L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 37
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 37: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 37. Wani irin iska me zafi ya fessr,zuciyarsa ta fara wani…
3,307 words
Wani irin iska me zafi ya fessr,zuciyarsa ta fara wani irin kumbura. Ashe dukkanin hasashensa ba wani da yayishi ba daidai ba?......
"Zeenatu.....ZAITUNA" Ya maimaita sunan a fili,sannan ya miqa hannunsa yana zaro wani file gami da komawa gefe ya zauna tamkar ya manta lokacinsa qayyadadde ne.
Dairy ne.....diary din mamminan data zauna ta rubutashi da hannunta cikin cikakken yaren oromo da babu algus ko kadan a cikinsa.
∞∞★ Cikin wani irin zafin jiki dana zuciya yake kaiwa da kawowa cikin bedroom din nasa.
Komai ya lafa,gobarar ta dakata kamar yadda yaso,bata kuma ci wani abu me yawa ba sai tarin hayaqin data turnuqe masarautar dashi. Sunyi aiki me kyau dukkaninsu cikin tarin qwarewa da gogewar da suka samu qarqashin *obbo muhammad haisam,code name dinshi na gurin aiki AL-SAAMIT(THE SILENT ONE)* Tinjimin aiki cikin yanayi na nutsuw kamewa da yin shuru,saidai yakan fidda sakamakon da yake qarawa NISS daraja martaba da daukaka a duk sanda ya kammala wani operation nasa,wannan ya sanya ya fita da wannan sunan cikin code name da ake bawa kowa a hukumar.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Yasan komai ya tafi daidai,tunda a nutse ya kammala bincika dukkan abinda zai bincika din,sannan ya maida komai a muhallinsa kamar ba'a taba komai din ba,saidai kuma ya gaza maida wannan dairy din cikin tarin tarkacen takardun. Tarin lifidi lifidin wasu documents dake dauke da sunan sultane muhammad hammud da kuma sa hannunsa,wasu a ciki kuma suna dauke da suna da signature na khadeeja muhammad hammud qarara a cikinsu,wanda tarin abubuwan da ya gani a rubuce cikin diary din mammina din ya janye hankalinsa daga duba ko zurfafa nazarinsa akam documents documents din.
Yana tattaki ne da wani irin sassarfa daya sake bayyana tsaho fadi da cikar halittarsa ta GIANT MAN,daga bango zuwa bango na dakin. Ko sau daya ya gaza ajiye wayar hannunsa da yaketa maimaita kirawa bobbo muhamamd dawud,ko sau daya kuma ya gagara ajiye diary din mammina dake hannunsa yana sake bin shafi bayan shafi yana karantawa.
Mamakin tarin qarfin halinta ke sake mamaye zuciyarsa da wani irin bacin rai masa misali. Har rashin imani rashin mutunci da zallar izgilancin dan adam yakai ya zauna ya rubuta tarin rashin imanin da ya aikata a rayuwarsa?. Har yakai ya zauna ya rubuta tarin alwashinsa akan rayayyu da matattu?. Iya littafin kawai yana jin ya isheshi hujja......ya isa dalilin da zai kama mammina a safiyar gobe cikin masarautar ya kuma bayyanawa duniya samun nasarar kama me laifin da suka kwshe shekaru masu yawa suna nema.
Bama iya laifin da suke hasashe bane kawai........ta dauki rayukan wasu mutane daban da bincike ma bai taba biyowa ta kansu ba. Kawai don ta kashe bakin munanan ayyukanta,kawai don ta rayu yadda takeso,kawai don taci gaba da wanzar da umarni da kuma mulkar kowa cikin wani irin SHURU da ma'abota zurfafa tunani da bincike ne kawai zasu fahimci hakan.
