L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 27
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 27: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 27. Daidai lokacin da yake takowa shida maleek,sanye da…
3,347 words
Daidai lokacin da yake takowa shida maleek,sanye da kuwaiti slim fit thobe me sulbi saqar qasar kuwait. Dogon hannu ne da ita me wani irin zagayayyen abu a hannun da kuma wuyan jallabiyyar,royal blue data wani irin haskashi da wani irin yanayi daya fidda kyansa da kuma kyan fatarsa dake da wani irin yanayi lum lum. Sak balaren da ya tashi cikin yare da al'adun qasar larabawa,don hatta da amama(rawanin da larabawa kan nada saman kansu me kama da mayafi)sak irin nadin da wayayyun matasan larabawa keyi ne. Gefansa maleek ne,hira suke abinsu,da wannan nutsuwar da izzar sarauta a jikin kowannensu da bazai sanya kaji abinda suke fadi ba ba,magana ce a nutse duk da tana basu nishadi saboda qawataccen murmushin da yake fita saman fuskarsu gaba daya. Baisan me ya sanya maleek yace zaya qara kwanakin da yayi niyyar yi masa ba,saidai koma meye hakan ya masa dadi,yana kuma kyautata zaton maleek din ya karanci yanayinsa a kwanakin ba yadda ya sanshi bane,kamar akwai wani kewa da emptiness a tare dashi,duk kuwa da cewa yana kewaye yana kuma rayuwa cikin mutane.
Daddadar iskar dake kadawa taja sosai tana fitar da ita daga qirjinta a hankali,yanayin dake qara rage mata damuwar da takejin ta mata qawanya a duk sanda zuciyarta ta tuna nata kwanaki biyar suka rage mata a daura igiyarta a hannun wani d'a namiji da sunan mijinta,duk da tana samun sassauci idan ta tuna ba abinda hakan zai sauya ko ya sanya cikin rayuwarta,iya yadda bai matsa da neman sake ganinta ko.wata magana ko qulla wani dangantaka na sabo tsakaninsu ba kawai yana rage mata zullumi fargaba da quncin da takeji.
Idonta ta zare daga kan flower da take kalla ta saukesu a hankali zuwa farfajiyar. Kai tsaye idonta ya sauka a kansa,yana kuma damqe da hannun maleek da yake gaya masa an samo wani littafi da haisam din ke nema shekara guda kenan,babu shi a Egypt babu shi a duk inda yake zaton za'a samu littafin wanda kudinsa ya kama million daya da rabi.
"Surprise" Maleek ya furta a hankali yana jin dadin yadda alamun farinciki suka bayyana akan fuskar haisam din.
Tattausan murmushin nan nasa ya saki,yana jin wani dadi a zuciyarsa. Allah ya jarabceshi da qaunar litattafan addini da kuma karatunsa fahimta da aiki dashi.
"You're a rock star" Murmushi shima maleek ya saki yana duban idanunsa.
"Zamanka a nan English yana qoqarin janye yaren oromo daga bakinka ba?". Kai ya girgiza a hankali,murmushin nasa yana sake fadada wanda hakan ya sake tsananta kyawunsa a bayyane.
"Ba wani yare sama da nawa.....na zabi yinsa ne for security purpose".
Wani abu ya tsarga cikin zuciyarta tana fatan janye idanunta a kanshi. The giant and calm sheikh din yana tafiya da wata irin nutsuwa da yanayin da bata taba ganinsa tattare da wani ba,duk da izzarta bata barinta kallon maza sam sam......wannan ya sanya take qoqarin janye idanunta a kansa,saidai ta gaza aiwatar da hakan.
