Kenza eBookz

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 71

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 71

Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 71: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 71. Sanin nauyin jikin Danish yasa salsabeel nannaɗe…

3,249 words

Sanin nauyin jikin Danish yasa salsabeel nannaɗe hannun jallabiyarsa ya daddage Ya ruƙo kafaɗunsa da hannayensa ya juyar dashi ya fuskanci ceilling, still fuskarshi bata bayyana ba saboda yalwatacciyar sumar kanshi data rufeta. Cike da zumuɗi prime minister yace da salsabeel"please, ka jinginar dashi kan headbored, Ka nannaɗe min sumar kanshi daga kan fuskarshi inason ganinshi da kyau" Cikin girmamawa Salsabeel Ya amsa mashi da toh, Kafin Ya daddage Ya ɗago da Danish Ya jinginar dashi jikin headboard, A hankali Ya soma janye sumar kanshi daga kan fuskarshi, Tunkafin Ya ƙarasa kau da sumar, Hankalin prime minsiter yai matuƙar tashi haiƙam, zuciyarshi ta soma harbawa da matsanancin speed, Yayin da idanuwanshi suka zazzaro waje, tamkar eye balls dinsa zasu fado ƙasa, haƙiƙa yayi matuƙar girgiza da ganin abunda idanuwanshi suke nuna mashi, kowa dake a ɗakin saida ya lura da yanayin da prime minister ya shiga na tsantsar mamaki da Al'ajabi, bashi ba hatta sheikh imam da Chief owais al'ajabine akan fuskokinsu. Muryar prime minister na rawa ya furta"Sheikh...! Owais Kuna ganin abunda nake gani kuwa? a ruɗe ya furta maganar yana ƙarema fuskar Danish kallo. Sheikh Imam da al'ajabi Ya gama kamashi, Baisan sa'dda ya furta"amma dai wannan yaron Jininka ne ko? don wannan yafi ƙarfin ace kamanceceniyace ta halitta sai dai ta jini, saboda kamanninshi sun 6aci dakai da kuma yarinyar wurinka Nazli, Tamkar kayi kakinsa, komai nashi kalar naka ne, tun da Allah Ya halicceni ban ta6a ganin kama irin wannan ba, gaskiya nayi mamaki....." Boss man yace"ai ba tun yau ba, nasha faɗama chief owais cewa Yaron Yana kama dashi, bani ba hatta abokanan aikin mu sun shaida hakan, sai dai wani abu daya ƙara ɗaure mun kai ayau, Yaron yafi kama da prime minister hateem, bai baro komai nashi ba, tun daga kan shape din bakinsu, dogon hancinsu da idanuwansu, Yalla6ai da zaka ga launin idonshi zaka sha ruwan mamaki, domin kuwa kalar nakune" Dafe kai prime minister yayi da hannun shi ɗaya, Hankalinshi Yaƙi kwanciya da kamanninsu da yaron. Gyaran murya salsabeel Yayi kafin ya soma yin magana yana duban su "Ni kaina na jima ina mamakin kamannin dake a tsakanin Chief owais da Danish, komai nasu kala ɗaya ne banbancinsu launin fata ne da kuma tsayin sumar kai, wani iko na Allah sai gashi Yalla6ai Hateem Yafi kama da Danish" Runtse ido prime minister yayi, baisan ya akai yake jin wani irin yanayin atattare dashi ba.

Muryarshi araunace ya furta"ban haɗa komai dashi ba, bani da alaƙa da shi, Yauce rana tafarko dana fara yin tozali da fuskarshi, amma meyasa nake jin wani abu agame dashi? Dan Allah ku fahimtar dani na shiga ruɗani, ya akai komai nashi kalar nawa"? Yana magana la66ansa na kerma.

"Owais ka faɗamin wanene Yaron nan? Su wanene Iyayenshi? Meyasa yake kama dani da ƴata Nazli"? Da kakkausar murya ya furta maganar saboda aruɗe yake da lamarin. Shi kanshi chief owais din Ya kasa furta komai, Lamarin Ya ruɗar dashi ya rikirkitar mashi da tunaninshi, bai ta6a tsammanin kamanninshi da yaron sun 6aci har haka ba.

