Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 - Chapter 74
Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 74: Kurkukun ‘kaddara (the prisoners) book 2 Chapter 74. Harta buɗe baki zata kuma yin magana mahboob ya…
3,073 words
Harta buɗe baki zata kuma yin magana mahboob ya tari numfashinta da cewa"Sis Ana, kiyi abunda aunty Aneelerh ta fada maki, nima zan tayata yin aikin" Gyaɗa kai Ana tayi cikin sanyin murya ta furta"nagode madam, Mahboob thank u" ta fada tare da juyawa ta nufi bedroom dinta da sauri, hatta yanayin tafiyarta babu natsuwa. Kallon juna Aneeelerh da mahboob sukayi, da ido tayi mashi nuni dayabi bayan Ana yaji masu meke damunta. Jinjina mata kai yai alamar toh, miƙewa yayi daga kan kujerarsa yakai hannu ya yago tissue Ya goge bakinsa. "mahboob harka kammala cin abincin"? Uncle ɗan Iya ne ya jefa mashi tambayar. "Ban ƙoshi ba daddy, ina son zan shiga toilet ne uziri gare ni" uncle ya amsa mashi da okey. Da sauri Ya juya yabar dining area din, Kasancewar Bedroom dinsa dana ana a 6angare daya suke shiyasa yai ƙaryar cewa toilet zai shiga. Tunkafin mahboob Ya shiga ɗakinta ya soma jiyo shessheƙar kukanta, Hankalinshi yayi mugun tashi, koda ya ruƙo handle din ƙofar room din nata adatse ya Ji ta, muryarshi ƙasa ƙasa Ya ambaci sunanta shiru bata amsa mashi ba, knocking kofar yayi"sis ana ki buɗe min ƙofa dan Allah, Inason yin magana dake, Aunty Aneelerh ce ta aiko ni" Jin ya ambaci sunan aunty aneelerh yasa tayi saurin shiga toilet ta wanko fuskarta, jiki na rawa tazo gaban ƙofar ta buɗe mashi ita. Ajiyar zuciya ya sauke yana bin fuskarta da kallo, idanuwanta sun kaɗa jawur da su. Ruƙo hannunta yai acikin nashi kamar wani babban mutun Yajata zuwa cikin dakin, Ya kulle ƙofar. Tare da goya hannayensa saman ƙirjinsa Yana kallon fuskarta Ganin ya tsareta da ido yaƙi yin magana ne yasa tace"mahboob lafiya kake kallona? Me aunty Aneelerh tace ka fada min" Numfashi yaja kafin ya soma yi mata magana "Meke damunki? daga ni har aunty Aneelerh mun fahimci bakya jin daɗi kamar akwai wani abu dake damunki" Adabarbarce ta furta"babu komai mahboob lafiyata qalou...." "Bazai yiwu ba Ana, saboda kafin na shigo ɗakin ki na jiyo sautin shessheƙar kukanki, taya zakice min bakomai? Bayan ga alamu nan nagani akan fuskarki, dan Allah Ana kada ki 6oye mana abunda ke damunki, kinga mun damu dake ni da aunty aneelerh dama sauran mutanan gidan"? A marairaice mahboob yayi mata maganar Baiwar Allah tayi zuru da ido, komai nata ya canza. Ƙoƙarin danne damuwarta tayi hawayen da suka taru acikin idonta tayi saurin mayar da su. Can ƙasan makoshi sound din muryarta ke fita
"Dagaske nake yi maka mahboob, babu abun da ke damuna, idan ma saboda shessheƙar kukan da kaji ina yi ne to ka kwantar da hankalinka, sister dina ce janet ta kirani awaya tana fadin halin da take aciki Na rashin kuɗin da zatayi amfani dasu, gashi bata da koshin lafiya ko aikin da take zuwa yi a hotel yanzu komai ya ta6ar6are mata, idan ba zaka mantaba na ta6a baka labarin ƴan uwana Janet da esther, har na fada maka cewa mu marayune bamu da kowa neman na kanmu muke Yi, A halin yanzu dai nice nake taimaka masu da kuɗin da suke siyan abinci da suturar sanyawarsu, nima idan natara kudin albashina ne nake samun wanda nake tura masu.....
