L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 36
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 36: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 36. Da sauri ta daga kanta zuwa ga morsa safiyya,zuciyarta…
3,371 words
Da sauri ta daga kanta zuwa ga morsa safiyya,zuciyarta na tafasa tana amsar duk wata magana data fita a bakinta tana farfasata,ba abinda zuciyarta ke gaya mata illa mammina take toxartawa da kalamanta. A qasan ranta karon farko tunda ta zauna a gurin tana jin wani zafin mammina ne a ranta akan zaben data mata,tana jin a wannan karon tana da tarin tambayoyin da zata yiwa mammina akan mijin data zaba mata......amma batasan me yasa takejin zafi da baqar magana ko baqar kalma guda daya da aka gaya mata ba.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Ta daga kai ne da niyyar tsare morsa safiyya da kallon da zai sanya ta fahimci ita din ba kowa bace da zata tasata a gaba da wannan tambayar,ba huruminta bane wannan bata da wannan ikon,amma kuma a yau a karon farko kallon dake cikin idanun morsa safiyya din wasu iri ne......wani kallo ne na daban daya sanyata dole ta juyar da fuskarta gefe tana jin wani abu me kama da tsananin nauyi yana sauka a idanunta da zuciyarta,tana kuma jin girman tambayar da nauyinta.
Siririn numfashi kawai morsa safiyya ta sauke,koda akwai rashin kunya da izza a idanun akhnan,amma ta gama samun amsar ba abinda ya hadata da almaz.
"Alhamdulillah" Ta furta a hankali tana miqewa. Hamdalar ta sake jawo hankalin akhnan din,me take nufi matar?,tana murna kenan da abinda ya sameta?. Me yasa wai ba zata canza ba?,me yasa ma take kiran kanta a matsayin qanwar mahaifiyarta?,bayan tana maraba da duk wani bala'i da zai sameta?.
Har cikin zuciyarta takejin wata nutsuwa tana saukar mata,duk wani tashin hankalinta akan auren yana sake gushewa,tana sake gasgata girman ubangiji da buwayarsa,komai zaiyi akwai hikimarsa a ciki amma ga ma'abota hankali.
*MAMMINA*
Sai data koma sassanta ta sauya shigar jikinta sannan ta nufi sassan akhnan. Sassan da tana sanya qafarta zata shiga morsa safiyya na fitowa da tata,saita samu kanta da wani irin faduwar gaba.
Bin juna sukayi da kallon kallo,zuciyar mammina cike da fargaba da shakku gami da tarin tambayoyin me yakai.morsa safiyya din sashen akhnan haka da wurwuri daga faruwar abun? Kada Allah ya bawa akhnan damar furta komai ga morsa safiyya din,duk da tana da yaqini,tasan abune me wahalar gaske wata magana ta shaquwa ko fahimtar juna ta shiga tsakaninsu. Ta dade da kashe wannan feeling din a tsakaninsu,ta dade da cusawa akhnan ra'ayi da hali na tsananin qyamar morsa safiyya da kuma sanyata a sahun farko na maqiyanta. To amma a yanzu bata da tabbas akan kowa da komai,har saita saita komai yadda takeso yaci gaba da kasancewa.
Sassanyan murmushi morsa safiyya ta saukewa mammina sannan a hankali ta dauke kanta tana fita a gurin cikin cikakkiyar nutsuwar nan tata data jima tana huda zuciyar mammina din..
Raga raga murmushin yayi da zuciyar mammina......ya sake ajiye wata qatuwar fargaba da kuma rashin tabbas a cikin zuciyarta,wannan ya qara mata qaimin sanya kai zuwa sassan akhnan da sassarfa.
Fitar morsa safiyya ta barta da wani irin tunani me zurfin gaske a kanta,tunanin da baiyi zurfi ba taji muryar mammina tana qwala mata kira da wannan muryar da kowanne lokaci take nuna zallar tashin hankali akan dukkan wani mummunan abu da zai sameta.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 62*
Idanunta ta lumshe kawai ba tare data waiwaya ba,idanunta ta lumshe kawai tana ci gaba da sauraron muryar mammina din maimakon ta tashi ta fada jikinta kamar yadda ta saba a dukkan wani abu da zai sameta.
