Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 28

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 28

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 28: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 28. "Mafi alkhairinku shine mafi alkhairinku ga…

3,351 words

"Mafi alkhairinku shine mafi alkhairinku ga iyalinku......gidan annabi s a w nake tunawa hairaan,annabi nake tunawa nake miki uzuri,maganansa ta qarshe a duniya ina muku wasiyya ta alkhairi akan mata,ta yaya zan take wannan?". Sannu a hankali sai wannan dabi'un nasa suka dinga saitata,suka sata ta dinga jin kunya itama ta masa ba daidai ba,sai zamansu ya zama me wani irin dadi,kowannensu yana duba Allah da annabi yana qoqarin kyautatawa dan uwansa da kuma kiyaye b'acin ransa.

Kai hairaan ta jijjigawa shehnaz a hankali

"To kin gani?,kawai don nasan samun soyayyarsu baya zama abu me sauqi a gurin mace......banda haka Allah mom Aaron tsaf zan iya bawa jamaal haquri......"

"........shehnaz?,jamaal din shima irin mijin da kike buri bane?".

"Irinsa ne,amma bai kama komai na sheikh haisam ba" Ta fada tana dan hade ranta kadan.

Idanu akhnan ta janye daga kan shehnaz,tana jin wani bacin rai,sannan ta aje dubanta kan hairaan.

"Don Allah su fita" Ta fadi a hankali,saboda yadda zuciyarta ke tunzura a yanzu batason tayi wani abu daba daidai ba. Ta gaji dajin maganganu a kansa,dazun falaak tabar gurin suka gama zancansa,wanda ta lura ma kaman akwai wani abu a zuciyar yarinyar game dashi,yanzun gashi shehnaz ta baro wani sabon hirar. Tana qoqarin danne zuciyarta dabin maganar da suka gama dazun da sassafe da mammina.

"Na gama miki dukkan abinda ya kamata ya cancanci uwa ta yiwa diyarta......duk wani motsinki akan aurennan abun bin diddiqi ne,yanayin walwala da farincikinki shine zai bawa mutane tabbacin ZAB'INKI kika aura,akasin haka kuma shine zai saka kokwanto a zuciyar mutane,ya bada qata wawakekiyar qofar zargi a kaina......akasin haka kuma zai zamana qalubale a kaina da kuma zarge zarge da zagin da ban da alhakin ayimin shi".

Cikin kokwanto hairaan ta dauke dubanta daga kan akhnan ta maida gasu shehnaz.

"Guys.....ko zaku bamu guri muyi shirin amarya?".

"Yanzu kuwa,muma so muke mu isa gurin da wuri don muji komai sosai" Shehnaz ta fadi tana murmushi sannan ta kwashi kayanta ta fita aisa ta bita.

Sama sama take fahimtar maganganun hairaan,wadda ta dage cikin hikima tana gaya mata haqqin aure da nauyin biyayyar miji dake a kanta cikin hikima. Idanunta kawai ta lumshe,cikin ranta tana fadin,inda hairaan din zatayi shuru ta hutar da sautikanta da yafi mata alkhairi,saidai dole ta qyaleta taci gaba da bayaninta ba tare da tana fahimta ko daukan komai ba.

Abinda yafi yankar zuciyarta a yanzu ME YASA SAISHI?. Shi za'a sanya wai yayi mata wa'azin aure?,duk da tarin kawunnanta da take dasu?. Me yasa ya kanainaye komai ne?,me yasa komai ya karbe?,komai ya shiga ciki?,wanne irin annamimanci ne wannan?. Saita furzar da siririyar iska daga bakinta tana sake jin matsanancin haushinsa a ranta.

*HAISAM*

Window din qarshe ya rufe na dakin,yasa hannu ya zuge curtain din dakin wai yana sanya rai ko hakan zai rage dauko masa hayaniyar dake cikin gidan zuwa dakin nasa. Hayaniyar da tunda aka fara shagulgulan yake jinta a tsakiyar kansa tana shiga masa dukka kunnuwansa. Ya sani mutum ne da bame son hayaniya da yawa ba,amma wannan yawaitar hayaniyar batayi qarfin da zata dinga damunsa har haka ba,baisan me yasa yake jinta a kurkusa da kunnuwansa ba.