tunda tafara magana jikin mahboob yai sanyi, tausayinta duk ya kama shi, har cikin ranshi ya yarda da abunda ta faɗa mashi. "kinsan da abun da ke faruwa da ƴan uwanki shine baki faɗa mana ba? Meyasa? Meya amfanin zaman taren Ana"? Fashe mashi tayi da kuka tana fadin"bana so ne na takura maku, shiyasa ban fada maku ba" Dafe kai mahboob yayi dahannu ɗaya ranshi ya 6aci afadace yace"kin ban mamaki yanzu ko aunty aneelerh baki Iya faɗama damuwarki ita da ta dauke ki tamkar jininta, gaskiya ni baki kyauta min ba Ana, banyi zaton hakan daga gare ki ba, ashe baki daukemu kamar yadda muka dauke ki ba" Ruƙo hannayenshi tayi acikin nata yayin da hawaye ke fita akan fuskarta tace"mahboob am sorry, idan ranka ya 6aci" Ta6e mata baki yayi"Ni zanje na fada ma aunty aneelerh halin da ƴar uwarki take aciki, nasan zata taimaka maki, Nima zanyi kokarin baki wani abu, ki cika, itama zahra zan mata magana, sai mu haɗa maki kudin da zaki tura masu ......" Godiya ta soma yi mashi "Nagode mahboob, naji dadin taimakon da zaka yi min" Sakin fuskarshi yadanyi"dan Allah daga yau ki daina sanya damuwa aranki, ni nafiso in ganki cikin kwanciyar hankali, fuskarki da annuri, idan ma wani abu na damunki, please ki runƙa sanar dani, zan taimaka maki da abun nake dashi, ga kuma aunty aneelerh itama ki dinga fada mata damuwarki" "Zanyi hakan mahboob nagode da kulawarku agareni" Sai da mahboob ya tabbatar ya sanyata farin ciki, kafin Ya fito daga dakin Ya nufi dining area Koda ya ƙarasa bai taras da Aneeleerh da zahra ba, Har sun kammala yin breakfast dinsu, daga can falo Ya hango mami da ummi, zaune suna fira tare da Uncle ɗan Iya da abie. Hatta kayan abincin an kwashe su daga dinning, harya juya zai nufi dakin Aneelerh ta wutsiyar idonshi Ya hango gifcinta a kitchen, da sauri Ya nufi kitchen tun kafin Ya ƙarasa ya jiyo muryar zahra ta zaƙe tana ba Aneelerh labarin shagalin birthday din obie da akayi, maimakon Ya shiga sai ya la6e gefe daya ya kasa kunne Yana sauraronsu.
Babu wanda ya lura dashi acikinsu saboda sun bashi baya. Aneelerh tana gaban Sink Ta tattara kwanukan da suka 6ata tana wankesu, zahra tana agefenta "Aunty Aneelerh ina baki labari, wallahi Anyi 6arin dollar a wurin nan, dangin obie sun gaji arziƙi gaba da baya, wai kinga manya manyan mutanan da suka halarta? Attajiran masu kuɗi masu manyan muƙamai, kowa kika gani a filin taron da matsayinsa, daga governor sai president, ga sanatoci da ministoci......" Murmushi Aneelerh tasaki tana fadin"Gaskiya naji takaici da ban biki munje taron nan ba, da nima na kashe kwarkwatar idanuwana" "Aunty Aneelerh duk yadda zan baki labari bazan iya fada maki kwatankwacin abun da idanuwana suka gane min ba, nifa lokacin da ƴa'ƴan baba obie suka fito tsakiyar fili sunayi mashi liƙi Yana taka rawa wallahi ji nayi kamar inyi wuff in shiga filin in tattara kuɗin in saƙe a hammata" Tuntsirewa aneelerh tayi da dariya tana duban zahra, hada kwatanta mata yadda zata kwashe kudin ta saƙe ahammata.
