Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 72
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 72: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 72. Abun da basu sani ba, tun ɗazu boss man Ya shigo…
3,330 words
Abun da basu sani ba, tun ɗazu boss man Ya shigo ɗakin, yana daga tsaye bakin kofar Ya goya hannayenshi saman kirjinshi, ɗaya bayan ɗaya yake binsu da kallo kafin ya tsayar da idanuwanshi akan Unaisah da ta zaƙe tanata jujjuya qugu tana bin waƙar, tsabar mamakine Ya hanashi yi masu sallama, bai ta6a tsammanin zata Iya yin rawa har haka ba,Yarinyar da kullum take acikin damuwa. Ummin america tana faman wurwurga eye balls dinta akansu karaf idanuwanta suka hango mata boss man dake atsaye yana kalonsu, da sauri ta kashe sautin, ta kama yin ƴan kame kame, su kuwa prisoners koda ta kashe sautin basu lura da shi ba, a shagwa6e Jemimah ta bubbuga ƙafa tana fadin"wayyo Allah aunty ummi, meyasa kika kashe mana abun, ni wallahi bangaji ba, dan Allah ki sake kunna mana muyi rawa mu girgije" ta faɗa tana karkaɗa ƙaramin qugunta, gaba ɗaya suka tuntsire da dariya.
Banda ummi data kame kanta
"Please aunty ummi ki kunna mana mu ƙarasa yin rawar" acewar parveen idanuwanta akan fuskar boss dake tsaye yana kallonsu, Sun juya mashi baya shiyasa basusan da zaman shi ba, ita kadaice take Iya ganin shi.
A wayance tace"nifa ba don wani abu na kunna maku sauti ba, kawai na fahimci kuna acikin yanayi na damuwa shiyasa nayi ƙoƙarin don in sanyaku nishaɗi, kuma Alhamdulillah naga canji atare daku...." tunkan ta ƙare maganar, Boss man ya ɗaga hannayenshi yai clapping da ƙarfi haɗi da furta"Sannunku da ƙoƙari" a firgice suka waiwayo baya suna dubanshi kamar wadanda suka ga dodo. Unaisah hada dafe ƙirji tana fadin"Boss tun yaushe ka shigo dakin nan"? "Tun time da kika fara rawa ina atsaye ina kallonki" wata irin kunyace ta kamata da sauri ta juya ta nufi saman gado ta haye ta kifa kanta jikin pillow tana dariya.
Hakan da tayi yayi matuƙar bashi dariya.
ɗaura idanuwanshi yayi akan fuskar ummin america sai faman ƙyafƙyafta idanuwanta take yi.
"Ummi Amanar da muka baki kenan? A matsayinki na mamansu kin tarasu akan idonki suke tiƙar ruwa, ke da kanki kika kunna masu sauti, ƙiri ƙiri so kike ki maida mana ƴa'ƴa ƴan rawa ko"?
A ruɗe ta furta"I'm sorry Sir if I offended you, but I didn't have any bad intentions. I was just trying to make them happy because I noticed they were worried about their brother's illness. That's why I tried to cheer them up......" aladabce tayi maganar, tana matuƙar girmama boss man saboda karamcin da yake yi mata, yafi sakar mata fuska akan sauran jami'an isod.
"Kada ki damu babu komai nima nayi maganarne kawai bawai ina nufin hakan ba, ai nasan ba zaki ta6a yin abunda zai 6ata masu tarbiyaba ba, yau dinma kinyine donki ɗebe masu kewa kuma naji dadin hakan Na yaba da tunaninki, tunda gashi nagani da idona kin taimaka masu da kika sanya su nishaɗi, Na jinjina maki" ya faɗa hadi da yi mata alamar jinjina da yatsanshi. Ƙayataccen murmushi tasakar mashi"nagode da ka fahimce ni" Mayar da dubanshi yayi akan su sajeed dake tsaye suna kallonsu "Ay min afwa na katse maku jin daɗin ku, nima ba laifina bane laifin sheikh imam ne daya buƙaci son ganinku don haka in akwai mai ƙorafi ya tanadi abunsa idan munje gabanshi sai ku faɗa mashi" da zolaya yayi masu maganar, murmushi kowan nan su yasaki. Unaisah jin an ambaci sunan sheikh Imam da kuma maganar yana son ganinsu yasa tayi sauri saukowa daga saman gadon, A kunyace ta kalli boss man tana faman noƙe kai tace"mu tafi boss" Ruƙo hannunta yai acikin nashi, da sauri Batool ta ruƙe ɗayan hannun nashi sukayi gaba su naufal suna abiye da bayansu, gaba ɗayansu suka nufi falon hada Ummin America.
