Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 10

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 10

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 10: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 10. Har cikin jinin dake harbawa a jikinsa yakejin zancansu…

3,368 words

Har cikin jinin dake harbawa a jikinsa yakejin zancansu bai shefeshi ba,burinsa su matsa shima ya wuce ciki kafin ruwan yakai ga bata masa waya ko katse muhimmiyar maganar da yakeyi da bobbo......amma a wannan gurbin baisan sanda yaja wani siririn tsaki ba.

Haka kawai yakejin wani bacin rai kadan kadan yana tasiri a ransa. Banda girman kan dake dawainiya da ita yana tunanin akwai tasirin jahilci. Wacce irin uwar goyo ya rabauta da ita wadda ke goyon bayan duk wani shirin shirme nata maras ma'ana?.

"Zai kasance ni na zaboshi......amma ki koyawa kanki nunawa duniya cewa shine zabinki......idan hakan bata faru ba,bana tunanin zan sake zama cikin matsalolinki irin wannan har abada". Kai ta girgiza sanda ruwan ya fara damunta saboda yanayin saukarsa daya qara yawa.

"Komai zai kasance kamar yadda kika buqata mammina ta......na gode da kasancewarki cikin rayuwata" Ta furta sanda suka miqe a tare,ta kuma matsa tana rungume mammina din sosai da tarin soyayyarta danqare cikin zuciyarta.

A hankali mammina din ta zareta daga jikinta tana sakar mata murmushi.

"Nan da kwana uku kawai zan gabatar miki da duk wanda nake ganin zaibi umarninki ne kawai".

" Ba buqatar hakan......koda zamu qare zamanmu ban ganshi ba bana buqata mammina.......buqatata daya na amintar da sultane.....na fita daga fushinsa"

"Idan har kikayi hakan kowa ma zai iya fahimtar komai" Amsar data bawa akhnan kenan ta soma takawa don barin gurin duba da yadda ruwan yayi qarfi lokaci daya.

Idanunsa ya maida ya lumshe yana jin yadda bishiyar ta gaza rufe saukar ruwan duka cikin kansa,duk da ta tare wani kaso da bai taka kara ya karya ba.

Maganganunsu na qarshe ne suka maimaita kansu cikin kansa,yayin da zuciyarsa ta yunquro da wani qaqqarfan yunquri tana gaya masa.

"Not your business haisam......not your business". Kansa ya gyada a hankali,har cikin zuciyarsa yana jin hakane,zuciyarsa gasiya ta gaya masa,wani sashen kuma na zuciyar tasa tana cike da wani irin yaqini da zargi me qarfi akan MAMMINA.

Yanajin tana sake cika dukkann wasu sharuddan zargi da zato me qarfin gaske a tattare da ita......yana jin a duniya a yanzu itace bakin zaren ZATONSU ta farko.......a jikinsa yake jin akwai wani abu binne.

Sultane ne kawai ya gilma cikin tunaninsa da idanunsa......yana ji da dukkanin yaqininsa akwai wani abu da ba daidai ba......amma kuma yana gayawa zuciyarsa da kansa cewa ba huruminsa bane......BINCIKE YA KAWOSHU AGADEZ.....aiki yazo yi kawai ya koma,aikin da yake sanya rai yake kuma jin cewa kwanakinsa qalilan suka rage. Ya rage baccinsa......ya hana kansa jin dadi walwala da tafiye tafiyen da yakanyi don kawai sake gane girman buwayar Allah saboda aikin kadai. Ya kasa samun nutsuwa na tsahon shekaru....baccinsa yakan yanke idan ya tuna koda kowanne lokaci rayuwar MOTII zata iya fuskantar barazana.

Barazanar dake gabansa.......aikin dake gabansa yafi gaban wannan abun da yake gani a yanzu.....bayajin kuma yana da sauran abunyi akai.....abu daya ne yasa hankalinsa yake kaiwa gurin,jikinsa yana bashi matar itace zata zame musu tsani na samun wani abu ko yaya ne game da AJANI AHMED.