A hankali Ya soma yin taku Izuwa gaban Prime minister hateem dake dubanshi fuskarshi a yamutse.

Cikin kwantar da murya ya furta"Uncle, bamu da masaniya akan su wanene Iyayen shi, saboda bai dasu a halin Yanzu, da shi da ƴan uwanshi dake ahannunmu bamusan komai nasu ba, tamkar marayu suke a hannunmu, Yarinya ɗayace mukasan Mahaifinta tajuddeen" ya faɗa yana nuna Boss man da hannun shi. Girgiza kai yaɗanyi numfashinshi na fita da huci yace"Owais kada ku maidani mahaukaci, nafasan me nake yi, taya za'ace babu danginshi? Kyakkyawan yaro kamar wannan?ni kawai so nake ku faɗamin meyasa muke Kama"!!! Ga dukkan alamu prime minister ya fara zaucewa, wata irin zuface take tsastsafo mashi saman goshin shi. Hankalin kowan nan su Yana akanshi, owais baisan taya zai fahimtar da uncle din nashi ba, Miƙewa Sheikh Imam yai tare da nufar prime minister Ya tsaya agabanshi, tare da kai hannu ɗaya ya dafa kafaɗarshi, a tsanake Ya soma yi mashi magana "Ka kwantar da hankalinka, yakamata ka fahimci abun da Awaisu Yake ƙoƙarin faɗa maka, su kansu basu da masaniya akan yaron, kaɗan daga cikin ikon Allah kenan, kowani ɗan adam yana da masu kama da shi A duniya....." tunkan sheikh Imam Ya ƙare maganar, prime minister yace"baba, wannan yafi ƙarfin ace kamace kawai, ka dubi fuskarshi dakyau, tamkar anyi photocopy dina, kamar dai nina haife shi, Ina jinshi tamkar jini na, ƙaunar da nake yi mashi kaɗai abun dubawace, ta zarce misali, saboda shifa na kasa runtsawa adaren Jiya, na damu da shi fiye da tunaninku........." gaba ɗaya sun rasa taya zasu shawo kan prime minister, a iya sanin su da shi bai ta6a haihuwar ɗa Namiji ba, balle ace yarom shine daya 6ata.

"Yanzu abun da za'ai, tun da kana ƙaunarsa kuma yaron baida iyaye, mai zai hana ka ɗauki ragamar kula dashi kafin komawarka canada? Wata'ƙil hankalinka zaifi kwanciya" acewar sheikh Imam, ya fadi hakanne donya kwantar masa da hankalinsa ganin irin ruɗun daya shiga.

"hakan yayi shiekh, Uncle ka ƙaddara cewa jininka ne shi, kana da damar da zaka Iya bashi kyakkyawar kulawa" Chief owais na ya furta hakan.

Kalamansu sun tausasa mashi zuciyarshi, har cikin ranshi Yaji dadin jin hakan.

"Inaso na taimaka mashi yayi wankan ya sanya sutura a jikinshi, zan kira ɗan uwana awaya don yazo ya ganshi, nasan shi kadaine zai ƙara tabbatar min da abunda nake gani a idona, sannan Idan yaron yaji sauƙi kafin in koma canada, zan je dashi gidana don in nuna ma gimbiyata shi da ƴa'ƴana nasan zasuyi mamakin kamanninsa dani musamman Nazli, hatta hasken fatarshi kalar nata ne" murmushi ne akan fuskokinsu, sunji daɗin sakewar da prime minister yayi, hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yayi ba.

Naɗe hannun rigarshi yayi, tare da cire agogon azurfarshi, da zoben hannun shi, Ya miƙa ma owais su, da sauri owais ya sanya hannu ya kar6a, gaba ɗaya kallon shi suke da mamaki akan fuskokinsu.