Tanaso ta karanci meye bambancin da yake dashi da sauran mutane da takejin kwarjininsa yana dukanta har daga inda take tsaye yanzu haka?. Tanaso ta qwaqulo dalilin da ya sanya yake da wannan IZZAR da JIN KAI da wannan calmness din data fassarashi da GIRMAN KAI?.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Kusancinta da sultane daya karbe......haduwar jikinsu har sau uku duk da har yanzu bata tsakanin yaqini da kokwanto akan shine mutumin hippodrome......shine mutum na farko.....namiji na farko a duniyarta daya taba taba jikinta. Tsaki taja dan siriri tana jin hakan yana mata wani irin zafi,ba namijin daya taba TSALLAKA layikan data shata rayuwarta saishi......a karo na farko ya tsallake mata iyakokinta masu tarin yawa,har yana iya ji da samun confidence ya tsaya a gabanta yana gaya mata magana mai cike da tsatstsauran umarni.
Abinda ya faru kwanaki hudu da suka wuce ya dawo mata. Me yasa saishi kadai?,me yasa saishi kadai ne zai dinga kubutar da ita daga hatsari?. Ko hakanne ya sanya yake ganin kansa a wani abu?,har yake da confidence din challenging nata?.
Aah.....ko a yanzu yanayinsa da abinda take gani a idanun nan masu wani irin haske da kwarjini,tana jin confidence din da yake dashi ba na iya kusanci da muqamin da sultane ya bashi kawai bane......akwai wata jarumta da qarfin hali tattare dashi. Wani irin taku yakeyi da a MASAURAUTA a kuma SARAUCE yake kama da takun QASAITA irin takun isashen basaraken da baya shakkar ko tsoron tunkarar komai.....baya buqatar komai daga kowa.......irin takun da sai me ilimi cikin sarauta yake iya fahimtarsa.
"Me ya hadashi da izza bayan shi din qasqantaccen malami ne kawai?" Tambayar ta sake bijiro mata,wanda ita kanta batasan sau nawa ta yiwa kanta tambayar ba.
Siririn tsakin da yafi na dazu ta kuma saki tana kuma tuhumar kanta kan lissafen lissafen data shiga yi marasa tushe ballantana makama. Ba lokaci bane na noticing dinsa yanzu......me yasa yake bayyana a duk sanda ranta yake a bace?,bayyanarsa me yasa take qara tunzura fushinta?
"Na tsaneshi" Ta gayawa kanta da kanta da wani dan qaramin sauti tana jin gargadin da zuciyarta ke mata na dauke dubanta daga kansa.
Fitar sautin sai ya zamana kamar saukar wani yanayi ne saman gangar jikinsa. Yana iya jin baqon kallo a jikinsa koda bai san ana kallon nasa ba,wani yanayi da aka haifeshi dashi,ya kuma sake masa tasiri sabda yanayin aikin intelligent security da ya zame masa jinin jikinsa.
Ya sani cewa cikin lissafinsa a yanzun akwai boyayyun idanuwa masu yawan gaske dake bibiye da kowanne motsi da kuma takunsa. Yana da wani irin zurfin lissafin da yakan iya auna komai da zai iya kasancewa a lokaci na gaba,don haka cikin qwarewa ya motsa idanunsa yana dagasu a hankali zuwa sashen da yafijin tasirin kallon.
Tsam tayi da ranta bugun zuciyarta yana qaruwa lokacin da taga kaman yanayin tafiyarsa ya canza,duk da a nutse dama can yake takawar amma yanzun ya sake zama low.....zuciyarta ta gaya mata yana dab da daga idanunsa zuwa inda take tsaye,sai tayi hanzarin zare idanunta daga kansa tana gayawa kanta babbar faduwa ce da asara ya sameta tana kallonsa.....ba izzarta bace wannan.....ba martabarta bace,ba kuma darajarta bace. Zaya dauka wani abun dabanne.....wataqila ya dauka yana burgeta ne,bayan a duniya ta bangaren maza shine namiji na farko da takejin taqi jininsa sama da kowa KODA KUWA ALMAZ dake dab da cakuda rayuwarsa da tata.