A tsakiyar falon su ka dakata da yin tafiyar Boss Man yace"Ku jira anan bari naje na sanar dashi" harya kama hanya zai tafi Unaisah ta kwala mashi kira, a hanzarce ya juya yana kallonta.
Sosa kai ta ɗanyi da hannunta kafin tace"am..dama inaso ne na tambayeka awani hali danish dinmu Yake aciki ne"?
"Ya dawo mutun" wani irin farin cikine Ya lullu6esu, musamman unaisah bakinta yaƙi rufuwa "sai dai babu ƙarfi a jikin shi, bai iya yin komai ko yatsan hannun shi bai iya ɗagawa" lokaci ɗaya murna ta koma ciki jin abun da Boss man Yace. jikinsu duk yai sanyi, Unaisah tace"baida lafiyane"? Ɗaga mata kai yai alamar eh, ya ƙara da cewa"kada ki sanya damuwa aranku, zaiji sauƙi in sha Allah, addu'arku yake buƙata" Cike da zumuɗi tace"zan Iya binka zuwa ɗakin nashi" Jim ya danyi kafin yace"No, ki tsaya tare da ƴan uwanki, zuwa anjima za'a baku damar ku ganshi" jiki asanyaye ta amsa mashi da toh. juyawa boss man yayi da sauri Ya haye upstairs. Ajiyar zuciya kowannansu ya sauke, ummi dake atsaye harta fara gajiya, wuri ta samu saman sofa ta zauna tare da ɗaura ƙafarta ɗaya bisa ɗaya, taci gaba da danna wayar hannunta. "Mu zauna kafin malamin Ya ƙaraso acewar Unaisah" Amsa mata su ka yi da toh, kowa ya samu wuri Ya zauna, sanyin A.c sai ratsa fatar jikinsu Yake Yi, sunyi shiru babu mai yin magana acikin su, sai faman ƙyafƙyafta idanuwansu suke Yi, duk sun ƙagara da son ganin malamin
Tsawon mintuna ƙalilan, suka soma jiyo takun takalmansu, a hanzarce su unaisah suka kai dubansu gare su.
Sheikh imam ne agaba, daga bayanshi boss man ne tare da Big Guy.
Tunkafin Ya ƙaraso cikin falon Yake binsu da kallo, hannunshi ruƙe da cazbaharshi, a tsakiyar sofa set din suka dakata da yin tafiyar, ummi sam bata lura da su ba, hankalinta na akan wayarta da take dannawa. Cikin girmama su unaisah suka sauko daga saman sofa, suka dawo kan carpet, atare suka haɗa baki wurin gaishe da shi, hakan ba ƙaramin burge shi yayi ba, sai faman sakin murmushi yake, "Masha Allah, kyawawan ƴan mata da samari, fatan na sameku lafiya" amsa mashi sukayi da lafiyalou. "Alhamdulillah, ubangiji Allah ya Albarkaci rayuwarku..." kafin Sheikh Ya ƙare maganar, Boss man Ya kira sunan ummi, a hankali ta ɗago tana kallon shi"bakiga sheikh imam bane"? Adabarbarce ta mamaita sunan malamin da boss Ya kira mata, kasancewar Ya juya mata baya bata samu damar ganin fuskarshi ba, Jin muyarta yasa sheikh imam yin saurin juyowa baya don ganin wacece.........."