Murmushin gefen fuska yasaki har dimple dinsa ya lotsa"kada kuga ina zumuɗi akanshi ƙaunarsa nake Yi" da zolaya ya furta maganar kafin yace" wazai taimaka min mu shiga da shi bathroom room"? da sauri Salsabeel Yace"ni Yalla6ai" "Yawwa, ruƙo min shi mu shiga ciki, ko da ya ke naga yana da girman jiki zaiyi nauyi, bari na kama maka" a hanzarce Ya zagaya ta 6angaren da salsabeel Yake, a lokacin sabeel Yayi koƙarin janyo danish da ƙyar ya kawo shi bakin gadon. Kafaɗunshi suka rurruƙe shi da prime minsiter suka miƙar dashi tsaye, wanda badan ƙarfin giant da sabeel yake dashi ba da kuwa babu mai iya ɗaga shi, jikin shi ya saki tamkar wanda baida ƙashi, kanshi ya kalli kasa sumar kanshi ta lullu6e fuskarshi, idanuwanshi suna arufe gam, zufa ta ko'ina take tsasstsafo mashi, a hankali suke tafiya dashi suna nufar toilet, har suka yi nasarar shigar da shi ciki' Bayan shigarsu, sheikh imam ya dubi boss man da owais "Inason ganin sauran Yaran da kuke ruko a hannunku" Da sauri Boss Man Ya amsa mashi da toh, Ya miƙa ma sheikh imam rawanin shi daya ruƙe a hannunshi tare da hularshi, godiya yayi mashi, har ya juya zai fuce muryar chief owais ta dakatar dashi "Boss, Ka tara yaran a main falo, Yanzu zamu sauko down" Amsa mashi yai da toh, kafin yasa kai ya fuce daga dakin Ya sauka down.

A hanzarce yake tattaka staircases din benan, har ya kusa saukowa down yai tozali da big guy dake tafiya cikin takun sauri, ganin boss yasa shi fadin"Ya ake ciki mutumina? Boss yace"Alhamdulillah Danish ya dawo ainihin suffarshi, Sai dai babu kuzari ajikinshi, Ko yatsanshi bai iya ɗagawa, ga tabonnin harbin bindigar da akayi mashi ta ko'ina saman fatar shi" Cike da jin alhini Big guy yace"bawan Allah, banji dadin jin hakan ba, wallahi yaron tausayi yake bani, ashe munyi mashi illa da harbin bindigar amma ina fata baiji mugun rauni ba ko"?

Ɗaga mashi kai boss yayi alamar eh, fuskarshi da damuwa yace"ubangiji Allah yaba shi lafiya, Allah kuma ya kawo mashi ƙarshen wahalar shi"Boss ya amsa mashi da ameen kafin yace"yanzu haka Prime minister da ɗan uwanshi, sun shiga dashi bathroom zasuyi mashi wanka, sheikh imam ne ya bada shawarar yin hakan" Zaro ido big guy yai da zolaya yace"Yanzu wannan ƙaton balagaggen zasuyi ma wanka? Yaron fa yakai chief dinmu girman jiki," Harara Boss man ya jefa mashi"laifina ne dana tsaya yin magana da ɗan ƙwaya, sai kace ba ka ji nace maka bai iya ɗaga koda yatsansa ba, lalura ce ko kai kanka akwai ciwon da sai dai adinga yi maka wanka, ba fata nake yi maka ba, ina dai kwatanta maka ne babu wanda yafi ƙarfin ƙaddara" Dariya big guy yasaki"Haba mutumina, nima fa wasa nake yi, nadai jinjina lamarin ne, amma baka fadamin ba prime minister baiyi mamakin ganin fuskar yaron ba"? Dariya boss yayi kafin yace"daɗina da kai shegen son gulma uwa mace" Cike da zumuɗi big guy yace"ni dai ka amsa min tambayata na ƙosa naji" Boss man yace"kallo yabarka, hankalin prime minister ba ƙaramin tashi yayi ba, kusan fa hauka yayi mana gaba ɗaya ya rikice tunda yayi tozali da fuskar yaron, daƙyar fa muka shawo kanshi, duk yabi ya ruɗe......" a tsanake Man ya labarta mashi komai. Dariyar shaƙiyanci Big guy yasaki hada tafa hannayensa yana fadin"ni dama nasan za'a rina wallahi, nifa tuntuni nake mamakin kamanninsu da yaron, koda ake maganar yana kama da chief namu saida na raya arainacewa duk ranar da hateem yayi arba da yaron sai ya sha mamaki, donni nafi ganin kamanninshi da nashi, sai gashi maganata ta tabbata" da ƙwarin gwiwa ya ƙare maganar, boss da zolaya yace"sannu malamin duba, aikinka na kyau, ka tsareni da surutu kamar kanyar da bata da daɗi, ka hanani ƙarasawa inda zanje" "Ina zakaje ne"? Big guy ya jefa mashi tambayar. "Sheikh imam ne Ya buƙaci atara mashi sauran yaran yana son ganinsu" Big guy yace"ai ƙwara yagansu domin kuwa suna buƙatarshi kodan saboda wannan jarin taka, ni ina da tabbacin ba'a rasa almatsutsai akanta....."dariyace ta kubce mashi daƙyar ya ƙare maganar, ganin yadda boss man ya haɗe fuskarshi. Harara ya jefa mashi"Idan ka isa ka maimaita maganarnan agaban chief" Big guy yace"ai ko giyar wake nasha bazanyi wannan gangancin ba," Fuskar boss ɗauke da fara'a Yabi ta gefen big guy Ya yi gaba abunshi Ɗaga murya big guy yai tare da cewa"Yaran suna a ɗakin Jarinka gaba ɗayansu na tarasu anan" Murmushi taj yasaki, haɗi da girgiza kanshi, bakomai yasa shi yin hakan ba face sunan da big guy yake kiran Babynsa angel, wato JARI, saboda yace mashi chief zaiba auranta yafi son inda zata huta shine fa ya ruƙe abun azuciyarshi har yake tsokanarshi da sunanta.