Har a ransa yakejin banda amanar masarauta da sultane yabar masa da gidansa zai koma,kamar hakan zaifi sama masa nutsuwa.

A hankali yake takawa zuwa gaban dressing mirror dinsa wanda a gabansa dressing table ne dake dauke da kayan shafawa na maza designers. Omar yasha tsokanarsa da cewa social sheikh,don idan kazo gurin zaka raina gayunka ne da ganin wasu irin designers perfume designers cream and oils,roll-on body mist da hair mist da baka taba ganin irinsu ba. Idan turare ake magana KAMFANIN ne shi da kansa dama,bayan personal wannan mayen turaren nasa,akwai turaruka daban daban da suke masa,kaman turaren gashi,dana underwear dinsa daya zama unique,nashi ne kawai a matsayinsa na mamallakin kamfanin. Kaman turarensa na jikin kaya,haka sanyayan body perfume dinsa da suka kama fatarsa da duk wani gashi na jikinsa babu inda zakaje kaf kasuwannin turare na duniya ka samesu. Maleek na dason turare,wannan ya sake sanya shaquwa tsakaninsu sosai,shima kuma daban ake masa nasa turaren,duk da baikai na CEO ba.

A hankali maleek yake binsa da kallo har zuwa sanda ya zauna saman stool,jikinsa sanye da wata tattausar milk color din bathrobe.

"Haisam" Ya kira sunansa kai tsaye,abinda ya janye hankalin haisam din kenan zuwa ga maleek.

"Kana lafiya?" Ya tambayeshi yana dubansa sosai. Manyan fararen idanunsa ya lumshe sannan ya jinjina kai a hankali ya furta.

"Alhamdulillah" Idanu maleek yadan kafeshi dashi,sai ya jinjina kai shima yana furta.

"Ma sha Allah" Saidai cikin jikinsa yana jin ba hakan bane abinda haisam ya fadi. Maida kansa ga cream dinsa haisam din yayi,bashi da tabbacin me yakeji a jikinsa ko kuma me yake damunsa,amma yasan ba lafiya komai yake tafiya daga gangar jikinsa zuwa zuciyarsa ba.

Mintuna arba'in ya kwashe aqalla kafin ya fito tsaf cikin shigar kurta pyjamas fari qal,kamar yadda tun daga half shoe din qafarsa da wani irin modern amam daya zagaye kansa dashi kaman na Indonesia ko Malaysia shima ya kasance fari din.

"Ma sha Allah" Hakeem ya fadi yana duban haisam da murmushi.

"Nayi burin su khadeem suna kusa.....zamana a nan sai nakejin kamar wani yawon bude ido nazo da ban taba zuwa irinsa ba" Murmushi kadan haisam ya saki,duk da yadda yakejin kansa kaman yana sara masa kadan kadan. Yasan me maleek keson fadi,ya saba da jin maganganunsu irin wannan a duk sanda yayi ado,don shi din dama ma'abocin ado ne koda ba inda zaya fita.

"Ba lecture bace takai tsaye ba......muna gurinmu suna gurin su" Ya furta yana daukan turarensa ya fesa kadan saman kayansa ya ajiye. Agogonsa dake ajiye a gefe Rolex brand yana daurawa a lafiyayyar fatar hannunsa dake da wani irin kwantaccen gargasa.

Murmushi maleek ya saki,haka tsarin haisam din yake,duk sanda lecture irin haka ya tashi indai ta mata ce saidai su ganshi jikin screen makeke da zaa saka musu a hall din,wannan shine abinda ya hanashi zama malamin university duk da yana da burin hakan don alfanun da ilimantarwa take dashi,ya tattara hankalinsa dukka akan kamfanonin sarrafa turarukansa da yanzu yake shirye shiryen bude branch a hadaddiyar daular larabawa wato UAE.

Takawa kawai yakeyi amma bayajin wani sauran karsashi a tare dashi,ya tsammaci ganin omari a qasa yana jira amma koda suka sauko baya nan,sai ya sanya hannunsa a aljihu ya ciro wayarsa ya fara neman omar din.

