Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 73
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 73: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 73. "Sannu da fitowa Yalla6ai" Boss man ne yayi…
3,266 words
"Sannu da fitowa Yalla6ai" Boss man ne yayi maganar, Big guy yace"barka da fitowa" amsa masu yayi fuskarshi asake, Sheikh Imam yace"ya jikin yaron? Prime minister yace"Yayi bacci shiyasa muka ƙyale shi zuwa time da zai farka" "Alhamdulillah, naji dadin jin hakan, baccin nan da yayi hutu ne agare shi"
"Babana, muna ƙara yi maka godiya bisa ƙoƙarin da kayi mana, mun hana ka sakat mun kuma hana ka huta, Allah ne kadai zai iya biyanka....." fuskar sheikh imam dauke da murmushi ya furta"bakomai Hateem, kada kaji komai, ai indai akan aikin lada ne bazani ta6a gajiyawaba, koda zan shekara inayi ne, ni dai fata na shine Allah ya dubi kyakkyawar niyarmu akan yaron nan ya bamu nasara akan ƙudirin da muke dashi na ganin mun raba shi da miyagun dake bibiyar rayuwarshi" jinjina kai kowan nan su yayi, shiekh imam ya daura da cewa"idan na samu natsuwa kafin zuwa dare, Zan turama shi Awaisun addu'o'in daya kamata arunƙa mashi akan komai da zaiyi amfani dashi, kada a kuskura abarshi ya yi gamon kan shi, tun da shi ba musulmi bane bai yi imani da Allah ba, shaidanun dake ajikinsa bazasu ta6a bari ya ambaci sunan Allah, ko ruwan addu'a zaku bashi ku tabbatar yasha akan idonku idan bahaka ba shaidanun zasu iya zubar dashi ko su canza mashi ruwan batare da kun ankareba, tun da su ba ganinsu akeyi"
"Insha Allah malam zamuyi ƙokarin yin hakan" acewar Boss man.
Ga dukkan alamu Prime minister Hateem bai lura dasu Batool ba, hatta shi kanshi chief owais din, wani iko na Allah salsabeel dake kallonsu har kallonshi sukayi babu alamun sun gane shi, nan take ya fahimci basu ruƙe kamanninshi ba, saboda sau ɗaya suka ta6a ganinshi kuma a lokacin basu acikin hayyacinsu, jamimah da Azeeza da parveen su dama basu ta6a ganinshi ba, asume aka fitar dasu daga kurkukun.
"Lahh! Ji wani mai kama da Danish dinmu" muryar Jemimah ce ta fargar dasu, kusan atare suka daura idanuwansu akan yaran Zumbur jemimah ta miƙe taje gaban prime minister ta tsaya hada ruƙe qugu tana ƙare mashi kallon mamaki da al'ajabi
Ɗaya bayan ɗaya yake bin yaran da kallon, Ya fahimci kallon mamaki suke yi mashi, Boss man ne yai masu gyaran murya tare da cewa"Sajeed, kuzo ku gaishe da Kawun Chief dinmu Owais sunanshi prime minister Hateem, wannan kuma shine chief dinmu Owais" ya faɗa yana nuna masu chief da hannun shi. Atare suka miƙe tsaye suka nufi prime minister cikin girmamawa suka gaishe da shi, kafin suka gaishe da Chief Owais. Murmushi prime minister yasakar masu har dimple dinshi ya lotsa, da mamaki suka kalli juna ganin yadda kamanninsa da danish suke ƙara bayyana. "Masha Allah, Naji dadin haduwa daku, My Son ina kuka samu kyawawan ƴan mata da samari masu kama da jinin family dinmu? Ai ni nayi tsammanin Danish ne kadai yake kama damu amma sai nake ganin fuskokin ƴan uwana akan faces dinsu kodai idanuwana ne suke nuna min badai ba"? Sheikh imam na murmushi yace"ba kai kadai ba Hateem, ni kaina tun da nayi tozali da yaran nan nake ta mamakin kamannin ku dasu"
