Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 14

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 14

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 14: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 14. "Na cika da mamakin yadda kika sarrafa almaz haka cikin…

3,362 words

"Na cika da mamakin yadda kika sarrafa almaz haka cikin sauqi tafisu?" Murmushi me dan qaramin sauti ta sauke,shudewar wasu daqiqu sannan tace.

"Kina manta cewa wannan jinin fa dake yawo a jiki ba qarya bane.....gado ba qarya bane.....ba kuma karambani ba.......komai lalacewar wannan tsatson sai wani abu yayi tasiri tattare dashi da zai tuna masa asalo da tushe.......makullan juya tunanin almaz......sarrafa almaz yadda kikeso shine......ki mu'amala dashi da karramawa......ki nuna kowa dake tare dashi ya girmamashi" Kai take jinjinawa,da gasken gaske taji dadin wannan shawarar ta tafisu.

"Kinci kyautar sulalla na gold tafisu guda hamsin".

"Godiya nake" Ta fadi tana rusunawa mammina din.

*BEENO*

Idanunsa na a kafe akan matan dake takawa cikin unguwar da ko gilmawar kare babu.

"Mata biyu ne.....saidai dukkansu fuskokinsu a rufe suke,koda zanyi hotonsu bana tunanin obbo zaka ga fuskokin nasu"

"Listen beeno" Haisam da ya dafe dukka hannuwansa saman dining table ya fada,sannan ya miqa hannun nasa yana gyara Bluetooth din kunnensa.

"Snap a pic.....quick" Ya furta da wani deep sound me cike da umarni.

Hotuna uku ya dauka,duk da cikinsu ba wanda fuskokinsu suka fito,saidai yana shirin matsawa baya don boyewa ganinsu busassun ganyaye suka motsa kadan,abinda ya sanya mammina kama hannun tafisu gami da tsaidata cak.

"Motsi kamar nakeji". Muryar ta sauka a kunnen beeno,abinda ya sakashi danna wani abu a gefen kunensa daya bawa haisam sign na DANGER.

"Ya muntaqeem.......ya hayyul qayyumu" Haisam ya fadi yana furzar da iska daga bakinsa.

"Keep calm beeno......kar kayi wani misbehaving......hold your breath for 30 second.....har sai sun wuce" Ya fada yana damqe hannunsa,yana jin kamar ya bayyana a gurin. Horon riqe numfashi abune me wahala koda a cikinsu ne.......amma ya aminta da beeno din,yana jin kamar zai iya......zaiyi succeeding.

"Banji wani baqon motsi ba.......banji wani baqon qamshi ba,inda akwai wani a nan dole iskar gurin ta sauyamin" Tafisu ta fada yana girgiza kai gami da ci gaba da sake watsa dubanta a kowanne sashe. Kai mammina ta jinjina a hankali.

"Na yarda dake......amma jikina yana bani haka har yanzu" Ta fada tana ci gaba da tafiya a hankali cikin takatsantsan fiye da yadda suka fara tahowa a dazu.

"Koda ba komai.....jin irin wannan yanayin a tattare dani bai fiya bani aminci ba......zan dage qafa har zuwa sanda almaz zai gana da me martaba"

"Hakan ba laifi bane" Tafisu ta fada tana bata qwarin gwiwa.

Qarar sakin numfashin beeno ya tabbatar masa komai ya tafi normal.

"Good job......kada ka motsa daga gurin sai bayan minti talati......ka isa gida lafiya" Haisam ya furta yana katse na'urar.

Wata kujera ya jawo ya zauna sasai akai,ya jawo personal system dinsa ya jona device din ya kunnata yayi connecting.

Kai tsaye ya wuce fannin tura hotuna,yayi clicking duka hotunan uku da beeno ya tura masa ya soma nazarinsu.

Nazari ne irin na qwaqwaqwafi da qwararrun jami'ai na binciken sirri ke yi a kan kowanne abu daya fado hannunsu da sunan bincike.

