L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 24
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 24: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 24. "Kafi gaban bada mamaki.....saidai kace al'ajabi,ina…
3,370 words
"Kafi gaban bada mamaki.....saidai kace al'ajabi,ina tsoronka sometimes" Omari ya fadi yana kurbe coffee dinsa. Maganan ya sanya haisam murmushi kawai,ya maida dubansa ga gabansa sosai yana hangen yadda iska ke wasa da ganyen bishiyoyin daketa rangaji a gabansu tare da ci gaba da karantar sauyawar kowanne motsi na bulama da yake iya qiddigeshi cikin kansa da yanayin lissafin ma'abota kakkaifar qwaqwalwa dake aiki da intelligence na security. Baiyi niyyar sake cewa komai ba......sai kuma sabon takun da yaji a bayansa ya sake waftar wani kaso na hankalinsa,saidai hakan bai iya janye nazarinsa akan bulama ba dake sake kusantosu cikin irin hikimar da yake zaton yana da ita,kamar yadda takun bai sanyashi ya juya bayansa ba kamar yadda omari yayi.
"Subhanal malikul quddus" Omari ya furta qasa qasa yana tabo haisam,still idanunsa suna kan akhnan da nata duban yake tsaye akan haisam kawai,haisam din da bai ko motsa ba bare ya waiwayo gareta.
"Haisam......princess din agadez ce da kanta" Omari ya furta a karon farko daya soma ganinta ido da ido kuma kai tsaye haka. Wani irin mamaki ke saukowa yana lullube omari,da gaske ne yadda ake radi radin kyawunta,yadda ake wassafata har bai kai yadda take a fili ba,ganinta a fili ya zarta yadda ake maganarta,tabbacin da gaske ba kowa bane ya taba tozali da ita.
"Idan har tazo nan ne saboda ni.....ka barta ta qaraso,banaso kaci gaba da damuwa da isowartata" Abinda yace da omari kenan still na abinda ya sauya daga tsaiwarsa a gurin hankalinsa na rarrabuwa gida uku yana kuma qoqarin kula da kowanne sashe.
Wani bacin rai me nauyin gaske ya soma narke mata yana ratsa kowanne lungu da sashe na zuciyarta. Ta tabbatar tayi imanin yaji takun tafiyarta,kamar yadda ta fahimci akwai wani a gefansa dake tsaye tare dashi da yaji alamun tahowarta,amma yanayin tsaiwarsa bai canza ba ballanta yakai ga waiwayo inda take. Me ya dauki kansa?,me yakejin kansa?,wannan kadai yana sake tabbatar mata ya shirya yin hakanne don ya wulaqanta ya toxartata ya qasqanta matsayinta a duniya,a yau kuma taci alwashin saita maida wannan martanin a kansa,saita sanya yaji fiye da zafin da ita taji.
Tazara kadan ta rage a tsakaninsu,ta tsaya cak tana goye hannayenta a qirji gami da sake zuba masa idanu ta baya tana sake zurfafa kallonta a kansa. Taku hudu omari yayi yana basu space,space din dabai nesantashi da ji da ganin abinda ke faruwa ba.
Yaji tsaiwarta a bayansa,saidai yanajin kamar kusancin dake tsakaninsu yayi yawa,amma duk da hakan bai juya ba sai bayan wasu sakanni da suke sake tabbatarwa da akhnan shi din MA'ABOCIN GIRMAN KAI NE.
Bataga alamun zai juyo ba....bataga alamun yasan da wanzuwarta a gurin ba,haqurinta kuma ragagge ne da ba zata iya jiran reaction dinsa ba,duk da tarin izzar da take cinta sai ta sake goye hannunta sosai a qirjinta,cike da izza,cike da jin isa ta motsa labbanta,tattausar muyar nan da bacin rai ya yiwa murfi ta soma yawo cikin iskar dake kadawa tana isar da saqonta ga kunnuwansa.
"Wannan itace hanyar da malamai suke bi don qasqantar da daraja kima da martabar 'ya mace.......da bautar da ita cikin aure da sunan addini da kuma musulunci da irin son zuciya da qarairayinsu!" Sosai sautin maganarta ya zauna masa cikin kai da zuciya da wani irin dumi da yaji yana mamayar zuciyar tasa.