Saidai kuma inaaaa,tayi wata kyakkyawar makara,da wani irin zafin nama irin na 'yan mazan da suke da gogewa ta fannin bincike ya sarqafe idanunsa cikin nata. Taji wani irin shocked,taji kuma wata irin faduwa da kunya gami da nauyin yadda ya kamata din. Wani bacin rai ya sauko mata sanda taga ya zare idonsa daga nata cikin kallon daya mata da duka duka bai wuce second biyar ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 46* _________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ____________________________
Da baya da baya ta koma tana sake sakin tsaki mai qarfin gaske. Don me yasa?,ita ya kamata ta fara dauke idanunta a kansa daga kallon farko don ta tabbatar masa da qarfin izzarta........me yasa ya rigata dauke idonsa?,me yasa ta bari har ya ganta tana kallonsa?.
"Sufa irin mutanen nan qarfin kurwa garesu......har yanzu na kasa gano siffar malunta ko daya tattare dashi idan ka dauke tarin nutsuwa kwarjini da kamalarsa.....wannnanzaifi kyau da GIDAN SARAUTA BA GIDAN MALUNTA BA". a mamakance ta bude idanunta sanda aisa dake tsaye jikin qarfen balcony din. Batasan sanda aisa din ta isa gurin ba,uwa uba ma sam ta manta dasu.....mamakinta shine na dogon sharhin aisa din na yau wadda ba kasafai ta fiya magana akan mutumin ba.
"Ashe bani kadai nake ganin hakan ba?.......na dade banga namiji irinsa ba......akwai maza ne hurul'eeni a duniya ne?" Shehnaz ta fada tana duban aisa. Dole aisa ta saki dariya sosai ganin yadda shehnaz tayi maganar da dukka iyakacin gaskiyarta.
"Wataqila an fara kawo mana sample daga kansa". A nutse ta miqe ta fara takawa tana ficewa daga gurin,tasan muddin taci gaba da zama zasu sake bata ranta ne akan mutumin da bata qaunar zancansa kwata kwata.
★Duk da ya kasance wani irin salon kalar aure da amaryar bata buqaci gudanar da kowanne shagali a bikin nata ba,amma hakan bai hana sauyawar masarautar ba da yanayin da zai tabbatar maka akwai wani gagarumin abun farinciki da zai faru cikin masarautar kamar na aurar da d'iya me daraja ta daya a yankin agadez dama nijer gaba daya.
A kowacce rana tun daga yammaci har zuwa lokacin da dokar taqaita zirga zirga zata fara aiki qananun wasanni da kide kiden gargajiya mammina ta zube akeyi. Kamar irinsu kidan qwarya wanda ake gaurayeshi da salon waqoqo da tsaffin wasannin al'adu irin na asalin buzaye.
Maroqa da makada musamman mata sai suka samu gurin yasar da zango,kusan wuni mammina keyi tana fidda kyaututtuka masu nauyi ga wanda Allah ya tsaga da rabonsa,kaman yadda zai wahala ka shigo gidan da qoqon barar nema daga taskar GIWA a wannan lokacin baka samu abinda kake nema ba.
Zirga zirgar hadimai ta yaiwaita sosai saboda shirye shiryen tarbar baqin da zasu iso don daurin aure. Abinciccika na alfarma,sutturu masu daraja da tsada take fiddawa kawai anata rabo zuwa ga bayi da hadimai da salon irin kyakkyawar shigar da takeso kowa yayi.
Zukata da dama sun sake nutsuwa da aminta da salon soyayyar da mammina ke gwadawa akhnan. Ko iya fuskarta kadai ka kalla zakasan tana cikin matsanancin farincikin aurar da gudar diyarta a iya hange da tsinkayensu. Yadda take narkar da dukiyarta wajen komai.....kyauta ta bajinta maroqan cikin fada kakarsu ta yanke saqa a cikin kwanakin. Kwana bakwai dukka ba wanda aka daga qafa a cikinsu,har zuwa yanzu da kwanakin daurin auren suka rage biyu tal!.
