Kwai cikin kaya book 2 complete - Chapter 49
Kwai cikin kaya book 2 complete Chapter 49: Kwai cikin kaya book 2 complete Chapter 49. Page 52 ................Wata tarbar karramawar na sake iskewa wajen…
4,647 words
Page 52 ................Wata tarbar karramawar na sake iskewa wajen ƴan office ɗinmu nima, suka baibayeni mazansu da matansu suna mai tayani murnar aure da samun boss matsayin miji, su Ada iyayen gulma harda cewa na musu wayo nai wuf da boss. Ni dariyama suka bani wlhy. Na musu godiya da fatan suma ALLAH ya basu nasu musha biki. Fassara muku farin cikin dana tsinci kaina a ciki saboda dawowar su Nazifa station ɗinmu ɓata lokacine, muka sake rungume junanmu daɗi na ratsamu, a karo na uku mun sake kasancewa tare, ALLAH dai yasa muci amfanin wannan ƙawance har a gidan aljanna. Gaba suka tasani da sheri wai nayi ɓul dani kodai an samar musu baby?. Yinai kamar banjisu ba, da suka isheni sai nace suje su tambayo boss ɗin. Dariya suka sanya kowa na miƙewa duk suka koma mazauninsu da aka basu suma a office ɗin namu. Daga haka na samu lafiya daga iskancinsu. Ban tarar da kowanne aikiba, Ummie ta sanarmin ai duk oga Jabeer ya bata ta ƙarasa ayyukan dana bari, naji daɗin hakan sosai, saina miƙe ƙafa ina hutawata, da wannan lokacin nai amfani wajen zurmawa duniyar tunane-tunane kala-kala, ciki harda neman amsar yanda akai aurena da Yah Qaseem ya fasu aka maida shi kan boss, sai abinda na gani yau a ɗakina da duk nama rasa wane tunani ya dace nayi akan hakan, dan duk wanda nayi mai ƙyau sai naga bai zauna da al-amarin ba sam, sai marasa ƙyawunne keyin dai-dai. Ban sakejin ɗuriyar boss ba har muka fita sallar zuhur, bayan an idar mun fito su Nazifa ke faɗin ya kamata muje muci abinci, dan wasu a cikinsu ma basu ko karya ba suka baro gida, nima ɗin sai yanzun na tuna ban karyaba, ruwan tea ne kawai a cikin nan nawa. Shiru nai ina tunani, ni dai banda damar cewa zan bisu wajen cin abincin nan boss bai saniba, ni kuma bana wani son zuwa Office ɗinsa.... Taɓanin da akai ne ya katse tunanina, na sauke numfashi da kallon Rebecca da hannunta ke a kafaɗata, "Matar nan ina kika tafine? anata magana". Murmushi na mata ina tura hannayena cikin aljihun wandona, "Ba komai, kinsan zuciya da tone-tone, inaga kuje kawai banajin wani yinwa nikam". Har Ummie ta buɗe baki zatai magana sai Zuhrah ta katseta, "Kai inagama fa bai kamata ta bimu ba mijinta bai saniba gaskiya, tunda yana cikin station ɗin shima ta fara sanar masa, yanzufa ba da bace da muka saba shirmen mu kai tsaye". "Hakane kuma gaskiya" cewar Nazifa tana komawa kalar tausayi. Fahimtar inda ta dosa yasa muka kwashe da dariya mu dukanmu, dan itama dai bai wuce nata auren da ya rage six weeks ta tuno ba. Office muka koma bisa shawar Zuhrah, ita da Ummie kuma suka tafi sayo mana abincin.. ★★★★★★ Tunda suka baro cikin Barrack ɗin Jay ke ƙullawa da kwancewa, lumsassun idanunsa da launinsu ya gushe da ga farare zuwa ɗan jaa ya buɗe a hankali yana furzar da nannauyan numfashin da har sadiq sai da ya saci kallonsa ta mirror. Wayarsa ya ɗauka ya shiga daddanawa kafin ya saka a kunne dayin sallama, Munkaila na amsawa bai tsaya bi takan gaisuwar da yake masaba yace, "Zan tura maka wasu sunaye guda huɗu, inason daga nan zuwa yammacin gobe idan ALLAH ya