"Uncle, waɗannan sune sauran yaran da muke kula dasu, Ƴan uwan danish ne" chief owais Ne ya faɗa yana nuna su da hannun shi. "My son Allah Ya tayaku ruƙo, Ina ƙara yaba maka da jinjina maka akan ƙoƙarinka" calmly chief ya furta mashi thanks" "Sajeed, mu tafi masallaci, Batool kija sauran ƴan uwan naki ku tafi ɗaki ku yi sallah, Boss man ne yayi masu maganar, Cikin sanyin murya batool tace"Idan muka kammala yin sallah zamu Iya zuwa ɗakin ɗan uwanmu Danish mu duba shi" da ta furta maganar har chief owais saida ya kalleta kafin ya kau da idon shi. Salsabeel ne yace"ku ƙara hakuri yanzu bacci yake yi, sai dai zuwa anjima idan sun farka" amsa mashi tayi da toh, tayi mamakin ganin yana sakar mata murmushi, yayi tsammanin idan sukaji muryarshi zasu gane shi amma still babu alamun zasu gane ɗin. "Ina ƴar uwarku Unaisah"? Ya jefa mata tambaya, kafin ta bashi amsa boss man ya rigata cewa"taje ɗakin ummi ne" Prime minister yace"In sha Allah zuwa anjima idan na dawo gidan zanyi magana daku" ya faɗa yana nuna su batool,' amsa mashi sukayi da toh, hadi da yi masu godiya.
Bayan tafiyarsu Batool taja sauran ƴan uwanta mata suka nufi ɗakin su.
*SIR MUBARAK✊*
Tun wuraren ƙarfe takwas na safe suka baro asibitin kafin tafiyarsu saida Sir mubarak yayima Dr fawan Alheri saboda yaji daɗin Yadda ya taimaka mashi wurin ganin Jazz Ya samu lafiya, da matsakaicin gudu motarsu ta haura saman titi, Major ne yake yin driving dinsu, yayin da sir mubarak da jazz suke zaune a back seat na motar.
Ya ruƙe hannun jazz acikin nashi, kamar ance za'a ƙwace mashi shi, Jazz sai faman lumshe idanuwanshi yake yi kamar mai jin bacci, "Jazz me kake tunani naji kayi shiru tun da muka fito daga asibitin baka ce komai ba," cikin kulawa Sir mubarak yayi mashi magana yana dubanshi In a cool voice ya furta"Ina tunanin khadija, bata sha maganinta na safe ba bansani ba ko salsabeel Ya bata" Murmushin gefen fuska Sir mubarak yayi"idan na fahimceka kana magana ne akan Yarinyar nan mai ta6in hankali ta gidan kajin da kuke kiwo ko ba haka ba" ya fada da zolaya yana ɗaga mashi gira, tuntsirewa sukayi da dariya gaba ɗayansu hatta major dake driving dariyar yake yi. "Daddy dan Allah mu daina tuna abun da ya wuce" sir mubarak ya ce"okey na daina my son, tun da baka so" Gyaran murya Major yayi sir mubarak ya dago yana kallon fuskarshi ta cikin mirror.
"Sir, ina zamu nufa? gidanka ko can gidan da Yaran suke?"
Shiru sir mubarak ya danyi kafin yace"mu wuce gida, jazz yana son ganin mommynsa, nasan tayi kewarshi, in yaso daga baya sai muje can gidan" Amsa mashi yayi da toh.
