Kenza eBookz

Kwai cikin kaya book 2 complete - Chapter 48

Kwai cikin kaya book 2 complete - Chapter 48

Kwai cikin kaya book 2 complete Chapter 48: Kwai cikin kaya book 2 complete Chapter 48. ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.by BilynAbdull *_Shin kina ko…

4,488 words

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.by BilynAbdull *_Shin kina ko kana sa sha'awar koyon ilimin ICT?_* *_Ko kuna da sha'awar yadda ake hada cartoon?_* *_Ko kana da sha'awar yadda zaka bunqasa kasuwancinka ta hanyar online?_* *_Matsalarki ko matsalarka rashin makarantun da zasu koyar dake/kai ilimin computer ta fannnin larabci?_* *ALBISHIRINKU KANAWA* *_Kukanku ya qare,matsalarku tazo qarshe,shahararren kantin nan na yanar gizo wato RAHAMALLS yazo muku da makarantar koyon sarrafa computer a sauqaqe wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI)_* _Sun tanadarmuku qwararrun malamai wanda zasu koyar daku bisa tsarin da kuma cikakkiyar qwarewa ta yadda zaki fahimta fiye da yadda kuke zato_ *ga masu buqatar aji na musamman har cikin gidajensu,makarantar ta shirya tsaf don baku darussa har cikin gida* *sannan akwai tsarin ajujuwa na musamman bisa yanar gizo wato(online classes)* *kaidai maza garxaya ka tuntubesu akan wanannan lambar waya* 08033990209 *_akwai ragin kaso hamsin cikin dari na kudin registration ga kowanne dalibi_*👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽 Page 51 ..................Gidan duk ya ajiye ƙananun ƙura, duk da ko'ina a rufe yake, haka na daure naɗan gyara ɗakinsa dan mu samu inda zamu kwanta, kafin a kira sallar magriba na kammala, shikam wanka ma yayi ya fita tun fara aikin nawa. Bai dawo gidanba har saida akai sallar isha'i, kusan tara sai gashi ya dawo mana da abinda zamuci. Gaba ɗaya banajin daɗin yanayinsa, ya koma min Boss ɗin dana sani a office mara walwala da yawan magana, komai nake sai dai yayta bina da ido kawai, abincinma da ƙyar na samu yaɗan ci yace ya ishesa, nima cire hannuna nai a ciki na ɗauke kaina gefe. “Miye hakan?”. Ya faɗa muryarsa can ƙasan maƙoshi. Ƙoƙarin miƙewa nai tsaye nace, “Na ƙoshi nima...” kafinma na gama rufe bakina naji caraf ya cafko hannuna ya maidoni ya zaunar, kallonsa nai ina kumbura fuska, ya zabgamin harara tamakar idanunsa zasu faɗo ƙasa, “Ina wasa da ke ko?”. Ƙasa nai da kaina dan bazan juri kallon nasaba, “ALLAH nima na ƙoshi to”. Banza yaymin bai tanka ba, ya ɗebo ya kawo bakina, zan ɗauke kaina yay saurin faɗin, “Kinsan ALLAH idan baki shiga hankalinki ba sai na sauya miki kamanin wannan fuskar taki, malama haa”. Idanuna cike da ƙwala na buɗe bakin, ya ko zubamin yana sake zabgamin harara da yin ƙwafa, inaji ina gani yaymin ɗurar dole, shiko yaƙi ya ci, sai yogurt yaɗan sha, hakanne yasa naɗan samu kwanciyar hankali. Kasancewar a gajiye muke ga mai gayya mai aikin baya tare da walwala, gashi zamu koma aiki gobe idan ALLAH ya kaimu sai mukai kwanciyarmu da wuri. WASHE GARI Tun kiran sallar farko na tashi, cikin sanɗa na fita daga ɗakin nasa, kasancewar barcin da muka kwanta da wuri sai na tashi jikina babu nauyi sosai, da wannan damar na fara rage aiki. Koda ya fito zai tafi massallaci ya ga ina aikin gyaran babban