Sauka ruwan yake da wani irin yanayi daya tayar da qamshin qasa. Sassanyar iska dake kadawa da walqiya me tsananin haske tsakanin zubar ruwan da iskar. A haka yake takawa cikin cikakkiyar nutsuwarsa,kamar ba ruwan sama ke sauka saman kanshi ba. Abu daya kawai yayi.......zare kewayayyar hular dake saman kansa,ya riqeta a hannunsa,wannan ya bawa ruwan damar sake kwantar da sumar dake kansa me yawa da kuma sulbi.

Ruwan farko kenan da ake sanya ran ya kasance tafe da tarin albarka,yaci gaba da takawa yana furta ALLAHUMMA SAYYIBAN NAFI'AN da kyawawan jajayen labbansa masu sulbi.

Yanayin ya tuna masa ne da jimma........tana da wani irin dadi a yanayin damina irin haka. Kyawawan shukoki da tsirrai,guraren da zaka kebe kanka cikin nutsuwa wanda yake sanyashi nishadi a yawancin lokuta. Akwai guraren na musamman daya warewa kansa cikin masarauta,wanda shi daya yake rayuwa ya kuma kebe kansa a gurin idan yaso. Gurine da ba kowa ma ya taba samun daman shigarsa ba cikin masarautar.

Bai manta randa omar ya taba samunsa a daya daga cikin gurin. Sosai ya daga kai yana shaqar iskar me dadin dake kadawa a gurin,wani irin tattausan qamshi daya wanzu a gurin sakamakon yawaitar kyawawan furanni.

"Gurin nan sam bai dace dakai ba......gurin nan yafi kyau da zaman masoya......ko ma'aurata.....za'a mori soyayya sosai ta gurin nan" Ya fada da dukkan gaskiyarshi. A sannan harara ya watsawa omar,yana ganin damuwarsu kawai dukka bata wuce soyayya?,amma sannu a hankali sai tunanin ya fara zauna masa.....dole ya janye shiga gurin gudun faruwar karkatar hankalinsa daga mission dinsa zuwa wani tsari da bai shirya masa ba a sannan.

_AKHNAN_

Duk da warwarar matsalar tazo mata da wani gundumemen sharadin da bata taba tsammanin zai gindaya cikin rayuwarta ba,amma hakan bai hanata jin sassauci a zuciyarta ba yayin da take takawa zuwa hanyar da zata sadata da sassanta. Ba wani tsoro yau tattare da ita saboda tare da birra suke takawa zuwa sassan nata,duk da tsoron ruwan sama sa take dashi wanda ya samo asali tun daga yarinta. Kamar yadda bataso ya daketa ba tare da wani qwaqqwaran dalili ba......tun zazzabi daya taba saka mata sau daya......hakanan bata son saukarsa saboda tsananin tsoron tsawa da take dashi,amma a yau din yadda zuciyarta ta fara taurarewa da yanayin dake fuskantota,sai ta baiwa ruwan daman sauka a kanta haka kai tsaye,saidai yadda taga yana qara yawa ya sanya tadan qara saurin tafiyarta,tana kuma dakatar da birra dake qoqarin lulluba mata wata qaramar lema.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Hannu kawai ta miqa mata ta karbi sabon cherry din da aka ciro mata,wanda ya zame mata al'ada shan fruit kowanne dare bawai abinci ba.

"Zan kwanta da wuri idan na shiga......kina iya tafiya" Ta sallameta don tasan akwai buhaina da bushira da yau zasu kasance a sassannata. Birran na qoqarin mata bayanin basa kusa a yau din amma tuni tayi gaba zuwa sassan nata.

Ruwan na sauka da wani irin nau'in sanyi,sanyin daya ratsa fata da tsokarta,ya kuma taba zuciyarta a hankali kuma yana sauke mata maganan da suka soma yi dazu da safe da tamim.

"Kiyimin afuwa.....na gaza gano komai a kansa.....dukka iya bincike na,saidai ban dawo haka a banza ba,na samo launin fatarsa......qwayar idanunsa.......da tsahonsa.....launin gashinsa......sannan an bani tabbacin dan qasar Ethiopia ne yankin jimma......" Yayi maganan yana buda mata envelope din dake qunshe da komai a ciki.