Ta kowanne fanni,ta kuma kowacce fuska tayi ruwa tayi tsaki,ta hana family din DIOARY HAMMANI tabuka komai akan diyar da take halalinsu ce......tsatsonsu ce. Kakannin da suka kasance su suka haifi SAFEENA amma a dole ta maidasu wash baqi ga rayuwa rai da duniyar akhnan. Bata kallonsu a matsayin wasu shaqiqai nata......ballantana kuma akai ga d'iyoyin qannen mahaifiyarta wato cousins dinta masu tarin yawa.
Duk da idan qaddara ta qaddara zuwansu gurin morsa safiyya da zummar gaisheta,hanya kuma tayi sanadin da suka hadu,tana ganin wasu alamu ko kamanni na jini tattare dasu wanda yake shige da nata.
Rashin wannan sabon,rashin wannan jituwar,rashin wannan shaquwar ya sanya ko a yanzun ba wata cousin dinta tattare da ita idan ka cire falaaq....aisa da shehnaz.
Sai HAIRAAN data iso qasar da yaranta anwaar da Aaaron,wanda wannan karon harda me gidanta daya kasance cikakken buzu,cousin dinta NAADIR. Zata dauki wata biyu aqalla cikin agadez,don ta kwana biyu basu zo ba,don haka da kayanta da yawa ta iso ta kuma fara sauka a masarauta har sai bayan kammala biki kafin ta wuce gidanta dake daura da titin gidan gwamnati.
★★Zaune take kawai saman tattausar kujerar data kasance daga cikin kujerun hutawa na cikin kebantaccen dakin gyaran jikinta. Sanye take cikin wata baqar gown wadda ta zauna a jikinta sosai,ta kuma fidda kyawunta me sanyinnan da wani qarin fayau da fuskarta tayi saboda gyaran gashin da akayi mata jiya daya bashi daman sauka gadon bayanta ya kwanta da wani irin glowing gami da sulbi kamar na 'yar tsana. Uwa uba kuma wani irin sarewa takeji,tana rasa inner peace daga kowanne bangare na zuciyarta.
Ko a yanzun data ware tafukan hannayenta tana kalla,wadanda sukasha zanen jan lalle da yake da wani irin maroon me daukan hankali saman jar fatarta dinnan dake samun tsananin kulawa da tattali......wani irin banbarakwai takejin lamarin idan ta tuna wai jibi zata zama matar aure?.
Akwai wani qunci da takura da takeji sosai cikin zuciyarta,saidai kuma ta laluba zuciyarta kaf bataji tsanar almaz ba saidai wani irin haushinsa dake danqare da ruhinta. Qila bata jin tsanar nasa ne ta yadda bai sake matsa mata da zuwa gurinta ko nemanta ta waya ba.....amma ta tabbatar sai ta sanya almaz ya tsani ganinta a gaban idanunsa,tsana ta har abada,ta tabbatar wannan ne kadai abinda zai iya bata peace da kuma kalar rayuwar da takeso.
Shi kanshi lallen dake hannun nata kallon baqo take masa,don ba zata iya tuna yaushe ne na qarshe data yishi ba. Kawai idan tanason taga wani launi a hannunta lokaci bayan lokaci tana saka nail polish ne kawai duk color din dataga dama,bata kuma fixing nails,saidai nata da take tarawa ya danyi tsaho kadan yadda bazai dameta ba,wanda sukayi kyau a yanzun da aka musu zanen maroon henna din. (Duk da yayi kyau haramunne barin farce a hannu ballantana kuma harka siya ka qara,shin meye marabarki da DABBA kenan?,musulunci ya lissafa yanke farce cikin tsarki na asali guda biyar da muke dashi,ciki kuma harda kaciya da akewa maza,kinga kenan barinsa najasa ne,yana jawo cututtuka na jinnu bayan na infection din mafitsara harda infection din ciki. Farce yana zama inuwar shedan ne a hannunki,kinwa shaidan inuwa kuma me ya rage?,me yayi saura....zan fadada bayaninsa a gaba in sha Allah,Allah yasa mu dace).
