L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 11
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 11: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 11. A tsanake ya juya a hankali yana nufar sashen qofar…
3,364 words
A tsanake ya juya a hankali yana nufar sashen qofar balcony din nata bayan wasu sakanni. Maqullansa ya zaro,cikin hikima irinta qwarrarun jami'ai da suka goge ta fannin aikin tsaro binciken sirri dana qwaqwafi ya bude qofar. Takowa yayi a nutse yana dawowa nashi qofar,tsugunnawarta ya bashi space sosai da ya samu ya wuce a tsanake,ya isa qofar balcony din nasa ya zura key ya bude qofar ya turata sanna ya sanya qafarsa a hankali bakinsa dauke da addu'ar shiga gida.
Da sauri ta daga kanta sannan ta waiwaya zuwa bayanta,daidai sanda yake maida qofarsa ya kulle abinsa.
Zumbur ta miqe tana waiwayen hagunta da damanta. A yanzun ba kowa a gurin,a yanzun ita daya ce sai ruwan saman dake sauka,wani tsoro ya sake mamayarta,ba shiri ta fara tattakawa da sassarfa tana nufar qofartata wanda ta sameta a bude,da hanzari ta shige sannan ta maidata ta rufe tana maida numfashi a jejjere kamar wadda tayi tseren gudu.
Sai data kusa kashe a qalla mintuna goma sannan numfashinta ya daidaita,ta saka hannu ta zare yalolon mayafinta daya jiqe ta yar a gefe,ya kuma sauka daidai kwandon Cherry dinta dake dauke da Cherry din. Wani tsaki taja baqinciki yana taso mata.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 18* _________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX __________________________
Yadda yayi matan yafi zubda Cherry din bata mata rai,ita zaya bari a gurin da ko izinin tafiya bata bashi ba?.....wai yana Manta wacece ita?......baiga yadda kowa ke treating nata ba da kulawa da kuma respect?.........matsayinta yake mantawa ko kuwa?.....lallai dole ta sanyashi yayi dana sanin aikinsa a kanta....dole ta sakashi ya koyi yadda zai girmamata......ko wanne matsayi kuwa sultane ya bashi dole ya gane akwai banbamci tsakanin d'an gida da yaron gida.
Inda wani abun ya sameta a inda ya barta ma kenan baida asara shi?. To waye ya bude qofar balcony din?,don tayi imanin ba wani a kusa ballantana ta dauka shine ya bude,saita dora tafin hannunta saman kanta tana jin gaba daya lissafinta yana dagulewa. Ta saba da a girmamata cikin kome da zata buqata........ta saba ta bada umarni nakai tsaye abi........ta saba tayi kome da takeso bame iya daga kai ya kalli qwayar idanunta ballantana yace tayi ba daidai ba......a yau din sai takejin kamar an mata babban wulaqancin da duk duniya ba abinda yake sama da wannan,sai kawai ta juya tana shigewa ciki cikin wani irin fusataccen yanayi.
Duk sunan hadimar da yazo bakinta shi take kira da qarfi,wani irin gini ne da ruwan da akeyi a waje sam idan kana ciki ba zaka sani ba saidai ko idan ka kalli windows ko glass doors din da aka qawata wasu bangwayen dasu,wannan ya bawa duk wadanda ke kusa da nan damar jin muryar uwar gijiyar tasu,suka kuma bar dukkan abinda sukeso kowacce ta taso don amsa kiranta.
Kamar kowanne mutum da ya kwana ya tashi cikin agadez qasa sukayi da kawunansu kamar yadda suke tsugunne a gabanta.
"Uban waye yace ku tafi ku kwanta ba tare dana shigo ba?" Tayi tambayar data bawa kowa mamaki a cikinsu,kasancewar sunsan tsarikanta. A lokuta irin wannan bata buqatar a dameta,bata buqatar kuma kowacce irin hayaniya a kusa da ita,kowa yasan wannan,kowa ya haddace wannan,don haka kusan tafiya kowa yake zuwa makwancinsa.