Iska ya kaiwa naushi a sanda kiran daya yiwa bobbo muhamamd dawud ya sake katsewa,wannan kiran shine kira na ashirin da takwas da yayi masa. Yanajin kamar zuciyarsa zata fashe ne,yana jin kamar ana jan jininsa ne,so yake kawai ya samu bobbo,so yake kawai yayi accepting ya bashi daman cafke mammina. Yanajin ma kamar safiya tayi masa nisa.......yana jin kamar yayi nisa ya jirayi safiya. Ta cutar da kowa.......ciki harda nanay dinsa. Ashe itace sila na barin nanay dinsa cikin wani irin yanayi......yanayin da a kullum ta tashi a cikinsa su kansu wunin ranar baya musu dadi. Ta kife sultane ta binneshi yadda ya kamata,bama sultane kawai ba......duk wani dake rayuwa cikin masarautar a binne yake,duk wanda yake rayuwa cikin masarautar yana qarqashin sarrafawarta ne,hakanan duk wanda yake rayuwa cikin masarautar rayuwarsa cikin barazana take.
SHURU da masarautar take ciki da ake masa kallon aminci......ba aminci bane......HADARI NE......wannan shurun ba ZAMAN LAFIYA BANE annoba ce......wata kwantacciyar annoba da ba wanda ya farga da wanzuwarta.
Cilli yayi da wayar yana cusa yatsunsa cikin gashin kansa,ya furzar da wata zazzafar iska daga bakinsa yana sauke idanunsa akan tarin document din da yayi snapping a wayarsa ya kuma dawo dakin ya fiddasu zuwa hardcopy ta wata mini printer ta masu aikin tsaro irin nasu.
Kafin yayi kowanne tunani akai kira ya shigo wayar,taku uku yayi cikin zafin naman nan na ingarman namiji ya isa ga wayar,ya miqa hannu ya dauka yana danna gurin amsa kiran da gaggawa ganin bobbo ne.
"Ina ka shiga bobbo?" Ya samu kansa da furtawa abu na farko. Mamaki kadan ya kama muhammad dawud,don ya sani,komai tsanani sallama itace abu na farko da haisam yake fara yi kafin komai bayan daga wayarshi.
"Muhammad mun shiga masallaci ne nida sultane......sai yanzu muka fito"
"Mission accomplished sir!" Ya furta da wani irin yaqini a muryarsa,zafin rai da kuma qwarin gwiwa dari bisa dari.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 64*
"Alhamdulillah" Bobbo ya fadi,yana jin wani abu me sanyi yana ratsa zuciyarsa. Wannan wahalar......wannan aikin na shekara da shekaru yau an kawo qarshensa.
"Izini kawai nake buqata daga gurinka obbo muyi arresting nata,zuwa safiyar gobe ko kuma daren yau".
" Zakayi hakan Muhammad da hannunka,zaka huce wahalarka gaba daya......but,inason wani yanki kadan daga hujjojin da ka samu zan duba kafin na sake maka dama".
"Done" Ya fadi yana katse kiran,sannan yayi snapping wasu daga cikin takardun ya tura masa.
Tsaye yayi harde da hannunsa a qirji,ba abinda yake imagination irin yadda zai shaidawa nanay dinsa ya kama azzalumar data raba soyayya da qaunarsu da 'yan uwanta na jini......ba abinda a duniya a yanzun yake buri irin Allah ya ara masa numfashi na wadannan awannin da zai kama mammina ya kuma damqata a hannun hukumar tsaro na Ethiopia. Ko a iya haka idan ya tsaya ya tabbatar yaci ribar aiki da security service. Wani irin zugi zuciyarsa take masa idan ya tuna jerin lissafin mutanen data batar wanda ta zauna da kanta cikin alfahari ta rubuta da hannunta. Ashe qeqashewar zuciyar dan adam takai ya iya zama yana tsara zunubinsa da kansa?.
Kiran bobbo ne ya katseshi ya maida dubansa kan wayar da hanzari yana daga kiran.
"Kama matar nan bazai yuwu ba muhammad..... Kamata zai zama abu mafi girma cikin dagulewar case dinnan" Ya tsinci muryar muhammad dawud tana sanar masa da wani mafi munin saqo.
