L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 35
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 35: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 35. *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
3,316 words
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 60*
*MORSA SAFIYYA*
Duk da cewa wani sashe na zuciyarta yana riqe da lissafin daga yanzu zuwa kowanne lokaci akhnan tana iya qaura tana iya barin gidan zuwa gidan mijin da har yanzu batasan wani mutum guda daya daya jibancesu da zai iya shaida fuskarsa ba........amma tana jin wani irin sassauci daga damuwarta data fara shiga a farkon maganar.
Batasan me ya kawo sassaucin ba......batasan hujja ko dalili ba,saidai tana kyautata zaton ADDU'O'IN da take shafe dare tana yi ne. Babu wani dare da zai keto sararin subhana ta kwanta tayi bacci ta kuma qarar dashi tas ba tare data tsaida duga duganta gaban mahaliccinta ba.
Tana saman dining hadimarta samiya tana shirya mata abincin rana,wanda bata samu zama ta cishi ba saboda sallamar baqi dake gabanta da suka samu halartar biki. Duk da bikin ba'a cikashi da kalolin bidi'a ba,amma kuma ahalin diory hamani sun nuna kara,sun kuma nuna zallar zumuntar data kasance abu mafi girma da qarfi a tsakaninsu.
A nutse ta amsa sallamar armelle da wannan kamilar fuskartata ma'abocin tarbar dukkan wanda yazo gareta da girmamawa.
"Qaraso mana armelle" Ta fada tana yin bismillah hadi da soma kai lomar abincin bakinta. Kamar yadda ta buqata haka armelle din ta qaraso,ta samu daya daga cikin kujerun dake nesa kadan da morsa safiyya din ta zauna akai. Wani abu dake bawa kusan kowa mamaki,tana da wani irin sauqin kai.....bata da izzar da zaka kiranta matar babban mutum me daraja ta daya a yankin wato sultane of agadez. Ta dauki hadimanta a matsayin nata,hadimanta wasu mutane ne da take ganin kimarsu sosai,girmamawa da mutuntawa take musu kamar yadda zata karrama kowanne dan adam.
"Lafiya dai ko armelle?"Morsa ta tambayeta tana tattara hankalinta a kanta. Dub daya ta yiwa morsa safiyyan,ta kalli abincin kuma dake ajiye a gabanta,sai wani irin tausayinta ya kamata. Ta sani ta dauki darare da kwanaki masu yawa bata zauna ta sanya abinci haka a cikinta ba,ta tabbatar a yanzu idan har ta isar mata da saqon da take dauke dashi to ba shakka wannan abincin ya haramta a tare da ita. Murmushi ta sakar mata.
"Ba komai....wata maganace nakeso muyi,amma da fari uwargijiyata ki kammala cin abincinki,don na tabbatar kin jima baki zauna haka don kawai kici abinci ba" Dan qaramin murmushi morsa safiyya ta saki,murmushin da ya narkar da zuciyar armelle gaba daya. Murmushinan dake dauke da tarin alkhairi.....murmushin nan dake qunshe da kyautatawa,murmushin kuma da ya sake bayyana kamanninta da SAFEENA SOSAI.
Safeenar da babu wata zuciya me alkhairi da zata iya mancewa da ita....safeenan da komai butulcinka cikin gidan baka isa kace bakaci arziqinta ba.....safeenar da aka tilastawa zukata masu yawan gaske lullube sunanta....danne ambaton alkhairinta.....tunata,ambatarta,dama ambatar dukkan abinda ya shafeta,saidai ita zuciyar da alkhairi ya cikata......zai wahala wani abu ya danne ganin alkhairin waninta.
Hawaye taji sun cika mata idanu sanda morsa safiyya ke cewa.
"Yau lelena akeyi armelle,shikenan bari nayi na kammala saimu zauna" Saita maida kai sosai tana qara hanzarin cin abincin,tasan kuma tayi hakanne kawai don ta saurareta,abinda ya saukar da wani abu me nauyi saman zuciyar armelle wanda ta kasa daureshi,har sai da tayi qasa da kanta tana boye hawayenta.