Maimakon ta dauki shurunsa a matsayin girmamawa,don babu me iya bata amsa a cikinsu,sai kuma hakan ya tunzarata da wani irin kalar bacin rai. Fada sosai ta dinga yi,kalar fadan daya sake bawa kowa mamaki a cikinsu......kalar fadan da ko sanda tasha guba bata yishi ba.
"Ranki ya dade...." Birra dake da wannan qarfin halin ta matso dab da ita ta fada da yanayin da yaja hankalinta kadan.
"Kayanki a jiqe suke,sanyi yanata shigarki.....kiyi haquri ki canza kaya sai kizo kiyi mana duk kalar hukuncin daya dace". Maganan birra kenan data sauketa,ta juya tana haurawa zuwa sama a zafafe ba tare data sake bi takan kowa ba,tana isa kuma ta wuce dakin data zaba kwana a ciki ta murza key,don ko birran bata buqatar ta kusantota a sannan.
Da d'aya da d'aya ya rage hasken fitilun dakin yana jin zuciyarsa wani iri ba dadi. Fushi ke motsa masa amma yanata maimaita a'uzubillahi minashshaidanir rajeem don ya sani saukowar fushi daga shaidanne.
Yana saisaita room heater ko zai samu sanyin jikinsa ya ragu ya fahimci omari yana nemansa,sai ya qarasa ya dauki na'urar ya azata saman table hade da wayarsa da damshi kadan ya tabata,ya sakata a hands free yana yana qoqarin balle links din hannun rigarsa don zare rigar daga jikinsa,ruwan da ya tabashin ya sanya wani lallausan qamshi na tashi a jikinsa na unique perfume dinsa.
"Barka da dare captain sheikh" Omari ya fada da salon tsokanar da wani lokaci yakanji sha'awar tsokanarsa da ita.
"Yauwa" Ya amsa masa can qasan maqoshinsa,adams apple dinsa yana motsawa daga sama zuwa qasa,daya daga cikin alamun fushinsa kenan.
Dan shuru omar yayi,yana jin sauyi tattare da haisam din,saidai kuma ya sani,shi din wani kalar introvert person ne,ko a yanzun daya dauka wayarsa yana kyautata zaton haisam din yana tsammanin maganar aiki ce,baisan wasu awanni zai nema a bashi ba.
"Ya palace din?" Ya tambaya a taqaice kada sakannin daya ware na amsashi ya qare.
"Fine" Kawai yace yana zare rigar samanshi,fara qal din cotton singlet dinsa tana bayyana wadda ta lafe a jikinsa,ta kuma fidda qirar ginannen jikinsa da faffadan qirjinsa dake cike da lallausar gargasa.
"Awa ashirin da hudu nakeso a bani aro" Omar ya fada
"Zuwa ina?" Ya tambayeshi yana duqawa zuwa ga fuskar wayar ranshi yana jin yana sake jagulewa.
"Zinder kawai zanje....."
"No..." Ya fada kai tsaye yana katseshi.
"Baka tambayeni abinda zanje nayi ba"
"Ba buqatar hakan" Ya sake amsashi a taqaice.
"Just 24hrs fa?"
"I said nooooo!....." Ya fadi a zafafe da wannan zuzzurfar muryar tasa.
Shuru ne ya ratsa tsakaninsa da omar din,lumshe idanunsa omari yayi yana ji a ransa akwai abinda ya taba zuciyarsa a yau din. Ya sani haisam din yana da fahimta yana kuma da sauqin hali.....saidai idan ya tashi baudewa ko bacin rai yana da tsananin taurin kai da kafiya. Ba ma'abocin fada bane.....don yafi ganewa shuru a yawancin lokutan da ransa ya baci maimakon magana ko nunawa a aikace......dole yasan akwai abinda ya taba ranshi daya sakashi replying masa maganansa a haka.