Dukkaninsu ba wadda ya samu nasarar ganin fuskarta kaman yadda beeno ya gaya masa,saidai kaya dai kaman wancan ranar.....kamar wancan lokaci. Tufafi ne na masu muqami sosai cikin masarautar agadez din.....manyan muqamai da sun kusa mata hamsin daga manyan sassan gidan uku. Iska ya furzar,yana jin lokaci yayi da zai sanya idanu yasan bayanan kowacce mace dake ta'ammali da uniform din,matsayinta da kuma iyakacin hurumin da take dashi a gidan.

Yana shirin rufe hotunan sai ya fasa,ya koma hoto na biyu yayi zooming nasa sosai. Hoton tafisu ne a farko,don haka shi ya fara zuqowa. Hannunta ya fito sanda take gyara itama lullubin kanta don sirranta fuskarta. Akwai wani abun hannu na duwatsu da suka zama ado wa tsintsiyar hannunta. Iya gurin kawai ya yanke ya fiddashi hoto me zaman kansa.

Dukka hotunan yayi marking sannan yayi forwarding nasu zuwa ga wani sabon adreshin,da rubutu taqaitacce da yaren Oromo a qasa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Ina buqatar bayanan tsaho da hasashen qiba na kowacce mata.......wannan hannun inason bayanai da binciken qwaqwafin me shi.......a fidda asalin halittar da me shi zata iya kasancewa dashi. Yana kammalawa ya tura,sai ya maida bayansa ya jinginar da makarin kujerar yayi relaxing sosai yana jin yadda a yau gajiya take bin sassan jikinsa.

Maher yayi kadan,yana buqatar kota yaya ya zuba ma'aikatansa Shima cikin gidan.......yana aqalla kowacce qofa ya zamana akwai mutuminsu koda mutum daya daya ne......tabbas zaiga sultane a gobe duk da bai shiryawa hakan ba,zaisan kuma yadda zai shigo da tsarin cikin sauqi.

Hannun rigarsa ya nannade ya kuma wuce zuwa toilet ya daura alwala,ya dawo ya shimfida lallausan abun sallarsa ya tayar da sallah a nutse. Sallar dare wani makaminsa ne ne qarfi da girman gaske tsakaninsa da ubangijinsa.......wani qarfinsa ne walwalar matsalarsa sannan kuma jagoransa a duk sanda ya sanya wani al'amari a gaba dama rayuwarsa ta yau da gobe.

Koda ya idar ya jima saman abun sallar yana karanta wasu addu'o'i,tsantsar dangantaka me qarfin gaske yake ji tsakaninsa da ubangijinsa a irin wannan lokacin. Gari yayi shuru,ko ina yayi duhu ciki harda dakinsa da yake zaune a yanzu haka,don yana jin dadin kebancewar da zaiyi da ubangijinsa ta zamana cikin sassauqan haske da ba can can zaka gane abinda ke dan nesa da kai ba.

Shafa addu'arsa sai ya zamana kamar maqullin budewar duk wata dabara tasa. Qaramin murmushi ya subuce masa yana sake imani da yaqinin cewa,tabbas idan ka roqi Allah kana da nufi me kyau,to tabbas ne zaya amsa maka addu'arka a kusa ko a nesa,sai ya miqe tsam yana kunna bedside lamp da yakeji haskenta kadai ya isheshi. Komai ya bude sosai cikin kansa........kai tsaye ya jawo wayarsa da har ya riga ta kasheta ya soma da kiran maher.

Bugu biyu kawai maher din ya daga,muryarsa da sanyi sosai da alama bacci nason fara daukarsa.

"Ka matsa daga qofa na?"

"Aah......lokaci baqai qarasa ba"

"Akwai buqatar koda lokaci yayi kada ka matsa din.......akwai qaramin hari da zai faru yanzu cikin gidan,kada ka aiwatar da komai banda abu biyu,basu hanyar shiga da basu hanyar fita cikin mintuna goma kadai.......ba wanda za'a cutar ba wanda za'a illata......kawai akwai hankulan da nakeso a tabasu da shiyyar da nakeso a bawa qarfi....."

"Done obbo" Ya fada cikin tsananin girmamawa da biyayya.