Wani irin abu yaji da bazai tantance mene ba......sam kamar kwanyarsa ta daina fahimtar komai.
"Bobbo......me kake fada ne?"
"Bazaiyuwu ka kamata ba muhammad" Ya sake maimaitawa haisam da karyayyar muryarsa wadda ba irin ta dazu ba kafin suyi magana. Amsar da bobbo din ya bashi sai yaji kamar ya samu wuqa ya karta saman zuciyarsa ne
"Me kake fada ne haka bobbo!......na samu dukkanin hujjoji fa!" Ya fadi da fada da zafin zuciya.
"Muhammad,Tasgabbaa'i (calm down),akwai abubuwan daya kamata ka tattara hankalinka ka fahimcesu".
"Hankalina a tattare yake guri daya bobbo.....na gama fahimtar komai,na kuma gama hada dukkan wata hujja a kanta,ba abinda ya ragemin banda na kamata!,ba abinda ya ragemin banda na kawo qarshen zaluncinta!,.......zan kamata bobbo kamar yadda doka ta tanada,zan kamata wannan ya zama dole!!!" Yayi maganar da zafin dashi kansa baisan a haka yakewa bobbo din magana ba yana me dukan table din dake gabansa,take ya amsa ya kuma tsage daga tsakiyar glass din,Allah ya taqaita bai fashe gaba daya ba da tabbas ba qaramin mummunan ciwo zaiji ba.
Kiran kawai ya katse,don a yanzu baya buqatar duk wani abu da zai dakatar dashi daga kama mammina.......a zafafe ya soma hada connection dasu beeno,yanaso a daren kowa a cikinsu ya zama cikin shiri,da asubar yau din da awanni uku kadai suka rage tayi yakeso mammina ta zama a hannunsu,a gobe warhaka kuma ya tabbatar mammina din tana hannun hukumomi a Ethiopia. Qasar data shuka manya manya laifuka ta kuma binnesu a ciki,ta dawo wani sashe daban na duniya ta samarwa kanta amintacciyar mafaka. Hakan kuma bai mata ba ta sake fesarwa sa baza gubar dake qumshe a bakinta zuwa ga duk wanda rayuwa ta kawoshi kusa da ita.
Da sauri da sauri yake qoqarin hada komai,saidai gefe kansa daya da yaji ya sara,ya sara ne tare da zabge kaso tamanin na karsashinsa gami da gilmawar sunan KHADEEJATU baro baro cikin idanunsa. Sunan daya gani rubuce a documents masu yawa dake gabansa yanzu haka.
A hankali ya saki wayar ya koma gefan sofa bed ya zauna akai. Sai yakejin kamar akwai wani gibi.....kamar akwai wani abu daya kamata yayi baiyi ba,a jikinsa yakejin kamar akwai wani gurbin wani abu.
*MUHAMMAD DAWUD*
Wani irin shuru yayi yana rungume da wayar a qirjinsa. Wani irin tsoron haisam ne yake shigarsa a karon farko. Karo na farkon daya soma ganin tsananin fushi a tare dashi,irin wanda bai taba ganin makamancinsa ba.
Akwai hadari me yawan gaske game da kama matar a yanzu. Idanunsa ya sauke a hankali akan sultane da yake amsa waya,amsa wayar da tayi tsaho,kuma yake ganin wani irin yanayi na tsoro da tashin hankali yana mamaye fuskarsa. A iya saninsa matarsa ce ta kirashi,a cikin matan nasa bai tantance ko wace ba......amma yanayinsa kawai yana gaya masa kiran yana dauke ne da wani saqo na mummunan tashin hankali.
Ya sani koda.muhammad ya shiga fushi irin wannan bazai aiwatar da komai ba saida izini,ya samu wani irin horo na cikakkiyar tarbiyya da bin na gaba. Rank dinsa a gurin aikin,da kuma matsayinsa na PRINCE OF OROMO bai sanya ya zama me take dabi'un musulunci ba nafin na gaba. Saidai yana jin wata shakka a tare dashi,yanayin haisam din na yanzu bai taba ganin irinsa ba,kamar yadda wayar da sultane keyi a yanzu take gaya masa akwai wani mummunan abu daya faru a qasar. Shin har ya zartar da aikin kamata dinne?.