Numfashi yaja ya aika har cikin hunhunsa yana kiran sunan Allah can qasan zuciyarsa da neman taimako kada shaidan ya rinjayeshi,sai ya saki qarfen da yake dafe dashi ya waiwayo a nutse idanunsa suna sauka a kanta.
Guri daya idanunsu suka sarqe,ya sake zare dubansa daga kan fuskarta data bayyana tarwai ta siririyar walqiyar dake haskawa kadan kadan wadda bata dauke da sautin komai,wannan shi zai baka damar ganin yadda iska ke wasa da mayafin saman kanta,da sassalkan wani siririn gashinta me santsi daya ratso ta gefan kunnenta ya fito.
Yadda ya zare dubansa a kanta kamar kullum kamar yadda ta kula al'adarsa ce ya sake tunzurata. A koda yaushe yana nuna shi din wani tsarkakke ne wanda ita ta jima da sanin son zuciya da son rai da kuma fakewa bayan addini suna aiwatar da son rai da son zuciyarsu babu wanda yakai malami yin hakan. Wanna fusatar ta sanya ta qara taku biyu zuwa gabansa,tana son ta bambance me yakeji dashi da yake mata wani kallo sannan ya watsar ta hanyar janye idanunsa a duk sanda zasu hadu irin haka.
"Kana tunanin bada aurena wani abu ne me sauqi da wasu qananun sulalla marasa darajar da ko takalmin sakawa a qafar hadimaina darajarsa tafi ta wadannan sulallan?" Ta sake fadi cike da tsiwa numfashinta yana dagawa sosai ta saman qirjinta. Numfashi ya sake ja yana aikewa cikin gangar jikinsa yana jin wataqila wannan zai taimaka wajen controlling kansa da zuciyarsa.
"Wannan itace hanyar daka zaba wajen qasqantar da darajata?wajen gayawa duniya abace ni me sassauqar daraja?......darajar da baka isa ka samu kwatankwacinta ba?!" Ta sake tambayarsa tana sane takawa zuwa inda yake tsaye kamar ta manta da tana qara kawo kusanci ne a tsakaninsu.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Labarina.......sunana.....daukakata da darajata wani abun tattaunawa ne tsakanin manyan masarautu,ba na iya agadez kawai ba......dole sadakina da aurena ya bambanta dana kowacce d'iya dake jin asali da gata!.....bakasan hakan ba?" Ta sake tambayarsa,idanunsa na sake hange mata wani irin calmness a tattare dashi. Kaman ba ihu take masa ba.....kaman ba fada take masa ba,tunzura take so yayi.......tanaso yayi wani abu guda daya da zai sanyata ta yaga wannan rigar maluntar.....rigar mutuncin da yakejin yana sanye da ita.
Tarin rufewa da idanunta sukayi ya sanya ya gaza ganin yadda adams apple dinsa ke sama da qasa yana qoqarin tura duk wani yunqurin bayyana fusata da fushi da zuciyarsa ke qoqarin turawa saman fuskarsa. Zuciyarsa na wani irin motsawa da mugun qarfi,yayin daya sanya kalar nashu qarfin yana danneta da dukka iyawarsa. Amanar da sultane ya damqa a hannunsa ke gilmawa cikin idanunsa........yardar sultane a kansa yake tunawa.......da rauninta na kasancewarta D'IYA MACE......d'iya macen ma da rayuwarta cikin wani yanayi na tagayyara da girman kanta son ranta da son zuciyarta ya hanata ta gane ramin da take shirin shiga ta binne kanta.
Hannunsa kawai omari yake dunqulewa yana qoqarin bin umarnin haisam ta hanyar danne na'aurar warning dake tsakiyar tafin hannun haisam din. Mafi girman qarar da na'urar keyi yake gayawa omari qaqqarfan warning haisam ke masa na kada ya soma matsowa ko sanya baki kome girman abinda zai faru.