falo baice dani komaiba ya fice abinsa, ajiyewa nai nima na koma ɗaki nai salla, ina idarwa ban hutaba na sake fitowa na cigaba, ana idar da salla shima bayan wasu ƴan mintuna sai gashi ya dawo, bayan mun gaisa shima sai ya cire jallabiyar jikinsa ya shiga tayani aikin. Duk da na roƙesa ya bari zan ƙarasa tunda na kusa bai saurareni ba, sai da yaga ya rage bedroom ɗina kawai sannan ya barni na ƙarasa. Ƙurar dana gani tasa nake sharo har ƙarƙashin gado kamar yanda nayi a ɗakinsa da ƙarƙashin kujerun falo ma, abu na sharo a ƙarƙashin gadon, wanda ya sakani dakatawa da sharan nasaka hannu na ida jawosa dan naga minene, wallet ce ƴar karama dan bata kai girman normal wallet dana sani ba, kamar zan buɗe sai kuma na ajiye da tunanin ko tashice, saman mirror na ɗaurata na cigaba da sharan harna kammala komai, ganin lokaci yaja na shiga bayi dan yin wanka sauri-sauri, ban wani ɓata lokaciba na fito. Idanuna ne suka sake sauka akan wallet ɗin nan, duk yanda naso na share a yanzun sai na kasa hakan, na matsa gaban mirror ɗin ina goge fuskata da ƙaramin towel dake a hannuna da hannun haggu, na damar kuma sai na fara ƙoƙarin buɗe wallet ɗin, ɗan ƙaramin hoton dana fara cin karo da shine ya sakani shiga mamaki, na fara fiddo abubuwan cikin wallet ɗin gaba ɗaya, ƙirjina sai wani irin mahaukacin bugawa ya keyi, banma san lokacin dana saki towel ɗin hannun nawa ba jiki na rawa, harda zufa ta fara tararmin a goshi, nagama zazzage komai a ciki, abubuwane masu muhimmanci da daraja dana san maisu bazai taɓa sakaci dasu ba da har zan gansu anan, to wama ya kawosu? Ni dai babu wanda ya taɓa zuwamin nan gidan a kaf mutanen gidan balle nace a mistake wani yazo da su. A fili nace, “To kodai boss ne ya kawo?”. Wannan tambaya na yitane badan zuciyata ta gamsu da ita ba, Duk da sallamarsa da naji a bayana ban iya na waiga ba. Ƙarasowa yay yana ɓata fuska ganin bama ta shirya ba, ya ajiye ƙaramin tiren da ya ɗoro musu tea a saman table kafin ya ƙaraso inda take yana jan tsaki. Ganin ko motsi bataiba har yanzu tanata juya abu a hannu sai kansa ya sake ɗaurewa, “Wai kina kallon agogo kuwa Miemaa!?”. Ya faɗa a ƙausashe. Ɗagowa nai ina kallonsa, cikin rawar baki da fargabar amsar dazan iya samu nace, “Dan ALLAH kaine ka kawo wallet ɗin nan ɗakin nan?”. Baice komaiba ya tako gabana tare da riƙo hannuna duka biyu yana kallon abinda ke ciki, cards ne masu muhimmancin gaske, ga sunan maisu kuma ɓaro-ɓaro a jiki da hotunan sa, “Ina kika ganta ke?”. Gado na nuna masa batare da nayi magana ba, ya kafe hannayena da nake sake jujjuya cards ɗin ƙo ƙyaftawa bayayi, nikam ƙirjina sake bugawa ya keyi da sauri-sauri, jira kawai nakeyi yace wani abu, amma yaƙi cewar. Hawaye suka sulalomin ina mai fatan kar abinda keta zomin arai ya kasance hakane, kai banama fatan hakan, sai dai idan anason min yawo da hankaline dan a ɓata masa suna. Muryata na rawar kuka nace, “Kace wani abu dan ALLAH boss”. Kansa kawai ya girgizamin yana mai cije leɓensa na ƙasa, ya saka hannu ya amshi komai dake hannuna ya maida a wallet ɗin ya sakata aljihu, taimakamin yay na shirya ina hawaye, wata gigitacciyar tsawa data nema haukatani ya dakamin, “Ke komai kuku! kuka!! kuka!!!, komai abin kukane a gareki, ya isheni haka banason ji kuma, malama ki sharemin waɗanan banzayen hawayen kafin nai miki bugun kayan wanki wlhy a gidan nan!!!”