Wannan tunanin ya zaburar dashi,ya soma rubutawa haisam din rubutaccen saqo na kai tsaye yana tura masa. Me yasa haisam ya kasa ganin abinda shi ya hango wannan karan?,baya ga wancan BAQIN QULLIN da ZARGE daya hango cikin daya daga cikin file din daya tura masa......MARTABAR sultane yanzu wani abune daya kamata a dubata. Kama iyalinsa kai tsaye irin haka a wulaqantaccen yanayin daya tabbatar zai zama wani labari dake trending a dukka kafofin watsa labarai na qasa dana duniya gaba daya......zasu bar masa wani tabo da zai iya shafar rayuwarsa ma gaba daya. Duk da cewa aikine zaibi ta kanta,amma zaiso haisam ya bashi aron wannan kamilar tasa nutsuwarsa da wannan zuzzurfan hankalin nasa ta yadda kama mammina din zai zama da tarin hikima.
"Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagees.....aslih li sha'ani kullah.....fala takilni ila nafsee d'arfata ainin" Ya dinga maimaitawa a hankali idanuwansa a rufe.
Gilmawar sunayen sultane kawai yake gani da na akhnan rubuce saman file din,zuciyarsa na nanata masa muhimmanci daukosu ya sake nazarin files din. Kuskure daya tak! Zakayi cikin aikinsu ya ruguza komai......ko ya bawa me laifi hujja ko damar kubuta.
Saidai kuma bayaso ya kalli file din......bayaso ya duba yaga abinda ya zamo doka a aikinsu da zai tilasta masa dakatar da damqe me laifi.
Wayarsa ce ke maimaita masa shigowar saqo me muhimmanci daga bobbo din,dole ya bude idanunsa da suka kada,ya miqa hannu ya dauki wayar yana duba saqon.
"The power of documents abbreviation........" Iya abinda bobbo ya rubuta kenan kawai.
Kamar an masa allura haka yaji,ya ajiye wayar yana miqewa da hanzari zuwa gurin daya ajiye dukkanin takardun,ya kuma zubosu qasa yana waresu daya bayan daya.
Awa guda cur ya share yana nazari,awa gudan data zame masa ta tashin hankali......awa dayan data bashi tabbacin da gaske bobbo ya fishi gaskiya.
Ta kowacce fuska babu hanyar kama mammina kai tsaye irin kamun da yake buqatar yayi mata. Tako ina ta qulla rayuwarta ta gaba da sunan akhnan,signature din akhnan duk da baisan ainihin signature dinta ba......da muma stamp din akhnan din dake dauke baro baro da sunanta da kuma title dinta AGADEZ PRINCESS. Ta qulla dukkan wani zare na rayuwar da tayi a baya da SULTANE......sultane din daya kasance aboki ga marigayi AJANI.
Sa hannun sultane caba caba a tarin yarjejeniyar kashe ajani. Stamp dinsa mafi tsaro da girma daya tabbatar iya warwareshi kadai wani abu ne da zai dauki wasu shekaru ana magana a kanshi.
"Hasbi rabbi!" Ya furta a bayyane da wani irin rudadden yanayi yana dukan table din a hankali. Ta kowacce fuska,ta kowanne yanayi ta qulla rayuwarta da mutum biyu,sultane da babbar diyarsa,tayi wani irin qulli da idan ta tashi faduwa ba ita kadai zata fadi ba.......idan ta tashi rugujewa ba zata zagwanye ita kadai ba. Faduwarta daidai yake da faduwar sultane,zubewar kima mutunci da martabarsa. Sa'annan kuma daidai yake da wulaqanta image na babbar d'iyarsa. Zata rasa tarin kima.....zata rasa girmamawa zata rasa dukkan wata martabarta. Duk wata dukiya da take mallakinta zata saraya daga hannunta,zata fuskanci mafi munin wulaqanci da tozartarwa.