"Ka qwace komai na matsayina daga hannun sultane......a zakutana mutane ma kanason qwace wannan martabar tawa?......ka gayamin......nauyin kudin da zai siya dukka ilimin da kake taqama dashi kana tunanin yayi daidai da abinda zai iya biyan sadaki na?!!".
Wani abu me tsini yaji ya caki tsakiyar zuciyarsa......wani abu daya sanyashi daga dukkan manyan idanunsa ya zubesu saman fuskarta,idanun da suka nutse cikin nata ba tare data shirya ba,suka kuma soma sakin wadannan magnet din masu wani iri kaifi da girma da suka sanyata yin taku biyu baya da kanta don rage tazarar da ita ta tsuke nisan dake tsakaninsu.
"Sadaki ba shine ke daga darajar mace ba ko ya sauketa......sadaki ba gasa bane.......haqqi ne da Allah yace a bawa mace.....sai kuma addininmu ya gaya mana mafi qarancin sadaki shi yafi albarka a aure......nayi abinda shari'a tafi so......idan har alfaharinki da girman kanki yana da nauyi sama MUTUNCI da KARAMCI ......wannan ba matsalata bane" Ya qarasa maganan yana zube hannayensa a aljihun jubah dinsa gami da dage dukka kafadunsa,manyan fararen idanunsa na zagayawa tsakanin blue eyes dinta,daga bayanta kuma yana hange masa kusantowar motsin da yakejin bai aminta dashi ba,saidai motsin bai janye hankalinsa daga duban kai tsaye da yake mata na ido cikin ido ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE PAGE 42*
Batasan ya akayi ta samu idanunta da zame kansu da kuma qwace dubansu daga cikin nasa ba bayan ba abinda ta tsara yi kenan ba.......tana jin idan ta bari ya gayamata ko ya maida mata magana ko qwaya daya ce yayi jayayya da girmanta,don haka cikin rashin yarda da izzarta takai qasa ta sake motsa labbanta fushinta na bayyana sosai.
"Me ka dauki kanka?......a tunaninka kai din waye?" Wani miskilin murmushi dake cakude da izza ya saki,wanda ya kusan tafiya da numfashinta na wucin gadi,cikin nuna halin ko in kula yana kuma sake raba hankalinsa da yadda yakejin hucin giftasu daga hagu zuwa dama ya maida mata amsa.
"Muhammad haisam wani ne.....wanda ya zame miki tilas ki dakata da qidddige iya adadin ikonsa......don zaki gaza a sanda hasashenki bazai taba iya cafko adadin qarfin ikonsa ba". A karon farko iya tsaho shekarun da tayi a duniya da aka taba challenge nata......da ta taba fadin magana aka maida mata......da aka tsaya a gabanta ana dubanta da duba na kai tsaye......irin duban da mammina ko sultane kadai keda iko da lasisin yi mata shi. Koda ya samu daman tsaiwa a inda ta tsaya.....koda ya samu daman maida mata magana ba zata bari ta kwana da ciwon rai ba.
"Idan kana jin dadin tozarta matan da kasan sunfi qarfin matakinka a rayuwa?,daga kaina ba zaka qara kusantar aikata hakan ba" A karo na biyu wani qasaitaccen murmushi ya subuce masa,yayi qas da kansa yana hangen tazarar inuwar boyayyen mutum daga bayanta wanda yake da tabbacin batasan da tsaiwarsa ba,sai ya daga kansa a nutse yana mata nuni da hanya cikin kamala.
"Idan kin gama fadin duk abinda yake ranki kina iya tafiya" Idanunta ta qanqance sosai,reshe yana neman juyewa da mujiya. Gurbi da muhallin fushi takeson gani saman fuskarsa akan maganganun data gaya masa.......amma sai yake maye gurbin haka da wani murmushi da iya tsahon zamanta cikin da'irar sarauta,gidan mulki da iko bata taba ganin murmushin dake cakude da zallar izza irinsa ba. Yabar mata ciwon fadin maganar a ranta?,kuma yana umartarta da tafiya daga muhallin daya kasance mallakin mahaifinta?......saman QASAR data kasance cikakken ikonta..
"Ki tafi nace" Yayi maganar wannan karon yanayin fuskarsa yana juyewa da wani matsanancin tsare gida yana kuma ajiye mata wani nannauyan kallo da taji ya mata wani mahaukacin kwarjini.