Wayar kawai omari ya sauke a kunnensa sanda yaji alamun ya gintse wayar,qaramin murmushi yayi ya ajeta gefe,ya jawo daya wayar tasa yaci gaba da amfani da ita,da cikakken tabbacin haisam din zai sake nemansa.
Silent ya maida wayar da kuma na'urar tasa,ya sanya dukka yatsunsa goma cikin jiqaqqiyar sumarsa yana jin yadda ransa yake sake dagulewa.
Kome meye ya zama dole ya gaggauta matse kwanakin aikinsa yabar masarautar. A dazun banda tasirin sabo da aikinsa da yayi,saura kadan wannan jinin na SARAUTA dake motsawa cikin jininsa ya sanyashi yin wani abu da yasan dole zai d'arsa zargin WAYESHI a zuciyar yarinyar.
"She's stubborn......" Ya fada yana motsa fresh lips dinsa da suka sake wani irin kyau da daukan hankali.
Numfashi sosai yaja ya kuma fesar,ya lumshe idonsa yana budesu sanda yake nufar hanyar bathroom. Me yasa?......me yasa?,tambayar da yaketa maimaitawa kansa da kansa kenan,ba tare da yasan akan ainihin meye yake tambayar ba.
Yana da hadari a karan kansa ya sani......aikinsa ya dauke hankalinsa daga kan komai da kuma qoqarin bin umarnin Allah da yake cewa.
"Ka gayawa muminai maza mu runtse ganinsu su kuma kiyaye farjinansu" Me yasa take qoqarin shiga kowanne runtse ganinsa?....kame kansa da idanunsa?.
"Me yasa kake damuwa bayan a baya baya damunka?" Zuciyarsa ta jefa masa tambayar sanda ruwan daya saisaita ta hanyar shower me tsananin dumi ya soma sauka tsakiyar kansa.
"Zaka kai lokacin da duk wani guje guje bazai maka ba saidai aure......kana da lafiya......cikakkiyar lafiyar da ba kowa keda irinta ba......kaga kuwa aure ya zama wajibi....dole a kanka.......ka gama duk ayyukanka na watanni ko shekarun daka tsara....wallahi dole sai aure.....shi kadai ne ya dace dakai". Daga daga cikin maganganun amjad kenan a wani yammaci da suka shirya picnic cikin gari jimma iya su yasu.
Baice da khadeem komai ba,shi da Amjad dake goyon bayansa,ya bishi ne da idanu kawai. Bakasafai ya fiya magana me tsaho da khadeem ba,don ta fannin magana ba zaka taba kadashi ba,don baya gajiya da ita......shi kuma daya daga cikin abubuwan dake masa wahala kenan,musu ko maimaita magana,yafi ganewa zama shuru don yafi bashi nutsuwa da nazartar abubuwa a yanayin da suka dace. Wannan ya sanya maleek wani lokacin yakan kirashi da mr introvert bayan mr lowering gaze da suka bashi.
Murmushi kadan yakanyi,bai hana kowa kiranshi da sunan da yayi masa ba a tsakaninsu su shidan,don kusan alaqa ce da aka ginata tun kafin a gama mallakar hankalin kai.
Duk wani magana da bayani da sukeyi akan aure ya sani.......ya karanta komai,yana da tarin ilimi akan aure da ma'amalolinsa wanda su sam basusan yana dashi ba.......ya tara ilimi akan fannnin aure da mu'amalar miji da mata masu tarin yawa cikin litattafan manya manyan malaman addini masana asalin ilimin zamantakewa wanda basu da adadi. Ya karanci zamantakewa a gidaje masu yawa......gidajen sahabbai gidan annabi S A W kanshi baisan adadin littatafan daya dubasu ba.....bugu da qari ya fisu sanin aure ya wajabta a wuyansa.......don idan akwai inda yake da rauni to ta wannan fannin ne.....shi yasa ya lazamci azumi ya kuma lazumci kame idanunsa da nesanta kansa daga dukkan wata mu'amala data shafi 'ya'ya mata.....to amma yanaso ya yishi ne a sanda ya samu gamsuwar zai iya doguwar rayuwar da BABU SAKI tsakaninsa da duk macen da zai aura din.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Yanason ya zabi macen da yakejin komai nata yayi masa,macen da hankalinsa bazai sake kaiwa kan kowacce 'ya mace ba bayan ita.......yanason kuma komai ya kasance a right time da zai spending rayuwarshi da ita cikin tarin nutsuwar da zataji a ranta gidanta na aljanna......mijinta na aljanna ne aka gaggauto mata dashi duniya.....ba a irin wannan lokacin da ta kowanne bangare tunaninsa yake a jagule da rashin samun gamsuwa da tsaro rai lafiya da rayuwar motii ba.