Idan muka koma 6angaren su unaisah, tuni sun kammala yin breakfast dinsu, kowa yaci ya ƙoshi yayi hani'an, sai dai damuwa ta hanasu sakat, Hankalinsu ba akwance Yake ba, sunyi zugudum saman carpet, kowa ya zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki, jefi jefi sukan buɗe baki suce Allah sarki danish dinmu, ko awani hali yake a yanzu, a lokacin ummin america ta shiga toilet din dakin nasu.

Batool ta kwantar da kanta kan kafaɗar unaisah, Azeeza ta ɗaura nata kan a shoulder din Sajeed, hannayensu ruƙe cikin na juna, Jemimah ta haye bisa laps din haris idanuwanta alumshe sai faman firgita take Yi tana jan numfashi kamar baccine ke ƙoƙarin yin awon gaba da ita, parveen da naufal sun jingina bayansu jikin gado fuskokinsu babu walwala, hannah kuwa ta ɗaura kanta saman laps din javed, sunyi shiru babu mai magana, daga tsakiyar carpet din tray din kayan abincin da suka kammala ci ne ba akaiga kawar da su ba, wasu daga cikinsu sai faman lumshe idanuwansu sukeyi alamun bacci suke ji.

Jin motsin buɗe ƙofar toilet yasa Batool yin saurin runtse idanuwanta ta ƙanƙame unaisah, gudun kada ta haɗa ido da aunty ummi, fitowa tayi daga cikin toilet din, sautin takalman ƙafartane ya fargar da masu gyangyadin cikinsu, gaba daya suka ware idanuwansu akan ummi dake tunkarosu.