"Na kammala armelle.....amma koma meye abinda ke tafe dake da alama yana da girma" Morsa ta furta cikin nuna kulawarta ga armelle din.
Idanunta da suka sauya launi kadan ta daga,ta kuma kalli morsa dashi.
"Yana da girma uwar gijiyata,don na jima banga ko banji abu me girma kamar wannan ba....." Kai ta gyada ta kasa cewa komai tana ci gaba da kallonta.
"Ko.meye zaki jishi daga bakina ina me roqarki ki karbeshi da sauqi ta sigar yadda zai sauka a zuciyarki.....amma ki tashi da dukkan zafinki wajen ganin komai bai sake maimaita kanshi ba"
"In sha Allah armelle.....in sha Allah" Ta fada cikin mutuntawa da dattako,don armelle din na cikin tsaffin hadiman gidan dake da wani irin girma na musamman.
"Auren akhnan ya mutu awa daya data wuce,mijin daya aureta ya saketa har saki uku" Wani irin abu me nauyin gaske morsa safiyya taji yana sauko mata. Banda armelle ce ga fada....banda ba wasa a tsakaninsu,banda kuma kuma ita din ba abokiyar wasanta bace bata yadda za'ayi maganan ya shiga kunnenta ya samu mazauni a zuciyarta,duk da haka sai data rutsa armelle da kallo kamar me kokwanto,kafin yanayin armelle din ya gasgata mata abinda ta fada din shine dai kwance kuma rubuce cikin idanunta.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine abinda morsa safiyya ta maimaita har sau uku,tana sanya hannuwanta gami da dafe kanta.
*MAMMINA*
Tun a cikin motar tafisu ke zaune gaban mammina,tana kuma shafa mata man zafi a qafarta data fara kumbura kadan. Saidai sam ciwon da takeji a cikin qafafunta baikai koda quarter din wanda takeji a jikinta da zuciyarta ba. Ta kammala sanya mata maganin ta maidashi jikin wani abu dake maqale jikin kujerun dake a gabansu,ta daga idanunta tana duban mammina din.
"Ta ina zamu fara gyara da fuskantar wannan matsalar?" Mammina tayi maganan kai tsaye ba tare data dubi tafisu ba. Numfashi ta sauke tana murza yatsunta,fuskarta da dukka yanayinta yana nuna itadin cikakkiyar baqar ba'abzina ce.
"Meye hasashenki uwar gijiyata,kada na miki azarbabi......amma banajin dama ya kamata mubar wannan ranar ta wuce ba tare da hasashen komai da zai iya faruwa ba da yadda zamu tunkareshi ba. Kai mammina ta jinjina,sannan tace.
"Da farko ban yanke zuwa gurin akhnan da wuri ba,domin hakan zai sanya zargi da dama a zukatan wadanda ke farautar motsina". Shuru kadan tafisu tayi sannan ta amsa mata.
" Zuwanki da wuri.yana da ma'ana da alfanu,kamar yadda jinkirin zuwanki shima zai zama yana da nasa alfanun,amma a wannan gabar na bar miki dukkan zabi". Idanu mammina ta sauke a kan tafisu.
"Dukka wannan ba wani damuwa bace me girma a guna,koda akhnan taga kyautatawar zuwana da wuri ko bata gani ba.....abi mafi girman damuwa a gurina shine sultane.......banaso na rasa YARDA daga gurin sultane.... Lokacin rasa yardata a tare dashi baiyi ba.....har yanzu akwai GABAR da ban isa gareta ba,muddin na rasa yarda da aminci daga sultane na rasa rabin shiri na,zai zabtare ne ya zube ya barni da tarin burikana......ta wacce hanya zan amintar da sultane tafisu?.....ta wacce hanya ce zanyi abinda zai sake karkatar da hankalin sultane zuwa gareni?,na kuma sake samun yardarsa da aminci?"
"Ta hanyar amintaccensa ranki ya dade" Tafisu ta furta tana qanqantar dakai cikin girmamawa. Duban tafisu kawai takeyi cikin rashin fahimta kafin ta iya buda baki ta tambayeta.
