Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 16

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 16

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 16: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 16. "KUSANCI" Abinda zuciyarta ta fara ayyana mata a kanshi…

3,344 words

"KUSANCI" Abinda zuciyarta ta fara ayyana mata a kanshi kenan,tana qoqarin sarrafa kalmar ya daga fararen idanunsa a nutse,abinda ya harba wani irin faduwar gaba a sassan zuciyarta ya sanya janye idanunta da sauri a kansa,saidai hakan bai hanashi fahimtar kallon qurillar data zube masa ba wanda tuni ya jishi a jikinsa tun daga shigowarta gurin.

"Zan iya tafiya idan hakan ya zamana ba damuwa a tattare da sultane?" Haisam din ya fadi qasa qasa cikin girmamawa. Kai sultane ya girgiza yana murmushi.

"Akwai sauran maganganun da bamu kammala ba ai,baka gayamin yuwuwar tafiyar tamu ba ko dagata zuwa wani lokaci?". Sultane yayi.maganan daidai qarasowar mammina. Sake dauke idonta tayi daga kansa daga kallon qurillar data sake shiga a kansa akaro na biyu.

Zamewa tayi cikin tsananin biyayyar nan da ba abinda ya sauyata tun daga wadancan shekarun xuwa yanzu ta soma gaidashi da salon gaisuwar da koda cikin bacci yake yasan ZAITUNA CE. Ta laqanci wani irin tarin girmamawa da sirrikan sake lulawa cikin zuciyarsa da samum matuqar girmamawa fiye da kowanne dan adam,saidai har yanzu wannan abun ya gaza canza MATSAYIN SAFEENA a rayuwarsa,abu daya daya fahimci mammina ta jima tana son samu kenan MATSAYIN SAFEENA daga bisani kuma ya karanci ta watsar da wannan ta shiga fafutukar gina nata matsayin,wanda ya ginu din kuwa da wani irin girma da kima.

"Daya biyu uku hudu" Can qasan zuciyarsa yake lissafa adadin tsahonta sanda ta miqe daga gaban sultane tana laluben muhallin daya dace da zamanta,gurbin da zai bata daman ganin komai daidai da lissafi da hasashenta. Da wani irin yanayi yake iya hangenta,wanda zaka rantse da Allah bai damu da kowa ba sai wayarsa dake hannunsa,saidai bayan ta gaba idanunsa ta gefen hagu da dama na idanunsa ya samu wani irin horo da yake iya monitoring motsi da reaction na komai da kowa.

Tsaf lissafinsa ya tuqe ga adadin tsahon mace ta biyu cif da cif.....daidai sanda take zama saman kujerar cikin wata nau'in izza dake cakude da taqama idanunta a kansa tana fadada fara'arta da zummar fara dasa harsashin farko a kansa na fara bashi kulawa ta musamman don shiga cikin komarta cikin sauqi.

"Barka da warhaka sheikh muhammad" Tunda ta shigo ta karanci akwai abinda xai iya faruwa masu shige shige da wannan......akwai wani abu daya tsinto cikin muryarta da yake gaya masa confidence din data aro,wataqila don ta cimma wani abu ne.....ko don ta nuna cikin harin jiya ba abinda ya tsoratata ko kadan......saidai yafi karkata ga cimma wata buqatar.....don tun daga daren jiya zuwa safiyar yau ya samu labarin nasarar dasa kakkaifan tsoro da sukayi cikin zuciyarta.

Da kalar girmamawar data bashi ya amsa mata gaisuwarta,sai taji wani iri,don bada wannan salon bada wannan harshen taso ya fara karbarta ba a karon farko ba a gaban sultane.

"Khadeejatu baki gama shiryawa yin maganan bane?" Sultane ya furta yana duba agogon hannunsa. Numfashi ta sake ja kamar zata zuqe dukka isar da tayi saura a gurin,ta daga kai a sace tana duban mammina. Taji a jikinta sanda mammina ta shigo mamminan zata saita komai......zata sanya sultane ya tashi wannnan malamin daga gabanta......daga cikin shirgin daya shafesu.....cikin al'amuran da suke kebantattu garesu.