Wani irin mugun bugu zuciyar ummi tayi lokacin da idanuwanta su ka yi tozali da fuskar sheikh imam, tsabar firgita har wayar hannunta sai da ta kubce mata, sheikh imam kuwa tunda ya tsayar da kwayar idanuwansa akan fuskarta bai ko ƙyafta ba, wani irin kallo yake binta dashi mai wuyar fassaruwa, lamarin ya ɗaurewa boss man kai, shi da big guy tare da Unaisah gaba ɗaya Hankalinsu na akansu babu wanda yayi yunƙurin dakatar dasu daga kallon da suke jefawa junansu tsawon mintuna ganin abun nasu ba mai ƙarewa bane yasa Boss man yin gyaran murya, adabarbarce ummi ta soma ƙoƙarin tattara natsuwarta duk tabi ta ruɗe kamar wadda taga wani mugun abu. Da sauri ta zuƙunna tare dakai yatsun hannunta dake kerma da niyar ta ɗauki wayarta data faɗi kan floor, sai dai kafin ta kai ga yin hakan sheikh imam ya rigata ɗaukar wayartata, lokaci ɗaya ta miƙe ta juya da gudu ta nufi cikin falon sai da tafara taka stairs sautin shessheƙar kukanta ya karaɗe falon.....
Hankalinsu Batool ba ƙaramin tashi yayi ba, Jin sautin kukan aunty umminsu ya jefa su cikin yanayi na damuwa.
da mamaki akan fuskar Boss man Ya furta"Sheikh meke faruwa? Ko kasan ta ne"?
Shiru ya ɗanyi jim yana jujjuya wayar ummi dake a hannunshi na tsawon sakanni, kafin ya soma magana da karyayyar murya"bansanta ba, Yau na fara ganinta" ya faɗa tare da juyowa yana fuskantarsu Da alamun ruɗu akan fuskar big guy yace"amma meyasa kuka dauki lokaci kuna kallon juna kai da ita? Sannan meyasa ta watsa da gudu tana kuka"? Fuskar sheikh imam babu walwala Yace"dan Allah kubar maganar nan, kasan dai bazanyi maka ƙarya ba geme geme dani, nima abun da yasa nake kallonta saboda kallon da take yi min, kuka kuma da take yi wata'ƙil nayi mata kama da wani ne da ta rasa a rayuwarta"
Jinjina kai big guy yayi badan Ya gamsu da bayanin shi ba.
"Ga wayarta ku ruƙe mata" ya faɗa yana miƙa ma Boss man, wanda yayi zugudum yana kallon yadda jikin sheikh imam ke tsuma sun fahimci da akwai wani abu da ya 6oye masu wanda baison su sani dangane da ganin ummin america da yayi.
Cikin sanyin murya Unaisah tace"Ni zan kai mata wayar," ta fada tare dakai hannu ta kar6e phone din daga hannun sheikh imam, ta nufi cikin falon da sauri.
Bayan tafiyarta, sheikh imam Ya mayar da dubanshi kansu Sajeed da suke a tsaye cirko cirko suna kallon shi.
"Allah ya yi maku albarka, ubangiji Allah ya kareku daga sharrin duk wani abun cutarwa, Allah ya daukaka rayuwarku......" addu'o'i ya dinga karanto masu suna amsa mashi da ameen ameen Bayan ya kammala yi masu addu'o'i, yace dasu"Ku faɗamin sunayenku ina son ji" hatta maganarshi da ƙarfin hali yake yinta duk ya rasa kuzarinsa.
Sajeed ne ya fara cewa"Ni sunana sajeed, wannan kuma Azeeza' ya faɗa yana nuna Azeeza, kafin Ya ɗaura yatsan shi kan Naufal"Sunanshi naufal ta gefenshi Parvin, ga kuma Jemimah da Hanna, sai Javid and Haris, da Batool, ƴar uwarmu data tafi kaima aunty ummi waya sunanta Unaisah"
duk wanda ya nuna sai ya fadi sunanshi bayan ya kammala sheikh imam yace"sannu da ƙoƙari Sajeed, nagode daka faɗamin sunayen ku" murmushi Sajeed yayi ba tare da ya ce komai ba.
A hankali Sheikh Imam Ya dubi boss man da big guy, bai yi mamakin ganin kallon da su ke yi mashi ba, yasan dole suyi tunanin wani abun daban, launin idanuwanshi har sun canza zuwa ja, kau da idonshi yayi daga kansu ya kalli su Haris muryarshi asanyaye yace"ku zauna muyi fira ƴan jikokina" zazzaunawa su ka yi kan carpet shi kuma ya zauna kan sofa, su boss ma suka zauna suna fuskantar shi.