Haka kawai yau bata jin saukar muryar saman zuciyarta,a yau din bata jin sautin da yanayin yana ratsa zuciyarta yadda ta saba jinsa.
Sak mammina tayi tana duban akhnan dake zaune kawai,ba wani alamun motsawa ko xuwa gareta kamar yadda ta saba a duk yanayi ko lokaci makamancin wannan.
Gabanta ya fadi,shakkarta da kokwantonta suka dadu,amma sai tayi saurin canza yanayinta da sake takowa gaban akhnan din da sassarfa tana fadin.
"Na shiga uku ni zaituna.......biftu,ya taba lafiyarki ne?" Ta qarasa maganan tana zubewa gaban akhnan,gami da sanya hannunta tana dudduba jikinta kamar me neman wani abu.
"Kiyimin magana mana biftu......na rantse da ubangiji dake busa mana numfashi bazan barshi ba".
" Zaki masa mene?,zaki iya goge abinda ya faru ne?,ko don bai bar tabo a jikina ba hakan yana nufin tabon dake zuciyata ma zai goge ne ko zai warke?,har abada" Akhnan ta amsa mata da wata irin dakakkiyar murya. Sosai mamaki ya tsarga a zuciyar mammina.......wanne irin magana akhnan din takeyi haka?,me takeson fadi?,anya safiyya batayi amfani da wata hanyar ba ta soma gotarwa da akhnan tunani?.
"Kuskurenki ne tun farko.....kuskurenki ne mammina.....kinyimin alqawarin zaki fiddani......amma kuma sai kika sake dilmiya ni cikin wata sabuwar matsalar.....mafi munin matsalar ma da gwara bijirewa maganan sultane da umarninsa akan wannan KARYAMIN DARAJAR da kikayi" Tayi maganar karon farko hawaye na taruwa cikin idanunta,duk da batajin zata bari hawaye ko daya ya zuba daga idanunta wai don aurenta ya mutu,koda zatayi kuka ma,zatayi kuka ne kawai saboda tabuwar DARAJARTA da kuma MARTABARTA.
"Me kikasha akhnan?.....baki da hankali ne?.....ni kikr tuhuma da jefa rayuwarki a wani yanayi bayan dukkan sadaukarwar da nayi?" Ta fadi da wani mugun hargagi da bata taba mata irinsa ba.
Da wani irin kallo kawai takebin mammina,tsawarta tana sauka saman zuciyarta da wani irin yanayi,saboda wani abune baqo kuma sabo da bai taba faruwa tsakaninsu ba.
"Ba komai biftu,na gode na gode" Mammina ta furta tana qoqarin dauke hawayen daya soma zarto mata daga ramin idanunta.
Har Tsakiyar kanta takejin fitar hawayen,a tsahon shekarun rayuwarta ashirin da hudu bata taba ganin duk girman tsanani mammina ta fidda hawaye ko sau daya ba,sai yau?,kuma a kanta?.
BAKI KYAUTA BA taji sautin yana sauka saman zuciyarta. A hankali ta dauke kanta gefe,muryarta dauke da izzarnan dake sake tsananta tsanarta a zuciyar mammina tayi magana.
"Bazanyi magana dake ba MAMMINA.....ina roqonki ki tafi daga nan". Idanu ta zuba mata sosai,tana jin wani abu yana taso mata. Ita kadai tasan me takeji akan yarinyar.......ita kadai tasan adadin kaiwa bango da tayi.
Ba shekara daya ko biyu ba,ta jima tana sanyata hidimta mata bawai kai tsaye ba.......ta jima tana bata umarni masu tarin yawa,kafin ita ta samu daman maidata qasa ta koma karbar umarninta.
"Zan tafi......amma hakan bai yana nufin xan kasa yin abinda ya dace ba a matsayina na uwa.....ko yau she xanbar miki qofata a bude,duk sanda kika buqaceni ina nan ina jiranki" Maganar mammina ta qarshe kenan ta juya tana fita da wani irin yanayi dake nuna sanyin jikinta.