. Na matuƙar tsorata da yanayinsa, na koma jikin madubi na maƙure ina ƙoƙarin haɗiye kukan, gaba ɗaya kamanninsa sun masifar sauyawa, idanunsa sun kaɗa sunyi jajur, baice dani komaiba ya juya ya fice daga ɗakin. Sake fashewa nai da kuka ina faɗin, “Ya ALLAH ka bani haske akan wannan al'amarin”. ƙarar takunsa dana jiyo ya sakani saurin goge hawayen na juya ina saurin ɗaukar soson hoda nahau shafawa. Bayana yazo ya tsaya yace, “Agogon wanene wannan?”. Da sauri na juyo gabana na faɗuwa na zubama hannunsa idanu, kusan mintuna biyu na ɗago na kallesa, Kaina na girgiza masa alamar ban sani ba. “Kin tabbata?”. Na ƙara ɗaga masa kaina. Bai sake cewa komai ba ya koma bakin gado ya zauna tare da ɗaukar kofin tea ɗaya ya fara sha yana cigaba da kallon agogon kafin ya ajiyesa gefensa. Ganin ya kafeni da idanu nai sourin ƙarasa kimtsawa zuciyata nata kaikawo da tunane-tunane kala-kala waɗanda gaba ɗaya sake zurma zuciyata suke a firgici. Tea ɗin ya ɗauka ya miƙamin, babu musu na amsa dan a yanda yake ɗinnan zai iya mammakeni idan nai masa gardama. Ni nafara fita daga ɗakin nakai kofunan kicin na ɗauraye da sauri-sauri na fito, a falo na iskesa jikkata na gefensa ajiye. Ɗauka nai tare da briefcase ɗinsa, baice dani komaiba nai gaba ya bini a baya, shine ya kulle ƙofar sannan muka ƙarisa inda Sadiq ya goge motar ƙal yana jiran fitowarmu shi da maigadi, mun gaisa dasu cike da girmamawa, suka buɗe mana motar muka shiga bayan kowannenmu ya karanto addu'ar fita daga gida.Tunda muka fice daga gidan hankalinsa nakan wayarsa, yayin da ni kuma na afka kogin ruɗaɗen tunanin da gaba ɗaya kwanyar kaina ta gaza ɗauka. Jinai kawai an riƙo hannuna, na juyo na kallesa, baice dani komaiba ya matsoni jikinsa tare da aza kaina bisa damtsen hannunsa yana shafa bayana. Shiru nai ina haɗiyar zuciya da hawayen dake taho mani. Tunda Sadiq ya tsaida motar muke ta yima station ɗin kallon mamaki, duk da dai safiyace sosai baici ace babu mutane haka ba, sai securitys da keta kai kawo, Sadiq ya buɗe masa ya fita, kafinma ya zagayo ta wajena nidai na buɗe da kaina. Na ƙara ɗan wawwaigawa na kalli ko ina, station ɗin tsit kamar babu kowa a ciki. Shima kansa kallon ko ina yake da mamaki, amma baice komaiba, ganin bai amsa jikkarsa ba nasan so ya ke saina kai har office ɗinsa kenan? Tare muka jera, baya bari ya tseremin da ko step ɗaya. Shine ya buɗe ƙofar, muna shiga kawai sai mukaji abu kanmu ana mana wanka da shi. Saurin ƙoƙarin fara share fuskkokinmu mukayi, amma abin yaƙi daina zubowa, sai ma ihun ma'aikatanmu da tafi daya karaɗe wajen. A sannan ne abun ya daina zubowa, muka share na fuskarmu sannan muka kalli juna kafin mu maida ga kallansu. A take kunya ta kamani kuma, dan gaba ɗayansu sukayo mana caa a ka da kalmar “Muna tayaku murnar aure!”