Bayajin zai iya tsaiwa gabatar da lecture din,don haka ya yanke kiran omar tun dazu ya jagorancin abun. Wani irin rauni yakeji a jikinsa da wani ciwon kai qasa qasa,yanayin kuma ya fara masa ne kusan kwanaki biyar baya,tun ranar da suka fara bukukuwansu na al'ada cikin gidan,a sannan yana zaune a balcony dinsa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

*AKHNAN*

"Ma sha Allah,tabarakarrahman" Hairaan ta fadi tana duban akhnan din. A yau take sake gamsuwa da baiwar kyan da Allah yayi mata dari bisa dari,duk da ko a baya bata inkari,don momma safeena dama tafi kowa kyau cikin dakinsu morsa safiyya.

"Wanne irin turare ne wannan biftu?" Hairaan ta dauke idonta daga kan kwalbar turaren tana duban akhnan. Nata idanun ta janye daga kan kwalbar turaren ta dubi hairaan din. Batasan yadda zata misaltawa hairaan din yadda take mutuwar son kamfanin turaren ba......bata da wani zabi a turare a duniya yanzu sama da turaren tun wata shekara data taba zuwa dubai ta siya product din ganin yadda ya mamaye shops dinsu a can da supermarket dinsu. Tana maitar son turaren kamfanin,tasha attempting halartar taron da sukeyi na product dinsu yearly a dubai amma bata samun dama,saboda yawanci yana zuwa ne a sanda sahel couture ke lissafin ribarsu na shekara da wasu gyare gyare a kamfanin.

"Bansan yadda zance miki ba,amma ki gwada amfani da kayan kamfanin" Ta amsawa hairaan a taqaice. Tun daga kansa bata sakejin turaren da yayi mata ba,sai wanda birra ke turara mata kayanta dashi na kamfanin INCENSE BY KABODAUGHTER +2348032119803. Tarin Gift na turarukan da falaak ta kawo mata batayi niyyar budasu ba bare amfani dasu,amma bayan fitarta qamshin yaja hankalinta,koda ta duba dai taga kamfani daya ne da wanda birra ke mata using dashi,cikin karramawa ta sanya birra ta kwashesu ta musu gurin ajiya na musamman. Qamshin yana bata wani irin nutsuwa,yadda kuma yake dada kama kayanta da jikinta abun yana bata mamaki. Dama turaruka na gargajiya irin wannan suna da qamshi me tasiri har haka da kama jiki?.

Suna shirin fita falaak na shigowa

"Subhanallah" Ta fadi tana murmushi,kyan da akhnan din tayi yana ratsata,saita miqa hannu ta kama hannun akhnan din suka tako tare,hairaan a damanta falaak a hagunta,abinda ya kusa sanya qwalla fitowa daga idanun morsa safiyya kenan sannan suka fito ga farfajiyar dake a tsare da hadimai sahu sahu suna jiran isar akhnan din kebantaccen gurin da zaa gudanar da taron.

Sam a zuciyarta batason auren,bata gamsu dashi ba,bata kuma nutsu dashi ba,amma batasan meye Allah ya boye ba daya dauke mata wannan quncin zuciyar,ya sanyaya mata rai akan auren. Ko iya yadda taga 'ya'yan nata data mallaka duk duniya jere da juna,abinda bata taba ganin irinsa ba shi kadai ya isheta farincikin da har ta mutu wannan hoton bazai matsa daga idanunta ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 48*

Dab da zasu shiga sassan da zai kaisu parlor din dake manne da dakin gabatar da taron,wanda a nan ne zai zauna da cameras din da zasu dauke video dinsa sukutum da guda sukai qawataccen dakin taron dake kama da parlor na alfarma me girman gaske,daidai lokacin da suke fitowa sannu a hankali bisa takewar bayan hadimai masu yawan gaske.

A kanta ita daya idanunsa ya fara sauka,sai ya zaresu a hankali sanda suke basu baya kan hanyar isarsu ga hall din,ya maida dubansa a hankali kan maleek,amma sai mamaki ya darsar masa sanda ya dubi idanun maleek din kafe a kansu. A nutse ya dauke kansa daga maleek yana maidawa gabansu don saita gurin da maleek keta kalla haka,kai tsaye idanunsa suka sauka akan falaak wadda ke gefan akhnan din kaman yadda suka fito a daxu.