"Me kike nufi tafisu?". Murmushi ta saki sannan ta dubi mammina.
"Qwaqwalwarki tafi tawa aiki nesa ba kusa a dukka shekarun da muka kwashe,amma bansan me yasa a yanzu komai nake yake sanyi sanyi ba......kinfi kowa sanin WAYE sultane wajen miqa soyayya da yarda gami da aminci ga duk wanda ya zaba da mallakawa hakan......kana sake samun aminci ne daga dan adam ta hanyar abinda ya amincewa......a yanzu ba wata hanya da zaki hana yaduwar labarin mutuwar auren akhnan......ba wata hanya da zaki hana rade radin isa ga kunnuwan sultane......amma ki tabbatar ke kika fara sanar masa.....kika hada masa kuma da mafitar komai,kinsan hikimar haka?" Kai mammina ta girgiza.
"Ban fahimta ba tafisu,mafita kuma ta ina?,maida auren almaz da akhnan dai kinsan abune daya haramta.....za'a shaidawa sultane haka,ko ba ta bakin kowa ba saita bakin malaman dake zagaye dashi,malaman ma irinsu wancan SHEIKH din days mallakawa dukkan yardarsa" Murmushi sosai me kama da dariya tafisu ta saki kafin ta dago ta kalli mammina.
"A idanun sultane din ke wankakkkiya ce......don bashi da wata masaniya ta kusa kota nesa akan cewa kece kika zabarwa akhnan miji.........zaki bayyana masa illar zaben da ya bari akhnan ta yiwa kanta na miji,zaki kuma kafa hujja da qoqarin da kika nuna na lallai yayi bincike akan almaz kafin daura auren......a nan kuma kin sake samun wata daman ta TARWATSA dukkan wani yarda kusanci da aminci da wancan SHEIKH din ya samu daga gareshi....nasan zaki tambayi ta wacce hanya ko?" Kai mammina ta jinjina da sauri,tana jin kamar tafisu na buda mata falle fallen littafi sosai a gabanta.
"Zakiyi ruwa da tsaki ta yadda sultane zai AURAWA akhnan malamin....." Wani abu mammina taji ya saukar mata kamar ana fusgarta,ta qanqance idanunta sosai tana duban tafisu.
"Kina hayyacinki kuwa tafisu?,ta yaya kike tsammanin akhnan zata auri malami?" Dariya kadan tafisu ta saki.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"A yanzu MAFITA ake nema.....ba yarda aminci ko gamsuwar akhnan nan ba.....duka daga baya zamuji da wannan" Ta fadi tana taqaitawa. Dubu bisa dubu mammina ta yarda da tafisu,tasha bata mafita da shawarwari kuma ko daya ba wanda ta taba faduwa a kansa.
"Ina jinki" Wannan tunanin ya sanya ta bawa tafisu daman ci gaba da magana.
"Zaku nunawa sultane a yanzu akhnan ta kawo zabinta,zabinta dinnan kuma bai haifar da d'a me ido ba,saboda haka ba wanda ya cancanci ma sultane ya sake bawa akhnan din sai amintaccensa wato malamin nan.....kinga a nan zaki sake haske a idanun sultane......zaki sake fari a idanunsa,kimarki zata dagu fiye da yadda kike tunani". Sosai mammina ke gyada kanta tana jin gamsuwa da gabar farko na bayanan tafisu.
"Gaba ta biyu kuma wannan wani sirrintaccen aiki ne.....kinsan ba wanda yakai malama dake zaune basa aikin komai sai karantaswa son banza?"
"Qwarai kuwa" Mammina ta amsawa tafisu kai tsaye saboda tuna wani yanki na rayuwarta na baya,mijinta na farko a rayuwarta. Kai tafisu ta jinjina.