Tsarin zubin halittarsa dake rubuce daki daki ta dinga kalla. Giant ne........launin fatarsa bata cika haske da yawa ba,saidai sam ba baqi bane.......idanunsa na da nau'in shape din almond......farin me haske sosai,baqinciki me duhu......fadin qirjinsa dana kafadunsa duka yana nuna halittar namijin daya kasance giant sosai.....me qirar qarfi kamar yadda ta shaida hakan daga riqon da yayi mata. Ta maida komai ta rufe tana kwantantawa da mutumin dake a mazaunin malami me karantaswa cikin masarautar mahaifinta. Akwai tarin kamaceceniya sosai a wadannan bayanan da abinda take iya gani tattare dashi......saidai har yanzu wadannan bayanan basu bata cikakkiyar gamsuwa da hujja me qarfi ba......amma ta rasa abinda yasa zuciyarta dari bisa dari taqi aminta da cewa bashi bane. Duk bata hangen wani qwarewa ko sanin rayuwa ga malamin addini da har zaisan yadda ake sarrafa doki haka da tarin hikima da kuma ilimin sanin sarrafa dabbobi,ta tabbatar ko waye zai aikata hakan dole akwai wani D'IGO na SARAUTA cikin jininsa.....koda ba ahalinta bane amma tabbas yana da alaqa da ita komai qanqantarsa.

Takan bata lokuta masu yawa tana nazarin......indai har shine yanzu c

Kai tsaye ta durfafi qofar sassan nata,saidai kuma ta samu a rufe take,da alama kuma me kula da wajen baya kusa. Sai a sannan ta tuna kusan ta sallami kowa sanda zata fita din. Tana da wani hali me kyau guda daya,a duk sanda bata buqatar komai takan sallami hadimanta na kusa dana nesa don suje su kwanta suma su huta,ba kasafai take barin kowa yayita tsaiwa akan hidimarta awa ashirin da hudu ba.

Wani siririn tsaki taja,gabanta yana wani irin faduwa saboda yadda rugugin hadari ya fara tasowa,wanda ta tabbatar zai wahala yazo ya wuce walqiya bata biyo baya ba.

Tsaiwan zai zama bata lokacine a wajenta,sai ta yanke bi ta qofa ta biyu ta sassanta dake dogon balcony din daya hada sashenta da sashen dake maqotaka da nata. Guri ne da takan dauki kwanaki bata bishi ba,musamman da yake ma ba mazauniyar agadez bace......saidai kuma idan tana buqatar kadaici,ko bata buqatar kowa ya ganta takan bi ta nan ta fice abinta zuwa dukka sassan da takeso.

*HAISAM*

Tun sanda ya fito da niyyar komawa ta qofar bayan ya fito. Tun sanda ya gama karantar duk wani lungu da saqo na sassan da kewayensa yasan da qofar,amma bai taba bi ta nan ba. Ba komai yake motsi ko wani action a kansa ba.....bayason yawaitar motsinsa akan abubuwa da yawa su jawo hankulan jama'a a kansa.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 17* ___________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX _____________________________

Akwai abubuwan da yasan dasu,amma yayi kamar baisan da wanzuwarsu ba.....akwai abubuwan da ya sansu amma yanayi kamar baisan komai akai ba ko bai fahimta ba. Yau din ya shirya bi ta nan ne don yasan inane mahadar da ta hada nan shiyyar da kuma sashen da qofar ke a ajiye.

Har cikin jikinsa yau din yakejin sanyi da saukar ruwan. Yanason damina sosai,yana cikin sahun yanayiyyikan da yafi so a dukka wasu yanayi da muke dashi cikin rayuwarmu,saidai kuma damina da sanyi sukan zama wani yanayi dake farautar nutsuwar gangar jikinsa gaba daya. Suna sauke masa wani irin feeling me matuqar nauyin gaske,don haka sau tari killace kansa yakan qara yawa ne a duk sanda aka samu mamakon ruwan saman daya sanyaya gari....ko kuma yawaitar sanyi sosai cikin dare zuwa safiya.