Document of abbreviation din da bobbo ya fara magana a kansa ya dauko ya bude yana masa filla filla.
Wani sabon babban tashin hankalin ya soma gani......komai na mammina ya canza,ta tashi kacokam daga haifaffiyar Ethiopia ta koma haifaffiyar qasar NIGER. Komai ya canza.....komai ya tashi daga ainihin yadda yake.
Girman abubuwan daya gani ya sanya yaji kansa gaba daya ya dauki wani irin dumi,saidai kuma bai hana bakinsa da zuciyarsa kiran sunan Allah ba. Abu guda daya yayi,ya fidda wayarsa ya turawa obbo saqo a taqaice,don yanaji a jikinsa cewa yana buqatar yayi quitting.....yanaso ya yanke kowa da komai na wani dan lokaci ko kwanyarsa zatayi kalar tunanin daya dace tayi.
_"I found her crime....i lost her name,she's no longer Ethiopian under the law,touching her will would ignite a diplomatic fire"_ abinda ya turawa bobbo kenan ya kashe wayarsa.
Wani sashe na zuciyarsa yana son gaya masa KAYI FAILING MUHAMAMAD?,wannan jarumar zuciyar tana qaryata hakan.
A karan kansa yakejin BAI FADI BA.....bai kuma gaza ba.....a cikin kansa da zuciyarsa yakejin kawai wani strategy sabo yake buqata.....a gangar jikinsa yakejin akwai sabon GAME da zasu buga tsakanin K'ARYA da GASKIYA......wani sabon shimfidadden babi ZAI BUDE kansa da kansa yanxu. Bai gaza ba......bazai kuma gaza ba......bazai kuma tafi yabar agadez ba sai da NASARA....bazai matsa daga agadez ba sai ya cika wannan alwashin......wannan alqawarin......wannan BURIN.
*_NATIONAL INTELLIGENCE SECURITY SERVICE TEAM (AGADEZ_*
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Dukkanin team din dake qarqashin jagorancin Senior Field Intelligence Officer sannan kuma Deep-Cover Operative me dauke da Code Name na Al-Sāmit (The Silent One) PRINCE MUHAMMAD HAISAM ABBA JIFAR. Cikin anihin kebantaccen gidannan nasa dake dake cike da jami'an tsaro daki daki ta kowacce fuska,ta cikin gidan,ta kusa da gidan,da kuma ta nesa da gidan.
Amintattun jami'ai da dukka suka samu horo ta hannunsa,ko sau daya basa wani motsi da zaibar zargi a zuciyar wanda ke rayuwa ma kusa da gidan ballantana cikin unguwar.
Parlor ne na alfarma dake zagaye da wasu irin lafiyayyun sofas dake nuna zallar izza da mulkin dake tattare da mamallakin gidan,saidai a yau a safiyar da ya wayi garinta a daren jiya ba tare da ya iya baccin komai ko kuma runtsa idanunsa ba......an canzawa parlor din fasali kadan ta hanyar rarraba kujerunsa,aka kuma ajiye qananun table gaban kowacce kujera.
Tun daga kan omari har salawi,beeno,abeer dama dukkan wani ma'aikaci da shigowarsa agadez ta ta'allaqa ne da gabatar da wannan aikin,dama sauran jami'ansu da suka jima cikin qasar saboda fara gano muhimman gurare a qasar.
Wani irin shuru ne ya ratsa dakin,banda qamshi da tururin coffee dake sake bayyanar da cewa lallai qabilar oromia ne wanze a gurin.....qamshin coffee din daya gauraya da qamshin sassanyan freshener din data kama parlor din,da kuma sirrintaccen turaren oga me gayya me aiki muhammad haisam.