"A bayan ka basu qofa sun fice ina buqatar basajar da zata bayyana cewa kaika fatattakesu daga shiyyar zaituna da suka nufaci zuwa......koda qaramin rauni ne ka samar dashi a jikinka......zan kula da wannan".

"An gama obbo"

"Ka fahimta?" Ya tambayeshi don gudun samun sabani. Kai ya jinjina

"Sama da yadda kakeso na fahimta" Ya amsa masa da qarfin gwiwa.

"Ka fara shiryawa,amma na'urarka ta kunne ta zama active to keep in touch"

"Yes obbo" Sai duka suka gintse kiran,sannan ya maida akalar kiran ga omari.

"A cire beeno a ciki......he done the best a wannin da suka wuce,a bashi relaxation hours" Ya bayar da umarni wa omari.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 24* ________________________ *Assalamu alaikum warahmatullah*

*_Ina me farincikin sanar daku in sha Allah gobe zan saki hotunan tsala tsalan takalmanmu da suka iso kai tsaye daga qasar sin wato CHINA_*

*_Takalman yara maza da wasu nau'ikan unisex DAKI BARI_*

*_MUNA MUKU ALQAWARIN AMINCI DA QUALITY IN SHA ALLAH_*

*_ZAKU IYA JOINING GROUP DINMU TA WANNAN LINK DIN_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX

*KO MAGANA DANI KAI TSAYE TA WATSAPP TA WANNAN NUMBER WAYAR*

08187255862

*SIYAN NA GARI....MAIDA KUDI GIDA*🙌🏽🙌🏽🙌🏽🙌🏽 ____________________________

*_WASHEGARI_*

Cikin wani kyakkyawan kurta pyjamas yake da akayi da sassauqan yadi navy blue a idanu,sadai asalin zare da audugar da aka saqa kayan masu tsadar gaske ne. Simple dinki akayi mata wanda ya fidda kyansa da kuma haibarsa,kamar yadda color din kayan ya fidda moderate hasken da fatarsa ke dashi me ban sha'awa.

Da alama cikin shirin fita yake,saboda gefansa agogo ne da farin rawanin da ya nadu ya zauna sosai saman gewayayyar hular da yakan sanya me wani irin yanayi me daukan hankali,rawanin da yawan mutane ko ince malaman Indonesia Malaysia ke amfani dashi.

Tsaye yake riqe da takardun guda biyu a hannunsa,tsaiwar data fidda siffa da zubinsa na GIANT GUY dake sa wani irin cikakkiyar suffa da kamala me janye hankali da idanu.

Takardar farko dake dauke da gwajin komai dangane da hoton matan jiya bata dauki hankalinsa ba kamar wannan ta biyu,wadda ke dauke da qerarren abun hannun daya gani daga hannun mammina......da kuma bayanan da bincike ya bayar akan abun hannun.

Abun hannu ne me dad'ad'd'en tarihi tabbas,wanda a yanzu ba kowanne gida ake samunsa ba cikin oromian region,sai gidajen sarakuna da manyan attajirai,wanda Shima yasan da hakan,amma abinda yafi janye hankalinsa shine an samu tabbacin akwai me irin abun hannun cikin iyalin gidan AJANI da ita daya ta taba mallakar irinsa,saidai kuma an samu bacewar abun hannun ba'a san kuma inda za'a ganshi ba bare a zurfafa bincike a kansa. Danyan gwal ne aka dunqule aka sarafashi a haka,wanda gidan mahmud ajani shine gida na farko da aka taba ganinsu da irinsa,wannan ya sanya nasu ya banbanta da irin na kowa.

Takardar ya maida ya ajiye kafin Shima ya zauna a gefanta yana fidda siririyar iska daga bakinsa. Yana jin wani qarfin gwiwa da yaqinij qarfafa zarginsa akan mammina. Meye hadinta da qasar Ethiopia?........meye hadinta da abun hannun daya kasance shaida ce kuma alama ce ta attajiran qasarsa?......ya akayi ta samu abinda ya kasance yana da alaqa me qarfi da zuri'ar AJANI AHAMED?.

Yatsunsa ya cusa cikin gashin kansa,ko yaushe abubuwa sake gabatowa suke gabansa da zafinsu,ta kowanne bangare ta kowanne sashe da qulli da dabaibayi komai yake zuwa masa.......amma zuwa yanzu ya samu cikakken hujjar da zai sanya idanu......cikakken hujjar da zai fara bibiyar al'amuranta da tsananin qarfi.

Faruwar komai a jiya kawai yasan wani babban mabudi ya samu,wata babbar hanya da komai zaizo masa da sauqi.....dole ya dauko asalin abun hannun daga can cikin dakinta zuwa hannunsa don ya aike dashi a sake duba masa tabbacin SHI DINNE?.

System dinsa ya jawo,yayi wasu rubuce rubuce sannan yayi saving ya maidata ya ajiye,ya miqe a nutse yana daukan Amama dinsa ya qarasa gaban madubi. Yaji dadin nemansa da sultane yayi a yau din,don dama yasan dole hakan tana iya faruwa......zaya nemeshin ko don abinda ya faru a jiya cikin wasu sassa na gidan. Wannan kjma shine target dinsa,zai ganshi ne a sanda shi sultane din da kansa ya nema zuwa gurinsa,ya kwana jiya yana addu'a samun sassauqar hanyar shigar da buqatarsa,ya kuma samu dukkan wani dama,komai ya tafi daidai,komai kuma ya tafi har fiye da yadda ya tsara.

Ya dora amaama din saman kansa,jelar da kanyi reto daga gefan kafadar damansa ya zagaye habarsa har zuwa saman hancinsa da ita yadda ya saba yi a yawancin lokuta,wannan ya santa dogon hancinnan da kyawawan labbansan masu daukan hankali.

A nutse yake saukowa zuwa qasa,inda ya samu cook dinsa ya kammala breakfast tsaf cikin tsafta da tsari. Yau din shi daya ya kwana cikin sassan,don abdii ma cikin plan din jiya bai kwana cikin gidan ba.

Cikin matuqar girmamawa ya rusuna yana gaidashi gami da yi masa barka da fitowa. Kai ya gyada masa,sannan a nutse ya shaida masa a kwashe komai,zaiga sultane ne,baisan kuma ko qarfe nawa zai shigo ba.

A nutse yake karantar yanayin sauyawar masarautar daga jiyan zuwa yau,yanayi ne da zai tabbatar maka akwai wani alhini daya faru. Gefan sassan mammina da morsa safiyya akwai qarin adadin masu bada tsaro Sosai fiye da ko yaushe......saidai na gefan mammina din har yaso ya dara na morsa safiyya.

Idanunsa ya janye yana lumshesu,wani qaramin murmushi dake boye qasan mayafin amaama dinsa ya qwace masa. Haka mutane ire irenta suke,basa qaunar mutuwa ko wani abu da zai kawo barazana ga rayuwarsu......iya wannan motsin nata kawai ya sake dasa zargi me qarfi game da ita a ransa.

Cikin girmamawa da martabawa sultane ya miqe da kansa don tarbarsa kamar yadda ya saba. Yana ganin girma da martabar dattijon basaraken da yakeji a jikinsa akwai abubuwa da yawa da suke boye daga saninsa. Akwai abubuwa masu yawa daya kamata ya sani smma baisan dasu ba,akwai al'amuran da suka yiwa saninsa b'atan dabo da badda bami. Cikin girmamawa daidai da yadda zaiwa motii ya bashi hannu sukayi musaba,murmushi kwance saman fuskar sultane,yana jin wannan feeling din wannan yanayin na tamkar yana tare da dan cikinsa daya rasa shekarun baya AHMAD.

"Bismillah" Sultane ya fadi yana nunawa haisam daya daga cikun kujerun dake kewaye da gurin,wanda dab dasu wata kyakkyawar table mat ce me girma da aka soma zube royal warmers da spoons na cin abincin sultane din.

Kafin su fara tattauna komai akayi sallama daga bakin qofar parlor din. Falaak ce sanye da baqar doguwar riga yalwatacciya sosai,ta kuma lullube kanta zuwa kafadunta da baqin mayafi mahadin doguwar rigar. Duk da kasancewarta me dan duhun fata amma shigar tayi mata kyau sosai,ta kuma fidda sanyin halin da take dashi.

A kansa idanunta suka fara sauka,gabanta ya fadi da wani irin kwarjini me yawan gaske da taji yayi mata. Dan kwanakin da suka tafi hutu kawai na tsakiyar lokacin karatu sai taji kaman ta jima sosai bata ganshi ba.

Ta nema dukkan wani dalili da zaya sa ta ganshin amma kuma babu,yau dinma ba zata ne,bata sanya ran zata ganshi ba,amma hakan sai ya mata dadi sosai.

Cikin tsanaki da nutsuwa take shigowa cikin parlor din,kanta a qasa tana jin wani irin nauyi fargaba da kuma faduwan gaba yana saukar mata.

"Ta kasa zaune ta kasa tsaye.....kada a rabata da dan tsohon babanta ko?" Sultane ya fadi cikin murmushi da salo na tsokana daya alamtawa haisam akwai sakewa sosai tsakaninsa da ita,da kuma kalar qauna da jituwar data banbamta dana 'yar uwarta.

Murmushi kawai ta saki,bata tsaya biyewa sultane yadda ta saba ba,ta qarasa gaban haisam ta tsugunna tana gaidashi.

Cikin girma ya amsa mata,abinda ya yiwa sultane dadi,saboda yanayin ya masa kama da yadda babban yaaya yake daukan girma wa qannensa.

"Abincin ya iso,a nan zan zuba maka bappi?,ko saman table?" Tayi tambayar idanunta akan sultane,amma duka hankalinta yana kan haisam da kacokam idanunsa akan wayarsa suke yana karbar wasu bayanai daga maher na abinda ya faru daren jiya.

"Aah zuba mana a nan,ga yayanki nan ma tare zamu karya dashi" Miqewa tayi a tsanake,duk da yadda takejin qafafuwa da hannayenta suna dan rawa,saboda har yanzu kwarjininsa dukanta yakeyi,abinda ya danja hankalin sultane kadan kenan a kanta,yaci gaba kuma da noticing yadda ta zagaya rukunin kujerun dake gabansu inda table mat din yake tana zuba abincin kamar ba nutsuwa sosai a tattare da ita yadda ya santa.

"Muhammad" Sultane ya kira haisam bayan ya maida dubansa kansa. Qaramin murmushi dake dauke da girmamawa ya saki,yana ajiye wayarsa gefansa.

"Ya mukaji da alhinin abinda ya faru damu a jiya?" Haisam ya fadi cikin girmamawa da son ya fara dora tattaunawarsu a gurbi da muhallin da zai sanyo buqatarsa.

"Mun godewa Allah.....ba wanda ya rasa rai ko yayi rauni me yawa,sai hadimi guda daya da akace shine ya bawa sassan zaituna kariya......ba'a samu rayuwarshi ba sai dazu da safen bayan qarfe takwas saura" Kai haisam ya jinjina,ko sultane bai dora komai ba yasan akan maher yake magana. Maher din yayi aiki me kyau har fiye da yadda ya zata,kuma komai ya tafi daidai da harshi kansa ya gamsu da acting din da yayi. Wannan dalilin ya sanya shi da kansa yake saluting kalar team din da yayi raising da kanshi cikin national intelligence security service. Team ne da babu rago.....babu malalaci a ciki,kalar team din da sai aiki na musamman ake fita dasu KAMAR KUMBO KAMAR KATANTA.....da gaske yadda shugaba ya kasance haka dole mabiyansa zasu kasance,yadda SHEIKH MUHAMMAD HAISAM yake jajirtacce......haka kowanne namiji dake qarqashinsa yake tashi da kalar wannan jajircewar....da kalar wannan qwarin gwiwar....da kuma kalar wannan jarumtar tabbatacciya daga ZUCIYA DA QWANJINSU.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Duk da inaji a jikina lamarin ba wani babba bane......amma zaituna ta tashi hankalinta da yawa......tun jiya har yau qoqarin fahimtar da ita nakeyi ako ina ana iya samun irin wannan yanayin amma bata fahimta din ba.....tadai nunamin damuwarta ba tata bace karan kanta,damuwarta kan mutanenmu ne,jama'ar da muke mulka wadanda suka cancanci samun zaman lafiya da tsaro me kyau qarqashin shugabancinmu". Idanunsa ya lumshe a hankali yana jinjina kanshi sannan ya sake budesu akan fuskar sultane.

Jinjina kansa bawai na gamsuwa da bayanai da sultane ya bashi ba......ba na gamsuwa da abinda mammina ta fada bane......na gamsuwa da cewa lallai matar ta iya buga wasanta yadda ya dace.....lallai ta iya amfani da kowacce kalar dama da zata gifta ta gabanta ne.

"Na fahimci akwai gaskiya cikin kalamanta,don ita daya ce damuwarta ta zama gaba da abinda zai sameta ita a karan kanta.......wannan ya sanyani tunanin irin tsaron da zamu qara cikin gidan nan don kaucewa faruwar irin abinda ya faru a jiya ko wanda yafi haka a gaba".

Komai sai haisam yaga yazo masa da wani irin sauqi da bai taba zata ba,duk da zai wahala ya kafu saman abun sallah ya yiwa Allah naci da neman dafawarsa akan wani abu kuma hakan bata tabbata ba.

"Gaskiya ne,haqqin kowanne shugaba ne ya kula da rayuka da lafiyar mutanensa......don kuwa Allah SWT zai tambayeshi ranar qiyama game da kowacce rai qwaya daya data yaya ta rayu qarqashin mulki da ikonsa" Kai sultane yake jinjinawa kawai,zamansa da haisam yana sake tuna masa girman nauyin dake kansa,wanda koda iya wannan kadai ya rabauta ya isheshi,ballantana kuma zuciya da ruhinsa cike suke da dorewar alaqar tafi haka. Gyara zamansa sosai sultane yayi yana tattara hankalinsa ga haisam

"Yanzu me kake ganin za'ayi?,wacce hanya da shawarwari zamu bi?" Ya tambayi haisam yana so yaji ta bakinsa.

*Mammina*

Ko qiftawa idanunta basu sakeyi ba tun daga lokacin da kunnenta ya jiyo mata babban motsi qararraki da ifce ifce. Daga sanda yalwa ta shaida mata kamar an kawo farmaki cikin masarautar kuma tunda ta sauka daga saman gadonta bata sake hawa kanshi ba.

Ba zatace bata zauna......ta zauna amma yayin da take tahiyar sallah,amma banda hakan,har yanzu da agogo ke nuna sha daya ta gota ba wani data aiwatar na dukka al'adun data saba yi daga safiya zuwa wannan lokacin.

Farmaki ne da aka kawo cikin gidan,farmakin da za'a iya cewa idan ya qazanta kai tsaye ya shafi kowa.......to amma cikin jininta da jikinta takejin kamar an kawo farmakinne kai tsaye saboda ita.......tamkar itace abun hari takai tsaye da aka nufata.

Hankalinta ya tashi qwarai sanda ta kalli maher da yayi kaca kaca da jini......abinda ya sake tabata,ya kuma saka mata shakka kokwanto da rashin nutsuwa me tarin yawa.

Da tafisu ta fara ganawa,don a ranar ba wanda ya smau ganinta cikin hadimanta,don ko wanka ma bata samu damar yi ba don tana jin a yanzu bata wannan take ba. Bata bari matsala ko yaya ta gilma mata,don ta riga ta canfa.....kowacce matsala daga qarama take farawa kafin ta zarce zuwa babba.

"A jiya naji a jikina akwai wani a sanda muka fito daga ganin almaz.......bayan na zargi wani abu kuma saiga wani baqon lamarin da nake zargin ba daga can ya biyo diddigi da sawunmu ba?" Ta furta tana duban tafisu.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 25*

Kai ta girgiza a hankali tana duban mammina.

Readers Also Read

More by Huguma