"Muhammad haidam D'ANA ne......dan sultane muhammad hammud agg abba ne daya cancanci komai.....yake da ruwa da tsaki da dukkan komai" Kai tsaye sultane yayi maganan data daure musu kai gabadayansu..basusan daga inda maganar ya samo asali ba,basusan daga inda maganan ya dauko ba.

Ido ta samu ta hada da mammina ko akwai wani taimako?,saidai idanu ta juya mata abinda ya alamtawa akhnan ba wani sauran abinda ya rage banda ta fasa maganar a gaban wannan malamin. Nazarinsa ya janye daga kan matar yana ganin yadda tayi amfani da idanunta ta sarrafa tunanin akhnan din,sarrafawar da lafazin mahaifinta ya gaza yinsa wanda ke dauke da sautin gargadi da wani tasiri kadan na bacin rai a cikinsa.

"Done" Ya fada can qasan ransa,abinda yake buqata ya tattara a kanta kaso saba'in cikin dari ya kammala,iya wannan kason kawai ya isheshi ya afka cikin bin diddigin kowanne motsinta har zuwa sanda zai san alqarta da mutanen da suke farauta.

"Bappi......na fitar da mijin auren kamar yadda ka buqata".

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 27*

Tsit parlor din yayi,wani irin shuru ya ratsashi kamar ba sauran halitta a cikinsa data rage. Zukatan mutane biyu suka shiga nazarin kalmomin da suka fita a bakin akhnan din.

D'aya bayan daya haisam ke fasa kalaman bakinta.......bawai don bada hankali akan masa'alar da bata shafeshi ba,don shiga nazari a kalamai daga bakunan mutanen da bai gamsu da maganganunsu ba ya zame masa dabi'a.

Introvert person ne na gasken gaske. Wanda shurunsa yakan zama nazari ne......kauda dubansa yakan kasance hakaltar dan adam. Yanayin kaman bai gani ba kuma ya gani,zaka dauka ya manta amma yana hankalce......yana ajjiye da komai. Ba komai ke burgeshi ba kaman yadda ba komai ke bata ransa ba,ko yaya yake akwai alamu na rashin gaskiya a tattare dakai yana iya fahimtar hakan,omari yakance.

"Me laifi kamar wani qamshi daban yake maka cikin hancinka?" Murmushi kawai yake baiwa omari amsa dashi,shi kansa a lokuta da dama mamakin kansa yakeyi. Sake janye nazarinsa a kanta yayi ya maida kan mammina da tayi qasa da kanta. Iya nutsuwar da yanayinta ya nuna kadai ya tabbatar masa tasan komai......iya yadda tayi shuru kawai ya tabbatar masa akwai wani abun a bayan shurunta. Me yasa sultane bazai fahimta ba wai?. Ya samu kansa da tambayar kansa da kansa. SULTANE BA IRIN KAI BANE......MUTANE DA YAWA BA IRINKA BANE. Amsar da zuciyarsa ta bashi kenan ta kuma tilastawa kanta da kanta yin relaxing.

"Kula da al'amuranta da suka shafi bincikenka shine priority dinka.....shine dolenka,dole komai ka barshi a inda ka ganshi,dole komai ka barshi a yadda yake indai bai taba bincikenka ba....hakanne kawai zai baka nutsuwa da tafiyar da aikinka kadai cikin tsari da yanayin daya dace" Ya fadawa kansa da kansa,sai ya samu kansa da zare duk wani yanayi da aikinsa daya soma hawa kan ruhinsa da zuciyarsa.

Zuciyar sultane taci gaba da harba jini a hankali,yana jin sauran buri da fatansa yana kwaranyewa. Mafarkin da yasha shafe darare yana yi......addu'o'in da yafi tunanin rashin alkhairi da rashin dacewar abun ubangiji ya kalla wataqila ya dakatar da amsar addu'arsa. Sai da yayi gyaran murya

"Ma sha Allah......Allah yasa albarka,na tayaki murna.....amma kuma.....sanda kika shigo banga kin gaida WALIYYIN naki ba" Ya furta maganan yana tsare akhnan da ido. Idanunta ta daga da sauri abubuwa biyu suna dukanta. Yadda SULTANE yayi accepting maganan cikin sauri?,cikin sauqi?,ba tare da kalar kowacce tambaya ba?,ba tare da kalar kowanne challenge ba. Maganan WALIYYI ita tayi Mata tsaye a rai,tana son banbance ma'anar waliyyin da ya furta,amma kwanyarta ta kasa wani cikakken aiki a wadannan mintunan,sai tayi qasa da kanta tana jin muzanci yana bin sassan jikinta da jininta gaba daya. Muzancin da bata taba jin kalarsa ba tana jin yadda kalaman sultane ke raunata duk wata izza tata daya kamata ya zama na farko wajen dagata tana fadin.

"Barkanka da safiya". Da fari kamar baiji maganan nata ba,don ba a nan hankalinsa da lissafin abubuwa masu muhimmanci a wajensa yake ba,amma sai zuciyarsa ta harbo masa muryartata,abinda ya jinkirta amsawarsa kadan kafin yace

"Barka". Kai sultane ya jinjina,yayin da yanayin amsawar tasa ta sake danqara wani irin zafi saman zuciyarta,zuciyar daketa kokawar gano WALIYYINKI da sultane ya fadi,saidai kuma bai barta tayi nisan zango a tunani ba ya gajarta mata komai ta hanyar fadin.

"Juma'a......juma'a me zuwa ba wannan da muke ciki ba za'a daura aurenki da mijin da kika gabatarmin din......in sha Allah sheikh haisam zai wakilceni zai zama madaurin aurenki!". A razane ta dago kai......ba kuma ita daya ba,hatta da mammina maganan ya razanata. Bata razana bane don daura auren akhnan da aka zabge masa kwanakin wata ba......ta razana ne saboda GIRMAN MATSAYIN da sultane ya dauka ya baiwa malamin. A iya saninta.....dauren auren d'iyar sarauta.....diya me cikakken gata,wadda izzarta darajarta da martabarta ya kerewa dukkanin diyoyin gidan sarautun da nijer ke dashi......waliccin aurenta wani abune me tsananin tsada da kowa ke yunwar a bashi,da kowa ke fatan sultane ya zabeshi.....wani abune da zai zama GIRMA da martabawa me tarin yawa da ba zata shafe ba cikin babin tarihin rayuwar dukkan wanda aka bawa......wanne irin GIRMA da MATSAYI ne yaron ya taka haka a zuciyar sultane cikin qaramin lokaci ba tare data ankare da haka ba?.......sai a yau ta sake yadda ta kuma tabbatar da gaske ne sultane YA D'IYANTAR DASHI......da gaske ne da sultane yace YA MAIDASHI D'ANSA da gaske yana nufin abinda ya fada din......iya yau kawai ta tabbatar mata da haka.

Amma kuma tana raye?.....ta yaya zata bari haka ta faru?.....ta yaya zata bari haka ta kasance?. Ta kasa haifawa sultane MAGAJI kamar yadda ta hana kowacce d'iya mace haifa masa magaji sai magajiya qwalli biyu da take jinsu kamar wutar dake cin naman jikinta a kowacce safiya idan ta kallesu. BAI KAMATA TAYI SAKACIN DA WANI ZAI HAURO ta saman kanta ba......ya rusa duk wani matsayi kusanci da martaba da tayi shekaru tana tattalinsu ba.....bai kamata ta bari wani ya fado tsakiyar wannan kakkauren zaren data debi shekaru tana saqashi ba ya tsinkashi. Waninma da har yanxu xuciya da gangar jikinta ke alamta mata DANGER a duk wani kallo da zata aza idanunta a kanshi ba.

"Bappi......bayan dukka wanzuwar su kawu mammani dake raye?". Akhnan ta samu kanta da furta tambayar tana duban sultane da wani irin sanyin mamaki daya daketa.

Kai tsaye yake duban idanunta shima,sannan ya jinjina kai.

"Bakisan MATSAYIN D'A a wasu guraben ya haura na DAN UWA BA?......Bakisan kuma matsayin D'A wajen yin waliccin auren qanwarsa ya zarta na kawunnanta ba?" Maganar tasa ta fito da wani nauyi me yawa daya sanyata maida kanta qasa kawai. Banda tauri da kafiya gami da tsaiwa da zuciyarta ke dashi.......banda tattalinnan da takewa GIRMA da IZZARTA ba abinda zai hanata fashewa da kuka a yanzun nan.

"Amma ranka ya dade......Allah ya taimakeka.......bai kamata kafin ka yanke rana da komai ka tsaya gana da yaron ba?......kasan wayeshi da asalinsa?" Tayi maganar da sanyin murya da sanyin zuciya,sanyin daya sanya haisam tattarasu dukka ya aza saman ma'auni daya.

"Ba buqatar hakan......indai ta iya gabatarmin dashi......ta sani ya dace da dukka wani tsarinta ne......ku shirya komai,zata zama matar aure nan da kwanaki goma masu zuwa.....kaji abinda na fada muhammad?" Ya maida dubansa da tambayarsa kan haisam da yayi kaman baya wajen.

"Indai wannan din umarni ne daga gareka zan cikashi in sha Allah"

"Umarni ne haisam.....umarni ne muhammad" Ya furta cikin nuna girman umarnin nasa da gasken gaske.

"Ranka ya dade......ba kuskure kuwa?,.......ya kamata a duba.....muna neman alfarma,aure ba wasa bane.....diyarka mafi daraja zaka miqa......."

"Zaituna ya isa haka......na rufe wannan babin har abada,na rufe matsalan akhnan akan aure har abada......bana son wani ko wata su sake tayar da ita......yin hakan zai iya sawa mutum ko waye ya fusakanci mummunan hukunci daga wajena kai tsaye kuma"

Runtse idanunta tayi tana jin kamar jiri na shirin kayar da ita daga zaunen da take. Ta gaji da zama a gurin,tanaso ta shaqi wata iskar daban bayan wannan,tana jin kamar wannan iskar ta gurbace da yawa,don haka ta miqe cikin girmamawa.

"Na gode bappi......" Ta iya hada kalmomin da qyar

"Madalla" Ya amsa mata a taqaice yana kauda idonsa daga dubanta,wani abu yana cakar zuciyarsa.

"Tafiyar zata yuwu?" Sultane ya sake tambayarsa,tambayar data aza masa wani tarin nauyi ta kuma sake jan hankalin mammina cike da mamakim wacce tafiya sultane din zaiyi wadda ita bata da labarinta?.

Tafiya da sultane wani abune da zaya bata tsarin aikinsa gaba daya......dukkan wani plan nasa na kammal aikinsa cikin wata daya zuwa wata daya da rabi yana jin zai iya samun naqasu ko koma baya. Amma kuma ta yaya zai fito ya gayawa sultane haka kanshi tsaye?.

"Na fahimceka muhammad......kada ka damu,zamu wuce da babban limamina......zan iya barin kulawar masarauta a hannunka?,sati biyu kacal da jagorancin wazeer hamza?". Wani nauyin ya sakeji sultane ya aza masa,amana komai qanqantarta tana masa nauyin gaske,baya qaunar dukkan wata amana da za'a bashi ace ya riqeta,idan kuwa har aka bashin yana qoqarin cikata da dukkan iyawarsa......da duk wani qarfi nasa daidai da yadda yasan yana da abun fada gaban Allah. To amma a yanzun idan yace zai riqe wannan amanar......yayi imani a jininsa yana jin SARAUTARSA zata iya motsawa......zata iya bayyana kanta da kanta daga lungun da yaje ya ajeta......zata danne matsayin da yaketa qoqarin daidaita kansa a yanzu......zata iya murqushe siffarsa ta MALAM ZALLAH ayanzun ta fito da siffar da har yabar agadez bazai yarda a sanshi a cikin ta ba wato SARAUTA.

To amma bai kamata ya wofantar da komai da sultane yazo masa dashi ba,don haka ya motsa kadan.

"Zanyi iya abinda dama da iko suka bani,bani da alaqa da mulki ko sarauta irin naku.....bansan ya komai zai tafi ba" Maganarsa ta harba wani abu saman zuciyar mammina daya tilasta murmushi fita saman fuskarta. DAMA ce wannan din da idan tayi amfani da ita da kyau zata zame mata silar samun abubuwa masu yawan gaske.

"Na yarda dakai,na kuma aminta dakai,nasan zakayi iyakacin iyawarka da dukka qoqarinka.....Allah yayi maka albarka,ya sakawa uwayen da suka kawoka duniya da alkhairi....."

"Ameen" Ya amsa yana lumshen idanunsa,addu'a da ya yiwa motii da nanay yana jin sun biyashi a komai.

Abinda ya kawota ya kammala,ta samu kuma sama da abinda take buqatar samu,don haka ta miqe tsam cikin girmamawa.

"Ina neman izinin zuwa babban asibiti......zan duba maras lafiyanmu da hari ya ritsa dashi a jiya,da sauran majinyata dake asibitin" Sirrintaccen murmushi ne ya kubuce daga can qasan zuciyar haisam

"Good job maher" Ya furta can qasan ransa. Shi ya buqaci maher da ya buqaci ganinta.....kuma kafin zuwanta an gama tsara yadda komai zai kasance. Yana buqatar fitarta daga masarautar koda na awa daya ne.....wannan space din yake buqata don isa ga abun hannun nan.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 28*

Murmushi kadan sultane yayi,duk da cewa baya cikin yanayin. Wani kyakkyawan dabi'arsa da haisam yayi noticing shine,yana da son farantawa iyalinsa da sauraren ra'ayinsu,dabi'ar da tayi kamanceceniya sosai data motii dinsa. Qoqarin shiga sahun mazan da manzan Allah yace sune mafi alkhairi a duniya...wato mazan da suka kasance mafi alkhairi ga iyalansu,wadanda suka samu shaida me kyau game da iyalansu kenan.

Dabi'un mammina da yawa suna burge SULTANE.....cikin su harda yadda ta zama me sakakken hannu da nuna damuwa ga mutanenta tsananin damuwa. Morsa safiyya hakan take itama,saidai nata da banbanci,tana duba abinda ya cancanta a yiwa hakanne,wanda bai cancanta ba tana dauke idanunta daga kai. Ba komai take bari a bayyana ba na alkhairinta.....sabanin mammina da takan bayyana motsinta na alkhairi komai qanqantarsa,takance tana yin hakanne saboda sauran masu sukuni suyi koyi da ita,su taimaki wanda baidashi....wanda ya gaza dame nema,hakan kuma sai sultane yaji shima hujja ce.

"Allah ya bashi lafiya shida sauran majinyata,masarauta zata ganshi in sha Allah".

"Giwa na godiya" Ta amsa cikin tsananin ladabi sannna ta juya tana takawa a nutse ta fice.

*HAISAM*

Jikinsa yaji yana mutuwa a hankali sanda yake baro sassan SULTANE. Akwai mintuna ashirin kafin lokacin sallar azahar. Sosai yaji gilmawar mutum daga bayansa,gilmawar da baka isa ka gane an wuce din ba idan ba irin mindset dinsa kake dashi ba,saidai shi yaga inuwar,yaga kuma wucewar ta inuwar gabansa,saidai yanayi zubi siffa da tsarin wanda yake kyautata zaton ya wuce din bai masa kama da suffa da zubin bulama ba........sai ya dauko qididdigar jikkunan TAMIM guda biyu. A tamim qarami lissafinsa ya tsaya,yadan maida tunaninsa baya kadan akansa kafin ya samu guri ya ajiye nazari a kansa zuwa lokacin da zai zama free,don yanzu akwai abinda yakejin yafi masa komai muhimmanci da ya aiwatar dashi.

Daga saba'in xuwa saba'in da biyar yaji ya sake matsar da matakin mammina. Ta shirya komai kuma ya faru kaman yadda taso shine abinda zuciyarsa ke faffasa masa shi. Tafi kowa sanin halin sultane,tafi kowa kuma karantarsa.....idan ranshi ya baci akan abu baya doguwar magana a kansa......tayi nasara,saidai tata nasarar shi ta zame masa wani.mabudin aikinsa.

A yau dinnan yakeso ya fara dasa masa tarakuna har guda biyu......don haka ya wuce Kai tsaye zuwa ga sassansa yana sanar da yaron gidansa qasa da mintina ashirin yana buqatar dukkan wasu masu alhakin kula da tsaron gidan dama wanda ke kula da kowanne sashe na gidan,hadimi da hadima,babba ko yaro,mace ko namiji a babban filin dake ajiye a bayan ginin masarautar daya tabbatar zai daukesu gaba daya,ya kuma aikewa da omari saqon karta kwana da dukkan tsarikan da yake ganin zai amfani dasu.

Dukkanin nazarinta da nutsuwarta ta hada guri daya,tana kuma sake zurfafa tunaninta gaba daya akan komai daya faru tsakanin jiya da yau din.

Tana jin wani iri da qyashin yadda sultane ke shirin miqa ragamar komai a hannunsa,a hankali kaman yana raunana power din kowa.......kamar yana son fara juya ra'ayin sultane da fara sarrafa tunanin sultane din. Kamar ya fara aiki da wani abu me qarfi da batasan meye ba wajen sarrafa sultane din da tunaninsa gaba daya.

Riqon qwarya wa fada da kuma damqa waliccin auren akhnan a hannunsa?. Wani siririn murmushi ya qwace mata,ta gyada kanta a hankali. Tana jin kamar lokaci ne wannan na samun cikakkiyar damar da zata sake wani abun fashewar,abun fashewar da take kyautata yaqini da zaton zai iya tashi harda shi,ya kuma zame masa mummunan bala'in da zaiyita binsa har qarshen rayuwarsa.

Can qasan zuciyarta kuma zafi takeji,zafi takeji sosai na yadda sultane ya yanke hukuncin damqa ragamar masarauta da auren akhnan a hannunsa. Da farko ta tashi a yau da zummar ta jashi a jiki don sarrafashi kaman yadda take sarrafa kusan duk wani me fada aji cikin masarautar.......to amma tana kokwanton yiwuwar hakan,don wani abu take hange tattare dashi da yasha banbam da wanda take gani gurin sauran mutane. Juyawa tunaninta yayi ga Maher......ta jima tana ganin matashin cikin gidan,tana kuma da haske a kansa kan baida matsala da kowa. Irinsa take so,irinsa ne kuma kewaye da ita,wadanda sukan iya sadaukar da rayukansu da rayuwarsu saboda ita,ba shakka ya cancanci ta duba wani gurbi ko muhalli kusa da ita tayi masa mazauni.

*HAISAM*

Cikin qanqanin lokaci ya kammale dukkan wasu masu tsaro na gidan. Hadimai ne bayi ne da sauran ma'aikata da masarautar ta qunsa,ya kuma yiwa taken laqabi da taren wayar da kai.

Qofofi hudu yasa aka fitar na shiga gurin taron. Uku na shigar mata,biyu na shigar maza. Kowacce qofa kafin ka shiga sai ka sanya sunansa saman takardar dake ajiye a bakin qofa a hannun manyan hadimai na gidan,ciki kuwa harda tamim babba da qarami da kuma bulama. Yana sane ya basu wannan aikin na tsaiwa kan kowa ya rubuta sunansa,hakan shine zai riqe masa su a gurin,ba wata dama ko hanya da musayen aiki ko matsawarsu a gurin har sai an kusa tashi a taron.

Duk wani hadimi da hadima dake tsaron sassan mammina an tsara rukunin zamansu a can ciki,yadda fita daga dakin taron zai zame musu long process,baya ga haka ya kasance doka ta zama dakin taron har zuwa sanda za'a kammala taron.

Shi da kansa yaso ya jagoranci shiga sassan mammina,saidai yana da wani irin fikira da tsananin hangen nesa. Bacewarsa a gurin zai iya zama babbar ayar tambaya ga duk wanda yasan wani plan daya shafeshi komai qanqantarsa. Duk da bai sani ba,amma yana jin a hankali wani abu me kama da ana ci gaba da babiyar kowanne motsi da daga qafa tasa.

Cikin hikima qwarewa da sanin makamar aiki yake hada ayyuka biyu. Aikin farko shine monitoring na shigar abdii sassan mammina,tun daga qofar farko da zaka taras ta shiga sassanta har zuwa gurin da suka nufaci zuwa. Camera ne qarama da ya sanya abdii maqalewa daga gaban rigarsa,ta yadda zai dinga ganin komai tamkar tare suke shiga gurin dashi.

Bai taba tunani ko kawowa a ransa zai bawa abdii wannan aikin ba. Amma yadda yaron ya tsaya a gabansa da wani irin confidence yaji a ransa bari ya gwada.

Ya dafa kafadarsa bayan ya gama shirya abdii din da yanayin shigar da yakeso ya shiga gurin.

Readers Also Read

More by Huguma