*MORSA SAFIYYA*
Wani irin shuru ne ya ratsa dakin,ba a abinda ke motsi banda bugun zukatansu dake cike da wani irin nauyi. A zaune suke suna fuskantar juna ita da hairaan,gwiwoyinsu suna gugar juna,hannuwan morsa safiyya din dukka cikin na hairaan data kama ta riqe sosai tana matsasu a hankali don samarwa da morsa safiyya nutsuwa,wadda bugun zuciyarta da numfashinta suke fita wani iri.
"Ki shaqi iska sosai momma......ki fitar ta bakinki don Allah" Hairaan ta fadi cikin tashin hankali. Yanayin da take ganin morsa safiyya din a ciki yafi daga mata hankali fiye da labarin mutuwar auren akhnan din da take sanar mata a yanzu.
Murmushi kadan morsa safiyya ta saki cike da wannan qarfin halin nata,idanunta akan hairaan.
"Kina tunanin na rude da yawa ko zan rasa hayyacina?...." Saita girgiza kai.
"Ni da naga mutuwar safeena tsakanin cinyoyina hairaan,naga mutuwar mahaifinki,bacewar ahmad a sanda nafi tsananin buqatarsa,bana tunanin akwai wani abu da yayi saura wanda zai bugani sama da buguwar da nayi a wancan lokacin. Tabbas inajin radadi,inajin tsananin baqinciki da kalar rayuwar da aka shiryawa akhnan take kuma yinta,wannan rayuwar a yanzu ba qaddararta bace.....rubuta mata ita akayi,a wannan karon kuma sai inda qarfina ya qare,koda zan rasa numfashina.....koda zata batar dani kamar yadda tayi mana a faro a Ethiopia. Barazanarta tazo qarshe hairaan.....ku shirya RASANI daga yanxu zuwa kowanne lokaci.....na yarda da amince zan narkar da rayuwata saboda safeena,saboda biftu ". Sosai zuciyar hairaan ta karye,wani irin abu takeji cikin jikinta yana ratsata da yafi girman tashin hankali.
"Ki daina fadar haka momma.... Muna tare dake......tare zamu kawo sauyi wa rayuwar akhnan.....ba kuma tare da komai ya sameki ba.....gyara za'ayi kawai,ba batu ne na rasa rayuka ko salwantar wani abuba" Wani murmushi momma ta saki tana duban hairaan din.
"Hairaan.....kece aminiya guda daya da nake magana da sirri dake.....kinsan komai ba abinda yake boye gaba gareki,amma har yanzu bakisan girman SHARRI da KAIDIN MAMMINA BA......bakisan wace zaituna ba....sannan bakisan wace zeenatu ba.....a kaf tarihinta ni kadaice na tsaye mata a gaba ta kasa bi ta kaina......nasan Allah ne yayimin da girman addu'a. Har yanzu tun bayan shekaru talatin da suka shude baya ban qara kwanciya nayi bacci ba irin na kowa da kowa hairaan,bacci na gaske dama bacci na ma'ana......inda ace nayi hakan da ban haifeki ba,da ban haifi falaak ba,koda tsananin rabo ya sanya na haifeku da a yanzu ba maganata akeyi a nan ba......ba komai falaak zata iya daukewa ba,shi yasa na aiketa kitchen ta kawo madara......amma ke din mun saba binnewa da rufewa dake....."
".....za kuma muci gaba tare momma.......wanne mataki ne kike ganin zai zama na farko don tseratar da rayuwar biftu".
Shuru kadan morsa safiyya tayi,wani abune daya jima yana mata yawo cikin kanta,wani al'amari ne da takejin kamar ana tilasta mata.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Hairaan" Ta kirata a hankali sanda falaak ta buda qofar dakin ba tare da dukkaninsu sun sani ba,saboda wani kalan qofa ne da baya bada alamu na an budeshi. Tana sane ta dakata daga bakin qofar,don tunda momma ta aiketa kitchen tasan cewa korarta kawai tayi,akwai abinda bataso taji,yanayin momma din da sakin bazatan da mijin biftunta ya yiwa biftu din ta tabbatar wani abu ne da dole zai gigitata fiye da zatonsu.