"Idan mun isa gida please ka kira tiger A waya ka tambaye shi awani hali yaran suke aciki, inason sani" Cikin girmamawa Major Ya ce"in sha Allah Yalla6ai zan tuntu6e shi' Ajiyar zuciya sir mubarak Ya sauke tare dakai dubanshi ga Dr jazz, "My son, ya zamuyi? Bansan ta yadda zanyima mommynka bayani ba, gashi ni ban iya ƙaryaba, nasan dole ta shiga damuwa idan ta kalli fuskarka," fuskarshi a yamutse yayi maganar, har cikin ranshi baison 6acin ran turai duk da yasan zata fahimce shi amma dole taji ba daɗi. "Daddy kada ka damu, idan mukayi mata bayani zata fahimce mu in sha Allah" "Allah yasa my son" daga haka babu wanda ya ƙara yin magana acikinsu, har suka shigo estate, Motarsu bata nufi ko'ina ba sai katafaren gate din Gidansa A harabar ajiye motocinsa sukayi parking, babu wanda yasan da zuwansu, da sauri Major ya fito ya zagaya ta baya ya buɗe masu mota, sir mubarak ne ya fara fitowa kafin Ya taimaka ma Dr jazz shima Ya fito, hannunshi ɗaya dafe da waist din shi. saboda baya iya tafiya dai dai, tun lokacin da sir mubarak ya cakumi rigarshi ya buga shi da ƙasa ƙafarshi ɗaya ta lanƙwashe daƙyar yake iya takata a yanzu.
A haka suka nufi cikin gidan, banda Major wanda tuni Ya nufi sauran ƴan uwanshi sojoji dake kai komo a cikin gidan. A zaune yake saman Sofa, ya ɗauki wankan dark jeans and white V-neck shirt kayan sun bi shape din jikinsa, hankalinshi a kwance yake operating laptop din gabansa dake ajiye kan table, Fitowa mom turai tayi daga cikin kitchen hannunta ruƙe da mugs guda biyu na coffee, ta nufi cikin falon fuskarta asake taje gaban table din Zaki ta ɗaura cup ɗaya "Ga wannan My son, Nasan zaka buƙace shi" ɗagowa yayi fuskarshi ɗauke da murmushi ya furta"mom nagode da kulawarki agareni, kina ji da ɗan nan naki" Kafin ta kuma cewa wani abu muryar ibad ta janyo hankulansu ga dubanshi, fitowarshi kenan daga cikin ɗaki Sai faman yin miƙa yake yi haɗi da yin hamma, daga shi sai short a jikin shi Muryarshi da shagwa6a ya furta"mommy nifa"? Zaki ne ya bashi amsa da cewa"Na ƙarfi ne zoka ƙwata, ɗan rainin wayau sai yanzu ka ga damar tashi daga baccin" Tur6une fuska yayi"babban yaya jiya fa bamuyi wani isasshen bacci ba, shine nake yin ramuwar na jiyan" Dariya mom turai tayi shagwa6ar ibad har mamaki take bata, duk da shima jazz idan abun ya motsa yana yi mata shagwa6a "Ranka zai 6aci ne idan ka ci gaba dayi min shagwa6a kamar wani ƙaramin yaro," Bubbuga ƙafafuwanshi yayi hada ruƙe qugunsa wato yayi sai dai ayanka shi Mom turai tace"sai fa kana haƙuri da shi, kasan autane kuma kai ka rainesa duk abun da yayi kai ne ka sangartar da shi" Ta6e baki Zaki yayi tare da kau da idonshi daga kan fuskar Ibad Ya miƙa hannu ya ɗauki mug Ya soma kur6ar coffee.. "last born zoka kar6i wannan" girgiza mata kai yayi"no mommy, na hannun shi nakeso yasha ya rage min, wannan nakine ki sha" a sukwane Zaki ya dakata da shan coffeen Ya waiwayo yana dubanshi, Ya rasa gane dalilin dayasa Ibad yake yi mashi haka, aduk lokacin da zai ci abu saiya sa rigima akan yaci ya rage mashi kamar wani tsaran wasan shi "Kada ka damu zan shiga kitchen in haɗa nawa, kai dai kar6i kasha" mom turai ce tayi maganar Ibad ya maƙe mata kafaɗa"mom ni ai nafison yasha ya rage min" Girgiza kai Zaki yayi tare da kallon mom turai yace"zan rage mashi" "Amma ai baida yawa taya zai isheku ku biyu abunda baifi rabin cup ba" "Idan bai ishe mu ba, zan turo shi ya ƙaro mana wani a kitchen" Gyaɗa kai tayi okey, Har ta nufi sofa zata zauna, sallamar sir mubarak ta katse mata hanzarinta, Kusan atare suka kai idanuwansu ga duban ƙofar falon Shigowa Sir mubarak yayi hannunshi dafe da dr jazz, tsabar firgice Yasa mom turai ta saki mug din hannunta gaba ɗaya ruwan coffeen Ya zube kan floor, Jikinta na 6ari ta nufe su, Hankalin kowan nan su ya tashi, zaki tuni ya dakata da shan coffeen a hanzarce ya miƙe ya nufi sir mubarak, Ibad kuwa hannayenshi biyu ya ɗaura saman kanshi yana ambaton"mun shiga uku, ɗan uwa Jazz meya same ka? Kayi hatsarin mota ne?