Wannan dabi'artata ta taurin kai da kafiya ita ta motsa.....izzarta ta taso ta lullubeta,ita dake bada umarni yau ita wani yake bawa umarni?......ita dake da iko na fada aji ita ake fadawa abinda zatayi?.
Sake tsareta yayi shima da kakkaifan kallonsa,yana sake irga motsi da takun bulama. Kaucewarta a gurin yafi buqata a sannan,don yanason nunawa bulama qarshen rashin qwarewa cikin aikinsa. Saidai kuma baya qaunar wanzuwarta a gurin,saboda ba gaban idanunta yake buqatar yin kowanne motsi nasa ba.....amma yana karantar kafiyarta da taurin kanta na shirin zame masa cikas,kaman yadda ya karanci bulama yana daf da kubcewa tsarinsa,don haka dole yayi wani irin taku da bai kai biyar ba,ya miqa hannu tsakanin shukokin dake daura dasu,ya damqi wuyan bulama cikin wani irin zafin nama,sannan ya fincikoshi daga duhu zuwa cikin haske,ya kuma watsar dashi a gurin.
Wani irin matsanancin bugawa kawai zuciyarta takeyi,cike da wani irin matsanancin tsoro da bata taba jin irinsa ba. Ta fidda manyan blue eyes dinta tana duban bulama din da haisam ya watsar a gurin,saidai yana riqe da hannayensa da ya banqaresu ta baya,wanda azabar irin wannan riqon da haisam yayi masa ya sanyashi fidda wani irin nishi a wahalce.
Iyakar saninta da hadiman gidan gaba daya batasan bulama ba. Batasan wayeshi ba,batasan kuma wannan fuskar ba......me ya kawoshi nan?,cikin duhun da babu komai cikinsa sai hasken walqiya?,cikin duhun bishiyoyin da ba wanda zai iya labewa ciki sai wanda ke dauke da alama da tambari na rashin gaskiya?. Ba ita ba......hatta da maleek dake kallon komai daga nesa.......amma zama da haisam da dadewarsu tare ya sanya yake fahimtar lokutan da haisam din yake buqatar wanzuwa a guri shi kadai,don haka sai ya tsaya daga ness yana kallon komai. Da fari hankalinsa da nazarinsa gaba daya yana kan akhnan din. Ya cika da wani irin tarin mamakin yadda haisam yake iya hadiye maganganunta,ya sani,yana da wani irin kaifin hangen nesa da qoqarin hadiye bacin rai,saidai kuma sam sam baya daukan raini ko qanqani. Yanayin tsiwarta ya daure masa kai sosai,dukkan wannan izzar a yanzun da take magana da haisam din sai yaga ta kwaranye ta barta da iya tsiwar. Akwai wani abu da yake hanga daga can cikin dabi'unta da yake ganin zuwansa daidai da wani salon ra'ayi na haisam din.
JARUMTA......irin salon jarumtar nan ta babu gudu babu ja da baya......wani irin qarfin hali da TSAIWA saman ra'ayi,sai ya saki wani sassanyan murmushi,wanda suke murmushin nasa keda wuya ya hangi yadda haisam din ya motsa cikin wani irin zafin nama ya kuma finciko bulama din.
Abun ya matuqar zuwa masa a bazata da kuma bashi mamaki. Baiga wani alamun wanzuwar dan adam a gurin ba......ta yaya haisam din ya fahimci hakan?,bayan kuma da kwanyarsa ta tuna masa SHEIKH HAISAM din sai mamakinsa ya dinga raguwa,ya fara tunanin me mutumin yakeyi a tsakanin duhuwar gurin?.
Kamar baisan waye bulaman ba,kamar kuma baisan wanne aiki yakeyi ya banqare hannunsa ta baya da kyau,da wani irin yanayi me cike da zafi yake duban fuskar bulama din wadda ke shimfide a qasa.