A mamakance ya maida dubansa kan maleek,still wannan basaraken murmushin yakeyi,sai ya motsa bakinsa a hankali,muryarsa can qasa ya furta.

"Ina kyautata zaton samun matar aure ne ya karkato da hankalina agadez......wani rabonne yaketa kirana,shi yasa na kasa nutsuwa sai dana zo gurinka" Ya qarasa maganan yana dauke dubansa daga kansu saboda sun bacewa ganinsa ya dawo da kallonsa kan haisam.

Shima haisam din shi yake kalla,yana mamakin yadda lokaci daya maleek din ya iya bayyana abinda ke ransa kai tsaye. Shi da maleek suna cikin mutum biyu a team dinsu dake da farinjini sama dana kowa kuma ake shakkar tunkararsu ace ana sonsu,amma har gwara maleek a kansa. Don maleek yakan tsaya ya saurari wadda yake ganin ta cancanci hakan na wasu kwanaki kafin ya gama karantarki,idan yaga tafiyar ba zata yuwu ba sai ya sallameki.

"Da gaske nake" Maleek ya furta cikin nutsuwa yana son jin abinda haisam zai fadi. Kasa cewa komai haisam din yayi,don da gaske yakejin kanshi yana sara masa,sai ya janye idanunsa daga cikin na maleek yana cewa.

"Booda haasofna(zamuyi magana wani lokaci)" Jinjina kai maleek yayi a nutse,bai sake takura masa da magana ba ya qyaleshi,don yanayinsa ya tabbatar masa da gaske baya jin dadin.

*AKHNAN*

Wani yanayi takeji na daban tattare da ita,wani sanyin jiki dama mutuwar jiki gaba daya,har zuwa sanda ta zauna muhallin da aka tanada wanda mammina ta shirya yi mata kamu bayan an gama lecture din.

Shuru ne gaba daya ya dauka a gurin lokacin da babban allon screen din da yaci bango guda na gurin ya fitar da hotonsa. Tsaye cikin tsaiwar dake nuna zallar kamalarsa da nutsuwarsa.

Murmushi me dan qaramin sautin wanda akhnan tana iya jinsa shine ya kubucewa falaak sanda idanunta suka sauka a kansa. A yau zata kalleshi son ranta,irin kallon da bata taba yi masa irinsa ba,Koda ya kasance ta cikin screen ne bawai ganin ido da ido ba.......yana da wani irin kwarjini da cika ido,tana jin ya mata wani girman da takejin nauyinsa har cikin jininta.

Cikin muryarnan tasa dake da nauyi da zurfin daya kutsa har tsakiyar zuciyar akhnan da batako daga idanunta ba tunda ta zauna yayi cikakkiyar sallama. Idanunta ta lumshe a hankali tana jin yadda sautin ya karade hall din,tamkar yana tsaye a gurin,da yadda muryoyin mutanen gurin ke amsa masa can qasa.

Tazarar wasu sakanni ya bada yana qoqarin hada taqaitaccen bayanin da zai gaya musu da yaren abzinawa daya soma koya......shurun daya kutsa can cikin zuciyar akhnan din,a hankali kuma ya soma tilastawa idanunta dubansa.

Fes ta zube idanun nata kan babban allon dake a gabanta. Ya bayyana tarwai har fiye ma da bayyanar da zaiyi a gabansu. Fararen kayan dake jikinsa gaba daya sune abu na farko da zai fara kashema me kallonsa idanu,wani irin kwantaccen kwarjini ne saman fuskarsa da tayi wani irin fresh da fatarsa dake glowing tamkar wani wanda ke shiga gyaran jiki duk wata.

Baqar sumar dake kumatunsa habarsa da qasan hancinsa ta sake fidda sirrintaccen kyan da Allah yayi masa. Uwa uba shemagh din dake kansa daya zauna masa kamar yadda matasan larabawa masu jini a jika kanyi.