kaimu a nemomin inda suke, sana'arsu ko aikinsu, abokan mu'amularsu na rayuwa dana kasuwanci". "Okay sir insha ALLAHU zanyi ƙoƙari, akwai ma waɗan can ayyukan na wajena guda biyu suma duk na kammala". "Saika haɗosu kawai". "Okay Sir" Munkaila ya faɗa cike da girmamawa. Suna isowa cikin station ɗin baima jira Sadiq ya buɗe masaba ya buɗe da kansa ya fita, sallamar Sadiq ɗin yay akan yaje zuwa biyar sai ya dawo, shi kuma kai tsaye massallaci ya nufa saboda lokacin salla yayi. Bayan an idarne ya fito zai koma office yaga su Bilkisu, sai dai su sam basu ganshiba dan hankalinsu baya ta wajen, yazo zai ɗan gittasu yaji hirar da sukeyi, ajiyar zuciya ya ɗan sauke da yaba hankalinsu, yanda yake musu kallon yara ƙanana bai zaton sunada zurfin tunani irin hakaba, dan daidai zai wucene maganar zuhura ke shiga kunnensa akan bilkisu bai kamata ta bisuba mijinta bai saniba. Sai da ya shiga office ya zauna sannan yay kiran gidan abincin da yaji su Ummie zasuje, umarni ya bada akan a basu duk abinda suke buƙata kar kuma a amshi kuɗinsu shi zai biya. Kasancewar sa babban Customer babu ɓata lokaci aka haɗa musu komai. Su Ummi basu san wainar da ake toyawaba, sudai sukaga an haɗa musu abinci kala-kala harma da wanda basuce ɗinba, amma dai-dai abinda zasu iya cinyewa ba almabazaranci ba, sannan akaƙi amsar kuɗinsu, da suka matsa da tambaya aka basu amsa akan an biya. Sosai sukaita mamakin da tambayar waye ya biya ɗin?, babu wani ɓoye-ɓoye aka sanar musu. Tunda suka dawo suka sanarmin yanda akai wajen sayen abincin sai naita mamaki akan yaya akai yasan zasuje? Shin kodai idanu ma yasa a sakamin ne? Kai bana tunanin hakan daga garesa, sai kace wanda bai yarda dani ba. waya na ɗauka na tura masa saƙon godiya da fatan alkairi.
Jawaad na zaune ya duƙufa aiki saƙo ya shigo masa, kasancewar Number da kowa ya sansa da itace ya zata akan wani aiki ne, dan ya kashe wayarsa da mutane masu muhimmanci kaɗai ke ciki, gudun kar Alhaji babba kosu Ummah su kirashi susan ya dawo, baiyi tunanin bily bace tunda bai saka Numbar ta anan ba, ɗauka yay ya duba, a mamakinsa sai yaga itaɗin ce ashe, yay murmushi da ɗan lumshe idanu ganin abinda ta rubuto, ajiye wayar yay kawai ya cigaba da aikin gabansa. Cak ya tsaya daga abinda yakeyi yana mai ƙure takardar daya saka sunayen da suka samo wajen Umm-Anum da ido, waya ya ɗauka da hanzari yay kiran Jabeer, yana ɗagawa yace, "Jabeer bama wani ya kawo min file ɗin matarnan". Daga can Jabeer ya amsa masa da "to". babu jimawa kuwa sai gashi ɗan aike daga jabeer yay knocking, damar shigowa ya bashi. Cikin girmamawa ya ƙame da sarama Jay kafin ya gaida shi, sannan ya ajiye file ɗin hannunsa. Ɗaga masa hannu Jay yayi alamar ya tafi kawai. Yana fita ya ɗauki takardar dake da sunayen bayan ya zagaye sunan macen dake a ƙarshe da jan biro, sannan ya buɗe file ɗin wajen Jabeer. tsai Jay yayi a zaune yana ƙarema sunayen kallo, sam babu wani banbanci hatta da sunan gari, waya ya ɗauka ya shiga dannawa. Kira yayi, bugu biyu aka ɗauka, bayan sun gaisa yace, "Malam Rabo, yanzun nan inason Ka binciko min Hajiya Safara'u a cikin ƙauyen nan naku, gashi nan zan turo maka cikakken sunanta da sunan mahaifinta nasan zaka gane, banason ɓata lokaci, yanzun nan nakeson kabar tasharnan ka tafi". "Insha ALLAHU