L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 15
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 15: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 15. "Inda akwai wani mahaluqi tabbas zan iya jin dumin…
3,346 words
"Inda akwai wani mahaluqi tabbas zan iya jin dumin numfashinta daga tazarar dake tsakaninmu......ba numfashin wani dan adam ta gurin sam sam......bana tunanin akwai wani daya wanzu a gurin" Kai mammina ta girgiza cikin rashin gamsuwa da bayanan tafisu.
"Lallai akwai wani baqon abu......akwai wani abu daban dake wanzuwa a muhallin da ba nashi ba.....a muhallin da ada babu shi a gurin"
"Akwai shigowar baqi ne masarauta?......ina cewa kin datse duk wata hanya da qofa da zata bawa baqo daman shigowa ko zama cikin masarauta?". Kai ta gyadawa tafisu,amma gefe guda tana zurfafa tunaninta.
"Ba wani sabon baqo da aka sake samu........saidai akwai baqon da yashigo tun kafin wannan lokacin..????" Ta qarasa maganar kamar tana yiwa kanta tambaya ko tuhuma game da haisam.
"Tafisu........maza kiramin bulama" Ta fada a dan rikice. Sama da qasa tafisu ta girgiza kanta alamun girmamawa sannan ta tashi zuwa hanyar fita.
Fitar tafisu tana jin kamar ta jawota ita da bulama din ta tsincesu a gabanta. Ta manta shaf ta bada aikin bibiyar mutumin,ashe tana da tarin hangen nasa har haka ita kanta bata sani ba?.
Samun kanta tayi cike da fatan ta samu wani abu da zaya bata haske game dashi,wasu bayanai da zasu iya haska mata shi......ba shakka idan har haka ta kasance YA SHIGA UKUN DA BABU FITOWA.
Abubuwa da yawa ta dinga hadawa game dashi cikin kanta. Bata taba samun halittar da take ganin kwarjininta sama dashi ba,hakanan kuma zuciyarta da ruhinta sam sun gaza jin aminci game dashi.....gefe daya tana jin wani qaqqarfan rashin jituwa dangane dashi dake zabalbala daga jininta a kansa.
Duk wani baqo daya samu gindin zama ya karbu hannu bibbiyu itace ta karbeshi.....dalili......bata abu a banza......bata aikata aikin da bazata samu yabo ko kwarzantawa ba daga bakin sultane mazauna gidan dama talakawan AGADEZ. Ta buda hannuwanta bibbiyu tana karbar baqi da 'yan gari dama dukka wanda rayuwa ta raunatashi......wannan yaja mata soyayayya farinjini da qauna me tarin yawa daga garesu.....don haka sai taji kamar FADUWA ce ace mutum kamar haisam din daya samu karbuwa a gun sultane da wani yanayi da har yau yake bata mamaki ace kuma SAFIYYA ce silar shigowarsa masarautar ba ita ba.
Da farko ta dauka iya wannan kawai shine dalilin da ya sanya ta fara jin rashin jituwa a kansa,sai daga bisani ta fahimci KWARJINI yake mata......yana da tasirin IZZA cikin jininsa,wanda ta saba kowanne malami ma da yake cikin masarautar neman gindin zama yake a gurinta don ya samu karbuwa daga sultane......amma shi wannan koda sau daya bai nemi ganawa da ita ba.....hasalima kamar baida labarin komai a kanta.....,kamar kuma baida labarin irin TASIRI da qarfin IZZAR da take da ita cikin gidan gaba daya.
Kwarjininsa da take yawaita gani ya sake dasa mata qatuwar ayar tambaya......yadda yake iya girgiza tsarinta da idanunsa kadai ya sanya takeson sanin komai a kansa,don tana jin kamar ba ordinary mutum bane.
Tunaninta ya yanke sanda tafisu ke shigowa ciki bulama na bayanta. Ya qaraso jikinsa na rawa ya zube a gabanta yana kwasar gaisuwa.
"Ina labari......wanne abune na daban daka samu ganowa cikin aikin dana baka?" Ta fada tana watsa hannuwanta kamar wadda ke jiran ya bata wani abu.