"Bazan tsaya bata bakina ina tambayarka wa kake bibiya ko me kakeyi ba a nan gurin a irin wannan lokacin......kaman yadda bani da lokacin tsayawa tambayarka WAYR YA SANYAKA......Amma zan aikeka da saqo guda days ka shaidawa wanda ya sanyaka din cewa......ni muhammad ina me shaida masa,yana wasa ne da FARAR WUTA wadda cikin ruwan sanyi take qona dukkan wanda ya raina raina LAUNINTA". Sai ya saki hannuwan bulaman,wanda hakan ya bashi daman qarasa zubewa a qasa cikin wani irin matsanancin radadi da kafadunsa da gadon bayansa gaba suke masa,sannan ya yunqura da wani qaramin hanzarin da qarfin hali ne kawai ya tattara masa ragowar kuzarin,da wata irin sassarfa yake jan qafafunsa yana bacewa daga gurin.
Taku uku kawai yayi ya koma zuwa bakin qarfen data sameshi a gurin,ya kuma juya mata baya yana kafe gwiwar hannunsa jikin qarfen ya koma salon durqushen da yayi dazu yana ci gaba da duban tsirran da sukaci gaba da kadawa da sauri sosai saboda qaruwar iskar data ci gaba da kadawa gami da damshin ruwa daya fara sauka yaf yaf mara qarfi.
Idanu ta zubawa bayansa tana sake jin wani tsoro yana sake shigarta na wanzuwar shuru a gurin,bata ganin kowa sai shi da ita,don omar ma tun sanda yaga yanayin reaction din haisam ya matsa yana kutsawa zuwa kewayen gidan ko zai samu wani evidence motsi ko wani dake tare da bulama din.
Runtse idanunta tayi da qarfi daga duban faffadan bayansa da yabar mata saboda sririyar walqiyar data haska sararin samaniya,ta kuma nuna yawan hadarin da take dauke dashi. Tsoro me qarfi dake cakude da bacin rai taji yana shigarta. Nadamar rashin amsar tayin da yayi mata tun farko na tafiya taji yana ratsata. Me yasa bata tafi ba sanda taga wani abu me nauyi cikin qwayar idanunsa?,me yasa bata tafi ba a sanda yayi mata kallo na kai tsaye......kallon cikin qwayar idanunta.....bayan taso wani kallo ne da bai taba yi mata irinsa ba.
To amma duk haka ita din,GIMBIYA AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD.....har rashin darajar da zai gwada mata yakai ya juya mata baya yana ci gaba da al'amuransa kamar baisan Allah yayi tsironta a gurin ba?. Yana qarqashin cin alfarma ta mahaifinta?,yana rayuwa cikin iko na mahaifinta?. Wayeshi?,banda ordinary mutum kamar kowa?......banda ordinary hadimi kaman sauran hadiman cikin gidan,wanda suke rayuwa cikin tattalin farincikinta.....kare dokokinta da iyakokinta,yau gata a tsaye a yashe......tamkar ba itace wannan gimbiyar da ganinta yake zama GAGARUMAR SA'A GA DUK MUTUMIN DA IDANIYARSA TA SAMU NASARAR GANINTA.
A cikin jikinsa yakejin tsaiwarta a gurin,saidai bayaso ya waiwaya gareta harta kalli irin nasa fushin. Yana jin tsaiwarta har cikin b'argonsa,bai kuma san abinda ya hanashi tafiya yabar gurin ba,saidai wani sashe na zuciyarsa yana nanata masa MARTABAR SULTANE ce ta jawo haka.
A duk sanda zai kwanta yana jin sauti da kuma maimaicin sautin sultane a maganarsu ta qarshe cikin airport.
"Dukkan masarauta......da dukkan wanda ke cikin ta na baka amanarsa......idan nace kowa da komai ciki harda AKHNAN. marainiya ce data taso batasan dadin mahaifiya ba,duk da ta shekara hudu da ita,amma kona shekara hudunma batasan dadin safeena ba,saboda ciwon hauka da safeena tayi daga randa akhnan tayi kwana arba'in a duniya.......safeena batayin cikakken wata uku da lafiya,saidai kuma a wata ukun duk sanda take a daidaita bata bari kowa yayi hidima ga biftu,kamar tasan tafiya zatayi ta barta,kamar tasan tafiyar bame nisa bace.