A gaggauce ya shirya kansa cikin wata long sleeve riga ne nauyi da zata bashi kalar dumin da yakeso,sannan ya sanya wandonta da yake mahadin rigar. Yana gaban mirror yana sake kwantar da sumarsa tunanin abinda ya faru dazu ya sake dawo masa. Dauke idonsa yayi daga mirror din yana jan tsaki jin yadda tsigar jikinsa ta zuba.
Bata da kunya ko kadan.......shi din kuma mutum ne me mutuntawa da baya shiri da masu wannan dabi'ar,wannan ya sanya ya tsaya tsayin daka akan ANANI sanda ta fara irin wannan dabi'un,sai daya tabbatar ya saitata yadda ya dace.
Da kanshi ya hadawa kansa coffee,yana jin sassan ya masa shuru. Dole tasa ya sanya abdii ya koma personal gidansa,don kwanakin kadan kadan ya tsara zai dinga yi yana komawa ainihin gidansu,harsai sanda yaga abdii din ya dauki saiti da salon da yakeso,ya kiyaye duk abinda yace ya kiyaye din.
Hannun hagunsa ya soke cikin aljihun wandon nasa,na damansa kuma yana sipping coffee din kadan kadan. Shan tea da coffee wata halittacciyar halitta ce a jinin duk wani dan Ethiopia,musamman jimma oromia dake noman coffee din gaba daya.
Cup din ya dire bayan ya shanye,omari yana fado masa,sai a yanzun yaji kamar baiwa omar din daidai ba. Aboki ne kuma dan uwa shaqiqi a gareshi,saidai wasu lokutan dole yanayin aiki ya sanya ya mu'amalanceshi irin mu'amalar uban gida da yaronsa.....don komai a rayuwa yana buqatar saiti.
Na'urar ya dauka ya kunna,ya kuma tura masa permission letter gajeriya ya tura masa. Sanda saqon ya sameshi murmushi ya saki,dama ya sani......indai haisam ne zai dawo. Dabi'unsa masu ban sha'awa ne qwarai da burgewa,saiya maida masa amsa cikin girmamawa a matsayinsa na ogansa bawai abokinsa ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 19*
★★★Dare makwantar mugu inji hausawa......tabbas haka yake,a irin wannan daya daga cikin wadannan dararen da suka kasance da busawar sanyi sakamakon saukar ruwan saman da aka samu a daren jiya,hakan sai ya zamanto sanadin daukewar sawayen mutane da wuri daga waje zuwa gidajensu dama dakunan baccinsu.
A tsakiyar wannan daren mammina ke ratsa cikin unguwar. Daga gefanta TA FISU ce......tafisun da sunanta yayi daidai da aikinta dama alfanunta a gurin mammina. Tafusun ta kasance wani bangare me girma da muhimmanci tattare da mammina wanda yawancin mutane basu san da hakan ba basu kuma fahimci haka ba.
Duk da kasancewar ta fisu me girman matsayi a sassan mammina din......amma dukkan wani aiki da motsi nata yana nuna zallar rashin jituwa da rashin samun fada da fuska tattare da mammina din.