Duk qaunarsu da coffee din a yau kowa nashi yana aje ne a gabansa kawai,takardun hannuwansu kowanne yake juyawa cikin zurfin tunani,mutuwar jiki da daurewar kai,yayin da haisam din ke kai kawo a tsakaninsu. Sanye da wani lafiyayyen trouser da long sleeve shirt,shigar da ba kasafai ya fiya yinta ba a yau din yadda yakejin zuciyarsa fayau sai shigar ta sake masa wani irin kyau,ta fidda kyawunsa da quruciyarsa qarara,har abdii ma yaso tsokanarsa da farkon shigowarsu gurin,saidai yanayin daya gani tattare dashi na seriousness ya sanya ya kama bakinsa ya b'ame.
Hannunsa daya yana soke a aljihun wandonsa,yayin da daya hannun yake riqe da qaramin cup yana sipping coffee dinsa a hankali,kamar yadda kowanne taku nasa yake cike da nutsuwa,har ya kawo gaban table din Omar ya zuqe sauran coffee din ya ajiye mug din akai sannan yaja baya kadan.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 65*
Gyaran murya yayi wadda ta sanya kowa ya tattara hankalinsa a kanshi,fuskarsu cike da damuwar da yana iya ganinta qarara a bayyane. Cikin muryar nan da sautin nan nasa dake bayyana asalin abinda ake nufi da kamala da nutsuwa ya soma musu magana yana duban fuskokinsu daya bayan daya,da wani irin accent da yaren oromo ke dashi wanda yake kama da harshen fillanci a nigeria.
"Waan hunda jijjiirte(she changed everything),Ta canza sunanta,shekarun haihuwa da komai da zai nuna ita din mallaki n qasar Ethiopia ce,tana da cikakken takardu da shaidar da zata bada tabbacin bata taba rayuwa a Ethiopia ba sam sam,dukkan takardunta kuma sun nuna ta halastacciyar hanya ta samesu. Ta samu sanya hannun manya dake da ruwa da tsaki akan kowacce takarda,tayi qoqarin samun shaida da lambar yabo iri daban daban na cewa ita din mutuniyar kirki ce,mutuniyar arziqi ce.....shaida da lambobi masu tulin yawa,ba a iya niger kawai ba,harda Nigeria dama maqwabtan qasashe dake kewaye da qasar.....ta shafe duk wani jini ko suna na Ethiopia daga gareta,ta yiwa kanta garkuwa da dokar da mukeso tahau kanta.....ta lullube kanta da tarin martaba da kariya ta gidan sarauta......da kariya da kowacce matar SULTANE take da ita. Tana cikin mata masu daraja da kamasu xai iya zama wani babban abun Allah wadai ga qasarmu,zai iya kuma canzawa aikinmu suna da ma'ana gaba daya,za'a kalli abun gaba daya a matsayin wulaqantarwa da tozarta da SARAUTA.....The law has already failed once. I must let truth speak instead.” ya qarasa fadi yana duban fuskokinsu muryarsa tanayin qasa sosai.
Kallon nashi dai sukeyi daya bayan daya,kalamansa na qarshe suna sakasu cikin kokwanto. Dan murmushi kadan ya saki yana goye hannunsa a baya yana ci gaba da takawa a hankali,yana kuma ci gaba da dubansu. A nutse ya sake dora maganarsa cikin qarfafa gwiwa.
"Kun gama aikinku kun cika wa'adinku,ina me sanar daku cewa,kowa a yanzun yana da 'yancin komawa qasarsa.....ni muhammad haisam zanci gaba da daukar nauyin aikin a wuyana da dukkan iyawata da qoqarina......dole wasan zai sauya salo,zai kuma zuwa wani YAQI na daban,bawai binciken me laifi ba.....zan sadaukar da numfashina ga qasata,zan bada rayuwata ga qasata......You're good to go You're free to leave All set! You all did an amazing job,perfect score!.i owe you one!.....well done!!!" Ya furta yana daga hannunsa alamun jinjina a garesu gaba daya,wani siririn murmushi na qarfafa gwiwa a garesu gaba daya yana fita daga saman fuskarsa.