*UNAISAH❤*
Koda Unaisah ta ƙarasa ƙofar ɗakin ummi dafe glass door din ƙofar tayi a hankali ta zugeta, bata sameta a adakin ba, sai dai ta jiyo shessheƙar kukanta acikin toilet.
Ɗaga murya tayi tare da cewa"Aunty Ummi, ga wayarki na kawo maki" shiru ummi bata tanka mata ba, kusan sau biyar tana maimaita maganar babu alamun za'a amsa mata. Saman gado ta ajiye mata wayar, kafin ta nufi ƙofar toilet din ta sanya hannu tayi mata knocking, "Aunty Ummi dan Allah ki daina yin kuka, bamu jin daɗi, idan wani ne ya 6ata maki rai, ki yi haƙuri" lallashinta Unaisah taci gaba da yi tun tana jin shessheƙar kukan ummi, har tadaina jiyo sautin kukanta, hankalinta ya ɗan kwanta juyawa tayi da sauri ta fuce daga ɗakin, maimakon ta sauka down ta koma falo sai ta kalla6a ta nufi ɗakin Danish, dama abun take yima zumuɗi kenan shiyasa ta kar6i wayar ummi da sunan zata kai mata.
Idan muka koma 6angaren Danish tsawon mintuna da suka shiga da shi bathroom, kafin su fara yi mashi wankan saida prime minister ya tofe ruwan da addu'o'i kamar yadda sheikh imam yace adinga yi mashi, batare daya cire mashi short din jikinshi ba yayi mashi wanka da ruwa mai ɗumi, tamkar ya samu jinjirin yaro, saƙo da lungu na jikinshi sai da prime minister ya cuccuɗa shi, bayan ya kammala ya ɗauko farin towel cikin jerin waɗanda ke sagale jikin hanger, ya ɗaure mashi a waist dinshi da dabara ya zame short din daya jiƙe duk don kada yaga tsiraicin shi, shanya short din yayi kafin salsabeel Ya taimaka mashi suka fiddo da shi daga cikin kwamin wankan.
Kafin fitowarsu Chief Owais kadai ya rage a ɗakin, Cikin takun sauri ya nufi faskekiyar closet din Danish ya buɗe yana bin jerin tsadaddun suturunsa da kallo A hankali ya tsayar da idanuwanshi wurin jerin jallabiyoyi yana da tabbacin zaifi samun walwala acikin jallabiya, launin fara ya ɗauko mashi, ya dawo ya ɗaura kan gado.
Jin motsin buɗe toilet door ne yaja hankalinshi ga kallon su A daddafe suka fito da danish hannayensu tallabe da shi, da sauri chief Ya ƙarasa gabansu Ya tallabo masu shi a saman shimfiɗeɗan gadonshi suka kwantar da shi. "Sannu da ƙoƙari Uncle," acewar chief Prime minister yace"yawwa my son, kaima sannunka da ƙoƙari, tun jiya mun hana ka runtsa"
"Bakomai uncle kada hakan ya dame ka aikina ne"
Murmushi prime minister yasaki haɗi da bubbuga kafaɗar chief owais alamar jinjina.
"Uncle yakamata ka koma gida, za'a iya nemanka, ni zan cigaba da kula maka shi"
Girgiza kai Prime minister yayi"No, ba yanzu zan koma gida ba, sai zuwa anjima" Chief bai musa mashi ba don ya fahimci baison tafiya yabar Danish.
"Sabeel, bring me some body lotion and perfume" cikin girmamawa salsabeel ya amsa mashi da toh sir.
Ya juya da sauri ya nufi dressing mirror ya ɗauko body lotion tare da turare yazo ya ajiye su kan gadon.
prime minster ne ya soma bin ko'ina na jikin danish yana shafe shi da mai haɗi da yi mashi tausa don yaji dadin jikin shi, chief ne ya taimaka mashi wurin burkito mashi da danish Ya juya mashi bayanshi, Ya shafa mashi man kafin yabi da turare ya feshe shi.
da taimakon chief suka sanya mashi jallabiyar, masha Allah, tayi bala'en yi mashi kyau, a karo na farko kenan don bai ta6a sanya jallabiyaba, tabi shape jikinshi ta bayyana kyakkyawar surar jikin shi, musamman broad chest dinsa da strong arms nasa sun fito ruɗu ruɗu ta jikin jallabiyar.
Ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, ganin sunci nasarar gyara mashi jikin shi, hatta sumar kanshi saida prime minister ya sharceta ya shafe mashi ita da mayukan gyaran gashi, ƙamshin turaren danish ya cika ɗakin kamar wanda akayi ma wanka da ruwan turare.
"Yanzu me ya rage mana"? Acewar chief, prime minister yace"nasan yana jin yunwa, Yana buƙatar abincin da zai ci"
Salsabeel yace "Yayi bacci yanzu, naga lokacin sallah yakusa cika, may be kafin mu kammala yin sallah ya farka sai mu bashi abincin"
"Kana nufin har muka yi mashi wanka bacci yake yi"? Prime minister ne ya faɗa yana duban salsabeel.
"A'a yalla6ai, idonshi biyu, tun lokacin da muka shiga dashi bathroom, Yanzu nan yayi bacci"
"Taya akai ka gane yayi bacci" da mamaki yayi mashi tambayar, chief dai yana atsaye yana sauraronsu.
"Yatsun hannun shi dana ƙafarshi, suna kerma yanzu kuma sun daina gaba ɗaya sun tsaya yadda su ke" Fuskar prime minister dauke da murmushi yace"ka karanci ɗan uwan nan naka sosai, naji dadin jin hakan, may be wankan da mu ka yi mashi ne yasa shi jin daɗi har yayi bacci" Saldabeel yace"ƙwarai kuwa yalla6ai, ay kayi ƙoƙari, Allah yasaka maka da mafificin alkhairinsa kamar yadda ka faranta mashi rai ka gatanta shi kaima inayi maka fatan Allah ya faranta maka ya ƙara ɗaukaka ka" Har cikin ranshi yaji daɗin kalaman salsabeel, "Yalla6ai kaima ban barka abayaba, domin kuwa kayi namijin ƙoƙari wurin ganin ɗan uwana ya samu lafiya, Allah ne kaɗai zai Iya biyanka" ya faɗa yana duban chief owais. Jinjina mashi kai yayi batare daya furta komai ba. Kiraye kirayen sallar Azhar da aka farayi ne Yaja hankalinsu da sauri chief ya zaro agogon azurfar hateem tare da Zobensa daga aljihu Ya miƙa mashi. Bayan ya saka a hannun shi, ɗaya bayan ɗaya su kayo alwala, kafin fitarsu daga dakin saida prime minister yaje har gaban gadon danish ya ɗan duka tare da kai small lips dinsa saman forehead din danish Ya manna mashi peck, ji yake kamar karya tafi yabar shi, ganin abun nashi bamai ƙarewa bane ga time ɗin salla na tafiya ya kafe danish da ido babu ƙyaftawa da sauri chief yaje ya ruƙo hannun shi ya janyo shi a hankali suka nufi ƙofar fita ɗakin.
Adai dai lokacin Unaisah dake la6e bakin ƙofar ɗakin tana sauraron su, jin motsin tafiyarsune yasa tayi saurin watsawa da gudu ta la6e a wata ƴar corner. Akan Idonta, Chief Owais Ya fito hannun shi ruƙe dana prime minister, still bata samu damar ganin fuskokinsu ba, sai dai salsabeel daya biyo bayansu shi tagani da kyau, tunani ta somayi aranta ko wanene wannan babban mutumin, taso ace taga fuskarshi shida chief, Allah bai bata sa'a ba, Har saida suka 6ace ma ganinta tukunna cikin sanɗa take bin bango tana nifar ɗakin danish cikin sa'a ta buɗe ƙofar ta shige, daddaɗan ƙamshin turarenshi ne ya daki hancinta har saida ta lumshe idanuwanta tana shaƙar shi ......