Idanunsa da suka dan rusuna kadan saboda ciwon kan da yakeji kadan kadan sun sake zama wani ado me jan hankali a tattarre dashi,duk da rusunawan nasu kuma hakan bai rage hasken da suke dashi da kyansu ba.

Batasan sanda idanunta sunkai kan labbansa ba sanda ya fara sarrafa harshensa da yarensu na abzinawa ba. A nutse yake gabatar musu da kanshi gami da neman afuwa,gami da kuma gabatar da sunan omari a matsayin wanda zai jagoranci taron,sannan ya tura kujerarsa baya,hoton omar sanye da baqar jubah ya mamaye screen din.

A hankali ta zame idanunta ta maida qasa,tana jin wani shuru cikin qirjinta,shurun daya mamaye qirjin da sautin bugun zuciyarta da takeji har cikin kunnenta.

"Me yasa ko a screen ma yake min kwarjini?" Ta tambayi kanta tana jin wani haushinsa yana mamayarta. Ta tsani wannan kwarjinin......wannan kwarjinin dake tattare dashi tayi matuqar tsanarsa. Bai kamata ace yana da kwarjini har irin haka ba,baida mulki ko sarauta don me zaiyi kwarjini sosai?.....har ya zama wani abu dake ratsa tsakiyar izzarta?.

*HAISAM*

A hankali yake takawa shi kadai yana dawowa sassansa,can qasan zuciyarsa cike da mamakin yadda yakejin zuciyarsa wani iri cike da wani yanayi maras dadi da baisan me ya haifar dashi ba.

Shamagh din kansa ya zare a nutse yaa ajiyewa gefansa bayan ya nutse sosai cikin sofa yana relaxing bayansa jikin kujerar da yake zaune akai. Idanunsa ya lumshe,a hankali yana zuqar iska sosai yana fesarwa a hankali. Ya jima a haka kafin ya bude idonsa yana furta.

"Subhanallahil azeem" Sai ya miqe ya zauna sosai. Yanayin da yakeji a jikinsa da zuciyarsa wani irin yanayi ne da yakanji idan yana kewar wani abu,musamman ma nanay,wannan ya sanya ya yanke shawarar kiranta,ko wataqila zuciyar nanay din take muradi.

Dab da zata tsinke aka daga kiran,nutsatsiyar fuskar matar dake cike da kamala da nutsuwar da tunda ya tashi a rayuwarsa yasan nanay din da ita ta bayyana.

Murmushi sosai ya wadaci fuskarta da ganin gudan jinin nata,saidai a kallon farko kadai da yayi mata ta cikin siririn farin gilashin idanunta ya fuskanci wata qanqanuwar kwantacciyar damuwa a tattare da ita ba.

Wani irin mutum ne me baiwar kulawa da duk wanda yake rayuwa dashi. Yakan damu da damuwar wasunshi,ko yaya damuwa take a tattare da kai yana iya fahimta daga kallon farko,muddin ya kalli qwayar idanunka,musamman ma mutum me matuqar muhimmanci a gurinsa irin nanay din.

"Ina cikin maganarka a raina saiga kiranka ta hannun noorah". Ta fadi bayan ya gama gaidata cike da qauna da kuma kulawa cikin asalin harshen oromo me zubi da yaren fulani a Nigeria. Murmushin ya danyi kadan yana qoqarin danne harbawar da kanshi keyi.

" Me ya samu nanay dina yau?" Ya furta a tausashe idanunsa a kanta.

"Yau ta tuna ne da obboleetti abaayo" Siririyar muryar noorah ya shiga kunnensa.

"Noorahty" Ya kira sunanta a hankali,abinda ya sanya yarinyar matsowa kusa da camera tana murmushi.

"Captain obbo" Ta fadi tana murmushi gami da daga hannunta alamun saluting nasa. Maida mata shima yayi kafin ta soma gaidashi da yaren oromo.

"Kina kula da nanay kuwa nurahty?" Ya tambaya da salon kulawar nan tasa.

"Sosai......amma yau har qwalla nanay tayi,har hoton obboleetti abaayo ta dauko" Ta fadi qasa qasa tana saukan da camera din kan hoton.