Tana so ta roqi su shehnaz suyi nesa da ita.......tanason ta gaya musu suyi nesa da inda take,saboda tanajin maganansu tana hawan mata kai.
Kuma ta zabi zama a nan ne saboda akwai qarancin jin hayaniya na abinda ke faruwa cikin gidan. Kade kaden da wasanni da aketa faman yi da kuma yadda maroqa suke wuni abu daya,neman abun duniya a hannun mammina.
A nutse tayi sallama tana shigowa,bayanta hadimarta ce ta amana wato haleematu riqe da hannun kyakkyawan yaro daya kasance qaramin d'an hairaan din wato Aaron. Yayi kyau sosai cikin suspenders,kana ganinsa kaga rainon turai.
Cikakkiyar buzuwar data amsa sunanta,me tsaho da kaurin jiki daidai gwargwado. Kyakkyawa buzuwa dake da wani irin kyau da ta debo wasu kamanni na SAFEENA ta wasu bangarori na jikinta dama fuskarta,sama da yadda ta debo kamannin morsa safiyya,wannan ya sanya KAMANNI na jini suke nunawa sosai tsakaninta da akhnan,duk da cewa akwai tarin banbamce babamce,don da kanta tasha fadin.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Biftu ta fini kyau,nesa ba kusa ba,inda nike da kyan biftu,zan ita gaddamewa cewa ni din hurul'eeni ce" Sosai maganan ke bawa 'yan uwa dariya,saidai kusan kowa ya sani akhnan din wani baiwar ajiyayyen kyau Allah yayi mata.
Kaurewa da hayaniya dakin yayi,har tsakanin ita da shehnaz da kuma aisa wani baya jin abinda wani yake fadi. Sun jima sosai suna karadinsu,tana zaune daga gefe ba tare data motsa ba,har zuwa sanda hairaan ta miqe a nutse tana baro su shehnaz amma tana ci gaba da magana dasu
"Qarfe biyar daidai za'a fara gabatar da lecture din,na minti talatin ne kawai,kuyi qoqari ku shirya don inajin saura mintuna ashirin biyar din tayi" Ta qarasa maganan tana zama gaban akhnan saman wani tattausan babban tuntum da jikinsa ke zane tsaf da tambarin masarautar agadez.
Idanunsu cikin na juna ita da akhnan din,akhnan na duban kamannin da ake yawan fada hairaan ta debo na mahaifiyarta,tana kuma qoqarin tuna kamannin mahaifiyarta na zahiri ba wanda take gani a hoto ba. Murmushi hairaan din ta saki da wannan tarin nutsuwar data gada daga mahaifinta da sashen hikimar data samu daga morsa safiyya,ba abinda bata sani ba,ba abinda bata fahimta ba,kuma ko yanzu kafin ta baro wajen morsa safiyya sunyi doguwar magana sosai da morsa din.
"Bana jin komai a zuciyata game da auren nan hairaan,bansan yadda akayi na wayi gari ba zuciyata tayi qaura daga tsananin quntata da labarin auren biftu ba zuwa wani irin sasssuci da tarin nutsuwa. Nayi addu'a kaman ba gobe hairaan,kuma inaji a jikina ubangiji bazai tankwabar da hannayena ba......hannun dake qarfafar zumunci yake kuma qoqarin ceton ruhin da baiji ba bai gani ba.......hannun dake qoqarin kare zumuntar Allah kada ta tozarta". Sosai maganganun morsa safiyya suka ratsa hairaan.