"Allah ya baki tsahon rai......ko a yanzu a bakin aikin nake kika sanya aka nemoni.......bana taba daga masa qafa tun daga safiya har zuwa sanda dare zai shigo......to amma komai da kike zato a kansa ba haka bane.......ba kasafai yake fita ba don baisan kowa a garinnan ba.......yafi zama yayi karatu shi kadai cikin dakin litattafansa. Abu daya ne da zan iya cewa na gani shine,kawai zuzzurfar alaqa ta aminci tsakaninsa da sultane da tsahon shekaru ban taba ganin wanda ya bawa aminci irin haka ba,yana kebewa dashi,daga shi saishi......yana kuma iya bashi ragama r yanke wasu hukunce hukunce da suka shafi lamuran masarauta,harma yana iya cin abinci tare dashi kamar dan cikinsa.....kamar dai yanzun,suna tare da zummar cin abincin safe shi dashi da gimbiya falaak,darensa duka bacci yakeyi,koda sallar dare a farkon dare na fahimci us fiya yinta,yana kwanciya bacci da wuri bai fiya wanzuwa ido biyu ba har zuwa asuba.....na biyu kamar yana da zurfi da kaifin tunani dana hangen nesa......akwai motsi da yawa da yayi wanda ya sanyani a zargin yana ganina koma ya ganni,to amma sai daga baya na fahimci bai fahimci ina biye dashi din ba kamar yadda na zata......yana tsarguwa ne da hakan".
"Indai zai tsargu da ana bibiyarsa kuwa tabbas akwai wani QULLI cikin zuciyarsa.... Wanda ke rayuwa sak baya raya wani zaya bishi.....koda an bishi ma yasan ba wani abu da za'a tsinkayo bare a bankadashi,ka sake kusantarsa kadan......ka kula da takunka da kyau......bana buqatar samun wani akasi ko wani abu na ba daidai ba" Tayi maganar da kakkausan gargadi cikin idanunta.
Qasa ya zube kansa yana maimaita mata shima.
"Ba zaki samu wani akasi ba ko sau daya na Miki wannan alqawarin" Ya amsa kanshi a qasa
"Kana iya tafiya,an sallameka" Tafisu ta bawa bulama umarni,ya yunqura yunqurawar data bayyana tsaho da fadinsa,ya fice a gurin da sassarfa don zuwa ya dora daga inda aikinsa ya tsaya.
"Duk da a daidai wannan lokacin nake sanya ran akhnan zataje gabatar da almaz wa sultane......ina buqatar shiga gurin" Ta furta a fili tana jin buqatuwar zuwa gurin sultane din don komai ya wanzu a idanunta.
"An gama" Tafisu ta fadi tana miqewa don bawa mammina daman shirya kanta.
"Ki nema tamim ki shaida masa.......nan da minti ashirin zan fito,zan kuma ganshi kafin na wuce gurin sultane".
"An gama" Ta sake fada tana rusuna mata sannan ta juya tana ficewa.
Cikin mintuna ashirin da biyu ta shirya tsaf,cikin madaukakin adon dake bayyanar da kalar cikar kamalar izzarta da kuma amsa sunan GIWAR SULTANE. Sunan dake matuqar yi mata dadi,sunan data tabbatar a duk sanda safiyya zata jishi yana haifar da wata susa sai qwarzane cikin zuciyarta.
"Tamim yana dakin baya yana jiranki" Tafisu ta gaya mata sanda ta fito cikin qasaitarta,da zubin taku da yanayin da baka isa ka tsinciki damuwa da firgicin da zuciyarta ke ciki ba tun daga daren jiya zuwa yau din ba.
Ita daya ta isa shiyyar,ta samu tamim din a tsaye,sanye d wadannan kayan dake sake nuna irin girman jikinsa da kuma dacewa da muqamin BAUTA. Ginannen jikin da ka iya razana me shirin kawo wargi.
Bayyanarta ya sanya tamim lanqwasa gwiwarsa ya kuma zube a kansu yana miqa gaisuwa,tamkar yadda dabi'arsa take a duk sanda yake gaban mammina ko gaba wani daga cikin ahalin sultane din.
"Tamim!" Ta kira sunansa da sautin daya tabbatar masa magana ce me tsananin muhimmanci a tattare da ita.
"Ki dade kiyi qarko" Ya amsa mata yana daga kuben takobin dake rataye a qirjinsa.