Muryar turai na rawa take fadin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, babe meya faru da jazz ɗina? idanuwanta har sun fara fitar da ƙwalla, Sir mubarak bai sauraresu ba, Ya nufi sofa da sauri zaki Ya taimaka mashi suka zaunar da jazz. A Hankali Ya ɗago Yana dubansu ɗaya bayan ɗaya kafin ya tsayar da idanuwanshi kan mom turai da tafara sharar ƙwalla, Jikinta asanyaye ta nufo su ta zauna gefen jazz ta ruƙo hannun shi acikin nata, "Kayi shiru bakace komai ba? Meya faru da jazz"? "Daddy kai muke sauraro," acewar Ibad wanda tuni ya dawo gefen ɗan uwanshi zaki ya tsaya hadi da ruƙe qugunshi A tsanake ya soma yi masu magana"ku kwantar da hankalinku....." tunkafin ya ƙarasa maganar, mom turai ta katse shi ta hanyar yi mashi tsawa tana fadin"taya zakace mu kwantar da hankalin mu? Yaro ya fita gida lafiyarshi qalau yanzu kuma ka dawo dashi goshi ɗaure da bandage ga tabonni akan fuskarshi, sannan babu kayan da ya fita da su a jikin shi, ni dama tun jiya hankalina bai kwanta da fitar jazz ba, babe ka faɗamin meya faru da yarona"!! idanuwanta azazzare tayi mashi maganar.
Tun da yake da turai bata ta6a gigin katse shi yana cikin yin magana ba sai yau, hakan ya ƙara tabbatar mashi da cewa ranta yakai maƙura a wurin 6aci, "Mommy, yaya zaki, Ibad" dr jazz ne ya ambaci sunayensu, a hanzarce suka kai dubansu gare shi.
"Zanyi maku bayanin komai" "A'a jazz shi nake so yayi min bayani, gaba daya a raunace kake, ka daina yin magana zaka fama ciwonka" ta faɗa tare da kallon sir mubarak wanda yayi shiru yana kallon fuskarta... "Meyasa ka tsareni da ido? Ba zaka yi min bayani ba"? Bai tanka mata ba har saida ya samu wuri saman sofa dake fuskantar su, Ya zauna, tukunna ya samu natsuwar yin masu bayanin komai daya faru....... A ƙarshe yace"bana buƙatar wani yaji abun nan saboda aikin sirri ne sukeyi, basu buƙatar kowa ya sani, Na faɗa maku ne don na wanke kaina daga zargin da zakuyi min na halin da na jefa jazz" Cikin sanyin murya turai tace"am sorry dear, nayi maka tsawa bisa rashin sani, kayi hakuri dan Allah, hankalina ne ba akwance ba" "Na fahimce ki," atakaice ya furta hakan Mayar da duban ta tayi akan jazz"dan Allah nan gaba kada ka ƙarayin wannan gangancin, duk wani abu da zakayi ka sanar da mahaifinka koda ace ni bazaka sanar min ba," amsa mata yayi da toh, Kafin ta juyo da dubanta kan sir mubarak"Babe, babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani dasu wurin yi maka godiya saboda irin kulawar da kake ba jazz....." kafin ta ƙare maganar sir mubarak yai hanzarin katseta"Kada na sake jin kinyi min godiya saboda nayiwa jazz abu, kinsan banaso" cikin sanyin murya tace"nadaina in sha Allah" "Daddy, sannu da dawowa, nayi missing dinka