Yana iya hangen qwayar idanun sultane a sanda yake masa maganar,yana iya ganin raunin dake tattare da sultane din ta cikin qwayar idanun nasa,raunin dake gaya masa wannan feelings din bame sauqi bane......me tsananin nauyi ne,nauyin daya gaza ture yaringar daga zuciyarsa,duk da girma da adadin kura kurenta a tare dashi,daci gaba da bijirewa zuwa ga umarninsa.
Damqe qarfen yayi da kyau yana jin yadda ruwan ke qara yawa. Yanason ya waiwaya ya tambayeta me ya hanata tafiya?,amma ya tabbatar idan yayi hakan zai sake gayyatowa kansa fushin da yake yaqi dashi. Kalamanta sun soki zuciyarsa sosai,sun masa wani irin rami da ya tabbatar zaibar gurbi da miki cikin zuciyarsa.
Iya adadin jurar tsaiwar da zaiyi ya kaita,sai ya zame hannunsa daga qarfen a hankali ya fara takawa. Taku hudu kawai yayi,idanunsa a gabanshi ba tare da ya ko waiwayeta ba,ya motsa labbansa da muryarsa da tayi wani irin zurfi yace.
"Ba iya mulki iko da ginin doguwar katanga bane ke lullube da masarauta ba.......akwai tarin abubuwan dake buqatar zurfafa tunani da kyau.....ba dukkan murmushi bane ke nuna kulawa......ba kowacce farar fuska bace me dauke da kyakkyawar zuciya fara qal.....ka fara kula da kanka kafin kowa ya kawo maka daukin kula da kai" Ya qarashe maganan yana tafiya kai tsaye ga steps din da zasu sadashi da balcony dinsa zuwa babban sashensa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Tafiyarsa cikin izza duk da ruwan dake jiqa rigar jikinsa......da bata tabbacin barinta a gurin a yashe yafi qona mata rai da tsaye mata cikin idanuwanta da tunaninta. Maganganunsa basu kasance abun maida hankalinta ba.......face aikinsa da ya sanya taji ya sake zama LAMBA DAYA cikin manyan halittun data tsana a duniya.
Ko a yanzun da birra ke taimaka mata tana rage kayan jikinta,shehnaz dake daga kwance tana qarewa fuskarta ne kawai kallo.
Wani irin kwantaccen fushi ne kawai ke yawo saman fuskartata,fushin dake qara jefa shehnaz a duniyar mamaki. Me yasa komai na sheikh haisam take zafafarsa fiye da na kowa?.....me yasa ta gaza maida hankali ga aurenta dake matsowa?,take sanyawa ranta damuwa akan kowanne aiki ko hukunci da zai zartas?.
Ko a yanzun da duniya ta karade da sautin saukar mamakon ruwan sama me nauyin gaske,akhnan din na gaban glass door saman sofa,sanye da wata sweeter me sulbi oversized,peach color ce data dorata saman sleeping gown din da birra ta dauko mata. Wani qawataccen blanket birra ta dora mata saman kafadunta kafin ta musu sallama ta fice bayan ta ajewa akhnan din hular sanyi me laushin gaske a gefanta. Komai na rayuwarta yi mata akeyi idan ka dauke wanka da sallah,har yanzu shehnaz tana mamakin yadda bata iya yin komai wa kanta ba.
A yadda ta zauna ta wani cure guri daya,wani zama tayi me shigen tsugunno cikin kujerar wanda yawancin lokuta shi takeyi idan har ranta yana a bace. Dukka idanunta suna kallon glass dinne da yadda ruwan kebi ta jikinsa yana sauka qasa. Gajiya da kallonta shehnaz tayi,ta yunqura ta sauka daga saman lallausan gadon nasu,ta tako a hankali ta dawo gabanta tana zama saman wata qaramar ottoman.
"Tunanin meye haka biftu?" Shehnaz ta tambayeta a tausashe. Kaman ba zata kalli shehnaz din ba,sai kuma ta cira kanta a hankali tana maido dubanta ga shehnaz din,kafin ta sauke dauke idonta. Ta motsa labbanta a nutse.