"Me yake faruwa a Ethiopia?" Ta masa tambayar Kai tsaye,tambayar data sanya shuru ya ratsa a gurin na wucin gadi,kafin tamim ya amsata.
"Komai yana nan kamar yadda yake.....komai yayi bacci,wasu abubuwan sun sume kuma suna dab da mutuwa......ba wani tashin qura ko razanannen motsi da zai farkar ko rayar da wadannan abubuwan" Kai ta girgiza tana duban tsakiyar qwayar idanunsa.
"Banajin gamsuwar haka a jikina......inaso a sake bincika min......idan nace a bincikamin bawai bincike na kwana daya zuwa sati daya ba.......a'ah,bincike na iya adadin kwanakin da komai zai fita da anihin amsarsa.........bana buqatar amsa da gaggawa,sakamako me kyau nake buqata.......sakamakon da shine zai zame mana jagora zuwa tayar da tsohon aiki ayi masa kwaskwarima zuwa sabo......na gaji da wanzuwa akan wasu turbobi da suke tsikarina suna tauyeni.......ina buqatar a kammala shirin komai a kuma kawo qarshen komai,koda kowa da komai zai mutu" Kansa ya kafe a qasa cikin tsananin biyayya.
"An gama" Ya fadi yana cake takobinsa a qasa,ya dogara da ita sannna ya miqe.
*akhnan*
Ta gama shiryawa cikin wani yadi me sauqi dake bayyana asalin qabila da yarenta na cikakkiyar buzuwa gaba da baya,shigar da take sanya ran zata sanyaya zuciyar sultane ya kuma kalli magana da zataje dashi da sassaqan harshe. Tana fatan yadda yake qaunar ganin safeena cikin irin wannan suturar,a yau ya dubeta da idanun da basu da maraba da irin duban da zaiwa safeena din,cikin soyayya qauna da martabawa. Ba mammina a gefanta......amma ta samu qwarin gwiwa me yawa daga gareta.
Ta yita kallon kanta da kanta a madubi,tayita kallon fuskarta a madubin tana juya yadda zata fuskanci sultane yau.....da zabin daya jima yana mata tana wofantarwa.......ta ture nasa muradin.....ta tunkude zabubbukansa har goma sha hudu.....ta kuma zo da nata zabin.
Amma tana ji a ranta akwai daidai me yawa cikin nata zabin data yiwa rayuwarta.....bawai tayi bane don ta watsawa sultane qasa a idanu.....bata yi bane don tozartashi ba.....ba kuma tayi bane don ta nuna masa bai isa ba......tayi ne saboda tattalin kanta da rayuwarta da a nan gaba take da tabbacin zai fuskanci haka duk daren dadewa.
Baya taja a hankali jikinta na fidda sassauyan qamshin turaren kabbasa na kamfanin INCENSE BY KABODAUGHTER daya mamaye ilahirin suturun sawarta,wanda ba wani cikakken motsi da zatayi sai sirrin wannan sirrintaccen qamshin ya fita. (Tasted and trusted,duk wani turaren wuta da khumras da zaku gani cikin novel dinnan ingantattu ne dana tabbatar da iyawarsu d qwarewarsu fiye da yadda kuke zata +2348032119803).
Birra kawai ke take mata baya,suna tafiya a nutse har zuwa sanda daya daga cikin wayoyinta dake hannun birra suka dauki tsuwwa. Cikin girmamawa ta matso dab da bayanta da zummar mata bayani,bata barta tace komai ba ba tare data waiwayo ba ta daga mata hannu
"Ko waye ki daga ki sanar dashi bazan iya daga kira ba a yanzun" Komawa tayi da baya,neesha ce ta kuma shaida mata abinda akhnan din tace. Batace da birra komai ba sai da suka kawo gabar da iya matsayin birra kenan kuma dole ta koma.
"Ki sake kiranta ki gaya mata,duk wani damuwan office tayi maganan da aisa,idan bata sameta ba shehnaz". Sannan taci gaba da takawa a nutse kamar wadda ke irga adadin takun da zata iyayi.
Da lallausar muryar nan tata dake da wani irin value da tsada gami da wahalar ji a kunnuwan maza da yawa tayi sallama,sallamar da bata bada wani sauti me yawa ko qarfi ba,amma ta bawa dukkan wanda ke cikin parlor din damar jin siririyar sallamar,ciki harda sultane dake zaune saman wani tattausan kilishi na daban yana fuskantar falaak da kuma haisam dake zaune saman wani kilishin na daban,gabansa shiryayye butar shayi ta wani nau'in qasa da tab'o da aka sarrafa me tsananin riqe zafi saboda gidan sarauta irin wannan.
Tea set ne da sultane ke ji dashi sosai,wanda ita daya a duniya ya iya mallakawa irinsa saboda girma da zurfin soyayyar dake tsakaninsu.
Ya tanqwashe qafarsa cikin nutsuwa,har kana iya hangen lallausar socks din qafarsa,duka hannuwansa biyu riqe da wayarsa yana sarrafata,don ba kasafai ya fiya son aza hankalinsa akan abinda bai shafeshi ba.
Magana ce tsakanin 'ya da mahaifinta,changing course falaak din ke sonyi kai tsaye zuwa bangaren qur'anic science.
Cikin sanyin murya take bawa sultane hujjojinta,saidai can qasan muryarta shi ya dago wani abu da sultane din bai hanga ba. Saidai baice komai ba,don yana ji a ransa na huruminsa bane.....bai shafeshi ba.
Hasalima ba komai yakeson sultane yaci gaba da sanyashi a ciki ba......don zamansa temporary ne,baya son sultane din yayi mugun sabon da rashinsa a kusa zai iya zame masa matsala da kuma damuwa.
A karon farko idanunta suka fara sauka a kanshi sanda sultane da falaak duka suke daga kansu zuwa gareta,saidai shi din labbansa ne kadai suka motsa alamun ya amsa sallamar,amma koda gashin idonsa bai motsa ba da nufin daga kanshi har ya sauke dubansa a kanta.
Wani irin abu taji ya saukar mata,zuciyar ta taji tana quntacewa guri guda tana matsewa a qirjinta. Banda sultane ya riga daya ganta.....banda irin wannan ranar yafi dacewa suyi magana da sultane su qare don ta samu daman komaqa Niamey a cikin wannan satin ba shakka da ba abinda zai hanata komawa da baya saboda ganinsa da tayi a wajen
"Me yasa ko yaushe?.....ko yaushe nake buqatar 'yancina?,ko yaushe nake buqatar magana da mahaifina shi din yake kasancewa a gurin?......me yasa na rasa 'yancinnan......wannan matsayin na kebancewa daga ni sai sultane tun daga sanda ya wanzu a masarauta?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar tana jin wani irin bacin rai yana sauka matar gami da gusar da dan guntun freshness din data samu na samun bulalliyar mafita.
Da wannan kallon dake cike da kulawa......da wannan kallon dake dauke da qaunar datasha banbam data sauran 'ya'yan da ya haifa......qaunar da a wannan karon yake qoqarin yaqi da ita yake dubanta.
Da rusunannun idanunta ta qaraso tana yiwa kanta muhallin zama daura da falaak. Numfashinta take qoqarin daidaituwa,tana jin yadda dakin gaba daya ya gauraye da wannan qamshin dai. Wannan qamshin da har yanzu ta rasa makamancinsa......qamshin nan daya zame mata tamkar jarrabi tun daga hippodrome kawo yau......qamshin da har yanzu ta rasa waye ainihin mamallakinsa?......wanne irin turare ne wannan me kassara gabobi?.
"Barka da safiya yaa biftu" Falaak ta gaidata cikin girmamawa qauna da kulawa irin ta 'yan uwantaka. Motsa labbanta tayi da qyar tana maidawa falaak.
"Barkanki.......barka da safiya bappi" Ta furta tana rusunar da idanunta da kanta don nuna girmamawa ga sultane din.
"Barkanki kadai khadeejatu". Ya kirata da asalin sunanta,sunan da ya sauka sosai saman zuciyar haisam ya kuma maimaitashi cikin qirjinsa har sau biyu
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 26*
Sunan wani suna ne da yake da tarin daraja martaba da kima a idanunsa,sunan NANAY dinsa......halittar 'ya mace ta farko daya soma so da qauna a rayuwarsa,yake kuma qauna har yanzu,yake martaba dukkan wanda yake da irin sunan bama ita kanta din ba.
Dauke idanunsa sultane yayi daga kan akhnan din data koma wani cool,yana karantar duk wani yanayi nata da motsinta,yana kuma ankare da yadda bata gaida haisam din.
"To kaji muhammad......ita kuma qanwar naka canjin course din da takeso tayi kenan" Sultane ya fada da murmushi saman fuskarsa yana duban haisam cikin tarin kulawa da kuma kwadayin shigar haisam din kowanne al'amari daya shafi iyalinsa. Ya fuskanci har yanzu haisam din bai shiga lamarin iyalinsa da zurfi yadda yakeso ya shiga ba. Yanaso ya saje dasu ya dinke dasu sosai,ya zama ba wani banbamci ko kadan a tsakaninsu.
Wani miskilin murmushi daya kashe zuciyar falaak ya kuma sanya gabanta tsananta faduwa ya saki,ya tashi ya gyara zamansa sosai yana duban sultane.
"Ana iya bata dama a ganina.......abinda ta buqata bai sabawa ra'ayinka da burinka ba......bai kuma sabawa addini da al'adarta......ubangiji zai sanya albarka sosai a ciki".
"Gaskiya ne" Sultane ya fadi cikin tsananin gamsuwa yana gyada kanshi. Daga qasan ransa yana jin kamar akwai wani saqo da yakeson isarwa ne me matuqar muhimmanci.
Iska ta zuqa sosai cikin kiyayewa da fitar numfashinta,ta qanqance idanunta kadan tana jin saukar maganarsa cikin tsakiyar zuciyarta,tana jin maganarsa kai tsaye tana tunkarota da wani irin yanayi me qarfin gaske. A hankali zuciyarta ta fara maimaita mata DAKE YAKE,maganan ta soma takura zuciyarta tana son tilasta mata jin muzanci,muzancin da alfaharinta da izzarta suka hana ya mamayeta.
"Zan baka mamaki......zan kuma kunyataka gaban sultane tabbas.......sai sultane yasan kaine namiji na farko daka fara hada jiki da diyar da yafi qauna duk duniya har sau uku!" Ta dire alwashin cikin zuciyarta tana jin qwarin gwiwar kiran sunan sultane din.
"Bappi......" Ta kirashi tana sunkuyar da kanta
"Khadeejatu" Ya amsa mata kai tsaye.
"Zan iya samun mintuna biyar?". Idanu sultane ya dan zuba mata sannan ya waiwaya ga falaak.
"Tashi kije mamana......zamu qarasa maganan". Gyada kai falaak tayi,sannan cikin girmamawa ta rusuna
"A fito lafiya" Tace da sultane da kuma haisam da hankalinsa yayi nisa wajen bin CCTV camera din dake sassansa wanda yayi linking nata da wayar hannunsa. Wani motsi yake gani very suspicious ta daukan da yaja hankalinsa sosai.
Numfashi ta sauke me nauyi,me yasa sultane ya gaza fahimtarta?,ba falaak take buqatar ya sallama ba......ba falaak take nufi ta matsa daga gurin ba,shine bata son gani a tsakaninsu.......shine bata qaunar wanzuwarsa a gurin.....tanason lokutan babanta ita kadai ne,tanaso ta kebe da mahaifinta ita kadai ba tare dashi a gurin ba. Tana ganin ya cancanci ya sallameshi......ya kamata ya fahimci akwai SIRRI cikin rayuwarta da wani bare bai kamata yaji ba.......magana ce data shafi rayuwarta da sirrinta,BATA SHAFI WANNAN SHEIKH DIN BA DAN GIRMAN KAI irin girman kan da take ganin yana batawa kansa lokaci ne.....irin girman kan da take gani bai kamata ya dorawa kansa shi ba a matsayinsa na ba kowan kowa ba,a matsayinsa na wanda baisan komai ba,baisan me rayuwa ke ciki ba. Tayi imanin koda cikin gida koda cikin fada tace zata zagaya dashi wasu guraren sai qauyancinsa da rashin wayewarsa sun bayyana muraran.
Shurun da tayi batace komai ba ya sanya sultane dauke dubansa a kanta,ba tare daya buqaci tayi magana ba ya aza kan haisam.
"Umra nake buqatar zuwa d'ana.......wannan lokacin na dauki lokaci me tsaho banje ba,ina buqatar zuwa gurinnan" Sultane ya fadi yana duban haisam.
Daidai sanda ya gama gane gilmawar wanda ya gani,ya kuma tsaida daukan a daidai inuwarsa,ya daga manyan fararen idanunsa yana duban sultane cikin girmamawa. Kai ya jinjinawa sultane din,ya sani koda sultane bai fadi ba,sultane din yana buqatar yawan zuwa gurin don ajiye buqatunsa.......ya kuma yarda ya aminta shi din me yawan zuwa gurinne......wataqila shi yasa gagarumar gobarar dake ci cikin gidansa ta qarqashin qasa ubangiji ya hanata tayi tasirin da zata qona gidan qurmus ta kuma hadiye hardashi.
Masarautar qunshe take da manyan al'amuran da idanun sultane basa iya gani.......tana dauke da manyan sirrika da manyan qullikan da haisam yakeji a jikinsa sun haura wadanda idanunsa suke gani. Inda shigowa rayuwarsu shine manufarsa.......inda ace shigowa rayuwarsu shine abinda target dinsa da farko,ya tabbatar akwai sirrikan da zai tonasu masu azaban doyi da rashin kyan gani. To amma tashi masarautar itace a gaba........tasa masarautar itace ta fiddoshi daga ainihin nashi izzar nashi sarautar da nashi qafin ikon dana mulki,ta maidashi wani malami dake zaune qasan alfarmar wasu cikin yanayi na karantarwa kadai.
"Idan zai yuwu wannan karon inaso mu tafi tare,don inaso nayi kalan umrar da ban taba yi ba tare dakai d'ana,inason sanin gurare masu muhimmanci da zan gudanar da addu'o'in dake tari tari a zuciyata,ban sani ba ko zuwan qarshe zanyi,qila shi yasa Allah ya jefoka cikin rayuwata". Sultane ya fadi still murmushin nan baibar saman fuskarsa ba.
Wani irin abune ya harba cikin qirjinta tana jin iskar da take shaqa wadda tun dazu ke gauraye da turarensa tana matse mata. Tun daga ranar data mallaki hankalin kanta itace take riga kowa sanin plan din sultane,tun daga sanda tasan meye ma'anar umara da aikin hajji ita sultane yake fara gayawa Lokacin da yakeson zuwa,su zauna kuma su tsara lokacin tafiyar.......ta dauki hutu daga company ta rakashi suje su dawo........yau duka wannan malamin ya samu nasarar ture dukka wadannan muqamai nata da sauri haka?.......anya baiyi amfani da asirin da taji da yawansu suna dashi ba wajen mallakar sarakuna ko juya akalar tunaninsu ba?. Dole ta zame cikin dabara ta zauna sosai,tana ji har cikin jininta yadda yau sultane ya maidata wata baquwa daban a gabansa,ya jawo bare......wanda babu dangin iya ko na baba a tsakaninsu yake fadimasa abinda ita ya kamata ita ya cancanta ta fara ji daga bakinsa. Baima maida hankali ga batun da tazo dashi ba......hankalinsa dukka yana kai wannan malamin da ayanzu jikinta ya fara bata akwai abinda ya yiwa sultane na janye hankali.
"Na tsaneka......na tsaneka,tabbas saina nisantaka da mahafina......mahaifina nawa ne ni kadai.....sirrakansa da komai nasa......nan din layikana ne da babu me tsallakeminsu na zuba masa ido" Tayi maganganun qasan ranta tana hadiyar yawu da qyar saboda wani abu daya tsaye mata a wuya.
Sallamarta da muryarta data fita fes da wani irin confidence shine abinda ya dakatar da maganan da sultane yayi niyyar fada ya waiwaya yana amsa sallamar tata,kamar yadda haisam da bai waiwaya ba ko motsawa daga zamansa ba ya motsa labbansa yana amsa sallamar muryarsa can qasa da sautin da bazaka jishi ba.
Shine mutum na farko da idanunta suka fara sauka a kansa,ta zube idanunta fes a kansa,zuciyarta na wani irin motsawa. Tana jin inama zata ita sanin zahirinsa da badininsa da iya kallonsa kawai da takeyi a yanzu?.