Mahboob dake a la6e yana sauraron su dariya ce kumshe abakinshi.
"Ni abun da yafi burge ni, haɗuwar ƴa'ƴan baba obie da jikokinsa, da surukansa sun ɗauki wanka na mutunci na kece raini kai komai ma sun haɗa, waɗanda suka fi burgeni kinga prime minister Hateem, da president dinmu Sharafudeen sun iya dattako, komai nasu da aji suke yin shi, matayensu sunfi kowa haduwa gimbiya mujeedat da Hajiya malikat sarauta, sai kuma mutuniyata Hajiya saratu inayin matarnan saboda tana ƙaunata mutane suna fadin masifarta ni wallahi bata ta6a yi min koda tsawa ba kamar ƴar cikinta haka take yi min magana...." da farin ciki akan fuskarta tayi maganar.
Aneelerh tace"Jinin ku Ya haɗune dana juna, Allah yasa ta zama surukarki kinga shikenan kema zaki samu matsugunni a obie estate" wani irin ihun farin ciki zahra tasaki hada jujjuya qugu tana fadin"Amen Ya Allah, Aunty Aneelerh Allah ya kar6i addu'arki"
Dariya Aneelerh tasaki yayin da take ɗauraye plates din da take wanke wa da ruwan dake fita a faucet.
"Zahra baki faɗamin haduwarki da mutumin ba"? Kwa6e fuska zahra tayi annurin fuskarta ya ragu.
"Bai zo taron ba, duk irin burin dana ci nason ganinshi bai halarta ba, banji dadi ba dama nasan zai yi wuya yaje saboda mutunne shi da baisan hayaniya"
"Eyyah zahra najiye maki baƙin ciki, in sha Allah wata rana zaku haɗu da shi"
Ta6e baki tayi"Ni yanzu ba wannan ba auntyna, Inataso in baki labarin Nazli da Yazrin Ƴa'ƴan Prime minister da ƙanwar Chief Owais hindu, kinga waɗannan dana lissafa maki ƙarshene su afagen kyau da aji, cikin maza kuwa in ka cire chief owais sai wani ɗan uwansu menene ma sunanshi....." ta faɗa tana cizon yatsa takasa tuna sunan.
"Namanta, shima a canada yake zaune, mutumin ya iya ɗaukar wanka, ga kyau da aji bayan shi sai twins sun haɗuwa sunyi kyau kamar dollars.
Dariya Aneelerh tayi, jin yadda zahra ta haƙiƙance tana bata labari ko gajiya batayi. "Yanzu faɗa min alherin da sukayi maki naji ɗazu kince zaki fada min" Gyara tsayuwa zahra tayi kafin tace "Kinga da farko Hajiya saratu tayi min kyautar tsadadden leshi guda biyu, da hand bag, hada set na agogo da zobe, da turarurruka......" jinjina kai Aneelerh ta yi tana fadin"masha Allah, zahra najiye maki daɗi, kin samu na sallah"
"Bangama fada maki ba, bayan kuɗin aikin decoration da hajiya saratu ta biyamu, prime minsiter yayi mana kyautar kuɗi duk mutun ɗaya 1.5 million" waro ido waje Aneelerh tayi mahboob dake la6e jin an ambaci kuɗi sai gashi ya dawo gefen zahra Yana raira waƙa.
"In rabo ya tsago dakai kuma abun ya tabbatar saida kai to rabbine yace sai da kai in sai da kai kawai sai da kai, don haka nima Allah ne ya tsaga da rabona ashe arziƙine ke kirana......" gaba ɗaya suka sanya dariya, Aneelerh tace"mahboob yaushe ka shigo kitchen din nan"
Da murmushi akan fuskarshi yace"tun ɗazu ina la6e bakin ƙofa na kasa kunne ina sauraron aku sarkin ɗumi, yau surutun zahra yayi min rana wannan arziƙi haka, wato saboda baƙin ciki zahra ƙiri ƙiri kika hana in rakaki obie estate da yanzu hadani za'ayi rabon kuɗin nan...."
Dariya zara tayi tana fadin"ai baka ji komai ba, bayan kuɗin da prime minister yabamu, president Ya ƙara mana, duk mutun ɗaya dubu ɗari takwas" dafe ƙirji mahboob yayi kamar wanda yaji wani mugun abun "Sannan Abokin Baba Obie, Jan kunne ya raba mana dubu ɗari biyar biyar da dollar ya bamu su" Kallon juna mahboob da Aneelerh su kayi. "Anya zahra dagaske kike kuwa? Wannan kuɗi haka kamar akan bishiya ake tsunkosu"
Hararar shi zahra tayi"an gaya maka kowa mai maƙone irinka, ai su a wurinsu kuɗin da suka bamu bakomai bane"
Jinjina kai mahboob yayi"Allahumma arzuƙni, Sister Yanzu ina kuɗin suke? inaso zan tayaki ƙirgawa"
Dariyar shaƙiyanci zahra tayi kafin tace"suna kwance cikin account bank dina suna bacci, dollar din da aka ba mu ne kaɗai suke a dakina kuma na 6oye su saboda nasan halinka sarai, tsaf zaka Iya zuwa ɗaki yi min halin 6era"
Dariya Aneelerh tasaki, a lokacin ta kammala yin wanke wanken, ta mayar da hankali akan fuskar zahra Mahboob Yace"kar dai kice zakiyi min rashin mutunci wallahi sai inyi zuciya inje in nemi auran ɗaya daga cikin jikokin baba obie"
Dariya suka saki gaba dayansu bayan sun tsagaita Aneelerh ta dubi mahboob"Ya ake ciki? Kunyi magana da Ana"? Ɗaga mata kai yai alamar eh, zahra tace me ya faru ne ko bata da lafiya"
Nan mahboob Ya kwashe komai Ya sanar dasu dangane da halin da Ana take aciki.
Shiru sukayi jikin kowa yayi sanyi, musamman Aneelerh, ranta Ya dan 6aci bata ji dadin ƙin gaya matan da tayi ba.
"Idan kuwa hakana Ana bata kyauta min ba,Yanzu har akwai abunda zata 6oye min duk irin shaƙuwar dake atsakanin mu?"
"Aunty Aneelerh please kada ranki ya 6aci, na riga da nayi mata faɗa, abun da ya dace ku harhaɗa mata kudin da zata turama ƴan uwan nata"
Zahra sarkin tausayi tace"nida da halima wallahi da sun dawo gidan nan da zama....." wata uwar harara Mahboob Ya watsa mata"saboda ke zaki ciyar dasu ko"? Fashewa sukayi da dariya. Aneelerh tace'baka da dama mahboob, yanzu fa ka gama fadin a harhada mata kudi aturawa ƴan uwanta shine kuma don tace su dawo nan da zama kake tada jijiyoyin wuya daga maganar taimako"
Yamutsa fuska mahboob yayi"abun da nake nufi Aunty Aneelerh, ɗan adam ba abun yarda bane, muna iya mu taimake su su kuma su butulce mana shine abunda nake jiye mana, kawai dai ƙwara in taimakon zamuyi masu mu tura masu can su ƙarata"
"Ka faɗi gaskiya mahboob, nima nayi wannan tunanin, Yanzu me yakamata muyi"? Acewar Aneelerh.
Zahra tayi karaf ta kar6e dacewa"kowa ya kawo abunda yake dashi hada kai mahboob nakama sai yafi yawa tunda kaine jagaba atafiyar"
Harararta yayi"zahra ki daina wannan maganar, ni bawai bazan bada ba, idan na bada ai ba faduwa nayi ba, duk wanda ya taimaki wani shima Allah zai ji ƙansa, ga lada da mutun zai samu, kawai dai ni bani da kuɗinne Yanzu....." ya fada yana soso keyarshi. da zolaya zahra tace"hmmm, Ana fa ba musulma bace, ta ina zamu samu lada idan muka taimake ta"? Banza yayi da ita baice komai ba, Aneelerh tace"babu ruwanmu da wannan, don Allah zamuyi da kyakkyawar niya, kidaina wannan tunanin" gyaɗa kai zahra tayi"shikenan naji, zan bata wani abu cikin kuɗin dana samu, Mahboob Idan kana da acct number dinta ka tura min" Aneelerh tace"Ina da ita, Idan muka koma ɗaki zan tura maki, Nima zan sanya nawa kudin" Farin ciki ne tsantsa akan fuskar mahboob, Yaji daɗi zasu taimaki Ana batare da ko sisin shi ba. "Allah yabarmun ku sisters dina, zahra Allah ya baki miji nagari mai sonki mai ƙaunarki, and aunty Aneelerh ubangiji Allah ya bayyanar mana da mijinki da ƴan uwansa , Allah ya raya mana baby junaid dinmu...." addu'o'i yadinga yi masu suna amsa mashi da ameen, kafin Ya juya zai fuce daga kitchen din "Mahboob" kiran sunanshi da Aneelerh tayine ya dakatar da shi daga yin tafiyar ya waiwayo yana kallonta "Please idan ka fita ka faɗama su mami, zuwa anjima Hajiya adama zata zo kawo mana baby junaid nasan bata sanar da ita ba"
"Aunty Aneelerh ashe yau muna da babban baƙo agidan namu, mutumina zai dawo, zamu dasa daga inda muka tsaya"
Murmushi Aneelerh tasaki, zahra tace"wallahi har na kosa in ganshi,Yau zaisha daƙuna duk saina sale mashi fatarshi" Aneelerh na murmushi tace"inaso zamu shirya masu abincin da zasu ci, tun da Ana bata jin dadin zuciyarta mubarta ta huta sai muyi aikin atare"
Zahra tace"Lafiyalou, dama na kwana biyu banyi girki ba, har cake zan haɗama baby junaid dina"
Sun jima suna yin fira a kitchen kafin daga bisani suka fuce zuwa ɗakin domin yin sallar azhar da aka fara kira.
*OBIE ESTATE🌃*
Idan muka koma 6angaren dattijon arziƙi, tunda garin Allah ya waye Hankalinshi ba akwance Yake ba, gaba ɗaya yabi ya furgice masu sun rasa gane kanshi, ko jiya da dare bai runtsa ba, sambatu yadinga yi masu yana firgita yana fadin ga macijij nan zai sare shi, Ina owais dinshi Yana gani za'a cutar da shi bazai kashe macijin ba, mutun biyu da suka taya shi kwana a ɗaki his excellency Deen ne tare da His excellency abdul razak, su kansu basu yi bacciba jiya saboda halin da baban nasu yake aciki, hatta sallar asuba agida sukayi ta yaƙi fita daga ɗaki, kuma ya hana su tafi subarshi, bawan Allah ba ƙaramin jiki yaji ba, hada ruɗun tsufa ke damun shi, daƙyar suka samu nasarar sanya shi yin baccin dole.
A yanzu haka Yana daga kwance saman gadonshi Ya ɗaura kanshi kan pillow, deen da Abdul razak suna a zaune saman arm chairs din dakin idanuwansu akan fuskar baba obie. Jin motsin buɗe kofane Yaja hankalinsu ga kallon mai shigowa Senate lateef ne, fuskarshi babu walwala. Daren jiya da damuwar abunda ya faru ya kwana Miƙa masu hannu yai suka gaisa da ƴan uwan nashi Kafin ya dubi baban nasu dake kwance kan gado yace"Bacci yake yi ko idon shi biyu"? His excellency Deen ne yace"bacci yake yi, daƙyar muka samu Ya runtsa" ajiyar zuciya senate lateef ya sauke kafin yace"banji dadin abunda ya faru jiya ba, gashi har yana neman zautar mana da mahaifinmu, wai taya ma akai har maciji ya shigo part din nan"? Rai amatuƙar 6ace yayi maganar His excellency Abdul razak Yace"abun da yafi ɗaura min kai shi Owais din Yace ba maciji bane mutunne ya rikiɗa...."tunkan Ya ƙare maganar Senate lateef yace"inko dagaske ne wannan maganar to kuwa ba mutun bane dama, Aljani ne sannan ita wannan ifritun yarinyar mai kasada dana gani atare da shi wacece ita!"? Kafin wani ya bashi amsa sallamar Pravin ta katse masu hanzarinsu, Shigowa yai cikin shiga ta black suit.
Cikin girmamawa pravin ya gaishe da su, bayan sun amsa masu fuskokinsu babu walwala, pravin ya soma yin magana "Baba bashi da lafiya ne? naga da asuba bai halarcin masallaci ba" "Baka ga abun da ya faru jiya bane"? Acewar senate lateef.
"Nagani, kar dai ace shi ne ya hana shi sukuni"? Cikin nuna kulawa yayi maganar.
His excellency abdul razak Yace"ai kuwa dai shine, don jiya ko bacci baiyi ba tsabar firgici, yanzu haka ma da kake ganin shi a kwance daƙyar muka samu yayi bacci' "Abu baiyi daɗi ba" pravin ya faɗa yana ɗan girgiza kanshi"ubangiji Allah ya bashi lafiya" atare suka amsa mashi da Ameen. Senate lateef ya ɗaura da cewa"ni yanzu so nake naji daga bakin shi Owais, ya faɗa min wanene macijin menene alaƙar shi dashi" "Bari na kira shi awaya, ai jiya yace zai shigo yai mana bayani amma shiru kake ji wai malam yaci shiru" Deen ne yai maganar tare da curo wayarshi daga aljihu ya danna ma Chif Owais Kira, kusan sau uku tana yin ringing bai yi picking ba.
"Bai ɗaga ba, may be baya akusane da wayar" ya fada yana kokarin maida wayar cikin aljihun, kwatsam kiran owais ya shigo wayar tafara ruri, ajiyar zuciya ya sauke tare da duban su yace"shi ne ke kira," ya fada tare da yin picking din kiran Ya kara wayar a kunnanshi, bayan sun gaisa deen yace"muna ta tsammanin zuwanka gida shiru baka shigo ba, ga babanku nan kwance ba lafiya saboda abun da ya faru jiya ko runtsawa baiyi ba sai firgita yake yi".
On the other hand chief Owais ya furta"I will come later, insha'Allah,"
"Okay, we'll be waiting for you, sannan inason sanin Ina macijin nan yake? Naji kace mutunne" Muryar chief owais tamkar bai son furta maganar yace"please uncle can i text you" deen yace okey ba damuwa", rejecting call din yayi, kafin wani ya furta magana ƙarar shigowar saƙo Ya dakatar da su.
Karanta sakon Deen ya soma yi duk sun ƙura mashi ido suna jiran jin me zaice masu, musamman pravin har wani zoƙa kai yake yi yana leƙen wayar Deen.
Ɗagowa yai da alamun mamaki akan fuskarshi yace"tabɗijancan, wallahi dagaske macijin mutunne wai shaidanun aljanune a jikinshi, yanzu haka ya rikiɗa ya koma mutun acan gidanshi yake zaune,........" aruɗe suke kallon shi.