Cikin takun sanɗa ta nufi gadon, yayin da idanuwanta suke hango mata Man dinta, hayewa saman gadon tayi daga gefenshi ta dakata tana bin body dinsa da kallo, from head to toe, wani irin farin cikine ya lullu6eta ganin shi cikin shiga ta farar jallabiya yayi mata kyau, aranta ta ayyana nasan waɗannan mutanan ne suka taimaka mashi wurin gyara jikinshi saboda boss ya faɗamin cewa ko yatsanshi bai iya ɗagawa, idan kuwa hasashena gaskiya ne naji daɗi ubangiji Allah ya saka masu da gidan Aljanna, ta ƙare zancen zucin fuskarta ɗauke da murmushin farin ciki.
Ta rasa gane bacci yake yi ko idonshi biyu, amma dai tayi missing dinshi na tsawon awannin daya ɗauka tun jiya a halittar maciji, ashe dai da rabon zata sake ganinshi da ainihin suffarshi, yayin da take kallonshi karaf idanuwanta suka sauka akan jan tabonnin dake akan farar fatar dogon wuyansa, harzuwa saman fatar hannunsa.
Ras taji gabanta ya faɗi, ta zazzaro idanuwanta waje tana fadin"My man meke damunka? Jan tabon menene nake gani a jikinka"? Ta ƙare maganar fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa, hawaye tuni sun jiƙe gashin idonta.
Ziraran yatsun hannunta ta ɗaura saman wuyanshi ta soma shafa tabonnin slowly ta zame fingers din daga neck dinsa zuwa kan broad chest dinsa, a hankali take 6alle links din gaban jallabiyar don ta samu damar ganin sauran tabonnin da ke akan fatarshi, da ta buɗe faffadan kirjin nashi, hankalinta yayi matuƙar tashi da ganin tabonnin ta ko'ina, ji tayi tamkar zuciyarshi bata bugawa da sauri ta kanga Kunnanta na dama saitin zuciyarshi, natsuwa tayi tana sauraran yadda take harbawa cikin kwanciyar hankali, tsawon mintuna bata ɗago da kanta ba saboda dadin sauraran heart beat dinsa da take ji, A hankali ta ɗago da kanta karaf idanuwanta suka sauka akan soft lips dinsa batasan ya akai ta tsinci kanta dayi masu kallon ƙurulla ba sun ɗan kumbura, zuciya ce ta soma tunzurata akansu, unaisah da kasada ta ɗaura yatsun hannunta na dama kan la66ansa tayi squeezing ɗin su, ba zato ba tsammani taji yaja dogon numfashi da ƙarfin gaske, tsabar kiɗima jiki na rawa ta rarrafa ta ta wulkita can ƙasan gadon ta faɗo ta labe zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi jikinta ya hauyin kerma duk tabi ta ruɗe gani take yi kamar ta fama mashi ciwon shi...
Runtse idanuwanta tayi hadi da matse pink lips dinta wani irin yanayi take ji mara misaltuwa atattare da ita, Jin shiru ya daina jan numfashin ne yasa ta lalla6a ta ɗago da kanta tana leƙenshi, babu abun da ya canza yaci gaba da yin baccin nashi. Ƙasa ƙasa da murya ta furta"I'm sorry to disturb you, I've missed you so much. I can't take my eyes off you."
Lalla6awa tayi a hankali ta haura saman gadon da rarrafe ta nufe shi, rumfa tayi mashi da sumar kanta ta natsu tana shaƙar ƙamshin turaren jikinsa, tabi ta addabi rayuwarshi da sunan tayi kewarshi tahana mashi sukuni abaccinsa, don taga babu kowa aɗakin shiyasa take yi mashi iya shege....
Lokacin da Chief da prime minister tare da salsabeel suka sauko down, kaitsaye suka nufi babban falon, tunkafin su ƙaraso takun takalmansu Ya isar da saƙon zuwansu, A hanzarce Sheikh imam da su Boss man suka mimmiƙe tsaye suna jiran ƙarasowar su, su sajeed dake zazzaune kan carpet suna kallonsu, lokaci ɗaya suka shiga ruɗanin ganin fuskar prime minister Hateem data chief Owais, duk da shi chief ya sanya face mask a fuskarshi, a matuƙar ruɗe suke kallonshi bakunansu asake babu alamun zasu motsa.