Dukkaninsu da sassarfa suke tako stairs din dake kallon juna,wanda zata sadaka da gajeriyar veranda data hade fuskokin balcony dinsu da zai sada kowanne da ainihin sassansa ta baya. Yadda bata kula da shi ba tana kokawa da dankwalinta da ya nace saiya sauka daga kanta saboda santsin jiqaqqen gashinta.......daya hannun kuma tana rungume da Cherry's dinta da mistake kadan zatayi su zube......idan kuwa har suka zube ta tabbatar zai zama ba rabonta bane,don ba komai yake taba qasa ba tacishi ba,dare kuma yayi da ba yadda za'a sake shiga garden din a debo mata wani.

Saidai duk da yadda takai ga takatsantsan da sauri idanunta sun rufe,kuma cike suke da tsoron da har ta iso dab dashi a sanda hankalinsa shima ke kan keys din hannunsa yana duba wanda yake na qofar.

Bangazar juna sukayi,kuma a take cherry din da yake tattali ya watse daya daya a gurin.

"Subhanallah" Ya furta da deep voice dinnan nasa dake cike da sound na nutsuwa a cikinta yana yin taku biyu baya,kamar yadda itama taja baya da sauri cikin matsanancin tsoro,bugun zuciyarta ya sake ninkuwa ta ware manyan idanunta sosai a cikin sassauqan hasken da bame yawa ba,tana jin wani irin yanayi yana shigarta a hankali saboda shaqar wannan qamshin da tayi. Wannan qamshin dai da har yanzu ta gaza gane waye ainihin mamallakinsa?.....wannan malamin dake a gabanta yanzu?......ko abokin tserenta ne daga hippodrome?. Wannan qamshin dai daya tsaye mata a kwanya......ya yiwa kansa kyakkyawan gurin zama tsakanin tunaninta zuciyarta dama kafofin hancinta.

Dukka idanunta ta ware ta zuba masa,duk da cewa bata iya ganinsa tarwai,amma tana iya ganin yadda sumarsa me santsi ta kwanta sosai har saman goshinsa ta kuma sauka sosai a qeyarsa.

Walqiyar data gilma me tsananin haske ita ta bata daman hango wadannan idanun.......wadannan idanun dai da suka hanata sukuni.....wadannan idanun dai dake sake bata qaimi cikin kowanne taqi da taku nason cimma mamallakinsa ta masa hukunci me tsauri.....wadannan idanun da ba abinda take hanga a cikinsu face kallon raini da qanqanci da suke mata,tun daga wancan ranar har zuwa yanzun da walqiyar shima ta bashi daman ganinta sosai,amma a nutse taga ya janye idanunsa daga dubanta kamar yaga wani abu mafi muni ko qyama.

Yanayin kallon daya jefa mata,ya kuma dauke idanunsa hankali kwance kaman baiga barnar da yayi mata ba ya tunzura zuciyarta sosai. Ba wani d'a namiji daya isa ya tsaya gabanta kamar haka koda baiyi mata barna irin haka ba,ballantana shi daya watsar da cherry din da bata taba daukar wani abu daga takun daya haura goma ba sai yau.

"Kamar dai baka gani......kamar dai makaho ne kai?" Ta fada cikin hasala tana laluben maganganun da zata fada masu zafi.

Tun daga wancan ranar da taga yadda sultane ke nan nan dashi wani kakkaifan haushi da tsana sauka sauka a ranta game dashi,daga sanda ta fahimci da gaske sultane ya bashi matsayin da nata ne ita kadai ta sake jin bata da sauran ABOKIN ADAWA da yayi saura duk duniya saishi.

Da gaske tana da kishin a dauki son da ake mata ko kalar kulawar da ake mata a bawa wani. Tsarinta ne haka,ta taso ta tarar komai nata ne.....komai ita daya akewa......ita kadai ake saurara......so ba zata juri hada komai da kowa ba.....koda kuwa falaak ce......bata lamunta ta tsaya matsayi d'aya daidai dana falaak din.