"Na dade a zuciyata inajin cewa sun dace da juna......haka kawai idan na kalleshi sai na dinga jin kamar D'ANA.....idan na ganshi hairaan sai na dinga ganin AMINCI kawai a tare dashi. Kusancin da sultane ya bashi cikin rayuwarsa da sarautarsa.......na tabbatar bayan K'AUNA da yake masa.....akwai wani abu da bai furtawa kowa shi ba......nasha mafarkinsa tare da ita.....nasha ganinsa a mabanbantan yanayi ya zame mata wata irin qatuwar GARKUWA......ina me yanke shawarar tunkararsa sheikh haisam kai tsaye......akan yayimin alfarma ya karbi auren AKHNAN.....koda bazai zauna da ita na har abada ba,ya cireta daga wannan cakurkudadden yanayin har zuwa sanda komai zai lafa,har zuwa sanda akhnan zata gane kanta.....har zuwa sanda zata fahimci WACCE RAYUWA TAKEYI.....fahimtar da sultane dama karbar yanayin shine yafi komai sauqi a gurina,don nasan tabbas shima yana burin mallakar suruki irinsa....."
Duk yadda falaak taso ta hana kwanukan hannunta rawa amma ta gaza......ta gaza tsaida rawar da hannuwanta keyi wanda ya warwatsu har xuwa sassan jikinta. Ta kasa controlling komai,har zuwa sanda tea tray din ya subuce mata ya kuma tarwatse a qasa,qararsa kuma ta qara adadin razanin da takeji cikin kwanyarta,saita saka tafin hannuwanta tana danne kunnenta saboda yadda taji girman sautin yana mata yawa cikin kwanyarta.
Bakin qofar suka kalla su duka biyun,morsa safiyya da hankalinta da kuma tunaninta yake a wajen ta zubawa falaak idanu. Wani abu ya harba a qirjin morsa safiyya,can qasan zuciyarta ta fara yiwa Allah magiya da ya taqaita faruwan komai.
Hairaan kam da batasan dawar garin ba ta soma magana cikin fada fada,don faduwar kayan a bazata ya tsoratata.
"Mene haka falaak?,wanne irin shashanci ne wannan?,daukar tray ma kawai kada kicemin baki iyashi ba". Bata iya amsawa tantee hairaan din ba,don ba ma fahimtar abinda take fada takeyi ba. Juyawa kawai tayi tana burin barin gurin kafin takai ga faduwa a gaban momma. Batasan rauninta ya bayyana a gaban momma din,muddin ya bayyana ba zata iya boyewa momma komai ba. Ta sani zata iya fighting akan batun,ba zata iya jurewa ba,saidai kuma sautin momma din shine abinda ya katse mata hanzari.
"Zonan ke falaak,ba magana ake miki ba?" Ta fadi da kaushin harshe sosai. Batason ta wuce bata amayar mata da abinda ke cikinta da zuciyarta ba. Tanaso ta san mene ainihin abinda yake zuciyarta......tanason ta tabbatar da gaskiyat zarginta,idan har ya kasance haka kuwa,to lallai zata taka biriki wa tunani da hangen falaak.
Qafafunta na hardewa guri guda ta qara so gaban momma ta durqusa.
"Me ya sameki?" Ta sake cusa mata tambayar tana dubanta.
"Kada ki tambaya momma....kada ki tambaya" Ta fadi muryarta na wani irin rawar dake nuna kuka yana dab da qwace mata.
"Ki fadamin falaak nace!" Momma ta furta a tsawace. Tasan halinta sarai,idan ba hakan tayi mata ba bazataji komai ba!. Tanaso taji komai tunda wuri.....tanaso ta yiwa tufkar hanci tunda wuri.
"Ki fadamin!" Ta sake tursasata a tsawace.
"Inasonshi momma......ina sonsa,don Allah karkiyi yunqurin hadasa da kowa" Falaak din ta furta kanta tsaye kuka yana qwace mata,idanunta cikin na momma din.
Sosai momma ta zuba mata ido,qirjinta yana bugawa,bataso haka ta kasance ba.....bataso wannan amsar bace zata fita daga bakin falaak ba,to amma ta shirya sadaukar da farinciki kowa saboda daidaita rayuwar akhnan.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 63*
"Inda ya halasta ya hadaku ku biyu zanyi qoqarin hakan ya kasance ne falaak......amma tunda hakan baixo cikin halastaccen nassi ba dole ki haqura ki barwa 'yaruwarki!!!.....dole ki cireshi daga zuciyarki....daga rayuwarki!!!....dole ki sadaukarwa da akhnan shi.....ta fiki buqatarsa!!!.....ta fiki buqatarsa!!!" Momma ta fadi da wani irin zafi na tausayin falaak dake qona duk wani sashe na zuciyarta,saidai tana ji a ranta ya zama dole ta gwadawa falaak qarfa qarfa,ya zama dole ta gwadawa falaak bata tausayinta.....ya zama dole ta gwadawa falaak bata tare da ita don ta ceto JININ SAFEENA.
"Momma....." Falaak ta kira sunan morsa safiyya tana jin kamar zata rasa wani sashen ne na jikinta.
"Banaso ki sake cewa komai falaak.....bana buqatar ki roqeni koki nemi canza hukunci na". Tsam kawai falaak din ta miqe,tasan cewa tunda har morsa safiyya ta fadi hakan ba wani abu da zai canza mata magana. Harhada hanya kawai takeyi,tana jin kamar zata suma kafin takai ga isa dakinta.
Da wani irin narkakken tausayi hairaan ta maida kallonta ga morsa safiyya.
"Amma momma......" Hannu ta daga mata tana qoqarin narkar da tausayin falaak daya tsaya mata a wuya.
"Kibi kawai hairaan,karki sharhi ko fashin baqi" Kai take jinjinawa hairaan din.
"Na fahimta momma.....na fahimta,kuma gaskiya kike fadi,akhnan tafi falaak buqatar haisam.....duk da cewa ita din batasan darajarsa ba.....ta yaya zaki fahimtar da ita?....falaak kuma still tana buqatarki,don Allah karki tsaurara mata da yawa". Jikin morsa safiyya a mace take duban hairaan.
"Bazan tsaurara mata ba hairaan,nasan wannna ciwon,nasan ciwon kubcewar abinda kakeso.....amma idan na riga falaak saukowa ba lallai na samu abinda nakeso ba,inaso ta aminta da kanta zatayi sadaukarwa.....inaso ta fahimta 'yar uwarta ta fita buqatarsa...." Saita dakata tana sauke numfashi.
"Akhnan ba.......ba zata taba fahimtar muhimmancinsa amfaninsa ko gata da akayi mata dashi ba sai a nan gaba.......na gama shiryawa da karbar dukkan wani abu da zata kalleni dashi hairaan......ki dafamin kawai a inda kikaga zan gaza"
"Na miki alqawari momma......sai inda qarfina ya gaza" Hairaan din ta furta tana dora hannunta saman na momma. Wannan hali.....wannan dabi'ar,wannan soyayyar da momma kewa shaqiqiyarta ya sanya itama ta tashi da qaunar 'yan uwanta,falaak da akhnan. Duk da kasancewar akhnan din me baudadden hali....duk da kasancewarta wadda ba jituwa tsakaninsu,amma wannan qaunar wannan soyayyar babu wani abu da zai canzata.
*_DARE MAHUTAR BAWA_*
Lokacin da gidan ya soma kaurewa da tashin hankalin ganin wutar da ba'asan daga inda asalinta ya kunnu ba......a daidai wannan lokacin ne shi kuma yayi nisa cikin killataccen dakin ajiyar mammina din.
Wani irin guri ne me sarqaqiyar da bai taba tunani ba,saidai yayi amfani sosai da salon irin qwarewar daya cikin NISS ya soma karantar gurin ta qaramar na'aurar daya cilla a ciki me kama da qwaro. Tun a sannan ya gama karantar taswirar gurin,ya kuma karanci irin na'urorin da aka zuba cikin duhun gurin kawai don bashi tsaro.
Kowacce na'ura idan ya juya bayanta da na'urar daya sanya a ciki din sai yaga ba wani aiki bane me wahala a kanta ba,don haka cikin kwanciyar hankali ya sauyawa kowacce na'ura fasalin aikinta kafin yakai ga shiga.
Abu daya ne daya dauki hankalinsa,har zuwa sanda ya shiga gurin yakai qarshensa baiga wani abu daya da zai iya kamawa a matsayin abun zargi ga mammina ba,baiga koda wata alama qwalli daya da zai bashi haske ba. Dukkan wani tunani da yakeyi na samun komai daga cikin dakin ya yanke.
Da hanzarin da bazai baka daman jin motsinsa ba yaci gaba da duba komai a gaggauce,gaggawar data cakuda da nutsuwa gudun kada ya bada wata alama ko sauti.
Tas ya kammala amma bai samu koda takarda qwaya daya ba. Yayi tsaye a Tsakiyar dakin,ya sake daga hannunsa yana duban agogon dake tafiya daidai da nasu beeno dake daure a hannuwansu,wadanda ke cikin mutanen dake qoqarin tsaida wutar,wasu daga cikinsu kuma suna kewaye ne da gurin cikin duffan bishiyoyi suna masa gadin hanyar.
Murza agogon yayi,ya qara mintuna goma akan mintunan da suka tsara da farko,yayin da sautin alamun qara lokacin ya isa ga agogon kowa,suka kuma fahimci me yake magana akai duk da bai furta kowacce kalma ba.
Hannayensa daya riqe qugunsa dashi ya sauke,haka kawai cikin jikinsa yakejin bai gamsu da cewar ba komai a dakin ba....zuciyarsa da gangar jikinsa dukka basu nutsu ba,sai ya waiwaya yana sake duban bangon qarshe na dakin.
A hankali ya zame kallonsa zuwa qasan dakin,soma lissafa adadin jajayen duwatsun dake iya bangaren yayi,wanda duka duka fadinsa bazai wuce na babban faranti ba. Ya sake maimaita irgen,yana comparing da adon cycle din dake kusa da wajen.
Akwai banbancin duwatsu jajaye goma a gurin,abinda yaja hankalinsa,ya soma takawa a hankali yana kusantar gurin.
Tsugunnawa yayi,yakai hannunsa ya shafa,ga mamakinsa wani shocking yaji a yatsunsa,sai ya dauke hannunsa yana kallon gurin sosai.
Fes komai ya dawo masa kansa,salon kebantaccen gurin ajiya na qarqashin qasa da tsofaffin sarakunan qasar Ethiopia keyi don adana muhimman bayanansu koda yaqi xai cimmasu. Wani qaramin murmushi ya subuce masa,yana tuna yadda ya cire shocking a daya daga cikin wasu gurare da suka taba shiga don yin bincike,sai ya cire jakar bayansa ya ajiye,ya koma soma lalata tsarin tsaron gurin.
Yana kammalawa gurin ya soma matsawa,yasa hannunsa ya qarasa matsar dashi gefe,take wani abu me kama da akwatin qarfe me zubin zinare ya bayyana. Shi kansa bai samu damar budeshi kai tsaye ba sai daya lalata zubinsa,bisa yaqinin zai iya maidashi kamar yadda yake.
Sannu a hankali ya fara fiddo da takardun bayan ya ture wasu nau'ikan gold dake zube saman takardun. Daya bayan daya yaci gaba da fito dasu yana karanta bangon kowanne file kafin ya ajiyeshi a gefe.
Sannu sannu qafafunsa yaji sun fara masa nauyi,kaman ba zasu iya daukarsa ba. Wani irin tsananta bugu zuciyarsa ta fara yi sanda ya soma cin karo da takardun da suka fara fayyace masa WACECE ZAITUNA sannan kuma WACECE ZEENATU.
Wasu irin bayanai da yayi imanin bacewar basira ce ta sanya ta binne komai a guri guda a muhalli guda ba tare data rarraba gurin ajiyar bayanan ba.
Katin daurin auren dake tsakiyar takardun yakai hannunsa yana budeshi a hankali. Sunanta ne da manyan rubutun da akayishi da yaren gumma......da kuma manyan sunayen AHMADE AJANI daga sama.