"Wannan shine dalilin da ya sanya nace miki ki zabeshi a matsayin wanda zai auri AKHNAN.......bisa sharadai da tarin dukiya me yawan gaske da zaki alqawarta masa,ki fara mallaka masa wata,idan ya cika watannin da zai saki akhnan ya saketa.......ki cika masa dukiyarsa ki sallameshi......a nan kin samu mafita biyu" Dubanta kawai mammina keyi har yanxu tanason jin qarshen bayanan tafisu.
"Mafitar farko kin samu hanyar da zaki maidawa almaz akhnan.....wannan idan lokaci yayi xakiji yadda zamu maida hakan ta yiwu cikin sauqi.....na biyu kuma kin lalata alaqar dake tsakanin sultane da shiekhh. Har abada sultane bazai sake ganin farin mutumin daya saki diyarsa ba.....har abada kuma bazai sake bada dama ga mutumin daya saki diyarsa ba ya sake zama makusancinsa ba kuma amininsa."
Kai kawai mammina ke jinjinawa,tana kuma jin aminci da yarda da dukka maganganun tafisu. Sai takejin kamar kowacce matsalatata tazo qarshe,saidai kuma can qasan xuciyarta da ruhinta tana jin wani irin qyashi na bawa haisam din damar maza mijin akhnan koda MIJIN WASA ne......tana jin qyashi bashi damar amsa wannan sunan koda na AWA DAYA NE TAL,mutumin da ya fara daga yatsa ga umarninta?,mutumin da ya samu wani irin kusanci da bata taba ganin wani ya sameshi ba a wajen sultane......bama sultane kadai ba,a dukka fadin masarautar. Ranar data zauna tayi nazarin kalar girmamawar da take ganin dukkan wani hadimi da bawa yake bawa haisam din sai da abun ya ratsata ainun. Kalar wani girma ne da har ya zarta wanda ake bata,duk da tarin izzarta da kuma isarta. Wani girma ne daya kusa daidai da wanda suke bawa sultane,ta kuma rasa wanda zai bata amsar DALILIN da yasa suke basa wannan girman daga dukkan hadiman data tara. Abu daya data lura dashi,yana da wani irin KWARJINI da ita kanta yakan doketa a duk sanda zasuyi gaba da gaba dashi,tasha tunanin ba ordinary sheikh bane.....amma a yanzun ta fara shiga kokwanto,don ta gaza gano komai daya kebanceshi da zai bata hujja a kansa.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 61*
Ba wannan ba gaba daya....,can wani sashe na zuciyarta ke tuna mata WAYESHI?. Da kalar wannan izzar da kusancin da yakeji ya samu zaya yarda da sharuddanta?. Tambayar data jefawa tafisu kenan.
"Yana da wata irin izza da girman kai na banza tunda ba kowan kowa bane.....ina hangen wani irin taurin kai a tattare dashi tafisu.....ina ganin koda zai amince bazai yarda ya karba sharuddana da auren ta cikin sauqi ba". Wani murmushi dake gayawa mammina tafisu tana da kowacce mafita ta matsala da zata tunkarosu ta saki.
"Ba wanda yafi qarfin barazana da takan iya juyewa ta zama gaske.....indai ba daga sama ya fado ba ai yana da ahali.....idan baida mahaifiya yana da mahaifi,idan duka babu akwai makusanta......ki tabbatar masa da daukan rayuwarsu daya bayan daya har sai sanda ya aminta da sharudanki,ruwansa ya karbi ladansa ruwansa kada ya karba". Ta fada hankali kwance.
Kai mammina ta girgiza
"Banajin barazana zata juya wannan.....amma a maganganunki na tanadi hanyoyi biyu da zan sashi karbar buqatata ta ruwan sanyi" Ta furta tana sakin qaramin murmushi.
"Ki samomin qaramin malami,ina buqatar wasu ayoyi da hadisai da zan riqe koda qananu ne"
"An gama" Tafisu ta amsa tana rusunar da kanta.
*MORSA SAFIYYA*
Ta jima tana maimaita innalillahi din,har zuwa sanda taji wata nutsuwa ta soma saukar mata a zuciyarta a hankali.
"Rakani armelle......inaso na ganta" Ta fadi tana miqewa daga kan kujerar,tana kuma jin jiri kamar zai kayar da ita.