Tana ganin sam bai cancanci matsayin da sultane ya bashi ba......malami fa?,me karantarwa?.....me sultane zaici dashi?,me sultane zai qaru dashi?,banda shi din da zai sake zamewa sultane din kayan nauyi?.

Tana tunanin zaya daga kai yayi mata kallo na biyu ne.....wanda yake fatan hakan ta kasance ko don ta samu hanya ta biyu da zata sake fadin magana me zafi,wataqila ta rage haushin dakw zuciyarta,amma ga mamakinta bai ko yi niyyar karkatar da kallonsa a kanta ba......tamkar ba wani halitta me rai dake tsaye a wajen,sai ya tsugunna a nutse yasa hannunsa yana tattare cherry din guri daya.

Ta fahimci so yake ya tattare mata ya bata abinta ba tare da komai ya sake cewa ba......a yanzun ba wannan take buqata ba.......ko yaya tanaso ta gaya masa magana me zafi da zata damu ransa,don haka sai taja siririn tsaki.

"Koda ka tattarasu........kimata ta wuce naci abinda ya watse haka a qasa" Cak ya dakata daga tattarawar da yakeyi,ya sanya tafin hannunsa saman gwiwarsa ya miqe cikin tarin nutsuwarsa ba tare da ya daga kai ya dubi inda take tsaye ba.

A nutse ya fara takawa yana nufar balcony dinsa. Tarin mamaki ya kusa daskarar da ita. Wanne irin mutum ne shi?,dame yake taqama?,ya manta qarqashin alfarmar mahaifinta yake rayuwa?,ya manta wace ita?,matsayinta?,da girman ikon fada aji da take dashi da bazai mata yadda dukka sauran hadimai ke treating dinta ba?.

Inda daya daga cikin mutanen dake rayuwa cikin gidanne,wadanda suke qarqashin ikonsu da kulawarsu kamar yadda yake shi din a yanzu ya aika mata haka,lallai da yanzu yana durqushe cikin feshin ruwan yana hurwar ta yafe masa,amma sai gashi shi cikin nutsuwa ma yake barin gurin.

Wannan fusatacciyar zuciyartata ke gaya mata.

"Waye shi da zai aikata mata hakan kuma ya wuce lafiya salin alin?" Wannan fusatar ita ta sanyata takawa d'af d'af,ta kuma sha gabansa sanda yake shirin dora qafansa saman step din da zai shiga balcony dinsa.

Da dukkanin blue eyes dinta take kallonsa da wani irin kwantaccen fushi. Tana son bashi assignment da har ya gama rayuwarsa cikin gidan bazai gama dashi ba.......idan har girman kai yakeji tanason ta yage wannan rigar girman kan. Ba jiya ko shekaran jiya ba......ta hangi wani tasiri na izza tattare da dabi'arsa,wanda take ganin baikai ace akwai wannan cikin jininsa ba,a matsayinsa na malamin da baisan komai ba sai karantarwa. Qasqantar da kai ne kawai ya kamaceshi ga masu mulki da sarauta irinsu,bawai nuna izzar da sam bai mallaketa ba,baibi hanyarta ba,baima san ina muhallinta da zai ajiyeta cikin qualities dinsa yake ba.

Tsakiyar idanunta yake kalla da kyau,duk da qarancin hasken dake wajen amma bai hanashi gano zallar girman kai da tsiwar dake dawainiya da ita ba. Walqiyar da aka sakeyi mai madaidaicin haske ita ta sake haska masa fuskarta sosai. Kwantacciyar sumarta data sauka har gadon bayanta da kuma kafadunta ta bayyana sosai saman zagayayyar fuskarta dake da wani irin sirrintaccen kyau me wani irin sanyi. Mayafin dake saman kan nata ya koma rabi saboda santsin gashin da kuma yadda iska ke kadashi kadan kadan.