Shuru yayi yana qurawa hoton idanu kamar yau ne karon farko daya soma ganinsa. Hoton sam ba baqonsa bane,tsahon shekarun da yayi wayo a duniya yake ganin hoton,amma yau daya sai yaga hoton ya zama sabo a idanunsa. Yau daya sai yake ganin kamar yasan fuskar dake cikin hoton.

"Noorahty" Ya sake kiranta a hankali

"Eeyyee obbo(na'am obbo)"

"Suuraa naannessaa(juya hoton nan)" Ya fadi hankalinsa yana sake kaiwa ga hoton.

Yadda ya buqata haka tayi masa. Cak ya dakatar da komai ya zubawa hoton ido yana kallonsa,duk sai wani jijiya ta jikinsa yaji kaman ta tsinke. Kamar yasan fuskar,sani kuma na kurkusa ba na nesa ba......kamar akwai inda yake ganin wannan fuskar lokaci bayan lokaci.

"Akhnan" Sunanta yazo ya tsaye masa a rai,abinda ya amsa kuwwa har cikin zuciya da kunnensa.

"Ina nanay?" Ya tambayi noorah. Sai data waiwaya ta kalli bayanta sannan ta bashi amsa.

"Gata nan ta fito daga toilet,alwala tayi" Kai ya gyada a hankali.

"Idan mun gama magana da ita ki dauki hoton da wayarta ki turamin,ki tambayeta idan da wani ma ki dauka duka ki hadomin".

"Me zakayi da hotunan obboleetti abaayo na?" Nanay ta tambayeshi tana karbar wayar daga hannun noorah.

"Ina buqatar labarinta nanay......inaso a wannan karon ki bani labarin abaayo" Dan qaramin murmushi ta saki tana gyada kai.

"Zan baka......amma ka biyoni bashi gobe.....yau din akwai.mutanen da zan rabawa tallafi,suna zauren jira suna jirana". Kai ya jinjina a hankali,ya qara da tambayarta motii.

"Ya shiga hidimar al'umma sosai kwana biyu,baya zama sosai,akwai qananun qauyukan da yaketa zuwa duba mutanensa" Dan shuru kadan haisam din yayi,ya sani koda ya hana motii yace ya sa ya wakili bazaiji ba,shi kuma a wannan qadamin da ake kai yana buqatar yawaitar zaman motii dinne guri daya maimakon zirga zirga,har yanzu bai amince da safety dinsu ba,duk da tarin jami'an tsaro harda na farin kaya dake tare dashi wanda shi kansa motii din wasuma baisan suna biye dashi ba.

"Allah ya tsare,a miqamin gaisuwa kafin na samu layinshi,Allah ya tsare"

"Allah yayi maka albarka duniya da lahira,ya tsareka daga dukkan sharri". Nanay ta fadi cikin jin soyayyar yaron nata. Baiwar haihuwa ta farko data samu,kuma ya zame mata baiwa ta gasken gaske.

"Idan na kira gobe zanyi magana da rumaisa da anani.....su zama a kusa"

"In sha Allah" Nanay din ta amsa cikin tsananin kulawa. Saboda yanayin aikin sai ya kasance shi daya ke kiya kiransu,ya tsara hakanne kuma saboda tsaro a garesu gaba daya.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

★Cikin wani irin salo gami da qwarewar da basu taba ganin irinta ba a yau karon farko yake gabatar da khudubar sallar juma'a a babban masallacin agadez me tsohon tarihi.

Kyakkyawan matashin me zubi da kamanni da BUZAYE kuma ba'anzine SAK!. Wanda ke sanye da cloak robe me daukan hankali fara tas da kuma ratsin adon zaiba,kamar yadda yayi amfani da kuwaiti thobe(jallabiyya zubin saqa da adon qasar Kuwait) fara qal itama me wani irin sulbi da daukan hankali,hakanan shill shamagh din dake kansa dan asalin qasar Kuwait daya yafashi saman kyakkaywar maroccon cap din dake kansa ya sake qarawa fuskarsa wani irin kwarjini na daban.

Readers Also Read

More by Huguma