. Murmushi Jawaad ya daure ya saki duk da iya fuskarsa ne, kafin ya maida dubansa ga Bilkisu datai ƙas da kanta, ya kamo hannunta cikin nasa yana faɗin, “Mun gode sosai, ALLAH yabar zuminci”. Ya ƙare maganar da kai hannun Bilkisu saitin bakinsa ya sumbata. tafi aka sakeyi, sannan kowa ya nufosu da ƙyautar dake hannunsa, tun jay na amsa har hannunsa ya cika bilkisu ma ta fara amsa, jabeer ne ya matso ya taimaka musu aka tarasu waje guda ya sake musu godiya itama bilkisu tai musu ranta fal mamaki. Gaban ƙaton cake ɗin da akai da hotonsu aka jasu, daga bilkisu har jawaad ɗin dai murmushine shinfiɗe a fuskarsu, bazaka taɓa gane sunada damuwa ba, bily ta fara ɗaura hannun ta saman wuƙar kafin Jay ya ɗaura nasa saman nata suka yanka. Ita ta fara cirar ɗan guntu ta saka masa a baki, yay mata murmushi mai sanyi ya ciro kaɗan itama ya saka mata yana jawota jikinsa ya rungume, saboda ganin yanda Rose take musu wani irin mugun kallo mai cike da tsana da takaici yay hakan, da farko baiyi niyyar bama Bilkisu cake ɗinba, amma saboda Rose yayi dan yana lure da ita ko kalma ɗaya bata togaba na tayasu murna, hakama wasu daga cikin matan gurin sai baƙin rai suke da bankama bilkisu harara.. Nanma tafin akayi, kafin Sir Ahmad ya farayin jawabin taya murna a garesu kasancewarsa head of department nasu, daga nan sauranma suka sake tayasu murna da fatan alkairi da bama Jay hannu suna musabaha, matan kuwa Bilkisu suke bama hannu itama suna mata, shikam Jay sai dai su ɗaga masa dan sunsan ƙa'idarsa ce baya hannu da mace ko wacece ita a station ɗin nan ko tana a gaba da shi kuwa sai dai a kuskure. Suma mazan duk da Bilkisu na ƙasansu hakan bai hanasu mata murna ba, tanata amsawa a kunyace dan wasuma ko magana ita bai taɓa haɗata da suba sai yau. Sai da aka gama ɗan kace nace sannan suka wuce office ɗinsa, ƙyaututtukan da suka samu kuwa tuni Jabeer ya saka an kaisu ciki dama. Jikkarsa na ajiye masa saman table ɗinsa na ɗan kallesa, ganin hankalinsa nakan files ɗin saman table ɗin ya ɗauki ɗaya yana dubawa saina ce “Sai anjima” kawai na juya zan fita. Caraf naji an riƙoni, kafinma na juyo ya maidoni baya ya jingina da table ɗin, kallonsa nai da mamaki, ya ɗan harareni batare da yace komaiba naji saukar laɓɓansa kawai saman nawa babu zato. Idanuna na lumshe kawai ban masa wani musuba ko sau ɗaya, dan inhar zai huce ta hakan to Alhmdllh, rabonsa dako kissing ɗina tun randa mukaje Saudia. Ganin da gaske yake sai kawai na shiga bashi gunmawa, nidai fatana ya samu nutsuwa wannan fushin da fusatar dana gani tattare dashi ya gushe. Burrum aka turo ƙofa babu ko neman izini, ƙoƙarin janye kaina nayi amma ya hanani kowacce dama, saima sake turani jikinsa yayi sosai da sake sauya salon sumbatar, ƙamshin turaren rose da naji ya sakani nima canja salo dan ta bani haushi ɗazun, dan batamin magana ba sam, nakuma gaisheta taƙi amsamin. Jin ta fita da gudu tana kuka ya janye kansa da ƙyar yana jan tsaki da harar ƙofar. Kallonsa ya maido gareni yana hararata, hakan ya sakani sakin murmushi dan harga ALLAH dariya ya bani, to ni miye laifina kuma?. Kaina ya dunguremin da faɗin, “Idan kika cigaba da wannan noƙe-noƙen da sanyi saita cigaba da raina miki ai, ki kwana da shirin cewar ke matar Jay ce a station ɗin nan yanzun ba budurwarsa ba”. Ya ƙare maganar a hankali cikin kunnene kamar mai raɗa. Lumshe idanuna nayi ina murmushi, bance komaiba na ɗauka jikkata nasa a kafaɗa sannan na kallesa, shima