sosai, meyasa jiya baka faɗamin halin da kake aciki ba ai da nazo asibitin na tayaka jinya" zaki ne yayi maganar yayin da yake ƙoƙarin zama gefen jazz Murmushi sir mubarak ya sakar mashi"sanyin idaniyata, ina fata na same ku lafiya"? Mayar mashi da martanin murmushin Zaki yayi"lafiyalou, sai dai jiya dukkanmu bamu runtsa ba saboda rashin ganinku da bamuyi ba" Sir mubarak yace"shiyasa naga idanuwanku sun kumbura, ashe bani kadai na kwana azaune ba" Tun da suka fara magana ibad ya haɗe ranshi, "Daddy ni baka ganni bane"? Ya faɗa yana duban sir mubarak Girgiza kai ya ɗanyi kafin yace"naganka ibad, amma nida kai wanene ya dace ya fara gaishe da wani? Yamutsa fuskarshi yayi ƙasa ƙasa da murya ya furta"sannu da dawowa dad" ta6e baki sir mubarak yayi saida na roƙa, bubbuga ƙafa ibad yayi Mom turai tace"mu shiga ciki, in taimaka maka kayi wanka" zaro ido Ibad yayi haɗi da furta"Mom wa zaki ma wanka? Jazz ko daddy"? Duk da halin da suke aciki na damuwa hakan bai hanasu yin dariya ba, shi kanshi jazz din saida ya murmusa, "Daddynku nake magana akai," hannu biyu yasa ya toshe bakinshi, Idan ya kalli sir mubarak sai ya kalli mom turai Ko kaɗan batajin kunyar ƴa'ƴanshi, saboda ita aganinta bawani abu bane donta furta hakan agabansu. "My son, zamu shiga" Zaki yace"okey, zan tafi da jazz ɗaki, zan taimaka mashi yayi wanka ya canza kayan jikinshi' "Hakan yayi," ta faɗa tare da duban Ibad Har yanzu mamaki bai sake shi ba, sai kace baiyi rayuwa a turai ba. "Akwai kayan abinci dana shirya mana a kitchen, ka shiga ka dauko su a dining zaka jera" Amsa mata yayi da toh, da sauri ya juya ya nufi hanyar kitchen Miƙewa zaki yayi tare da ruƙo jazz ya miƙar dashi, "Allah ya baka lafiya my jazz," amsa mata yayi da ameen, kafin suka nufi ɗakin shi Bayan tafiyarsu ta dubi sir mubarak"ina ƙara baka hakuri, kasan ba halina bane" Murmushi yasakar mata"kada hakan ya dame ki, ni dama fargabana halin da zaki shiga, but Alhamdulillah tun da kin fahince ni, yanzu bani da sauran damuwa" Ya faɗa tare da ruƙo hannunta suka nufi bedroom dinshi "Jiya nayi kewarka, idanuwana sunyi maraicin ganinka, dole na haƙura na rungume pillow amadadinka" tayi maganar ayayin da take taimaka mashi wurin cire Rigar jikinshi Daɗaɗan kalamanta ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya sukeyi ba, shiyasa akoda yaushe yake ƙara jin sonta, saboda ƙaunar da take nuna mashi, tun farkon auransu bata ta6a barin ya shiga toilet yin wanka shi kadaiba sai idan wani uzirinne mai ƙarfi ya hanasu shiga atare, sannan ta hana ya ajiye mata masu aiki agida ba yadda baiyi da ita ba akan baison tanayin aikin wahala amma taƙiya saboda kishinshi da take yi, batason wata ta ƙwace mata mijinta, Atare suka shiga toilet.
