fargabar macijin nan ba.
Motsin buɗe ƙofa ne Yaja hankalinsu ga kallonta, Atare suka shigo hannun su ruƙe cikin na juna, wani irin farin ciki ne ya lullu6e su, da gudun gaske Jemimah da Azeeza suka diro daga saman gadon suka nufi unaisah, tunkafin su ƙaraso ta ware masu hannayenta fuskarta dauke da yalwataccen murmushi, zubewa tayi saman gwiwowinta yadda tsawonta zaiyi dai dai da nasu, gaba ɗayansu ta haɗasu ta rungume a ƙirjinta, tare da zagaya hannayenta saman bayansu, jemimah tuni ta fashe mata da kuka hada bubbuga bayan Unaisah alamar ranta ya 6aci.
Batul dake a tsaye tana kallonsu sam bata ji takun tafiyar Parveen ba, Sai dai taji muryarta"Batul tun ɗazu muna ta jiran ki shiru baki zo ba, Ina fata babu wani abu daya same ki"?
Kallonta Batul tayi da ido tayi mata alamar tayi shiru bata son Unaisah taji komai daya faru, jinjina kai parveen tayi don ta fahimci me take nufi.
"A ina kika sami kayan jikin ki masu kyau"? Ta fada tana duban Kayan sanyin jikin batul" Murmushi batool tasaki kafin tace"Aunty ummi ce ta Bani su" Parveen tace"ko a ina ta same su, ban ta6a ganin kayan da suka yi maki kyau ba kalar waɗannan" kafin batool tayi magana muryar Jemimah ta katse mata hanzarinta, A lokacin sun ɗago da kansu daga rungumar da Unaisah tayi masu, fuskokinsu sharkaf da hawaye kamar waɗanda suka yi shekara basu ganta ba.
"Meyasa jiya kika tafi kika barmu? Inata kiran sunanki baki amsa ba, tsoron wannan abun ya kamamu"
Shafa fuskarta Unaisah tayi"Am sorry nasan ban kyauta ba, amma kuyi haƙuri, bawani wuri na tafi ba, Ina atare da ɗan uwanmu Danish bashi da lafiya......"
Tunkan ta ƙare maganar, hankalinsu yai mugun tashi jin cewa danish dinsu baida lafiya, damuwace ƙarara akan fuskokinsu
"Unaisah meke damun shi? Meyasa jiya ba kizo kin kaimu mun ganshi ba"? Acewar parveen Batul tace"ni da ma saida naji araina ɗan uwanmu baida lafiya, Allah sarki danish din mu, Yanzu yana a ina? Ina son ganin shi" ta fada idonta akan unaisa dake ƙoƙarin miƙewa tsaye tana dubansu.
Ruƙo hannunta Azeeza tayi acikin nata"dan Allah ki kaimu wurin shi, muna son ganin shi" idanuwanta sun ciko tab da ƙwalla tayi maganar.
Numfasawa Unaisah tayi kafin ta soma yin magana"na yanke shawara ƙwara na faɗa maku halin da danish yake aciki, saboda bana son ku guje shi ko ku dinga jin tsoron zuwa wurinshi......." shiru ta ɗanyi na wani lokaci duk sun ƙura mata ido cike da zumuɗin son jin ƙarashen zancen.
"Amma kafin nan inason ganin sauran ƴan uwanmu, naga babu Hannah! Ina taje ne"? Atare suka hada baki wurin bata amsar cewa suma basu sani ba, tun daren jiya basu ganta ba.
Aruɗe Unaisah take dubansu, Kafin ta furta magana, sallamar Big Guy taja hankalinsu ga duban ƙofar, shigowa cikin ɗakin yai hannun shi ruƙe dana Hannah, daga bayansu Ƴan uwansu ne maza tun daga kan Sajeed, Haris, Javed and Naufal, ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, Hannah sai faman zare ido take yi kamar wadda aka faɗa ma saƙon mutuwarta, sakin hannunta big guy yai jiki na rawa ta nufi Unaisah ta rungumeta, sunyi farin cikin ganin ƴan uwansu, Sajeed ya nufi azeeza fuskarshi dauke da murmushi yai hugging dinta, Naufal yajanyo parveen ya rungumeta Yana bubbuga bayanta da hannu ɗaya, Batool da Haris suka rungume junansu, Ran jemimah ya 6aci ganin babu wanda ya rungumeta, harta fara tatta6e la66anta za ta yi masu kuka, javed yai saurin ɗaukarta saman jikin shi, Fashewa tayi da dariya saboda an dauketa. Big guy dake a tsaye yana kallonsu ya goya hannayensa saman broad chest dinsa, Yaran sun yi matuƙar burgeshi.
Tsawon mintuna suna a manne da juna, kafin daga bisani kowan nan su ya rabu da jikin ɗan uwanshi, gyaran muryar da Big guy yai masu ne yasa suka mayar da hankalinsu gare shi a tsanake Ya soma yin magana.
"Inaso ku natsu ku saurareni, dalilin dayasa na tara ku a ɗakin nan, saboda na fahimci haryanzu baku daina jin fargaban abunda ya faru jiya ba, Ga ƴar uwarku nan Unaisah zatayi maku bayanin komai yadda zaku fahimta, sannan please bama buƙatar ganin gifcin kowan nan ku a falo! Ku tsaya a ɗaki, mai buƙatar shiga toilet ya shiga, wanda zai yi bacci ga gado nan ya kwanta,........" kafin Ya ƙare maganar Parveen tayi ƙasa ƙasa da murya tana fadin"breakfast din mu fa? ni ina jin yunwa, Jiya da dare bamu ƙarasa cinye abincinmu ba" murmushi big guy ya saki ta cikin face mask dinshi Da zolaya yace"ki kwantar da hankalinki foodie, Indai abincine har sai kin gaji da shi, kamar kina a gidan manomi ne, Yanzu zansa a kawo maku lafiyayyan breakfast" ya faɗa tare da nufar kofar fita yana fadin"Unaisah Ki kula da su" amsa mashi tayi da toh, kamar jira su ke yi ya fita, Har suna haɗa baki wurin tambayarta meke faruwa da Danish.
"Zanyi maku bayani, amma kafin nan ku jira waɗanda basu yi salla ba su yi tukunna, batool tace min ba ta yi sallah ba" Badan sunso ba suka amince mata
"Kunyi sallah"? Ta jefa masu tambayar Sajeed yace"munyi a ɗaki" "Kufa" ta faɗa tana nuna su Azeeza Girgiza mata kai su kayi alamar a'a, Hannah ma tace nima banyi ba, saboda babu hijabi.
"Okey, yanzu abun da za'ai ku shiga toilet ku yi alwala, kafin ku fito zan dauko maku hijabin" amsa mata sukayi toh.
Ɗaya bayan ɗaya suka shiga toilet, bayan sunyi alwala kowaccensu ta sanya hijabi, asaman carpet din da ta shimfiɗa masu su ka yi sallar, bayan sun kammmala suka cire hijaban suka bata ta ninke ta maida su a wardrobe.
Zama sukayi kan carpet din gefen gado, mazan suna fuskantar matan, sun ƙurama Unaisah ido suna jiran jin me zatace masu.