kallona yake, murmushi na sake sakar masa da ɗaga masa yatsun hannuna biyu alamar bye-bye. Kafin ya samu damar cewa wani abu harna fice abina daga office ɗin. A jikin ƙarfen lifter na iske Rose tsaye sai cika take da batsewa, kallo ɗaya nai mata na ɗauke kaina, “K!!” ta faɗa a daƙile, banza nai mata tamkar banjiba na haye lifter ɗin abuna, wani tsalle tayi zata cakumoni naji muryarsa a bazata kanmu, “Koda kuskure karki sake wlhy hannunki ya taɓamin mata”. Ya faɗa a kausashe. Murmushi nayi da ɗage masa gira na ɗauke kaina, banajin amsar da take bashi dan nayi nisa da su, ina sauka kuma na sake ɗaga masa yatsun hannuna, shima ɗagomin yay, nai gaba abina na barsu bansan yaya suka kwashe ba.Bily na ɓacema ganinsa ya juya office batare da ya sake ko kallon inda rose take ba, ta cika tayi fam da baƙin ciki tamkar zatai bindiga a wajen. Ganin zai shige sai tabi bayansa a guje. Tana shiga office ɗin yana zama a kujerarsa, tsabar wulaƙanci sai yay kamar baisan ta shigo ba ya fara ƙoƙarin haɗa Computer ɗin saman table ɗinsa. Kuka maicin rai Rose ta fashe da shi tana dafe tebirin da hannu biyu, “Boss! Ni zaka wulaƙanta akan yarinyar da tazo station ɗin nan jiya-jiya? Ni zakaci amana ka yaudara saboda waccan ƴar tatsitsiyar yarinyar da bata wuce ɗiyar cikinka ba?, ko kunya bakaji kake iya nuna ƙaramar yarinya matsayin matarka wai?”. Jawaad ya ɗan lumshe ido yana buɗewa akan Computer ɗin da ya kunna, jikkarsa da bily ta ajiye masa ya ɗauka ya buɗe batare da yama rose ko kallo ɗaya bama balle tai tunanin samun amsa. Rose dake binsa da kallo ta sake fashewa da kuka tana faɗin, “Yanzu nan boss ina maka magana kana sakemin wani wulaƙancin?”. Sake yimata banza yay yama fara aikin gabansa. A wannan yanayin su Jabeer suka shigo office ɗin dan sunyi knocking har kusan uku yanaji ya share, shigowar tasuma baisa ya ɗago ya kallesu ɗin ba, su dai suka zauna a kujerun gaban tebirin suna kallonsa suna kallon Rose dake kuka. Hafiz ya jawo kujerar dake can gefe shima ya zauna yana jan ƙaramin tsaki dan shifa Rose takaici take bashi da halintan nan. Ganin yamaƙi kallonsu Jabeer yace, “Boss wai mike faruwa ne?”. Bai tankaba bai kuma kallesun ba yanzuma, dama cikin damuwa yake, ya fito gida da fushi, ita kuma yanzu sake kunna zuciyarsa take tana cikowa saman ƙirji, idan kuma har ta bari takai masa wuya to lallai zatayi nadamar biyosa office ɗinsa tana masa ihu a kai. Jabeer zai sake magana Aliyu ya girgiza masa kai alamar kar yayi, Rose ɗin ya kalla da take kallon Jay tamkar zata haɗiyesa, kuma har yanzu kukan take, “Rose miya faru?”. Juyawa tai ta kalli Aliyu hawaye na sake ziraro mata, “Aliy na gaji wlhy, na gaji da wulaƙancin da boss yake min, dan na soshi shine ya zama laifi? Shekara nawa na ɗauka tare da ku, kuma ban gazaba wajen nuna masa ina sonsa tun yana tare da wancan matar tasa, ya cemin shi bashi da ra'ayin yin mace fiye da ɗaya, karka manta har suspension yasa aka bani lokacin da matsalarnan taku ta faru, saboda ina sonshi na haƙura na mance da komai kamar bai faruba, yazo suka rabu da matansa muka tafi U.S ɗin nan, babu roƙon da ban masaba muyi aure a lokacin tunda dai ai baida mata, amma ya dinga shareni da zancen har muka dawo, yanzu duk ƙoƙarin nan da nai masa bai ganiba sai daga ƙarshe ya auri wannan yarinyar da tazo jiya-jiya cikinmu, bakuga yanda ya yarfani a gabanta ba yanzun, mi take da shi da har zai wulaƙantani a kanta?”. Kasa magana duk sukai, dan wannan faɗan kam dai yafi ƙarfinsu, duk da sunsan komai, amma ita rose banda haukarta ai ba lallaine ka SO a SOKA ba ko? Su shaida ne boss bai taɓa cewa yana sonta ba, sannan bai taɓa wulaƙantata ba. Hafiz ya taɓe baki cikin takaici yace, “Ikon ALLAH, so kike ya wulaƙanta matarsa a kanki kenan komi? Mtsoww! Lallai aiki ya sameki, kuka kuwa yanzu kika fara s.....” hannunsa Aliyu ya riƙe da sauri yana murmushi, yasan hafiz da iya yaɓowa mutum zafafan magana, yanzu sai ya sake birkitata. Duk da hakan kuwa sai da Rose ta hayayyaƙo ma Hafiz akan dama ta lura ita tuni ya tsaneta. Da sauri Jay ya bugi tebirinsa, cikin tsananin ɓacin rai ya nuna mata ƙofa yana faɗin, “Rose fitarmin a office!!”. Rose ta nuna kanta tana faɗin, “boss ni ka.......” cikin ƙaraji ya katseta ta hanyar sake doka tebir ɗin, “Nace! Ki fitarmin daga Office”. Yanda taga idanunsa sun masifar kaɗawa ya sakata firgita, tasan shi tasan shiɗin wanene idan yay fushi, ta kuma san abinda zai iya aikatawa bayan hakan, ta kalli su Jabeer ta sake kallonsa. Tashi Jabeer yay ya kama hannunta ya fitar da ita dan ya tabbata wlhy idan har ta sake wasu mintuna bata fitaba komai yazo masa rai zai aikata mata, sai da ya kaita har waje sannan yace, “Rose miyasa kikai haka? Kinfa san wanene boss?”. Zatai magana yace, “Kinga kije zanzo na sameki muyi magana, amma Please ki daina masa haka babu ƙyau, wlhy na tabbatar yana ɗaga miki ƙafane darajar kina cikinmu, kinsan fa yana gaba dake, sannan boss bayason raini, kije zanzo ni da Aliyu mu sameki”. Badan taso ba ta tafi tana sharar hawaye da kissima irin tashin hankalin da zata saka Bilkisu a station ɗin nan.(🤔Rose mi kike ƙullawa kuma?). ★★★★★★★ Tana fita Jawaad ya daki kujerarsa daya tashi akai yana faɗin, “Wlhy yarinyar can saita bar aiki a cikinmu, kai ama station ɗin nan gaba ɗayansa”. Da sauri Aliyu ya taso yana faɗin, “Please Boss! calm down, don't waste your time for her, ba yanzu ya kamata ai wannan ba”. Hafiz yace, “Gaskiyane maganar Aliyu boss, micece rose da har haukarta zai dameka, nifa dama can bataimin ba, duk da tana da ƙwazo tana da siffofin mutane masu bala'in son kansu, ka barta saita gama shagala bazaka ɗauki matakin komai a kanta ba sannan ka ɗauka. Amma idan aka maida mata murtani a yanzu anma damu da ita kenan, abinda kawai za'ai mata shine winning, ayi bala'i bala'in winning ɗinta akan Mami, idan tace zata shigar mata hanci kacimin ubanta iyakar iyawa”. Ƴar dariya Jabeer da ya shigo yayi jin furucin Hafiz ɗin, ya zauna yana faɗin, “ALLAH kai mugune Hafeez”. Zama duk sukayi suma, Hafiz yace, “ALLAH kuwa jabeer haukar yarinyar baimin ba, haka ake so ne banda hauka?, ni dama ni tace tana so ALLAH kuwa ko, hummm”. ya ƙare maganar da cije leɓe irin na tsantsar mugunta. Basu Jabeer ba hatta Jay sai da ya murmusa yana mai girgiza kansa, dan yasan Hafiz shegen kansane a iya mugunta. Ya sauke ajiyar zuya da jan guntun tsaki. Aliyu yace, “Kayi haƙuri boss, mu munzo musha labarin Honeymoon shashashar ta wargaza komai”. Harara ya balla musu, dan haka suka kwashe da dariya suna tafawa. Jabeer yace, “Wlhy Jay kayi wani ɓul-ɓul da kai fa, ka kuma ƙara haske”. “Kana baƙin ciki ne ɗan sa ido?”