Yana da wahala ka samesu sun kebe.....kamar yadda yake da wahala kaji ta ambaci sunanta idan har wani muhimmin abu ya taso mata. Hasalima saita kasance me yawan tafiye tafiye.....don kusan cikin gidan kowa ya sani cewa tana tafiya wasu qasashen sarin kayan kasuwancinta,tazo dasu gidan ta siyar tas ta sake komawa ta saro wasu ba tare da takurawa ko saka takunkumi daga wajen mammina din ba.
Daga nesa can suka baro mutum biyun da suka zamo amintattunta na gaske gaske,wadanda ta sanya suka musu tattaki cikin shigar da ba zaka gane daga ina suka fito ba. Tayi hakanne saboda daren daya soma yi,daren yayi nisan da fitar zata iya zame musu qalubale,duk da cikakken yaqinin amincin da yankin nasu yake dashi.
*HAISAM*
Sanye yake da long sleeve hoodie shirt a jikinsa baqa wadda ta dace da yanyin sanyin da yake busawa a gari ta kuma dace da skinny jeans din jikinsa.
Saman kansa baseball cap ne wanda ya lullubeta da hular dake maqale da rigar jikinsa.
Boots ne a qafafunsa masu tsananin daukan idanu,duk kuwa da duhun daren da kuma kalarsu da suka kasance baqaqe. Dukka hannunsa zube yake a aljihun wandonsa saboda sanyin da yake kadasu,idan ka ganshi a lokacin ba zaka taba dauka shine sheikh haisam ba. Dressing dinsa baqo ne da sam ba kasafai ya fiya yinsa ba,amma yana tsananin fidda wani irin sirrin kyau tattare dashi gami da bayyanar da zallar quruciyar dake yawo cikin jinin jikinsa.
Sosai wannan tsahon nasa ya fito,tsahon da dole ka kirashi da GIANT kai tsaye a iya kallon farko kawai,tsahon ya dace da yanayin cikar jikinsa da kuma murjewarsa,wanda kai tsaye wasu lokutan zaka iya kiransa gabjeje saboda yawan motsa jiki da qarafuna da injina masu nauyi da yake yawaita yi.
Ko a yanzun daya kasance wani irin dare me yawan shuru,cikin nutsuwar nan data zame masa dabi'a yake takawa abinda,kai bakace ya dauki duhun dare ko nisansa a bakin komai ba. Ba wani tsoro ko firgici a tattare dashi,daga fuskarsa har zuwa zuciyarsa,zuciyarsa dake motsawa can qasan qirjinsa tana kuma maimaita ayoyin qur'ani da maimaitasu din ya zama wata dabi'a ta ruhi da zuciyarsa a duk sanda ya samu kansa cikin shuru da kadaicewa kaman haka,ayoyin shafi na biyun qarshe na cikin suratu al_imran,wanda ke bayani akan halittar sammai da qassai da kuma jujjuyawar dare da yini,tsarkake girman ubangiji kan yadda ya halitta ya kuma tsara komai. Bayan haddar qur'ani gaba dayansa da Allah ya azurtashi dashi......akwai tafsirinsa daya kammala tun yana da shekaru goma sha takwas a duniya zuwa sha tara,don haka a duk sanda yake karantashi yana jin kamar yarensa yake magana dashi saboda fahimtar fassara da ma'anar kowacce aya,don haka ko a yanzun da yake karanta ayoyin yana sake girmama zatin Allah daya halicci dare,daren kuma ya zama mahutar kowanne bawa.....mahutar kowacce irin halitta. Shuru yakan mamayi ko ina,zirga zirga tana taqaita a bisa dole,jikkuna suna kusantar makwancinsu zuwa ga bacci,baccin da yake tamkar dan uwan mutuwa saboda karbar ruhin kowa da Allah yakeyi. Yana dawo da ruhi da rayukan wadanda yaso suci gaba da rayuwa,ya kuna riqe ruhikan wadanda kwanakinsu suka qare a duniya. (Fahimtar ma'anar qur'ani a sanda kake karantashi abune me wani irin gard'i da ba zaka fahimta ba sai in kana gane ma'anoni da fassarar ayar,kuyi qoqari yaranku su fahimci hakan,zai taimakawa hankulansu imaninsu da tarbiyyarsu,hakanan BACCI abune daya kamata a kiyaye ladubban yinsa,akwai addu'o'in da sukazo na bacci kala kala,a cikinsu kuma akwai wadanda suke dauke da addu'ar neman gafarar Allah idan daga wannan baccin rai yayi halinsa,shi yasa akeso kafin ka kwanta ka cika da aiki me kyau,kamar nafila ko karatun qur'ani istigfari da sauransu,da yawa cikin novel nasan muna qoqarin saka nafila yayi sannan ya kwanta ko shafa'i da wuturi,duka muna qoqarin nuna muku kafin ya kwanta ko ta kwanta wani aiki me kyau tayi,do bakasan zaka tashi ba ko ba zaka tashi ba,Allah ya bamu cikawa da kyau da imani).