Ta fahimci tsantsar damuwace atattare dasu, tun ɗazu da suna cin abinci ta lura da kyar suke cusa abinci abakunansu, tasan bai wuci damuwar halin da ɗan uwansu yake aciki bane" "Aunty ummi, Inaso zanje dakin danish in duba jikinshi" unaisah ce tayi maganar Ummi tace"a'a, ba'a bada iznin wani daga cikin ku Ya fita ba" Ya mutsa fuska unaisah tayi tamkar zata fashe da kuka ta kuma cewa"aunty ummi batool ta manta doguwar rigarta a ɗakinki jiya da su ka je kwana, zanje na ɗauko mata" Girgiza kai ummi tayi"basai kinje ba, zuwa anjima da kaina zan dauko mata rigarta" zumbura mata baki Unaisah tayi duk yadda taso tayi ma ummi wayau taƙi barinta ta fita. A ƙule unaisah tace "To waimu haka zamuyi ta zama a ɗaki kamar an kulle kaji a keji" Dariya ummi tasaki har fararen haƙoranta suka bayyana tar dasu kamar gonar auduga "Kin gaji ne"? Ɗaga mata gira unaisah tayi alamar eh. Gyaɗa kai ummi tayi"okey, bari na taimaka maku ku girgije jikinku," basu fahimci me take nufi ba. Zura hannu tayi cikin aljihun doguwar rigar jikinta ta zaro iphone dinta, duk sun ƙura mata ido suna jiran ganin me zatayi da wayar. Zira ziran yatsun hannunta ta ɗaura kan screen din wayar ta soma yin pressing dinta, jim kaɗan daddaɗan sautin kiɗa ya soma karaɗe bedroom din nasu, taken waƙar ed shareen mai suna Shape of you.

Fuskarta ɗauke da shu'umin murmushi take kallonsu, sun ƙura mata ido suna kallonta, ganin ta fara jujjuya qugunta tana taka rawa.

"Idan kuna ra'ayi ku taso muyi rawa" ɗaure fuska Unaisah tayi ranta a6ace take dubanta har ta buɗe baki zatace mata bazasuyi rawarba, Sajeed Ya miƙe Yana taka rawa ya nufi tsakiyar ɗakin, miƙewa Azeeza tayi da sauri tabi shi Ya ruƙo hannunta Yana jujjuyata, tuntsirewa Ummi tayi da dariya tana kallon su, abu kamar wasa sautin kiɗan yafara kai masu karo, Naufal ya miƙe ya ruƙo hannun Parveen suka nufi tsakiyar ɗakin suma suka fara yin rawa, Aruɗe unaisah take kallonsu kamar waɗanda akayima asiri, lallai ummi ba ƙaramar shaidaniya bace hakanan taja hankalinsu da sautin kiɗa, ruƙo hannun Hanna javed yai suka miƙa suma suka nufi tsakiyar dakin, Haris Ya miƙe Jemimah ta like mashi tana fadin itama zatayi rawar, ya ruko hannunta suka bi sahu, Ya rage saura Unaisah da Batool su kadai ne suka ki tashi.

"Sanya damuwa aranku bazai ta6a yi maku maganin matsalarku ba, Ni taimakon ku nake sonyi don na fahimci baku san me ake nufi dajin dadin rayuwa ba, kunfi so kuyita ƙuntata kanku bayan kowani ɗan adam yana da damar da zai sanya kanshi farin ciki, If you let me do my job, you'll see the positive results soon."......" muryarta da kwarkwasa take yin magana tana kallon Batool da Unaisah.

"Idan kunaso mu zauna lafiya daku, to ku bani haɗin kai, Ni kuma zan wayar maku da kanku, zan sanyaku farin cikin da zai kawar maku da damuwarku" da shaƙiyanci take yi masu magana tana ɗage girarta.

Sunyi shiru babu alamun zasu tanka mata, shu'umar dariya tasaki tare da cewa"Na fahimci unaisah kece mai taurin kai, Saboda ke Batool taƙi tashi ta taka rawa ko"? Murguɗa mata baki unaisah tayi. "Idan kika bani hadin kai mukayi rawa zan barki ki fita daga ɗakin nan kije wurin ɗan uwanki danish...."tunkan ummi ta rufe baki unaisah tayi saurin furta"a'a sai dai ki bari in fara zuwa dakin shi, Idan na dawo sai muyi rawar" "Zaki rasa damar da kike da ita" acewar ummi, Ta furta maganar tare da miƙa ma batool hannunta alamar ta taso suyi yawa, cike da jin shakkarta Batool take kallonta, fuskar ummi a ɗaure tace da ita"Come to me" sai da batool tafara kallon unaisah jikinta sukuku kafin ta yunƙura ta miƙe tare da ɗaura hannunta na dama saman hannun ummin america, gam ta ruƙe hannun tajata zuwa tsakiyar ɗakin rawa suka soma takawa kamar mace da namiji haka take juya batool tana rungumeta idonta akan unaisah data haɗe fuska tana satar kallonsu.