*ANEELERH❤🔥*
Tun bayan da ta shiga toilet tabar Zahra atsaye tana kallon hoton su, lokacin da ta fito daga wanka bata taras da zahra a dakinta ba, shaf shaf ta shirya kanta cikin shiga ta abaya maroon colour, ta yafa mayafi akanta, fitowa tayi daga dakin a dining room ta taras da su gaba ɗaya sun hallara kan dining chairs, tun daga kan abie dinta, uncle ɗan iya, mami da ummi da kuma mahboob, sai zahra kaf dinsu ne, kowa ya kimtsa domin yin ɗa'amin, Ana ce take yin serving dinsu tana daga tsaye hannunta ruƙe da serving spoon. Sautin takun takalmantane Yaja hankulansu ga dubanta, fuskarta da fara ta ƙarasa cikin girmamawa ta soma gaishe da iyayenta "Barka da safiya, ina kwananku, kun tashi lafiya" Fuskokinsu asake suka amsa mata. Mahboob Yace"Gm Auntyna, bismillah zoki zauna gefena" ya faɗa yana nuna mata empty chair din dake gefenshi Zahra dake kallonsu, murmushi tasaki ganin yadda mahboob Yake yima Aneelerh fadanci abunda bai saba Yi ba. Bayan Aneelerh ta zauna, Ana ta gaishe da ita, a mutunce ta amsa mata"two days bana ganin ki, kin 6oye min sai kace ba gida ɗaya muke a zaune ba, sai dai idan ni na matsu da son ganinki in shiga kitchen time da kike Yin girki ko"? Sunnar dakai ƙasa Ana tayi yanayin fuskarta babu walwala, Mami tace"Ai ba tun yauba na lura halinta ne batasan sakewa cikin mutane, kullum kina ƙumshe daga kitchen sai ɗaki, yakamata kina fitowa falo muna yin fira dake" cikin kulawa mami tayi maganar. Cikin sanyin murya ta furta"ay min afwa zan dinga futowa daga yanzu" Mami tace"haka nakeson ji, ki daina daukar kanki a matsayin ƴar aiki, damu dake duk abu ɗayane awurin Allah, so please adaina kuntata kai adaki" murmushi Ana tadan saki har cikin ranta taji dadin maganar mami, zahra tace"idan ma bata fitoba ni dakaina zan dinga zuwa dakinta ina takura mata da surutu" dariya Ana tasaki, ummi tace"dako ta shiga uku dake, har bacci sai kin hanata saboda zafin ɗuminki" tur6une fuska zahra tayi, jin abun da ummi tace, harara ummi ta jafa mata"lafiya kike kallona, ko nayi maki ƙaryane? Kafin zahra tayi magana mahboob yace"wallahi ummi gaskiya kika faɗi" yai maganar yana kokarin tura chips abakin shi"Zahra badai ɗumiba, kamar aku, inta fara zuba kamar radio mai jini, ga tambayar tsiya kamar tsohuwar ƴar jarida" gaba ɗayansu suka sanya dariya, ran zahra ya 6aci a ƙule tace"hmmm mahboob ai ƙwarani, wai talla zaiwa audi gori, idan ni surutu gare ni kai fa? Saboda shegen maƙonka ko kuɗi zaka ƙirga sai ka shiga toilet don kada wani ya gani" dariya su ka yi, Abie Da uncle ɗan Iya sun kasa kunne suna sauraran su, ganin surutun nasu bame ƙarewa bane yasa uncle dan Iya yi masu gyaran murya hankalinsu ya dawo kanshi"surutun Ya isa haka, kun cika mana kunne, Yakamata ku maida hankalinku akan abun da ku ke ci, kun riga da kunsan babu kyau ana cin abinci ana surutu" tunda ya ambaci hakan kowan nan su yaja baki yayi shiru, baka jin sautin komai saina cokulansu kwas kwas tamkar zasu fasa plates din abincinsu, gaba daya hankalin Mahboob dana Aneelerh yana akan Ana, ga dukkan alamu sun fahimci babu lafiya atattare da ita, tun daga kan yadda take faman zazzare idanuwanta.
Cup din lemu Aneelerh ta dauka takai baki tana kur6arshi, bayan ta kammala sha tace"ki koma ɗaki ki zauna ki hutu" ta fada tana duban Ana "Inaso ne ku kammala cin abinci in kwashe kayan, akwai sauran aiki da zanyi wanke wanke da gyaran kitchen idan na kammala sai in huta"
Aneelerh tace"kada ki damu zanyi maki aikin, just ki tafi ɗaki ki huta"