Tafiya kawai takeyi amma tana jin kamar tana taka qasa ba daidai ba. Takawa take da wani irin yanayin da takeji kamar iskar daminar dake kadawa zata kayar da ita
Qirjinta da zuciyarta a quntace,idanunta suna dauko mata shekarun baya. Sanda safeena ta amsa sunan BAZAWARA a qasa da shekara daya tal da aure.....bata fata hakan ta kasance akan akhnan,bata fata itama wannan sunan ya bita,duk da cewa ta sani basu riga da sunkaita gidanta ba,amma bata da tabbacin dukkan abinda ya faru a bayan idanunta.
Da idanunta take hangen tsaiwar jama'a biyu uku daga taku xuwa wani takun nata. Mafi yawancinsu mata ne,kuma a take jikinta ya fara gaya mata suna tattaunawa ne kan al'amarin,tabbacin magana ya fara yaduwa kenan,abinda ya sake quntata qirjinta.
*AKHNAN*
Duhun da dakin yake dashi a yanayin yafi mata komai dadi,tanajin kamar ta tserewa duk wani kallo na tuhuma ko tozartarci da zata iya fuskanta.
A wani irin soye takejin zuciyarta da wani irin yanayi da ba zata tantance wanne iri bane. Abu daya da takejin yana zagayawa a jikinta da zuciyarta gaba daya shine TOZARCI da QASQANCIN da almaz ga ajiye mata cikin tarihin rayuwarta,wani irin mummunan tarihi data tabbatar har a gama sarauta a agadez ba za'a manta da ita ba.
Wannan shine ABINDA TAKE GUDU shine abinda ya sanya taketa gudun wuce sa'a tsakaninta da kalmar AURE. Ta sani cewa,ba komai a cikinsa sai tarin bin umarni da barin dukkan wani da zuciya keso ko muradi ko kuma buri,dukka don kawai ka cika muradin NAMIJI. Mammina da sultane tana iya kiransu da cewa SUNE SILA......duk da ta fannin sultane tana masa uzuri da cewa ZIGA ce da qoqarin shiga tsakaninsu da akeyi tun can can.
Amma ta fuskar mammina fa?......makancewa tayi?,tunaninta ya gushe ne data dauko makakke mashayi ta damqa ragamar igiyar aurenta a hannunsa?.
Me yasa mammina bata qure duba cancanta ba?,me yasa bata zagaye kusan rabin duniya ba saboda ita?....me yasa?.....me yahau kanta ta zabo mata mutumin daya munana kyakkyawan tarihinta?.
A hankali morsa safiyya ta murda qofar dakin tana shigowa idanunta zube akan akhnan din. Kallon kusan sakanni talatin tayi mata sannan ta saki qofar tana takowa a hankali zuwa inda akhnan din ke zaune.
Fuskarta tayi wani fayau a iya awannin kawai.....wannan blue eyes din sun rune da surkin jaja jaja a cikinsu. Kusa da window take zaune,saidai ba dukkanin fuskarta bane ke kallon window din. Sosai morsa safiyya ke hangen wani irin yanayi tattare da akhnan din,yanayin data tabbatar UWA ce kawai zata iya hangensa akan d'iyarta. A firgice take gaba dayanta,saidau rashin sanin makomar rayuwarta da abinda ke mata ciwo da zafi........abubuwan da suka cancanta da rayuwarta gaba daya ya sanya bata fahimci komai ba,ta yanke kebe kanta a matsayin wani hukunci daya dace da ita. Tana iya hangen yanayin cikin idanun akhnan din,kamar an qara mata shekaru tsakanin kwanaki ukun da aka daura mata aure. Ta sake zama wata mutual data tabbatar girman igiyar data yanke cikin kwanaki uku ne ya haifar da hakan.
Har cikin jikinta taji shigowar morsa safiyyan,saidai zuciyarta na gaya mata ne.....ta shigo taga fitar hawaye ne daga idanunta?....kota shigo ta nuna farincikinta na mummunan abinda ya sameta?.....ko ta shigo ta bayyana mata cewa ta samu nasara a dukka shirinta.