K'irjinsa cike yake da jiran sakamakon abun hannun da ya tura a qera masa,a yanzun tunaninsa yayi nisa zuwa ga yadda zai fidda asalin abun hannun daga ma'ajiyarsa zuwa gurinsa don gudanar da binciken da zai zame masa mabudi na farko kuma tsani na farko da zai fara takawa zuwa ga inda mai laifinsu yake.
Zuwa yanzu ya gama karantar tsari da yanayin unguwar gaba daya,kusan ya gama da komai daya shafeta cikin dararen da yake fita. Ya gama sanin manyan mutanen dake rayuwa a cikinta,adadinsu sunayensu dama ayyukansu.
Idonsa ya sake daukewa daga sararin samaniyar da yau sam ba alamun hadari sai taurari data bar musu,yana sauke dubansa a gabansa,daidai sanda ya sake ganin gilmawar mata biyu.
Mata biyu kamar wancan karon,kamar wancan lokacin,da irin suturar daya gani a wancan lokacin,saidai banbancin kawai a yanxun ba wata mota daura dasu,da qafafunsu suke shiga layin.
Da wani irin hanzari ya jawo baseball cap dinsa da hoodie dinsa ya rufe fuskarsa da kyau,da wani irin kuzari kuma ya nufi layin da yaga sun shiga din cikin kula da takatsantsan da motsinsa.
Sanda ya isa babu su ba alamarsu,ya qarasa a hankali qasan wata matashiyar bishiya data bada rassa ba masu yawa ba,wadda aka dasata daga farkon layin,ya jingina sosai da ita yana sake sajewa a jikinta.
Da dukka wannan fikirar da basirar yake bin gidajen dake jere cikin layin da kallo cikin nutsatsen nazari. Layi ne da yake jerin sahun layikan da suke dauke da manyan mutane sosai fiye da kowanne layi......layi ne kuma da yafi kowanne qarancin zirga zirga na jama'a koda kuwa da rana ne.
Ci gaba yayi da kallon gidajen,kowacce qofa a rufe take,ba wata qofa guda dake a bude,abinda yaso cakuda hankalinsa kenan ya kuma so kauda tunaninsa ya gaza sanyawa kowanne gida a ciki wata ayar tambaya.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Kai ya girgiza a hankali,ko kadan bazai yarda da kwanyarsa a lokacin ba,lokaci ne daya kamata tayi aikinta yadda ya dace. Ganin gilmawar wasu mata sanye da uniform na gidan sultan of agadez......a dare irin wannan daya zama doka ce ta hana shiga da fita cikin lokaci irin wanna har sai safiya tayi. Da wani salo da yanayi na tafiyar da batayi daidai da tafiyar da ake yinta bisa qwarin gwiwa gaskiya da rashin tsoro ba. Yayi nisa......akwai tazarar da zai zamana zai wahala ace kusanci ne ya kawosu unguwar.....ko cudanyar maqotaka,unguwanni ne dake maqotaka ada juna,saidai kuma mabanbanta ne.