kuwa oga yanzun nan zanbi motar datai lodi kuwa, koma na amshi mashin ɗin Madu naje yanda zanfi sauri". "Hakan yayi, ka zuba mai idan ka dawo sai a bashi wani abu shima". "To oga babu damuwa, sai ka jini". Jay na ajiye wayar ya maida dubansa ga file ɗin yana bin komai dalla-dalla, dogon nazari ya shiga akan abinda ke cikin file ɗin da wanda ke a ƙwalwar kansa, 'Wato na fahimci akwai wani kuskure da nayi ƙwarai da gaske' yay maganar a fili yana dafe kansa, takarda ya ɗauka ya hau rubutu, sai kuma ya ajiye biron ya kwanta jikin kujera da faɗawa duniyar tunani. Rasuwar gimba ta rikitashi ainun har yama manta abubuwan da ya kamata ace ya bibiyesu. Akwai Number ƙarshe da gimba yay waya da ita ya kamata yasan wanene ma? da wuri, sannan matarnan da gimba ya ambata ta gidan Alhaji kokino tabbas da itane suka taɓa haɗuwa a gidan Alhaji Kokinon, kuma itace tai aiki a gidansu kenan? Idan binciken ya zama dai-dai. Yaya akai hakan ta faru bai taɓa fahimtaba kai tsaye, kalamanta na wancan karon sun isa su bashi dukkanin amsar da yake buƙata. tabbas wani baƙon al'amarine da bai taɓa sakashi a lissafisa bane ya shigo masa kai yanzun nan musamman akan kashe Gimba da akayi yake tunanin da babu gaira babu dalili. Abinda yake tunanin ya faru akan kisan gimba ba shi bane ashe. Alhaji kokino sunyi abotar siyasa da Abba kamar yanda Ummuna ta faɗa, sun kumayi ta kasuwanci, indai har matarnan tayi aiki a gidanmu mizaisa ta koma can gidan tana aiki? Lokacin da aka sace Alhaji kokino itace ta bani dukkan sirrikan da nabi na samosa a hannun ƙaninsa, maganar gimba a al'amarin, yace akwai dalilinsa na zuwa aiki ƙarƙashina, na kuma nemeta zanji abubuwa masu muhimmanci. Idan har zan haɗa wannan maganar tashi da maganganunta na waccan ranar da muka taɓayi to lallai tamin farin sani kenan?. Miƙewa Jay yayi yana ɗan dukan tabirinsa da faɗin, "Yah ALLAH ". Ya sassauta tie.. ɗinsa yay ƙasa da shi, saima ya fincikesa gaba ɗaya ya jefa saman kujera ya shiga safa da marwa a office ɗin, duk da ac dake aiki hakan bai hanashi haɗa gumi ba, tun randa yasan akwai alaƙa tsakanin Alhaji kokino da Mr Gebrail ya saka ake bibiyar masa Mr Gebrail, ta hakane ya gano kuma alaƙar Mr Gebrail da ɗaya a cikin Uncle ɗinsa, idan ya dunƙule maganar waje guda hakan na nufin, Uncle ɗinsa, Mr Gebrail, Alhaji Kokino duk sunada a laƙa ta baɗini, dan a zahirance babu wannan alaƙar kota gaisuwa a tsakaninsu sai a ɓoye. dolene a daren nan a sato masa wayoyin Alhaji kokino, sai dai waye zai masa aikin? 'Dan dole ya kasance ɗan cikin gidanne zaiyi hakan' ya ƙare maganar a fili yana dafe kansa da furzar da huci mai azabar zafi. Tunanin kiran bilkisu ne yazo masa a rai, dan kosu Hafiz bayason sakasu a wannan case ɗin yanzu, saboda ya haɗa da family nashi, sannan yanada sarƙaƙiyar yarda da wani, kai tsaye zai iya zama ganganci, bawai dan bai yarda dasu bane, dan su Jabeer sun wuce duk hasashen mai karatu a garesa, amma ciki ba'a yisa dan abinciba kawai ai. Bilkisu na ɗagawa yace, "Ina jiranki a office". Ya yanke wayar. Kallon wayar kawai na tsaya yi da mamaki, to amma yanda naji muryarsa tamin kama da ta mai damuwa, miƙewa nai na fice, inajin Nazifa na tambayata ina zuwa? Ban sauraretaba na ɗaga mata hannu kawai. Koda nai knocking ba'a amsamin ba, dan haka kawai na shiga kaina tsaye. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ganinsa ba yanda nai zatoba, ya ɗago ido ya kalleni sannan ya maida ga abinda yakeyi. Takawa nai na ƙarasa garesa, murya a sanyaye nace, "Wlhy nazata ko baka da lafiya, ya aikin?". Baice dani komaiba ya nunamin wajen zama, shima zagayawa yay ya zauna a kujerarsa, yanda ya tsatstsareni da idanu duk sai naji na takura, na risinar da nawa ƙasa ina kallon yatsun hannuna. Numfashi naji ya sauke mai ƙarfin, kafin nace wani abu ya fara min bayani akan kiran, ya ƙare maganar da faɗin, "Dole ne musami wayar a daren nan, dan itace zata bamu haske akan komai da gaggawa, aikin nan kuma dole mu biyu kawai zamuyisa ni da ke kawai, ko su Aliyu banason na saka sai na gama fahimtar komai". Naji daɗin karrawarsa gareni sosai, dan banyi zaton hakanba, na gyara zamana, "To ina ganin mizai hana muyi amfani da cikin ƴaƴansa ko ma'aikatan gidan?". Shiru yay yana kallona da goga ƙasan biro akan laɓɓansa, kusan sakan goma ya janye ya maida kan takardar gabansa, ɗan rubutu yayi sannan ya sake ɗagowa ya kalleni, "Wannan shawarar taki tayi, amma babu wani ƙarin bayani a kanta?". Tsai na ɗan ƙarayi na tunani kafin nace, "Akwai, ya kamata wadda zamu saka ɗin cikin ƴaƴan nasa ta kasance mace, sannan mu nuna mata za'a cutar da shine shiyyasa muke son wayoyin na wasu awanni kawai za'a maido mata ta maida masa bayan mun saka matakan tsaro. Ko baiyi ba?". "Ihum inajinki cigaba" ya faɗa cikin lumshe idanu. Naɗan sauke ajiyar zuciya da cigaba da faɗin, "Idan muka amsa maimakon mu ajiye wayoyin a hannunmu kawai muyi copy ɗin komai na ciki sai a maida mata ta maida masa zuwa safiya". Lallausan murmushi ya saki yana ɗagemin gira ɗaya, "Ashe matar tawa ƙwaruwa ce?". Yanda yay maganar cikin zolaya yasa na rufe idanuna da tafin hannu ina murmushi. Yace, "Thanks Miemaa, da duk kaina ya kulle". Nace, "Haba dai, kaine kanka ke kullewa?". "Oh ni ba mutum bane? Duk ma ba kece kika rabamin hankali biyu ba". "Nidai babu ruwana". "Humm", ya faɗa kawai yana miƙewa. "Kinga tashi muje, da zafi-zafi ake dukan ƙarfe". Koda muka fito sai da ya shiga office ɗin Aliyu, babu jimawa ya fito riƙe da key ɗin mota, da kansa ya buɗemin na shiga sannan shima ya zagaya ya shiga, nidai addu'a nake a raina karyay gudu damu, yanda naci abincin nan na ƙoshi matsala za'a samu ai. Kasa daurewa nai na roƙesa karyay gudu dan ALLAH, ƙin tankamin yayi, sai ma waya daya ɗauka yay kira, kasancewar a Hans free ya sakata sai naji duk abinda suke faɗa, na fahimci da wani ma'aikacin gidan Alhaji kokinon yay magana, dan ya faɗa masa gamu mun taho ya fito mu haɗu a bayan layin. Dai-dai saitin wani shagon saida kayan abinci dake farkon layin muka tsaya, wani dattijon tsoho ya fito daga shahon, kallo ɗaya naga yayma motar ya ɗauke kansa, sai kuma naga ya buɗe ya shigo baya. Motar boss ya harba gaba batare da yayi magana ba. Nidai mamaki nake tayi a raina, wannan aikin namu gaskiya saida jajircewa da cire tsoro, sai kuma ka iya kowanne irin salo na mutane masu wayo. Gaba ɗaya muka fita daga layin muka shiga wani, shima muka fita muka shiga na gaba, yana tuƙin yana kallon mirror, na fahimci dubawa yake yaga ko ana binmu, ganin babu wani mai bibiyarmu sai yay fakin gefen babban titi da