Yanayin akhnan bai hana morsa safiyya kusanta kanta da ita ba,daga can qasan zuciyarta takejin wani irin rauni,yanayin yana daukota mata hoton safeena sak a irin wadancan shekarun tun kafin samuwar akhnan din.
Bata dakata ba har sai data isa dab da akhnan din,a nutse ta zauna saman kujerar dake fuskarta ta,kujeru qwara biyun da aka ajiyesu kawai a gurin me dauke da qaramin table a tsakiya.
"Ba buqatar ki tambayeni komai......labari nasan ya riskeki,ba sai kin taso ganin hawaye a idanuna ba kafin ki samu tabbaci.....da gaske ya sakeni,ya sakeni saki uku.....shikenan dukkan wani fata da buri sun gama cika?" Akhnan ta fada da wata murya me nauyi,wanda duk daga harshen da zatayi wani irin d'aci takeji yana sauka saman harshen nata.
Mamaki sosai ya saukarwa morsa safiyya,saidai har yanzu tana jin cewa ita din UWA ce......a yanzu ne kuma takejin lokaci yayi da zata kusantar da kanta da rayuwar akhnan din,wannan zargin da wannan zaton da take mata tana jin ya kamata ta maidashi reality.....abu d'aya daya rage tayi,koda zata zargeta......koda zata tuhumeta nan gaba ko bayan babu ranta zatasan bata da wata UWA a duniya bayan ita.
"Ba wata uwa dake burin ganin ibtila'i cikin rayuwar d'iyarta........sau da dama fuskokin dake murmushi a garemu ba sune asalin fuskokin masoyanmu ba......hannuwan dake miqo kansu garemu,ba sune hannayen daya cancanci mu kama mu riqe don samun kubuta da tsira ba,wani lokaci suke fincikarmu zuwa ga shiga kowacce matsala da muke tsintar kanmu a ciki.......na samu amsar tambayar farko daga gareki" Morsa ta fadi da wani irin yanayi da akhnan din bata taba jin morsa safiyya din tayi magana dashi ba.
Bata sake cewa komai ba,taci gaba da kallon akhnan din tana karantar wasu halaye da akayi mata horo dasu. Tana daukan nesanta kai a matsayin AMINCI,shi yasa koda wanne lokaci take zabar nesanta kanta da kowa da komai idan tashin hankali ya sameta.....saidai ba haka siddan aka koya mata hakan ba,an koya mata hakanne saboda ta zama me karbar kowacce shawara idan aka kusanceta da shawarar.......ta zama me ragaggun hanyoyin samawa kanta da zabawa kanta abubuwan da suka dace.
"Zanyi nesa dake,don na samu tabbacin bai taba lafiyarki ba.....to alhamdulillah.....amma hakan ba yana nufin zanyi nesa da rayuwarki ba,zan zama maras abun cewa akan abinda ya shafi rayuwarki......sam sam.....tun kina qaramarki akwai wani SHAMAKI da aka sanya tsakanina dake......akwai wanda yake kururuta samuwar TSORO cikin kunnuwanki.......akwai wanda ya koya miki ganin ABOKAN GABA DA ADAWA a inda sam sam babu su........a wannan lokacin zan kasance tare dake koda ban zauna kusa dake ba......zan kasance me ruwa da tsaki gurin yanke hukunci akan RAYUWARKI ta gaba.....koda hakan yaha nufin ba zaki sake kallona a matsayin QANWAR SAFEENA ba har abada......ban damu ba muddin zan bawa jinin safeena qwaya daya tal daya rage kariya.....banzo don na zauna nayita tambayarki ba......don iya abinda nakeji game da sakinki na tabbatar KARIYA ce ubangiji ya baki,duk da ke a wajenki zai miki kama da MASIFA da TASHIN HANKALI.....tambayata guda daya ce......kun hada jiki dashi ko baku hada ba?" Morsa ta yiwa akhnan tambayar kai tsaye tana tsareta da wani irin zazzafan kallo.