. Jay ya faɗa yana jefa masa biron hannunsa. Dariya suka sake kwashewa da ita. “Mtsoww, kufa wataran shashashancinku yawane da shi wlhy, ku ajiye wannan shiriritan muyi abu mai muhimmanci, kosu sir Ahmad banje na gaida ba, so nake mu gama sannan, dan na dawo da ayyuka masu yawan gaske, amma inason na fara jin mike tafiya daga wajenku?”. “Akwai nasarori masu yawa da zasu sakaka farin ciki kuwa, dama mun barsu ne harka dawo muyi maka surprise”. Murmushi Jay yayi mai sanyi da jin duk ɓacin ran daya toshe masa ƙofar zuciya yana faɗawa. Aliyu ya ajiye masa files ɗin hannunsa. Ɗauka Jay yayi ya fara dubawa, a take fuskarsa ta bayyanar da annuri, sai da ya gama dubasu duka sannan ya ɗago yana kallonsu, “Woow! Ina alfahari daku sosai da sosai wlhy, gaskiya kunmin babban albishir mai darajar gaske, yanzu kuna nufin waɗanan duk sunzo hannu? Kun gama mana da waɗan nan ayyukan?”. Jabeer yace, “Ƙwarai ma kuwa, dan wanda yasa aka kashe jami'inmun ma yanzu haka gobe za'a miƙasa kotu”. “Masha ALLAH, gaskiya naji daɗi wlhy, kuma nayi farin ciki sosai, maganar yaran canfa?”. Jawaad ya faɗa yana miƙewa ya ɗakko wani file a drawer ɗin bayansa. Yanzunkam hafiz ne ya bashi amsa, “Ai boss maganar ƙungiya ta wuce duk yanda mukai zatonta, lokaci kawai zamu samu ko zuwa anjima sai muje office ɗin nasu kaga komai da idanunka zaifi, ko zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”. “Hakan yayi Hafiz, mu barsa kawai zuwa gobe sai muje, kuma sannunku da ƙoƙari, Jabeer maganar matar nan fa, har yau baka kammala ba ne?”. Na kammala komai, sai dai abinda ba'a rasaba, shima akan binciken mitaje yi inda take ne, inason binciko ƴan uwanta ne kokuwa? Gashi yanzu ma na daina samun wayarta gaba ɗaya kuma”. Saurin kallonsa Jay yayi “Bata aiki wayar kokuwa?”. “An kasheta dai kusan kwana uku kenan, nafi kawoma raina matsalar caji ne”. Numfashi Jawaad ya ɗan sauke da faɗin, “Okay to ALLAH ya dafa mana, yanzu dai bara na leƙa na gaida su sir Ahmad, idan na fito zan ɗan fita wani waje, dana dawo saimu zauna akan wasu cases ɗin da muke dasu a ƙasa tunda kun kammala waɗannan”. Duk kai suka ɗaga masa, kafin duk su miƙe su fito, shi ya hau lifter yay sama su kuma kowa ya nufi office. Sai da ya shiga suka gaggaisa da oganninsa, office ɗin sir Ahmad ne ya zama ƙarshe, bayan sun gaisa shima da tattauna abinda ya shafi aiki Sir Ahmad ke cewa, “Nasan kasan Qaseem ya dawo ai?”. Da mamaki Jay yace, “Qaseem kuma sir!? Wlhy ban sani ba. Yaushe ya dawo?”. “Ya dawo kwana uku kenan, sai dai kuma yanzu haka sun killacesa, duk da shi ya dage akan shifa lafiyarsa ƙalau, shima Alhaji Ali ya kirani akan maganar wai ya kamata muyi wani abu a sakar masa ɗa dan baida wata corona”. Jawaad ya gyara zama yana ɗan murmushi da mamaki, yace, “To ALLAH ya kiyaye, amma kunje ɗin ku?”