"Barka da yammaci amarya" Hairaan ta fada da murmushi saman fuskarta,bata wani damu da rashin gaidata da akhnan batayi ba,don ta sani mulki da sarauta ba qarya bane. Ita din bata gaji sarauta ba don mahaifinta ba basarake bane,attajirin malami ne ma'abocin tsantsar ilimin addini,nata mulkin na kudi ne da ilimi da yasha banban da sarauta.
"Barkanki....kinzo lafiya?" Akhnan ta fadi a hankali. Hairaan na daya daga cikin mutanen dake d'an yiwa akhnan din kwarjini kadan,ta girme ma akhnan nesa ba kusa ba,don kusan tayi quruciya sosai a gaban hairaan,kuma a wancan lokacin duk da yadda mammina taso raba tsakani da nunawa hairaan bata da hurumi akan akhnan idan tayi wani abu na rashin daidai a quruciyarta,ita din agola ce da uwarta tazo da ita gidan mahaifin akhnan cin arziqi amma hairaan din bata yarda ko aminta da hakan ba. A zamanin da ba wanda ya isa ya yiwa akhnan fada ko ya hantareta koya gyara mata idan tayi wani abu ba daidai ba,kaman yiwa babba tsawa magana a sake kota harareshi,ko wani abu daya kamata tayi taqiyi ita hairaan rufe idanunta take tayi mata. Duk da hakan ya haifar da rikici da bacin rai sosai tsakaninta da mammina din,amna taurin kai da kafiya shigen na akhnan din gareta,don haka idan anyi yau gobe ma sai an kuma,abun bazai kashe mata gwiwa ba.
Ko sanda mammina ta fidda tsarin budewa akhnan aji ita kadai a dinga karantar da ita a gida saboda tsabagen gata hairaan ce tayi ruwa tayi tsakin hana hakan faruwa. Ita dinma kaman morsa safiyya a wasu lokutan,bata da shakka ko tsoro,kai tsaye ta wuce gurin sultane a sannan ta bashi hujjojinta,kuma take yaji ya gamsu,ya kuma sanya akhnan taci gaba da binsu makaranta. Makaranta ce me tsadar gaske da turawan France suka bude suke kuma koyarwa a cikinta,don haka sosai ake karatun da zaka dauka yaro ba cikin qasar niger yake karatunsa ba.
"Alhamdulillah biftu.......ina fatan kin shirya saboda quracewar lokaci?" Hairaan ta fadi tana jawo akwatin dake gefanta wanda haleematu ta ajiye. Idanu akhnan tabi hairaan dashi sanda take ciro wata fara tas din gown da aka wadatata da wasu irin swarovski masu tsananin kyau da daukan hankali.
"Lecture din yau akan aure da morsa ta shirya......"
"Sheikh muhammad haisam ne zai gabatar,na tabbatar zamuji abubuwa da yawa......inaso naga guy dinnan a fagen aure......matarsa ta gama morewa rayuwar duniya wallahi" Shehnaz ta karbi zancan tana ajiye kayayyakin hannunta kan wani sofa daban. Murmushi hairaan ta saki
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 47*
"Har yanzu shehnaz tana nan da halinta bai sauya ba" dariya ta dan saki.
"Da gaske maman Aaron,ke kinfimu sanin muhimmancin auren irinsu ai ko?" Shehnaz tayi maganan da dukka gaskiyarta. Murmushi sosai hairaan ta saki tana tunawa da maigidan nata. Dan boko ne sosai,amma kuma yana da wadataccen ilimin addini daya sanya komai nasa yake me tsari da ban sha'awa. Tasha masa wauta......tasha masa abubuwa masu yawan gaske da zasu iya bata ran jahilin namiji ya tunzura harma yakai ga saki,amma a lokuta da dama yafi zabar yin shuru idan ta bata masa rai a maimakon magana,yafi zabar yayi nesa da ita har sai ya sauko,yasha gaya mata