Canza masu waƙa tayi ta sanya masu waƙar rema mai taken baby come down, tunda sautin kiɗan Ya fara ratsa mata zuciya takasa jurewa ji tayi kamar ana janta a hankali ta miƙe tsaye tana kallon ƴan uwanta dake ta tiƙar rawa suna dariya, itama sai taji tana buƙatar yin nishaɗin kota ɗebe kewar danish dake damunta. Ganin ta miƙe tsaye sototo tana kallonsu yasa ummi miƙa mata hannu ɗaya alamar tazo gareta. Maƙe mata kafaɗa tayi alamar bazata zo ba, batool tace"please sister kizo muyi yawa atare dan Allah" harara ta watsa ma batool, muryar sajeed ce ta janyo hankalinta ga dubanshi. "Sister zo mu taka mana, muna buƙatarki afilin nan" murguɗa mashi baki tayi. "Genie dan Allah kizo muyi rawa, kinga ni banda abokin yi haris baiyi dani" da shagwa6a jemimah tayi mata maganar, hada marairaice mata fuska. Magiya suka dinga mata akan tashigo suyi rawar, tun tana maƙe masu kafaɗa, har dai jemimah tazo taja hannunta suka shiga filin, ai tunda tafara taka rawa kamar ɗiyar roba, daɗi ya kamasu ganin unaisah ta saki jiki tana tiƙar rawa, nan fa kowa ya bada himmah, sosai suke jijjiga qugunansu, wani abun ƙayatarwarma sai sun yarfar da sumar kansu kamar indiyawa, sautin kiɗan ba ƙaramin ƙara masu ƙaimi yake yi ba, ummi ce kaɗai take bin waƙar suma tun basu iyaba har suka fara bi saboda harshen turancine tamkar yarensu ne........: Dawo da waƙar farko tayi jin sun fara dauka suna bi, aikuwa gaba daya suka kware murya suna bin waƙar

Baby, calm down, calm down Girl, this your body e put my heart for lockdown For lockdown, oh, lockdown Girl, you sweet like Fanta, Fanta If I tell you say I love you no dey form yanga, oh, yanga No tell me no, no, no, no, whoa-whoa-whoa-whoa Oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh Baby, come gimme your lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-love You got me like, "Whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa" Shawty come gimme your lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-love, mm-mm

Cike da nishaɗi suke bin waƙar suna dariya fararen hakoransu kamar gonar auduga, ita kanta ummin america ba ƙaramin burgeta sukayi ba, Kamar sakarya haka tasaki baki tana kallonsu, a ƙarshe saita bar masu filin rawar ta koma gefe ɗaya tamkar dj ta goya hannayenta saman kirjinta tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi, sun bata mamaki, daga kunna masu waƙa har sun haddace ta, aranta ta ayyana lallai yaran suna da kaifin basira, yanayin yadda sukeyin rawar suna jujjuya qugunansu yafi komai tafiya da hankalinta, musamman unaisah da parveen sunfi zaƙewa sai kuma uban gayya Sajeed dama shine yafara koya masu rawa tun agidan kurkukun ƙaddara, salon rawarshi kalar ta ƴan club ce, da aji yake yinta hannun shi ruƙe dana Azeezarshi Sun tsunduma suna tiƙar rawa ko gajiya basayi. Da ƙarfi Sajeed Yace Aunty Ummi ki canza mana wata waƙar mai daɗi" Da sauri ta ɗauki wayar ta kunna masu waƙar alen walker. Unaisah na soma jin taken waƙar tayi saurin kamawa tafara bi saboda tasanta tun da jimawa, sajeed ma ya iya waƙar, atare suka haɗa baki suna bin waƙar Lost in your mind, I wanna know Am I losin' my mind? Never let me go If this night is not forever, at least we are together I know I'm not alone I know I'm not alone Anywhere, whenever Apart but still together I know I'm not alone I know I'm not alone I know I'm not alone I know I'm not alone Unconscious mind, l'm wide awake Wanna feel one last time Take my pain away......."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull