Kenza eBookz

Kwai cikin kaya book 2 complete - Chapter 32

Kwai cikin kaya book 2 complete - Chapter 32

Kwai cikin kaya book 2 complete Chapter 32: Kwai cikin kaya book 2 complete Chapter 32. dai bai taɓa ce mata yana son nata ba, ɗagowa tai da nufin satar…

4,345 words

dai bai taɓa ce mata yana son nata ba, ɗagowa tai da nufin satar kallonsa sai suka haɗa ido, dan shima kallonta yake ƙasa-ƙasa idanu a narke. Cike da salo ya wani ɗagemin girarsa ɗaya, maida kaina nai ƙasa zuciyata na motsawa. Ban sake gigin kallon sashen da yakeba nima na maida hankalina ga kallon mawaƙa da suketa baje fasaharsu cikin daɗaɗan waƙoƙi da duk an raira baitocinsune da sunayenmu. Umar m shariff, Ado gwanja, Nura m inuwa, Naziru Ahmad, Hamisu breaker, Isa ayagi, Abdul D one, kai abunfa ba'a magana, ƴan uwa da ƙawaye da abokan ango nata casar rawa, duk yanda mc keta magiya da roƙon amarya da ango su fito filin rawa ya hanani ko motsi, duk wanda ke buƙatar mana liƙi sai daifa yazo nan inda muke zaune ya liƙa mana ɗin, amma ko sau ɗaya bamu shiga filin rawarba. Lokacin da Anum da Nabeelah suka hawo domin yima su Jay liƙi ba ƙaramin faɗuwa gabansa yayiba, itama ɗin dai sai da ta ɗora hannunta a ƙirji alamar gaban nata faɗuwar ya keyi, dama tun sanda su bilkisu suka shigo saida gabanta ya faɗi, jikinta a sanyaye ta liƙa masa kuɗin shi da bilyn suka sauka ko jin surutun da Nabeelah keyi bataiba. Duk bilkisu na kula da yanayin da boss da Anum ɗin suka shiga, dan harta sauka yana binta da kallone. Tun ɗazun nake wuwwula idanu ko zanga Yah Anuwar, haka kawai nakeji a raina bana son su haɗu da boss yanzu anan, to bammaga su Abdur-raheem bama. Da hannu na yafito Anum, ta taso zuwa gareni. Cikin magana ƙasa-ƙasa nace, “Ina Yah Anuwar?”. Tace, “Tab aishi bayason bidi'a, da wahala idan zaizo wajen nan, amma bakiga yanda mijinki ke kama da Yah Anuwar ba? Nifa dana kallesa gabana sai ya faɗi wlhy bilkisu”. Murmushi na mata da cewa, “Karki damu zamuyi magana amma ba anan ba”. Kanta ta ɗagamin ta koma wajen zamanta. Ina kallon irin kallon tuhumar da boss kemin nai kamar ban ganiba, dan rashin zuwar Anuwat ɗin yasa naji hankalina ya kwanta. An buƙaci mu fito domin yanka cake. Ganin bai motsaba nima nai zamana, Ina jiyo fitar guntun tsakinsa alamar bayason yi, ni kaina bason nakeba, dan duk a takure nake matuƙa. Sai da Jabeer yazo yayta roƙonsa da ƙyar ya amince muka miƙe zuwa gaban cake ɗin da yay masifar ƙyau. Mun yanka cake tamkar yanda tsarin yake, ni na fara cira ɗan guntu da zan saka masa a baki cike da jin matsananciyar kunya, dan da ƙyar na iya control ɗin tsumar da jikina keyi nakai hannuna bakinsa, hannun nawa ya riƙe shima muka saka masa gaba ɗaya wanda na ciroɗin kasancewar ɗan ƙaramine a baki. Ina ƙoƙarin janye hannun ya maidashi cikin bakinsa ya tsotse yatsun biyu dana ɗauki cake ɗin dasu suka ɗan ɓaci kaɗan. tafi hall ɗin ya ɗauka. Jinai tamkar na nutse dan kunya. Shi kam Maimakon ya ciro ya bani kamar yanda nai masa sai ya lakato ya samin a saman hanci kawai dan wulaƙanci, ban gama fita daga takaicin salon nasaba naji saukar numfashinsa kan fuskata, kafin na sami damar magana ya lashe wanda ya lakatamin ɗin da bakinsa. tafin yanzun kam har yafi na ɗazu, dan yanzu harda waƙar Ali jita aka sake saki ta Bilkisu gimbiya. Ƙasa nai niyyar duƙewa dan kunya yay azamar riƙoni jikinsa, sai kawai na ɗora kaina saman ƙirjinsa ina sakin murmushin jin kunya, shima ya ɗaura hannunsa ɗaya saman bayana yana ɗan bubbugawa. Da ƙyar mc ya samu hayaniyar ta lafa, zamu koma wajen zamanmu aka dakatar damu. Jabeer ya fara bayani kamar haka.... “To jama'a kowa sai ya buɗe idanu domin dai zamuga wasan manya ne, kunsan daga amaryar har angon jarumaine a filin daga”. Ya nuna bindigu guda biyu dake saman wani table duk an buɗesu, “Kuna dai ganin bindiga guda biyu ajiye ko? To munason ango da amarya su haɗasu cikin minti ɗaya yanda suke, wanda ya fara gamawa yana da ƙyauta ta musamman”. Ni abinma dariya ya bani, hakan yasa naɗan murmusa, batare da tunanin zanyi nasaraba muka ƙarasa, sai da oga Jabeer ya irga uku sannan duk muka fara ƙoƙarin haɗawar cikin hanzari, ina kammalawa nai saurin ɗagowa na nunasa da bindigar fuskata a ɗaure, dai-dai da shima ya nunani data hannunsa fusakarsa babu wasa. . Wani irin ihu hall ɗin ya ɗauka da tafi. Murmushi ya saki tare da tanƙwa

ɓe hannuna bindigar tai ƙasa ya caɓe cikin hannunsa, nai ƙasa da kaina ina murmushin nima dan naji kunya. Duk da kusan tare muka gama ni aka bama ƙyautar dai dan nina fara nunasa da bindigar, wajen zamanmu muka koma, muna zama mc ya fara sanar da babban saƙo daga ƙannen ango na musamman Princes, sunce a basu wannan filin su kaɗai, dan ga waƙa ta musamman daga garesu da suka tanada domin amarya da ango. tsit hall ɗin yayi kowa ya buɗe kunne yaji ya kuma ga waɗanan ƙannen ango na musman da kowa ke ƙyautata zaton ƴaƴane daga masarauta. Matasan samari masu ji da jini a jika da wautar ƙuruciya, Abdul-Raheem, Abdur-rahman, Ameen, suka miƙe, dan da gaske Anuwar bai zoba (su ustazu🤐 lol). sunsha ƙyau harsun gaji cikin shadda kalar sararin samaniya, kansu tsaye mazaunin ango da amarya suka nufa, yayinda Hamisu breaker ya miƙe ya fara raira musu waƙar........ Ashe da rai yake sanki jaruma bada zuciyatai ba, komai ruwa da iska akanki jay baza ya daina kewa ba, tunda dai ya samu zarrar samunki baza ya tanka kowaba, shi baiga mai hararaba, balle ya waiwaya baya. Indai a kankine zaya jure wahalar zuwa garin nisa, da an taɓaki ajirasa danko tilas yazo ya ɗau fansa..........

(Man kaina ya tsiyaye dole mukoma wajen breaker ya ƙarisa🚶🏻😫)

Breaker na fara raira waka sukuma suka farke ƴan dubu-dubu suka fara zubama Jay da bily liƙi, gaba ɗaya hall ɗin ya yamutse da hayaniya, masu ɗaukar video nayi a waya masu hotuna nayi, masu yima breaker liƙi nayi masu yima ango da amarya dasu Abdur-raheem nayi. Daga hakafa aka tafi casun ƙarshe. Alhmdllh taro ya tashi lafiya kowa cikin farin ciki, anci ansha kowa yayi haniƙan banda amarya da ango, dan ko ruwa bily batasha a wajen nanba har aka tashi, haka shima Jay ɗin.

★★★★★

Ana tashi aka fice dani daga wajen, ganin mun barsa acan ba'a mota ɗaya zamu tafiba kuma farin ciki ya kamani, dan nazata dai masarauta za'a maidani. Sai dai ana sakani mota naji suna faɗin daga nan gidan amarya za'a nufa, idan anje ana kaita mutane su fito dan ba zama za'aiba dare yayi shabiyu saura. A take zuciyata ta shiga tsitstsinkewa, hawaye suka fara gudu a kumatuna, dan nama manta da wata kwalliyar fuskata, ALLAH bansan wannan shirin suka shirya ba, duk zatona sai gobe idan ALLAH ya kaimu ganin bamuyi sallama da Ummu ba a masarauta. Tun ina kuka a hankali har ya bayyana fili. Lallashina Mah-mah take tayi da sakemin nasiha ƙasa-ƙasa har muka isa, dazan fita a motarma sai da ta sakani nai addu'a, hakama da zan saka ƙafata a falon, kaina lulluɓe yake da alƙyabba banajin komai sai ƙamshin fenta da ya haɗe dana turare dana sabon kaya ya bada yanayi na musamman.

An miƙa amarya Bilkisu ɗakin mijinta, inda basu wani ɓata lokaciba dan basufi mintuna ashirinba aka saka kowa ya fita ya shiga mota, dama wasu sun wuce gida daga wajen dinner, acewarsu zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sazo suga gidan amarya da ƙyau. Cikin mintuna ƙalilan gidan yay tsit, motocin duk sun juya, Aunty Batool kawai aka bari, itama zata ɗan zaunane kar abar Bilkisu ita kaɗai kafin Jay ya shigo. Bayi ta shiga ta haɗa ruwan ɗumi da turaruka masu ƙamshi tazo ta tada bily da har yanzu take kuka. “Kukan ya isa haka amarsu, tashi ki daure ki watsa ruwa dan wannan kukan naki nasan ya ɓata kwalliyar”. Ban musa mataba dan inada buƙatar yin wankan kasancewar a yanayin da nake ciki. Alƙyabar ta taimakamin na cire kawai ta fita ta barni, ban zauna jan jikiba dan tace nai sauri boss zai iya shigowa koda yaushe, bai kuma dace ya iskeni a haka ba. Wanka na shiga nayo sauri-sauri na kimtsa jikina na fito, harta kwashe kayan dana cire ta ajiye min riga da zani na atanfa. Shiryawa nai a gurguje, ina kammala saka kayan tana shigowa. Tace, “Yauwa kinga ai hakan yafi, bara aɗan gyara fuskar”. Bance komaiba nidai taɗan shafamin fauda da lipsgloss a baki kaɗan sai turarurruka data fesheni dasu ta bani babban gyale na yafa tare da sake feshe ɗakin da Air Fresheners masu daɗin ƙamshi. Inda ta zaunar dani ta matso tana murmushi, “To Amarsu angonki ya shigo, bara naje hasu Aliyu can na jirana zasu

saukeni a gida, mu kwana lafiya ALLAH ya huta gajiya”. Hawayen da suka ziraromin na share, nace, “Aunty Batool dan ALLAH ki kwana anan mana, kingafa dare yayi”. Murmushi tayi tana riƙe haɓa, “Inani ina kwana gidan amarya, kinga nayi nan”. Hawaye masu ɗumi ne suka sake gangaromin, na zame na kwanta inayin kayana dan jinake ma duk haushin kowa nakeji, ni banason auren a maidani gidan Dad kawai na cigaba da zamana hankalina kwance.

__________________________

Lokacin da shagali ke gudana a gidan Dad tashin hankali suke fuskanta, dan kuwa dai Salman ne ya gano hotunan biki na yawo a yanar gizo waɗanda ke wajen dinner nata ɗorawa, kunsan mutane da waya a hannu tamkar abu na cizonsune idan suka gani, tun fara dinner ɗin suketa ɗakar hotuna suna ɗorawa wasuma harda videos. Aiko Salman yaci karo da su, shigowa gida yay ya kunna tv dan son ganin wainar da ake toyawa a wajen kasancwwar babu wanda yaje a cikinsu Momy ta hana. Yana zama Aamilah na fitowa, zama tayi suna kallo tare da zagin Bilkisu da Jawaad, hayaniyarsu ta saka Shahudah dake kwance a ɗaki zazzaɓi ya rufe fitowa, aiko tai mummunan gani, dan kuwa dai-dai wajen da Jay ya lashe cake ɗinan daya saka a hancin Bilkisu taci karo dashi, idan ba kallon tsaf kaima wajenba zaka ɗauka kissing ɗin Bilkisu ya keyi. Ƙara kawai ta ƙwalla ta yanke jiki ta faɗi. Duk kanta sukayi da ihu har Momy Da Dad dake sakkowa daga sama. Girgizawar duniya da sakama Shahudah ruwa taƙi koda motsi, a take hankalinsu ya ƙara kaiwa ƙololuwar tashi suka kwasheta zuwa asibiti likitoci suka rufu a kanta. Har zuwa yanzun dai babu wani bayanin farfaɗowarta kuma.............🤦🏻✍

Duk wanda suka kirani jiya ban ɗagaba suyi haƙuri, ngd sosai kuma da addu'oinku gareni na samu lafiya🤦🏻.

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭Billyn Abdul: Page 39

.................Tsaye kawai Jawaad daya shigo yay yana kallon Bilkisu da keta faman shashashar kuka, ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana girgiza kansa. Sai ya tuna da randa aka kai masa Shahudah, cikin kayan barci ya shiga ya sameta zaune hankalinta a kwance tana buga game a waya, amma ita jiba duk da ba daga ainahin iyayenta aka rabotaba ta kasa barin kuka. Idanunsa ya lumshe a hankali da ƙara sauke ajiyar zuciya. Ya cire hular da babbar rigan, daga shi sai wando da ƴar cikin da iyakarta rafin cinyarsa. Ƙarasawa yay gaban gadon ya zauna kusa da ita, dauriya kawai yake dan kansa ciwo yake masa shima, hannunta ya kamo batare da yayi magana ba. Gaba na ne ya faɗi dan banji motsin shigowar kowa ba, gyalen dana rufe har fuskata da shi nai saurin janyewa dan naji tsoro, ya murza hannuna dake cikin nashi yana faɗin, “Tashi zaune, K baƙya gajiya da kukane?”. Yay maganar da kamoni sosai ya miƙar. Koda na tashi zaunen ban yarda na kallesa ba, ya sake murza hannuna da har yanzu yake a cikin nashin. Idanuna naɗan rumtse ina ƙoƙarin danne abinda nakeji. Jay dake kallonta ya girgiza kansa kawai tare da kai hannu ya janye gyalen data rufe fuska “Jiba yanda wannan kukan ya saka miki zazzaɓi, amma bazaki tausayima kankiba ki barsa haka, indai danni akeyi a ya isa haka na yafe”. Kamar jira take yay magana wasu hawayen suka sake zubowa sharrr. Kai Jawaad ya dafe kawai yana lumshe ido da sake buɗewa a kanta, shi kukan natama ya fara bashi dariya, sudai mata a duniya suyi kuka shine jin daɗinsu, ya sauke numfashi kaɗan yana ƙoƙarin danne dariyarsa. “Tashi muje kici abinci kisha magani sai mu dawo ki cigaba da kukan kamar ƙyafi samun ruwan hawayen sosai ai”. Mamakin maganarsa yasa na ɗago na kallesa. Yace, “To miye na kallon nawa? Ba daɗi kukan yake miki ba?”. Ɓata fuska nayi nasa hannu na goge hawayen. Bai sake cewa komaiba ya miƙar dani tsaye, kunyace ta kamani nai azamar ɗaukar gyalena daya zame zan maida, amma sai ya riƙe, yana nunamin hanya alamar muje. Cikin rawar murya nai magana a karo na farko tun shigiwarsa, “To ka bani gyalen”. Matsowa yay gab dani sosai, hakan yasa naja baya idanuna na sake tara ƙwalla, Hannuna kawai ya kama batare da ya bani gyalenba bai kuma cemin komaiba muka fito falo. Dukda kaina a ƙasa yake nasan falon nan ya haɗu, ga wani ƙamshi mai kwantar da zuciya na tashi a cikinsa. Cikin kujera ya zaunar dani shima ya zauna kusa dani, ya buɗe filet ɗin dake akan centre table ɗin falon, ƙamshi mai daɗi ya daki hancina, kajine guda biyu da suka sami gashi mai ƙyau da tsafta. Yace, “Kici abinci kisha magani jikinki yayi zafi da yawa”. “Nifa na ƙoshi”. Na faɗa murya na rawa. Banza yaymin ya ɗebo naman da hannunsa ya kawo min a baki. matsar da fuskata nai ina girgiza kaina da sake faɗin, “ALLAH da gaske nake na ƙoshi”. Shiru yay na wasu sakanni baice komaiba yana kallona, kafin ya ajiye wanda ya ɗebo ɗin ya matsoni sosai, Hannunsa kawai naji saman haɓata ya ɗago fuskata, muryarsa babu alamar wasa yace, “Iyayi zakimin danma kinga zan baki kazan ƙyauta, ALLAH garama kici da arziƙi, bar ganin period kikeyi inada hanyoyin da zan sakaki kukan da kike sha'awar yi mai dalili, idan kuma kinji ƙarya kar kici na nuna miki ainahin kalata da baki saniba”. Tunda ya fara maganar idona ya cika da ƙwalla, na fara ƙyaƙyƙyaftasu. Fuska Jawaad ya haɗe sosai, dan ya kula sai ya buɗe mata wuta zasu dai-daita, a ɗan kausashe yace, “Miemaa!”. Da sauri na ɗago na kallesa jin yanda ya kira sunan a daƙile. Ya tsatstsareni da idanunsa dake tattare da ɗumbin gajiya, duk yanda naso janye nawa ya hanani. “Na miki kama da abin wasanki?”. Kaina na girgiza masa da sauri. “Inhar kika bari waɗanan hawayen suka zubo ALLAH saikin gane kurenki”. “Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy nima bada sona suke zubowa ba, wani irin tsoro nakeji a raina, saina dinga ganin kamar gilmawar inuwa kuma idanuna, sannan a ƙasan zuciyata wani irin zafi nakeji, kamin addu'a a cikin ruwa”. Kafeta yay kawai da idanu na wasu sakanni, ya ɗan ciza leɓensa na ƙasa yana jawota jikinsa ya rungume. “Ki daure kinji, ki dinga ƙarfafa zuciy

arki, insha ALLAHU babu abinda zai faru ALLAH na tare damu da duk al'amuranmu, kefa jarumace na sani, ko kinaso suci galaba a kanki?”. A hankali na girgiza masa kaina hawayen da nake maƙalewa na sauka masa saman ƙirji, nace, “Insha ALLAH zanyi kamar yanda kace”. Yace, “Yauwa my sweet princess, tashi kici abinci ki manta da komai dake zo miki a rai kinji”. Munkai tsahon mintuna uku a haka kafin ya ɗagoni, addu'ar yaymin a cikin ruwa kamar yanda na buƙata ya bani na sha, a take na fara zufa duk da kuwa falon fanka na aiki, wata nutsuwace ta fara saukarmin a hankali har naji nauyin da kaina yayi ya ragu sosai, sai ajiyar zuciya kawai naketa saukewa. Da kansa ya bani naman, duk da a kunyace nake matuƙa haka na daure naci, sai dai banci da yawaba nace na ƙoshi, amma ƙin saurarena yayi ya cigaba damin ɗurar dole. Daƙyar na samu ya barni, tashi yay babu jimawa ya dawo ɗauke da ɗan box a hannu, ni dai harma na ɗan fara gyangyaɗi dan sosai naji nutsuwa a daga ruɗanin dana fara shiga ɗazun, dama ga yunwa kuma. magani ya bani na sha. “Tashi kije ki kwanta dare na sake yi”. Kaina dake a ƙasa na ɗaga masa na miƙe, rashin gyalenan a jiki duk jina nake a matuƙar takure. Jay ya bita da kallo harta shige, ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana jingina da kujerar tare da lumshe idanunsa, tausayi take bashi sosai, kallo ɗaya zakai mata ka fahimci tanada damuwa sosai, yasan zafin rashin iyaye, dan haka yake tausayin duk wanda bai dasu, balle mace ma mai rauni irinta dake zagaye da ruɓaɓɓun dangi gaba ɗaya, garashi dangin uwa na ɗauke masa kewa da damuwa ma. Yanzukam ya samu kwanciyar hankali duk wani motsinta zai kasance a kan idanunsa, a yanzune zai binciko abinda ke binne da iznin ALLAH. Da wannan tunanin ya tashi ya shiga ɗakinsa, wanka yayi da ruwa mai zafi yay shafa'i da wutiri, maganin shima yasha dan kansa ciwo yake masa sosai dauriya kawai yakeyi.

★★★★★★

Kasancewar maganin da ya bata harda na barci tuni barcin yay awan gaba da ita, kayantane a jikinta bata canjaba, hakan ya saka Jawaad daya shigo tsura mata idanu, komanta ya ƙara canjawa, musamman ma fatarta tai wani irin gogewa sai ƙyalli takeyi, a fuskarta kawai zaka karanci bata da son hayaniya, komai nata tsaka tsakine, hakan yasa ƙyawunta ya kasance mai sanyi, a kallo ɗaya bazaka taɓa ganin sirrin ƙyawunta ba dan batada cika ido irin na Shahudah, yanda take nutsatstsiya haka ƙyawuntama a hankali yake bayyana ga mai kallonta. Tanada kwarjini da cikar haiba na isassun mata masu kamun kai. Yaɗan lumshe ido ya sake buɗewa a kanta, a fili ya furta, ‘Sai jan ajin tsiya da miskilanci ga tsoro kuma ba’. Yay maganar yana nufar akwatinta da aka jiye alamar kayantane a ciki, buɗewa yay, a sama yaci karo da kayan barci har kala uku, doguwar riga da bazata wuce rabin cinyaba, sai riga da wando kala biyu. Riga da wandon ya ɗauka dan sun ɗanfi kauri da mutunci, yasan dai saka matasu akayi daga gani. Zama yay bakin gadon kusa da ita, ya janye bargon data rufama ƙafafunta zuwa ƙugu, zif ɗin rigar ya janye ƙasa bayan ya zame ɗan kwalinta gashinta da yasha gyara yanata ƙamshi ya bayyana. Cikin barci naji ana ƙoƙarin ciremin kaya, da ƙyar na buɗe idanuna sai naci karo da shi, ai babu shiri na miƙe zaune duk da jikina babu wani ƙarfi, na dafe rigar da har ya ciren hannu guda batare da na yarda mun haɗa ido ba. Kayan daya ɗakko mata ya ajiye saman cinyarta yana miƙewa, “Ki canja waɗanan kayan dan zasu takuraki sunyi nauyi da kwanciya barci”. Da kallo kawai na iya bin bayansa ina haɗiye tsoron da saura kaɗan ya hudan zuciya, gaba ɗaya mamaki al'amarinsa ke bani, wai dama haka yake boss ɗinan ashe, yanzu daban farkaba nufinsa shine zai sauyan kayan? Tabɗi wlhy daya gama dani kuwa. Saida yaje ƙofa zai fita sannan ya juyo yana kallona, “Idan kika bari mintunan dana ɗiba miki ya cika baki tashi kin sauya kayan nanba, hummm..” yay maganar murya ƙasa-ƙasa amma daɗan karsashi sannan ya fice. Kamar nayi kuka haka naji, na kalli kayan barcin da ya ajiyemin tare da ɗagasu, riga ce ƙarama dan ko ɗuwawuna bazata saukaba, hannunta ɗan si

riri sai wando da nasan iyakar gwiwa zai tsaya min. Sanin halinsa ya sakani miƙewa ina sauke ajiyar zuciya, dan nasan zaiyi duk abinda yace ɗin, canja kayan nai ina addu'ar ALLAH yasa bazai dawo ba dai. Ina kammalawa na kwanta. sallamarsa ta daki dodon kunnena. Sosai na waro idanu waje naja bargo na rufe duk jikina, ganin ya zagaya ya kwanta ta ɗayan gefen Cikin in ina nace, “A a..nan za.. ka kwanta?”. Ba tare daya kalleniba yace, “Uhmm”. Baki na tura ina lullumshe idanu, Cikin ɗan haushi-haushi nace “Ammafa kowa ance da ɗakinsa ai”. Ganin ya juyo yana kallona, nai saurin jan bargon na rufe har saman kaina da shi. Murmushin da baiyi niyyar yi bane ya suɓuce masa, ya matso inda take sosai tare da ɗaga bargon ya shiga shima, saka hannu yay ya yaye na saman fuskartata tare da ɗora kansa saman filon data kwanta suna fuskantar juna, tuni jikinta ya fara tsuma, ta kuma rumtse ido kam, fuskarta duk ta bayyana tsoronta a fili. Hannunsa ya ɗora saman kanta ya shafa gashinta dake kwance luf yasha gyara tun daga goshinta har inda yake ɗaure da ribbon, a hankali ya zame ribbon ɗin gashin ya warware. Ƙoƙarin danne dariyar dake neman kufce masa ya keyi. Tsabar yanda take a tsorace har bugun zuciyarta yanaji dan suna gab da junane sosai, hannunta data sakane ta matse ƙirjinta yay musu kantanga. Da biyu ya tura yatsun hannunsa cikin gashin nata da wani irin salo. “Na shiga uku ni balki”. Ta faɗa babu shiri muryarta na rawa tamkar zata fashe da kuka tare da ware idanunta gaba ɗaya kansa. Jay daya kasa riƙe dariyarsa yanzun kam ya saki lallausan murmushi da ɗora goshinsa saman nata, “Kinsan baki da ƙarfi miyasa kika nemi faɗan?”. “To yi haƙuri dan ALLAH” ta faɗa tana son jan jikinta baya. “Daga baya kenan yarinya” ya bata amsa shima da sake matsota jikinsa sosai ya matse yanda tilas ta janye hannunta data kare ƙirji da shi dan taji numfashinta na neman barin ƙirjinta. Jawaad kam da yasan da biyu ya matsetan dama ya sake sakin murmushi da manna dukan fuskarsa akan tata har labbansa na gogar nasa. Cikin raɗa-raɗa yace, “Nifa idan aka takaloni faɗa banajin bari saina maida raddi”. Hawayen da bily ke maƙalewane suka zubo mata a kumatu, tace, “To ai na baka haƙuri ko”. “Ni kuma sai ban haƙura ba ai hajjaju” yay maganar da manne laɓɓansu yanda babu damar sake magana ma. Duk yanda take mutsu-mutsu ya hanata kowacce irin damar da take buƙata, karan farko a rayuwarta da hakan ta faru da ita, abinda takema kallon ƙazanta idan ta gani a film yau shine ake mata a zahiri, ba kowa ke matanba kuma sai boss, innalillahi...... itakam taga takanta dama haka mutuminnan yake.......?

(To nima dai bansan hakan yakeba bily sai yanzun, duk zatona waliyyine fa kamar yanda Jabeer ya faɗa😂🚴🏼🚴🏼😜).

★★★★★★★★★

Barcin da suka gaza samunyi da wurine ya ja musu makara, Jay ya janye bilkisu daga jikinsa da ƙyar ya tashi zaune bayan ya kunna fitilar ɗakin, hannunsa dafe da kansa da har yanzu yake jingim alamar ciwon bai saukaba gaba ɗaya, bargon ya gyara mata yana kallon fuskarta da duk hawayen da tai suka bushe, idanunsa yaɗan lumshe yana mai tunanin yanda zasu kwashe da wannan uwar tsoron randa yace mai gaba ɗaya zaiyi, a daren jiyanma ba wani abun kirki yay mataba amma tabi ta ishesa da kuka. Numfashi ya sauke da sauka a gadon. Yasan tilas ne yay wanka kafin yace zaiyi salla, dan haka ya fita zuwa ɗakinsa a gaggauce kafin a tada sallar.

A hankali na buɗe idanuna dake jingim da barci nabi bayansa da kallo harya fice, tunda ya motsa nima na farka, sai dai matsananciyar kunyarsa da nakeji bazata barni na nuna masa na farka ɗinba, abinda ya faru daren jiya ya shiga rige-rigen dawomin a zuciya, hannuna na ɗora saman laɓɓana da sukasha gurza a hannunsa, da wanine ya cemin abinda yay a daren jiya zai iya wlhy sai na ƙaryata, kamar ba boss ɗin nanba na office gwanin hayaƙi da mazurai, sai yaso kaga walwalarsa balle akai ga dariya, yanda yake mara hayaniya a zahiri haka yake a komaima nasa babu hayaniyar, ajiyar zuciya na sauke murmushi na suɓuce mani, tashi nai nima dan ina buƙatar gyara jikina dukda barcin da nakeji na fitar hBillyn Abdul: ankali. Gadon na gyara sannan na nufi bayi, wanka nai da ruwa mai zafi ina addu'a a raina ALLAH yasa kar jinin nan ya ɗauke yau, dan nasan a ƙa'idar kwanakin da nakeyi zuwa rana zai ɗauke, dama yanzun kaɗanma na gani a jikin pad ɗin amma bai ɗaukeba, to na tabbata zuwa azhar bazan gansaba. Ina fitowa doguwar riga na zura na koma gadon dan har wani jiri-jiri nake gani saboda barci, yau ko azkar na kasayi, aiko kafin na farga na lula.

Ɓangaren Jawaad ma ana idar da salla da ƙyar ya daure yay azkar ɗin, yana kammalawa ya nufo gida, sama-sama suka gaisa da maigadi ya shigo gidan, yasan Bilkisu barci take tunda dai ba salla zata tashi yiba. Ɗakinsa ya shige, jallabiyar jikinsa kawai ya zare ya haye gadonsa shima sai barci.

_________________________________

Da ƙyar likitoci suka samu Shahudah ta farfaɗo kusan ƙarfe biyun dare, ba ita kanta dake cikin mawuyacin halinba harsu kansu sunyi matuƙar jigata, gasu Dad duk sunbi sun ruɗa musu asibiti sai kace ran ƴar tasu a hannunsu yake. Aiko koda ta farfaɗo allurar barci kawai sukai mata ta sake komawa, suna fitowa su Momy dake wujiga-wujiga suka yo musu caa da tambaya. A yanzu bazasu iya wani zaman musu bayaniba dan haka sukace kawai ta farfaɗo. Koba komai su Dad sun sami kwanciyar hankali, dan shi kansa ɗazun harda hawaye yayi, baisan irin ƙaunar da yakema Shahudah ba a rayuwarsa, musamman ma a rin wannan lokacin da wani gagarumin abu mai taɓa zuciya da tashin hankali keson faruwa da ita, sam zuciyarsa bazata iya ɗaukaba gaskiya, bama zai yuwuba, dolene ya nema mafita kafin lokaci ya ƙure. Shahudah sa, ɗiya mafi soyuwa a zuciyarsa, kai ina bazai yuwuba, dolene yasan mai yuwuwa, ya yarda ya rasa komai akan Shahudah wlhy. Haka suka kwana a asibiti hankalinsu tashe har ALLAH ya wayi gari lafiya.

Misalin takwas na safe Shahudah ta farfaɗo bakinta na kiran sunan Jawaad, kuka take rurus da roƙon a kira mata Jawaad ya saki Bilkisu inba hakaba zata kashe kanta. Kasancewar har mama Atika da bama lafiyar ƙafane da itaba tazo asibitin itama tunda safe suka rufu kanta suna lallashi da bata baki akan cewar ai Bilkisu bata tareba wai, kuma ta kwantar da hankalin Jawaad zaizo anjima kaɗan. Sam taƙi sauraren kowa, daga ƙarshe dai dole Doctor ya sake zuwa yay mata allurar barci mai ƙarfi dan jininta yay masifar hawa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull