Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 12

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 12

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 12: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 12. Da cikakken kuzarinsa ya miqe daga jikin bishiyar,ya…

3,314 words

Da cikakken kuzarinsa ya miqe daga jikin bishiyar,ya kuma tsaya qyam da qafafunsa yana sake zube hannuwansa a aljihun wandonsa sosai yana sake zube idanunsa akan gine ginen.

Iska sosai ya zuqa yakai hunhunsa sannan ya furzo da ita daidai sanda lissafinsa yazo kan gida na shida.

Idanunsa cak ya tsaida akan gidan yana qare masa nazari. Kowanne gida dake layin yana da sassauqan fenti da bai tsufa ba bai kumayi sabunta da yawa ba,amma shi wannan gidan sabon fenti gareshi. Kowanne gida akwai sassauqan haske dake nunawa kadan,alamun wani girin fitilunsa a kashe suke,wani gurin kuma a kunne,amma wannan gidan dundum yake,ba wani alamun haske komai sirantarsa a tattare dashi.

Akwai mazubin shara gaban kowanne gida don inganta layin,amma daya lura sosai babu mazubin sharar a gaban wannan gidan......

Sake zagayawa yayi da idonsa sauran gidajen kafin ya sake maida dubansa gaban gidan. Daga alamunsa daga waje yana da yalwa da wadatar da za'a iya shigar da mota cikinsa kamar sauran dukkanin gidajen unguwar da layin,amma motar tana fake a waje ita daya qwallin qwal......

So samu ya qarasa jikin motar,ya duba wadanne lambobi ne a jiki,duk da motar daya taba gani anbi diddigin lambobin jiki,saidai duk zurfin binciken da sukayi basu samo komai a kanta ba,hasalima plate numbers din isn't valid a region na agadez dama nijer gaba daya.

Saidai kuma a tsari irin na aikinsa yasan hakan zai iya zama da hadari......takawa koda d'ani guda ne daya inda yake tsayen zuwa gaba,komai zai iya faruwa,wanda inda sabon ma'aikaci ne shi ko maras gogewa yasan abinda zaiyi kenan,saidai a aiki irin nasu......akwai wasu damarmaki da kana ji kana gani zaka barsu hakanan su wuce su subuce maka saboda wani dalilin da yafi wannan qarfi da amfani.

Sake bin layin yayi da kallo,akwai dan kiosk qwara biyu tal,wanda a binciken layukan da yayi na wancan lokacin dukkaninsu suna saida qananun abubuwan da shiga kasuwa zai zamewa mazauna unguwar wahala. Sai ya janye manyan idanunsa da suka rusuna kadan,ya saka yatsansa cikin kunensa,take wani red light yayi blinking na wasu sakanni sannan aka fara magana.

"Ina buqatar beeno yanzun nan,a bunu street,banaso ya haura mintuna biyar don ina hanyar barin layin.......gida ne number ta shida.......ya zama shine target din" Ya qarasa fada yana kuma gimtse kiran kai tsaye.

Ya samu iya abinda yake buqata a nan din,yanaso yayi gaba kafin wadanda suka wuce din su dawo ko zai samu nasarar sake samun wani abun da zai bashi haske daga hanya har zuwa cikin gidan sarautar,sai ya maida hannayensa zuwa ga aljihun wandonsa ya soma takawa a nutse da kuma lura yana barin gurin.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 20*

*MAMMINA*

Tun daga farfajiya ta biyu take iya jiyo sautin almaz cikin hargagin data tabbatar tashin hankali akeyi dashi. Idonta ta lumshe kafin ta budeshi cikin bacin rai gami da jan qaramin tsaki.

"Kamar muryar yaron nan nakeji" Mammina ta fadi don samun tabbaci.

"Shine......ba shakka shine" Ta fisu ta fada tana jinjina kai. Shuru ya biyo baya,tamkar mammina din ba zata ce komai ba kafin ta sake magantuwa.

"Banda target ne cikin rayuwarsa gaba daya......banda wata shiryayyar qaddararsa ce data ahalinsa ke tunkararsa wadda ba makawa saita samesu......tabbas da na canza yaron nan". Wani murmushi ta fisu ta saki

"Dabi'unsa zaki canza bawai shi din zaki canza ba,aikinmu na yanzu shine mu canzashi zuwa yadda mukeso din,mu canzashi zuwa kalar mijin burin AKHNAN.....abun harinmu shine ya mamayi rayuwarta ta soshi fiye da yadda takeson SULTANE dole muyi sadaukarwa me yawa akan hakan don tabbatuwar wannan MANUFAR don samun zuri'a daga garesu cikin sauri kaman yadda buri da mafarkinki suke......ki barni dashi" Tafisu ta fadi suna buda qofar da zata sadasu da ainihin gidan,don tuni sunsan da zuwanta,anbar komai kuma ta yadda zata samu daman shiga ciki ba tare da kowa ya fito ko yazo ya bude mata ba.

"Na rantse idan baka bani ba......zan kubce muku irin kubcewar da ba zaku taba samoni ba!!!" Ya fadi da wata tsawatacciyar muryar data sanya wata mummunar faduwar gaba saukarwa mammina......muryar ta cilla can qololuwar cikin tunaninta,ta lalubo wani sauti da yayi sak da sak da wannan sauti da muryar da almaz.

"Akwai wani dan tasirin kamanceceniya a sanda yake magana cikin fushi?" Ta yiwa kanta tambayar data saka zufa tsatstsafowa a goshinta.

"Tafisu.....banaso ya sake magana cikin fushi.....banaso na sakejin yanayin sautinsa yana fita cikin fushi"

"Na fahimta" Tafisu ta fada tana jinjina kai wani kalan murmushi na fita saman fuskarta. Wannan murmushin wani kalar abune da a wasu lokutan yake bawa mammina mamaki. Duk yadda takai ga iya wasan kwaikwayo cinye firgici da damuwa.....maye gurbin tsananin tashin hankali da sassanyan murmushi tafisu ta fita iya buga wasa ta wannan bangaren.

"Amma kuwa da ka yiwa kanka da kanka asarar tulin arziqi......tulin jin dadi maras yankewa da yake jiranka....." Muryar tafisu ta ratsa hargagin almaz da wani irin murmushi.e taushi saman fuskarta tana dubansa.

A fusace ya waiwayo,suka zubawa juna ido shi da tafisu suna yiwa juna kallon kallo har sai daya janye dubansa yana furzar da iska daga bakinsa,wannan ya bawa tafisun daman isa gabansa. Zamewa tayi cikin salo na sarauta ta durqushe a gabansa cikin tsananin girmamawa tamkar tana gaban sultane

"Ranka ya dade....... Kai da kake shirin zama suruki ga qasaitaccen sarkin africa irin sultane?.....kai da kake shirin mallakar da jagorantar gurin da yafi ko ina kawo maqudan kudade kaf dukiyar surukinka?......kai da kake shirin zama mutum me qololuwar martaba?....ina kai ina wadannan tarkacen a yanxun?......" Idanu ya zubawa tafisu yana jin wani abu me kama da girma girma yana sauka saman zuciyarsa.......tasirin girman ya soma danne tasirin fushinsa,yana saukar da wani sassauci a dukka zafin da zuciyarsa da jikinsa ma ya dauka. Ta fahimci hakan tafisu,bama ita kadai ba hatta da mammina din,saita dan dago a hankali.

"Inda zaka nutsu ka kwantar da hankalinka......ka bamu aron nutsuwarka da kamalarka na wani dan lokaci......gaba kadan daki guda zaka mallaka na dukka kalar kayan da kake kwadayin sha kakejin labarinsu kuma baka taba samunsa ba......ko daga wacce qasa yake kuma ko daga wanne yanki ake kawoshi sarrafashi ko nomashi......amma fa lallai sai kayi haquri na wani dan taqaitaccen lokaci". Idanunsa ya dauke,yana jin wani girma yana saukar masa.

Karon farko da cikin dabi'arsa yakeso da buqatar wannan girmamawar da bai taba samunta ba,a yanzun sai tazo masa da wani irin yanayi da yaji kome akeso yayi zaiyi,indai zaici gaba da samun wannan girmamawar,don haka ya koma ya zauna dabas saman daya daga cikin tsadaddun sofas din dake masa dadin kwanciya sosai tun xuwansa gidan.

A sace ta kalli mammina,mammina din ta jinjina kai cikin tsananin mamakin yadda tafisu ta iya sarrafa komai cikin qasa da mintuna biyu kacal. Almaz din dake da wahalar sha'ani,tsananin taurin kai da rashin jin magana,kafiya da tsaiwa cak akan abinda yasa kanshi amma ta iya cinsa da yaqi haka da sauri?.

Qarasowa tayi ta zauna kan kujerar dake fuskantarsa tana dubansa. Yayi fresh yayi kyau a kwanakin kamar yadda ta buqaci ganinsa haka,saita dauke idanunta ta maida kan tamim dake tsaye,wanda tunda suka shigo bai sake cewa komai ba.

"Kana iya komawa masarauta,yau a ciki zaka kwana,akwai yiwuwar sultane ya nemeka da safe koda asubahi" Kai ya jinjina yana rusunawa cikin girmamawa,sannan ya juya yana nufar hanyar fita zuciyarsa tana matsewa guri guda.

Shuru dakin ya dauka na wasu sakanni,kafin ta fisu ta matso tana ciro wata jaka daga qugunta. Wareta tayi ta fito da wasu takardu da kudade ta zubesu saman table din data jawo zuwa tsakiyarsu.

"Muna maka murna......zaka samu 'yanci fiye da yadda tsuntsun dake shawagi a sararin samaniya ke samu".

Kalmar 'yancin da tafisu ta ambata itace taja hankalinsa har ya dago da kansa da a dazu suke kallon sama. Yanci itace kalmar da yafi buqatar ji,yasha gwada yin nisa da rayuwarsa dama duk mutanen da ya sani don yayi rayuwar tasa a yadda yakeso cikin sakewa.......amma baya nisan zango yake sake tsintar kansa cikin wadannan mutanen dai da yake tunanin ya yiwa nisa. Duk inda ya motsa rayuwarsa kamar ana monitoring dinta ne.......rayuwar sa tana zagaye ne da wadanda keda iko a kansa wanda ba kasafai ya fiya banbancesu ba.....kamar yadda yake rayuwar ba tare da sanin hagunsa ko damansa ba,daidai da rashin daidai dinsa ba.......saidai ba abinda ya gane daga qarshe illa KUDI.

Ya fahimci sune suke da ikon sarrafawa mutum komai yadda yakeso.......ya fahimci sune suke da qarfin ikon sawa ayi koda ba'aso,a kuma bari koda ba'aso ba,don haka har ransa yakejin ya karbi tayin wannan aikin don kaiwa ga buqatarsa,wannan ya sanya ya miqe ya zauna sosai yana duban bayanan da tafisu ta soma masa kan takardun da adadin abinda zai iya zama nasa.

Murmushi kawai yakeyi yana jin mafarkansa suna budewa zuwa reality. Aikin duka ya masa wani irin sauqi,don tako ina ribarsa yake hangowa ba wata faduwa a ciki. Matsalarsa da damuwarsa qwaya daya ce.......kayan mayensa da suka zame masa jini da tsoka.......kayan mayensa da baisan yadda zai sarrafa kansa ya haqura dasu na watannin da suke fadi ba. Amma dukka yana hangen ba laifinsa a ciki,dasu aka ciyar dashu aka shayar dashi kuma aka tufatar dashi tun haihuwarsa. Tunda ya fara wayo,tunda ya fara sanin me ake kira da DUNIYA da RAYUWA sune ababen karin kumallonsa.....abokan rayuwarsa safiyarsa zuwa darensa gaba daya. Wuninnika da darare masu yawa suna zuwa su shude ba tare daya sani ba,ba tare da yasan me ya faru a cikinsu ba,ba kuma tare da yasan kwanakin sati nawa ya shafe a bugensa ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Ci sha da sutura dukka ba matsalarsa bane.... Duk da tun tasowarsa baya aikin komai.....bai iya aikin komai ba.....ban taba shiga makaranta ba,bai taba riqe biro ko fensir ba sai sanda ya cika shekara ashirin cif.....aka masa mummunar tarkiyar da baisan dalilinta ba,baisan kuma daga ina abun yazo ba aka koya masa rubuta sunansa da sauran abubuwan da zaka tsammaci karatu yayi.....daga nan ya koma rayuwarsa ta baya,amma bai taba rasa lafiyayyen abinci da sutura ba. Kaman yadda dakinsa yasha banban da dakin kowanne d'an gata,saidai baisan cikakkiyar ma'anar rayuwarsa ba.

Suturunsa masu kyau da tsada da cimarsa ya sanya wasu suke kallonshi a ne girman kai. Girman kan da baisan ma ma'anarsa ba. Kawai dai ya sani yana da tsananin zafin zuciya,ba ruwansa da kowa don bayason raini ko maganan banza,yanzun nan ya yima mutum dukan mutuwa ba komai bane a wajensa,kuma ba wata hukuma dake iya kamashi,wanda Shima baisan me yasa hakan take faruwa ba.

*HAISAM*

Daga nesa dashi cikin duhuwar yake iya hasashen wani kalar motsi a tsakanin wasu shukoki da aka qawata street din dasu,idanunsa ya qanqance kadan yana kaifafa ganinsa gami da rage hanzarin tafiyarsa,cikin qwarewa kuma yake sake kusantar inda yake iya hasashen motsin,saidai kadan ya rage ya isa kunnuwansa suka dauko masa motsin wani sauti daga bayansa wanda kwanyarsa ta bashi akwai 'yar qanqanuwar tazara a tsakaninsu. Da hanzari idanunsa suka bashi gurin tsaiwa daya dace,hakan yayi ya saje da duhun gurin yana duban agogon dake d'aure a hannunsa yana irga taku da daqiqun da suke shudewa har zuwa sanda yaji an wuce ta gabansa. Idanunsa ya aza sosai yana bin bayan wanda ya wuce din da kallo yana lissafa fadin kafadunsa zubin tafiyarsa da komai take kuma kwanyarsa ta harba masa BABBAN TAMIM ne.

"Asitti maal hojjechaa jirtu?" Tataccen yaren oromo ya sauka a kunnensa da salon tambayar ME KUKEYI A NAN? tamkar yana cikin qasar Ethiopia yanki oromo. Hannun nasa ya sauke da wani irin hanzari. Sautin babban tamim ne......hakan yana nufin shima YAREN OROMO NE?.

"Dhiifama,nuti Madame eegduu(muna neman afuwa,uwargida muka rako)" Muryar wani ta bayar da amsa,wanda take ya daidaitata da muryar tamim qarami.

"Tsaiwarku a nan kuskure ne,kuma hadari ne,don lokaci ne na hana zirga zirga ga kowanne mazaunin cikin fada.......idan lokacin dawowarta yayi kowacce hanya zata kasance mata a bude.....muje ciki zan saita hakan" Tamim ya fadi sannan kuma takunsu ya dadu alamun dukkaninsu suna komawa ne ciki.

Wani irin mamaki ya hanashi motsawa daga gurin har zuwa shudewar wasu mintuna daya tabbatar ba za'a samu wanzuwar kowa a gurin ba,koda me jira da bibiya ne sannan ya ciro jikinsa daga gurin yana takawa a nutse yana nufar katafaren ginin masarautar dake gabansa.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE PAGE 21* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ____________________________

Kenan ba mutum daya ba kawai.....ba kuma mutum biyu ba,akwai qarin wasu mutanen dake jin da amfani da yaren oromo?.

Yana takawa a nutse amma yanason tantance waye asalin TAMIM cikin mamallaka sunan guda biyu?. Suna ne baqo da ba kasafai aka fiya sakashi ba cikin qabilar oromo......tabbas dole akwai mamallakin sunan na asali.....akwai wanda kuma ba asalin sunansa bane.

Cikin kulawa ya zagaya ta shiyyar da yakan koma cikin gidan. Ya tarar da HILAL tsaye bakin qofar cikin shiga ta masu tsaron qofar kamar yadda suka saba tsaiwa da kuma sanya suturarsu,ya dage masa qarfen tsaron da akan rufe qofar cikin matuqar girmamawa yana bashi hanya. Hannunsa kadan ya motsa alamun yabawa hilal da jinjina yana wucewa cikin gidan.

Kansa tsaye ya wuce sashensa yana qoqarin jingine tunanin don bibiyar beno akan aikin daya turashi. Agogo ya kalla,zuwa sannan ya tabbatar beno yana dab da isa gurin indai ya isa akan daidai lokacin da ya tsara masa,don haka ya qara sauri yana murza key ya buda sassan yana shiga yana motsa labbansa da sallama.

Saman kujera ya hangeshi,abdii ne kwance rigingine,ya kife wani littafi saman qirjinsa da alamu suka nuna yana tsaka da karantawa bacci ya daukeshi.

Can qasan ranshi yayi murmushi wanda sam bai nuna ba koda saman labbansa,ya taka a hankali ya zare littafin yana ajiyewa gefe.

Ko yaushe abdii yana maida kansa yaro saboda shi. Koda yaushe abdii baida zuciya indai a kansa na,baya fushi sam,ko me zai gaya masa don yayi nesa dashi kaman yadda ya buqata baya yarda da hakan,baisan wanne irin qauna haka yake masa ba. To amma a irin wannan yanayin da al'amura suka fara bayyana kansu sam bayason abdii din ya cika kusanci dashi.

Gefan qafafunsa ya tsaya ya miqa hannunsa kadan ya tabashi,sai ya bude idanunsa kuwa da sauri.

"Ka koma ciki ka kwanta" Yace masa kawai yana haurawa sama idanunsa kan agogo yana ci gaba da lissafa lokaci.

Kayan jikinsa ya zare bayan ya samu signal na beno,ya kuma musanyasu da wasu farare qal din pyjamas masu dogon hannu da tsananin taushi. Wani irin kyau yayi duk kuwa da cewa ba tufafi bane na ado,sassalkar sumarsa ta kwanta luf saman kansa ta kuma dan hargitse kadan garin sanya pyjama din jikinsa,sai ya qara fita ya duba ma'ajiyar coffee dinsu,ya sameta cike da zazzafan coffee. Yana da sauqin kai a abubuwa da dama,da kansa ya zuba cikin wata qawatacciyar tea pot.

Sosai balcony din ke masa dadi,wannan ya sanya ya taka zuwa ciki dauke da tea tray din,ya kuma dora saman wani stool dake da wata zagayayyar sofa me taushin gaske.

*AKHNAN*

Tafukan hannayenta duka biyun ta shafa saman lallausar fuskarta data haska cikin rolling din dake saman kanta,wanda ta yishi da mayafin after dress din jikinta data sanya saboda sallar isha'i da tayi yau a makare.

Duka yau din bata iya tsinana abun arziqi ba,tun bayan da sukayi magana da mammina akan gobe zata gabatarwa da sultane mijin data zaba. Zataje ita daya,ba zata mata rakiya ba wannan karon,fuskarta kuma ba zata bayyana ba,don magana ce tsakanin uba da d'iyarsa.

Tana jin nauyin sultane har cikin jininta na yadda zata iya kallonsa ta gaya masa ga mijin da ita take so ta aura,ga kalar zabinta. Mijin da ko sau daya taqi yarda taga koda hotonsa.

Maida idanunta tayi ga aisa dake kwance rub da ciki sama gadonta,yau haka kawai tayo qaura ta taho dakinta kwana. Ta taho da dukka ayyukan sahel couture tace a nan zatayi,wai ko hakan zaisa hankalin akhnan ya koma ga kamfanin. Tun dazu take aikin tana kuma mita.

"Komai na enterprise ya tabarbare.......komai baya tafiya akan tsari da doka,kina wasa sa shugabancinki,komai yana shirin lalacewa,iya abinda zamu iya riqawa nida shehnaz munyi......mammina ta kasa aiwatar da komai akai,ban sani ba,tsananin yardar data bawa mutanen ne ko kuwa?" Aisa ta fada da gasken gaske tana hango downfall na kamfanin. Tana gano yadda wani taqi kadan ya rage kamfanin yakai qasa warwas,ta soma jin kishin wahalar da sukasha a kamfanin,ta soma jin ANYA BA ZATA KARBA ba kamar yadda mammina ta fada?.

"Ta rayuwar me sahel couture din ake yanzu haka........idan sahel ta fadi dasa hannunki a ciki......mammina tace ki karba saboda tasan a yanzu banda energy din komai amma kin wofantar......ki daina complaining min komai aisa" Ta furta tana miqewa daga saman abun sallar. Iska me kyau takeso ta shaqa sama da wadda ke cikin dakin ko zatayi tunani me kyau,saita ware rolling din,saidai bata sauke dankwalin duka a kanta ba,ta doshi qofar da zata sadata da private bedroom balcony dinnata.

Da kallo tabi akhnan,ba wani abu da yake daidai a yanzun a tare da ita da gaske ne........tana jin kawai zata karba......zatayi accepting,ba tare da TUNANIN KOMAI BA ta soma rubuta doguwar wasiqa me dauke da sharhin karbar office din akhnan din a madadinta wadda za'a sanar da kowanne department.

A hankali take takawa a cikinta tana zuqar fresh air din da kyau tana aikewa hunhunta,ta kama dankwalin da kyau cikin jikinta tana curewa guri daya saboda sassanyar iskar dake kadawa wadda keda dan qarfi kadan kadan. Gaba ta matsa jikin qarfen da ya yiwa gurin qawanya ta sanya hannunta ta dafeshi tana duban qasan stairs din daya kasance wata farfajiya dake bayan gidanta da takan zauna lokaci lokaci.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Iska ta fitar sirirya daga bakinta,tana dan ji a jikinta kamar ba ita kadai bace tsaye a gurin,saidai ta sani,ba wani mahaluqi daya isa ya tsaya a inda take tsaye a lokaci irin wannan idan ba aisa ko shehnaz ba,wanda dukkansu ba daya daga ciki. Ido ta lumshe sannan ta budesu tana jin wata kewa tana ratsata,a wasu watannin baya da suka shude,ba wani abu da yake bata nishadi irin wannan lokaci. Tana jin dadin tsaiwa a wajen,tana jin dadin irin iskar da gurin yake bayarwa,tana kuma sake samun cikakken nishadin da tunda ta tashi a rayuwarta nishadin kawai ta sani,batasan wani abu waishi baqinciki qunci ko bacin rai ba,sai a wadannan kwanakin,sai a wadannan lokacin da aka hana rayuwarta da tunaninta sakat akan 'YA'YA MAZA!.

Yunqurin shigarsu rayuwarta kawai yana neman gigita mata rayuwa,ina ga ance yau gasu cikin rayuwartata?.......da dukkan qarfin ikon da zasu mallaketa su kuma sarrafata?.....ita ta dade da fahimtar sam BA ALKHAIRI ciki wannan halittar a rayuwar mace me gata da 'yanci irinta.

Readers Also Read

More by Huguma