muka fito. Sai lokacin ne dattijon yay magana. "Na tabbata babu wani mai binmu insha ALLAH". Kashe motar yayi ba tare da yace komaiba, ya ɗan kalleni sannan ya juya yana kallon dattijon. "Wannan itace matata, sunanta Bilkisu". "Masha ALLAH, kai ALLAH ya sanya albarka ya bada zuri'a tagari". "Amin" ya faɗa, ni kuma na juya muka gaisa da shi yanata sakamin albarka. "Baba wannan karonma aiki ya sake kawoni gidanku, kuma ina buƙatar taimakonka kamar wancan karon". "Karka damu ɗana, zan baka dukkan taimakon da kake buƙata insha ALLAHU". "Nagode baba, akwai dattijuwar mai aikin nan da naji kuna kira maman yara ko tana gidan har yanzun?". Jimmm mai gadi yayi kafin ya sauke numfashi, "Gaskiya bata nan, a ƙalla zata kai kusan wata biyu ma kenan bata gidan nan". "Aiki ta ajiye kenan?". "A'a bata ajiyeba, mudai bamusan miya faruba, rana tsaka ɗanta yazo yana nemanta wai kwana uku bai samunta a waya" kallonsa Jawaad yake cikin nazari, "Kana nufin Yazeed?". "Ƙwarai shi kuwa, to dalilin zuwan nasane muka fahimci muma bata gidan, ita dai Uwargida tace ta tambayeta zataje gida wajen rasuwar ɗan yayarta, to nidai ALLAH shine shaida ranar data cika kwana uku da tafiya naganta da idanuna ta dawo gidan lokacin ina sallar isha'i, to amma abin mamaki sai naji ana cigiyarta bayan kwana biyu wai bata gidan". "Ban gane bata gidanba? Kai kuma bakaga fitarta ba?". "Wlhy ban ganiba yarona, dan ita macece mai yawan barkwanci inhar zata fita a gidan nan kota shiga saimun tsokani juna, to a randa ta dawo da yake salla nakeyi sai ban kawo komai a rainaba, abinda ma ya ɗauremin kai da sukace su basu gantaba randa ta dawo ɗin". Shiru boss yayi alamar tunani, dan haka nikuma nace, "To amma baba a wannan daren kana tunanin zata iya fita?". "Gaskiya bazata iyaba ƴata, dan maman yara ma tana da ciwon ƙafa bata cikason yawan kai kawoba". "Hakan na nufin tana cikin gidan kenan kokuma an fita da ita a daren, ko kaine idonka bai nuna maka dai-dai ba?". "Wlhy bana ko tantama itace ta dawo da mangaribar nan, to ƴata wazai fita da ita kuma sai kace wata kaya batare da an gani ba?, shaiɗanin daya taɓa kwatanta hakama mijinki yasa an kaisa gidan maza ai". Murmushi nayi kawai, na ɗan juya na kalla boss ɗin dake saurarnmu sannan na maida ga baba, "Baba a wannan ranar mota nawa ta shiga gidan ta kuma fita bayan dawowar maman yara?". "Babu wanda yazo tunda Alhaji baya gari ma, sai wani yaro ɗan dogo baƙi mai dogon hanci da ya kanzo lokaci-lokaci idan Alhaji na nan, to ni a ranarma da yazo ɗin saida na sanar masa baya nan ai Alhaji, sai yace ai ya sani saƙo zai bama hajiya inji Alhajin. Daga haka ban sake tofa komaiba na barshi ya shiga ni kuma na shige ɗakina, to baifi mintuna goma sha biyar da shigaba ma naji yana horn nazo na buɗe masa ya fice". "Kasan sunansa baba?" "A'a gaskiya ƴata, ban saniba wlhy". Waya boss dake saurarenmu ya ɗauka ya shiga daddanawa, kafin ya miƙama baba wayar yana faɗin, "Shine wannan?". Amsa baba yay ya kalli hoton, cikin jinjina kai da murmushi yace, "Tabbas shine kuwa ɗana". "Baba ka tabbata?". "Babu tantama a zancena". "Shikenan mun gode, bara mu maida kai, sai dai zamu iya dawowa gareka a ko wane irin lokaci". "Babu damuwa wlhy ɗana duk sanda kake buƙatar wani abu ka kirani". Godiya muka sake masa, ya tada motar yay reverse, a wani wajen muka saukesa saɓanin inda muka ɗaukesa. Jin yayi shiru sai na ɗan kallesa, "Hoton wanene ka nuna masa dan ALLAH?". "Zaki gani yanzun" ya faɗa yana karya kan motar muka shiga wani layi. A ƙofar wani gida madaidaici yay fakin, ganin zai fita nima sai na buɗe na fita. Mun gaisa da samari uku da alama ta nuna suke tsaron gidan, yanda suke gaishemu cikin girmamawa nasan lallai shine ya ajiyesu. Ɗakin farko dake a gidan muka shiga, inda muka iske matashin saurayi zaune, shigowarmu ta sakashi miƙewa yana murmushi da mana sannu da zuwa. Na buɗe baki zan amsa kawai naji tass!!!. Idanu na zaro baki a hangame ina kallon boss da ya saukema saurayin mari, ban gama fita a mamakinba naga ya hau dukansa. Dukansa yake ta ko ina, a take jikina ya fara rawar tsoro, nasa hannu na rufe fuskata ina ambaton "innalillahi....." da sauri na buɗe fuskata jin ƙarar ɗana kunamar bindiga, nai masifar sake zazzaro idanu waje ina faɗin, "Boss badai kashesa zakai ba?". Harara ya balla min ya ɗauke kansa yana huci. A tare muka saki ƙara ni da saurayin saboda harbinsa da yay a ƙafa, zufa ta shiga rige-rigen karyo masa, jikinsa na wani irin rawa, ko kallon inda nake baiba ya ranƙwafa kan saurayin yana hure bakin bindigar dake ɗan hayaƙi da faɗin, "Kaga bindigar nan cike take taf da alburusai, kuma idan zan ƙarar dasu tas a sassan jikinka babu mai tambayata yaya nai da su?, wannan harbin danai maka na ƙaryar daka mince, idan wata ta biyo bayanta yanzun kuma wlhy saina faffasa gaɓɓanka ɗaya bayan ɗaya da alburusan nan kafin na aikaka lahira dan ubanka. Ina kakaita itama?". Jikin ɓaleru na rawa ga jini na malala a ƙasa cikin hakkin kuka da azabar shigar harsashi yace, "Bansan wacce kake maganaba oga, dan ALLAH karka kasheni, nayi kuskure a farko amma wlhy bazan sake kwatantashi ba". "wani rainin hankalin zaka sakemin?" ya faɗa a taƙaice yana sake ɗaure fuska da ɗana kunamar bindigarsa. "A'a wlhy oga ba haka bane ba, na tuba dan ALLAH zan faɗa maka komai, bata a garin nan". "Amma ranar ca kaimin baka da alaƙa da Alhaji kokino, bama ka sanshiba ko?" ya faɗa yana ɗora masa bindigar a saman kai. a take jikin ɓaleru ya ƙara ƙarfin mazari, harya jiƙe wandonsa da fitsari, "Oga kawa ALLAH da MANZONSA karka kasheni, ka yafeni, komi kake buƙata yanzu wlhy zan makashi, harma abinda baka saniba zan faɗa maka". Ƙafa Jay ya saka ya danna ƙafar ɓaleru daya harba. Ya sake sakin wata wahalalliyar ƙara jikinsa na karkarwa. Da sauri nazo na riƙe hannunsa ina hawaye. Janye ƙafar tasa yay ya juyo yana kallona da wani murmushi irin na tsagwaron muguntarnan, ya lakacemin hanci da faɗin, "Ki rage wannan tausayin malama". Rungumesa nai da sauri ina faɗin, "To dan ALLAH kayi haƙuri ka barshi haka tunda yace zai faɗa mana". "To na barsa" Jay ya faɗa yana ballama Ɓaleru da keta kukan wahala harara da shafa bayan bily data lafe a jikinsa. Sai da ya tabbatar tayi shiru sannan ya ɗagota ya share mata hawayen tas da sumbatar goshinta. Jikkata ya amsa ya buɗe, ya fiddo biro da ɗan littafi dake ciki ya jefama ɓaleru, duk da halin da yake ciki haka ya ɗauka ya rubuta masa address ɗin. Yana sharar hawaye da sauke numfarfashi yace, "Oga gidan akwai matakan tsaro sosai, hanyar da zaku iya fiddota cikin sauƙi itace kiran masu tsaronta da wayar Alhaji kokino". Uffan baice masaba, saima waya daya kira, mintuna kaɗan saiga ɗaya daga cikin masu tsaron gidan ya shigo. A daƙile yace, "A cire masa wannan bullet ɗin a tsaida jinin". Da girmamawa ya amsa da "Yes Sir" hannuna ya kama kawai muka fice, sai binsa nake da kallo da ɗunbin mamaki, ban taɓa zaton tsaurinsa ya kai hakaba, nikam tsoroma yake ƙara bani yanzun. Sai da muka fara tafiya sannan yay magana hankalinsa nakan tuƙi, "Tunaninmu na samun wayar kokino yana a kan hanya, wannan tsoron da tausayin naki kuma dole ki cireshi dan aikinmu baya buƙatarsa". Kallonsa nayi sai naga bani yake kallo ba, yama fuske abinsa tamkar bashine yay maganarba. Nima bance komanba amma sai juya lamarin nake a rai, 'sai kace a cikin film? kai anya kuwa ban sako kaina inda yafi ƙarfina ba? Wani ƙarfin zuciyar ai sai maza dole'. Da wannan tunanin a raina muka iso wani waje saɓanin station da nai tunanin zamu koma. Fakin yay sannan ya ɗauka waya yay kira. Yanda ya kwantar da murya tamkar ba shine ya gama hargagi yanzunba sai ya bani mamaki, jin kuma da mace yake maganar dan a hans free yasa sai naji wani abu ya dunƙulemin a ƙirji na takaici. Ƙin kallona yay ya cigaba da wayarsa, "Kiran da nai miki yanzu ai ya tabbatar miki ban manta da ke ɗinba". Cike da yanga daga cikin wayar akace, "Kai dai kanason kare kanka, shekara biyar ai ba kwana biyar bace". Baki naga ya wani taɓe da ɗauke kai kamar yana a gabanta, a zahiri kuma sai ya sake kwantar da murya da faɗin, "Tom nayi laifi, amma nima bana ƙasar ai, yanzu ma dai akwai wani taimako da zakimin akan Dadynki". tace, "To yanzu na fahimci dalilin kiran, tunda ba taɓa kirana kayiba, inma na kira baka ɗagawa" "Humm" ya faɗa batare da ya bata amsar zancen nata ba, "Yanzu dai bazakimin taimakonba na nema wani?" "Ah haba, kaima kasan bazan iyaba ai, ko karan gidanka ka aiko da buƙata ai zan biya masa balle kai ɗin da kanka" "Yayi" ya faɗa a taƙaice, sannan ya cigaba da faɗin, "Wani ƙulli da ake sonma Dadynki mukeson kwancewa batare da ya saniba, dan haka mukeson ki ɗebo mana dukkan phones nashi a daren yau zuwa safiya insha ALLAH za'a dawo dasu ki maida masa batare da ya saniba". Jimmm tai alamar tunani, kafin ta sauke numfashi da faɗin, "Tab wannan aikin baiyi girmaba kuwa Jay, Dady fa ko Momy bai bari ta taɓa masa waya balle mu, to ta inama zan fara hakan?". "Yanda za'ai ɗin ke ya kamata kiyi tunani, inba hakaba komai zai iya faruwa da shi, idan kuma kin zaɓi komai ya farun akan ki bada haɗin kai a taimakesa kafin ya farun to babu damuwa sai anjima....." da sauri tace, "A'a tsaya-tsaya, ka bani lokaci zanje nayi tunani, nanda magriba idan da yuwuwar hakan zan turo maka saƙo, dan matsalar shine kasan shi business yake, komai dare kuma amsa waya yakeyi, to tayaya za'a ɗauka har sai zuwa safiya a maido bai fahimta ba?". "Kidaiyi ƙoƙari mugani". "Shikenan sai ka jini" ƙitt ya yanke wayar tare da juyowa ya kalleni. ɗauke kaina nai gefe batare da nace komaiba. Shima ɗin baice min ɗinba, saima sallama da naji ya sakeyi alamar wata wayar. kiran oga Hafiz yay aka yayma su Jabeer magana su zo su samemu a office ɗin da aka buɗe na karɓar cases ɗin masu fyaɗen nan, dan yanada buƙatar sanin komai a yau ya fasa gobe, amma kafin sannan su fara turo su Ummie sannan, kafin su su biyo bayansu nanda mintuna talatin. Duk da abin ya bama Hafeez ɗunbin mamaki sai bai tambayi dalili ba ya amsa masa da to kawai, dan yasan zai musu bayani. Wayar ya ajiye yana sauke numfashi, ya kamo hannuna cikin nashi tare da saka ɗayan hannunsa ya juyo da fuskata garesa. "Na matan ne ya motsa?". Yay maganar gab da fuskata yana wani ɗagemin gira. Fuska naɗan ɓata nace, "Miye na mata?". "Kishi mana" ya bani amsa da lakacemin hanci. Bansan sanda murmushi ya suɓucemin ba nace, "Nidai ai ban faɗaba". "Ai shi ba sai an faɗaba, a fuska ake ganoku". Mintsininsa nai a hannun da yake murzamin cinya. Ya ɗauke da sauri yana faɗin, "Ouch!, muguwa". Dariya na ƙyalƙyale da ita, dan yanda yay da fuska kamar wani ƙaramin yaro. Murmushi Jay yay yana kwantar da kansa a kafaɗarta da lumshe idanu dan dama soyake yaga ta dawo cikin walwalarta. Babu jimawa sai gasu Zuhrah sun iso, cayay na fita na samesu mu shiga wajen tare, shi zai jira su Oga Aliyu. "Anacan anashan soyayya an barmu" cewar Ummie sanda na iso inda suke. "Ya ranki ne?" na faɗa ina mata gwalo. Dariya su Zuhrah suka sanya mana, Ummie kuma tace, "Fari ƙal, muma ai tana tafe garemu, a lokacin wasu sun tsufa". "Ko kuma mun zama gwanaye ba" na bata amsa ina mangare ƙeyarta. Yanayin yanda aka tsara wajen ya birgeni sosai wlhy, ga matansu Oga Jabeer sunata aiki tuƙuru, gaisuwa mukai cikin girmama juna suna tsokanata wai har mun dawo daga Honeymoon ɗin. Dariya kawai nayi bance komaiba. Muka rungume juna da Amina ina tambayarta ya mama da yaya sule?. Babu jimawa da zamanmu su boss suma suka shigo, bayan anyi ɗan gaishe-gaishen juna matar Jabeer data kasance shugaba ta fara mana jawabin cigaban da aka samu musamman ma ni da Boss da bamusan yanda ake ciki ba. "Ƙasarnan danƙare take da cases na matsalolin fyaɗe, wasu sunma kai kotun amma rashin gata yasa an watsar da shari'oinsu, daga baya an saki waɗanda suka aikata laifin, wasu ko tsoro yama hanasu fitowa su faɗa. A yanzu haka dai munada ƙararraki kusan saba'in da uku a cikin kwanaki goma sha shidda kacal da shelanta ƙunyar, mun gama bincike akan ashirin da ɗaya kamar yanda muka sanar maka, mun tabbatar da gaskiyarsu kuma harma munsa an kama wasu daga cikin masu laifin, wasu kuma muna kan fakonsu, sai cases Goma sha huɗu masu kamanceceniya da irin wanda muke nema". Kai Jawaad keta jinjinawa yanajin daɗi da ƙaunar abokan nasa, ya ajiye file ɗin hannun nasa da matar Hafiz ta bashi yana gyara zama, "Wace shawarace da ku yanzu akan goma sha huɗun da muka samu? Dan kunga idan muka haɗa da baƙwai ɗin dake ƙasa sun zama ashin da ɗaya kenan". Aliyu yace, "Hakane, ni dai a nawa ganin shine mu fara bincike akan gidajen da duk abin ya faru, dan abinda zai baka mamaki da ɗaure kai waɗanda abin ya faru dasu dak ƴaƴan masu gidan ne, ko ƴaƴan ƴan uwa, kuma babu gidan talaka, ƴaƴan talakawan da tsautsayin ya hau kansu duk masu aikine a gidajen". "Shawararka tayi Aliyu, yanzu zamu rarraba yaranan cikin ofisoshin waɗanda abin ya faru a gidansu a gobe idan ALLAH ya kaimu, kowacce zata lurar mana da abu biyu, na farko zobe, na biyu sana'ar mutumin ko aikinsa". Duk kai muka jinjina masa na gamsuwa, daga haka aka ƙara ɗan tattaunawa muka fito bayan an damƙama kowa aikin da zaiyi.............✍