. “To Jay mu zamu biye musu ne, wannan hurumine na hukumar lafiya ai, kuma sunce nan da sati biyu idan bata basuga komai ba zasu sakesa ai”. “To ALLAH ya kaimu lokacin”. “Amin” sir Ahmad ya faɗa sannan sukai sallama ya fito. Bai koma office ba ya nufi inda Sadiq ke jiransa, buɗe masa mota yay ya shiga sannan suka fice. ★★★★ Cikin Barrack sukaje wajen baba ƙaura, baba ƙaura na zaune yanata fiƙar tsinkayen iccen ƙwari Jawaad ya shiga da sallama shi da sojan da yay masa rakkiya. Ɗagowa baba ƙaura yay yana amsa musu da musu sannu da zuwa, ya nunama Jawaad wajen zama shi kuma wancan sojan ya fice. Sai da suka gaisa da tambayar ya kwana biyu sannan baba ƙaura ya kalli Jay yay murmushi da ɗauke kai. “Malam Jawaad kenan, mi kuma ya faru?”. Jawaad yaɗan murmusa yana kallon ƙwarin da baba ƙauran ya feƙe ya zube gefe kusan ashirin, “Baba na zone akan wata magana daka faɗa ranar a dajin nan”. “Tofa wace magana ce?”. Hannu Jay ya saka aljihun wandonsa ya ciro wuri da gurun nan na hannu sai zobe ya ajiye gaban baba ƙaura”. Kallon kayan baba ƙaura yay ya ɗauke kansa yana murmushi, “Kun sami huɗu kenan?”. Kai Jay ya jinjina masa. Cigaba baba ƙaura yay da aikin gabansa kamar ba zaice komai ba, kusan mintuna biyu sannan ya sake duban Jawaad ɗin da maida dukkan hankalinsa ga resa, “Yanzu ina ɗayan yake?”. “Bamu ɗakkosa ba, yana acan gidan data zauna ɗin”. Baba ƙaura ya ɗauki zoben ya jujjuyashi sosai a hannunsa sannan ya ajiye, “Lallai kun samu damar amsar babban makaminsu, amma yaya akai kuka iya samun zoben nan? dan abune mai daraja ga mai shi”. Muryar Jay cike da ɗaci ya zayyane ma baba ƙaura komai da ya faru, harma da maganar fyaɗen da aketa bibiyar Bilkisu da shi da sai a randa ta cire zoben ta iya tunawa. Nannauyan numfashi baba ƙaura ya sauke, yace, “Ai dama na faɗa maka yarinyar akwai duhu dake biye da ita, wannan yana ɗaya daga ciki, amma akwai wanda ya fisa girma ma sai dai bansan minene ba, ku cigaba da gayama ALLAH shi mai komai da kowa ne, ba ita kaɗai ba abubuwa da yawa zasu fito dalilin wannan zoben, dan duk inda maishi yake hankalinsa baya a kwance yanzu, har dama duk wanda ke zagaye a ƙungiyar shaiɗancin, ka turata gidan ta ɗakko wancan ɗayan wurin, idan har ta tarar an hargitsa ɗakin data ajiye to lallai mai bibiyarta da wannan sheɗancin na fyaɗe yana cikin wannan gidan, kuma shaiɗaninsu sun tabbatar masa wurin data cira a farko yana a gidan, an basa damar ya nemosa gudun karku haɗasu kamar yanda muke buƙata, dan inda tace maka ta ajiyesa babu wani shaiɗani da ya isa ɗaukarsa saboda darajar Al-Qur'ani, shiyyasa shi akace ya ɗakko, inaji a raina kuma bazai gansaba insha ALLAHU, dan daya gansa komaima zasu iya aikatawa a kanku domin halakaku baki ɗaya musamman ma ita, suma kansu basusan taka mai mai inda ya keba bayan sanin yana cikin ɗakin kawai”. Jay dake ta tauna lip ɗinsa na ƙasa sai jinjina kai kawai ya keyi, ya furzar da huci mai zafi a bakinsa yana sake jinjina kansa. Baba ƙaura yace, “Idan ta ɗakko ku yanka wannan gurun, ku zira zoben da wurin guda biyu cikin gurin, zoben ya zama shine a tsakkiyar wurin, sai ku ƙulle gurun ku ajiye. wannan ba tsafi bane, ba kuma wani shaiɗanci bane, zakuga abinda zai biyo baya insha ALLAHU, dan cikin sauƙi zakuyita gano abubuwa masu ban mamaki da al'ajabi insha ALLAH..............✍ Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull