Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 25

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 25

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 25: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 25. zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta…

3,370 words

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE PAGE 42*

Batasan ya akayi ta samu idanunta da zame kansu da kuma qwace dubansu daga cikin nasa ba bayan ba abinda ta tsara yi kenan ba.......tana jin idan ta bari ya gayamata ko ya maida mata magana ko qwaya daya ce yayi jayayya da girmanta,don haka cikin rashin yarda da izzarta takai qasa ta sake motsa labbanta fushinta na bayyana sosai.

"Me ka dauki kanka?......a tunaninka kai din waye?" Wani miskilin murmushi dake cakude da izza ya saki,wanda ya kusan tafiya da numfashinta na wucin gadi,cikin nuna halin ko in kula yana kuma sake raba hankalinsa da yadda yakejin hucin giftasu daga hagu zuwa dama ya maida mata amsa.

"Muhammad haisam wani ne.....wanda ya zame miki tilas ki dakata da qidddige iya adadin ikonsa......don zaki gaza a sanda hasashenki bazai taba iya cafko adadin qarfin ikonsa ba". A karon farko iya tsaho shekarun da tayi a duniya da aka taba challenge nata......da ta taba fadin magana aka maida mata......da aka tsaya a gabanta ana dubanta da duba na kai tsaye......irin duban da mammina ko sultane kadai keda iko da lasisin yi mata shi. Koda ya samu daman tsaiwa a inda ta tsaya.....koda ya samu daman maida mata magana ba zata bari ta kwana da ciwon rai ba.

"Idan kana jin dadin tozarta matan da kasan sunfi qarfin matakinka a rayuwa?,daga kaina ba zaka qara kusantar aikata hakan ba" A karo na biyu wani qasaitaccen murmushi ya subuce masa,yayi qas da kansa yana hangen tazarar inuwar boyayyen mutum daga bayanta wanda yake da tabbacin batasan da tsaiwarsa ba,sai ya daga kansa a nutse yana mata nuni da hanya cikin kamala.

"Idan kin gama fadin duk abinda yake ranki kina iya tafiya" Idanunta ta qanqance sosai,reshe yana neman juyewa da mujiya. Gurbi da muhallin fushi takeson gani saman fuskarsa akan maganganun data gaya masa.......amma sai yake maye gurbin haka da wani murmushi da iya tsahon zamanta cikin da'irar sarauta,gidan mulki da iko bata taba ganin murmushin dake cakude da zallar izza irinsa ba. Yabar mata ciwon fadin maganar a ranta?,kuma yana umartarta da tafiya daga muhallin daya kasance mallakin mahaifinta?......saman QASAR data kasance cikakken ikonta..

"Ki tafi nace" Yayi maganar wannan karon yanayin fuskarsa yana juyewa da wani matsanancin tsare gida yana kuma ajiye mata wani nannauyan kallo da taji ya mata wani mahaukacin kwarjini.

Wannan dabi'artata ta taurin kai da kafiya ita ta motsa.....izzarta ta taso ta lullubeta,ita dake bada umarni yau ita wani yake bawa umarni?......ita dake da iko na fada aji ita ake fadawa abinda zatayi?.

Sake tsareta yayi shima da kakkaifan kallonsa,yana sake irga motsi da takun bulama. Kaucewarta a gurin yafi buqata a sannan,don yanason nunawa bulama qarshen rashin qwarewa cikin aikinsa. Saidai kuma baya qaunar wanzuwarta a gurin,saboda ba gaban idanunta yake buqatar yin kowanne motsi nasa ba.....amma yana karantar kafiyarta da taurin kanta na shirin zame masa cikas,kaman yadda ya karanci bulama yana daf da kubcewa tsarinsa,don haka dole yayi wani irin taku da bai kai biyar ba,ya miqa hannu tsakanin shukokin dake daura dasu,ya damqi wuyan bulama cikin wani irin zafin nama,sannan ya fincikoshi daga duhu zuwa cikin haske,ya kuma watsar dashi a gurin.

Wani irin matsanancin bugawa kawai zuciyarta takeyi,cike da wani irin matsanancin tsoro da bata taba jin irinsa ba. Ta fidda manyan blue eyes dinta tana duban bulama din da haisam ya watsar a gurin,saidai yana riqe da hannayensa da ya banqaresu ta baya,wanda azabar irin wannan riqon da haisam yayi masa ya sanyashi fidda wani irin nishi a wahalce.

Iyakar saninta da hadiman gidan gaba daya batasan bulama ba. Batasan wayeshi ba,batasan kuma wannan fuskar ba......me ya kawoshi nan?,cikin duhun da babu komai cikinsa sai hasken walqiya?,cikin duhun bishiyoyin da ba wanda zai iya labewa ciki sai wanda ke dauke da alama da tambari na rashin gaskiya?. Ba ita ba......hatta da maleek dake kallon komai daga nesa.......amma zama da haisam da dadewarsu tare ya sanya yake fahimtar lokutan da haisam din yake buqatar wanzuwa a guri shi kadai,don haka sai ya tsaya daga ness yana kallon komai. Da fari hankalinsa da nazarinsa gaba daya yana kan akhnan din. Ya cika da wani irin tarin mamakin yadda haisam yake iya hadiye maganganunta,ya sani,yana da wani irin kaifin hangen nesa da qoqarin hadiye bacin rai,saidai kuma sam sam baya daukan raini ko qanqani. Yanayin tsiwarta ya daure masa kai sosai,dukkan wannan izzar a yanzun da take magana da haisam din sai yaga ta kwaranye ta barta da iya tsiwar. Akwai wani abu da yake hanga daga can cikin dabi'unta da yake ganin zuwansa daidai da wani salon ra'ayi na haisam din.

JARUMTA......irin salon jarumtar nan ta babu gudu babu ja da baya......wani irin qarfin hali da TSAIWA saman ra'ayi,sai ya saki wani sassanyan murmushi,wanda suke murmushin nasa keda wuya ya hangi yadda haisam din ya motsa cikin wani irin zafin nama ya kuma finciko bulama din.

Abun ya matuqar zuwa masa a bazata da kuma bashi mamaki. Baiga wani alamun wanzuwar dan adam a gurin ba......ta yaya haisam din ya fahimci hakan?,bayan kuma da kwanyarsa ta tuna masa SHEIKH HAISAM din sai mamakinsa ya dinga raguwa,ya fara tunanin me mutumin yakeyi a tsakanin duhuwar gurin?.

Kamar baisan waye bulaman ba,kamar kuma baisan wanne aiki yakeyi ya banqare hannunsa ta baya da kyau,da wani irin yanayi me cike da zafi yake duban fuskar bulama din wadda ke shimfide a qasa.

"Bazan tsaya bata bakina ina tambayarka wa kake bibiya ko me kakeyi ba a nan gurin a irin wannan lokacin......kaman yadda bani da lokacin tsayawa tambayarka WAYR YA SANYAKA......Amma zan aikeka da saqo guda days ka shaidawa wanda ya sanyaka din cewa......ni muhammad ina me shaida masa,yana wasa ne da FARAR WUTA wadda cikin ruwan sanyi take qona dukkan wanda ya raina raina LAUNINTA". Sai ya saki hannuwan bulaman,wanda hakan ya bashi daman qarasa zubewa a qasa cikin wani irin matsanancin radadi da kafadunsa da gadon bayansa gaba suke masa,sannan ya yunqura da wani qaramin hanzarin da qarfin hali ne kawai ya tattara masa ragowar kuzarin,da wata irin sassarfa yake jan qafafunsa yana bacewa daga gurin.

Taku uku kawai yayi ya koma zuwa bakin qarfen data sameshi a gurin,ya kuma juya mata baya yana kafe gwiwar hannunsa jikin qarfen ya koma salon durqushen da yayi dazu yana ci gaba da duban tsirran da sukaci gaba da kadawa da sauri sosai saboda qaruwar iskar data ci gaba da kadawa gami da damshin ruwa daya fara sauka yaf yaf mara qarfi.

Idanu ta zubawa bayansa tana sake jin wani tsoro yana sake shigarta na wanzuwar shuru a gurin,bata ganin kowa sai shi da ita,don omar ma tun sanda yaga yanayin reaction din haisam ya matsa yana kutsawa zuwa kewayen gidan ko zai samu wani evidence motsi ko wani dake tare da bulama din.

Runtse idanunta tayi da qarfi daga duban faffadan bayansa da yabar mata saboda sririyar walqiyar data haska sararin samaniya,ta kuma nuna yawan hadarin da take dauke dashi. Tsoro me qarfi dake cakude da bacin rai taji yana shigarta. Nadamar rashin amsar tayin da yayi mata tun farko na tafiya taji yana ratsata. Me yasa bata tafi ba sanda taga wani abu me nauyi cikin qwayar idanunsa?,me yasa bata tafi ba a sanda yayi mata kallo na kai tsaye......kallon cikin qwayar idanunta.....bayan taso wani kallo ne da bai taba yi mata irinsa ba.

To amma duk haka ita din,GIMBIYA AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD.....har rashin darajar da zai gwada mata yakai ya juya mata baya yana ci gaba da al'amuransa kamar baisan Allah yayi tsironta a gurin ba?. Yana qarqashin cin alfarma ta mahaifinta?,yana rayuwa cikin iko na mahaifinta?. Wayeshi?,banda ordinary mutum kamar kowa?......banda ordinary hadimi kaman sauran hadiman cikin gidan,wanda suke rayuwa cikin tattalin farincikinta.....kare dokokinta da iyakokinta,yau gata a tsaye a yashe......tamkar ba itace wannan gimbiyar da ganinta yake zama GAGARUMAR SA'A GA DUK MUTUMIN DA IDANIYARSA TA SAMU NASARAR GANINTA.

A cikin jikinsa yakejin tsaiwarta a gurin,saidai bayaso ya waiwaya gareta harta kalli irin nasa fushin. Yana jin tsaiwarta har cikin b'argonsa,bai kuma san abinda ya hanashi tafiya yabar gurin ba,saidai wani sashe na zuciyarsa yana nanata masa MARTABAR SULTANE ce ta jawo haka.

A duk sanda zai kwanta yana jin sauti da kuma maimaicin sautin sultane a maganarsu ta qarshe cikin airport.

"Dukkan masarauta......da dukkan wanda ke cikin ta na baka amanarsa......idan nace kowa da komai ciki harda AKHNAN. marainiya ce data taso batasan dadin mahaifiya ba,duk da ta shekara hudu da ita,amma kona shekara hudunma batasan dadin safeena ba,saboda ciwon hauka da safeena tayi daga randa akhnan tayi kwana arba'in a duniya.......safeena batayin cikakken wata uku da lafiya,saidai kuma a wata ukun duk sanda take a daidaita bata bari kowa yayi hidima ga biftu,kamar tasan tafiya zatayi ta barta,kamar tasan tafiyar bame nisa bace.

Yana iya hangen qwayar idanun sultane a sanda yake masa maganar,yana iya ganin raunin dake tattare da sultane din ta cikin qwayar idanun nasa,raunin dake gaya masa wannan feelings din bame sauqi bane......me tsananin nauyi ne,nauyin daya gaza ture yaringar daga zuciyarsa,duk da girma da adadin kura kurenta a tare dashi,daci gaba da bijirewa zuwa ga umarninsa.

Damqe qarfen yayi da kyau yana jin yadda ruwan ke qara yawa. Yanason ya waiwaya ya tambayeta me ya hanata tafiya?,amma ya tabbatar idan yayi hakan zai sake gayyatowa kansa fushin da yake yaqi dashi. Kalamanta sun soki zuciyarsa sosai,sun masa wani irin rami da ya tabbatar zaibar gurbi da miki cikin zuciyarsa.

Iya adadin jurar tsaiwar da zaiyi ya kaita,sai ya zame hannunsa daga qarfen a hankali ya fara takawa. Taku hudu kawai yayi,idanunsa a gabanshi ba tare da ya ko waiwayeta ba,ya motsa labbansa da muryarsa da tayi wani irin zurfi yace.

"Ba iya mulki iko da ginin doguwar katanga bane ke lullube da masarauta ba.......akwai tarin abubuwan dake buqatar zurfafa tunani da kyau.....ba dukkan murmushi bane ke nuna kulawa......ba kowacce farar fuska bace me dauke da kyakkyawar zuciya fara qal.....ka fara kula da kanka kafin kowa ya kawo maka daukin kula da kai" Ya qarashe maganan yana tafiya kai tsaye ga steps din da zasu sadashi da balcony dinsa zuwa babban sashensa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Tafiyarsa cikin izza duk da ruwan dake jiqa rigar jikinsa......da bata tabbacin barinta a gurin a yashe yafi qona mata rai da tsaye mata cikin idanuwanta da tunaninta. Maganganunsa basu kasance abun maida hankalinta ba.......face aikinsa da ya sanya taji ya sake zama LAMBA DAYA cikin manyan halittun data tsana a duniya.

Ko a yanzun da birra ke taimaka mata tana rage kayan jikinta,shehnaz dake daga kwance tana qarewa fuskarta ne kawai kallo.

Wani irin kwantaccen fushi ne kawai ke yawo saman fuskartata,fushin dake qara jefa shehnaz a duniyar mamaki. Me yasa komai na sheikh haisam take zafafarsa fiye da na kowa?.....me yasa ta gaza maida hankali ga aurenta dake matsowa?,take sanyawa ranta damuwa akan kowanne aiki ko hukunci da zai zartas?.

Ko a yanzun da duniya ta karade da sautin saukar mamakon ruwan sama me nauyin gaske,akhnan din na gaban glass door saman sofa,sanye da wata sweeter me sulbi oversized,peach color ce data dorata saman sleeping gown din da birra ta dauko mata. Wani qawataccen blanket birra ta dora mata saman kafadunta kafin ta musu sallama ta fice bayan ta ajewa akhnan din hular sanyi me laushin gaske a gefanta. Komai na rayuwarta yi mata akeyi idan ka dauke wanka da sallah,har yanzu shehnaz tana mamakin yadda bata iya yin komai wa kanta ba.

A yadda ta zauna ta wani cure guri daya,wani zama tayi me shigen tsugunno cikin kujerar wanda yawancin lokuta shi takeyi idan har ranta yana a bace. Dukka idanunta suna kallon glass dinne da yadda ruwan kebi ta jikinsa yana sauka qasa. Gajiya da kallonta shehnaz tayi,ta yunqura ta sauka daga saman lallausan gadon nasu,ta tako a hankali ta dawo gabanta tana zama saman wata qaramar ottoman.

"Tunanin meye haka biftu?" Shehnaz ta tambayeta a tausashe. Kaman ba zata kalli shehnaz din ba,sai kuma ta cira kanta a hankali tana maido dubanta ga shehnaz din,kafin ta sauke dauke idonta. Ta motsa labbanta a nutse.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 43*

"Sultane yayi sadakar mutuncina irin wanda bai taba yi ba tunda ya haifeni........inda nasan haka zai sadaka da martabata har ta bawa wani bagidajen malami daman takata ko zama a kanta......tabbas dana yarda na auri duk wanda sultane yake da ra'ayi.......KIMATA da DARAJATA shehnaz......ba wani abu da yayi daidai da ita" Ta furta tana jinjina kai,abinda ke tabbatarwa da shehnaz wannan EGO din nata baya tabuwa.

"Biftu......a ganina yanzu lokacine da zaki maida hankali akan aurenki ba wadannan tunanikan bafa"

"Aure?" Shehnaz din ta waiwayo tana jifan shehnaz da tambayar. Kai shehnaz ta gyada tana dubanta itama kai tsaye.

"Eh aure......nan da kwanaki bakwai zuwa goma fa....."

"Hmmmm" Akhnan din ta fadi d wani abu me nauyi da taji yana sauka cikin qirjinta,sannan ta maida dubanta ga qofar,wasu abubuwa suns yawo gami da kutsa kai cikin tunanikanta.

"Biftu.......shin bake kika zabi almaz ba?.....auren almaz zakiyi fa?,zabinki" Shehnaz ta fada tana dora hannunta saman cinyar akhnan din.

Akwai alamun shakka da kokwanto cikin muryar shehnaz,abinda ta tabbatar yana cikin sharadinsu da mammina,don haka ta sake juyowa tana duban shehnaz din

"Don ni na zabi almaz......ba hakan yana nufin ra'ayina zai sauya ba......ba abinda zabin ya zamemim face zallar qasqanci.....kamarni zaya karbi sadakina da wasu tsirarun sulalla?" Tayi maganan tana nuna kanta da yatsarta,da alamun bacin ranta ya sake motsuwa.

"Kuka zaki masa biftu?" Shehnaz ta furta a hankali bayan ta gama qarewa qwayar idanun akhnan kallo wadda ta hada ruwan hawaye daya sanya qwayar idanun nata qara qyalli.

"Jamais de la vie(Allah ya sawwaqe)" Ta fadi tana jifan shehnaz da harara kamar wadda ta yiwa fatan mutuwa. Yadda tayin ya sanya shehnaz sakin wani qaramin murmushi. Batasan me yasa ba,batasan kuma me ya faru ba.....izzarta bata barinta nuna jin zafin abubuwa,ba'a mata ma abinda zataji zafin ballantana ta nuna,amma yanzun.....tashi daya.....lokaci daya gaba daya sheikh haisam din ya birkita tunaninta,ya dagula lissafinta,ya sanyata tanajin zafi dama haushin komai.......ME YASA?. Tambayar da shehnaz ta yiwa kanta kenan sanda akhnan take tattara ya nata ya nata. Ta tabbatar daki zata canza,wannan din kuma salonta ne,dabi'arta ne idan suka bata mata rai ita da aisa,ko sukayi mata zancan da bata so. Sai batace mata komai ba,bata kuma hanata fitan ba,don tasan zai wahala ta iya kwana ita daya yadda ake tsula ruwannan,duk kuwa da cewa wani irin kurman gini ne da bakajin qara ko sautin saukan ruwan,saidai kuma baya hana walqiya ratsowa har inda kake,mafi girman abinda akhnan din tafi tsoro kenan.

"Kiyi qoqari ki tashi da wuri,don gobe ne naji nanay tana maganan za'a fara gyaran jiki" Ta gayawa akhnan din cikin daga murya kadan tana boye dariyarta can qasan ranta. Ita abun su

Inda ace tana da sauran energy a tattare da ita,a yau din zata tsaya ne suyi abinda ta jima bata yishi ba,tabbas da sai an shiga tsakaninsu da shehnaz,to amma ba wannan ba......kowacce gaba ta jikinta ba abinda take buqata sai KADAICI da KEBEWA.

*HAISAM*

A tsaye kawai maleek din yake rungume da hannayensa daya riqe lallausan towel a tsakiyarsu yana kallon yadda haisam ke zare jiqaqqun kayan jikinsa yana zubesu saman sofa bed.

Dukkan wani motsi na haisam din maleek yana biye dashi,har zuwa sanda ya rage fara qal din vest din jikinsa,ya juya a nutse yana laluben towel sai maleek ya daga masa na hannunsa yana duban qwayar idanunsa da bai kalli kowa dake tsaye carko carko ba tun a parlor.

Fararen manyan idanunsa da suka sauya launi kadan ya daga ya kalli maleek din,sannan ya miqa hannu ya karbi towel din,sai maleek ya sakar masa ba tare da yace masa komai na,shima ya karba yana juyawa a nutse ya nufi toilet.

Ajiyar zuciya me nauyin gaske maleek ya saki,ya jinjina kai a nutse ya tsugunna ya kwashe kayan haisam din. Yaga abinda yakeson gani din,wani irin fushi ne kwance cikin idanun haisam,irin fushin da akan samu jikin jinin SARAUTA saboda wata dabi'a ta rashin son raini dake tattare da wannan jinin wanda irinsa ne a jikinsa shi da haisam. Wannan ya sanya sau tari yafi kowa saurin fahimtar haisam.....saboda wasu irin dabi'u da jini kusan irin daya ke zagayawa a jikinsu.

Abinda yake gani a idanun haisam a yanzun me zurfi da girma ne,irin abinda bai taba gani ba a idonsa akan kowa. Ya tabbatar dukka shurun da yayi da qoqarin kaucewa hada ido da kowa yana yine cikin yunqurin controlling kansa fushinsa da kuma bacin ransa. Yayi imanin inda ba tasiri na ilimin zamantakewa da addini a tattare dashi......akhnan din zata gane girman kuskuren data tafka Kai tsaye. Yana YAKANA yana da DAUKE KAI......amma a duk sanda qura takai bango yana da wahalar sarrafuwa yana kuma da wuyar sha'ani. A mganganunta yasan ta tabo abu mafi girman da yafi tsanar a taba masa ADDININSA,dole yasan fushinsa yana iya fin haka ma. Yana kammale masa kayan ya taka a nutse yana ficewa a dakin don ya bashi daman shiryawa da daukan adadin lokutan da yaga sunyi masa.

Bai jima ba sosai ya fito ya fara shiryawa,yana shiryawan yana ambaton sunan Allah don neman agaji da samun sassaucin dacin da yakeji tun daga harshensa zuwa cikin maqogoronsa. Yanata qoqarin manta maganganunta,amma koda ya cillasu baya saisun dawo masa cikin kansa.

"Subhanallah" Ya fadi a hankali lokacin daya kammala fesa wannan mayen turaren nasa ya ajiye bottle din saman madubi. Tafin hannunsa ya sanya ya shafa qirjinsa har sau uku yana furta addu'ar sassauta fushi da bacin rai. Baisan me yake samunsa ba a kwanakin nan.....baisan me yasa a kanta fushinsa yake yawa ba.....baisan me yasa kome tayi yake bata ransa fiye da yadda ya kamata yaji ba.

Yayi iyakacin bakin qoqarinsa na kaucewa kowanne shirgi nata,don ba dominta ya shigo AGADEZ ba,ba zamanta yakeyi ba.....bata kuma cikin lissafin mutanen da yake hangen bincikensa zai iya wucewa ta kansu,amma kuma baisan me ya sanya lamuranta ke sake shiga cikin rayuwarsa ba.

Duk yadda yakai ga yakicewa da dojewa amma sultane yana sake jawoshi da sakashi cikin al'amuranta......banda girmamawa ga sultane sam baiga hadinsa da karbar sadakinta da kuma zamowa waliyyinta har ya daura mata aure ba.

Komawa yayi ya zauna a hankali gefan sofa bed din yana sake maimaita addu'ar. A hankali a hankali yaji yanayinsa yana daidaituwa,fushin kuma yana raguwa,sai ya miqe a hankali ya soma takawa bayan ya sanya flip flops dinsa masu tashin gaske,don kawai fitowar ta zama dole saboda maleek da omar da yasan ba gidan zasu kwana ba.

"Nifa na kasa jurewa......batasan gonar da take shiga bane?......inda a Jimma ne tana zaton shekara daya ma ta isheta ta samu daman tsaiwa kawai a gabansa......iya tsaiwa kawai obbo maleek,bare harta samu daman fadin maganganu masu zafi?" Abdii dake balbalin fada ya fadi yana nuna yatsarsa ga maleek dake zaune hankali kwance yana shan coffee dinsa,da alama kuma ya tattara dukka hankalinsa akan abdii din daketa zirya yana fada.

Murmushi omar ya saki yana ajiye remote din hannunsa daya dauka don kashe Ac din parlor din

"Ina hakaitota ni kaina cikin masarautar jimma........rashin sani yafi dare duhu,inda cikin jimma ta fadi wadannan maganganun data zama nama".

Readers Also Read

More by Huguma