Idanunsa ya zare daga kanta da wani irin mutuwar dukka gabbansa yana maida dubansa gefe daya. Tsaiwarta a gurin wani abu ne da zai iya masa tasirin da baya buqata,dukan da ruwa ya yiwa jikinta ya sanya doguwar rigar silk material din mannewa a jikinta sosai,ta kuma fidda shape na gurare da yawa a jikinta,shin ita bata ganin hakane?. Yaji tambayar tazo kansa.

Idanunsa ya lumshe sannan ya budesu,yana jin yadda feshin ruwa ke sauka saman fuskar tasa,yana kuma jin yadda taci gaba da qananun mitoci wanda ya cakuda da sautin ruwan dake sauka saman roofing din veranda din. Siririyar muryar dake da wani irin taushi......taushin da bai hana bayyanar tsiwarta qarara ta cikin maganganunta ba.

Dare ne......wanda saukar ruwan sama kan iya hana kowanne mutum dake nesa dasu qarar kowanne sauti komai girman sautin. Tana tsaye gaba kadan dashi da tazarar da bame yawa ba......duk wanda ya gansu a haka a irin wannan lokacin a kuma irin yanayin da ita take ciki ba shakka ba abinda bazai iya ayyanawa ba a ransa.

Baya son ya sake aza idanunsa a kanta,don ya tabbatar duk yadda zaiyi don ya kaucewa kallon guraren da bai halatta ya gani din ba abune me wahalan gaske,don kusan rabin sumarta a bude yake.

"Zaki iya matsawa kiban guri na wuce princess?" Ya fada calmly ba tare daya waiwayo ko ya aza idanunsa a kanta ba,saidai kuma can qasan ransa fushinsa ne yake motsawa kadan kadan,wanda bayason yayi wani motsi da zai tasirantu a kanta. Fushinsa na yadda ta tsare masa hanyar shiga sassansa,duk da akwai sauran space da zai iya wucewa din,saidai yayi qanqantar da zai wahala ya wuce lafiya ba tare da sun gogi jikin juna ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Ranta ya sake baci,ta sake zubawa gefan fuskarsa da kwantaccen qasumbarsa me tsari ta sake kwanciya saboda jiqewa da tayi idanu. Abinda take magana akai daban?,abinda yake fadi daban?,damuwarsa kawai ya wuce?.....tana magana dashi yana dauke idanu zuwa wani sashen na daban?.

Ko waye ko kuma meye sultane ya daukeshi wannan karon sai ta sanya an hukunta matashi,irin hukuncin da nan gaba bazai sake mararin koda hada hanya da ita ba.

Daidai sanda ta bude qaramin bakinta daidai lokacin wata irin walqiya me kashe idanu da wata irin tsawa gauraye ta karade sararin samaniya. Idanunsa ya lumshe yana motsa labbansa a hankali da addu'ar tsawa da ma'aiki ya koyar

"Alhamdulillahil lazi yusabbihur ra'adi bi hamdihi.....walmala'ikatu min kifatih". A hankali ya bude idanunsa suka kuma sauka a kanta. Tana tsugunne a qasa ta cure guri daya. Ko ina na jikinta rawa yake,wanda yake bayyanar da tsananij tsoro a tattare da ita me yawan gaske.

Idonsa ya sake daukewa ya maida gefe,sai ya qara sautinsa yana maimaita addu'ar a fili daidai da yadda zata iya ji.

Duk da muradinsa shine ya wuceta abinsa kafin bacin ransa yakai ga bayyana......amma fuskar sultane yake iya hanga a gurin......kebantattun maganganunsa da sukayi......maganganun da suka tilasta masa aminta da alfarmar da sultane ya nema a tare dashi bai ko iya musa masa ba.

"Ko yaya idan akhnan na cikin hadari.....nakanji wani abu a jikina,nauye nauye sunyimin yawa.......bazata samu kulawata yadda ya kamata ba,don Allah ko yaya koda sau daya ka zama me kula da lamarin daya shafeta daidai yadda zaka iya,ba don kowa ba saidon GIRMAN ZATIN ALLAH" Sautukan dake dawo masa kenan a yanzu.....yana kuma sake ji da ganin yadda dan qaramin amincin dake tsakaninsa da sultane keson takurashi.

Readers Also Read

More by Huguma